【Pg9&10】
Gabansu ba k'aramin fad'uwa ya yi ba dukkan su har Mom. Jikin Mom na rawa ta nufi Babaah dake shigowa cikin suit da jaka hannun sa. Kafin ta iske shi ya d'aga mata hannu ya yi kan Ajwa dake tsaye kikam kaman gunki taki motsawa daga inda take. Jakarsa ya yi wurgi da ita yana zare belt d'in wandonsa yana cewa
“yau d'in nan ba gobe ba zan sauke miki duk wasu almutsutsai dake kan ki. Zan sake tabbatar miki da ni ne Uban ki kuma dole ki bi hukuncin dana yanke”
Da k'arfin sa ya daga belt d'in ya zuba mata shi a jiki, amma Ajwa yanda kasan dutse ko motsi sai Mom da Suliem ne ke ihun bashi hak'uri. Yanda tayin kuwa ya k'ara tunzura Babaah ya hankad'e Mom dake rik'esa ya sake d'aga belt d'in da dukkanin wani k'arfi da Allah ya masa ya zuba mata a jiki,still Ajwa na tsaye ta zuba masa jajayen idonta da sukayi wani irin ja kaman garwashi don zuciyarta ta k'ek'ashe. Shi kansa Babaah saida gabansa ya fad'i da yanda tayi amma hakan bai hana ya sake d'aga belt d'in zai sake zuba mata a jiki ba k'arar wayarsa ya katseshi. Dakatawa ya yi yana zuba wani irin huci ya ciro wayar daga aljihun wandon sa. Suliem da Mom kam ba'a cewa komai hankali Mom ya yi tsananin tashin saboda ganin irin reaction d'in Ajwa. Matsanancin kuka take shi kenan ya gama kashewa y'ar ta zuciya. Sunan wanda ya gani jikin wayar yasa ya d'aga cikin sauri.
“slma, Alhaji Sultan”
D'an shiru ya yi yana sauraran magana da ake daga can b'angaren kafin yace
“to shikenan babu laifi. Har ya shigo kenan? To Allah ya kaimu. Yauwa to sai anjima.”
Kashe wayar ya yi ya kalli Ajwa da har zuwa lokacin take tsaye gabansa tana fidda wani irin huci da jajayen idanuwanta. Kwafa ya yi ya juya ya kalli Mom dake kuka sosai tana kallon Ajwa ita da Suliem.
“yaron da nace na fiddawa Suliem matsayin miji, zasuzo gobe shida d'an uwansa kaman yanda nace ya dawo saboda haka gobe zasuzo ya ganta su daidai ta. Wlh ko da wasa kar ku kuskura ku bada wata k'ofa da zaisa zargi ya shiga zuk'atansu. Kuma aure ne nace babu fashi ke Suliem. Idan Uwar ki bata gaya miki ba to yanzu kinji na zab'a miki mijin da zaki aura gobe kuma zaizo ku daidai ta.”
Kuka Suliem ta sake rushewa dashi tana kallon Babaah da ido a zare. Miji kuma?innalillahi auren dole Babaah zaiyi mata?. Juyawa kan Ajwa ya yi da har zuwa lokacin tana tsaye kaman wata gunki ya ciji lebe rai b'ace yace
“ke kuma zan dawo kan ki ban gama dake ba yar iska kawai ”
Fuu ya wuce kaman iska ya haura sama. Sai a lokacin Ajwa taja wani irin dogon numfashi ta sauke Mom na kallonta hawaye suka sake kwaranya daga idonta. Shikenan ya sake k'arfafa gwiwa wajen sake saka zuciyar Ajwa ta zama dutse. Jiki a salube ta matso ta kama Ajwa dake kallon kasa kaman wacce taga wani abun birgewa. Kama fuskarta tayi ta d'ago da ita suka fuskanci juna. Hawaye suka sake wankewa Mom fuska takai hannu tana shafa fuskar Ajwa. So take ko yane ta bada reaction amma Ajwa kir taki sai ido da take ta kyiftawa babu kakkautawa.
“Mamaa kina jin abunda Babaah yace? Aure zaiyi min Mamaa?”
