Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
laifin gaba d'aya a kanta duk da cewa ba ita ce ta girka abincin ba. Ta riga da tasan babu wani matsala da abincin don Mom karshe ce wajen girki kawai Babaah yana neman hanya ne da excuse da zai daki mahaifiyar su a banza kaman jaka. Babaah na wani irin kumfar baki ya daka mata tsawa “rufemin baki, wato ke kad'ai ce wuyanki ya isa yanka ina fad'a kina maidawa ko?. Wato ke ga mai uwa zaki shigar mata fad'a ? To baki nunamin ke ishashshiya y'a bace da uwar ki ce kad'ai ta tsugunn ta haifa ki, sai kin d'aga hannun kin dake ni yar iskar yarinya kawai mai kama da aljanu” “ Ajwaah ” Mom ta sake kirantan da k'arfi amma Ajwaah tak'i motsi daga gaban Babaah. “sai na fad'a Mom. Ai nasan Babaah kana yin hakan ne kawai don kaci mutuncin M.....” Bata kaiga k'arasa maganan ba ya zuba mata wani irin mahaukacin mari da gaba d'aya falon saida ya amsa. Batayi mamaki ba don wanna kad'an ne daga ciki aikin Babaah. Saboda yanda ya sauke hannun nasa kan fuskarta da mugun k'arfi saida hak'oranta suka had'u da juna ta datse harshe. Hawaye suka taru cikin idonta na tsananin azaba ta kai hannu ta dafe kuncinta. Suliem dake kusa da Mom tayi wani irin tsalle kaman ita aka mara ta b'oye bayan Mom tana sake fashewa da matsanancin kuka. Mom ta kasa motsi sai ido data zubawa Ajwaah dake kallon Babaah da jan ido zuciyarta tana k'una. She wish tana da k'arfi da zata kwatarwa ya'yan ta y'anci wajen wannan azzalumin mutum. Yanzu take jin haushin sanyin ta da kuma raunin ta don bazata iya yin komai kan Babaah ba. Duk yanda take buri wajen ganin ta kai kararsa wajen magabata, bazai yiwu bane saboda Babaah irin mutanen nan ne masu fuska biyu a waje Musa yake ciki kuma Fir'auna. Babu wanda zai yarda da wai yana da wasu miyagun dabi'u bayan halayyarsa na kirki da kowa yake kallonsa dasu. “wane mugun aiki ne haka ki ke koyawa ya'yana?ki na koya musu suyi jayayya dani ubansu ,ko Measha Begum? Wow.” Ya fesar da wani huci kaman wani bijimi sai hura hanci yake. Kwafa ya yi ya wuce su bayan ya yi jifa da kujera yana cewa “abincin ma baza'a barka kaci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali ba?banzar mace, mai rashin godiya Allah ” Da gudu Mom ta bishi tana cewa “don Allah kaci wani abu mana” ko juyowa baiyi ba ya fice yana hargagi. Yanda Mom tabi Babaah sosai ya konawa Ajwaah rai sai da hawayen da take riƙewa suka biyo kuncinta ta tayi saurin gogewa ta matsa ta zauna kan kujerar da Babaah ya tashi ta fara cin abincin kaman zata had'a da kwanon ta cinye tsabar baƙin ciki da b'acin rai. Suliem na tsaye gefe tana kallon kanwar ta ta dake cin abinci hannu baka hannu kwarya har Mom ta dawo ta sameta. Da hanzari ta k'arasa wajen Ajwaah ta kama