Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta k0 ina harabar gidan maza ne, tana dawowa dinning table ta 'nufa ta karya sannan ta mike ta koma bedroom dinta ta'nufi bandaki ta watso ruwa ta fito ta sakawata ‘yar sassaukar doguwar riga, sannan ta yi sallar azahar tana gamawa ta fito ta sauko falon qasa ta kira Mansura kukunta, wadda ke shirya abincin ‘safe dana rana, sai Emanuel shi ke dafa na dare. 'Mansura yarinyar ce wadda ba za ta wuce shekaru' ashirin da biyu ba, musulma ce amma ba bahaushiya ba, tana dai jin Hausa sosai, ‘yar asalin , qasar Ghana ce, Saudat ta yaba da girkinta don tafi Emanual iyawa, don haka ta kira ta don ta fara koya jama,a waishin ina yaya rabiu ne?zai dawo ko bazai dawoba? wani saqo ya bama inna mai danwake ta bama saude?meya faru dashi bayan malam bala ya sake masa korar kare daga gidansa a karo na biyu? amsar tambayarku na cikin YAR TALLA CHAPTER35 wanda zan kawo muku gobe idan mai sama ya nufemu da kaiwa kuma yasa ina numfashi naku mai qaunarku mai sonku har cikin ransa qaninku kuma abokinku YAR. TALLA THE END QARSHE CHAPTER35 ASHA KARATU LAFIYA mata. A yau inda aka fara da yadda ake sarrafa shinkafa, tunda suka shiga kicin sai karfe hudu na yamma suka fito Saudat ta nufl sashinta ta yi sallar la’asar. Dr. bai dawo gida ba sai sha daya da ‘yan mintina na dare a lokacin har Saudat ta. gaji da jiransa ta kwanta, don haka ya ajiye mata tsarabar da Momy ta bada a kawo mata, sannan ya fice ya koma bangarensa. Saudat ba ta samu ganin tsarabar tata ba sai da gari ya waye, bayan ta gama shirinta cikin Wani tsadadden materiyal ruwan zuma mai sulbi wanda aka yi wa dinkin riga da siket, matiriyal din ya haska ta sosai. Ta fito falon a nan ta yi karo da ledojin, ta zauna ta zubesu a falon tana duddubawa duk_ kayan girke-girke ne irin na Kasashen larabawa, sai wata hadaddiyar sarka ta azurfa wadda aka yi wa yarfin gwal a cikinta, sarkar ta yi matukar burge Saudat, ta tattara kayan ta maida kicin sannan ta dauki sarkar da yan kunnayenta ta makala, ai kuwa sun yi mata matukar kyau, sun haska ta fiye da wadanda ta fara sakawa daga farko. Ta nufi falonta ta karya, ra mike ta nufi Bangaren maigidan nata don yi masa sannu da zuwa ta kuma jin tadda ya samu Momy din da su Nabil da kuma Nabila. , Tana taka matattakalar dazata'sadatada falonsa sai ga Asma kuma na saukowa.‘ Gabanta ya yi wata mummunar faduwa, kallo daya ta yi wa ,Asma ta dauke idanunta ba tare da ta nuna ta ganta ba. Asma ta bi Saudat da wani razanannen kallo, zuciyarta na wani irin tuquqin baqin ciki, ji ta ke tamkar ta shakaro Saudat har sai ta mutu, hakan ya sa ta lumshe idanunta ta ci gaba da saukowa daga matattakalar bench tana kiran sunan Allah kamar yadda Ahmad din ya vata shawara. ‘ Saudat ta yi matukar mamakin yadda suka hada hanya da Asma salin'alin,to k0 ta fara saukowa me? kai da wuya don irin kallon da ta ga ta watsa mata babu komai a cikinsa bayan tsagwaron tsana da ‘ qiyayya, Saudat