Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta d'an yunk'ura tana rike ciki. Da sauri ya zuba cikin plate ya matso sosai kusa da ita yana k'ok'arin debo abincin cikin fork. Tana kallo ya kawo abincin ta d'auke kai bazata ci ba tsabar taurin kai. Cak ya tsaya da abincin yana kallonta ga yunwar tana ji amma bakin naci da tauri kai ya hana ta k'arba. Ganin zata b'ata nasa lokaci ya maida abincin ya ajiye yana cewa “fine, kar kici cikin ki..” D'auko kit nashi ya yi ya fito da wasu magunguna da allura ya ajiye kan gadon. Da sauri ta sake kallon sa ganin yana hada ruwan Allura a sirijin. Wa zaiyiwa Allura?tab lallai kuwa za'a yita. Yana gama had'a ruwan kawai taga ya yo kanta gadan-gadan yana k'ok'arin janye bargon data rufe jiki dashi. Bata san sanda tayi wani irin tsalle ba ta dire can gefe ta manta da ciwon da take ji. Tsayawa sukayi suna kallon juna shi yanda tayi tsallen nema yaso bashi dariya. Dan zare manyan idansa ya yi kanta yana sake tamke fuska yace “girl ,kina fa wuce gona da iri. Kina batamin kyakkyawan lokacina da bai kamata ko na sakan ki samu ba. Don't upset me.” Ko numfashi bata bari ya shak'a ba ta mayar masa muryar ta na rawa “ waya saka?. Lokacin ka d'in banza da wofi. Ka tafi mana ai bance ka tsaya ka kula dani ba zan iya kulawa da kaina” Wani irin kallon wulak'anci ya mata yace “ inke baki san ma'anan aure ba to ni na sani. Ko ki matso na miki allura ko kuma kici abinci kisha magani. Saboda dole ayi d'aya cikin biyun nan don ni ba jahili bane.” Yana nufin ita ce jahili kenan? Hawaye suka taru cikin idan Ajwa tayi maza ta shanye. A zafafe ta juya zata shige banɗaki tana kai hannu jikin k'ofar taji anyi sama da ita kaman yar tsana. Ihu tasa ta hau shure-shure tana kai masa duka yana kaucewa. A zafafe ya jefata kan gadon ya wani hauro da zafin rai yana k'ok'arin kama cinyarta ta saki k'ara da k'arf tana cewa “ zanci abincin, zanci abincin ” Wani irin kallo ya watsa mata da idanuwansa da suka sake rinewa . Murya ya d'an gyara ya saki k'afarta daya rik'e yana cewa “good. Next time ki sake min irin wannan zan nuna miki ni ba yaro bane kaman ki ” Sauka ya yi daga kan gadon ya d'auko abincin ya mik'a mata. Duk yanda take rik'e kukan dake cinta saida ta sake shi hawaye suka fara gudu kan fuskarta kaman an bud'e fanfo tsabar bak'in ciki. Anya kuwa zata iya cimma manufarta kan Asad?. Tana kuka ta k'arbi abinci tana ci . Tunda ta fara cin abincin bai waiwaye inda take ba sai waya daya ciro yana sake gwada number Far'aan ko zai samu. Duk irin dad'in abincin amma tsabar bak'in ciki ta kasa ci ga yunwa ta cinye ta tas. Loma hud'u kawai tayi ta ajiye abincin gefe. Jin ta ajiye abincin ya juyo ya kalleta fuska nan a cunkushe. Baki ya d'an tab'e ganin ba wani abun kirki taci ba. D'auko maganin ya yi ya bata bata musa ba ta k'arba ya mik'a mata ruwa ta kora dashi. Yana ganin ta shanye ya miƙe ya yi ficewar sa. Da idonta bishi yana fita kaman wacce aka sakewa baki ta saki k'ara ta hau jifa da fillowa dake kan gado tana kuka. Saida tayi mai isar ta koma ta