taja baya zuciyarta na bugawa da k'arfi. Kwayar idanuwansu ne ya sarke cikin na juna a zuci tace ya Rabbi. Ida suka zubawa juna komai ya tsaya chak ya daina motsi. Wannan fuskar tashi dake very cold ya wani yamutsa kafin ya d'auke kai gefe kaman yaga kashi. D'an murmushi dake kan fuskar Ajwa tuni ya kau ta d'ura wani uban ashar cikin ranta. Kan uba. Duk da haka yak'e tayi ance bak'on ka Annabin ka. Saboda Suliem da Mom zata jure wannan wulak'ancin da yar siririyar murya tace
“sannunku da zuwa, ina wuni?.”
Wani irin cold look ya sake bata kafin ya sake watsarwa gefe. Wayyo zuciyar Ajwa kaman tayi bindiga. Abunda bata jurewa kenan cin mutunci da rainin hankali. Wani irin yunk'urawa tayi zata zuba masa bak'ar magana taji ance
“hi, cutie. Ya ki ke?”
Da sauri ta juya tana kallon Far'aan dake k'ok'arin zagayowa fuskarsa d'auke da murmushi. Su biyu ne? Ta sake cewa cikin ranta. Waye ne to mijin Suliem? Su'ad shima ya fito daga gidan gaba da murmushi kan fuskarsa yace
“slma ”
Ya Rabb. Sun d'aure ta gaba d'aya. Asad ta sake kallo dake kallon gefe yanda kasan da duwatsu yake tare. Koma waye mijin Suliem cikin su wannan kam tasu bazata zo d'aya ba. Saurin juyawa tayi tana cewa su shigo ciki. Da azama Far'aan ya bita ya jera da ita sai shegen murmushi sa yake mata irin nashi na mayaudara.
“Cutie baki gayamin sunan ki ba. Ni sunana Far'aan, wancan kuma Asad basai nayi miki bayani ba we are twins. Wancan kuma Su'ad brother namu ne daga wata uwar.”
Ya cika surutu tace cikin ranta amma a zahiri d'an yak'e tayi ta juya a kaikace ta d'an watsa idonta kan Asad dake takowa da wannan majestic tafiya tashi. Yaci sunan sa Asad amma babu hali.
“kinyi shiru Cutie ”
Dan ya mutsa fuska tayi bata son wannan Cutie da yake kiranta dashi ,amma ta mishi uzuri tunda baisan wacece aka hadashi da ita ba. Murya can ciki tace
“sunana Ajwa ”
“Ajwa” Ya maimaita yana mata wani irin sihirtaccen kallo. The girl is just perfect ne gaba d'aya gata so innocent. Da sallama suka shiga falon Ajwa a gaba. Babaah dake ta safa da marwa ya wani taho da sauri yana zuba uban murmushi. Sosai yake kallon su yana tasbihi cikin ransa hakan ya'ya Alh Sultan d'in suke? Lallai kuwa ba banza ba.
“sannunku da zuwa, sannunku da zuwa”
Gaba d'aya suka durkusa har k'asa don gaida Babaah Ajwa ta wuce da sauri ta haura sama Far'aan ya bita da wani mayen kallo ta k'asan ido.
. °•★|•°∵ TAURA BIYU ∵°•|☆•° . *
®𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵𝓸𝓿𝓮
08140754777
𝐜𝐡𝐚𝐭 𝐦𝐞 𝐮𝐩 𝐤𝐮 𝐬𝐚𝐦𝐮 𝐥𝐢𝐭at𝐭𝐚𝐟𝐚𝐢𝐧𝐚 𝐛𝐢𝐬𝐚 𝐫𝐚𝐡𝐮𝐬𝐚 𝐦𝐚𝐢 𝐬𝐚𝐮𝐤'𝐢.