fuskarta da gefen fuskar harya kumbura shatin yatsu sun kwanta raɗau abunka da farar fata. Ajwaah bata da haske sosai kaman Mom da Suliem ita fatan ta ya gauraye da duhun Babaah sai ta tashi kaman irin fatar y'ar Ethiopia. “Me ki ka yi haka Ajwaah?, kin b'atawa mahaifin ki rai?” bayan abubuwan da Babaah yake musu, Mom tana k'ok'ari taga ta kyautata masa ta kuma nuna musu muhimmanci Babaah cikin rayuwar su, amma Babaah baya gani a koda yaushe ita yake d'urawa laifi ,baya tunanin halinsa ne yasa ya fara gani chanji daga tarbiyar Ajwaah. A hankali ta d'aga da idonta taga kan plate tana kallon Mom softly tace “Amma Mom baki ga yanda yake miki ba?, bazan iya kallo ba banyi komai ba” “ni matar sa ce Ajwaah yana da iko a kaina ke wace da zaki shiga abunda bai shafe ki ba?” Kun gani, bayan abubuwan da yake mata Mom a koda yaushe tana kare shi. Bak'in ciki yasa hawaye suka wanke wa Ajwaah fuska tayi saurin gogewa tana kallon Mom data zubawa gefe ido bata son ta kalle ta. “Iko Mamaa, a wane aya ko hadisi aka ce an bawa namiji iko ya dinga dukan matarsa saboda ita d'in damar sa ce Mamaa?” Numfashi Mom ta sauke a hankali ta kai hannu ta kama fuskarta cikin taushin murya tace “Me yasa ki ka yi haka Bint?,me yasa ki ka tunzura mahaifin ki?wata rana ina tsoro ya kashe mun ku. Ki saurari magana na kiyi abunda yace kaman yanda Suliem take. Kar ki sake yin magana haka a gabansa. Shi d'in namiji ne dake sama dani kuma yana da power da zaiyi komai. Kar ki sake kinji?” Cije baki tayi hak'oranta suka had'e waje d'aya saboda b'acin rai. MAZA. Mahaifinta shine ummul'aba'isin daya saka ta tsani maza gaba d'aya jimla. Gani take kaman duk haka suke halinsu d'aya sun d'auki mata ba'a bakin komai ba face property's nasu da zasu nayin dukkanin abunda sukaga dama dasu. Bata k'ara cewa komai ba ta miƙe tayi d'aki ta barsu nan tsaye suna binta da kallo. A idon mutane ana kallonta so reckless and impulsive, amma a zahiri ita d'in emotional mutum ce dake feeling hurt da dukkanin abunda ya faru. Duk da haka bata bari anyi amfani da wannan weakness nata ba a kanta. Tana nunawa kowa she's this strong and independent d'in kanta babu abunda yake damunta. Hawayen daya zubo daga idonta ya sake proving she's as weak and emotional kaman Mom amma ta goge wayen da sauri very harshly. Kai tsaye banɗaki ta shige bayan ta shige d'akin ta. A gurguje tayi wanka ta fito saboda kiran sallah magriba da aka fara. Sanye da doguwar riga ta fito ta wanka da k'aramin tawul tana goge gashinta data wanke. Kan gadonta ta same Suliem zaune tana duba litattafenta da take karantawa na makaranta kafin yaran nan su saka ta fice bata gama karatun ba. Murmushi tayi tana kallon Suliem ta k'asaro wajen single bed d'in ta don ta