ta taho dakin tare da murda Kofar falon maigidan ta shiga da sallamarta. ~ Yana kwance saman gado daga shi sai short ‘ niker riga a jikinsa, ya dora ipad saman ’ kirjinsa yana lallatsawa, yana ganinta ya ture ipad din tare da miqewa tsaye ya rifito ta yana fadar, “Kun hade da Asmako? Allah yasadai bata miki irin haukan nataba?” ~ Saudat ta girgiza masa kai cikin sanyin jikinta. Ya shafi fuskarta yana fadar, “Allah har gabana ya fadi". ‘ Ya zaunar da ita saman gadon shi kuma ya zauna a Kasa yana fadar, “Jiya na dawo na sameki kina ta bacci, kin yi adalci kenan mijinki yana kan 'hanya amma har ki iya runtsawa ba tare: da kin kira ni kin ji ko na isa lafiya ba? Kai Saudat anya kin damu dani kuwa?” Saudat ta langwabe kai tana fadar, “Allah fa na kira ka ta Ki shiga Ya kada kafada tare da fadar “Allah ya sa da gaske ki ke”. Ta dan yi murmushi tare da fadar “Ni na zata fa zanzo in sameka kana shirin tafiya ne Ya girgiza mata kai, “Jirgin Karfe hudu ai zan bi na yamma, k0 kayan ma da zan yi tafiyar dasu ban hada ba” Ya langwaBe kai, “Allah ji nake tun yanzu harna. fara missing dinki my baby bacin karatunki da ba abin da zai hana na tafi tare da ke”; ‘ Saudat ta lumshe ido ta bude saboda yadda maganar tasa ta yi mata dadi, ta mike tana fadar, “Bari na hada maka kayan” Ya ce “Yauwa tawan, da kuwa kin kyauta” Saudat ta nufl bedroom dinsa inda ta samu duk ya wargaje shi komai ya yi watsawatsa Ta girgiza kai cike da takaicin yadda har ya iya rikita dakin baccin nasa haka. Ta kada kai, ta soma gyara masa tare da mayar da komai a muhallinsa, ta cire bedsheet dinsa ta canza masa sabo, ta gyara dakin ya dawo yadda ya kamata, ta dauko boner ta zuba turaren wuta ta jona a dakin. Nan da nan ya soma. fitar da wani sanyayyen kamshi * Ta nufa wurin ma adanar kayansa da takalma ‘ (walk and closed) budadde mai girman gaske, an jera komai a indayadace, Saudat batayi mamakin ' yawan kayan nasa ba k0 daga yadda ta lura bata taba ganin ya maimaita kaya ba. Ta dauki wani jakar kaya ’ trolley bag ta zuge ta ta soma shirya masa kayan a ciki komai set ta kce hadamasa‘ don ta fahinci maigidan nata ya yarda da tomarch. Asma kuwa da kyar ta iya kai kanta bangarenta saboda bacin rai da zafin kishi, kuka ta ke sosai, tabbas Ahmad ya wulaqantata, ya qaskantar da ita, wai yau ita ce ya hada kishi da ‘yar aikinta, ‘yar * matsiyata, yarinyar da ta ke gani daKiKiya, mara ~ ilimi, kuma ‘YAR TALLA! 'Tabbas Ahmad ba qaramin wulakantata ya yiba a idon duniya, wai a ce kamarta mijinta ya auro ‘yar aikinta, wannan wane irin cin fuska ne? Ta suri makullin motanta ta fice dAga gidan tana faman shar barkwalla tamkar za ta tashi sama haka 'ta ke tuqin don haka cikin Kankanin lokaci ta iso ‘Ministcr’ Quarters, maigadi na bude mata qaton gate . din gidan ta kutsa motarta, bata tsaya gyara fakin ba _ ta tsaida motar ta flce a guje ta nufi cikin gidan Hajiya Zakiya ita ce mahaifiyar Asma, ita ke nan tilo Allah ya basu mahaifinta