Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ihu ya saki harda tsalle ji yake kaman ya taka rawa. Yes ya kusa cinma burin sa. A guje ya k'arasa ficewa daga hotel ya fad'a mota ya tasheta a guje zuwa airport's . Toh fa. Ana wata ga wata inji y'an caca. Kuna ganin Far'aan zai cimma burin sa. Shin Javaria sa gaske kuma wane tuggu take had'awa haka.? . °•★|•°∵ TAURA BIYU ∵°•|☆•° . * ®𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵𝓸𝓿𝓮 08140754777 No edit! 【Pg15&16】 Tunda ya d'auko Asad daga Airport gaba d'aya yake jin wani irin on easy feeling musamman yanda Asad d'in har zuwa lokacin yak'i yi masa magana haka fuskarnan tashi tana nan babu wani emotion a kanta. D'an fesar da huci ya yu yana kallon titi da danja ta basu hannu ya wuce da sauri ta gefen ido ya sake kallo. Asad dake kallon waje . D'an gyaran murya yi kafin yace “kaji maganan kai kud'ina wajen Kawu? Sun amince next week za'a d'auramin Aure da Ajwa. How lucky I'm ” Sosai k'afad'un Asad suka sake tense bai juyo ya kalli Far'aan ba bare ya ga yanayin da yake ciki. Sake kallonsa Far'aan ya yi jin ya yi shiru baice komai. “wai lafiya ko nayi maka wani laifin ne? Ko har yanzu fushin ka ke baka huce ba?” Sai a lokacin Asad ya juyo ba watsawa Far'aan wani irin mugun kallo kafin yace da kaushin murya “kayi mun k'arya Far'aan, why? Dama akwai abunda zaka b'oyemin?” “Ban gane wace irin magana ka ke ba. K'arya wace iri kuma Asad?, menene a duniyar nan da zai faru na b'oye ma?” Sosai Asad ya zuba masa manyan idanuwansa kafin ya furta maganan data sa Far'aan ya kusa taka birki tsak'iyar titi. “ka yi aure a b'oye babu wanda ya sani. True or false?” Saurin kallon Asad ya yi dake kallonsa da wannan cold expression d'in ya yi saurin maida kai kan titi k'irjinsa na wani irin harbawa. Taya akayi Asad yasan wannan maganan?. Faka motar ya yi gefen titi kafin ya juyo gaba d'aya yana kallon Asad. Mugun had'e fuska ya yi kafin yace “wace irin magana ce ka ke haka? Kana tunanin akwai wani abu makamancin haka da zai faru kana duniyar nan baka sani ba? Waye ya gaya maka wanna tatsuniyar?” Ido cikin ido Asad yace “Javaria” Sosai yake so yaga reaction d'in Far'aan don yana son ya gane gaskiyar lamarin. Dum k'irjin Far'aan ya sake bugawa da mugun k'arfi har wata y'ar zufa ce ta karyo masa amma a fuska ya yi hanzarin b'oye hakan. Yatsina fuska Far'aan ya yi cikin kwarewa da juya magana yace “wacece haka?, yanzu har akwai wata mace da zata tare ka ta gaya maka magana banza kuma ka yarda da ita Hussein? Har zaka yarda da wata sama da ni ?” Wannan cold expression dake fuskars Asad ya d'an kau ya sauke hannun sa dake hard'e a k'irji. Gaba d'aya kansa ya yi zafi ya rasa ma menene gaskiya cikin lamarin amma ya yarda da maganan Far'aan yasan abune da Far'aan bazai tab'a aikawata ba. Sauke numfashi ya yi a hankali ya d'an runtse ido kafin ya buɗe su kan Far'aan dake kallonsa yana jiran yaji mai zafi. Kaf ya kwashe yanda suka had'u da Javaria ya sanar dashi har hoton su da marriage certificate data nuna masa. Can k'asan