zubawa kayan ido. Hawaye kawai taji suna bin kumatunta tsabar bak'in ciki. Anya kuwa zata iya rayuwar aure da mutumin da bata sani ba dabi'un sa, halayyarsa sa ba. Idan shima irin Babaah ne fa? Da kyar ta iya rarrashin kanta saboda gajiya haka ta kwanta kan gadon zuciyar ta cike da tunani har yana neman saka mata ciwon kai. Ba ita tayi barci ba sai wajen d'aya sannan ya fisge ta da mugun k'arfi gefen fillow da take kwance ya yi sharkaf da ruwan hawaye.
Tsabar yanda barcin nata ya yi nauyi sosai har aka yi asuba bata farka ba saida aka buga k'ofar Mom na kwala mata kira. Da kyar ta iya miƙewa kanta na mugun ciwo duk uban barcin da tayi. Haka ta nufi k'ofar kaman wadda tasha wani abu sai layi take. Tana buɗe k'ofar Mom ta shigo ita da Nonna rike da faranti.
“ba dai sai yanzu ki ka tashi ba bakiyi sallah ba kenan?”
Bata ce komai ba ta matsa suka shigo. Nonna ta kama gashin ta daya bushe tana kallo tace
baki shafa masa mai bane naji gashin ya yi tauri?”
Murya a d'an sanyaye tace “wanke kan nayi”
“Hmm, to maza ki wuce ki sake wani wankan kizo ki shirya k'arfe takwas zaku tafi saboda hanya ”
Kaman tayi kuka ta juyo ta kalli Mom dake juye tsumi cikin cup ta juyo fuskar ta da irin kallon na ban hak'uri. Mik'a mata kofin tayi ta shanye Nonna ta tura ta banɗaki . Jiki babu kuzari ta sake wani wankan ta fito ta data sallah a gurguje saboda lokaci dake ta sake kurewa. Gaba suka sata bayan ta idar suka shafeta da mayuka masu saka laushin jiki tafar d'aya irin masu mugun tsadar nan kafin Nonna ta kunna wani turaren wuta data zo dashi daga Saudiya akayi mata. Cikin d'an k'ank'anin lokaci harta farcen hannun ta saida ya d'auki wannan kamshi. Suna gamawa ta buɗe jakar ta ta saka mata shi a ciki tana mata bayanin yanda zata dinga amfani dashi. Ita dai Ajwa ido kawai take binsu dashi. Wata hadad'd'ediyar Ash less d'inkin riga da sket suka shirya ta a ciki da katon mayafi daya sha adon stone. Fuskar nan tayi fayau babu makeup sai hoda da lan man lebe da suka saka mata amma duk da haka ba k'aramin kyau tayi ba, ga uban sarka na gwal da Nonna ta saka mata da abun hannu. Suna gama shirya ta suka fito k'asa inda baga d'aya mutanen falon duk suka hallara ana karya kumallo. Zaunan da ita sukayi kusa da Ammi dake ta zuba murmushi. A hankali Baffa da Abba suka juyo wajen Ajwa da kanta ke k'asa suka hau mata nasiha sosai mai ratsa jiki suna gamawa Babaah shima ya d'ura da nashi. Jin muryar Babaah na mata nasiha ta d'an d'ago a fakaice don ta tabbatar. Shine kuwa yasha manyan kaya fuskar nan ta cika da annuri. Kai Ajwa ta d'an jinjina ta sauke mayar k'asa taba tunanin wane shiri ne kuma haka yake yi?