kuma bai yi ’ shekara da rasuwa ba. sakamakon hadarin jirgin da ya, _ rutsa da shi a kan hanyarsa ta zuwa qasar Uganda bayan shekara biyu da ‘yan watanni da auren Asma Allah ya yi masa rasuwa. Asma ta shigo falon mahaifiyar tata wadda ke tsaye a gaban dinning table tana jera kulolin abincin rana ita da ‘yar aikinta, Asma ta fada jikin Umman tata ta rungume ta tana kuka mai daga hankali. Hankalin Hajiya Za'kiya ya yi matukar tashi, ta ruKo ta tana fadar, “Ke Asma lafiyarki? Me ya faru ne? Yau na shiga uku ni Zakiya Ta bambare ta daga jikinta tareda janta cikin falon ta zaunar da ita kan kujera, ta dauko ruwan tambulan mai sanyi ta mikamata, "‘Karbi ki sha don Allah zuciyarki ta yi sanyi’ Ta karBi ruwan ta soma sha, Hajiya Zakiya ta juya kan mai aikinta a fusace 'tana ‘fadar, “To ke kuma uban me ki ke jira ki ka yi mana tsaye a ka?” ‘Yar dattijuwar ta rusuna, “ yi hakuri Hajiya”. Sannan ta juya ta yi gaba jiki na rawa. Hajiya Zakiya ta raka ta da harara kafin ta maida kallonta a kan ‘yar tata ‘wadda ta kurbi ruwan ta hadiye da kyar tamkar ta kurbi madaci‘ _ Hajiya Zakiya ta dafo tana, Fadar me ya farune?” Asma ta sa bayan hannu tana goge hawayenta _‘ Cikin ‘muryar kuka ta soma fadar, . umma wlh zuciyata tarwatsewa zatayi bazan iya a gidan Ahmad ba, baqin ciki kashe ni zai yi ldan :naci gaba ‘ da zama a gidansa, Umma 'Ahmad ya wulakanta ni, ya tozarta ni na rantse da Allah na hakura da aurensa, ba -. dan bazan iya zaman Kaskanci ba. ..” Kuka ya ci qarfinta tamkar wadda aka aiko wa da sakon muntuwa. Hajiya Zakiya ta ja tsaki kafin ta ce “Amma wallahi Asma kina bani kunya, yanzu ke ba abin kunya bane a zo a iske ki kina kuka a kan da namiji da, kyanki da yarinyarki da komai ke k0 ni da make tsohuwa ba zan iya tsayawa namiji ya ci kashi a kaina ba tare da na nuna masa bambanci tsakanin ruwa da hawaye ba. Haba sma Ahmad din banza da zaki zauna yana wulakata ki a banza tun lokacin da ya bijiro da‘maganaar zai auri ‘yar aikin gidanki na ba ki shawara ki .bar masa gidansa inyaso ya biyo ki da takardarki amma sai kayi kunnen uwar shegu dani, ke ga ki mai miji, yo namijin banza kayan amai ma don zuciya ta ki tashi ba za ki barshi ba? Yo namijin me Allah na tuba? Ke kin san k0 sakinki Ahmad ya yi ba za 'a kwashe kwanaki ba tare da maza sun soma ’ go slow a kanki ba. Ki duba yadda Allah ya yi miki "” baiwarkyau, haba Asma sai ka ce ba ki duba madubi, ga maza nan birjik a gari sai kalar wanda ya yi miki amma ki maqalewa namiji guda kamar gam, sai ka Ce ba Asmar da ke cudanya da maza ba a kan lamarin siyasa, haba don Allah don Annabi ki rabu da yawonan. nan, ya sake ki haka nan k0 dole ne za ki zauna namiji yana qaskantar da ke ya bata miki suna a gari don kawai ya lura kina sonsa, ba ki iya rabuwa da shi kamar wadda aka yi wa asiri, haba don Allah don Annabi Asma ki guntile ,wannan Kaskantaccen auren naki don ban ga amfaninsa ba. . .” Asma ta zame daga rikon da Hajiyartata tayi ‘ mata ta