ran Far'aan ya tsine mata yafi a k'irga. Baiyi zaton zata kusanci Asad haka ba. Wato huld'a da bature babban matsala ne. Ya godewa Allah da yasa ya rabu da ita daidai lokacin daya dace. Zancen ya barta da ciki k'arya ne tun yaushe ya rabu da ita amma bata san da cikin ba sai yanzu da take neman tarwatse masa rayuwa?. To a hir d'in ta dole yawa tufkar hanci tun kafin taje ta samu Ajwa. Don tunda har ta iya bibiyar Asad to la shakka babu abunda baza tayi ba don ganin ta hanashi farin ciki da samun kwanciyar hankali. Kai ya jinjina har da d'an b'ata fuska irin yaji haushin nan yace “just because wata banza ta tare ka ta tuna maka wasu fake hoto da takarda sai ka yarda da maganan ta d'ari bisa d'ari?. Haba look at me mata nawa ne suke so suga sun shiga rayuwata haka saboda sun kasa samun abunda suke so. Tsk. I'm disappointed” D'an sanyi jikin Asad ya yi ya kalli Far'aan daje k'ok'arin tada mota yace d'an sanyaye “I'm sorry. Bai kamata na yarda da wata sama da kai ba. Im sorry ” Shiru Far'aan ya yi amma can k'asan ransa wani b'oyeyyen numfashi ya sauke ya tada motar ba tare da juyo ya kalli Asad ba. Baya so ya fuskanci yanayin daya ke ciki. Har suka isa gida babu wansa ya sake cewa uffan. Can k'asan ran Asad yana so yace 'to Amma Ajwa fa, kana sonta ko kuma sha'awar ta ka ke Far'aan? ' amma ya kasa sai leben nashi da yake ta taunewa duk yana jinsa cikin damuwa dashi kansa ya rasa ta mece. Saida Asad ya yi wanka sannan ya kira Su'ad da yau kwana biyu kenan shima daya wuce can Kano wajen iyayen sa. Sun jima suna magana kafin ya kashe wayar ya koma ya kwanta kan gado kafafuwansa zube k'asan kafet. Numfashi yaja mai k'arfi ya fesar hannun sa guda d'aya kan fuskarsa ya rufe idon sa. Menene yake damun sa ne? Why yake jinsa so on edge kaman wani abu gagarumi na shirin faruwa?. Sake janyo wayar sa ya yi ya buɗe ya shiga contact nashi yana scrolling kafin ya tsaya kana LITTLE TIGER ya zubawa number ido. Bai son me yasa ba yaji yana son ta sake kirashin tana mishi wannan tsiwar nata. Gata yar mitsitsiya da ita amma akwai tsiwa. Shi kansa bakin wani d'an mitsitsi dashi baza kace daga cikin sa wannan tsiwar yake fitowa ba. Ko ya bakin zai kasance idan aka sumbace shi? 'No, tunanin me ka ke haka?'. Ya wani furta da k'arfi ya miƙe zaune yana zare ido kaman wanda ya yi wani mugun laifi. Far'aan ne ya shigo d'akin Asad ya sake d'an zabura irin na marasa gaskiya. Wani irin kallon tuhuma Far'aan ya watsa masa kafin ya wuce toilet fuska babu Walwala shi wai dole ya nuna b'acin ransa saboda nan gaba koda zata kara zuwa ta same shi bazai yarda da abunda tace ba. Da kallon irin na marasa gaskiya Asad ya bishi yana shigewa ya saki wata irin ajiyar zuciya kafin ya koma da k'arfi ta baya ya kwanta kan gadon. A zuci yake cewa 'Why ka ke wannan tunanin kan yarinyar da Far'aan zai aura? You don't even know her yet' To shi kansa baida wannan amsar. Yana nan kwance Far'aan ya fito d'aure da tawul a kugu har zuwa lokacin fuska babu Walwala. Duk Asad sai yaji baiji dad'i ba sai binsa da kallo