kwanta duk wani d'an ragowar k'arfi jikinta ya k'are. Tana jin yanda har yanzu ake sharara ruwa kaman da baki kwarya ga masallatai sun fara kiran magriba. Haka dole ta sake jan k'afa ta koma banɗaki dan sake wani wankan. Bata jima ba ta fito tayi sallah. Yanzu ta d'an ji dad'in jikinta ba kaman daz'u ba. Cikinta dake ta kukan yunwa yasa dole ta d'auko abincin daya ajiye ta cinye kaman munafuka tana yi tana kallon k'ofa. Saida tayi sallah isha ta haye gado gadon ta kwanta saboda wani irin barci da take ji. Bayan ya koma d'aki sosai ya yi fad'a da zuciyar sa da halin daya shiga. Tsananin laushin fatanta duk da cewa bawai wani tab'a ta ya yi ba kuma da kaya ya tab'a, amma yanda yatsunsa suka nutse cikin cinyarta da sket d'in dake jikinta saida yasa zuciyar sa harbawa. Maganin sa ya d'auko daga cikin drawer ya watsa a biki ya taune amma still yana jin wannan feeling kaman zaiyi hauka. A hargitse ya fad'a toilet ya sakarwa kansa ruwan sanyi duk uban sanyi da ake a garin ga ruwa da ake tsugawa. Ya jima cikin shawar sannan ya fito d'aure da Alwala ya yi sallah. Yana idarwa ya d'ura da tilawa karatu saida akayi isha. Bayan ya idar zama ya yi yana tunanin yaje ya sake dubata ne ko ya kyale ta kawai? Dole zuciyarsa tayi galaba a kansa ya miƙe ya sake canza kaya daga farar jallabiya dake jikinsa zuwa na barci doguwar riga bak'a mai mad'auri da wando wadda ake d'aure rigar daga tsakiya duk k'irji a waje. Saida ya feshe jikinsa da wasu turarruka masu sanyin kamshi da suka game jikin sa koda yaushe ko yasa ko baisa ba. Dan sandal ne k'afarsa kaman silifas mai laushi ya fito rike da wayarsa da kuma mukulli koda zaije ta rufe. Ya yi mamaki da yaga k'ofar a bud'e bata rufe ba kamam daz'u. Murmushi ya yi na gefen baki ya tura k'ofar a hankali ya shiga. Ajwa da barcin ya fara nisa ta sake wani zabura idao cike da barci ta miƙe tana kallon Asad dake k'ok'arin maida k'ofar ya rufe. Kallo d'aya ta maa gabanta ya yanke ya fad'i. Ganinsa cikin wannan kayan sai taga ya sake wani girma musamman yanda take d'an hango k'irjinsa ta dan duhun fitilar data haske d'akin. Me kuma ya dawo yi? Kai tsaye gadon taga ya nufo ya zagaya d'aya barin ya ajiye wayarsa kan drawer sai taga yana k'ok'arin hawa gadon ya kwanta. Ai tuni ta wartsake ta wani tashi da bala'in gudu ta dire daga kan gadon taba cewa “menene haka kaye yi?” Baice komai ba saida ya haye gadon ya zaune ya jingina da gadon sannan ya d'ago ya wata wani shekakken kallo yace “nida gidana, d'akina ki ke tambaya ta me zanyi?” Taune harshe tayi dan ta rasa abunda zatace. Can tace “amma yanzu nan ai ba d'akin ka bane” “Inja wa?” Ya yi maganan d'a gaggiyar gira. Cije baki ta sake yi saboda ya fita gaskiya kuma bata da amsan da zata bashi. “Hmm. Abunda nayi tunani kenan baku da amsa. So on kinga dama ki kwanta in bakiga dama ba ki fita. Is not like I'm dying to touch you” Wani irin hade gira Ajwa tayi tsabar b'acin rai. Wai waye ne shi haka yake zuba mata rashin mutunci? “sai dai kuwa ka mutum. Keep your hopes high ni Ajwa nafi k'arfin ka” Y'ar