kwasa da gudu ta yi Bangarenta wanda ta yi rayuwar ‘yan matancinta a cikinsa. Hajiya Zakiya ta raka ta da idanu cike da takaici idan akwai abin da ta tsana bai wuce Bacin ran ‘yar tata ba, k0 kadan ta tsani abin da zai Bata wa ‘yartata, ta ja tsaki ta dauko wayarta a gefen kujera ta danna wa sirinkinta kira. A lokacin yana zaune kusa da Saudat suna cin abincin rana, ya dauko wayar ya rusuna tamkar yana gabanta, ya soma gaishe ta. Hajiya Zakiya ta dakatar da shi ta hanyat fadar, Dakata ba gaisuwarka nake nema ba, ka gane ina gida ina jiranka ka iske ni da takardar sakin Asma ‘ yanzu-yanzun nan”. Ba ta saurari abin da zai fada ba ta datse wayar, ta bar Ahmad riqe da kan wayar. Saudat ta zuba masa ‘ido ganin yadda ya yi Kasaqe idonta na kanshi kafin ta ce “LafIya dai k0?" Ya yi saurin dawowa cikin nutsuwarsa ya ci gaba da cin abincin tare da fadar “No.lafiya lau ba komai" Ganin yadda ya saki jiki ya ci gaba da cin abincin shi yasa. Saudat ta saki jiki ta ci gaba da cin _ nata abincin ita ma. Suna kammalawa bandaki yanufa ya watso ruwa ya shirya cikin‘ qananan kayansa ya nufi . Bangaren Saudat ya same ta a kicin ita da Mansura tana ganinsa ta saki yankan 'alayyahun da ta ke ta nufe shi, tana fadar, “Ba dai tun yanzu xaka tafi ba?” Ya daga mata gira alamar eh, ta langwabe kai, ‘ “Kai don Allah duka yanzu fa qarfe biyu, kaida kace jirgin karfe hudu za ka bi?” ‘ Ya riko hannunta yana fadar, “Akwai inda nake so na dan biya shi ya sanya. amman zakimin rakiya k0?,, Jikin Saudat ya yi sanyi qalau, ba yadda ta iya haka ta bi shi suka nufi harabar gidan inda direbansa ke sa masa jakarsa a mota, sai masu tsaronsa har uku suna tsaitsaye a bakin'motar. Ya riko hannunta yana fadar, “To Madam sai na dawo, ki kula min da kanki, _ akwai kudi na nan na ajiye miki a bed side drower dinki, daga gobe za ki fara zuwa makaranta dircba zai rinka kai ki, don Allah ki maida hankali ban da shiririta, ban da biye wa tarkacen kawaye kinji?” Saudat ta daga masa kai alamar eh don‘ta san tana bude baki kuka ne zai kwace mata, Dr; ya lakace mata hanci ya fada. mota yana mata dariyar Karfin hali, don ya lura ta yi matukar kuluwa, shi kansa ba don ya so zai tafi ya barta ba, don "a yanzu Saudat ta -' ida zama wani Bangare na rayuwarsa wanda ba zai iya rayuwa in ba tare da ita ba Ya soma daga mata hannu lokacin da direba ya ja shi. » Saudat ba ta iya motsawa ba, tana tsaye har suka fice tajuya ta nufi cikin gidan tana sharar kwalla girkinda ba a karasada ita yauba kenan tana ~dakin 'baccinta ta fada kan gadonta ta qudundune tamkar mara lafiya. ' ' Dr Ahmad bai bar Nigeria ba sai da ya biya ta gidan su Asma, sai dai abin da Hajiyar ta yi masa ba qaramin kuntata masa zuciya ya yi ba, tunda ya durKushe a qasa bai iya dagowa ba, yana saurarenta ta inda ta ke,shiga ba ta nan ta ke fita ba. Shi dai bai 'iya tankamata ba har sai da ta gaji' don kanta ta yi shiru sannan ya soma magana kansa a qasa. ‘ “A yi haquri don Allah