kimtsa shi. Miƙewa tsaye Suliem tayi tana kallon gefen fuskar tata da har zuwa lokacin da shatin hannu gurin ya yi jaa sosai. A hankali tace “Me yasa ki ka yi haka, Ajwaah?” Gira Ajwaah ta d'aga cikin ko in kula tace “Me nayi?” Numfashi Suliem ta sauke tace “kalli fuskar ki har yanzu yatsun hannun sa na nan. Me yasa ki k'ara tunzura zafin ransa?” D'an b'ata fuska Ajwaah tayi tana d'aga books nata daga kan gadon tace “ki na kallo yana k'ok'arin dukan Mamaa. Bazan iya tsayawa ina kallo ba” “ kuma gashi nan ke ya daka ba Mamaa ba. Kinsan waye Babaah da yanda yake very violent a kanmu. Babaah baya d'aukan raini. Mamaa tayi gaskiya data ce wata rana zai iya kashe mu saboda harshen ki. Da kin bari Mamaa zatayi handling nashi kaman yanda ta saba why ki ka shiga abunda bai shafe ki ba?” Juyowa Ajwaah tayi da k'arfi. “handle him?da cewar ta na ya yi hak'uri kan abunda batayi ba ta kuma taci duka a banza shine ki ke cewa handle him?. Nafa d'an d'ana abincin babu abunda ya yi yawa ko ya rago a ciki for God's sake. Komai ya yi daidai. Kawai yana neman hanyar da zai sauke b'acin ransa ne kan Mamaa saboda ita ce easy target nashi. Na rasa me yasa har yanzu take zaune da mutum kaman Babaah, in nice Mamaa tuni na gama zama dashi wlh his a devil” “Ajwaah, kula da bakin ki” Suliem ta fad'a da d'an fad'a tana tsoro mahaifin nasu zai iya dawowa gida yaji maganganun da Ajwaah take. Wa ya tab'a tunanin mutum kaman mahaifinsu wanda bai rasa komai ba zai kasance haka cikin gidansa?. Wannan ita ce gaskiya. Dabi'u basa chanzawa da kyakkyawan suna ko kuma kyakkyawan guri. Wannan gwaji da Maza da yawa suke na dabi'u marasa kyau saboda matan su basu haifa masu yara maza , haka mahaifin su Khalid na daga cikin irin wannan jimla na maza. Ajwaah ta girgiza kai idanta ya cika da hawaye tace “na kasa yarda daku duk ku biyun” Wuce Suliem tayi har tana d'an buge ta da kafad'a. Matsawa Suliem tayi ta bata hanya ta wuce. Kwaba nata ta buɗe ta d'auko doguwar riga ta saka kirar dubai mai adon stone daga sama. K'aramin hijabi daya tsaya mata iya wuya ta d'ura da mayafi ta suri dadduma da Al'qurani ta fito ta bar Suliem na kallonta ta baya wajen d'an garden nasu da suke shan iska. Saida tayi sallah ta jima tana Addu'a sannan ta buɗe Qur'ani tana karantawa don ta samu sauk'in zafi da tukukin da zuciyarta yake. ──────────────────────── 𝖠𝖡𝖴𝖩𝖠 Ido ya zubawa wayarsa kaman ya kasa gasgata yawan followers nashi na IG dake k'aruwa duk sakan d'aya. Mugun smirk ya saki yana k'ara shiga gallery nashi . Cikin hutunan sa ya zab'o wani da bashi da riga a jikinsa ya sake uploading. Kafin kiftawar ido hoton ya cika da uban likes da comments. Kaf saida ya bi comments d'in ya karanta ko wanne murmushi nashi na k'aruwa sama dana baya ďaya wuce. Sosai yake jindad'in yanda mata duk suka rikice suke zubda miyu kansa sai aiko masa da text na kishi suke kaman 𝑤𝑎𝑦𝑦𝑜 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ, 𝑘𝑎𝑛𝑎 𝑑𝑎 𝑘𝑦𝑎𝑢 G𝑜𝑟𝑎𝑦𝑒𝑛 𝑐𝑖𝑘𝑖𝑛 𝑠𝑎 wayyo. 