An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
* . °•★|•°∵ TAURA BIYU ∵°•|☆•° . *
®𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵𝓸𝓿𝓮
18+
𝓬𝓸𝓹𝔂𝓻𝓲𝓰𝓱𝓽 /𝔀𝓪𝓷𝓷𝓪𝓷 𝓵𝓲𝓽𝓽𝓪𝓯𝓲𝓷 𝓱𝓪𝓴𝓴'𝓲𝓷 𝓶𝓪𝓵𝓵𝓪𝓴𝓪𝓷 𝓶𝓪𝓻𝓾𝓫𝓾𝓬𝓲𝔂𝓪 𝓷𝓮.
'بِسْمِ ٱللَّٰهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
【Pg1&2】
Tsananin zafi da rana da ake yau mussaman wannan rana ta Juma'a, bai hana mutane fitowa da kuma gudanar da harkokin su ba na yau da kullum, kaman yanda aka sana. malam bahaushe , duk wuya duk tsanani bai hanasu fitowa cigaba gudanar da al'amrunsu . Saboda zafi da tsanani rana da ake duk inda da ka wuce zakaji mutane na maida zancen wannan rana, kai harta tsuntsaye da dabbobi nata kuka saboda zafin rana. Daga can gefen wani matsakaicin fili da titi ya raba ,wanda ke dauke da wani matsakaicin stairs , yara ne suke ball filin hankali kwance duk wannan tsananin zafi da rana da ake bai damun su sai ihu suke da guje-guje ta yanda zaka san ball d'in sosai take musu dad'i. Yaran sun kasu kashi biyu Team Blue da Team Black. Wasa ya yi zafi d'an Team Black ya yiwa d'aya daga Team Blue k'afa. Yaro kuwa ya zube a k'asa rik'e da k'afa yana zuba kuruwa kaman za'a cire masa harshe. Lokaci guda wasa ya kacame da fad'a, ko wanne Team yana son karewa nashi. Suna cikin fad'an aka bud'e babban black gate na gidan da suka juyawa baya. Kaf yaran suka nutsu lokaci guda duk suka juyo suna kallon Gate d'in da aka bud'e.
Budurwar yarinyar ce ta fito da bazata haura sha takwas ba. She was a petite girl(siririya ce). Tana sanye da dogon bak'in wando mai kaman buje da rigar sa kaman three quarters an rubuta I'M THE BEST wajen k'irji, sai d'an siririn bak'in mayafi data d'ura a kanta tayi d'an rolling dogun gashinta data nad'e kaman gammo. Sanye take da farin glass daya zauna rad'am kan dogon hancinta kaman wanda aka zana. A hankali ta tako inda yaran suke tsaye curku-curku suna kallon ta fuskarta cike da tuhuma. Gabansu ta tsaya ta kai hannu d'aya ta rik'e kugu tana k'ara tura glass d'in ta daya d'an zamo kan hancinta , cikin ido. Saida ta k'are musu kallo d'aya bayan d'aya a tuhume tace da y'ar siririya muryarta
“ihun na menene?, mene yake faruwa a nan?, tun daz'u kun hanani barci kun hanani karatu? Hayaniyar ta mace?”
Wuf d'aya daga cikin Team Blue ,wani dan siririn yaro wanda da alama duk ya girmi sauran yaran ya bata amsa da sauri
“Kinga KHALA(aunty)wlh kawai muna wasa shine suka fara fad'a ”
Gira ta d'aga tana kallon yaran da suka fara fad'an cike da tuhuma. Shi wanda aka dakanma har zuwa lokacin kuka yake yana share majina.
“me ya maka?”
Ta jefawa wanda ya fara kai harin tambaya. Baki yaron ya turo yana k'unk'uni yace
“ai shine ya fara duka a kunne Khala, kuma sai ya dinga shigowa cikin Team namu bayan ga nasu Team d'in nan”
“k'arya yake Khala, shine ya fara duka na kuma ni ba shiga Team nasu nake ba, a tsakiya kawai nake tsayawa”
A harzuk'e yaron da ya yi dukan ya matso yana neman sake kamashi da dambe yace
“tsak'iyar banza da wofi. K'aryar banza kawai”
Da azama Ajwah ta shiga tsakaninsu tare da buga tsawa
“kai to ya isa haka. Wuce muje a sake sabon wasa ina gani. Duk wanda ya sake fad'a sai ransa ya b'aci ”
Hannu tasa tana kad'a yaron kowa ya koma nashi Team d'in. Y'ar ajiyar zuciya ta sauke ganin ta shawo kan matsalar da wuri. Mafi aka sari itace dama referee nasu. Da wuya ayi wasan ba tare da anyi fad'a ba amma tana k'ok'ari ta shawo kan matsalar cikin hikima. Wannan dabi'u nata da hali nata yasa ta fita daban cikin jerin y'an mata, ko nace yaran zamani dake tashe yanzu. Ajwa yarinyar ce da bata da shakka kuma bata da tsoro. Bata ganin rashin daidai da rashin da'a wajen wani ko wata ta barshi. Kai ko dabbace ka zalunceta inshaAllahu idan har ta gani da idonta to sai inda k'arfin ta ya k'are
Bata da hayaniya idan baka shiga hurumin taba, haka tana da sauk'i wajen wanda suka santa. Saboda haka ne iyaye da dama suke mata kallon yarinya Y'AR KANTA,MAI GIRMAN KAI DA KUMA RASHIN TARBIYA.