yake saboda hukuncin shirun ya yi masa tsauri. Shi idan zaiyi baijin wani abu amma yanzu da Far'aan d'in yake masa duk ya shiga damuwa. Yana kallo ya saka gajeren wando ya feshe kansa da turare kafin ya hauro gadon ya kwanta ya juya masa baya. Numfashi kawai ya sauke baice masa komai ba ya yi Addu'a ya shafe jikinsa. To ko washe gari da suka tashi saida Dad da Mamee suka fuskanci yar tsamar da suke don Far'aan koda suka had'u wajen breakfast yak'i kallon Asad bare ya amsa yar maganan da yake masa jefi-jefi. Suna tsak'iyar cin abincin ya mik'e kaman wansa aka tsikara duk suka zuba masa ido. “ba dai har ka koshi ba Far'aan?” “Yes” kawai yace ya juya ya fice da sauri. Yana fita mota kawai ya fad'a ya fice daga gidan. Saida ya fita daga layin ya faka motar a gefe ya d'auko waya ya dannawa Javaria kira. Bugu d'aya ta d'auka murmushin ta ya ratso cikin wayar. “yes,Far'aan” Huci ya sauke mai zafi jijioyin kansa sun fito radau saboda b'acin rai yace “listen and listen good Javaria, ni nafi k'arfin kice zaki shiga tsakanina da d'an uwana. Your smart but not smart enough. Brother d'ina bazai tab'a yarda da duk wata magana da zaki sake yiba so drop and cut all this nonsense don nafi k'arfi ki. Nace bana son ki why har yanzu ki ke bibiyata?. Munyi aure once kuma munyi divorce. Move on with your life and let me be. Kar kisa nayi abunda zamuyi regretting nida ke. Ina da wata a rayuwata yanzu so ki barni nayi focus a kanta. ?” A zafafe itama tace “na rantse da Allah baka isa ba dole kaima sai ka d'and'ana kunci da uk'ubar rayuwa dana shiga. Saboda kai na rasa abubuwa da dama cikin rayuwata. Dangi, iyaye, y'an uwa. To baka isa ba wlh baka isa ba. Idan har kana ganin wannan shi ne plan d'ina na k'arshe a kan ka ,to tabbas kai wawa ne. Kana manta ni wacece Far'aan. Yarinyar daka kwallafa rai a kanta yanzu zanga yanda zaka aureta matuk'ar ina numfashi. Ina nan d'auke da cikin ka kace min zakayi aure? Do you think I'm that stupid na barka ka samu farin ciki a rayuwar ka bayan abubuwan daka min?ka jira ka gani. Naga ta yanda zakayi auren nan” Ko kafin yace wani abu ta kashe wayar. Wai me yasa take ta insisting tana d'auke da cikinsa? Kaman ya yi hauka ya hau dukan sitiyarin motar yana ihu shi kad'ai. Can ya d'aga wayar sa ya kira Anila yarinyar data zo tun daga Somali ta masa kyautar mota har yanzu tana nan bata koma ba. Yana zuwa wajenta suka fara shashancin su ya manta da wata Javaria da kuma treat data masa na hanashin auren Ajwa. After all menene zatayi? K'ark'ari tace zata tona masa asiri ne kawai yana da brain da zaiyi manipulating abun ya kuma k'arya ta ta kaman yanda ya yi wa Asad ya nuna masa shi Victim ne. Idan tasan wata bata san wata ba ba banza ba yake Far'aan. Tsawon kwana biyu suna wannan y'ar tsamar don duk wata hanya da Asad zaiyi masa magana baya kulashi. So yake sosai ya nuna masa yaji haushin hakan amma kuma a zahiri ba gaskiya bane. Duk abunda Javaria ta fad'a gaskiya ne babu k'arya a ciki. Shi a ganinsa abu ne daya riga ya wuce bai san menene yasa take