To mazan na gam mata fad'a suma matan suka d'ura banda Mom dake ta k'ok'arin ganin ta hana kanta kuka haka Suliem dake can gefe cikin wasu y'an mata. Daga k'arshe kasa jurewa sukayi saida hawaye ya biyo kumatunta. Har yanzu Mom ta kasa yarda Ajwa d'in ta ta girma gashi yau zata tafi gidan wani. Zata tashi daga care d'inta. Shikenan yanzu bata da iko da ita. A guje Suliem ta taso taa rungume Ajwa tareda fashewa da kuka. Itama matsowa tayi ya had'asu ta rungume suka hau kuka saida suka bawa kowa tausayi. Da kyar Baffa suka lallashe su sukayi shiru kowa ya koma inda yake. Ganin sun d'an nutsu kuma da sauran lokaci Nonna tasa mai kunshin dake jira ta rangad'e Ajwa da wani haddedden lalle ja da ya yi masifar yi mata kyau gashi nan da nan ya bushe kaman rani. Amma lallen sosai yake da kamu. Ita kanta duk kuncin da take ciki saida lallen ya masifar birgeta. Kaman wanda aka buga da inji.
Kaman kuwa jiran bushewar lallen suka saiga Lamin d'an gidan Baffa ya shigo da sauri yana sanar musu dazuwan Asad da Su'ad. Maza gaba d'aya suka fito harda Babaah daya riga su ficewa da mugun sauri. Tunda ya hango Asad cikin wata dakakkiyar shadda blue tazarce kansa babu hula sai gashi sa daya zubo gaba da bayan wuyansa ya kwanta kaman hular. Tsananin kyau da ya yi abun ba'a cewa komai. Baki Babaah ya lashe ya nufi motar da sauri yana jin zuciyar sa kaman ta tsinke . Hango Babaah ya nufosu Su'ad dake zaune wajen direba ya d'an tab'a Asad daya jingina jikin kujerar da ido a lumshe. A hankali ya d'an bud'e idon nasa ya wurga su kan Su'ad dake nuna masa Babaah dake tunkaro su. Numfashi ya d'an fesar kafin ya kama murfin motar ya fito da d'an sauri daidai Babaah na karasowa. Da girmawawa ya yunk'ura zai durkusa Babaah ya wani saurin tareshi ya mik'ar ya kama k'afad'un sa ya rik'e kafin ya rungume shi yana murmushi. Shi kansa Asad wani irin ban bara kwai yaji abun amma bai motsa ba saida Babaah ya janye har zuwa lokacin murmushi kan fuskarsa.
“babu formalities yanzu tsakanina dakai Asad. Ka d'auke ni kaman aboki kuma uba kaji.”
Kallonsa Asad ya yi sai kuma ya sunkuyar da kai don baisan me zaice ba. Shi kuma haka yake daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak'i? To ai y'ar sa yake aure dole ya bashi girman siriki koda kuwa baya so. Su Baffa ne suka k'araso har k'asa suka durkusa da Su'ad suka gaishe su suka amsa fuska a sake kafin suyi musu jagora zuwa ciki. Babaah kam ya kasa daina zuba murmushi sai kallon Asad yake ta gefen ido yana sake tasbihi cikin ransa. Tabbas bazai bari ya kubce masa ba. Dole yasan duk wata hanya da zaiyi ya raba auren kafin waccen shegiyar yarinyar ta d'and'ana zumar da yake mafarkin ta.
Suna suka shiga falon ya rangad'e da gudar Nonna y'an matan dake wajen duk suk rikice tun suka fara kuskus suna fad'an wannan namijin Ajwa? Tab wannan wane irin ya'ya zasu haifa haka. Suliem dake jinsu ido cike da hawaye ta sulale babu wanda ya lura ta haursa sama da d'an gudu. Daga shi har Su'ad nan bakin k'ofa suka durkusa suna gaida Nonna dake masu tsiya dasu Ammi. Baffa yace duk y'an matan su tashi su basu guri idan zasu tafi za'a kirasu. Kusa da Ajwa Nonna tasa ya zauna saboda kujerar mai cin mutum biyu ce. Zamansa kusa da ita saida zuciyoyinsu ya harba lokaci d'aya. Kamshin turarenta daya daki hancinsa saida yasa ya d'an lumshe ido kad'an ya buɗe yana kallonta ta k'asan ido duk da baya ganin face nata saboda mayafin da Ammi ta rufa mata gashi kuma kanta na k'asa bare yasan wane hali take ciki.