𝑧𝑎𝑘𝑎 𝑧𝑎𝑚𝑎 𝑛𝑎𝑤𝑎. 𝑀𝑟.𝐻𝑎𝑛𝑑𝑠𝑜𝑚𝑒? 𝑧𝑎𝑘𝑎 𝑎𝑢𝑟𝑒 𝑛𝑖 𝑦𝑎𝑟𝑜 𝑚𝑎𝑖 𝑘𝑦𝑎𝑢? Comment d'in karshe shiya bashi dariya har saida ya dara 𝑤𝑎𝑑'𝑎𝑛𝑛𝑎𝑛 𝑦'𝑎𝑛 𝑚𝑎𝑡𝑎 𝑑𝑎 𝑚𝑎𝑓𝑎𝑟𝑘𝑖 𝑛𝑎𝑠𝑢). Koma waye ya rubuta bai yi k'arya ba. Abu ne da yake so banbarakwai wajan Far'aan kan irin wannan statement. Amma yanda mata suke mutawa a kan fuskar sa, ingarman jikinsa yafi komai sashi farin ciki. Fuskar sa da jikinsa sune tarkon sa da yake juya y'an mata yanda yaga dama yana juya su kaman waina a tander. “Me ka ke wa murmushi?” D'ago kai ya yi ya kalli babban matar dake zaune a gabansa wacce zata haura shekara 40 zuwa 50. Uban heavy makeup da janbakin dake fuskarta, bai b'oye tsufa da shekarun da take son b'oyewa ba, don duk da haka kana hango tattarar fatar ta. Yanda ta dage wajen ganin ta maida kanta yarinya ta sanya skin-tied white top da jan wando shima bai taimaka ba sam. Sai mayafi jaa data d'ura kan gashinta daya fara furfura ta gaba amma anyi masa deyin ya zama jaa. Ganin bai bata amsa ba ta miƙe ta fisge wayar daga hannun sa. Ya fito yawon shak'awata ne da ita wanda turawa ke cewa DATE. Yanzu haka suna wani kebantaccen restaurant ne kuma wajen tsakiyar dare ne. Ya d'an firgita da yanda ta warce wayan amma yaja dogon numfashi don saita nutsuwar sa yace “Ina so ne kawai na d'auki kyawun ban mamakin matar dake zaune tare dani da kuma cikin zuciyata” Ya yi magana cike da yaudara tare da kashe mata ido d'aya. Nan da nan kuncinta ya fara ja tana fara wani munafukin murmushi wai ita kunya. Da katuwar muryarta da take ta nokewa ita dole yarinya tace tana wasa da gashinta cikin yatsan ta “to me yasa har yanzu nake zaune a gabanka ka kasa yin komai a kai?” “saboda ina so na haddace ko wane dak'ik'a dake, mai kyau ” Ya sake kasheta da wasu mayaudaran kalamai a zuci kuwa yana shek'a dariya. Aikuwa fuskarta ta sake wani mugun jaa tsabar bilicin, ta kai hannu ta mintsine shi a k'irji suka saki dariya gaba d'ayan su. A b'oye ya sauke ajiyar zuciya ganin plan nashi ya yi aiki. Da sauri ya d'auki hoton nata yana murmushi. Ya gode Allah da yasa bayan kyawun sa da hadad'd'en jikinsa abu na biyu da yake ji dashi shine kwakwalwar sa. Yasan raunin matan kaf tun daga kan budurwa har zuwa manyan mata kaman wannan matar domin ya yi mastering a kansu k'arshe. Wannan matar kusan rabin shekarun ta yake, yasa babbar mace bazawara ta mutu a soyayyar sa ta karya. Yana samun abunda yake buk'ata ne. Wato kuɗi da kuma kyaututtukan da basu da iya ka. ❝ Hmmmm omo readers. Kuna hango abunda nake hangowa kuwa?