son dawo da hannun agogo baya ba. ──────────────────────── To b'angaren Ajwa itama dai abun sai a hankali don sosai take cikin wata irin matsananciyar damuwa har wata y'ar rama ta yi. Idan kaga yanda Babaah yake nan nan dasu da basu kulawa sai kasha matuk'ar mamaki musamman Mom da naya shakkar nuna mata soyayya gaban kowa. Ajwa tasha attempts na furta bakaken magana duk sanda taga ya yi wani abu gaban su Baffa da Ammi kansu ko Mom, idan Mom da Suliem yake hanata furta komai. Lokaci yana tafiya Ammi da Aunty Raihana a shirye suka zo don tun washe gari da suka tashi suka fara jike-jike suna bawa Ajwa tana sha. Da farko sosai tayi tijara saida ran Ammi ya b'aci tayi mata jan ido sannan ta k'arba tasha. Tun daga ranan da b'acin rai ake yin gyaran jikin. Har mamaki suke ganin yanda ta tsani abun matuk'a saida Baffa suka saka baki da Lallashi. Mom da Suliem babu wanda yake cewa komai idan tana wannan tijarar ,har da Babaah ake had'uwa dasu Baffa ana lallaminta amma tasan kasan ran Babaah kaman zai shaketa ne don tana lura da mugun kallon da yake jefa mata a kaikaice. B'angaren Suliem kam ta sake yanzu sosai take Walwala baza kace itace kwana biyu take cikin kunci ba. Sai ya kasance Ajwa ta maye wanna gurbi. Ta zama wata irin silent kullum tana kulle d'aki in kaga ta fito to Ammi tasa ta a gaba saboda gyaran jiki. Badan wannan gyaran da suke mata ba tsab zata lalace ta sake figewa saboda yanda ta sawa ranta damuwa duk ta tsangwami kanta. Ance rana dai bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya. Daran yau na Juma'a saboda yanda ta tsananin saka damuwa a ranta haka ta tashi da wani bala'in zazzab'i har rawar sanyi take saida aka kira doctor yazo ya saka mata ruwa. Babu wanda bai shiga damuwa ba matuk'a saboda yanayin data tashi a ciki amma hakan bai hana su cigaba da gudan da hidimon su ba musamman ma saboda su Nonna dake hanya sun taso tun asuba. Wajen goma kuwa suka dira Nigeria lokacin sa suka k'arasa har Ajwa na barci saboda ruwa da aka saka mata. A hankali Nonna ta zauna gefen gadon rike da y'ar sandan ta fuska d'auke da farin glass na k'ara k'arfin ido. D'akin ya cika da dangi kowa cikin damuwa amarya guda babu lafiya. Hannu Nonna ta kai ta shafa fuskar Ajwa da tayi wani fayau ta d'ashe kaman wata vampire. “Bint, ya Binta. Subhanalla. Meke damun ki haka ya Bint?” Sama-sama Ajwa take ji muryar Nonna tana k'ok'arin bud'e ido. A hankali ta sauke su kan Nonna da sauran dangi dake d'akin. Bata san sanda ta wani yunk'ura ba da wani bala'in gudu ta fad'a jikin Nonna ta fashe da wani irin kuka mai sosa rai. Jikin kowa ya yi sanyi Nonna duk ta kalle su tace kowa ya basu guri ta lallashe ta. D'aya bayan d'aya duk suka fice jiki a sanyaye. Da kyar Nonna ta samu Ajwa tayi shiru. Cike da lallami tace “haba ya Bint. Kaman a kan ki za'a fara aure?,munan duk ba ta hanyar auren aka same mu ba? Wannan ramar da ciwon duk na menene? Saboda zaki raya sunnan Ma'aiki? Kar kiyiwa Allah butulci mana ya rufa miki asiri . Menene abin gudu game da aure humm?” Kai Ajwa