Maganan su Baffa yasa ya maida hankali kansu kansa a k'asa yana sauraran nisiha da suke musu kafin daga k'arshe suka bisu da Addu'a. Miƙewa ya yi ya ajiye rafar dubu gudu uku gefeb Ajwa kafin ya yi sallama dasu Baffa ya fice Babaah ya sake binsa da sauri ya rakashi har wajen mota. Yana k'ok'arin bud'e motar ya shiga Babaah ya rigasa bud'ewa ya kama murfin yana masa murmushi yace
“Allah ya baku zaman lafiya kaji d'ana. Idan har tayi maka wani abu da ba daidai kar kayi nauyin baki wajen fad'a. Allah ya yi maka albarka ya kuma sauke ku lfy”
D'an taune baki Asad ya yi ya kalli Su'ad suka had'a ido kafin yace amin can k'asan mokashin sa. Shigewa motar ya yi Babaah ya maida murfin ya rufe ya juya ya shiga gida. Samu ya yi ana tijara da Ajwa tak'i tashi daga inda take. Rai a b'ace ya dakata mata tsawa Abba ya yi saurin da fashi yana girgiza masa kai. Yaran yanzu saida lallashi. Da kanshi ya matsa ya kamata ya mik'a yana lallashi aikuwa ta saki wani irin kuka mai tab'a zuciya. Nonna da sauran matan dake d'akin suka kasa jurewa duk suka fara sharar kwalla. A haka suka fito kaman wacce za'a kai gidan mutuwa. Babaah tsabar bak'in ciki kaman ya yi bindiga saboda yanda zuciyar sa ke tafarfasa. Koda suka k'araso gaban motar ma kon shiga tayi ta juya ta rungume Mom da Ammi suka cigaba da rera kuka. Babu wanda ya rabasu saida aka gama saka mata kayanta cikin boot sannan ta janye ta d'ago tana neman Suliem amma babu ita a wajen. Kafin tace ina Suliem Aunty Raihana ta kamata ta tura gidan baya.
Tana shiga Su'ad ya tada mota ta wani kankame murfin motar tana kallonsu Nonna dake ta d'aga mata hannu suna Allah ya kiyaye sai zunzo. Da gaske barin gida zatayi. Kama murfin tayi zata buɗe motar ta fito Su'ad kaman ya ganeta ya yi saurin fisgar motar da d'an gudu. Wani irin kuka ta fashe dashi tana kallo Mom dake kuka yana daga mata hannu har suka fice daga gidan. Haka kai tayi ta gwiwa ta cigaba da rera kuka kaman babu gobe. Asad daje jingina jikin kujera da ido a lumshe ya d'an saki karamin tsaki. Shifa a duniya baya san kuka sosai yake damunsa. Haka suka d'auki hanya baka jin komai cikin motar sai kukan ta dake tashi. Basuyi wata tafiya mai nisa ba taji alamun motar ta tsaya. A hankali ta d'ago da jajayen ido sai taga sun fice daga motar Asad ya zagaya wajen direba shi kuma Su'ad ya d'an leko ta windo da murmushi kan fuskarsa yace
“to amarya sai anjima ko? Allah ya sauke ku lfy”
Maimakon ya bashi amsa saita maida kanta ta had'a da gwiwa. D'an murmushi ya yi ya daga ya bawa Asad mukullin suaka sake rungume juna kafin ya wuce da sauri wajen wata Accord dake fake d'aga hannun hagu. Da tsananin gwanancewa Asad ya fisge ya harba ta kan titi.