🤔. I'm proud to say wannan tafiyar ta musamman ce you will not regret reading inshaAllahu. ❞ * . °•★|•°∵ TAURA BIYU ∵°•|☆•° . * ®𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵𝓸𝓿𝓮 18+ 【Pg5&6】 Zama ta gyara tana k'ara matso da kujerar ta sosai kusa da tashi. Hannun sa ta rik'o cikin nata fuskarta babu wasa tace “kana ji ko Darling?.” “yeah , Baby.” Ya bata amsa gabansa na d'an fad'uwa saboda chanjin ta lokaci guda. K'ara matsowa tayi kaman zata shige jikinsa tace “lokaci ya yi daya kamata muyi Aure. Kaga ni ba yarinyar bace ,lokaci ya yi daya kamata na sake settling waje d'aya ” Wani irin murmushin mugunta ne ya kusa kubce masa ya yi maza ya matse shi. Anzo wajen. Tsira mata ido ya yi kaman mai tunanin sai kuma ya d'an sake fuska kaman mara lafiya yace “me yasa ki ke so muyi aure yanzu Baby? Kin manta bani da aiki, bani da komai?” Kai ta girgiza cike da so da tausayi ta shafa fuskarsa tana cewa “wannan ba matsala bane Darling. In har mukayi aure zan baka dukkanin abunda ka ke buk'ata. Dukiya ta taka ce” Murmushin da yake ta b'oyewa ne ya kwace masa saida hak'oransa suka fito. Wani shegen kallon ya mata na yaudara ya kai hannunta wajen bakinsa ya sumbata. “duk yanda ki ka ce Baby haka zamu...” Ding. K'arar sak'on daya shigo wayarsa ya hanashi k'arasa maganan da yake. D'an murmushi ya mata na ban hak'uri ya zaro wayar daga aljihun wandon sa yana duba sak'on. Gabansa ne ya yanke ya fad'i saboda ganin number da kuma sak'on da aka turo kaman haka. '𝐹𝑎𝑟'𝑎𝑎𝑛. 𝑊𝑙ℎ 𝑘𝑎𝑟 𝑘𝑎 𝑘𝑢𝑠𝑘𝑢𝑟𝑎 𝑘𝑎 𝑘𝑎𝑖𝑛𝑖 𝑏𝑎𝑛𝑔𝑜. 𝐾𝑎𝑟 𝑘𝑎 𝑚𝑎𝑛𝑡𝑎 𝑚𝑢 𝑚𝑢𝑡𝑎𝑛𝑒 𝑛𝑒 𝑑𝑎𝑘𝑒 𝑟𝑎𝑦𝑢𝑤𝑎 𝑎 𝑑𝑢𝑛𝑖𝑦𝑎 𝑑𝑎𝑏𝑎𝑛 -𝑑𝑎𝑏𝑎𝑛 𝑘𝑢𝑚𝑎 𝑑𝑢𝑘 𝑑𝑎 ℎ𝑎𝑘𝑎 𝐴𝑙𝑙𝑎ℎ 𝑦𝑎 𝑦𝑖 ℎ𝑢𝑘𝑢𝑛𝑐𝑖𝑛 𝑠𝑎 𝑚𝑢𝑘𝑎 ℎ𝑎𝑑'𝑢 𝑛𝑖𝑑𝑎 𝑘𝑎𝑖. 𝐾𝑎𝑟 𝑘𝑎𝑦𝑖 𝑡𝑢𝑛𝑎𝑛𝑖𝑛 𝑘𝑜 𝑛𝑎 𝑠𝑎𝑘𝑎𝑛 𝑑'𝑎𝑦𝑎 𝑏𝑎𝑧𝑎𝑛 𝑖𝑦𝑎 𝑏𝑖𝑦𝑜 𝑘𝑎 ℎ𝑎𝑟 𝑖𝑛𝑑𝑎 𝑘𝑎 𝑘𝑒 𝑏𝑎. 𝐷𝑜𝑛 𝑘𝑎 𝑔𝑢𝑗𝑒 𝑚𝑢𝑛 ℎ𝑎𝑘𝑎𝑛 𝑏𝑎𝑧𝑎𝑖 ℎ𝑎𝑛𝑎𝑛𝑖 𝑠𝑎𝑚𝑜 𝑘𝑎 𝑏𝑎 𝑑𝑢𝑘 𝑖𝑛𝑑𝑎 𝑘𝑎 𝑘𝑒 𝑓𝑎𝑑'𝑖𝑛 𝑑𝑢𝑛𝑖𝑦𝑎𝑟 𝑛𝑎𝑛. 𝑇ℎ𝑒 𝑤𝑜𝑟𝑠𝑡 𝑎𝑏𝑢𝑛𝑑𝑎 𝑘𝑎𝑦𝑖 𝑠ℎ𝑖𝑛𝑒 𝑏𝑎𝑟𝑖𝑛 𝑛𝑢𝑚𝑏𝑒𝑟 𝑛𝑎𝑘𝑎 𝑘𝑎 𝑘𝑒 𝑎𝑚𝑓𝑎𝑛𝑖 𝑑𝑎 𝑖𝑡𝑎 ℎ𝑎𝑟 𝑦𝑎𝑛𝑧𝑢. 𝑖𝑛𝑎 𝑠𝑎𝑘𝑒 𝑏𝑎𝑘𝑎 𝑑𝑎𝑚𝑎 𝑘𝑎 𝑘𝑖𝑟𝑎𝑛𝑖 ,𝑖𝑛 𝑏𝑎 ℎ𝑎𝑘𝑎 𝑏𝑎 𝑤𝑙ℎ 𝑧𝑎𝑛𝑧𝑜 ℎ𝑎𝑟 𝑖𝑛𝑑𝑎 𝑘𝑎 𝑘𝑒 𝑛𝑎 𝑡𝑜𝑛𝑎 𝑚𝑎𝑘𝑎 𝑎𝑠𝑖𝑟𝑖 𝑤𝑎𝑗𝑒𝑛 𝐷'𝐴𝑁 𝑈𝑊𝐴𝑁𝐾𝐴. 𝐷𝐴𝑁 𝐼𝑆𝐾𝐴 𝑀𝐴𝑌𝐴𝑈𝐷𝐴𝑅𝐼' Gaba d'aya duk wani annuri dake fuskarsa ya d'auke. Wai me yasa yarinyar nan take neman sake shiga rayuwar sa ne tana neman kawo masa matsala?. “menene Darling?,waye?” Wani irin hucin numfashi ya sauke ya d'ago ya watsa mata manyan idanuwansa da suka fara riked'ewa yana k'ok'arin miƙewa tsaye yace “I'm sorry Baby, Dad nawa ke nemana. Muhimmin abu ne ya taso shi yasa zan tafi, in ba haka ba kin san ko Dad nawa bai isa ya sani barin ki ba” Kai ta d'aga cike da fahimta ta mik'a masa mukullin motar tana cewa “shikenan ka tafi da motar kawai ,idan ka gama ka dawo da ita” “are you sure Baby?, ke kuma fa?” “kar ka damu zansa a kawo min wata yanzu. Kaje kawai da ita” Zagayowa ya yi inda take ya sumbaci goshinta