Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na aiki. Ciki naka ne ko ba naka ba dole ka k'arbe shi inba haka ba zakai regretting abunda zanyi next.” Wata wawuyar ajiyar zuciya Far'aan ya sauke ya watsa mata wani irin kallo kafin ya juya kawai zai fice. Idan ya cigaba da tsayuwa da ita to tabbas zai iya shek'ata. “Far'aan ” ta kirashi amma bai juyo ba ya cigaba da tafiya. Yana kai hannu jikin k'ofar sai wushh abu ya wuce gefen kunne sa tare da wata k'ara mai kashe dodon kunne. Mummunan fad'uwa gaban Far'aan ya yi ya zubawa hudar da abun ya ratsa ya fice hayak'i na fita daga gefen sa . Da wani irin sauri ya juyo inda take tsaye rik'e da y'ar k'aramar pistol data harba yanzu saitin kansa. Ido waje yake kallon Aria data saitashi da bindigar tana murmushi tace “ka d'auka wasa nake ko? Kana tunanin nayi miss ne? Wannan abun da kaga gani hannuna tun bayan rabuwar mu nake training d'inta saboda rana irin wannan. In har kaga ka bar d'akin nan to sai in ka amince da buk'ata ta ka fasa auren da zakayi a maida namu, in ba haka ba yau ko ni ko kai cikin d'akin nan” Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Yarinyar nan kuwa tana da hankali? Hannu ya d'an daga k'irjinsa na harbawa kaman zuciyar zata fito waje. Wani irin matsanancin tsoro ne ya riske Far'aan da bai tab'a jinsa ba. Murya shi na d'an rawa yace “kinga Javaria wannan ba abun wasa bane. Ki ajiye bindigar nan muyi mugana ta nutsuwa ” Y'ar dariya tayi tana cewa “ni zaka yaudara da kalamai Far'aan ? Kar ka manta kaf y'an matan ka babu wacce tasan ka sama dani. Nasan abunda ya fito daga zuciyar ka da kuma wanda ya fito daga kan harshen ka.” K'ok'arin sake harba masa bindigar take Far'aan ya wani yi tsalle da zafin nama ya rik'eta suka hau kokawa kowa yana son kwace bindigar. Cikin rashin sa'a wajen kokawar da yake hannunta yana cikin wajen matsa abun ta harbi kanta gefen cikinta. A guje Far'aan ya saketa suka zube a tare a k'asa bata ko numfashi. Cikin tsananin rudu da firgici yaja baya yana kiran sunanta, amma shiru ka ke ji inda take kwance tuni ya mamale da jini. A guje Far'aan ya fito daga d'akin tsabar tashin hankali baisan inda ya nufaba saida ganin kansa kawai ya yi airport. Jiki na rawa ya fito ya shiga yana neman ticket zuciyar sa nata gaya masa 'Kayi kisan kai Far'aan, kayi kisan kai' Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Wannan wace irin musifa ce da bak'ar rana a rayuwar sa?. Yana gama settings d'in ticket din ya kashe wayar sa. Ko cikin airport's d'in a d'ad'are yake gani yake kaman kowa yasan abunda ya yi yana neman hanyar tsira. Allah ya taimakeshi ma daya je hotel d'in gari bai gama wayewa ba gashi yana sanye da mask da kuma bak'ar hoodie da bak'in wando. Cikin Hoodie d'in akwai farar riga a ciki don haka ya cireta ya wurgar. Yana cikin Airport d'in ya kira babban amininsa ya sanar masa kaf abunda ya faru. Shima hankalin sa ba k'aramin tashi ya yi dajin wanna batu ya rankayo Airport d'in wajen FAR'AAN. shi ya sake bashi shawara ya tafi inda zai kwana biyu ba'a jisa ba ko waya kar ya