Hajiya, abu ne wanda Allah ya riga ya qaddara Sai ya faru babu makawa sai ya faru, amma aurena da Sauclat wani mukaddari ne na Allah wanda ba mu isa mu guje masa ba, amma Wallahi ba don ba ni son Asma ba, duk da komai ya faru badasa hannunta ba amma ni ban riqe ta da komai ba, aurena wani mukaddari ne daga Allah, wanda,,,, ‘ “Saurara min haka Malam, ai tun kafin a haife ka na san wannan guntun wa’azin, tunda da ma budurwar zuciyarka ta ja ka izuwa ga kisisinar: ‘yar . aikin gidanka har ka aure ta ai dole xakake fadar komai muqaddari' ne. Sai dai abin da nake bukata a yanzu .kawai ka rubuta takardar Asma ka ba ta: amma aure dakai tagama kodakuwa kaine autan maza banda rufewar ido k0 meye abin naci a tattare da kai? Yo a tauna qashi k0 a karya haKori?’ ’ Ahmad ya mike tsaye ba tare da ya saurari umarnin hakan daga gare taba, ya zura hannu cikin aljhu ya zaro bandir din‘ yan dubu-dubu har guda ‘ biyar, wato na naira dubu dari biyar kamar yadda ya ba wa Saudat ya ajiye a kan kafet yana fadar, “Ga wannan a ba ta Hajiya ta ‘yi maneji kafin na dawo, amma ni bazan saki matata ba tunda’ har yanzu ina sonta”. Bai tsaya sauraren abin da zatacevaya fice abinsa ya barta tana faman kumfar baki ,,,,,,,,,, ,,,,,,,,,, ,,,,,,, Al’ amarin rayuwa ke nan, a kWana a tsahi babu wuya wurin Allah, Saudat ta kwashe “Sati hud'u tana. zuwa makarantar boko da islamiyya, cikm ikon Allah kuma duk abin da aka koya mata saita dauke shi kasancewarta mai budaddiyar Kwakwakwa don hatta tukin motar da ta ke zuwa koyo cikin sati guda ’ta ' kware don haka a sati na uku ta fara hawa titi ita * daya, yanzu haka ita ke tuka kanta ta je makaranta ta , dawo gida Saudat ta Kara gogewa tai ‘ wani fresh tamkar ba ‘YAR TALLA ba fatar" jikinta yayi wani luwai luWai har ‘yar qiba ta yi Wadda ta da yanayin jikinta, ga wata wayewa data qara samu ta musamman. , » ‘ A yanzu haka Saudat ta ita rubutun 1Hausa, Turanci ne dai take dan daddagirawa Hausa kam ta yi matuqar iya ta, don har karanta littafan Hausa ta ke na Mambuta dabamdaban, ‘ abin da ya Kara bude kwakwalwarta da Kara wayarmata da kai, ta qara samun experience din yadda za ta kula da kanta da shi kansa maigidan kenan Yau asabar ce ta yi daidai da cikar DR Ahmad sati hudu da tafiya kuma itace ranar isowarsa cikin ikon Allah, don haka tunda ta tashi daga islamiyya Karfe sha biyu da rabi ta dan wuce wurin gyaran jikida kunshida kitso ba ita tabar wurin ba sai qarfe hudu na yamma, don haka tana dawowa‘ gidan kicin ta nufa don hada abin da zata. ma maigidan kamar yaddata sanarda Mansura tana son girkamasa dambun shinkafa tareda pizza da kuma alkubus cake, potatoes chicken sai lemun‘karas tareda Creamy mango. Duk wannan zaBi nena Saudat don a yanZu itake bada umarnin komaima kondan Ayanzu. takwarene don har littafan girkin tana . Za ki dauko Barzazziyar shinkafarki ki bakace ta, ki cire garin sai ki zuba wa ‘shinkafar ruwa ki tsiyaye ruwan ki sa hannu ki matse, don ‘yan ruwan da suka yi saura su tsiyaye tsaf. Sannan ki zuba ' Barjinki a madambaci ki rufe ki batta ta turaru minti" goma zuwa sha biyar, sai ki sauke ki zuba a mara mai dan fadi ki barbaje shi sosai. * Sai ki kawo mangyad'a mai dan yawa ki zuba ki jajjaga attarugu ki zuba ki yanka albasa qanana, ki Sai .ki kawo dafaffiyar hantarki wadda kika .