Lokacin da Ajwaah ta koma gida wani irin gauran numfashi ta sauke hango motar mahaifin su da tayi fake harabar gidan. Ya shigo ta can babban gate daya fita main titi. A take taji wani sabon ciwon kan ya sake kawo mata ziyara tun ma bata k'arasa shiga b'angaren mahaifiyar tasu ba. Cin Mutunci da tozarci ga kuma fad'a, shine abunda ya zame musu ruwan dare kullum babu dare babu rana.
Chak k'afafuwanta suka tsaya wajen corridor nasu jiyo ihun mahaifin nasu kaman zai cire harshe. Wani numfashin ta sake saukewa ta maida ido ta lumshe kanta na k'ara wani irin matsanancin sarawa. Wannan ba sabon abu bane domin ihun mahaifin nasu yanzu ya zame musu tamkar kalangu ne da ake bugawa kullum safe, rana, dare.
“wai ke wace irin mata ce da har yanzu shekara ashirin da biyar kin kasa iya girki ?. Wace irin dak'ikiyar mace ce ne ke komai baki iya ba?”
Ya k'arasa maganan da mugun k'arfi yana buga tablet sai da dinner ta amsa gaba d'aya glass suka fad'o ji ka ke tartsassss suna fashewa.
“na...na...na d'and'ana abincin don naji ko gishirin ya yi daidai, sanda na duba normal naji sa”
Mahaifiyar Ajwaah,Mom (MEASHA BEGUM )ta yi magana da y'ar siriyar murya ta dake da mugun rauni .
“OK ,nayi miki k'arya kenan ko? Ga mak'aryaci kuma mahaukaci ko?”
Da wani irin hargagi Khalid Yaqoob ya miƙe yana magana yana kumfar baki ya yi kan Mom yana ihu
“har kin isa ina magana kina mayar min da martani, wuyan ki ya isa har ki kirani da sunan mak'aryaci?”
Hannu ya d'aga da dukkanin k'arfin sa zai sauke mata su kan fuska, Ajwaah data kasa jure tsayuwar da tayi ta wani fad'o dinner d'in tsalle d'aya tayi ta riƙe hannun mahaifin nata da wani irin k'arfi da ita kanta bata san tana dashi ba. Daga ita harshi ido duk suka zubawa juna komai ya tsaya ya yi chak. Cike da mamaki take kallon hannunta data rike na mahaifin nasu . Murya cike da rashin gasgata abunda tayi tana kallon mahaifin nata ido cikin ido, kaman yanda ya zuba mata jajayen idanuwansa da suka fito sukayi mugun jaa kaman gauta tace
“Me ka ke shirin aikatawa haka Babaah?”
Saida taja Babaah din sak yanda suke kiransa da harshensu na larabci. Yanda yake kallonta da bloodshot eyes kaman wuk'a, ya isa ya sakata sakin fitsari saboda tsoro amma Ajwaah ko d'ar a ranta ta cigaba da kallon sa take da wani irin challenge look kwayar idonta kaman mai cewa try me father.
────────────
𝙱𝙸𝙱𝚄𝚁𝚈/𝙴𝙽𝙶𝙻𝙰𝙽𝙳
Tsaye yake jikin window riƙe da mug a hannun sa da tea a ciki sai zuba tururi yake. Dark blue three pieces suit ne a jikinsa sa da sukayi mugun kama ingarman jikin nasa. Hannu sa guda d'aya yana sanye cikin aljihun wandon ne tsintsiyar hannu da hadad'd'en wrist watch na Prada. Daga inda yake tsaye yana hango Kyakkyawan kauyen garin tanan. Ko ina ya yi shar da bishiyu da filawoyi masu tsananin kyau da burgewa. Murmushi ne kwance kan fuskar sa dake boye da black mask. A koda yaushe yana samun irin wannan k'auye waje mai saka nutsuwa da farin ciki,shi yasa yana sha'awar zuwa irin wad'annan k'auye don hakan yana sama masa nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali. Babban of abunda yasa yake k'ara son irin wad'annan k'auyuka saboda mahaifiyar sa data taso daga k'auye cikin manoma. Tun yana yaro ya taso zuciyar sa da gangar jikinsa suna da tsananin son noma ko wani abu daya shafe shi. Yaso ya samu dama yasan asalin dangin mahaifiyar sa ko dan ya cika burinsa na ganin ya sake had'ata da dangin ta,to amma Allah bai nufa ba duk irin k'ok'arin sa wajen ganin hakan ya kasance har k'asa ya rufe mata ido and his Dad, shi ne mutum na k.....
