Ajwa da har yanzu bata fito ba kaman yanda ta saba. A karo na uku ya sake d'aga kai ya kalli hanyar corridor ko zaiji motsin ta amma shiru. Numfashi ya d'an ja ya fesar don bak'aramin yunwa yau ya tashi da ita ba. Tunda yaji yanayin girkin ta da yanda ta masifar iya girkin yake kwad'ayi ta fito ta sake d'urawa kaman jiya idan taji shiru. Kallon haddedden agogon hannun sa ya yi daya nuna masa tara saura y'an mintina. To me take har yanzu bata ta fito ba?. Ko sanda yake kai mata abinci d'aki yana samun ta tayi wanka ta shirya tana zaman jiransa ,shi d'an aikin nata. K'aramin tsaki ya saki ya miƙe zai shige kitchen wayarsa ya hau ringing. Kaman bazai d'auka ba saboda ganin bak'uwar number amma tunawa da ya yi zai iya kasancewa kira ne maimuhimmanci ko daga Far'aan ma ya yi saurin d'agawa ya k'ara a kunne yana sallama.
Wani munafukin numfashi Babaah ya sauke a b'oye kafin yace
“waslm Asad. An tashi lfy? Nasan baka gane wake magana ba. Mahaifin wannan y'ar ne. Alhaji Khalid .”
Da sauri Asad ya d'an russuna duk da ya yi mamakin kiran cikin girmawawa yace
“ina kwana Babaah an tashi lfy?”
“lfy lau alhamdulillah. Ya naku kwanan? Da fatan dai babu wata matsala ko? Ina taso na kira naji yanda ku ka sauka to kuma uzuri ya hanani. Ina fatan kuna lfy?”
Saida Asad ya d'an taune harshe ya bashi da 'lfy lau '
“to MashaAllah. Dama nace bari naji yanda ku ke . Sai kayi saving number ta ko Hussein saboda halin rayuwa. Ina mai sake tunama kar kaji komai ka kira idan har kaga ba daidai ba wajen yarinyar nan saboda nasan halin ta da kafiya da kuma taurin kai. Kayi hak'uri da abunda zata maka kaji inshaAllahu zamu cigaba da ja mata kunne. Allah ya yi muku albarka ”
Da kyar Asad ya iya amsawa da “to Babaah. Amin ” saboda gaba d'aya wayan ta gundureshi shi ba ma'abocin san magana bane amma baisan me yasa ba gaban Ajwa ya zama parrot. Ance zama da mad'aukin kanwa gashi ta shafa masa kashin kaji. Shaf ya manta yana kan waya ya d'an saki murmushi mai sauti a fili ya yace a hankali
“Little tiger ”
“Naam, kana magana ne Asad ”
Da azama ya cire wayar daga kunne sa kunyar duniya ta ishe shi. Walahi shaf ya manta yana waya da mahaifinta. D'an gyaran murya ya yi kafin yace
“aa Babaah. A gaida su Mom. Sai anjima”
Bai jira Babaah ya sake cewa wani abu ya kashe wayar da sauri ya ajiye yana maida numfashi. 'To yanzu duk firgicewar da kayi ta menene? Saboda ka kirata da pet name kunnen mahaifin ta shine duk ka rikice kaman wanda ya yi sata?kar ka badamu mana ko ka manta kudurin mu a kanta?. Make her love us sannan muyi crushing wannan girman kan da tsiwar.' Wani b'angare na zuciyar sa yake wannan babatun ya yinda d'aya b'angaren yace 'hmm, ko ita tasa ka fad'a soyayyar ta ba'
Da wani irin k'arfi yace “ita d'in banza. Me zanyi da wannan y'ar ficiciyar yarinyar?mtsw. Nonsense ”
Komawa ya yi ya zauna amma mind nashi ya kasa samun nutsuwa rashin ganinta. Dole ya miƙe ya shige kitchen ya d'ura indomie yana ta wasi-wasi ya dafa da ita ne ko ya barta kawai?