Bazatace ga iya tsawon lokacin data d'auka tana kuka ba har tayi lallashi kanta tayi shiru. Wajejen Azahar suka faka wani katon masallaci dake kan hanya Kaduna Road. Jin motar ta tsaya yasa ta d'ago a hankali tana kallon window ganinsu a masallaci yasa ta juya a hankali ta kalli Asad dake k'ok'arin ficewa daga ciki motar. Tunda ta shigo motar kurar ma data debora bai kalla ba bare tayi zaton ko zaiyi mata magana. Harta ci kukantata koshi bai juyo ya kalli inda take ba sai ita ta rarrashi kanta. Wane irin zuciya ce dashi haka ta marasa imani da rashin tausayi?. Tana kallo yasa kai ya fice daga motar ko waiwaye baiyi ba ya shige masallaci. D'an cije baki tayi ta buɗe motar a hankali ta fito itama ta shige wajen mata. Saida ta fara kama ruwa sannan ta fito tayi alwala ta shige masallaci. Data idar da sallan tana sane ta share d'uwawa ta zauna taki fitowa har sama da minti arba'in . Aikuwa Asad ya shak'a don kiris ya rage bai barta a nan ba. Yana k'ok'arin tada motar sai gata ta fito duk da ta hango shi baisa tayi sauri ba saida taga ya data motar yana k'ok'arin reboost babu shiri ta tattare sket ta k'ara da sauri ta fad'a motar ko rufewa batayi ba dakyau ya fisgeta a guje ya harba kan titi.
Wayyo Ajwa kaman ta tashi tsananin bak'in ciki. Wajen saurin shiga motar har bigewa tayi amma inda take yaki kallo kace ba tare da mutum yake tare ba. Wato tafiya zaiyi ya barta inda bata san kowa ba kenan? Lallai bak'in halinsa ya wuce inda take tunani. Kamshin gashin tsiren daya doki hancinta yasa ta kalli gefa saiga ledojin nama da lemo. Take kuwa cikinta ya fara kuka amma tsananin taurin kai saita d'auke kai ta kwammace ta zauna da yunwa da dai taci abunda ya fito daga hannun sa. Wajen la'asar suka shiga Abuja birnin tarayya. Garin ya had'e ya yi bak'ikk'irin sai iska da walk'iya ake. Ido Ajwa ta ware tana kallon Abuja. Lallai kuwa taci sunan ta Abuja. Yau gata garin Abuja zatayi zaman aure. Lallai Allah buwayi gagara misali. Nan unguwa Maitama haddedden gidan yake. Suna shiga layin kuwa aka barke da ruwa kaman da bakin kwarya. Wani katon bak'in gate taga ya dannawa horn aka bud'e da sauri ya danna hancin motar ciki. Katon flat house ne dake dauke da enough faking space da garden daga cen gefe sai boy's quarters dake bakin gate. Ko ina gidan tar yake da fitilu kaman rana. Gida kam ko Ajwa ta sheda ya had'u babu k'arya. Tana kallo ya faka motar k'ofar wata baranda bai juyo ba ya saka kai ya fice abunsa. Da ido ta bishi har ya haura kan baranda kafin ya kai kuwa ya jike sharkaf. Tana kallo ya buɗe hadad'd'ediyar k'ofar ya shige ya maida abunsa ya rufe. Harga Allah har cikin ranta ta d'auka lema zai d'auko mata shi yasa batayi yunk'uri. Fitowa ba. Shiru-shiru babu Asad babu labarin sa tana zaune ciki motar har sama da minti biyar ga ruwa yana k'ara tsanani harda k'ank'ara. Tabbas barinta ya yi cikin motar tasan inda zata kenan?