dariya Asad ya yi can k'asan makoshinsa data fito so deep. Ido ya zuba mata ya hard'e hannu a k'irji. Yanayin kallon da take masa mai tattare da tsana, zafin rai da kuka ban haushi kaman zata cinye sa d'anye ya masifar burgeshi. Gata dai y'ar mitsitsiya da ita amma zafin ranta yafi k'arfi kanta. So little tiger sosai ya yi fitting d'in ta. D'an karkata kai ya yi gefe yana kallonta ta k'asan ido yace “kaman yanda ki ke ganin wannan auren dole a wajen ki haka yake a gurina. So stop thinking ko akwai wani abu bayan hakan. Babu abunda zaki samu a wajena. Far'aan yaki auren ki ni na aure ki,so think this as a favour na ceceki daga mufarcin duniya da zund'enta” A zafafe tace “gwanda Far'aan sau dubu a kan ka don ka fishi bak'in hali. Babu wanda ya saka da sai kace baka so ko ka sakeni tun a lokacin da aka d'aura” Dan d'aga kai ya yi kaman mai tunani sai kuma ya saki wani mugun murmushi yana kallonta yace “wannan ma tunani ne mai kyau, amma banga damar hakan ba wata kila saboda ina so nayi crushing naki ne” Ya k'arasa maganan da wani shegen smirk kan fuskarsa daya masifar k'ara masa kyau. Numfashi Ajwa taja tana ji idan ta cigaba da biye masa to tsab zata d'auko wuk'a ta daba masa. Juyawa tayi tana tunanin ina zata kwanta. Har tayi hanyar waje aka buga wata gigitacciyar tsawa da babu shiri taci birki tsak'iyar d'akin. Bawai tana da tsoro bane amma kasancewar ta nan inda babu kowa bata san kowa ba ita kad'ai dole akwai tsoro. Tunanin kwanciya take kan kujera don bata jurewa saboda takura take. Tafi so ta jita baja-baja kan gado tana juyawa yanda take so. Numfashi ta sauke a hankali ta sake shak'ar wani ta fesar kafin ta juya kan gadon. Har yanzu ita yake kallo da hannu harde kan k'irji da wannan shegen murmushin da take ji kaman taje ta take da k'afarta. So yake ya samu wick spot nata yana mata abunda yaga dama ta lura, to bazata bashi wannan damar ba daidai take dashi. Gadon tayi kai tsaye ta fara kwasar fillo tana jerawa tsak'iyar gadon saida ta raba shi tuh daga farko har k'arshe sannan ta rab'a can k'arshen gadon ta kwanta wanda idan tayi wani kwakwaran juyi tsab zata fad'a. Duk yana kallonta ta wani cure guri d'aya zanin gadon ma tak'i rufa dashi sai mayafinta ta saka ta rufe kanta. Shi sai yanzu ma ya tuna da kayan ta dake cikin mota bai d'auko ba. Murmushi kawai ya yi ya kanta ya yana Addu'a shima ya juya baya kaman yanda tayi. ──────────────────────── Washegari kusan daga shi har ita makara sukayi, shi kansa ya yi mamakin barci da ya yi. A hankali ya buɗe idansa bakin sa d'auke da salati. Yunk'urin miƙewa yake zaune amma yaji kaman wanda aka d'aure. Da d'an mamaki ya sunkuyu da kansa saitin k'irjisa da yake ji kaman an d'ura masu abu mai d'an nauyi. Suprise, suprise Ajwa ce nannad'e a jikinsa ta nannad'e shi kaman wata maciji. Baki ya d'an bud'e cike da mamaki yana kallonta ya mik'a kai yana kallon fillow data jera duk ta watsar dasu can gefe ta mirgino inda ta nannad'e shi. Lallai suprise kuwa lallai zaiso yaga yanda zatayi idan ta farka. Komawa ya yi ya kwantar da