kira sai komai ya lafa . Shiya koma da motar gida. Gabda jirginsa zai tashi ya kunna wayan yana son kiran Asad don yasan yana can cikin tashin hankali. Yana kunnawa kiran Asad d'in na shigowa. Murmushi Far'aan ya yi wanda aka ce yafi kuka ciwo wasu hawaye suka cika masa ido. Koya Asad zaiyi idan yaji kaddarar data sameshi?. Bayan ya kashe wayan hawaye suka wanke masa fuska. A hankali ya furta 'I'm sorry Asad. Ina nan zan dawo. AJWA my cutie I'm sorry da abunda nayi miki, nayi alkwari ina nan zan dawo na aure ki' Da wannan ya shige jirgi saboda kiransu da aka fara. ──────────────────────── AFTER THE WEDDING. Yanda jikin Asad ke rawa saida ya bawa Su'ad d'an tsoro ya kama k'afad'un sa ya saka shi cikin mota. Zagayawa shima ya yi ya shiga ya yi saurin d'aukan ruwan gora ya bawa Asad d'in dan ya jika makoshi. Da kyar Asad ya iya d'aga ruwan ya kai bak'in sai yake ji shi kansa ruwan d'aci yake masa. Wannan wane irin mafarki ne? Taya za'ayi ace an d'aura masa aure haka nan kawai baida ra'ayi. Ita kanta yarinya babu wani abu daya tab'a had'asu bare aje ga zancen soyayya? K'afad'ar sa Su'ad ya d'an dafa yace “relax mana, duk wannan birkicewar ta menene? Aure ne fa aka d'aura kawai Asad . Kar kaga laifin Dad, Far'aan is the one to blame shi ya yi wasa da hankalin mutane da ita kanta yarinya da iyayen ta. Wannan abun da Dad ya yi, ya yi shi ne don cetar mutuncin ku dana ita yarinyar da kuma kareku daga shiga zargi da alkunya wajen al'umma. Ka duba tarin mutanen da aka tara saboda wannan rana mai muhimmanci. Dama can Allah ya riga da ya rubuta faruwar hakan kuma yana daga cikin kaddarar ka. Ka kwantar da hankalin ka for now musan inda Far'aan ya tafi da kuma sanin abunyi.” Sauke ruwan ya yi daya shanye tas amma sam ya kasa isarsa. Ji yake gaba d'aya mak'ogaron sa ya bushe kamas. Komawa ya yi a hankali ya kwanta jikin kujerar ya maida idansa ya lumshe. Gaba d'aya ji yake duniyar tayi masa zafi. Ina zaisa kansa? Dame zaije ne ,guduwar Far'aan ko auren dole da akayi masa tafar d'aya? To ita Ajwa ma zata amince ta zaune dashi yanda ta tsane su haka?. Buɗe ido ya yi a hankali saboda hayaniyar dake d'an shigowa ta mota. Kallon window ya yi ya hango su Baffa da Dad bakinsu ya kasa rufuwa sai yiwa juna sambar ka suke kaman yanda ko wane iyaye suke idan suka auran da d'a ko y'a. Gefe ya hango Babaah dake murmushi da kyar. Kallo d'aya zakayi masa kasan yana yin murmushin ne don dole. Ko meke damunsa Allah masani. ──────────────────────── To b'angaren Ajwa lokacin dasu Baffa suka shigo gidan duk suna zaune falo kowa yaci ado na kece raini sai shewa da wasa da dariya ake, kowa ka gani yana cikin nishadi banda Ajwa da take jin kaman tayi tsuntsawa ta bar falon ga k'irjinta da taje jin yanda yake bugu kace zata samu heart attack. Su Baffa na shigowa saida zuciyarta ya kusa tsayawa ta zuba musu ido kaman yanda kowa ya d'ago yana kallon su bayan sun zauna an baje musu abinci kala-kala irin girkin larabawa. Saida suka fara cin abinci tukun sukayi hamdala sannan Baffa ya fito da rafar kudi ya kalli Ajwa da