wuce kitchen saboda kallon Nonna har tana tuntube. Tana shiga ta iske sai hira suke suna girki suna ta shewa abunsu da yiwa juna tsiya. Da farko data kama musu girkin kaman kace kyet ta kwasa a guje sai d'ari-d'ari take. Duk suna lura da ita amma sukayi banza da ita sai ita dan kanta ta ware kuka sai gata tana kwasar dariyar labarin da Reemah ke basu. Suna gab da gama girkin suka jiyo muryar Nonna tace cewa
“aa mijina ,mijin k'arfe lfy lau an tashi lafiya? Fita zakayi ne?”
Da wannan deep voice nashi Ajwa taji yace
“eh Nonna, anyi tafiya ne zuwa Dubai ”
“Aa yanzu yanzu haka?, to Allah ya kai ka lafiya ashe kai zaka rigamu tafiya ma. To ubangiji ya yi albarka ya bada nasara inda aka je nema”
Gaba d'aya harsu Mom suka amsa da Amin. Addu'ar kuwa sosai tayi masa dad'i. Da alama kaman ita yake nema ne taji Nonna na cewa tana
“shiga kitchen d'in tana ciki”
Wani irin zabura Ajwa tayi ,tayi saurin ajiye apple d'in dake hannun ta zata yanka ta matsa gaban sink ta wake hannu da sauri ta juyi zata fito, sai dai kafin ta fito ya sawo kai cikin kitchen d'in in all his glory. Gaba d'aya sai taga ya wani cike k'ofar. Wata arniyar dark blue suit ce a jikinsa three pieces da tayi masifar kama faffad'an k'irjinsa. Hannun sa d'aure da dank'areren diamon Rolex. Sai jaka ta matafiya dake goye bayansa. Gashin kasuwa ya tufke shi daga tsakiya ya jeyar ya sake shinya zubo bayan wuyansa. Ga fuskarta tashi sanyi da farin glass daya zauna rad'am kan dogon hancinsa. Wayyo kyan da ya yi ita kanta bata san sanda ta d'an bud'e baki ba tana kallonsa amma idan su na had'uwa tayi saurin sauke nata k'irjinta na harbawa. Nufota ya yi kaman baison takawa yana masu Suliem murmushi dake gaishe shi. Tsintar kanta tayi tana ja da baya har ta had'u da sink daidai yana tsayawa gabanta ya wani rufeta gaba d'aya ko hangota su Reemah basayi sai kunshe dariya suke sun cure guri d'aya kaman zasu shigewa juna.
Kasa kallonsa sa tayi ta sunkuyar da kai kasa don bazata iya kallan saba saboda rashin kunyar daya aikata mata jiya. Ita kanta mamakin yanda ta kasa yi masa komai tayi. Hannun sa taji ya d'ago habarta dashi dole tasa ta kalleshi. Kaifin idansa da sakon daya fito daga nashi ya shiga nata ta kasa jurewa tayi saurin rufe idonta. Ji tayi kaman ya sake matsowa kusa da ita sai kuma taji maganan sa sosai kusa da bakinta a hankali yana cewa da wata irin murya
“zan tafi Dubai yanzu. Akwai wani abu da ki ke buk'ata?”
Yanayin yanda ya yi maganan yasa dole ta buɗe ido ta sakashi cikin nasa. BADUM,BADUM,BADUM zuciyarta ta fara fidda wani k'ara na daban. Bata san sanda ta d'an girgiza masa kai ba a d'an shagwabe. Babban yatsan ya kai ya shafa gefen bakinta ya k'ara cewa a mugun hankali
“are you sure?”