To b'angaren Ajwa kam tun bayan tayi sallah asuba ta kwanta da wani irin ciwon mara. Tun dare take jinsa kad'an-kad'an dama ta shirya masa tana saka ran zuwansa ko da safe ko da yamma. Sai kuma wajen asuba har tayi sallah bai zoba ba amma tana kwanciya ciwon ya k'ara wani irin tsanani ko tashi ta kasa sai murkususu take kan gado. Tsabar azaba saida tayi hawaye. Bata tab'a ciwo irin na yau ba. Tana samun cramps idan zatayi period amma ciwon ba wani ciwo bane da yake hanata sakewa kuma da tasha magani shikenan ,amma yau ciwon ji take kaman zata mutu gashi ta duba maganin nata bata ganshi ba cikin kayanta ba. Tana wani irin nishi ta juyo ta kalli k'ofar d'akin da taji kaman ana d'an kwankwasawa kafin ya buɗe k'ofar ya sawo kai ciki gaba d'aya rike da d'an bowl daya zuba mata indomie da kwai . Turus ya tsaya yana kallon d'akin saboda duhu sai y'ar side drawer dake bada haske kad'an kad'an masu kala. Ko window bata bud'e ba bare rana ta shigo. Hannu ya kai ya kunna switch haske ya gauraye d'akin ya bi d'akin da kallo. Can kudundune ya hangota cikin bargo sai nishi take da kyar. Gabansa ne ya d'an fad'i yanayin daya hango ta. Badai zazzab'in bane har yanzu? Da sauri ya nufi bakin gadon Ajwa sai k'ok'arin k'ara jan zani take zata rufe kai. Ajiye abincin ya yi kan drawer ya d'an rankwafa wajen kanta daga tsaye yace
“what's wrong? Badai har yanzu zazzab'in bane? ”
Shirun da tayi bata bashi amsa ba ya kama bargon zai janye shi tayi saurin rik'eshi duk uban ciwon da cinta. Da kyar ta juyo ta watsa masa jajayen idanuwanta da suka kankance saboda ciwo. Saida yaso ya yi dariya saboda yanda ta dage tana zuba masa harara. Wani irin shan kunu ya yi fuska babu wasa yace
“idan har baki gayamin meke damun ki ba zan duba da kaina na gani. Kuma wlh ki ka yi wasa sai nayi miki allurar da baki so”
Baki ta bud'e kamam zatayi magana sai kuma ta rufe ta mayar da ido ta runtse tana d'an cije lebe saboda wani irin murd'awa da mararta ya yi lokaci guda kuma taji abu ya biyo k'afarta kaman tayi fitsari. Wani irin nishi ta saki saboda d'an sararin dataji na ciwon. Duk abunda take yana ankare da ita kuma tas ya gano musabbabin ciwon. Cikin ransa yace 'haka take shan wahala dama idan zatayi period?' . Gani kawai tayi ya miƙe ya fisge bargon da k'arfi a bazata. D'an k'ara ta saki saboda tad'an sakankance tana maida numfashi saboda lafawar ciwon. A rud'e da rashin k'arfi jiki ta fara k'ok'arin jawo filo ta rungume saboda doguwar rigar barcin dake jikinta mara nauyi. Inma ya lura da abunda tayi bai nuna ba saiji tayi kawai wuff ya yi sama da ita kamar y'ar tsana,ashe ba k'aramin b'aci tayi ba don gaba d'aya ta b'ata inda take kwance. Daga shi har ita wajen suka zubawa ido kowa da tunanin dake ransa. Nasa mamakin bleeding d'in datayi ne duk da yasan cewa akwai mata da yawa da farkon al'ada suke zubar da jini haka da yawa amma kuma daga shi shikenan sai dai kad'an kad'an zaka dinga ganinsa. Yana kuma mamakin yanda baiji wani kyenkyemi ba kaman yanda wasu maza da yawa suke yi. Like he is not gross about it at all. Akwak mazan da Idan matan su na al'ada ko abincin ta sun daina ci sai ta gama kuma babu kunya su dawo suce zasu nemeta.