Kwafa tayi ta kama motar ta fito tana kankame jiki ta taka da gudu wajen barandar amma duk da haka saida ta jike. Jiki na rawa ta kama k'ofar k'irjinta na harbawa kar ya rufe sai taji k'ofar a Bude. Kaman munafuka ta tura kai cikin hadad'd'en tangamemen falon. Ganin babu kowa ta sanya jiki a hankali ta shiga ta maida k'ofar ta rufe. Wani irin sanyi mai ratsa bargo da kashin jiki ya mata sallama ta sake wani irin kankame jiki leben ta suka had'u waje d'aya. Da ido take kallon haddedden falon da babu wani tarkacen sai haddeddun fararen kujeru da cushion masu kaman gado da scenter tabir. Daga gefe wasu hadad'd'un flowers ne dake d'auke da wasu irin fitilu maau masifar kyau. Sai plasma ta bango data cinye rabinsa kaman glass. Daga gefe hannun hagu irin abun kifin nan ne da kifaye a ciki ga ruwan blue da wasu irin fitilu dake k'ara masa armashi. Komai da dake falon fari tas tun daga kan labule har kafet. Sosai ta ware ido da hanci tana kallon had'uwar falon. Babu zato taji muryar sa gefenta. Da zaman ta juya inda taji yana tsaye kan wasu yan matakalai guda biyu da suka zagaye falon wajen wata yar hanya mai zurfi.
“muje ga d'akin ki”
Kawai yace ya juya da wannan izzar tashi. Ji tayi kaman ta bishi ta shak'e tsabar haushi. Kwafa ta sake yi tana tarashi ne duk zata rama. Da d'an sauri ta haura ganin ya b'ace mata. Gaban wata k'ofa ta sameshi ya tana karyowa ya kama k'ofar ya buɗe ya watsa mata kallo fuska a cunkushe babu emotion. Da kai ya d'an nuna yana cewa
“wannan ne d'akin ”
A hankali ta matso tana zuba masa harara ta rab'a ta gefen sa ta shige d'akin. Tana shiga ya maida k'ofar ya rufeta da mugun k'arfi saida ta d'an firgita ta juya tana kallon k'ofar cike da takaici. Kwafa ta sake yi ta juya da sauri tana kallon katon d'akin daya kashewa dukiya. Kai ta jinjina ta matsa wajen makeken royal bed dake can k'uryar dakin dake kewaye da net da fitala tsakiyar sa ga uban pillows dake kai masu shegen laushi. Kaman falon shima d'akin komai fari kal yake. A hankali ta kwanta kan gadon jikinta gaba d'aya babu kuzari don mugun yunwa take ji amma taurin kai ya hanata taci abincin daya siyo musu a hanya. Ko ina Jakarta tana son kiran su Mom ta sanar musu da saukan ta. Tunani tayi bari ta d'an watsa ruwa wata k'ila zataji d'an kuzari a jikinta. A hankali ta miƙe ta shige banɗakin dake can gefe. Shi kansa banɗakin abun kallo ne saida ta gama bawa idanta abinci ta cire kayanta ta had'a ruwa cikin abun wanka dake tsakiyar banɗakin ta shige tana sauke ajiyar zuciya. Zafin ruwa da yanda yake ratsa sosai ya saka mata nutsuwa saida ta jima cikin sa sannan ta yi wanka ta fito tana bin bad'akin da kallo. Can ta hango tawul rataye jikin handler ta matsa da sauri ta d'auko ta d'aura sannan tayi alwala ta fito.
Fitowar ta daga cikin banɗakin ya yi daidai da sawo kan Asad ciki d'auke da d'an tire da yar kula karama da ruwa na gora a kai. Daga ita har shi sandarewa sukayi a tsaye kafin Ajwa ta zare ido ta fara k'ok'arin zata juya aguje ta koma cikin banɗakin cikin rashin sa'a tawul nata ya zame ya fad'i k'asa.Wani irin gigitaccen ihu Ajwa ta kurma mai kashe dodon kunna kafin ta juya da wani bala'in gudu hannu rungume a k'irji ta koma toilet d'in. Asad kam ya kasa motsawa don sosai ya daskare a gurin saida yaji k'arar fad'uwar tiren dake hannun sa ya yi wani irin blinking idanuwansa da suka kafe inda Ajwa ke tsaye. Bai san ya rike numfashi ba saida yaji yana neman shek'awa lahari ya wani ja numfashi da mugun k'arfi kaman mai shirin tada Asma. A hanzarce ya juya ya fice daga d'aki jikinsa na wani irin rawa da kyar ya iya kai kanshi k'ofar d'akin sa.