kansa kan fillow yana sauke ajiyar zuciya a hankali. Yanda ta nannad'e shi sosai ya jefashi cikin wani yanayi mararsa lokaci guda ta fara harbawa saboda yanda k'afarta ke kan marar tashi. Motsi ta sake yi tana kara jan k'afarta saman tashi yaja wani irin dogon numfashi kaman zai shid'e. Idan ya bari suka cigaba da kasancewa a haka zaiyi abunda bai shirya ba. Da sauri ya fara gyaran murya da d'an k'arfi yana d'an k'ok'arin tashi. Kaman a mafarki taji motsi kansa a firgice ta wani tashi fii kaman isaka tana zare ido. Ganinta kwance kan Asad ya masifar d'aga mata hankali ta saki wani ihu a gigice ta wuntsula can gefe tana rufe jiki da nunashi da yatsa amma bakin ya kasa furta komai. Maida idansa ya yi lumshe ya yana fesar da numfashi a hankali kafin ya yunk'ura ta miƙe zaune. Kallo d'aya ya mata ya mik'e da sauri ya fice daga d'akin ta bishi da kallo baki a hangame. Sai bayan ya fice ta sauke wata irin k'atuwar ajiyar zuciya tana kallon inda ta kwanta. Tabbas yanzu ma laifin tane don ita ta bar inda take ta matsa har can wajen sa. Cike da takaici da haushin kanta ta shige toilet tayi wanka ta d'auro alwala a gurguje tazo tayi sallah asuba. Tana idarwa ya shigo d'auke da akwatin ta ya yi wanka ya shirya cikin k'ananan kaya bak'ar riga da wando gashin kansa yana ta zubar da ruwa da alama bai dad'e da wanka ba. Bai kalleta ba ya ajiye akwatin ya fice abinsa. Numfashi ta sauke a hankali ta tashi da sauri ta laluba ta ciro wayarta ta kunna. Kaman kuwa jira ake saiga kiran Mom da Suliem. Da kuka ta d'aga wayar jin muryar su. Daga jiya zuwa yau ji take kaman ta shekara d'ari tayi bata jisu ba. Da kyar Mom ta lallashe ta yi shiru kafin ta hauyi mata nasiha mai ratsa jiki Nonna dasu Ammi duk suka suka k'arba suna sake mata nasiha. Sun jima kam wayar sannan sukayi sallama da mata alkwarin kafin su koma Saudiya zasuzo suga gida. Miƙewa tayi tana k'ok'arin cire mayafin jikin ta ta chanza kaya sai gashi ya dawo d'auke da wani tiren a hannu sa. Da harara ta bishi har ya ajiye kan drawer da magani daya bata jiya ya juya ya sake ficewa ta bishi da muguwar harara. Saurin zuwa tayi ta kulle k'ofar ta bar mukullin a jiki. Yanzu bata yiwa kanta ba ta zauna ta sharci abincin tana tananin inda ya samo shi . Tana gamawa ta kora da magani ta koma kan kujera ta zauna ta zuba uban tagumi. Yanzu ya zancen makarantar ta fa? Shikenan ya yi mata sanadi kenan? Haka taita sake -sake ita kad'ai har tayi barci nan kan kureja bata canza kayan ba. ──────────────────────── SINGAPORE. Yau kwana sa biyu kenan da saukan sa k'asar Singapore. Tunda ya sauka bashi da nutsuwa har yanzu ciyar sa da gangar jikinsa sun kasa daina tunanin Ajwa da abunda ya aikata mata. Shin ko dai bayan sha'awar ta da yake akwai so ne?. Tuninta sosai yake damunsa dan sam bai cika tunanin Javaria ba kaman yanda Ajwa ke cikin tunanin sa ko da yaushe. Bai sani ba Javaria ta mutune ko tana raye? Hankalin sa har yanzu ya kasa gasgata shine ya yi wanna harbin shi yasa tunda yazo yake ta baza ido kafafen labarai ko zai ji wani labari