A hankali ta sake d'aga masa kai suka sake kafe juna da ido sannu kuma a hankali yana sake matso da fuskarsa wajen ta ta har ya had'e bakinsu da wani irin deep French kiss. Wani uban ihu Su Nuriyahh suke harda tsalle kaman wadda aka ce musu an basu Aljanna. Sai kaname juna suke kace suna dariya ita da Reemah banda Suliem dake kallon bayan Asad idonta cike da hawaye. Murmushi tayi wanda aka ce yafi kuka ciwo. ASAD shine wanda ta so kuma ta mutu a sanso tun bayan data tab'a ganin hoton sa shida Far'aan daya d'ura. Lokacin da suka zo neman auren bayan ta gansu tayi tunanin Asad ne sai da taji Su'ad na kiran Far'aan sannan ta gane ba Asad ne zata aura ba. Ta shiga cikin tsaka mai wuya matuk'a sai kuma Allah ya dubeta Far'aan d'in yace ya fasa aurenta. Kukan datayi sosai na farin ne ciki don a ganinta kaman tana da wata daman da zata samu soyayyar Asad. Sai kuma Allah ya yi shima ba mijinta bane na Ajwa ne. Har yau tana fama da soyayyar sa amma Alhamdulillah ba kamam daba a yanzu tafi kowa farin cikin irin soyayya da kulawa da Asad ke bawa Ajwa. To dama ance' a broken hearts take some time to heal.' Bazata gushe ba zata cigaba da Addu'a har Allah ya cire mata sanshi gaba d'aya daga cikin ranta. Wannan wane sirri na nata ita kad'ai sai Mahallicin daya sani. Ita tasan Allah na sane da ita kuma wannan wata jarabawa ce a gareta da take fatan cinyeta with full marks.
Ihun su Nuriyahh da Reemah baisa Asad ya daina kissing Ajwa da wani irin kaman zai cinyeta. Da alama tunanin sa da hankalin sa sun gushe saida yaji tana dukan k'irjinsa a hankali sannan ya wani janye bakinsa daga nata ya d'an fitar da pop k'ara yawunta da nashi ya biyo gefenta ya kuwa saka harshe ya lashe. Da azama ta tureshi k'afafuwanta suna rawa tayi baya luu zata fad'i ya yi saurin taro kugunta ya dawo da ita k'irjinsa ya matse ta tayi saurin d'ura duka hannuwanta kan k'irjinsa.
“Ehhhhhhhhiihhhhĥhh”
Reemah da Nuriyahh suka saki wani munafukin ihu suna tsalle kaman agwagwi. Saida Asad ya yi y'ar dariya ya janye Ajwa da tayi mutuwar tsaye daga k'irjinsa ya juyo yana kallonsu. Wayyo kaman zasu shid'e. Dariya ya sakeyi yana girgiza ya sake kallon Ajwa ta gefen ido kafin ya kama hannunta ya saka mata Atm card nashi da sake sumbatar goshin sannan ya saka kai ya fice abunsa. Wayyo yana fita suka sake rushewa da wani uban ihu da wani uban tsalle
“ahhhhhhhh, wayyo soyayya ruwan zuma. Wannan shine ko a film ko romantic novels albarka. Ahhhhhhhhh”
Firgigit Ajwa ta dawo tunanin ta a guje ta kwasa zata fice daga kitchen d'in Reemah ta tare ta.
“wai ihun me ku ke haka ne kaman wasu tabab'bb'u?”
Nonna ce tayi magana daga can falo Ajwa ta samu dama ta kwasa a guje ta fito daidai su Baffa na sawo kai ciki duk sun shirya cikin manyan kaya. Kowa ka gani fuska cike da annuri banda Babaah da duk ya yi wani zuru-zuru kaman wanda ya shekara a kwance yana ciwo. Duk babu wanda bai lura da yanayin Babaah ba kafin wani ya yi magana Nonna ta rigasu
“Khalid lafiyar ka kuwa duk ka fita hayyacin ka kaman wanda ya shekara a kwance? Ko baka da lafiya ne?”
Saida ya yi d'an yak'e ya kalli Mom da ku kurar data deboshi bata kalla ba yace
“walahi Nonna jiya kwana nayi da zazzab'i ne bansan me yasa ba ko chanjin waje ne”
“hakan zai iya kasance kuwa. Allah ya k'ara lafiya amma idan kaga bakaji sauk'i ba gwanda muje muga likita”
Abba ne ya yi maganan yana kallon Babaah daya girgiza kai yace “aa na warware fa. Ai tun jiyan nasha panadol”
Ajwa bata tsaya ta gama jinsu ba ta haura sama da sauri bayan ta gaishe su.