Suliem tayi magana da rawar murya. Lumshe ido Mom tayi ta sake sauke ajiyar zuciya kafin ta juyo kan Suliem. Murya a taushashe tace
“kiyi hak'uri mubi umarni mahaifin ku. Mu bari yaron yazo mu ganshi duk lalacewar mahaifin ku nasan bazai tab'a zab'a muku wanda zai cutar daku ba. Aure rahama ne Suliem, at least zaki tafi ki bar gidannan ina kuma fata can inda zaki ku samu nutsuwa da kwanciyar hankali. ”
Anya kuwa hakan mai yiwuwa ne?. Babaah zai sama musu mazaje wanda zasu kula dasu? Kai abun da kamar wuya. Itafa akwai wanda ta jima tana dakon soyayyar sa. Sau d'aya ta tab'a ganin sa a IG tun daga lokacin kuma Allah ya jarrabeta da son shi. Babu dare babu rana take Addu'a Allah ya had'ata da wannan bawa nashi ,idan kuma hakan bamai yiwuwa bane to Allah ya gaggawar cire mata shi daga cikin zuciyarta. Tun tana b'oyewa har Ajwa ta san halin da take ciki. Lokaci da dama har tausayi Suliem d'in ke bata ganin yanda ta mutu a kan san wanda baisan tana yiba bare yasan da wanzuwarta a fad'in duniyar nan. Ance so mugun ciwo. Juyawa Suliem tayi a guje ta haura sama tana kuka. Numfashi Mom ta sake saukewa ta juyo ta kalli Ajwa tace
“wuce kema kije kiyi sallah ki kwanta bari na d'ura mana abinci ”
Bata musa ba ta wuce Mom ta haura sama. K'ofar d'akin Suliem ta fara tsayawa tana sauke ajiyar zuciya. A hankali ta kama murfin ta shiga can k'uryar gado ta samu Suliem ta rungume filo tana rigzar kuka. Kai ta girgiza cike da tausayin ta ta k'arasa shigowa d'akin. Ta wani b'angaren tana ganin sauk'i ne waje Suliem wannan auren. Idan Allah yasa guy d'in da zata aura ya sota wata k'ila zaiyi sanadin da zata manta da koma waye mutumin data kamu da son sa. Jawo Suliem d'in tayi ta rungume kawai batace mata komai ba don tana ganin abunda tafi buk'ata kenan. Saida taji Suliem d'in tayi barci sannan ta miƙe ta gyara mata kwanciya ta sake rufeta kafin ta juya ta fice tayi nata d'akin. Gaban mudubi ta tsaya ta tsirawa kanta ido na tsawon mintina kafin a hankali takai hannu ta fara cire kayan jikinta. Miƙewa ta sakeyi ta tsaya dakyau gaban mudubin tana k'arewa kanta kallo zir d'in ta.Tsak'iyar k'irjinta da ya yi wani irin ja sanadin belt bin Babaah ta kai hannu a hankali ta shafa tana runtse ido. Hawayen da take ta k'ok'arin b'oyewa suka biyo kuncinta. Sake mik'a hannu tayi wajen cikinta daidai kasan cibinta inda nan ma ya yi jaa da shatin belt. Har sai yaushe ne Babaah zai kalle su matsayin ya'ya sa na cikin sa ba bunching bag nashi ba?. Sai yaushe ne zai kallesu da idon soyayya da kulawa, bare magana mai dad'i ta shiga tsakaninsu? . Hannun ta k'ara kaiwa ta sake shafo gefen mamanta da belt d'in ya d'an tab'a wajen duk yafi ko ina yi mata ciwo. Cije lebe tayi hawayen ta suna k'ara gudu kan fuskarta. She's tired of all this. Allah ya sani ta gaji, ta gaji da wannan uk'ubar ta Babaah. Jiki a mace taja k'afa ta shige toilet. Nanma saida ta b'ata lokaci tana gasa jikinta kafin ta fito d'aure da Alwala.