‘ yanka gutsin~gutsin ki zuba kisa garin kurkur cokali " guda sai kisa magi da gishiri da curry tare da thyme dadan garin citta da tafarnuwa sai ki juya sosai . sannan ki maida a madambaci ki rufe ki barsu su turaru minti goma zuwa sha biyar, sai ki sauke. Ki zuba a farantin maigida ki kawo dafaffen kwanki ki Bare, ki ‘masa yankan fadi, sai ki jejjera a saman abincin. Ni ma haka na ga Saudat din ta yi, sai na ga ta sa wani faranti ta rufe Sannan na ga ta dauko kwano mai fadi ta kalli Mansura. ' ’ “Yanzu kuma zan hada Pizza”. Ga yadda na ga ta yi. PIZZA lol Saudat na idarwa ta fice daga kicin din ta nufi babgarenta don magruba ta kawo jiki, don haka tana shiga ruwa ta watso .wa jikinta ta dauro alwala ta gabatar da salla, sannan ta nuifi gaban madubi ta ja stool ta zauna, kwalliya sosai ta yi irin wadda ba ta san ta iya ta ba, ta mike ta nufi kan gadonta ta dauki sabuwar atamfarta cikin wadanda ta kai wa ‘yar islamiyyarsu ta dinko mata. Tana cikin fesa turaren cool water ta ji wayarta ta soma rurin neman agaji, ta yi sauri ta nufi kan bed side drawer dinta ta dauki wayar, ganin sunan da ya fltO a kan madubin baro-Bare ya sa ta yi saurin shafar kore da dan' yatsanta, sannan ta kara wayar a kunnenta cikin tsananin doki ta ce, “Yallabai ‘ har kun iso?” Daga can ta ji ya karya murya yana fadar.“Wayyo tamyau, don Allah ki gafarce ni, na iso, amma ba zan samu isowa ba yau, za mu yi meeting a majalissa” ' Ai Saudat ba ta san lokacin da ta datse kiran . ba, saboda takaici ta wullar da wayar a kan gado cike da Bacin rai, don ganinta idan ya yi mata haka bai mata adalci ba. Ta ja tsaki tare da mikewa da niyyar ta cire kayanta, ta ji an turo kofa tare da sallama. Ai bata san lokacin da ta wuntsira ta nufe shi ba, shi kuwa ya bude hannayensa ta fada cikin jikinsa. “Madam kin yi kyau, kin Kara girma, wallahi kamar musanya min ke aka yi”. Ta sa dariyar farin ciki, “Mu je YallaBai ka ci abincin da na shirya maka sai ka yi wanka ka huta”. Bai musa mata ba ya miketa riko hannunsa tamkar wani qaramin yaro ,suka fice, har dinning area, ta ja mass. kujera ya zauna sannan ita ma ta zauna. Duk abin da ta girka sai da ta zuba ta tura masa, babu abin da bai ci ya yi santiba Wayarsa dake kan tebur ta soma‘ruri ya mika hannu ya dauka, ganin sunan Momy ya sa shi saurin dauka ya kara a kunne, “Hello Momy ina wuni, eh ga ta ma”. Ya kara wa Saudat wayar a kunne, muryar Momy dinta ce ta ji tana fadar, “Hello Saudat, albishirinki? Yau na ga yayanki Rabi u, an ganshi yanzu haka yana zaune a falona“ Ai Saudat ba ta san lokacin da ta fasa wata uwar Kara ba, ta saki wayar cikin tsabar