ta sauke wasu hawaye suka biyu kuncin ta. Babu wansa zai fuskance ta yanzu ya san halin da take ciki. Tana ji tana ganin ruwan na k'arewa Nonna tasa aka yi mata wanka aka shirya cikin wani Jan less da suka zo dashi tun daga can Saudiya yasha uban stone da gwal. Basuyi mata wani kwalliya ba suka barta don sunga har zuwa lokacin bata da wani kwari. Wajen azahar mutanen Abuja suka iso . ──────────────────────── Goshin sa Asad ya dafe saboda wani irin matsanancin ciwo da kan nasa yake ga gaban sa dake ta fad'uwa kaman zuciyar sa zata fito waje. Hadad'd'ediyar blue shadda ce a jikinsa data sha surfani ya bala'in kyau idan ka gansa baza ka iya d'auke ido ba. Hular sa ya cire ya shafa lallausan gashin sa daya turashi baya ya kwanta k'eyarsa. D'an huci ya fitar mai zafi yana sake kai wayarsa kunnen sa bayan ya danna kira. Har zuwa wannan lokacin wayar dai a kashe take. Su'ad dake tuk'i shima yasha Ash shadda yace “har yanzu wayar tashi a kashe take? To ina ya tafi yasan kuma akwai tafiya a gaban mu ” Sake fesar huci Asad ya yi kafin yace wani abu wayan nashi ya hau k'ara. Da sauri ya d'ago ya yi tunanin ko Far'aan ne sai yaga akasin hakan. Dad ke kiransa. Suna motar baya shida Kawu da kuma wasu y'an uwa daga cikin dangin mahaifin nasu. D'an lumshe ido ya yi kafin ya d'aga wayar “Hussein ya ya ne ka samu Hassan d'in kuwa gashi muna gab da shiga garin Bauchi?” Saida ya d'an cije baki kafin yace “no, ina dai sake gwada number nashi. ” Da fad'a sosai Dad yace “wannan wane iskancine da rashin mutunci irin na Hassan? Ko ya manta yau d'aurin auren sane ya saka k'afa ya fice tun asuba kuma ya kashe waya? Duk abunsa wanna auren babu fashi zai kuma dawo ya sameni daidai nake dashi. ” Kashe wayar ya yi kafin ya kashe Asad yana jin yanda Kawu suke bawa Dad d'in hak'uri. Komawa ya yi ya jingina da kujerar ido a lumshe yana fesar da wani irin huci mai zafi. Tunawa ya yi da fitar Far'aan d'in suna dawowa daga masallaci ya fice a sukwanne daga gidan bayan ya gama wayan da Asad d'in ya same shi yana yi a d'aki. Da sauri Asad d'in ya bisa yaba kiransa yace masa yana zuwa yanzu zaije ya dawo abu zai k'arbo. Baiyi tunanin komai ba saida gari ya waye shiru-shiru babu Far'aan babu labarin sa daya gwada wayan sa ma a kashe. Bai sake shiga tashin hankali ba saida Su'ad yazo da sauran y'an uwa nan hankalin Asad ya k'ara tashi don har zuwa lokacin babu wayan Far'aan har zuwa yanzu da suka d'auko hanya. Koda suka iso ma kallo d'aya duk zakayi musu ka fuskanci akwai damuwa tattare dasu musamman Asad. An k'arbe su hannu bibbiyu saida sukaci suka sannan aka wuce masallaci har zuwa lokacin Asad da Su'ad basu daina kiran wayan Far'aan ba. Ana idar da sallah aka fara shirin d'aura aure. Gaban Asad idan yafi dubu ya fad'i. Hankali tashe ya fito daga masallacin yana sake kiran wayan Far'aan d'in abun mamaki yanzu yana kira ta shiga tana shiga kuma ya d'aga. “Far'aan. Kana da kai kuwa kasan abunda kayi? Kana ina yanzu ? ” Da k'arfi ya yi maganan yana ji kaman ya shiga wayar ya rufe shi da duka. A