B'angaren Ajwa tsabar firgice da kunya yasa ta zama kaman gunki. A zahiri wajen take kallo amma a bad'ini tayi irin suman nan ne na wucen gadi. Bata dawo hayyacin ta ba saida taji ya juya ya yi hanyar toilet. Wani irin zabura tayi kaman wacce wuta taja ta fara k'ok'arin sauka daga jikinsa tana kai masa yakushi da cizo. In ance tana cikin hayyacin ta ita kanta tayi k'arya don da zata san muguwar wawurar data kaiwa kumatunsa da hak'oranta kaman wata vampire. Duk k'ok'arin kaucewa da Asad yake saida ta damki kumatun nasa cikin bakin ta hakan kuma ya yi sanadin da wani jiri ya kwasheshi saboda wani irin abu daya tsarga tun daga tafin k'afarsa zuwa kwakwalwar sa. Tim suka zube gaba d'aya nan k'ofar banɗakin ya danneta da katon jikinsa.
Tsit Ajwa tayi tana zare ido dake waje tana kallon silin k'irjinta na wani irin bugawa kaman zuciyarta zata fito. Bama ita kad'ai ba harshi kansa Asad da ya yi wani irin shiru kansa na cikin wuyanta. K'ok'arin ihu take amma yanda ya sake mata nauyin sa gaba d'aya yasa numfashin shi kansa yake mata wahalar fita. Sun d'auki sama da minti biyu a haka ta kasa wani kwakwaran motsi shima kuma yaki motsawa ,numfashin nasa ma ta daina ji . Gaban tane ya fad'i kar taje fa ko mutuwa ya yi? Innalillahi ta shiga uku. Daga cizo kuma sai mutuwa?.
Shiru-shiru Asad bai motsa har wata minti biyun ta sake shud'ewa. A yanzu kam tsoron Ajwa kaman zata had'iye zuciya tsananin firgici. Ta shiga uku ita Ajwa yanzu idan aka tuhumeta saboda me ta kashe shi tace me? Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Sai shar hawaye suka fara wanke mata fuska a fili ta fara
“Allah na tuba, Allah na tuba kar ka tuhumi da abunda bada niya nayi ba. Wahala bada niya na kashe shi ba. Na shiga uku. Allah na tuba, Allah na tuba”
Asad dake jinta duk da cewa yana can wata duniya da Allah kad'ai ya sani ya fara dariya sosai jikinsa na jijjaga. Yanda yake jijjaga a jikinta yasa a rud'ud'e ta kai kallon ta kansa. Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma tayi saurin rufe ido saboda borin kunya. Kai yana ta shammatar ta tana yin abubuwan da ita kanta bata san tana da halin su ba. A hankali ya mirgina gefen ta still yana dariya sosai harda hawaye. Saida ya yi mai isar sa sannan ya d'an gicgiya gefen hagun sa ya tallafe kansa da hannun sa yana kallonta. D'an murmushi ya sake ganin yanda ta wani sandare sai k'ara damke ido take duk dan karta bud'e. Sauke idansa ya yi kan d'an k'aramin bakinta da take ta motsa shi tana turoshi gaba irin yanda sagalallun yaran suke idan zasuyi shagwaba. Leɓen sa na k'asa ya cije yana kallon bakin nata data sake turoshi tana d'an motsashi alamun ita kanta batasan tana yi ba. Ahh, she's driving him crazy.
Komawa ya yi yana shima yana kallon silin ya lumshe ido yana fesar da hucin numfashi kafin ya yunk'ura ya miƙe zaune yana kallon stain d'in da tayi shima duk ta b'ata masa jiki. Murya ya d'an gyara sai kuma ya cunkushe fuska
“vampire ki ka zama zaki cinyen kumatu daga taimako?. Is this how you repay wanda ya taimake ki nemi cinye shi d'anye?”