“to Mr.Hussein. yaushe zamuji labari ne mai dad'i?”
Abokin sa Su'ad ya katseshi daga tunanin da yake. Da wani irin isa ya juyo inda Su'ad ke zaune da d'an murmushi kwance kan fuskarsa da alama ya yi maganan ne don tsokana. Manyan Onyx dark eyes nashi da kusan gashinsa daya zubo wajen goshin sa ya rufe ya watsawa Su'ad. Gira ya had'e da wata irin cold voice yace
“what good news?”
“shekara 33 ka ke yanzu ka tafi 34. You're a successful well established doctor da duniya keji dashi. Rich and f# handsome ,gorgeous, Kyakkyawan mutum. So sai yaushe zakayi aure?”
Ya k'arasa maganan yana wani irin kallon Hussein tun daga sama har k'asa da smirk kwance kan fuskarsa ya k'ara cewa
“haba kaifa thousand percent ne ba hundred ba in da sa'a da nake da the one and Mighty ASAD ALHUSSEIN AL-SULTAN matsayin aminina, kuma d'an uwa daga wata uwar Walahi”
Da ihu ya k'asara maganan harda miƙewa tsaye yana cilla hannu kaman wani mace. Da wani irin mugun gudu ya kaucewa hucin iskar daya gifta wajen fuskarsa zuwa bayan sa jinka ke tass abu ya daki bango . Wani irin juyowa ya yi ya d'ura hannu a k'irji ya zaro ido waje ya juyo yana kallon Mug d'in da Asad ya jeho masa. Shar saiga wani munafukin hawaye daga ido d'aya ya biyo kuncinsa ya juyo yana kallon Asad dake kallonsa har yanzu very coldly kaman yana jira ya k'ara cewa tak ya sake kawo masa wani harin. Far Su'ad ya watsa masa harara sai kace mace
“sai dai kayi ka kaji ni da kai mutu ka raba walahi takarmin kaza. In kaga na barka to lokacina ne ya yi.”
Lumshe manyan idanuwansa Asad ya yi saboda wani headache da yaji ya ziyarce shi. Wannan shine rayuwar sa duk lokacin da yake tare da wannan alak'akan. Is like kaman yaba kulawa da babban mutum dake da tunanin yara . Tasowa Su'ad ya yi har inda yake tsaye lokaci guda wannan wasa dake kan fuskarsa ya kau. Da serious magana da kuma kulawa ya kai hannu ya dafa Asad daya kereshi a tsaye.
“Mu ajiye wasa a gefe Asad, lokaci ya yi da yakamata kayi aure ko dan saboda condition naka. Kai likita ne amma akwai maganin da bazaka iya bawa kan ka ba bare ka warkar da abunda ke damunka inda zaka iya da tuni kayi. Duk wad'annan magunguna da ka ke sha ka ke had'awa kan ka baza su cigaba taimakon ka ba koda yaushe. Ina jin tsoron ranan da hakan zai maka illah please ka saurareni ko sau d'aya ne ka manta abunda ya faru kayi aure.”
“no” A kausashe ya bashi amsa kai tsaye da wani irin cold voice mai saka tsigar jikin ka ta tashi. Ko d'ar Su'ad baiji ba bare hakan ya sake masa gwiwa yasan waye Asad tun suna yara ko Uwar sa da Ubansa basu kaisa sanin Asad ba bare HASSAN. Hannu ya hard'e a kirji yana kallon Asad d'in daya juya masa baya ya maida hankali jikin window da duka hannun sa biyu cikin aljihun wandon sa. Sosai yake kallon sa da karantar sa da tunanin wace lucky mace ce zata samu chance na ta k'arya zuciyar the icy cold King?. Wace macece bayan ita zata samu ta sake buge bangon daya gina ya rufe zuciyarsa?Wacece ita kuma tana ina?