daya danganci kisan da yake tunanin ya yi amma shiru, babu wani labari ta ko wane lungu da sak'o. Yana sauka ya kira Faris amininsa ya sanar masa da saukan sa don haka shi kad'ai yasan inda yake ya kuma sake tabbatar masa ko daga nan Nigeria har yanzu baiji wani labari cewa anyi kisan kai a hotel d'in ba. Da wannan Far'aan ya d'an samu sauk'in damuwar da yake ciki ya d'an fara cigaba da harkokin sa. To amma duk macen dazai kasance da ita Ajwa yake hangowa tattare da ita. Yasha kwatanta kiran Asad amma yana shakka don baisan me zai gaya masa ba, kuma yana tsoron Asad d'in yasan abunda ya aikata. Yasan cewa indai ya kira Asad to tabbas Dad zaisan inda yake yanzu kuma bai shirya fuskantar su ba tukun sai komai ya lafa, amma Ajwa ta hanashi sakat. Anya kuwa zai iya jurewa rashinta bazai koma ba ayi wacce za'ayi ya auri Ajwa ya huta ko ya saukewa kansa wanna ishi da tak'i kasuwa?. To amma idan ya koma aka tuhumeshi da kisan kai fa duk da cewa ya yi ne cikin kare kai da kuma rashin sani? Me yasa Javaria ta shiga rayuwar sa ta wargaza masa ita cikin k'ank'anin lokaci?. Koma dai menene yana nan zai dawo ya mallaki Ajwa ko zuciyar sa zata huta. ──────────────────────── Tun bata saba da zaman kad'acin ba har ta saba. Yau kwanan ta biyu kenan gidan Asad har yanzu banda mugun kallo da harare-harare babu abunda yake had'ata dashi. Tun ranan daya kwanta d'akin bai sake shigowa ba sai in zai kawo mata abinci shima daya ajiye zai juya ya fice abunsa ko kallo bata ishe shi ba. Tana tsaye gaban mirro fitowar ta kenan daga wanka. Cikin kayanta ta d'auko wata riga da sket yan kanti marasa nauyi ta saka sai mayafi k'arami data d'ura kanta tayi rolling. Fuskar nan tayi wani fayau da ita amma ba k'aramin kyau tayi ba. Fitowa tayi don ta gaji da zaman d'aki a ranta tana cewa itama tana da iko da gidan bazata dinga kulle kanta ba kaman wacce ke cikin kurkuku. Tana shawo kwanan corridor d'in gabanta ya yanke ya fad'i ganin Asad zaube falon sanye da wani gajeren wando da singlet irin mai wawakeken hamta nan. K'aramar laptop ce gabansa daya d'ura kan kafarsa daya dura kan Centre table idansa sanye da farin glass gashi duk a yamutse. A hankali ya d'ago ya watsa mata manyan idanuwansa kafin ya d'auke ya mayar kan abunda yake. Kasa motsawa tayi kaman wacce aka d'aure sai taga kaman ya k'ara wani irin girma kodan kayan dake jikinsa ne? Ganin ya maida hankali kan laptop nashi ta tako a hankali ta haura matakala ta zauna can nesa dashi a d'an d'ad'are. Shiru ta zubawa TV dake aiki ido zuciyarta na harbawa. Ta kasan ido ta sake kallonsa taga sam ko kurar data debota bai kalla ba aikin sa kawai yake lokaci-lokaci yana d'an miƙewa ya shiga kitchen. Sosai tayi mamaki ashe shi yake girka abincin da yake kawo mata? Lallai kuwa wannan shine aka kira da mijin tace ga wacce tayi sa'ar samun sa matsayin miji. Tana kallo ya zubo a abincin ya dawo ya zauna yana ci ya cigaba da aikin sa hankali kwance. Yau baiga daman kai mata abincin ba kenan?. Y'ar kwafa tayi babu kunya ta tashi itama ta shige kitchen d'in