────────────────────────
ᴅᴜʙᴀɪ
K'arfe hud'u daidai ya sauka babban birni na Abu Dhabi. Kai tsaye daga nan Airport motar dake jiransa tayi asibiti dashi. Yana zuwa ko hutawa baiyi ba suka shiga aiki. Bashi ya fito ba sai wajen goma duk ya gaji amma can ransa yana ta Allah-Allah ya kira Ajwa. Office da aka fara bashi kafin ya tafi masaukin sa nan ya fara shiga don d'aukan jakarsa. Yana shiga ya sandare a tsaye saboda fuskar da bai tab'a tunanin zai sake ganinta ba cikin rayuwar sa zaune cikin office d'in. Yanda yasan fuskar a da da kyau da gayu yanzu abun ya chanza duk taci wani uban surgery banda ma ya yi mata farin sani bazai tab'a gane ta ba. Tana ganinsa ta miƙe da sauri tana masa murmushi wanda a da yake tsananin jefashi cikin shauki amma a yanzu ji ya yi kaman zaiyi amai ransa ya mummunan b'aci. A kausashe ya kira sunan ta
“AYAH?”
Nufoshi tayi taja murmushi Sam bata damu da yanda ya kirata da kaushin murya ba. Da yar siririyar murya tace
“Asad, Hi”
Har ta k'araso gabansa yana mata wani mugun kallo. Saurin kaucewa ya yi ganin ta kawo kai tana shirin rungume shi. Wata mahaukaciyar tsawa ya buga mata
“ke ,what do you think you're doing?”
Yanzu gabanta saida ya d'an buga amma duk da haka tana bawa zuciyarta soyayyar ta tana nan cikin zuciyar Asad. Kawai b'acin rai ne yasa yake fushi da ita. Murmushi tayi mai kama da yak'e murya a raunane tace
“kayi hak'uri Asad nasan nayi maka laifi na gane kuskurena don Allah. Tunda naji labarin zakazo Dubai nake ta zaman jiran zuwan ka saboda ina so na baka hak'uri na gaya maka nayi nadaman abunda nayi ma mu maida soyayyar mu”
Kafin ta k'arasa ya wani tare ta da tsawa “are you mad? Bibiyata ki ke? Are you a stalker?Da auren naki ki ke kiran muyi soyayya dake?.”
Anya kuwa wannan Asad d'in ta ne. Asad da ko kallon baza baya iya mata bare wani ya d'aga mata murya a gaban sa amma yau shine yake mata ihu haka. Asad baya jure ganin hawayenta nan da nan zai shiga tashin hankali don haka ta matso hawayen dole tana kallon Asad. Wani irin hucin numfashi ya sauke har ta d'an saki murmushi sai taga ya juya a zafafe ya buɗe k'ofar da kyau ya juyo ya watsa mata mugun kallo.
“get out.”
Baki ta hangame cikin matsanancin mamakin sa
“Asa..”
“get out.”
Kafin ta k'arasa kiran sunan nashi ya buga mata wata muguwar tsawa da bata san sanda ta zo ta wuce a guje ba har tana tuntube. Mugun tsaki yaja ya maida k'ofar ya rufeta bam. Ji ya yi ma bazai iya zaman office d'in ba saboda kamshi turarenta da duk ya cika office sai hawar masa kai yake. Jakarsa kawai ya fisga ya fito daga office d'in. Abun mamaki yana fitowa harabar wajen ya sameta zaune a wajen. Tana hangoshi ta sake nufoshi da sauri ya yi maza ya fad'a motar dake jiransa kafin ta k'arasa sun bar gurin sai kurar motar da suka bad'eta da ita. Baki a sake tabi motar da kallo ranta na kuna. Ita Asad yake gudu kaman wata abar kyama? Shima fa auren fa ya yi sa yanzu haka ma da matar sa yake zaune, amma ita fa? Ai koma menene ya kamata ya duba uzurin ta ya bata dama a karo na biyu. Zakuwa ta cigaba da bibiyar sa koda zai kasheta har sai ya sakko ya gane har yanzu yana santa su dawo da soyayyar su.