𝐒𝐔𝐋𝐓𝐀𝐍𝐀𝐀𝐇 /
𝐆𝐔𝐃𝐔𝐍𝐀 𝐀𝐊𝐄/
𝐊𝐀𝐈𝐃𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐂𝐄/
𝐒𝐀𝐔𝐘𝐈𝐍 𝐋𝐀𝐌𝐀𝐑𝐈/
𝐙𝐔𝐁𝐀𝐑 𝐇𝐀𝐖𝐀𝐘𝐄/
𝐌𝐔𝐋𝐊𝐈/
𝐙𝐔𝐂𝐈𝐘𝐀𝐑 𝐌𝐔𝐓𝐔𝐌/
𝐍𝐎𝐎𝐑/
𝐒𝐈𝐋𝐀𝐇/
18+
❝𝙽𝚘𝚝𝚎: 𝙳𝚘𝚗 𝙰𝚕𝚕𝚊𝚑 𝚖𝚊𝚜𝚞 𝚔𝚒𝚛𝚊 𝚍𝚊 𝚌𝚑𝚊𝚝 𝚍𝚊 𝚊𝚞𝚍𝚒𝚘 𝚜𝚞𝚗𝚊 𝚜𝚘𝚗 𝚌𝚘𝚖𝚙𝚕𝚎𝚝𝚎 𝚋𝚘𝚘𝚔, 𝚢𝚊𝚗𝚣𝚞 𝚗𝚊𝚔𝚎 𝚝𝚢𝚙𝚒𝚗𝚐 𝚙𝚕𝚎𝚊𝚜𝚎, 𝚜𝚘 𝚙𝚕𝚎𝚊𝚜𝚎 𝚋𝚎 𝚙𝚊𝚝𝚒𝚎𝚗𝚝 𝚠𝚒𝚝𝚑 𝚖𝚎. 𝚝𝚑𝚊𝚗𝚔 𝚢𝚘𝚞☺️❕❞
【Pg11&12】
Tana shiga d'aki kai tsaye gado tayi k'ok'arin hayewa Mom ta d'an watsa mata harara ta kama Suliem zasu fito ta juyo kan Ajwa
“zoki wuce anyi bak'i ki ke k'ok'arin sake kwanciya bayan kinsan Babaah yana nan”
Baki Ajwa ta d'an zumbura. To ita kuma yanzu idan ta sake fita me zatayi? Badai ta shigo dasu ba? Dama ai wajen Suliem suka zo. Idan ta sake fita Asad ya mata kallon banza to zata manta wai bak'ine don zuba masa rashin mutunci zatayi babu ruwanta da Babaah. Tana k'unk'uni ta biyo bayan Mom da Suliem dake ta kankame Mom kaman za'a ce kyet ta kwasa a guje. Tunda suka fito bugun kirjin Suliem ya ninniku har tana ji kaman zuciyarta zata fito waje. Suna sakkowa Babaah na k'ok'arin hawowa yana cewa bari ya kira su. Yana ganin su ya watsa musu mugun kallo a kaikace mai tattare da kashedi. Ajwa dake bayansu ta wani taune harshen ta cikin bakin ta. Kamshin turarensu gaba d'aya ya cike falo saida Suliem ta d'ago don taga mamallakin sa. Gabanta ya sake yankewa ya fad'i. Mafarki take ko idan ta ne yake mata gizo? Mutumin data jima tana dakon soyayyar shi shine haka gabanta? Lallai ance Allah buwayi gagara misali. Bata san sanda ta saki wani irin murmushi ba duk wani damuwa da b'acin rai dake cinta ta nemeshi lokaci d'aya ta rasa. Kan kujera dake facing tasu Mom ta zaunan da ita kafin ta zauna gefenta tana musu murmushi. Sake zamowa sukayi su duka suna sake gaida Mom cikin ladabi ta amsa fuska a sake. Babaah kam duk ya rasa ma inda zai saka su duk ya wani birkice kace saboda shi suka zo. Kusa da Mom Ajwa taja tunga ta tsaya tana kallon gefe don yanda take jin haushin Asad bama zata iya zama ba. Babaah ya watsa mata harara ta gefen ido amma bata san yanayi ba. Bayan y'an gaishe ,gaishe Mom sosai ta yaba da hankalin su. miƙewa tayi ta ja Ajwa zuwa kitchen tasata fara fito musu da abinci. Kan tebir ta jere abinci fuska a cunkushe. Duk tsawon wannan lokacin kaf gaba d'aya hankalin Far'aan yana kanta full attention nashi ya bata kota kan Suliem dake zaune gabansu bai bi b. Yanzu dai ya fuskanci Suliem itace yarinyar da zai aura sosai kuma hakan bai masa dad'i ba. Like Suliem bawai bata masa bane don itama ba baya ba wajen kyau, amma hankalin sa yafi karkata kan Ajwa. D'an murmushi ya yi don tuni ya gama tsara plan nashi. Ajwa itace yarinyar da zai aura inba haka ba kuwa a fasa auren. Hadad'd'en coconut drink da sukayi musu ta zuba musu a cup ta d'auka saboda al'ada irin nasu na larabawa ta miƙa musu d'aya bayan d'aya daya. Su'ad ta fara mik'awa ya k'arba yana murmushi tare da godiya kafin ta matsa wajen Asad dake tsakiya ta mik'a masa shima fuska babu yabo babu fallasa.