Mom bata yarda ta haura saman ba saida ta gama abinci don sosai take cikin fargaba da sake had'uwa da Babaah. Bayan ta gama girkin ta juye masa nasa a flask ta Jere kan tire sannan ta haura sama. K'ofar su Suliem da Ajwaah ta fara bugawa ta sanar dasu ta Kammala abincin sannan ta wuce d'akin Babaah. Da jarumta ta buga K'ofar Babaah yana jinta ya share ta saida ya tabbatar ta gaji da tsayuwa sannan ya buɗe k'ofar fuska babu yabo babu fallasa. Matsa mata ya yi ta shigo ta ajiye abinci kafin ta juyo kansa zatayi magana. Yanayin dataga fuskarsa yasa ta had'iye koma menene take son cewa da tarin tambayoyin dake cinta. Kama k'ofa ya yi da ido ya mata alama ta inta gama tazo ta fita. Bata musa ba ta matso ta rab'a shi ta wuce. Tana fita ya maida k'ofar sa ya rufe. Zubawa k'ofar ido kawai Mom tayi ranta na suya kafin ta kad'a kai ta wuce nata d'akin.
────────────────────────
Xx
Lokacin da sak'on Asad ya shiga wayar sa dama wasu sak'onnin, yana can wani kebantaccen hotel a room 402 da sabon kamun da ya yi. Yarinyar da yake tare da ita tun daga Somali tayi tattaki tazo har nan Abuja wajen sa. Yarinyar ce data fito daga gidan arzik'i gaba da baya. Zatayi shekara 25 zuwa da shida. D'akin da suke k'aramin d'akine da aka k'awata da katon gado da kujera mai cin mutum biyu. Sai bedside drawer dake fitila a kanta wanda ita da kad'ai ce a kunne. Gaba d'aya d'akin ya cika da ihun yarinyar kace yanka ta ake. Haushi duk ya rufe Far'aan saboda yanda ta wage mak'ogaro tana zuba ihu kaman wacce yake yankawa. He knows a kan sex his an expert don duk wata mace da zai kasance da ita to kwatankwacin reaction d'in da zata bayar kenan, amma wannan ta fisu harshe ihu take zubawa kaman zata kashe masa dodon kunne. D'an fuska ya sake yatsinawa yana kallon yanda jikinta ke wani jijjaga idonta sai farfar yake kaman mai shirin hawa farfadiya. 'Damn ' yace cikin ransa da alama wannan sabon hannu ce ko kuma tsabar dad'i ne. Yunk'urawa ya yi kaman zai tashi sai kuma ya sake komawa jikinta da wani bala'in gudu aikuwa yarinya ta sake wage baki tana zuba uban ihu da surutai.
“ahhh, yesssss. Yesss. Right there. OMG I'M GOING TO DIE”
Wani irin toshe kunne Far'aan ya yi ,ya yi maza ya rufe mata baki saboda yanda ta wage harshen babu tantama yasan anji a waje. Chak ya tsaya da abunda yake ya zuba mata ido cike da takaici yana ji kaman ya rufe ta da duka.
“ke are you mad?kina so mutane su d'auka yanka ki nake? Have some class mana”
Ina bata sanma yanayin ba sai k'ok'arin motsa kugunta take da nashi jin ya tsaya. Murya na rawa tace da turanci
“me yasa ka tsaya Baby ?”
Kaman ya make ta ya zuba mata harara sai kuma ya yi wani shegen murmushi ya sake kwantowa jikinta.
“kina so na cigaba?” kai ta jinjiga kaman ta fashe da kuka. Smirk ya sake saki ya kai hannu da wani irin slow k'asanta ya danne da kugunsa. Aikuwa ta zabura ta wage baki zata sake zuba ihu ya yi saurin tosheshi yana dan sakin d'an 'tsk' k'ara daga bak'in sa.
“idan har na cigaba da baki wannan pleasure menene nawa sakamakon?”