𝗧𝗔𝗨𝗥𝗔 𝗕𝗜𝗬𝗨
®𝐀𝐬𝐡𝐚𝐧𝐭𝐲𝐥𝐮𝐯
/No edit!
【Pg29&30】
'Join exclusive @500 to
8140754777,
Aisha Sani Hassan.
Opay.
Free page's namu are counting!.'
Koda ya koma masaukin saboda b'acin ran Aya wanka kawai ya yi ,ya yi sallah ko tunanin abinci bai ba sai coffee kawai daya iya sha ya haye gado ya kwanta rik'e da wayarsa. Ajwa ya dannawa akira amma harta gaji ta iske ba'a d'auka ba ya sake danna mata kira still shima shiru babu amsa. Saida ya mata wajen kira hud'u bata amsa ba sannan ya hak'ura yana jin rashin dad'in d'agawa wayar. Wata k'ila ko tabar wayar a d'aki tana wajen su Mom. Su'ad ya kira dan yasan shima yana jiran wayan tashi idan ya sauka. Sun jima suna magana kan had'uwar sa da Aya da shawarwari da Su'ad d'in ya basa kafin sukayi sallama ya kashe wayar. Ajwa ya sake kira ko Allah zaisa ta d'aga har ya fidda rai don wayan tana gab da tsinkewa ta d'aga y'ar siririya muryarta ta biyo cikin kunnen sa da sallama. Wani numfashin Asad yaja ya fesar yana gyara kwanciya kan gado yaji tana
“Hello, wake magana?”
Saida ya d'anyi murmushi daya sa dimples nashi lotsa
“it's me”
Shiru ne ya ratso wayan ya sake d'an murmushi yana jan pillow k'irjisa yace
“Ina ki ka ajiye wayar tun daz'u ina kiran ki ,uhmmm?”
Daga b'angaren Ajwa baki tad'an cije ta miƙe a hankali daga cikin falon da suke ita dasu Nonna ana ta hira ta sulale ta koma d'aki. Saida ta mayar da k'ofa ta rufe sannan tace a mugun hankali ita kanta bata san yanda akayi ta bashi amsa ba. Kaman zuciyarta na firta abunda ke cikin ranta kuma yana tilasta mata fad'an shi. A hankali tace
“nasa wayan a ji ne banji ba”
“ok. How are you?. K'arfe nawa a nan?”
Saida ta zauna gefen gado tana dan juya yatsun hannun ta tace
“K'arfe biyu na rana”
“OK, ku kun juya kenan?. Munan dare ne na sauka tun yamma aikine ya hanani kiran ki. Hope duk kuna lfy ko?”
Da wani mugun hankali ta sake cewa “eh”
Kai wai meke damunta ne? Duk ina tsiwar da alwashin data ci kan zuba masa rashin mutunci har sai ya gaji da zama da ita ya sake ta dan kansa? Tun jiya badan su Nonna dake gidan ba jinta take kaman wacce wani abu gagaru ya sameta. Bini-bini tunanin Asad ya fad'o mata a rai. D'an fad'an nan nasu da bakaken maganganu da suke gayawa kansu sai taji duk tayi missing nasu. Jiya tunda ya tafi taki yarda ta amince zuciyarta tana jiran kiransa. Koya taji d'an motsin wayar zata d'auko ta duba ko shine sai taga akasin hakan. Saida tayi ta fad'a da zuciyarta sannan ta iya daurewa haka ta kwanta tana tunanin sa.