A wani yangance ya d'ago ya watsa mata manyan black eyes nashi kafin ya mik'a hannu kaman baya so zai k'arba , sai kuma ya mik'a ya d'auki ruwa ruwan roba dake kan tire ya barta da lemo a hannu bisa iska. Waiii, kankame kofin Ajwa tayi cikin hannunta idonta tuni ya fara rinewa lokaci d'aya saboda b'acin rai, kafin tayi wani yunk'uri Far'aan ya yi maza ya k'arbe daga hannun ta yana zuba mata murmushi da wata irin sexy murya a hankali yace
“thank you. Cutie ”
D'an runtse ido tayi ta fesar da wani huci mai zafi kafin ta sake bud'ewa kan Asad da yanzu ma ya fito da wayar sa yana dannawa kaman gunki ne tsaye a gabansa. Leɓen ta na k'asa ta cije ta d'an juya inda Babaah ke zaune karaf kuwa idonta ya fad'a cikin nasa yana mata wani irin kallon na warning 'wato kiyi wani abu yanzu kici uwar ki a nan'. Wayyo zuciyar Ajwa kaman tayi bindiga. Da zafin rai ta wuce fuu zata haura sama Mom tayi saurin rik'eta tana murmushi ta dawo da ita ta zaunan kusa da ita. Da yake Ajwa tana tsaye gaban Asad ne basu lura da abunda ya faru tsakaninsu ba. Kallon Babaah, Mom tayi suka tashi don basu guri. Shiru falon ya d'auka kaman babu mutane idan ka cire Far'aan daya kafe Ajwa da mayun idonsa kaman wanda ya warke makanta. Suliem sai wasa take da gefen mayafinta Allah kad'ai yasan meke cikin ranta. Ganin shirun ya yi yawa yasa Su'ad yin y'ar gyaran murya yana kallon Suliem yace
“to amaryar mu, fatan mun same ki lfy? Y ki ke ya kuma karatu?”
A kunyace tana sake jan mayafi fuskarta tace “lfy lau alhamdulillah ”
Ajwa ta tab'e baki cikin ranta tace 'aikin banza'. Cike da tsanan Asad ta kalleshi da wata muguwar harara unexpected kaman wanda aka ce ya d'ago sai cikin idonsa. Aikuwa ta sake zare manyan idanta da suka sake fitowa rau ta cikin glass da wata muguwar harara. Yanda idanuwan suke wani farfar ta cikin glass d'in kaman mai shirin hawa aljanu ,duk yanda Asad yaso daurewa saida ya buɗe baki cike da mamaki ya mayar ya rufe kafin wata irin deep dariya ta biyo makoshinsa dimples nashi suka lotsa. Gaba d'aya suka juyo kallon sa Far'aan da Su'ad ya yi saurin shanyeta yana gyaran murya ya wani waske ya cigaba da duba wayar sa a ransa yana cewa
'Interesting. Yarinyar tana da abun dariya matuk'a. She's a fiesty one'
Kwafa Ajwa ta sake ja ta kai hannu ta tura glass nata kan fuska kafin ta mayar ta harde shi cikin K'irjin tana turo d'an k'aramin bakinta. Duk wannan action da tayi kan idon Far'aan. Wani lashe baki ya sake yi tabbas baida ja she's one in million. Komai tayi wani irin kyau take k'arawa da alama ita bata san hakan ba. Su'ad ya sake gyara murya yana kallon Suliem da har zuwa lokacin kanta ke katsa Allah kad'ai yasan meke cikin ranta.
“da fatan dai zaki k'arbe mu hannu bibbiyu don mu bamu da matsala inshaAllahu, ko ba haka ba Far'aan?”
Yana kallon Ajwa ya yi wani d'an iskan murmushi ya kai lemo bakinsa kafin ya mayar da idonsa kan Suliem.