ya bita da kallo bata sani ba. Saida ta debo abunda taga dama ta dawo ta zauna tana ci tana kallo. Y'ar dariya ya yi kawai ya girgiza kai cikin ransa yace rashin kunyar banza da wofi. Sallah ce kawai ke tashin Ajwa daga falon da zarar tayi kuma zata dawo ta zauna. Sai ya dawo masallaci ya ganta zaune ta hakimce falon fuska a murtuke. Tana zaune ya girka na rana dana dare haka kuma zata tashi taje ta debo babu kunya ta zauna ta tirki abunta yana kallonta. Idan ya fuskance ta wannan shine yak'in nata kenan? To su zuba daidai yake da ita. Washegari yana sane yak'i dafa abincin har ta fito nan falon ta same shi yana kallo da y'ar singlet da gajeren wando. D'an tsaki taja cikin ranta tana cewa shi kuma haka yake sam babu kunya ya yi ta zama tsirara a gida. Kullum yana yawo da gajeren wando a gida sai kace shi kad'ai ne a ciki. Kaman yasan tunanin me take ya wani sake gyara kwanciyar sa kan kujerar ya sake ware k'afa yana kallon TV. Saurin kauda kai tayi daga kallon sa k'irjinta ya wani iri mummunan harbawa . Kai gaskiya wanna shi a y'an iskan ma karshe ne kalli yanda ya wani turo mata kugunsa wai ta gani da kyau ko?. Can kasan ranta tace 'Dan iska kwai' Ashe a fili ta fad'a don wani irin juyowa ya yi ya watsa mata idansa da gira a d'age.Saurin wucewa tayi kitchen ita kanta bata san sanda ta fad'a ciki ba. Turus ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya to kuma menene na firgita ta tambayi kanta tana d'an tsaki. Kitchen d'in tabi da kallo taga yanda komai yake tsab gwanin sha'awa babu wani tarkace. Bata san yanda akayi ba sai ganin kanta tayi tana dube-duben kayan girki ta d'ura abinci. Tana gamawa ta shake plat da lemo ta fito ta zauna abunta tana ci bata yarda ta kalleshi ba saboda idansa da take ji sosai a kanta. Mamaki ya yi sosai ganin ta dafa abincin ya yi d'an murmushi ya mik'e ya shige kitchen d'in shima ya zubawa kansa. Suna gamawa da kansa taga ya kwashe kwanukan harda nata ya wuce kitchen ya wanke. Baki ta tab'e a fili tace ' Mijin tace kawai ' Duk yana jinta ya yi murmushi yana d'an girgiza kai. ──────────────────────── Sautin nishinsa ne kad'ai yake fita d'akin sai sunan Michael da yake ta jerawa kaman danshi aka rad'a. Wani irin gunji ya yi jikin sa na jijjaga ya saki abunda ke mararsa kan laptop d'in sa dake gaban sa yana video call da Michael. Shima nashi b'angaren yana ganin yanda Babaah ya yi shima ya rufa masa baya yana gunji da kiran Babaah. A hankali Mom dake tsaye jikin k'ofa ta maida k'ofar ta rufe jikin ta na wani irin matsanancin rawa kaman mazari tayi saurin toshe bakin ta saboda wani irin kuka dake k'ok'arin kwace mata mai gunji. Tun lokacin daya fara neman binta ta dubara ta fara zargin sa ,amma ance zato zunubi kuma akwai maza da yawa da suke sab'awa Allah wajen neman matansu ta dubura saboda hakan a gurin su yafi musu dad'i kan su nemi mace ta gabanta. Tayi tunanin Babaah yana cikin jerin sune musamman ma yanda ta fuskanci baya son ya'ya mata. Da kyar ta iya kai kanta d'akin ta yi kuka tayi kuka kaman me. Tayi istigfari da