da kumatunta yana cewa 'I love you Baby '. Aikuwa bakinta kaman zai yage tsabar murmushi. Nan ya barta ya tafi yana dariya can k'asan ransa. ──────────────────────── Kai tsaye office nashi ya nufa daga Theatre . A gajiye yake tubus dan tun past 6 suke cikin Theatre suna aiki. Yau Su'ad bai biyoshi ba ya barshi can masaukin su. Yana shiga office nashi ya fara cire kayansa yana jifa dasu. Kan wata k'atuwar cushion ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya daga shi sai dogon wando da rigar sa daya b'alle botiran ta duka. Faffad'an k'irjinsa da cikin sa da gumi yake d'an bi a waje tabarakallah. Hannu ya kai ya cire mask dake fuskarsa wadda take a fuskar ko da yaushe kaman ibada. MashaAllah dole ya dinga saka mask. Numfashi ya fesar a hankali ya maida manyan black eyes nashi ya rufe. Kaman jiran shigowar sa Office d'in ake kuwa wayar shi ya fara ringing. K'aramin tsaki yaja ya mik'a hannu a kasalance ya zaro wayar daga aljihun wandon sa. Miss calls ne rututu kan wayar musamman na Far'aan da Su'ad sai kuma Dad nashi wanda shi yake sake kira yanzu haka. Saida wayan ta kusa tsinkewa sannan ya d'aga ya kara a kunne kafin yace wani abu aka rigashi daga d'aya b'angaren “𝑰𝒏𝒂 𝒌𝒂 𝒔𝒉𝒊𝒈𝒂 𝒏𝒆 𝒕𝒖𝒏 𝒔𝒂𝒇𝒆 𝒊𝒏𝒂 𝒌𝒊𝒓𝒂𝒏 𝒌𝒂 𝒃𝒂𝒌𝒂 𝒅'𝒂𝒈𝒂 𝒃𝒂?” Saida ya fesar da wani numfashi ya kai hannu ya tura cikin gashin sa ya yamutsa sannan yace “ina cikin Theatre.” Daga yanda ya yi maganan zaka san babu wata shak'uwa ko kad'an tsakanin su ta d'a da uba. “𝑶𝒌, 𝒚𝒂𝒖𝒔𝒉𝒆 𝒛𝒂𝒌𝒂 𝒔𝒉𝒊𝒈𝒐 𝒈𝒂𝒓𝒊?.” D'an jim Asad ya yi kaman mai tunani kafin yace “zuwa next week zan gama aikina a nan inshaAllahu, amma daga nan zan wuce Mexico ,akwai wani abu ne?” “eh da da hali ina so kazo maganan Auren Hassan. Akwai yarinyar abokina Alh Khalid da nake so yaje ya ganta su daidai ta. Da kai nace zan nemawa ita to kuma sai nayi tunani shi Hassan shi yafi buk'atar auren yanzu ko Allah zaisa ya nutsu tunda ance aure mai gyara mutum. Idan zai yi yu ka fara shigowa ka rakashi yaje yaga yarinyar don su daidai ta da wuri saboda ina so ayi auren ne cikin d'an k'ank'anin lokaci. Daga b'angaren yarinyar dai basu da matsala Hassan ne dai nasan zai iya bada matsala shine Babba amma ka fishi hankali Hussein. Shi yasa nake so kazo komai ya kasance da kai za'ayi ” Shiru Asad ya yi yana sauraran Mahaifin nasu. Tabbas ta wani b'angaren Dad nasu yana da gaskiya shima wannan kule-kule matan da Far'aan yake sosai yake damunsa. Gashi yaki tsayawa ya maida hankali ya nemi aiki kullum sai yawace-yawace da bazasu amfane shi da komai ba. Fesar da huci ya yi mai zafi yace “shikenan zan shigo next week d'in inshaAllahu.” “yauwa to shikenan Allah ya kawo ka, amma kar ka gaya masa tukun sai kazo.” “ok.” Daga haka ya kashe wayarsa bai jira mahaifin