“I miss you”
Babu zato taji ya furta da wata irin murya da saida tsigar jikinta ta wani tashi yamm. A guje ta cire wayar daga kunne ta kashe ta koma da gudu ta fad'a gado k'irjinta na wani harbawa Badum,Badum,Badum. Hannu ta kai ta dafe saitin zuciyarta tana mamakin meke damunta ne? Ita kanta idan tasan murmushi ne kwance kan fuskarta bazata yarda ba amma wani irin murmushi ne kan fuskar tata bakin kaman gonan audiga. Pillow taja ta rungume a k'irji tana jin wani irin abu shiba farin ciki ba kuma bakin ciki ba. Kai ita kanta bazata ce ga taka maimai abunda take ji ba. Hayaniyar Nonna data jiyo kaman tana fad'a yasa ta miƙe a hanzarce ta fito falon
“wace maganan banza ce ki ke yi haka Maesha? Ban gane bazaki koma gidan mijin ki ba mu zaki bi?”
Turus Ajwa ta tsaya daga bakin benen tana kallon Mom data wani irin shan kunu fuskarta babu wasa tace
“yanda ki ka ji haka ne Nonna. InshaAllahu gobe tare zamu wuce Saudiya. Aurena da Khalid ya k'are tuntuni. Idan baki yarda ba gashi nan a zaune ya gaya miki”
Wani irin gumi ne ya karyowa Babaah murya na rawa yace
“tabbas tazo ta same ni sai na saketa ta daga min hankali. Nayi nayi ta gayamin abunda yasa take neman saki taki yanayin data shiga a lokacin na rubuta mata saki d'aya. Amma dama ina niyar da zarar mun koma gida zan maida ita”
A zafafe Mom tana masa wani irin mugun kallo tace
“babu batun kome nida kai. Aurena da kai ya k'are. Wlh kome za'ayi babu ni babu komawa gidan ka wanna rantsuwa ce nayi matsayina na musulma. Babu abunda zai sani yin kaffara. Nonna da Baffa kar kuce zaku shiga ko mana silhu ko kuce sai kunji ba'asin dalilin daya sa na yanke wannan hukuncin. Abu d'aya da zan iya fad'a muku shine a yanzu bana son shi. Dama ke nayiwa biyyayya Nonna na aure Khalid. Yanzu kuma Nonna bazan iya cigaba da danne zuciyata ina zama dashi ba alhalin ina cutar kaina. Wlh idan har kun dage sai na koma gidan sa zan d'auke Y'ata mu koma can wata duniyar da zama ko kuma na maka ku koto a kwatar min y'anci na”
Wani irin shiru falon ya d'auka kowa yana cikin dumbin mamaki da al'ajabi. Babu wanda ya tab'a ganin b'acin ran Mom sai yau bare har ya kaita ga d'aga murya haka. Shi kansa Babaah baki buɗe yana kallon Mom dake zuba huci fuskarnan ta ta tayi jazur. Gaba d'aya babu wanda bata d'aureba musamman Babaah da yake jin zuciyar sa kaman zata fito waje. Anya kuwa Mom babu wani abu data sani? Inba haka har ta tada jijioyin wuya haka kuma ta dage bazata koma gidan sa ba har tana cewa zata kaisu koto idan an tilasta ta?. Ganin kowa ya yi shiru yana kallonta ya juya fuu ta wuce d'aki idonta cike da hawaye amma ta hanasu zuba. Da azama Ammi da Aunty Raihana suka bita. Baffa da Abba suka dafa k'afad'ar Babaah da gumi keta karyo masa idan nan ya yi ja shima saboda b'acin rai. Babban bak'in cikin sa shine da bashi da ikon cin uban Mom yanzu.