ko kyefta ido batayi ta zama kaman wata mutum mutumi. Babaah dake gefe ya share wata y'ar zufa data karyo masa yana kallon kud'in shima Allah kad'ai yasan menene cikin ransa. Da kataccen murmushi Baffa yace “to alhamdulillah kaman yanda ko wane uba damu kanmu ke farin ciki ganin wannan rana gashi Allah ya nuna mana cikin yardar sa. Ga sadakin naki Ya Bint. An d'aura auren ki da angon ki ASAD alhamdulillah muna godewa Allah ,ya baku zaman lafiya ya kuna sanya alheri da albarka cikin rayuwar auren ku.” Duk falon suka amsa da Amin banda Suliem data d'aga cup d'in lemo tana k'urba babu shiri tayi wani irin kwarewa ta hau zuba wani uban tari kaman zata shid'e. Tsananin mamaki itama Mom ta kasa motsi daga inda take sai Babaah data kalla suka had'a ido ya yi saurin kauda kai. Tun bayan an d'aura Dad yaja shi gefe ya yi masa bayanin abunda ya faru da kuma dalilin da yasa ya yanke hukuncin haka ba tare da ya yi sharawa ba. Nonna dake kusa da Suliem ta hau buga mata baya tana ta mata sannu dasu Ammi dama sauran mutene dake falon. Ajwa fa tunda ya furta sunan Asad tayi suman zaune babu wanda ya lura saida Aunty Raihana ta k'arbo kud'in gurin Baffa ta kawo gaban Ajwa ta kama hannun ta zata bata, sai taga hannun ya tafi yaraf ya kwanta. A d'ure ta kama Ajwa tana kiranta tab'atan da tayi ta tawo luu gaba d'aya jikinta ta zube. Gaba d'aya falon ya cika da sallallami kowa ya rikice duk sukayi kanta. To Ajwa dai bata farfado ba sai wajen biyu na dare. A hankali ta buɗe idonta cikin duhun d'akin. Sake mai idon tayi ta lumshe ta sake bud'ewa tana d'an gurwurgasu gefe da gefe. Kanta taji ya d'an Sara tayi saurin kawo hannu ta dafe shi tana d'an wash. Nauyin dataji hannunta na hagu ya tabbatar mata da wani k'arin ruwan aka mata. Maganan Baffa ya dawo kunnenta 'an d'aura auren ki da Asad ' iya nan kawai yake ta mata amsa kuwwa. Da bala'in sauri ta miƙe zaune ta manta da wani ciwo. Kai anya kuwa taji daidai? To ko dai Baffa baisan sunan Far'aan bane ya kirashi da Asad. Ai da auren shi gwanda Far'aan d'in tunda shi taga alamun zai fishi sauk'in kai kuma ita zata gasa masa aya a hannu yanda taga dama, amma Asad sai dai tace ita dashi babu wanda zai ragawa wani don tabbas tasan duk macen daya aura kashinta ya bushe. Yunk'urin sakkowa take daga kan gadon haske ya dalle d'akin. Nonna ce tsaye wajen makunin fitila sai Aunty Raihana dake kwance kasan shimfiɗa da akayi mata tana k'ok'arin tashi zaune. Da sauri Nonna ta matso da d'an sandan ta “Bint kin tashi?, ya jikin naki? Akwai inda yake miki ciwo yanzu?” Kai Ajwa ta girgiza sai taji duk tausayin su ya rufeta saboda yanda duk suka damu. A hankali tace “Nonna dawa naji Baffa yace an d'auramin aure dazu?” D'an kallonta Nonna tayi tace “ dawa kuwa inba shi yaron da yazo neman auren ki ba. ASAD ne sunan nasa ko Raihana?” “eh shi ne Nonna.” “to kuma tambayan me ki ke bayan ke ki kawo shi kuma kina tambaya? Idan kinji d'an kwari tashi maza ki watsa ruwa bari muje mu d'umama miki wani abu kisa a baki sai kiyi sallah ko?” Kai kawai ta iya d'agawa tana kallon