nashi ya sake cewa komai ba. Komawa ya yi ya kwanta yana wasi-wasi cikin ransa. Anya Far'aan zai amince da wannan auren kuwa?. Sama da minti biyu ya yi haka a kwance ya yi zurfi cikin tunani. Lokaci d'aya ya fara sauke wani irin nishi kaman mai shirin tada asma ya fara had'a wani irin zufa kace cikin oven aka sakashi. Da kyar ya yunk'ura ya miƙe tsaye ya nufi tebir nashi yana wani irin nishi kafin ya kai kuwa ya zube k'asa tim saida rarrafe ya k'asara. Jikinsa gaba d'aya na rawa ya buɗe cikin drawer ta tebir d'in ya fito da wasu magunguna ya watsa cikin baki ya taune ko tunanin ruwa baiyi ba. Maimakon ya samu sassaucin abunda yake ji kaman wanda aka k'ara masa ciwo haka ya zube k'asan wajen yana ta juyi da murkususu. ──────────────────────── Hadari ne ya had'u ganga-ganga sai tsawa da walk'iya ake ga iska da ake kaman zata d'auke mutum, amma Ajwa tana zaune d'an garden nasu bata da niyar tashi bare ta shiga gida. Sanye take da doguwar riga Ash mara nauyi sai hula data d'ura a kanta ,tun la'asar ta fito karatu saboda exams da zasu fara next week. Saboda rashin nutsuwa da kwanciyar hankali sam ta kasa maida hankali tayi wani karatun kirki. Kai ta d'aga ta zubawa sararin samaniya ido tana kallon yanda ake ta zuba walk'iya garin ya had'e sosai ya yi bak'ikk'irin daga nesa kana jin masallatai nata jera kiran sallah magriba. Dis,dis ruwa ya fara sauka kan fuskarta ta maida ido ta lumshe tana sauke ajiyar zuciya. “Ajwa, wai baza ki shigo ciki ba kina kallo an fara ruwa.” A hankali ta juyo inda Suliem d'in ke tsaye bakin realer da faranti a hannunta dake d'auke da flask da cup na shayi zata kaiwa Babaah. D'auke kai Ajwa tayi bata bata amsa ba ta cigaba da kallon sama ga ruwan ya d'an fara k'arfi. Suliem ta k'ara cewa “kina jina fa ko Ajwa. Kinsan ke ba cikakkiyar lafiya ce dake ba baki son sanyi ko. Ki dawo ciki” Murmushi Ajwa tayi mai ciwo tace “waye zai so ya dinga kwanciya cikin wannan kurkukun gidan idan ba kaddara ba?. Nan d'in yafi mun cikin gidan sau dubu ko babu komai, mutum yana da y'anci kansa.” “Ajwa” Suliem ta kirata da d'an tsawa “baki da hankali ko?.” “eh bani da hankali Suliem. Na gaji,na gaji. Bazan iya cigaba da rayuwa haka ba. Bazan iya cigaba da rayuwa cikin wannan prison d'in ba. Daga makaranta sai gida ,haba. Ko sau d'aya Babaah bai tab'a yi mana magana da dad'in rai ba. Duka, fad'a, hantara, cin Mutunci da kuma controlling namu shine abunda kad'ai muka sani tunda muka fara mallakan hankalin kanmu saboda me? Saboda mu ya'ya mata ne ba maza ba kaman yanda yake so? To wai shine yake bada haihuwar nan ne, ko shi ya isa ya zab'awa kansa ya'ya maza ne?” Jikin Suliem ya d'an yi sanyi ganin hawaye nabin kuncin Ajwa. Duk cikin su itace mai k'arfin zuciya dake