kaduwa ta soma fadar, “YallaBai an ga Yaya Rabi’u, wayyo Allah na bari in dauko mayafina mu tafi Dr. ya waro ido, “Muje ina Saudat? Ba ki san k0 Karfe nawa ba ne yanzu? Takwas saura fa". Saudat ta marairaice masa, “Don Allah ka zo mu je, wallahi ba zan iya runtsawa ba yau in ban ganshi ba, k0 ka sa direba don Allah ya kai ni”. Dr. ya dan yi kasaKe yana kallonta, yadda duk ta firgice lokaci guda a take kuma sai ya ji tausayinta ya kama shi, tabbas ta yi kewar yayan nata, za ta iya ma shiga kowane irin hali. Ya sauke kansa daga kallonta ya mike ya suri wayoyinsa da ke kan teburin, ya ce, “Dauko mayafinki kizo muje”. Sai kuma tausayinsa ya kama ta, k0 awa 'daya bai yi da dawowa daga wata tafiyar ba, sai dai ba yadda za ta yi, tana son ganin yayan nata a yanzu fiye da komai. Ta juya ta dauko mayafinta kalar atamfar ta dauko wayarta da jakar takalman kafarta ta tattara kudaden da Dr. ya ba ta wanda ko dubu hamsin ba ta taBa a cikinsu ba ta zuba a jakar, sannan ta fito. Yana nan tsaye inda ta bar shi yana jiranta. Yana ganin ta flto ya yi gaba ta biyo shi a baya, sabuwar motarsa ya shiga. ‘ Saudat ta dube shi, “Ba direba zai kai mu ba Yallabai?” Ya ce, “A’a mu je kawai na tuqa mu, zamu fi sauri”, , ' Ba ta sake tankawa ba ta zagaya kujerar da ke gcfen direba ta bude ta zauna, ta samu ya kwantar mata da kujera, don haka ta kwanta sosai, shi kuma ya yi wa motar key suka fice daga gidan suka hau hanyar Katsina, inda suke sauraren karatun alkur’ani mai girm wanda Dr. ya kunna musu a motar, hakan yasa kowane ya nutsu yana saurare sai ‘yar maganar da ba a rasa ba. Ba karamin gudu ne Dr. Ahmad , yake sharawa ba a kan titi, don Karfe goma da minti talatin ta yi musu a cikin Katsina a gidan su Saudat. Tun kafin ya ida tsayawa Saudat ta Balle murfin Kofar ta fito a guje, ta nufi cikin gidan tana Kwalla wa Yaya Rabi’u kira. Tana shigowa ' falon tana wurwurga idanu, can hango shi cikin doguwar kujera yana shan fan-milk, Saudat ta fasa wata uwar Kara ta kwatsa a guje ta fada jikinsa ta kankume shi tana ihun dariya. , * Shi kansa dariyar yake yana ambaton sunanta ‘ tare da Kokarin dago ta don ganin yadda ta koma amma taKi sakinsa, su Nabil da Nabila ma ‘suka rufa mata baya suka rungume ta suna murnar ganinta. ’ . Momy dai dariya kawai ta ke musu zuciyarta dauke da matuqar farin ciki da shaukin ganin sanyin idaniyar nata 'Dr ya yi sallama ya shigo falon rike da jakar Saudat da wayarta ya durkusa agaban Momy yana gaishe ta cike da girmamawa, Saudat ta zame daga jikin yayan nata tana kallonsa, kuka ta ke sosai shi kansa sai da kwallar ta zubo masa cikin karfin hali ya soma share mata hawayen yana fadar, “Ya isa haka Saudat, ba kuka za mu yiba, sai mu gode wa Allah” “ Dr Ahmad ya mike har zuwa inda suke ya mika wa Yaya Rabi u hannu yana fadar, “Your welcome Yayanmu, mun yi farin cikin ganinka” . Rabi u ya ce “Ni ma haka, amma yanzu cikin ,daren nan ta taso ka? ” Dr ya cc, “To ya na iya‘? Ai yayanmu yana