Tana haki tace “kome ka ke so Baby. Ka fad'i komai ka ke so zan baka”
Wani irin murmushin ya saki saida hak'oransa duka suka bayyana. A hanzarce ya juya ya kalli side drawer inda ta ajiye hadad'd'un wayoyinta kirar Galaxy fold, da IPhone 12 nata sai mukullin motar ta da tazo da ita tun daga Somali aka saka mata ita a jirgi. PORCHE 911. Itama kallon drawer tayi kafin yace wani abu tayi saurin rigashi
“na baka. Badai mota ba? You can have it”
Wata shak'iyar dariya Far'aan ya yi ya wani had'e bakinsu da wani irin sexy move yana cigaba da bugunta da dukkanin wani k'arfi da Allah ya bashi. Cikin d'an k'ank'anin lokaci tayi suman wucin gadi yafi a k'irga. Saida ya mata lasa-lasa ta bugu yanda ko yatsa bata iya motsawa sannan ya koma gefe yana maida numfashi. Duk tsawon wannan lokacin daya d'auka a kanta baiyi wani enjoy ba. Duka duka baifi sai biyu ya kawo ba shima da kyar saida ya yi imaging wasu yan matansa tukun. Like yarinyar gaba d'ayan ta bata da wani ni'ima na azo a gani sai shegen baki da kyau kaman ita tayi kanta. Kallonta ya yi yaga yanda ta wani bararraje kam gadon kaman matacciya duk inda take ya b'aci sai kace wacce tayi fisari. Y'ar dariya ya yi ta mugunta ya miƙe ya suri key d'in motar ya yi toilet yana cewa
“idoit”
Bai jima ba a toilet ya fito d'aure da tawul ruwa nabin hadad'd'en jikinsa sai zuba shek'i yake. Yana fitowa wayarsa ta sake k'ara alum sak'o ya sake shigowa. D'an tsaki yaja kafin ya nufi wayar dake kan drawer ya d'auke. Yana dubawa kuwa dukkanin wani annuri dake kan fuskar sa ya kau ya yi maza ya buɗe sakon kaman hakan
'𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑖𝑠 𝑦𝑜𝑢𝑟 𝑙𝑎𝑠𝑡 𝑐𝒉𝑎𝑛𝑐𝑒 𝑤𝑙𝒉 𝐹𝑎𝑟'𝑎𝑎𝑛. 𝑖𝑑𝑎𝑛 𝒉𝑎𝑟 𝑏𝑎𝑘𝑎 𝑘𝑖𝑟𝑎𝑛𝑖 𝑏𝑎. 𝐼 𝑝𝑟𝑜𝑚𝑖𝑠𝑒 𝑦𝑜𝑢 𝑖𝑛𝑎 𝑛𝑎𝑛 𝑡𝑎𝑓𝑒 𝑘𝑢𝑚𝑎 𝑑𝑖𝑟𝑒𝑐𝑡 𝑧𝑎𝑛𝑗𝑒 𝑤𝑎𝑗𝑒𝑛 𝑏𝑟𝑜𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑛𝑎𝑘𝑎 𝑑𝑎 𝑓𝑢𝑙𝑙 𝑒𝑣𝑖𝑑𝑒𝑛𝑐𝑒 𝑑𝑎 𝑝𝑟𝑜𝑜𝑓. 𝑑𝑜𝑛'𝑡 𝑡𝑒𝑠𝑡 𝑚𝑦 𝑝𝑎𝑡𝑖𝑒𝑛𝑐𝑒. 𝑘𝑎 𝑘𝑖𝑟𝑎𝑛𝑖 𝑦𝑜𝑢 𝑙𝑦𝑖𝑛𝑔 𝑐𝒉𝑒𝑎𝑡.'
Ji ya yi kaman ya yi jifa da wayar. Wai wannan yarinyar me take so dashi ne? Saboda ita bata isa tasa ya chanza number ba. Me yasa ma ya yi soyayya da ita ne gashi ya jawowa kansa alak'akai mai shegen nacin da basu san an rabu ba. A zafafe ya bi number yana huci gwanda ya gama da ita once and for all. Buga d'aya kuwa ta d'aga
“wow, har haka ka ke tsoron brother naka yasan mugun halin ka Far'aan you lying cheat?”
Kaman wacce ta watsawa garwashi a zafafe yace
“ki cire brother d'ina daga cikin bakin ki. Me zakiyi? So what idan kina da proof?your blackmail bazaiyi aiki a kaina ba. Nace bana son ki yanzu ko ana dole ne? Ki fita daga rayuwata dana brother d'ina and get a life.”
Wani irin shiru tayi na sakanni kafin tace “haka kace?.”
“haka nace. Mtsw”
Yaja dogon tsaki a zafafe ya kashe wayar har ya d'aga zaiyi jifa da ita ya hango sak'on Asad.