Addu'a Allah ya yafe mata ranan da Babaah yaci galaba a kanta babu kakkautawa. Tabbas zamanta da Babaah ya k'are domin shi d'in abun gudu ne da kyema. Ya cuceta ita da ya'yan ta. Barcin da Mom batayi ba kenan ranan haka ta kwana a sujjuda tana nemawa Babaah shiriya idan mai shiryuwa ne. Da safe kafin kowa ya tashi ta shiga d'akin Babaah ta same shi yana shiryawa zai fita aiki. Kallo d'aya ta masa taji wata irin tsananshi kaman tayi amai saboda kyenkyemi. Dan nesa dashi ta tsaya tana kallon sa yana saka hula gaban mudubi. Ta mudubin ya kalleta fuska babu wani walwala yace “kin shigo kinja kin tsaya min aka. Lafiya?” K'arasowa tayi ta ajiye biro da takardar data boye cikin hannunta ta wani watsawa Babaah mugun kallo mai d'auke da tsananin tsana da kiyayya tace “yanzu, yanzu nan ba gobe ba nake so ka sake ni ko kuma na tona maka asiri duniya tasan irin k'azantar da ka ke aikatawa” Omooooo tashin kai 😧. Wa MOM ta burge yau?😆 𝗧𝗔𝗨𝗥𝗔 𝗕𝗜𝗬𝗨 ®𝐀𝐬𝐡𝐚𝐧𝐭𝐲𝐥𝐮𝐯 /No edit! 【Pg23&24】 Gaban Babaah ba k'aramin fad'uwa ya yi ba amma ya sake had'e fuska “wane maganan banza ki ke yi haka? .” “Kasan me ka ke yi bazan fad'i ba don abun kyema ne da kyenkyemi. Tur da wannan mugun hali da ka ke ,kuma walahi sai Allah ya bi min hakk'i ni nida ya'yana ko ba dade ko ba jima. Ka rubuta min saki yanzun nan ko walahi yanzu na saka ihu da zan tara maka dangi cikin d'akin nan sunan abunda ka ke aikatawa .” Yanda take maganan ya tabbatar babu wasa cikin lamarin kuma tabbas akwai abunda ta sani. Me ta sani? Wata irin zufa ce ta karyowa Babaah ya warce takardar ransa a b'ace. Zai bata abunda take so yanzu saboda akwai mutane a gidan amma idan sun tafi sai tayi nadaman abunda tayi masa. A zafafe ya rubuta mata saki d'aya ya wani wulla mata takardar yana binta da wani mugun kallo. Bin takardar Mom tayi ta d'auka ta bud'e sai taga saki d'aya ya rubuta. Ji tayi kaman wacce aka saukewa wani katon abu a k'afad'unta saida hawaye suka biyo kuncinta wanda ita kanta bata san ko na farin ciki bane ko akasin haka. Numfashi taja mai k'arf ta juyo ta sake watsawa Babaah kallon tsananin tsana da kyama kafin ta juya da sauri ta fice daga d'akin. Tana fita ya koma gefen gado ya zauna ya yi wani shiru yana tunani. Shin menene ta sani? Bai tab'a bada k'ofa ko bada wata hanya da zatasan abunda yake ba, kuma yasan cewa tabbas yana taka tsantsan a kan hakan. To menene ta sani game dashi har take masa barazana? Y'ar kwafa ya yi yana jin haushin kansa ma da ya yi saurin karaya ya bata abunda take nema. Yanzu haka burga ce kawai saboda tasan yanzu ne kad'ai zata samu wannan y'anci tunda bai isa ya tab'a ta da mutane a gidan ba, amma ai zasu tafi. Fuska ya shafa ransa na suya ya fito da wayar sa ya shiga contact nashi kai tsaye number Asad daya samu ya dannawa wa kira. ──────────────────────── Ko kafin wayar ta shigo yana zauna falo ya yi nisa kan laptop nashi yana had'a wasu files na wasu patience da zai duba su idan yaje Dubai next week. Duk da cewa hankalin sa ya yi nisa wajen duba abunda yake tunanin sa na kan

Chapter 10 of 15