“yes, bani da matsala. ”
“to alhamdulillah, Allah ya ubangiji ya sanya albarka a ciki wannan aure naku ya kuma Baku zaman lafiya da kuma fahimta.”
“Amin. ”
Duk suka amsa harda Asad daya sauke wata boyayyiyar ajiyar zuciya. Abun yazo da sauk'in da baiyi tunani ba. Miƙewa sukayi Asad ya ajiye ledar da Mamee ta bashi gaban Suliem da bandir
D'in dubu guda biyu da d'an k'aramin card nashi yace da deep voice yana kallon Suliem.
“duk sanda ki ke buk'atar wani abu, feel free to call me. ”
A hankali Suliem ta d'ago ta kalleshi yana k'ok'arin juyawa , saurin maida kanta tayi k'asa k'irjinta na cigaba da harbawa. Tunda ya sunkuya yake kallon Ajwa ta gefen ido sai zuba masa harara take kaman idon zai fad'o k'asa, da ya yi magana ma har wani tab'e baki tayi tana juya ido sama tana magana kaman mai maimaita abunda yake cewa amma a zahiri cewa take
'yenyenyenyenyen. Shegen iyayen banza da wofi''
Duk yana lura da ita ya saki murmushin gefen baki ya juya suka fice da Su'ad suka bar Far'aan dake zaune har lokacin yana kallon su. Da sauri itama ta tashi ta haura sama ta barsu su sake ganawa. Da kallo ya bita kafin ya sauke kan Suliem yana murmushi. D'an karkatar da kai ya yi gefe yana k'are mata kallo. Yarinyar tayi amma hankalin sa yafi kwanciya da k'anwar. Thirst nashi gaba d'aya yana kanta ne kuma sai ya sauke shi. Baice mata komai ba ya mik'e ya yi waje abunsa ransa tas.
Wani gauran numfashi Suliem ta sauke bayan ya fice hawaye suka taru cikin idonta. Jiki a salube ta miƙe itama ta haura sama. D'akin Ajwa ta shiga ta sameta kwance tana duba waya. D'agowa Ajwa tayi tana kallon Suliem dake shigowa da kaya ta yunk'ura ta miƙe zaune
“har ya tafi?”
“Hmm”
Kawai Suliem tace ta zauna gefen gadon batace komai ba. Sake kallonta Ajwa tayi ganin reaction nata ta sake cewa
“menene ko baiyi miki bane guy d'in? If you ask me. Mutumin ya yi babu k'arya. You will learn to love him idan kin aure shi Suliem”
Ita dai Suliem batace komai ba ta buɗe jakar da Asad ya ajiye mata. Kayan turarrukane masu tsada sai tarkacen chocolates da wata dankareriyar sarka ta duwatsu. Ajwa bakin kwadayi tuni ta k'arbe chocolates din ta fara kaiwa baki. Shigowar Mom ya katsewa shirun da sukayi ta samu guri ta zauna tana murmushi da kallon Suliem. Sosai ta yaba da hankalin su kuma ta nuna amincewarta d'ari bisa d'ari kan auren Far'aan da Suliem. Ita dai Suliem tana jinsu bata ce komai ba musamman yanda Mom keta yabon su. Ita kad'ai tasan meke cikin ranta. To bayan sun tafi Ajwa ta fito da sauri don kwashe abincin ta kai musu d'aki saboda ko cokali basu tab'a ba. Ga mamakin ta tana saukowa ta iska Babaah ya saka abincin a gaba yana ci hankali kwance. Turus ta tsaya tana kallon sa cikinta ya fara kukan yunwa. Harara ya watsa mata tana tsaye ya gama cin abincin ragowar ya kwashe ya yi kitchen dasu. Kai tsaye ya maida su store ya sake gark'amewa da kwad'o kafin yazo ya wuceta ya fice yana mata kallon mu zuba nida ke. Idan kin isa kije ki buɗe.
Bak'in ciki kaman tayi hauka. Ta jima a tsaye tana sak'awa da warwarewa kafin taja wata mugun kwafa ta koma sama. Har lokacin Mom da Suliem suna d'akin ta, Mom sai sake kwantarwa da Suliem hankali take game da aurenta da Far'aan. A zafafe ta zauna ta fisgi sauran chocolates da biscuits tana ci amma sam ta daina jin dad'in su saboda yunwa take ji sosai.