su har suka fice. A hanzarce ta cisge robar ruwan dake hannun ta ta fisgo wayarta dake kan side drawer ta dannawa Asad kira jikin ta na wani irin rawa ko tunanin cewa dare ya yi batayi ba. Abun mamaki bugu biyu taji ya d'aga da wata irin kasalalliyar murya kaman wanda ya shekara yana ciwo. Saida k'irjinta ya harba domin duk wata mace mai lafiya idan taji yanda muryar sa ta ratso wayar sai ta shiga cikin wani yanayi. Murya da tsananin masifa tayi magana a mugun hankali kaman mai rad'a “me ku ke tunanin kun mayar damu ne kaida d'an uwanka? Wane irin mutane ne ku marasa adalci dasan kan ku haka da yawa?. Kun d'auka mu abun wasa ne da zakuna juyamu yanda ku ka ga dama? To na rantse da Allah you will regret marrying me. Sai na jefa rayuwar ku cikin garari da sai kaji ka tsani mata a duniya kaman yanda na tsane ka kaida d'an uwan....” “enough .” Asad ya wani katse ta da wani irin cold voice da bata san sanda ta shanye abunda take cewa ba. Shiru tayi tana zuba huci k'irjinta na dukan uku-uku. Murya a kausashe ya cigaba da cewa “kar ki yi tunanin da amincewata koda yarda ta aka d'auramin aure dake. I hate it kaman yanda ki ka tsane shi if not more ma. So listen to me. Bazan lamunci raini ba daga yarinya k'arama kaman ki. You're nothing special and will never be. Ki kiyaye harshen ki wajen yi mun magana I'm your husband afterall and i promise you duk sanda ki ka k'aramin wani rashin hankali akwai consequence da heavy punishment. I dare you ki cigaba. .” Can k'asa yana k'ok'arin kashewa taji yace 'laifin kane Far'aan 'sai kit ya kashe wayar. Tsananin shock da mamaki yasa ta kasa cire wayar a kunne har ya kashe ta daskare a zaune da ido a waje. Tun yanzu yana da power da yake gaya mata magana har haka ta kasa bashi amsa? To gaskiya da sake tab. To yama akayi ta kasa mayar masa da martani?. Ranta na wani irin tafarfasa ta ciro wayar zata sake kiran shi saiga su Nonna sun dawo d'auke da kulan abinci harda Mom. Sata sukayi a gaba cike da kulawa taci abinci kafin suka kamata suka kaita banɗaki. Koda ta shiga banɗakin tsayawa tayi gaban mirro ta zubawa kanta ido tana kallon kanta idonta ya yi ja tsabar b'acin rai. Har ita yake cewa she's nothing special?. To zata nuna masa she's a very special mutum kuma tayi crushing nashi. Babban mistake nashi ,shi ne aurenta da ya yi. Da wannan kudurin tayi wanka ta d'auro alwala ta fito. K'asa -k'asa ta samesu suna magana tana fitowa sukayi shiru Mom ta miƙe ta kamara da sauri ta taimaka mata suka k'araso d'akin. Doguwar riga suka bata tasa mara nauyi da hijabi sannan ta kalli gabas don gabatar da sallolin da ake binta. ──────────────────────── Yana kashe wayar ya yi jifa da ita yana fesar da wani huci mai zafi. Baisan me yasa ba wannan tsiwar ta ta sosai yake affecting d'in sa. Hannu yakai cikin gashin sa ya yamutsa tare da lumshe ido kafin ya janye hannun a hankali ya shafa k'irjinsa dake waje wanda rigar dake jikinsa mai mad'auri bai rufe ba. Gaba daya marar shi ta wani masifar kullewa har yana jin bazai iya zama ba. Wani numfashin ya sake saukewa da