da _ muhimmanci a rayuwarmu”. Dadi ya kama Rabi’u ya yi na’am kuma da zamowar Dr. Ahmad mijin ‘yar kanwar tasa. Saudat ta mike ta nufi wurin mahaifiyarta tana fadar, “Don Allah a ‘ina ku ka ganshi?” Momy wadda bakinta yaqi rufuwa ta ce, “Saudat, yanzu cikin daren nan ki ka taso mijinki, tsakaninki da Allah kin kyauta? Ai da na ‘sani da sai gobe na fada miki Saudat ta ce “Kai don Allah Momy, shi fa ya ’ ce mu taho”. Ta yi maganar tare. da satar kallon Dr. wanda aka yi sa’a shi ma ya kallo ta ta yi saurin dauke kai, “Don Allah Momy ina ku ka ganshi?” Momy ta ce, “Ta hanyar Inna mai danwake, tunda ki ka fada min Rabi’u ya bada sako a baki nake aikawa wurinta a kan a karBo min sakon mijinta ke fadamana vata nan ta yi tafiya zuwa garinsu har ‘ ,ta kai ga ,ina zuwa da kaina, amma ban yi nasarar ' samunta ba, tsawon wata daya da sati biyu sai yau na tayar da direba na tura shi kasancewar mijinta ya ba mu tabbacin yau ne za ta dawo. Cikin ikon Allah kuma ya yi nasarar samunta ta dawo daga garin nasu a jiya, aka yi sa’ a kuma ta bawa direban saqon cikin waccan jakar”. Momy ta yi musu nuni da wata ~leda mai tambarin Aminci Super Market Katsina, ta ci gaba da fadar, “Direba na kawo. min jakar na zazzage, ba komai bane a ciki sai wasu lesussuka guda biyu, atamfa super Holland guda, sai takalma da jaka da kuma sabuwar waya a cikin kwalinta tecno p.2 da'sabon layi a ciki. Jikina na rawa na kunna wayar sai ga lamba Kwara guda a ciki, a take na danna kira cikin sa’a kuma lambar ta tafl. Bugu biyu ya dauka muryar har rawa ta ke wurin sanar da shi k0 ni wace ce, shi kansa ya shiga rudani kuma k0 minti talatin bai Bata ba ya iso nan gidan”. , Saudat ta cd“Wayyo Yayana, Allah sarki ashe ba ka manta da ‘yar qanwarka ba? To yaya da baba ya kore ka kai ina ka nufa?" ‘ _ Rabi’u ya dan yi‘ murmushi kafin ya ce“Ai *duk halin da na shiga Saudat ban tunanin zan manta dakeba sai dai in har ba na numfashi, don a lokacin da Baba ya kore ni na dauki hanya ina ta tafiya amma ban san inda zaniba ina ta tafiya ga *gajiya ga yunwa ga duhun marece ya fara. Ina cikin tafiyar nanne na fara shigowa gari nayi karo da wata leda kamar zanwuce saikuma watazuciyar tabani shawarar induba ko Allah zaisa wani sauran abinci ne a. ciki in samu abin da zan ci. Da wannan tunanin na tsaya na dauki ledar,ina dubawa amma damamakina sainagawani kwali ina duba kwalin sai ga sabuwar waya a ciki, dadi yakamani nasamu abindazan siyar inci abinci, don haka da kwanrin gwiwata na ci gaba da tafiya harna shiga cikin gari da tambaya aka nunamin wurin saida wayoyi harna isa kasuwar tsaitsaye wadda ke cikin garin Katsina donna bada wayata a siya, sai dai abindaya dauremin kai shine farkon tayi aka tayata naira dubu dari da hamsin mamaki yasa na gaza cewa komai, shi kuwa mutumin dauka ya yi k0 ba zan siyar masa bane ya hau kora min jawabi. ‘ “Malam damaka siyarmin dawayarnan haka don ba wata uwar ribace zanciba don dubu dari

Chapter 25 of 26