sanyaye Far'aan yace “I'm sorry brother amma ni yanzu ina Airport zan bar k'asan nan.” “What me ka ke cewa ne kana da hankali kuwa?. Zaka bar k'asa kaman ya?” Numfashi Far'aan ya fesar ta cikin wayar mai k'arfi kafin yace “Yes yanda kaji haka ne. Zan bar k'asan nan yanzun I'm sorry amma ban shirya yin aure ba yanzu. Nasan kana da tarin tambayoyi nayi alkwari idan komai ya daidai ta zan gaya maka gaskiya dukkanin abunda ya faru, amma yanzu bani da lokacin yi maka bayani. Ina so ka sani duk inda zanje I will always be with you Asad. I love you so much. Ka gayawa Dad I'm sorry duk da bai cancani hak'uri na ba. I will see you soon” Kaman Asad ya yi hauka yake kiransa amma tuni ya kashe wayar daya sake kira ma sai akace masa wayar a kashe take. Ya Rabb menene yake faruwa ne? Rike kansa Asad ya yi ya juyo da sauri zai kira Su'ad abunda bai sani ba tun fitowar sa Dad ya biyo sa. Duk abunda ya faru cikin kunnen sa. Ran Dad na wani irin suya ya juya a zafafe ya shiga masallacin daidai ana kiran iyayen ango. Da sauri Dad ya matsa kusa da Kawu dake neman sa. Kallan Babaah ya yi da bakinsa yaki rufuwa shida su Baffa kafin yaja numfashi ya kalli liman yace “Angon da za'ayi auren dashi sunan sa Asad Al-Sultan. Ga sadakin sa na bayar matsayina na mahaifin sa. ” Iya wanda suka san waye aininhin angon wato Babaah, Asad, Su'ad sai dangin Dad duk suka d'ago cikin mamaki musamman Babaah da lokaci d'aya farin cikin dake kan fuskarsa ya kau ya wani zubawa Dad ido kaman wanda yake da kai biyu. Asad dake k'ok'arin shigowa kiris ya rage bai fad'i a gurin ba Su'ad ya yi saurin tare shi. Ko kafin ya k'arasa shiga masallacin tuni limami ya d'aura auren mai shela ya rangada da Babbar murya. 'AN D'AURA AUREN ASAD AL-SULTAN DA AJWA KHALID KAN SADAKI NAIRA DUBU D'ARI BIYU.' Jiri ya kwashi Asad yana neman fad'uwa Su'ad ya kamashi da sauri ya fito dashi daga cikin masallacin. To Babaah dai kam Allah kad'ai yasan menene ke cikin ransa don ya kasa motsi sai su Baffa ne keta Sam barka da farin ciki ana ta musabaha. SOME HOURS BACK. Y'an awanni da suka wuce. °•★|•°∵ TAURA BIYU ∵°•|☆•° . * ®𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵𝓸𝓿𝓮 08140754777 No edit! 【Pg17&18】 Kusan zance Far'aan kwana ya yi da wani irin farin ciki don ko barcin kirki baiyi ba, yana ta lissafin da safe iwar haka Ajwa ta zama tashi. Tun Asad na biye masa yana d'an tsokanansa har ya zuba masa ido kawai yana kallon sa sai fito da kaya yake yana tunanin wanda zai saka. A haka Asad ya yi barci duk da cewa shima barcin ba wani na kirki bane. Daga wannan lokacin zuwa asuba Asad zai iya rantsewa bai tab'a ganin Far'aan cikin irin wannan farin ciki ba, amma daga asuba komai ya canza. Bayan sun dawo daga masallaci text d'in Aria ya shigo wayar sa. Ya yi mamaki matuk'a daya ga bak'uwar number ce kuma daga nan Nigeria. Da farko ya watsar da number don ko text d'in bai duba ba saida wani text d'in ya sake shigo ya ciro wayar daga aljihu yana d'an tsaki ya zauna gefen gado yana duba sak'on. Wani irin mummunan fad'uwa gabansa ya yi ganin abunda sakon ya kunsa kaman haka. ' 𝘴𝘶𝘳𝘱𝘳𝘪𝘴𝘦, 𝘴𝘶𝘳𝘱𝘳𝘪𝘴𝘦 𝘺𝘰𝘶 𝘫𝘦𝘳𝘬. 