k'arf kafin ya yunk'ura da kyar ya buɗe drawer nashi ya kwashi maganin sa ya watsa a baki duk da cewa maganin yanzu cikin kashi d'ari kashi d'aya ke masa aiki. Aikuwa shan maganin nashi ya tashi a banza don ciwon sai k'ara tsanani yake yana ji kaman marar shi zatayi bindiga tsabar yanda ta kulle. Maganan Su'ad ya tuna daya ce masa ya daure ya dinga Azumi ko litinin da alhamis ne zai samu sauk'i inshaAllahu ko bai warke lokaci d'aya ba zai rage wani abu da samun sarari har zuwa lokacin da Allah zai bashi lafiya. Sam da Abun nashi bai kai haka ba yanzu ne dai abun ya sake tsanani. Ganin babu sarki sai Allah haka ya miƙe a daddafe ya fad'a toilet. Wanka ya sake yi ya d'auro alwala ya fito. Saida ya saka doguwar riga fara mai hula ya feshe kansa da turare sannan ya kalli gabas ya tada nafila. ──────────────────────── To washegari Ajwa haka ta tashi wani sukuku da ita babu kuzari. Allah kad'ai yasan abunda take kissimawa cikin ranta. Koda aka hadu wajen cin abinci kowa yana ta raha da wasa da dariya idan ka cire Suliem da Ajwa. Ta k'ara zama wata silent ga idonta ta da Ajwa ta lura kaman wacce tasha kuka sai sunkuyar da kai take k'asa. Gaba d'aya Ajwa tana lura da yanda Suliem d'in tayi ta kuma shiga damuwa tana tambayar kanta ko menene kuma yake damunta? Ko Babaah ya sake yin wani abu ne bayan idon su?. Speaking of which ina ma Babaah d'in? Kowa ya hallara a wajen banda Babaah. Kaman sun shiga cikin zuciyarta taji Baffa da Abbi na maganan fitar Babaah tun asuba saboda kiransa da akayi wajen aiki. Mom ta kalla da suke ta hira da Nonna itama ta juyo suka had'a ido kafin ta d'auke kai. Hmm ita tasan babu wani aiki da aka kirashi ya tafi yawonsa ne dai kawai. Y'ar kwafa tayi tana tunanin abunda zatayi ta tona masa asiri kafin lokaci ya k'ure. Suna gama cin abinci su Ammi suka sata gaba suka kulle a d'aki. Sosai suka dirjeta da kayansu na gyaran jiki yau Ajwa ido kawai ta zuba musu babu musu dan ita kad'ai tasan abunda take shiryawa cikin ranta. Da yamma gida ya k'ara d'aukan wanka an k'awata tsakar gidan da decoration da kujeru. Yar walima ce za suyi da Baffa ya d'auki nauyi ta. Sun shirya Ajwa cikin wani gown mai tsananin kyau ash, gaba d'ayan sa kaman irin less d'in nan. Simple makeup akayi mata hakan kuma ya sake fito da aininhin kyanta. Kaf suka hallara nan tsakar gida ana yan rawa-rawe sai zuba mata kud'i suke kaman basajin su. Da kyar take iya murmushi ta gefen ido tana kallon Suliem can ta samu guru d'aya ta ware taki shiga ma cikin y'an matan dake ta cashewa abun su. To menene yake damun Suliem ne?. Kyest aka d'auke da wata camera mai shegen haske saida ta d'an rufe ido. Hoton kuwa ba k'aramin kyau ya yi ba ta juyo a hankali don ganin wanda ya d'auka te. Ga mamakin ta sai taga Su'ad yasha manyan kaya sai zuba mata murmushi yake. Hannu kawai ya d'aga mata ya cigaba da d'aukan hoton da direct saboda connection da ya yi da wayar sa, direct mailbox din Asad yake wucewa. Yana jin yanda wayan nasa keta harbawa da karan sak'o amma yaki d'auka bare ya buɗe. Ido kawai ya zuba mata haka nan kawai zuciyar sa na racing. Tunda su Baffa suka kira jiya suka sanar dasu walimar da asuba Su'ad ya saka shi a gaba suka sake d'auko hanya suka dawo. Koda suka zo babu juyin da Su'ad baiyi ba amma yace shi bazai zoba. Da jarumta ya d'auko wayar bud'e ta sak'on. Gaba d'aya numfashin sa ya wani tsaya ya zubawa hutunan ido. 