'𝐼'𝑚 𝒉𝑒𝑟𝑒'
Da wani bala'in gudu ya tashi ya suri kayansa dake yashe a kasa ya fice daga d'akin kota kan Babe nashi bai bi ba. Koda yaje gida bai jira ya gama faking motar ba ya fice a guje ya yi b'angaren su. Lokaci daga Asad har Su'ad sun kwanta saboda gajiya banyan sunyi sallah isha. Dad bai dad'e da fita ba ya kawo musu abinci har Asad d'in yace masa ya sanar da iyayen yarinyar gobe yake so suje shida Far'aan d'in suga yarinyar don yana son wucewa Mexico ranan Juma'a. A guje ya fad'a kan Asad dake barci cikin wasu lallausan kayan barci farare riga da wando mai mad'auri. Yanda ya fad'a kan Asad din saida y'ar k'arar 'Uff' sound ya fito daga bakin sa. A wahalce ya buɗe shanyanyun idanuwansa kan Far'aan dake kansa yana zuba masa murmushi. Wani irin yunk'urawa ya ya kamo Far'aan d'in ya sake matsewa cikin k'irjinsa gaba d'aya suka saki ajiyar zuciya. A hankali Far'aan yace
“I miss you”
K'ara matseshi ya yi cikin k'irjinsa kafin yace
“I miss you more”
Sun jima rungume da juna kaman wani zai kwance d'aya daga cikin su. Yanda suka matse juna zaka san akwai tsananin soyayya da blood and flesh tsakaninsu.
“to lovebirds. Wato Asad ne kad'ai cikin d'akin nan ko Far'aan?”
Su'ad dake kwance gefe ya yi magana yana hard'e hannu a k'irji da turo baki. Dariya Far'aan ya yi ya zame daga jikin Asad ya fadawa Su'ad suna dariya. Wani irin deep murmushi Asad ya yi ya jingina da gadon yana kallon yanda suke wrestling cike da wasa. He loves them too much zai iya bada rayuwar sa saboda su. Saida sukayi wasan ya ishesu sannan Far'aan ya juyo kan Asad dake kallon su.
“but ya akayi ka dawo? Na d'auka Mexico zaka wuce ranan Juma'a?”
Zama Asad ya gyara fuska babu wasa ya sake tsaida idanuwansa cikin na Far'aan kafin yace
“yes, zanje Mexico on Friday. Abunda yasa na biyo tanan saboda auren ka. Dad ya kirani kan ya samo maka mata da zaka aura. Banyi objecting ba saboda naji yarinyar da yake so ka aura d'in y'ar mutum ce mai dattako, da kuma kamala. Duk wani uba yana so yaga d'an sa ko y'ar sa ya yi aure gidan mutnci. Beside ina so ka nutsu waje d'aya Far'aan. Wannan y'an matan duk bashi bane cinyewa ko burgewa aure shine. So zamuje gobe Bauchi already na sanar ma Dad. Zamuje kaga yarinyar idan ta maka is fine za'ayi aure babu Jan lokaci ”
Wani irin zuba masa brown eyes nashi Far'aan ya yi abunda yake iya banbantasu kenan idan ka cire gashin su. Na Asad yafi na Far'aan don shi yana aski kuma yana tura gashin sa ,amma Asad nashi bak'ikk'irin yake kaman gawayi daya kwanta har wajen wuyan sa. Baki ya buɗe ya mayar ya rufe ya sake bud'ewa cikin mamaki yace
“are you serious? Ni ne za'ama auren dole kaman wani k'aramin yaro? Kai me yasa bai kawo maka matar da zaka aura ba sai ni?. And why yake showing care a kan mu all of a sudden? ”
Ajiyar zuciya Asad ya saki ya matso ya kama hannun Far'aan.
“pls just this once. Kayi abunda yace. Zamuje muga yarinyar ne kawai idan ta maka kana da ikon kace kana so ko baka so. No one will force you. Pls”
Zubawa juna ido sukayi kafin Far'aan yaja doguwar ajiyar zuciya.
“fine. Amma ka sani zanyi ne kawai saboda kai. Kuma wlh idan batamin ba babu wata yarinya da zan aura.”
Murmushi Asad ya yi ya sake jawoshi ya rungume. Shikam Su'ad ido ya zuba musu yana murmushi. Wannan soyayya tasu taba burgeshi matuk'a. Fatanshi hakan ya d'ure har zuwa lokacin da zasu koma ga mahallicin su. Allah karya kawo wani abu dazai shiga ya fita ya raba tsakaninsu.