Chapter namu is short today. Manage please 😧🙏
TAURA BIYU
/No edit!
【Pg21&22】
Matsanancin kuka ta fashe dashi tsabar bak'in ciki Allah ya isa kuwa tayi masa babu kakkautawa. Yau wani banza yaga tsiraicinta a banza a wofi. Durkushewa tayi bakin k'ofa ta had'a kai da gwiwa ta cigaba da rera kuka kace wani mugun abu ne akayi mata. Saida taji kukan na neman sa mata ciwo ga yunwar dake cinta sannan ta hak'ura ta yi shiru tana tunanin idan ta kwanta ciwo waye zai bata kulawa?. Sama da minti goma tana ta sak'awa ta warware kafin tayi k'arfi hali ta miƙe a hankali ta kasa kunne jikin k'ofar banɗakin ko zataji motsi sa daga cikin d'akin. Jin shiru babu wani motsi yasa ta buɗe k'ofar a hankali ta d'an leko da kanta ganin babu kowa ta wani fito wuf kaman iska a guje tayi wajen k'ofar ta danna mata key sannan ta wuce wajen kayanta data ajiye kan gado ta mayar tana yi tana kallo k'ofar sai kokawa take da rigar taki sakuwa tsabar yanda babu nutsuwa a jikinta. Tana gama saka kayan ta koma kan gado ta takure don sosai take jin zazzab'i da take ta k'ok'arin gujewa. Ba kuma wani abu bane yunwa ce da kuma gajiyar hanya yasa zazzab'in nata sake tashi. Babu dadewa kuwa ta fara rawan sanyi tayi maza taja bargo ta kankame jik'i.
Tunda ya koma d'akin ya kasa samun nutsuwa da kyar ya iya saita nutsuwar ya sake fitowa jiki babu kwari ya koma kitchen ya sake dafa abu mara nauyi da d'an fresh drink ya jero kan tire ya nufo d'akin nata. Tafiya yake amma tunanin sa da hankalin sa nacan kan surarta. Bai tab'a tunanin yanda take yar mitsitsiya haka ba tana da irin wannan kira mai tsananin jan hankali. Sosai idan yace baiji mamakin ganin k'irjinta ba yanda suke a ciki ya yi k'arya. Shi mutum ne da sam bai cika son nono wanda suka cika yawa ba haka bai son wanda suka cika kankanta . Shi yasa ya yi mamaki daya ga sosai irin test nashi ne. Bak'in k'ofar ta ta ya tsaya ya yi shiru zuciyar sa na cewa 'menene duk kabi ka damu da ita? Ka barta mana idan taga dama taji yunwa zata fito ta nema. Yanzu idan ka koma gani zatayi kaman kaji wani abu ne saboda ganin surarta, kuma zatayi tunanin akwai abunda ka ke nema wajen ta'
Wani b'angaren yace 'aa ai hakk'in sa ne bata kulawa, bazai barta da yunwa ba tunda Allah ya d'ura masa nauyi dole ya sauke koda baya sonta'
Numfashi ya fesar mai zafi saboda yanda yake jin shawarwarin zuciyar sa. Kai kawai ya jinjina ya tabbata dole ya sauke nauyin da Allah ya rataya masa a wuya. Yanzu da da ba d'aya ba. A hankali ya kai hannu jikin k'ofar sai ya jita a gark'ame. Dan tsuka ya yi ya juya nashi d'akin ya d'auko wasu spare keys ya dawo ya buɗe k'ofar . Tana kwance ta nannad'e cikin bargo taji an buɗe k'ofar tayi wani irin zumbur ta tashi tana zare ido. Kallo d'aya Asad ya mata fuska a murtuke ya d'auke kai ya matso gaban drawer ya sake ajiye mata tiren abincin ya juya zai fice. Da ido ta ke binshi tayi tunanin fita zaiyi sai taga ya tsaya wajen abincin daya zubar ya durkusa yana kwashewa. Sosai bakinta ke d'auke da bakaken maganganu amma ciwo ya hanata furtawa sai bakin nata dake ta rawa. Har yasa kai zai fice bayan ya gama kwashewa ya juyo ya sake kallonta suka had'a ido kowa da abunda ke cikin ransa. Sosai yake kallonta ya d'an kankantar da idonsa yana k'are mata kallo. Shi likitane yasan kuma mara lafiya idan yaga d'aya. 