'She's is so beautiful ko?' Daga kasan hoton aka rubuta wanda take d'an murmushi Ammi na mata liki. Baisan sanda ya wani jijjiga kai ba sai kuma da sauri ya ce 'No' yana d'an gyara murya daga karshe ya ajiye wayar da sauri ya canza kaya zuwa k'anana ya fito cikin sauri ya nufi wajen motsa jiki da yaji akwai anan hotel d'in da suka sauka. Har yanzu ya kasa gasgata wai shine yake da aure kuma gobe zai wuce da Ajwa gidan sa daya gina nan Abuja. Dad har yanzu baisan yana da gida ba saboda bai taba samun chance sunyi wanna maganan bare. Kuma dai rashin kusancin su yasa bai tab'a nuna masa yana gini nan Abuja ba har ya gama. ──────────────────────── To Babaah dai duk wannan hidimar da ake bai dawo ba yana can wani kebantaccen gidan daya gina wata sabuwar unguwa da babu mutane sosai. Gida ne na kece raini don ko daga waje aka d'auko shi aka ajiye sai haka. Gidan gaba da bayansa uban security ne da wasu shegun karnuka irin na k'asar waje wanda aka yiwa training d'in bada tsaro. Duk yanda gidan ya kai ga had'uwa ana shakkar kusantar k'ofar gidan bare ace za'a haura ko yin sata. Yana tsaye jikin wani katon windo da yake nan kaman irin mudubin nan na glass. Daga shi sai dan kanfai hannun sa rik'e da glass yana k'urban abunda ke ciki. Hannu aka zuro k'irjinsa kafin aka rungume shi ta baya. Wani kyakkyawan bature ne da bawai wuce 25yrs ya sumbace shi a kunshi. Da harshen su na nasara yace “menene yake damun ka Babe? Naga hankalin sam baya tare dani. Ina gabanka amma baka ganina.” Wani iri sauke numfashi Babaah ya yi saboda k'irjinsa da yake shafawa da wani iri salo. Janyo guy d'in ya yi ya dawo gabansa ya zuba masa ido yana k'are masa kallo. A da Michael shine kad'ai namijin da yake gani yana jin babu kamar sa. Amma tun ranan daya ga Asad da Far'aan ya shiga cikin wani mawuyacin hali musamman saboda Asad. Tunanin sa da mafarkinsa kullum yana kan Asad. Duk yaransa da yake kasancewa dasu yana hasasho Asad ne. Yana so yaji zumar sa wannan faffad'an k'irjin yana son ya kwanta a kansa. Kallo d'aya yawa Asad yasan cewa ya wuce makorar da yake tunani. Sai gashi lokaci d'aya burinsa na neman wargajewa. Taya ma zai bari wannan fitsararriyar yarinya ta mallaki abunda ya kwallafa rai a kansa? Abune da bazai tab'a yiwu ba wai ance malam yaci shirwa. “yes Michael ina ciki damuwa. Ka tuna wannan yaron dana baka labarin sa?.” Wani irin juya ido Michael ya yi da d'an kishi yace “yes na gane shi. Badai yaron da kace ka kasa ganin mutum mai kyau kaman sa ba. What about him?.” Da wani irin d'acin rai Babaah yace “he is married .......to my daughter ” Saida yaja fasali sannan ya k'arasa kaman wanda aka zubawa kashi a baki. Ido Michael ya zare sai kuma ya kwashe da dariya yana kallon yanda