Kaman dama jira take ta wani tashi fii tana zuba masa harara tuni abunda tayi ya fece. A zafafe tace
“ni ba mayya bace ehe. Kuma babu wanda ya saka taimako na kana shiga sharu babu shuni. ”
Murmushi ya yi yana k'ok'arin kaucewa kallon ta saboda yanda k'irjinta ke bouncing da don babu bra a jikinta. Abunda ya sashi mutuwar kwance kenan daz'u. Baiyi expecting haka suke so floppy. Fuu ta tashi tayi toilet a guje ta banko k'ofar. Hannu ya kai ya shafa fuskarsa yana fesar da wani huci kafin ya yi jarumta ya miƙe ya yi kan gadon ya cire zanin ya yi waje dashi.
Wanka take amma yanda kasan ruwan shine ya yi mata laifi sai kamfatar sa take ta zafin rai tana zubawa ajiki lokaci-lokaci tana goge hawaye dake biyo kuncinta da mugun k'arfi. Bak'in ciki ne, takaici ne, haushi ne, tsana ce kai ita kanta bata san me take ji yanzu. Saida ta jima a banɗakin sannan ta fito d'aure da tawul yanzu ko shakkar yana nan ko baya nan batayi ba. Tadai ci alwashin zata bishi da game nashi kuma itace zatayi winning. Turus ta tsaya bakin gadon tana kallon ledar daya ajiye mata ta pad da kuma magani ga kuma abinci daya ajiye mata kan drawer amma da alama takeaway ne. Baki ta tab'e a fili ta sake cewa MIJIN TACE kawai. Kiran sunan bai hanata taja abincin ba taci ta koshi ta kora da maganin kafin ta kimtsa kanta cikin wata doguwar riga yar kanti mai gajeren hannu tabi lafiyar gado ta kwanta tana kiran Suliem. Sun jima suna waya don saida suka gaisa dasu Nonna sannan ta kashe wayar saboda barcin dake ta fisgar ta.
────────────────────────
'𝑙𝑖𝑡𝑡𝑙𝑒 𝑡𝑖𝑔𝑒𝑟 '
'𝑙𝑖𝑡𝑡𝑙𝑒 𝑡𝑖𝑔𝑒𝑟 '
'𝑙𝑖𝑡𝑡𝑙𝑒 𝑡𝑖𝑔𝑒𝑟 '
Abunda keta masa amsa kuwwa kenan cikin kunne yana sake hasasho yanda muryar Asad d'in ta koma . Tayi wani irin deep gata so husky daya sa dole ya fasa zuwa office kai tsaye ya nufo estate nashi tare da wani yaro daya d'auko can wani b'oyeyyen club. Rungume yaron ya yi yana wani irin gurnani jikinsa har ya juye masa abunda ke mararsa yana kiran sunan Asad. Kai anya kuwa zai iya jurewa har zuwa wani lokaci bai aiwatar da kudurin sa ba?. Karfa yaje garin kallon ruwa kwad'o ya yi masa k'afa. Allah yasa ba wannan yar iskar yarinya yake kira da little tiger ba don d'azu kad'an ne zuciyar sa bata buga ba. Gefe ya koma yana sauke numfashi kafin ya mik'a hannu ya d'auko wayarsa ya dannawa wata number dake b'oye cikin contact nashi kira.
────────────────────────
B'angaren sa yana kawo mata abinci ya sake wani wankan a gurguje ya fice daga gidan saboda kiran gaggawa daya sameshi daga wani private asibiti. Yana zuwa kai tsaye sukayi masa iso wajen theatre don shi kad'ai aka jira. Kaman yanda ya saba da Addu'a ya shiga kuma alhamdulillah an samu nasara. Bai fito ba sai wajan azhar ,yana fitowa kuma kai tsaye gida ya yi k'ok'arin yi amma sai ya tsinci kansa shiga wani katon Mall daya gani nan kan hanya. Samun kansa ya yi yana ta kwasar chocolates, cookies da snacks ga uban drinks kala-kala. Shi kansa baisan me yasa ba duk abunda idansa ya gane masa zuciyar sa zata bashi zataso shi don haka kawai yake kasowa babu lissafi. Yana zuna kayan cikin boot tare da wani staff na gurin sai ga kiran Dad yana neman sa.