────────────────────────
To washe gari tunda sukayi sallah asuba Babaah ya tashi da hargagin sa ya hanasu komawa barci. Mom tana d'aki ya bita ta fito maza su fara d'ura abincin baki. Haka taje ta taso Suliem data kwana tana kuka bata samu barci ba sai wajen asuba tana barcin kuma asuba tayi kafin ta samu ta runtsa Babaah ya hanasu. Haka Suliem ta fito da ido duk a kumbure ga kanta dake mugun ciwo. Sanda ta shiga kitchen d'in ta iske Babaah ya zuba ya fito da abunds za'a dafa da kayan nama dasu kaji harma da drinks amma store d'in a gark'ame yake da kwad'o. Kai kawai ta girgiza ta fara aikin tana sharar hawaye. Ajwa na kan dadduma Mom ta shiga ta sameta.
“maza ki fito idan kin gama kije ki kamawa Suliem aiki a kitchen kafin Babaah yasa mana ciwon kai.”
Bata tashi ba saida ta gama lazimin ta sannan ta fito sanye da hijabin ta dake sharar k'asa. K'ofar kitchen d'in ta tsaya tana kallon yanda Suliem keta aiki tana kuka. Kai kawai ta girgiza ta shiga ta kama mata suka hau girki. Basu gama sai wajen goma na safe Babaah nata kai da kawowa kitchen d'in. Suna gamawa kowa ya yi d'akin sa don yin wanka. Mom wajen Suliem tayi da wasu jajayen less d'inkin riga da sket. Da kanta ta shirya Suliem d'in ta yane ta da mayafi. Kyan da Suliem d'in tayi abun sai wanda ya gani. Sunana k'ok'arin fitowa Babaah ya shigo a hanzarce cikin manyan kaya ya yi masifar kyau sai zuba kamshi yake.
“yauwa kun gama?. Ga bak'i nan zunzo suna waje bari naje na buɗe musu gate kisa wannan y'ar ta shigo dasu”
K'irjin Suliem ya sake wani irin mummunan fad'uwa ta rik'e Mom kaman za'a kwaceta. Tuni hawaye suka cika mata ido tabi Babaah da kallo daya juya da sauri ya fice. Numfashi Mom taja ta kama hannun Suliem suka fito d'akin Ajwa. Tana tsaye gaban mudubi tana rolling kanta sanye da wata doguwar riga pitch da aka yiwa ado da flower daga k'asa. Rigar daga k'ugu zuwa sama ta d'an kama hakan yasa tabi d'an siririn shape nata ta zauna kaman a jikinta akayi ta. Babu wani kwalliya kan fuskarta sai farin glass nata data saka daya k'ara mata kyau matuk'a. K'afarta flat takarmi ne mai igiya daya shiga da kayan. Sosai tayi kyau ita kanta Mom saida tace MashaAllah a fili tana kallon yaran nata. Zaunan da Suliem tayi ta kalli Ajwa dake fesa turare irin mai sanyin kamshin nan wanda yabi jikinta ko da yaushe.
“idan kin gaba jeki shigo da bak'i sun iso”
Batace komai ta kama hanya ta fito. Tana fitowa taci karo da Babaah da duk ya rikice anyi bak'i tunma basu shigo ba. Yana ganinta ya wani bata fuska babu Walwala murya a d'an taushashe yace
“yauwa maza kije ki shigo dasu suna haraba”
Sosai take kallon Babaah tana kyestima irin kyau da ya yi. Tabbas Babaah kyakkyawan mutum ne dake cin duniyar sa babu tsinke. Yau Babaah ne yake mata magana da taushin murya saboda yana tsoron kar duniya tasan uk'ubar da yake gana musu?. Wucewa kawai tayi zuciyarta na wani irin zafi ita kad'ai tasan irin kunan da take. Tana fitowa harabar wajen daidai suna faking motar su.