Nonna kam tayi shiru amma jikinta duk ya yi sanyi. Zubawa Babaah ido tayi anya kuwa Khalid yana adalci zamansa da Measha?. Khalid kanin tane amma kuma Measha y'ar tace. Shin wane kuskure ne tayi tun farko? Ko kafin Abba yace wani abu ya miƙe da sauri ya fice daga falon suka bishi da kallo. Daga Ajwa harsu Suliem dake zaune falon babu wanda ya yi motsi sai bayan fitar Babaah. Ajwa ji tayi kaman ta daka tsalle saboda murna tayi maza ta kalli Suliem da itama ta hango tsantsan farin ciki dake fuskarta da take ta k'ok'arin b'oyewa. Lokaci guda kuma hawaye ya cika idon Ajwa tunawa da tayi taji Mom tace gobe zasu wuce Saudiya? Gobe-gobe zasu wuce su barta ita kad'ai a nan? A guje ta juya d'akin su Mom ta tsaya baki k'ofa saboda jin muryar cikin kuka tana cewa
“walahi Ammi ,Ya Raihana. Duk abunda zakuce bazan koma gidan Khalid ba. Na gama auren sa. Ku daina tambaya dalilin daya sa na yanke wannan hukuncin don ban shirya sanan daku yanzu ba. Idan lokaci ya yi gaskiya zatayi halin ta. Amma yanzu don Allah ku daina tambaya ta abu d'aya zan iya cewa shine bana son shi”
Tausayin Mom sosai ya rufe Ajwa ta juya a hankali ta koma falon ta samu guri ta zauna duk sukayi jugum-jugum. Baffa da Abba ne suka dawo bayan sunbi Babaah. Da nutsuwa da fahimta Baffa yace
“Nonna ina ganin tunda abun ya kai haka kiyi hak'uri ki bari mu tafi dasu d'in. Idan munje sai a zauna a nutse ayi magana ko Allah zaisa ta fad'i abunda yasa tace ta gama zama da Khalid. Shima yanzu mun sameshi yace mu tafi da itan zai biyo mu daga baya sai ayi sulhu.”
Nimfashi Nonna taja a hankali tace “to shikenan Allah ya kaimu da rai da lafiya. Sai a k'arbi passport d'in nasu suma a sama musu jirgi.”
To kusan rana duk haka suka kwanta zuciyoyinsu babu dad'i musamman Babaah da yake ji kaman ya kashe Mom tsabar bak'in ciki. Asubar fari kuwa kafin kowa ya tashi shi ya fara barin gidan ya juya Bauchi. Sai a hanya ya kira Baffa yace masa shiya wuce. Suma sunayin sallah suka fara shiryawa Ajwa data ga da gaske su Mom zasu bi su Nonna su barta ai sai kuka kaman wacce aka yiwa mutuwa. Duk yanda Momi da Suliem ke daurewa suma saida suka saki kuka suka rungume ta suna lallashi. Jiki babu kuzari haka duk suka shirya suka fito. Wayyo data ga da gaske tafiya zasuyi ta rike Mom tana kuka kaman zata shid'e. Wannan karan har Nonna saida ta share hawaye da kyar da lallashi suka samu ta saki Mom da Suliem dake kuka suma gurshanshan. Tana kallo suka fice daga gidan ta durkushe a gurin taba kuka sosai saida ya saka mata zazzab'i. Da kyar ta iya jan k'afafuwanta ta koma ciki. Sai taga gidan ya mata wani irin fad'i lokaci guda tsoro ya shige ta.
A guje ta wuce d'akin ta maida k'ofar ta rufe harda mukulli kafin ta fad'a kan gado tana wani irin kuka gwanin ban tausayi. K'arar wayanta ya d'an firgita ta d'auka wayan da sauri ganin number Asad ne ta Dubai ta d'aga wayar da sauri. Tsintar kanta kawai tayi ta cigaba da rera masa kuka. Asad dake k'ok'arin shiga office ya yi maza ya maida k'ofar ya rufe yana cire safar dake hannun sa hankali tashe yace
“Baby what's wrong? Menene kar ki d'aga min hankali please. Menene ya same ki?”
Tana kuka sosai tace ta wani b'angaren idan kaji yanda tayi maganan zakace zallan shagwaba ce.
“Ma...Mamm. Mama”
“meya samu Mamaa. Ina su Nonna?”
Hankali tashe ya sake jefa mata tambayar. Saida ta dan had'iye zuciya tace
“sun tafi ...sun.....barni”
Wata wawuyar ajiyar zuciya ya sauke ya koma a hankali ya zauna kan kujera. Saida ya fesar da numfashi sannan yace da murya lallashi
“kinji yanda ki ka dagamin hankali kuwa hmm?. Saboda sun tafi ki ke kuka Baby?”