A hankali ya sake kai hadad'd'ediyar tuwon masara da miyar d'an yen kubewa da Mamee tayi taji uban kifi busheshesh ,ganda da kuma nama. Shi mutum ne mai son abincin gargajiya musamman ma tuwo. Saboda haka ne yanzu daya zo ya riske tuwon a gida bai musa ba ya zauna yana ci rabin hankalin sa nacan kan Ajwa. Zama Dad ya sake gyarawa yana nannad'e jaridar dake hannun sa ya sake kallon Asad dake cin abinci cikin nutsuwa. D'an murmushi ya yi Allah kad'ai yasan irin dad'in da yake ji saboda sakewa dashi da Asad d'in ya d'an fara. Yana so ya yi maganan gidan nasa da yaji mamaki lokacin da Asad d'in yace masa yana da gidan sa. Bai k'ara jin mamaki ba saida yaje yaga gidan yaga dukiyar da Asad d'in ya zuba. Sai yake jin kansa wani irin so proud amma duk da haka ya kasa samun courage nayi masa maganan ko yana buk'atar wani abu.
“har yanzu babu wani labari daga wajen Hassan? Bai kira ka ba ko ya bada wata k'ofa da za'a gane inda yake?”
Bai amsa ba saida ya cinye lomar dake bakinsa ya kora da haddedden lemon madara da kwakwa sannan yace
“No”
“kai wannan yaro dai Allah ya shirya min shi. Bazanyi fushi ba don nasan duk laifina ne ya jawo hakan ,amma naso ace ko yane ya kiramu muji halin da yake ciki. Ya yi gaggawar yanke hukunci da yace baya son auren sai a fasa babu wanda zai masa dole. Yanke hukuncin guduwa ba shine masalaha ba.”
Shidai Asad baice komai ba yana can yana tunanin wata k'ila Far'aan bai gudu ba bazai samu chance na auren ta ba. Da duk wad'annan childish behaviour, tsiwar ta da kuma rashin tsoron ta duk Far'aan ne zai sansu. Daga can d'an k'asan zuciyar sa daga wani b'angare yaji d'an wani abu ya tokare shi wanda shi kansa baisan menene. Da Far'aan ta aura mai zai faru dashi kenan?. Fitowar Mamee da wata kuka mai hudu wacce ake had'eta gaba d'aya ne ya d'an ja hankalin sa. Ajiye masa kullan tayi tana cewa
“ga tuwon na zubawa Y'ata nasan za taji dad'i cinsa sosai. Idan ka samu lokaci ka kawo mun ita ta wuni.”
“To .”
yace mata ya miƙe tsaye harda d'an murmushin sa.
“Yauwa Asad ya maganan lefe fa? Sai yaushe zaka had'a mata ka bata?.”
Dad ya yi maganan yana kallon Asad d'in dake k'ok'arin ficewa. D'an juyo ya yi yace
“nan da 4day zance Dubai aiki. Ina so sai naje can zan had'a na tawo dasu.”
“to shikenan babu wani abu da ka ke buk'ata?.”
Kai kawai ya girgiza ya yi saurin ficewa.
Tunda ya doshi gate nashi yake jin zuciyar sa na dancing out of excitement. Allah-Allah yake ya shiga ya ganta su fara wanna dagun nasu don ba k'aramin nishadi yake sashi ba. Yana fakin motar ya fara fitowa da kayan yana ajiye su baranda saida ya gama ya buɗe k'ofar ya shiga bakin sa da yar sallama. Daskerewa ya yi tsaye bakin k'ofar shi bai shigo ba shi bai fita ba saboda ganin Ajwa da ya yi zaune falon daga ita sai wata yar k'aramar half vest mai Kaman bra da dake da mad'auri guda biyu data gazaya dashi cikinta ta d'aure ta baya ya yi kaman star. Ga wani shegen skin tight wando jikinta daya kwanta lum jikin k'afar. Gashinta kuwa ta tufke shi tsak'iyar kanta kaman bon.Shigowar sa ya yi daidai da kai cup d'in fresh madara da kwakwa data dafa bakinta. A tare zuciyoyinsu duk suka harba tsabar yanda tayi nisa wajen kwad'ayi yasa bataji motsin Shigowar sa gidan ba har ya buɗe k'ofar tana ta Allah ta gama ta koma d'aki.