'She is sick' yace can k'asan zuciyar sa. D'aya b'angaren na zuciyar sa yace ' to sai me?' . Wannan shine dalilin dayasa gaba d'aya auren baya so. Duk wani nauyi da wahala an d'urawa mutum bai shirya ba. K'aramin tsaki ya sakeyi Ajwa duk tana kallonsa da wani irin mugun kallo kaman ta shak'e shi. Dawowa ya yi a hankali ya tsaya gefen gadon yana kallon yanda take chukwikiye zanin gadon a k'irji tana d'an sake ja baya kadan kaman zata shige fuskar gadon. Mtsw. Ya k'ara jan wani mugun tsaki cikin ransa me take tunani? Ita ko matan duniya sun k'are menene zaiyi da ita har take wani b'oye jiki?. Da wannan muryar mai kaushi yace
“ke baki da Lafiya ne? Meke damun ki?.”
Maimakon ta bashi amsa sai ta sake zuba masa wata muguwar harara bak'in ta na rawa saboda sanyi. Lura da rawan d'arin da take yasa yaja d'an k'aramin tsaki da ajiyar zuciya dake neman zame masa gado daga jiya zuwa yau . Juyawa kawai ya yi da sauri ya koma d'akin sa ya d'auko first Aid kid nashi ya dawo d'akin. Tana ta k'ok'arin tashi ta sake rufe k'ofar amma saboda rashin k'arfi ta kasa. Tana jin motsin dawowar sa ta sake ware idanta kansa da sukayi ja sosai saboda yunwa. Da isa ya k'araso gefen gadon ya zauna ya ajiye kit d'in gefe duk tana kallo ya tsiyayo fresh milk cikin glass cup ya juyo kanta ya mik'o mata fuskarsa nan babu emotion. Mugun kallon data jefa masa bai hanashi nufar bakinta da cup d'in ba. Wani irin zabura tayi ta buge hannun sa da mugun k'arfi cup d'in ya fadi can gefe madarar ta zube jikin su gaba d'aya. Tsananin b'acin ran da Asad ya shiga kasa yi mata magana ya yi sai mayun idanuwansa daya kafeta dasu. Yanayin kallon da yake mata saida ya saka k'irjinta bugawa d'an tsoro da shakkar sa ya ratsa ta amma bazata bashi wanna sa'ar ba ya fuskanci halin da take ciki.Sosai kwarjinin sa da girman ya hanata sakat. Saida ya yi clicking harshen sa sannan yace da murya mai kaushi
“kar ki kuskura ki sake wannan gangancin. Bawai ina yi ne saboda na damu dake ko ke wata aba bace a wajena , ina yi ne saboda amana aka bani kuma ya zame min dole na sauke nayi da Allah ya d'ura min. So kona minti guda kar kiyi tunanin you're something special .”
Wayyo zuciyar Ajwa duk yanda take son tayi magana ta kasa kaman wacce aka d'aure mata bakin sai rawa kawai da take. Kai ya d'an jinjina don ya lura yanda bala'in ke cinta amma yunwa ya kashe bakin. Buɗe hadad'd'ediyar jalof ya yi daya dafa dataji busheshesn kifi da hanta, ga uban kaji. Kamshin abincin na dukan hancinta cikinta ya wani irin kullewa da k'ara saida tayi d'an ihu. Ta koma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 15