𝘯𝘢𝘴𝘢𝘯 𝘣𝘢𝘻𝘢 𝘬𝘢 𝘥𝘶𝘣𝘢 𝘴𝘢𝘬'𝘰𝘯 𝘣𝘢 𝘴𝘩𝘪 𝘺𝘢𝘴𝘢 𝘯𝘢 𝘴𝘢𝘬𝘦 𝘵𝘶𝘳𝘢 𝘮𝘢𝘬𝘢 𝘸𝘢𝘯𝘪. 𝘬𝘢 𝘬𝘪𝘳𝘢𝘯𝘪 𝘯𝘢 𝘣𝘢𝘬𝘢 𝘮𝘪𝘯𝘵𝘪 𝘣𝘪𝘺𝘶 𝘪𝘯 𝘣𝘢 𝘩𝘢𝘬𝘢 𝘣𝘢 𝘯𝘢𝘯 𝘥𝘢 𝘢𝘸𝘢 𝘥'𝘢𝘺𝘢 𝘪𝘯𝘴𝘩𝘢𝘈𝘭𝘭𝘢𝘩𝘶 𝘻𝘢𝘬𝘢 𝘨𝘢𝘯𝘯𝘪 𝘬'𝘰𝘧𝘢𝘳 𝘨𝘪𝘥𝘢𝘯 𝘬𝘶, 𝘢𝘯𝘥 𝘣𝘦𝘭𝘪𝘦𝘷𝘦 𝘮𝘦 𝘪𝘥𝘢𝘯 𝘩𝘢𝘳 𝘬𝘢 𝘣𝘢𝘳𝘪 𝘯𝘢𝘻𝘰 𝘪𝘯𝘥𝘢 𝘬𝘢 𝘬𝘦 𝘴𝘢𝘪 𝘬𝘢𝘺𝘪 𝘥𝘢𝘯𝘢 𝘴𝘢𝘯𝘪𝘯 𝘴𝘢𝘯𝘪 𝘯𝘢 𝘢 𝘳𝘢𝘺𝘶𝘸𝘢𝘳 𝘬𝘢' Wata irin zufa ce ta karyo masa jiki na rawa ya dannawa number kira. Bugu d'aya ta d'aga da wani irin mugun murmushi tace “kazo ka sami a room 112 ,hotel xx” A hanzarce ya ya fito har yana tuntube daidai Asad daya shiga wanka ya fito ya hango Far'aan d'in na shirin ficewa ya bishi da sauri yana kira. Da azama Far'aan ya juyo ya kalli Asad dake tsaye da tawul “yanzu zan dawo ba nisa zanyi ba, sako zan k'arbo yanzu” A tuhume Asad ya “wane irin sak'o kuma yanzu asubar fari?” “Na gaya maka yanzu zan dawo wlh, inma tunanin wajen wata zanje ba nan zanje ba. Sak'o ne mai muhimmanci zan karb'o” Bai jira Asad d'in ya sake cewa wani abu ba ya juya da sauri ya fice Asad ya bishi da kallo. Kaman yanda tayi masa kwatance kai tsaye hotel d'in ya nufa. Babu b'ata lokaci aka yi masa iso zuwa d'akin data bashi don tuni ta sanar da zuwan sa. Bak'in koya tsaya yaja wani irin dogon numfashi ya fesar ta cikin mask d'in dake fuskarsa. Sai yanzu yake jin shakka da tsoron zuwansa saboda gudun abunda zaije ya dawo. Da kyar ya tattaro nutsuwar sannan ya buga k'ofar. Kaman jira take don bugu d'aya ta buɗe tana murmushi sanye da wata fitinanniyar riga da wando. Saurin kauda kai Far'aan ya yi daga kallonta k'irjinsa ya d'an harba saboda ganin d'an cikin nata daya d'an tasa kad'an kaman mai tumbi. Da gaske dai cikin ne da ita? Amma taya tun yaushe take da ciki?. Murmushin mugunta Javaria tayi ta sake wangale k'ofar tace “shigo mana, ko kana jin tsoro ne?” Wani irin mugun kallo Far'aan ya mata kafin ya ratsa ya shigo cikin d'akin ta maida k'ofar ta rufe tana wani irin murmushi. Juyowa ya to a zafafe yace “gani, menene ki ke so dani? Why are you doing this?” Bata bashi amsa ba ta wuce shi wajen center tables data d'ura d'an faranti da jug a kai. Lemo ta tsiyaya ma sanyi ta juyi wajen Far'aan ta mik'a masa tana murmushi tace “ka fara sanyaya mak'ogaron ka tukun, ance bak'on ka Annabin ka” Kallon rainin hankali ya mata rai a b'ace yace “ba abunda ya kawo ni ba kenan. Ki gayamin abunda yasa ki ka kawo ni nan ina da abunyi ” D'an murmushi dake fuskarta ne ya b'ace ta rikid'e da wani irin mugun kallo “ahh ,na manta yau ne zaka sake angwancewa ko a karo na biyu. Kana tunanin zan barka kayi aure ne cikin salama. Shi kuma wannan ya ka ke so nayi dashi” K'arasa maganan tayi tana nuna cikin ta tare da zuba masa wani mugun kallo da yana kisa da Far'aan ya shek'a lahari yafi a k'irga. Muguwar harara Far'aan ya watsa mata yana cewa “k'arya ki ke Aria. Ni nasan wannan ba cikina bane. Wata nawa da rabuwar mu tuntuni cikin bai nuna ba sai yanzu saboda kin rainamin hankali ko?” Y'ar dariya tayi tana tafa hannu “wow, ashe bayan corrupt mind naka brain d'inka

Chapter 7 of 15