Babaah ke huci cike da kishi. Saida ya yi mai isar sa harda hawaye yace “taya akayi to hakan ta faru? Na d'auka zaka ja hankalin sane har ka samu kansa. Ya akayi hakan ta kasance yanda ka ke mutum mai kafiya da naci musamman kan abunda ka kwalla masa rai. What are you going to do?.” Wani irin murmushin Babaah ya yi ya d'aga cup d'in dake hannun sa ya shanye abunda yake ciki yana kallon waje yace “just wait and see. Sai na same shi kota halin k'ak'a. To he'll with the Daughter. Babu wanda ya isa ya rabani da shi. I love him.” Haushi ya d'an kama Michael saboda kishi Ya wani ture Babaah a d'an fusace zai fita ya rik'oshi yana murmushi. To fa Ikon Allah. Tab subhanalla, Allah yasa mufi k'arfin zuk'atanmu. °•★|•°∵ TAURA BIYU ∵°•|☆•° . * ®𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵𝓸𝓿𝓮 08140754777 /No edit! 【Pg19&20】 Babaah bai shigo gidan ba sai wajen magriba har zuwa lokacin suna ta tashewa a tsakar gida. Da fara'a sosai shima ya shiga sawun so Baffa da bakin su yak'i rufawa aka cigaba da damawa dashi. Jin an fara kiraye-kirayen sallah Baffa yace a akashe kowa yaje ya yi sallah tukun. Babu musu masu dj suka kashe Dj suma suka bi sawun samarin gidan dake tare dasu Baffa aka wuce masallaci gaba d'aya . To bayan an idar da sallah saida aka ci aka sha sannan suka sake d'urawa daga inda aka tsaya. Wannan karan Su'ad shi ya yi mata barin kud'i kaman baya jin ciwon su bai kuma fasa d'aukan hoton ta yana turawa Asad ba. Basu suka tashi ba sai da akayi isha kowa ya shiga gida ana ta maida zance. Kai tsaye Ajwa d'akin ta ta sulale ,tana shiga kuwa ta cire kayan jikinta tana wurgi dasu tana jin kaman cikin wuta aka sakata. Banɗaki ta fad'a da sauri ta sakarwa kanta shower. Ta jima ruwan na dukanta kafin ta kashe ta fito d'aure da d'an tawul k'arami daya tsaya mata iya kugu sai k'arami da take goge gashin kanta daya bi jikinta luf ya kwanta. D'an zarana tayi ganin Nonna da Ammi sai Aunty Raihana zaune kan gado da akwati a gabansu ga kayanta baje kan gadon suna shiryawa cikin akwati. Da mamaki ta k'arasa shigowa tana kallonsu bakinta na d'an motsi. Ammi ce ta kalle ta da sauri ta d'auko cup data d'ura kan drawer tace “yauwa kin fito?, maza karb'i wannan ki shanye.” Bata musa ba ta k'arba tana k'ok'arin zama kan dressing mirror. Kasa jurewa tayi bayan ta shanye maganin ta kalli Nonna “ina za'a kaimun kayan Nonna?.” Ba tare da Nonna ta kalleta ba tace “ina kuwa daya wuce gidan mijin ki? Gobe zaku wuce da mijin naki ai tunda yazo basai mun kai ki ba. Daga baya mazo muga gidan kafin mu tafi” Yanda k'irjin Ajwa ya buga da mugun k'arfi saida Ammi dake tsaye gefenta ta juyi ta kalleta amma bata ce komai ba. Wata irin zufa ce ta karyowa Ajwa data bi ruwan dake binta. Innalillahi da gaske dai barin Mom da Suliem zatayi?bata sake cewa komai ba sai ido tada dinga binsu dashi har suka gama shiryan kayan suka jere su gefe. Babu wanda yace mata komai suka saka k'afa suka fice. Jikinta babu wani kuzari ta miƙe a sanyaye ta rufe k'ofar da mukulli ta koma bakin gadon ta zauna ta

Chapter 8 of 15