Daga Mom har Suliem babu wanda yace mata komai don sun san b'acin ranta yana da nasaba da Babaah.
────────────────────────
Ana kiraye-kirayen sallah magriba suka shiga cikin Abuja. Nan masallaci dake kusa da layin nasu suka fara tsayawa sukayi sallah. Koda suka k'arasa gida saida suka fara wanka sannan suka had'u babban falon gidan kaman yanda Dad ya nema. Cikin nutsuwa suke cin abinci mara nauyi da Mamee ta dafa musamman saboda Asad. Daga shi har Far'aan babu wanda ya wani saki jiki saboda Dad dake zaune. Da Far'aan ya dage ma zabai zoba saida Asad ya d'an nuna b'acin ransa sannan ya fito kuma yana so dama ya fad'i hukuncin daya yanke. Yanda kuwa sukayin ba k'aramin sosa zuciyar Dad ya yi ba. Dan gyaran murya ya yi yana kallon Far'aan daya kai drink bakin sa yace
“ina fatan babu wata matsala da yarinyar ko Hassan? Tayi maka ka bada dama a tura gidan nasu neman auren ta ko?”
Saida ya k'urbe lemon sannan ya ajiye kofin yana kallon Dad yace
“yes na amince amma da sharad'i”
Asad dake zaune gefen sa ya yi saurin daga manyan idanuwansa kan Far'aan. Da mamaki sosai Dad yace
“wane irin sharad'i kuma Hassan?”
“na amince zanyi aure, amma ba wacce ka ke so na aura nake so ba. K'anwar ta nake so. Ita nake so na aura”
Ba Dad ba har Asad saida gabansa ya yanke ya fad'i shi kansa baisan dalilin hakan ba. Ran Dad kuwa in ya kai dubu ya b'aci da fad'a ya kalli Asad yana cewa
“kaji ko, kaji irin halin nasa ko? Yana so ya maidani k'aramin mutum. Yaje da bakinsa yace zai auri yarinya yanzu kuma ya ce wai ba ita ba. Wane irin zubda mutunci ne wannan ?”
Wani irin lumshe ido Asad ya yi ya kai hannu ya dafe goshinsa daya fara masa wani mugun ciwo. A zafafe Far'aan ya tashi yana huci
“kaga Dad. Wannan auren dama saboda Asad nace zanyi badan kai ba. Shekara nawa baka taba damuwa da damuwar mu ba sai lokaci guda kawai kace ka fidda min mata?. Na saka nemamin mata ne ko nace maka ina son yin aure? I'm doing this sobada Asad bawai saboda kace nayi bane. Kace nayi aure nace ga wacce nake so, so ruwanka ka gaya musu d'aya yarinyar nake so ko kuma a fasa auren gaba d'aya. Dama ai ba shawara kayi dani ba bare kaji ta bakina.”
“Hassan”
A tare Asad da Dad suka kirashi da tsananin b'acin rai. Mugun kallo Far'aan yawa Asad irin don't. Kar ka shiga abunda babu ruwanka kafin ya wuce fuu yabar site d'in. Sauke numfashi Asad ya yi ya kalli Dad da jikinsa gaba d'aya ya yi wani irin sanyi. Sam baiji dad'in rashin kunyar da Far'aan d'in ya masa ba ko ba komai yana da wannan matsayin na uba a gurin su. A hankali yace
“kayi hak'uri Dad. Zan masa magana”
Da sauri Dad ya d'ago jin muryar Asad d'in. D'an murmushi ya yi yana d'an jinjina kai. Mamee ta d'an yunk'ura tana kallon Dad da Asad tace
“ina ganin shawara tunda har yace zaiyi aure, kuma dama ance ne yaje yaga yarinyar idan tayi masa. To tunda yace k'anwar ta ta yake so ba auren ya fasaba da a kira a gaya musu sai a basu hak'uri ya nemi k'anwar kawai ko?, ina ganin auren wajen Hassan shine mafita yanzu”
D'an shiru sukayi gaba d'ayan su. Su'ad ya dan jinjina kai yace
“maganan Mamee gaskiya ne. Tunda mukaje na lura hankalin sa yafi karkata kan Ajwa. Ina ganin idan akayi hakan ma babu laifi a ciki.”