────────────────────────
K'aramin tsaki Far'aan ya sake ja a karo na babu adadi saboda kallon tuhuma da Asad d'in yake masa tunda suka d'auki hanya. Lokacin da suka fito zasu tafi daga Dad har Mamee saida suka musu rakiya bakin mota. Gogan yana sanye cikin wata dark blue suit three pieces da tayi mugun kama jikinsa. Gashin nan an tufke shi a tsakiyar kai wasu sun zubo gefe da gefen goshin sa. Kyau kam ya yi abun ba'a cewa komai. Far'aan kuma yana sanye da farar shadda d'inkin doguwar riga da wando sai bak'in takarmi da hula baka daya sa. Sosai ya yi kyau saboda Su'ad shiya tursasa ya saka manyan kaya. Shima ya shirya cikin blue shadda light data haska bak'ar fatar sa sosai ya yi kyau. Tunda suka fito Dad sai sake jawa Far'aan kunne yake yabi a hankali kar yaje ya yi wani abu da zai basu kunya ya kuma zubar musu da k'ima da mutunci. Haushi yanda Dad d'in yake nuna kulawa yasa Far'aan bai amsa masa ba ya wuce wajen notar daya zo da ita. Gaba d'aya sula tsaya turus suna kallon motar da Far'aan d'in ya shiga don babu wanda yasan yazo da wata mota saboda dare ne. Ganin yana neman ficewa daga gidan dole haka Asad da Su'ad suka shiga motar badan ransu yaso ba. Zasu tafi Mamee ta bada katuwar leda cike da kaya tace ya bawa Suliem. To shine tunda suka d'auko hanya Asad din ke kallon sa cike da tuhuma ko kyeftawa bayayi.
“kallon duk na menene haka ne wai haba? Ko baka ga ina tuk'i bane kana so naje na buga motar ne?”
Ta glass d'in mirror ya daga suka had'a ido da Asad ganin yanda ransa yake a b'ace. Ko ba'a fad'a ba yasan motar macece don ga alamomi nan sun nuna kayan mata cikin motar. A hankali da kaushin murya yace
“motar waye wannan?”
Harara Far'aan ta juyo ya zubawa Asad “waye ne ka gani a ciki?”
“motatace. Happy? . Look kaga bana son tuhuma wannan motatace hakk'in mallakata. An bani ita matsayin gift so qiut acting kaman kaine babba. I'm the oldest a nan don't judge me. Ok”
Wani irin zuba masa ido Asad ya yi yana kallonsa ransa in ya yi duba ya b'aci. Murmushi Su'ad shima ya yi yana girgiza kai tunda suka fito bakinsa ke d'auke da magana amma yabar Asad d'in yaji da d'an uwansa. Har suka k'araso Asad bai sake kallon Far'aan ba bare ya amsa maganan da yake jansa da ita daga karshe ma kwanciya ya yi bayan motar ya lumshe manyan idanuwansa har suka isa. Sanda Far'aan ya kunna hancin motar sa ciki Ajwa na fitowa saida gabansa ya yanke ya fad'i. Daga shi har Su'ad suka zuba mata ido kowa na tasbihi cikin ransa.
Daga d'an nesa kad'an ta tsaya tana jira su k'arasa faking. Wow Far'aan ya furta cikin ransa. Wannan hotty ita ce yarinyar da zai aura? Indai itace kuwa bashi da matsala. Yarinyar tayi masa hundred percent
Bata da jiki kaman sauran y'an matansa amma tana da abubuwan da basu dashi. D'an curve nata yabi da kallo zuwa faffad'an kugugunta daya baje cikin rigar kafin ya haura da idansa saman k'irjinta. Duk da yaga alamun kaman bata cika boobs ba amma yasan nan gaba in sukaji hutu sosai zasu tashi ,da alama kuma irin wanda yake so ne. Wani lashe leɓensa na k'asa ya yi yana mata kallon kurilla har ya samu guri ya faka motar. Juyawa ya yi kan Asad dake kwance har zuwa lokacin da ido a lumshe. D'an girgiza kai ya yi kafin ya yi murmushi yace
“mun iso ko mu bar...”
Kafin yama gama maganan tuni ya buɗe motar ya fice. Fitowar sa ya yi daidai da k'arasor Ajwa data taho ganin an bud'e bayan motar. Kaman a slow motion ya sawo jiki waje ita tana k'arasowa. Sanda ya k'arasa fitowa ya tsaya gabanta saida zuciyoyinsu suka buga lokaci d'aya. Kaman magnet daya jata haka ta tafi zata fad'a masa tayi saurin cin birki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 15