Sai yanzu ta farga da sunan daya kirata. BABY ta sake maimaitawa sai taji zuciyarta na d'an dancing na joy. Sake matse pillow tayi kan k'irjinta ta maida ido ta lumshe.
“to ki daina kuka kinji Baby. I'm here. I'm sorry bazan iya dawowa yanzu ba amma zan dinga kiran ki regularly kinji?”
Kai ta d'aga kaman yana kallonta. “yanzu me ki ke? Safiya ce a nan ko? Kinci abinci?”
A hankali tace “aa”
“Why?”
“banajin yunwa”
Saida ya fesar da numfashi yace “please ki daure kici abinci kar ki zauna da yunwa kinji? Ko kina so na shiga damuwa?”
Ikon Allah Ajwa tace cikin ranta. Wai menene ya chanza su daga ita har Asad d'in? Daga can background ta cikin wayan taji alamun kaman an buga k'ofa. Sai kuma taji muryar mace tana sallama da kiran sunan Asad. Wani irin abu Ajwa taji ya tsaya mata a k'irji ya kasa wucewa. Menene hakan kenan? Asad taji ya sauke a hankali taji yace da wata irin murya
“listen Baby. Zan kira ki anjima OK.”
Kafin tace wani abu ya kashe wayar. Ido Ajwa ta zubawa wayar kawai. Can kuma zuciyarta tace to menene kuma na damuwa? Baki da abun damuwa tunda ba sonshi ki ke ba. Tabbas kuwa da wannan tunanin ta miƙe ta shige banɗaki amma can k'asan ranta ta kasa cire abun a ranta.
────────────────────────
Baby
Baby
Aya keta nata sunan tana kallon Asad daya zuba mata ido fuskarsa babu annuri. Wani abu taji ya daki k'irjinta na tsananin kishi da bak'in ciki. Ita Asad yakewa wanna kallo kaman yaga kashi? Yanzu ta shigo ta sameshi yana cikin wani iri nishadi da annushawa sai murmushi yake saboda yana waya da matar sa, amma tana shigowa duk wani annuri dake fuskarsa ya d'auke. Har k'iyayyar da yake mata ta kai haka?. Tsawar da Asad ya buga mataya dawo da ita cikin hayyacin ta tsaya chak tsak'iyar office d'in.
“what are you doing in my office?.”
Raurau tayi da idanuwanta “Asad don Allah kayi hak'uri ka rufamin asiri. Wlh na gane kuskurena. Mutumin dana guje ka a kanshi walahi mayaudari kuma d'an damfara ba sona yake ba sha'awata ce kawai yake. Ko sati biyu bamuyi da aure ba ya sake ni sake uku ya kwashe komai nawa ya gudu dashi ya barni k'asan da bansan kowa ba. Tun lokacin daya gujeni nake neman hanyar da zan dawo gareka amma saboda bani da komai da kuma kunyar abunda na aikata maka na kasa fuskarta sai yanzu na samu kwarin gwiwa aikata hakan. Don Allah kayi hak'uri ka yafemin walahi ina so....”
“Kar ki kuskura ki k'arasa wannan kalman Aya. Ai baki ga komai ba tukun. Kije indai ni ne na yafe miki ,so please kar ki sake shiga rayuwata. I have someone that I'm deeply inlove with”
Ya k'arasa maganan yana wani irin murmushi da saida Aya taji kaman ya suka mata wuk'a a kahon zuci. Bata so ta amincewa kanta soyayyar da Asad yake wa matar nan tasa ko ita lokaci da duniya ta sheda irab soyayyar sa a gareta, bata tab'a ganin irin wannan deep affection d'in ba. Matsowa tayi ganan tebir sai ta zube k'asa da gwiwoyinta tana kuja sosai
“don Allah Asad ka rufamin asiri wlh bazan iya rayuwa babu kai ba. Na amince kayimin duk abunda zaka min don Allah ka aureni koda zaka dinga yagan naman jikina kana zubarwa zan jure matsawar na kasance tare da kai.”
Tasowa ya yi gabanta ya durkusa da gwiwa daya. Wani irin mugun kallo ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 15