Asad kam wani irin numfashi ya sauke baisan me yasa ba yake jinsa wani iri. Waya Dad ya fito da ita ya dannawa Babaah kira babu b'ata lokaci. Saida suka sake gaisawa yana musu ban gajiya sannan Dad ya sanar dashi hukuncin da aka yanke. B'angaren Babaah babu wani danuwa yace hakan ma babu laifi duk da Ajwa da Suliem duk d'aya suke. A take Dad yace sati mai zuwa zasuzo a kawo kudi a kuma saka rana don ya matsu ne ayi auren cikin gaggawa.
Jikin Asad babu wani kuzari ya miƙe ya fito bayan gama wayan Dad. Shima Su'ad biyoshi ya yi. Kwance suka sami Far'aan falon su yana waya sai zuba murmushin nan nasa yake na mayaudara. Kallo d'aya Asad ya masa ya wuce d'aki don har zuwa lokacin ransa a b'ace yake dashi. Su'ad shine ya zauna nan falon don sanar masa da hukuncin da aka yanke. Wanka ya sake shigewa kaman wani d'an ruwa. Shower ya sakarma kanshi ya jingina kansa ruwan na sauka a kansa. Unexpected Ajwa ta fad'o masa cikin ido sanda tana wannan hararar tashi. Saurin runtse ido ya yi fesar da wani huci mai zafi. Me yasa daga daz'u zuwa yanzu ta y'ar yarinyar ke naman damunsa ne. D'an wannan zafin kan nata sosai ya burgeshi shi kansa baisan dalili ba. Fesar da huci ya yi mai zafi ya kai hannu ya tura cikin jikakken gashin sa yana jin yanda numfashin yake fita da sauri da sauri alamun ciwon sa na neman tashi.
────────────────────────
Washe gari k'arfe bakwai Ajwa ta fita exam bata ko karya ba saboda bak'in cikin Babaah duk da cewa da safe ya fito musu da abunda zasu karya dashi. Daga jiya zuwa yau dai sun dan samu sauk'in bala'in sa. Don har Ajwa ta fice baiyi hargagin sa ba. Babaah da Mom ne zaune falo ya baza uban takardu a gaba yana bi Mom na zaune gefe tana kallo jefi-jefi tana satar kallonsa. Suliem ya kwalawa kira tana fitowa yace ta kawo masa tea. Jiki na rawa ta wuce kitchen. D'aga kai ya yi ya kalli Mom fuska babu wasa yace
“yauwa jiya bayan tafiyar yaran nan mahaifin su ya kira ya sanar dani cewa shi yaron Ajwa yake son aure, saboda haka maganan auren ya tashi daga kan Suliem ya koma kan waccan fitsararriyar. Wani satin zasuzo tambaya da kawo kudi. Anjima zan kira Saudiya na nasar dasu domin duka duka bana tunanin auren da komai zai wuce sati biyu”
D'an shiru Mom tayi tana kallon sa kafin tace a d'an sanyaye
“amma kana ganin in anyi hakan an kyautawa Suliem? Ita fa yazo ya gani kuma ya koma gida sai yace ba ita ba bayan itace aka ce yazo saboda su daidai ta?”
“to ya ki ke so ayi tunda yace ba ita yake so ba? Da ita da Ajwa menene ya yi su duk ba abu d'aya bane?. Ajwa ko Suliem duk wacce yace yana so a ciki ita zan bashi magana ta k'are ”
Bai jira ta sake cewa komai ba ya tashi ya kad'a takardunsa ya haura sama. Jikin Mom ya sake sanyi tabi sa da kallo. Sam Babaah bai damu halin da yaransa zasu shiga ba a zahiri ko a b'oye. Shi kawai buk'atar sa ta biya shikenan burin sa koda kuwa hakan na nufin zaita wasa da zuciyoyinsu. Suliem dake tsaye tun daz'u bakin k'ofa ta kusa yarda tiren dake hannun ta. Wani irin kuka ne ya kusa kwace mata amma tayi maza ta shanye kafin ta fito da d'an yak'e kan fuskarta. Bata nunawa Mom dake kallon ta ba taji maganan su ba ta ajiye tiren ta wuce da sauri saboda kukan dake cinta. Har Ajwa ta dawo Suliem na d'aki taci kuka har ta gode Allah saida kanta ya fara ciwo. Tana shigowa kai tsaye d'akin ta nufa don watsa ruwa. Sosai yau taji dad'in exams d'in duk da batayi wani karatun kirki ba shi yasa tana fitowa direct gida tayo. Cikin karamar riga da wando baki ta shirya sai hula data d'ura a kanta ta saki gashinta ya zubo gadon bayan ya iska nata kad'ashi. D'akin Suliem ta shiga rike da d'an Qur'ani a hannun ta zatayi tilawa. Tana shiga d'akin dumd'in babu haske Suliem nacan k'uryar gado Ida nan ya yi luhu-luhu tsabar kuka. Da d'an mamaki Ajwa ta k'arasa shiga bayan ta kunna fitila. Yanda taga Suliem d'in ya d'an daga mata hankali a tashe ta fara jera mata tambaya.