Zabura tayi da mugun gudu tayi wani wancakali da kofin dake hannun ta kwasa a guje tana ihu ita kad'ai kaman wacce wani mugun abu ya biyo. Saida ta b'ace ya yi blinking idansa ya sake blinking sai kuma ya kwashe da y'ar dariya yana girgiza kai. Yarinyar is pure comedy wlh. Idan tana waje bazai tab'a zama boring ba. D'akin ya bita ya samu ta gark'ame k'ofar ta ciki. D'an murmushi ya yi ya buga k'ofar a hankali yace
“ki buɗe abinci na kawo miki”
Shiru babu alamun zata buɗe . D'an murmushi ya yi ya sake cewa
“akwai Chocolates, cookies, biscuits, ice cream, burger, shawarma. Chip. Drinks ga kuma tuwo Mamee tace a kawo miki wanne ki ke so?”
Kyekiii yaji tana tab'a mukulli k'ofar tana ko kawar bud'ewa. D'an murmushi ya yi mai kama da dariya a hankali ya d'an ja baya yana kallon yanda ta d'an zuro kai tana kallon ledar dake hannun sa. D'aga ledojin ya yi ya d'an jijjaga da d'aga gira. Babu kunya ta mik'o masa hannu. Ya sake d'aga gira yana d'an b'ata fuska ya ce
“akwai nauyi. Ki buɗe na ajiye miki a ciki. Na rasa menene ma ki ke hiding like girl baki da wani abu da zaki rud'une ko ki chanza tunani na kan ki. So ki daina bawa kan ki too much credit. You're so little not to my taste.”
Kam bala'i. Ita yake kira da kwaila? Bata da abunda zata rud'ud'e shi. Bata san sanda ta wani hangame k'ofar da zafin rai ta rike k'ugu tana jefa masa mugun kallo dake d'auke da magana. 'K'arya ka ke wlh. Kalle ni ka k'ara kallo na na wuce yanda ka ke misali. Ni nasan baka tab'a ganin wannan had'uwar ba.' D'an k'aramin shak'akken numfashi yaja ya wuceta da sauri ya shige d'akin yana murmushi. Tabbas yanzu ya k'ara tabbatar da duk inda yaro yake yaro ne. Sam bata da wayo. Kallon sakan d'ayan da ya yi mata tsab ya karance komai dake jikinta. Ya Rabb. Ta wuce yanda yake tunani. Tana kuma so ta kashe shi da ransa. Yana gama ajiye kayan ya juyo har yanzu tana tsaye bakin k'ofar sai zuba masa harara take ita dole taji haushin maganan sa. Y'ar dariya ya yi sai shigen tsiwa da rashin kunya amma ta iya k'arban abinci taci idan ya kawo. Gabanta ya tsaya suna kallon juna sai kuma ya fesar da numfashi kafin ya d'an kalli gefen k'afad'unta yace
“mene wannan?.”
Da azama ta juya bayan nata tana dube dube ganin babu komai ta juyo zata chab'a masa magana ,babu zato taji saukan leben sa kan kumatun ta kaman wucewar iska. D'an peck d'inta ya yi da sauri ya janye bama zakace leɓen nasa sun sauka kan fuskarta ba. Katon karan na gasp ne ya fito daga bakin ta sai kuma luu ta zube a k'irji sa. What? Did she just faint? Saboda kawai ya b'ata d'an peck shine ta sume?. Shi bai tab'a ganin wannan abu ba. Tsabar tsoron ya sumbace ta ta sume masa to ina kuma da idan real sumbata ya mata?. Sosai yake dariya yana k'ara matseta cikin k'irjinsa tabbas she's trying to kill him ne kawai.
────────────────────────
TURKEY.