shanye dukkanin wasu kalub'ale da suke fuskanta daga wajen Babaah, ko sau d'aya bata bari abunda Babaah yake musu ya sata kuka saboda ita ke k'arfafa musu gwiwa. “me zamuyi Ajwa? Wannan ita ce kaddarar mu. Babaah bazai tab'a sanmu ba amma bawa baya fidda rai ga hukuncin ubangiji. Wata rana sai labari inshaAllahu. Ki yi hak'uri ki shigo ciki ruwan yana sake k'arf... ” Ko kafin ta k'arasa maganan wani mahaukacin ihun Mom yasa ta saki farintin dake hannun ta kafin tayi wani yunk'uri tuni Ajwa ta wuceta da bala'in gudu ta rufa mata baya suka haura sama. A haukace Ajwa ta kai hannu jikin k'ofar d'akin Mama tana bugu da jijjaga handle d'in tana kiran Mama kaman zata tsaga mak'ogaronta. Wani irin bud'e k'ofar a kayi daga ciki ta daki bango kaman zata b'alle. Babaah ne ya fito sanye da jallabiya sai zuba huci yake . Daga Ajwa har Suliem saida gabansu ya yi wani mummunan fad'uwa yanayin da suka ga Babaah d'in. Tuni Suliem ta mak'ure jikin bango tana wani irin kuka kaman ranta zai fita. Ajwa kam k'ok'arin ratsa shi take ta kutsa d'akin ya wani fisgo jelar gashin kanta ya dawo da ita baya da mugun k'arfi ya buga da bango yana cewa “don uwar ki kece mai tsaurin idon da zaki wuce ni ki shiga ciki har kina k'ok'arin tureni ? Mara kunya fitsararriyar yarinya mai bak'in hali. Duk iskancin dake kan ki zan sauke miki shi don uwar ki. ” K'ara fisgota ya yi ya k'ara had'awa da bango da mugun k'arfi. Duk yanda Ajwa ke danne tsananin azaban da take ji yanzu saida ta saki ihu don ba k'aramin buguta ya yi ba. Wayyo kar kuso kuga Suliem kaman zata shid'e da kuka har fitsari ta fara saki a tsaye. Mom data farfado ta yunk'ura da sauri ta miƙe daga inda take yashe ta suri kayanta jikinta na wani irin rawa ta saka ta fito da dogon hijabi. Tana saka hijabin hannunta na mata wani irin zugi kaman zata saki fitsari. Tana had'a hanya ta fito daidai Babaah na sake had'a Ajwa da bango da wani mugun k'arfi. Bata san sanda tayi wani haniniya ba ta nufeshi da bala'in gudu tana ihu. Wani jifa ya yi da ita gefe ya juyo ya watsawa Mom mugun kwallo da kwafa ya wuce fuu kaman iska. Janyo Ajwa tayi da bata wani motsin kirki ta rungume tana kuka kaman ranta zai fita. Zakuyi mamaki idan nace idan Ajwa ko d'ar babu ruwan hawaye sai numfashi kawai da take saukewa saboda tsananin azaba idon ya yi jazur . Da kyar ta mik'a hannu ta gogewa Mom hawayen dake gudu kan fuskarta. Aikuwa hawayen suka cigaba da gudu kaman an bud'e fanfo. Suliem dake gefe ita ta matso kaman zata shid'e Mom ta had'asu ta rungume. Sun jima a haka kafin Mom ta yunk'ura da taimakon Suliem suka kama Ajwa da jikinta ya fara zafi alamun zazzab'i. Ruwa Suliem ta fara had'a mata na zafi tayi wanka ta d'an gasa jikinta ta fito da

Chapter 2 of 15