“ya Suliem menene? Ko baki da Lafiya ne?”
Wani sabon kuka ne ya kare kwace mata bata ,ba ta amsa ba. Hankalin Ajwa ya sake tashi. Saida Suliem tayi kuka mai isarta sannan ta share majina ta kalli Ajwa da jan ido murya a dashe tace
“wai Far'aan ne yace ke yake so zai aura. Next week za'a kawo kudi kuma a saka rana dake”
“kutumar uba. ”
Ajwa ta d'ura wani uban ashar. Lallai ana yinta. Wani irin miƙewa tayi jikinta na rawa
“mai suka maida mu? K'ananan yara da zasuna juyawa yanda suka ga dama kaman wasu abun wasa? Billahillazi basu isa ba. Daga su har Babaah banga wanda ya isa ya sani wannan auren ba”
Fuu ta fice da bala'in sauri kaman zata tashi sama. D'akin Mom ta kutsa ko jiran a bata izni batayi ba. Zaune ta samu Mom kan dadduma tana Jan carbi ta hau ihu
“Mamaa wane irin magana nake ji haka?saboda me Babaah zai amince da maganan su suna juya mu kaman waina?. Suliem yace ya zab'ama wannan mutum kuma kawai sai yace ni zai aura saboda ya raina mana hankali?”
Sauke numfashi Mom tayi ta kalli Ajwa dake ta girgiza kaman mai shirin yin dambe. Sake sauke ajiyar zuciya tayi ita dama tasan za'a sha daga da ita. Kafin Mom ta ce wani abu Ajwa ta sake cewa tana huci
“na rantse da Allah sai sunga tashin hankali idan basu janye wannan rainin hankalin ba. Mu ai ba k'ananan yara bane marasa tunani”
“zagaye zagayen me ki ke. Ki fito fili kawai kice ni ubanki dana amince ni ne bani da hankali kinji ko. Bari kiji ko yanzu ya sake cewa Suliem yake so zan bashi saboda na isa kuma na kai. Idan har kinga ba'ayi wannan auren ba to sai in mutuwa ki ka yi ko shi yace ya fasa. Shashasha yarinyar kawai mai bak'in hali wacce arzik'i ke bi tana gudu”
Murya Babaah ya ratsa kunnen su. Ashe tun shigowar ta yake tsaye bakin k'ofa yana k'ok'arin fita bata lura dashi ba saboda idonta daya rufe. Ido kawai Mom ta lumshe tanajin duniyar gaba d'aya tayi mata zafi. Mugun kallo Babaah ya kewa Ajwa yana jira tayi masa tizajar data saba yaci ubanta yanzu nan. A guje tazo ta rab'a ta gefen shi ta fice tana danne kukan dake taso mata. Wlh babu wanda ya isa ya sata auren nan sai wani ikon Allah. Wajen Suliem ta sake fad'awa da har zuwa lokacin tana kwance. Kaman wacce aka wurgo ta fad'o d'akin tana
“ya Suliem baki da number wayar sa?.”
Jajayen idonta ta d'ago ta watsawa Ajwa tana girgiza kai can kuma ta d'an zare ido ta miƙe da sauri ta bud'e drawer ta d'auko dan card d'in da Asad ya bata. A guje ta warce shi ta juya da sauri ta fice daga d'akin. A haukace ta d'auko wayarta ta hau kiran number Asad dake rubuce jikin katin . Saida ta jera kira wajen hud'u amma shiru ka ke ji babu amsa. Kaman tayi hauka bata fasaba ta k'ara danna masa wani kiran.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 15