ISTANBUL.
Numfashi ta sauke a hankali ta sake kai kallonta kan hoton Asad dake kan wayar ta. Shafa hoton tayi zuciyarta na harbawa da tsananin gudu. Ya sake wane irin kyau da girma ba kaman yanda ta sanshi ba.
“yanzu ya za kiyi kenan naji ance ya yi aure fa?”
A hankali ta d'aga idanta ta kalli k'awar ta ta dake zaune gabanta. Fesar da numfashi tayi ita tana da yak'inin mo mata d'ari Asad ya aura bazai tab'a daina sonta ba. Tayi masa laifi kuma yanzu a shirye take ta fuskanci hukuncin abunda ta aikata masa matsawar hakan zai saka ya yafe mata ya kuma dawo gareta.
“in ya yi aure sa me? Kina tunanin duk yarinyar da Asad zaiso ko ya aura zata maye gurbin soyayya ta ne a zuciyar sa? Ko kin manta soyayyar Asad a gareni?.saboda soyayya ta babu abunda baiyi ba. Ni nasan idan na koma masa na bashi hak'uri he will forget everything ya k'arbe ni hannu bibbiyu. ”
Hmm kawai d'ayar tace a zuci tace 'iska tana wahalar da mai kayan kara. Rayuwa ta wuce abunda ki ka masa kina tunanin zai bari ki sake shiga rayuwar sa? So delusional. I hope matar sa taci ubanki then zaki fuskanci irin kuncin rayuwar da ki ka jefashi.'
Finally Asad fast life sun fara shigowa da full force 🤭. Tafiyar fa akwai ta da tsayi🤣. Gefe kuma ga Asad da Ajwa na developing zamantakewar su a hankali. Nasan da yawa wannan zama nasu na saku nishadi😂🫠.
𝗧𝗔𝗨𝗥𝗔 𝗕𝗜𝗬𝗨
®𝐀𝐬𝐡𝐚𝐧𝐭𝐲𝐥𝐮𝐯
/No edit!
【Pg25&26】
Saukan abu da taji kam goshinta mai laushi da d'an ruwa a jikinsa, yasa ta d'an yatsina fuska tana sake sakin jiki kan gadon da take jinsa da tsananin laushi ga kamshi da yake fitarwa mai dad'in gaske. Can kum ta wani buɗe ido da sauri kaman wacce aka d'alawa mugun duka. Zare manyan idanuwanta tayi ganin kwance rasha-rasha kan k'irji Asad dake kallon ta da murmushi kan fuskarsa. Kama wata mage tayi wani tsalle ta daga jikinsa tayi gefe tana kallon sa cike da takaici. Da hannu ta nuna shi tace
“me ka ke tunanin ka ke aikatawa haka? .”
Yunk'urawa ya yi kad'an ya dago ya talle fa jikinsa da gwiwar hannun sa dake kan gado. Saida ya d'an tab'e baki yace
“me nake aikawata kaman ya? Wannan tambayar kan ki ya kamata kiyiwa don idan ban manta ba ke ki zo har inda nake. Nayi nayi kuma sake ni kin ki”
Yanda ya yi maganan fuska babu wasa ya hanata yi masa tsiwar dake cinta. Tunani ta Lula anya kuwa ita ta matso wajen sa? To yaushe ma tayi barcin bata sani ba. Abunda ya faru daz'u ya dawo mata da ya yi sanadin sata d'agowa ido waje ta kalli Asad dake mata wani irin kallo. Sake nunashi tayi bakin ta na rawa tace
“you kiss me? How dare you?”
Anzo wajen da yake so azo. Wani shegen murmushin gefen baki ya saki yana cewa
“what kiss? Wannan ki ke kira kiss? Ni babu wani kissing naki da nayi yarinya ”
Kaman ta makeshi tsabar haushi. Asad ya iya rainin hankali.
“idan ba kiss bane ba menene? What did you call it a naka duniy.. ahh”
Ko kafin ta gama fadar abunda take cewa kawai taji ya fisgota ta da k'afar sa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 15