“ya kamata kayi tunanin kan ka yanzu Asad. Lokaci ya wuce. Kai baka sha'awar kaga yanda Hassan yake da y'an mata yana neman yin aure kaima kayi? Baka sha'awar kaga kunyi aure tare da gudan jinin ka?, besides ni ina buri naga an fara kirana da uncle Su'ad ”
Ya k'arasa maganan cike da zolaya. Shiru Asad ya yi baice komai ba amma kiran sunan Far'aan da ya yi ya saka masa wannan nutsuwa cikin ransa yaji dukkanin wata damuwarsa ta ya ye ya d'an saki murmushi kan leɓen sa. ASAD na matsanancin son twin nashi da zai iya bada rayuwar sa saboda shi.
Su'ad dake karantar sa ya cigaba da cewa
“ya kamata ka manta da ita ka daina tunanin abunda ya faru ya kuma wuce. ”
Murmushin dake kan fuskar sa lokaci guda ya kau ya wani irin juyowa da wani irin cold stare ya watsa onyx eyes nashi cikin na Su'ad daya d'an ja baya kad'an ganin yanda ya juyon yana d'aga hannu sama in defeat. Da wani irin d'acin rai da force magana a d'aid'ai ce yace
“Don't.. don't ever.. kar ka sake.. kiramin wannan sharar a nan”
“Alright, shikenan. Far'aan ya kira d'azu kana Theatre nace idan ka fito zaka kirashi.”
Su'ad ya yi saurin chanza zancen don yasan Asad in har akan wannan maganan ne yana loosing dukkanin wata temper nashi. Ido ya lumshe yana jin yanda jijioyin kansa suke motsi alamun sun fito raɗau goshin sa. Numfashi ya sauke a hankali zuciyarsa na wani irin zugi. Ya tsani wannan feeling da yake ji duk lokacin da akayi brought up na wannan issue. A ganin sa she's not worth litte of his reaction bare damuwa.
“Dr Asad, mun samu emergency na wani patients da aka kawo yanzu , ya samu mummunan rauni a k'afa saboda hatsarin mota da sukayi.”
Wata baturiya nurse ce ta shigo cikin gaggawa bayan tayi bugu sanye da kayansu na nurse. A hanzarce Asad ya fisgi coat nashi dake kan kujera ya bita da sauri suka fice Su'ad ya bishi da ido da tunani kala-kala cikin ransa.
Yana fitowa daga office d'in kuwa corridors na asibitin ya cika da kuke-kuke. A guje dangin wanda hatsarin ya shafa sukayo kansa suna kuka, mahaifin yaron ya tawo ya riƙe hannun Asad yana kuka sosai yana cewa da turanci
“don Allah ka ceci d'ana ina rokon ka. Don Allah ”
A hankali ya d'ura hannun sa dake cikin safa kan k'afad'ar mutumin yace
“inshaAllahu zanyi k'ok'arina. Allah zai bashi lafiya”
Bai jira amsan mutumin ba ya wuce da sauri nurses suka rufa masa baya zuwa emergency. Bayan gama shiryawa cikin Ot kit nasu, bai yarda ya tab'a patient d'in ba sai da ya yiwa Àllah kirari a zuci da Addu'a da kuma neman nasara daga gareshi, domin yasan nasarar sa daga wajen Allah take shi yasa Asad baya gajiya da nemon taimako wajen mai duka . Allah (S.W.T) yace ku rokeni na amsa muku komai girman buk'atan ku. ALLAH Yana da arzik'i da bashi da iyaka kuma bashi da k'arshe. Hak'ika Allah yana fushi da wanda yaba rokonsa.
Sun d'auki sama da awa 7 suna aiki babu hutu kan patient d'in amma Allah da ikonsa sun samu nasarar ceto rayuwar sa. Asad yana da kwazo wajen aikinsa shi yasa yake cikin top list na likitoci da duniya keji dasu, amma Asad yasan cewa nasarar sa tana zuwa ne daga wajen Allah (S.W.T) da kuma k'arfin addu'ar mahaifiyar su. Saboda hatsarine daya faru sanadiyar tseren mutuci, lokacin daya fito daga Theatre d'in tuni police sunyiwa asibitin k'awanya. Babu wanda ya hanasu aikin su aka bar su suyi investigating sanadin abunda yaja hatsarin. Malam Bature kenan a komai sai anyi masa bincike da bin ka'ida shi yasa a ko ina a duniya suke cigaba a rayuwa.
Kai tsaye daga nan masaukin sa ya wuce bai koma office ba bare ya sanar da Su'ad tafiyar sa. Ya barshi a can idan yaji shiru ya tawo kuma yana da tabbacin ma Su'ad d'in baya nan yanzu saboda dare ya yi sosai tun wajen la'asar suka shiga theatre gashi yanzu to 1 na dare. Yasan halin Su'ad zai iya jiransa ko k'arfe nawa zai kai ne amma yana fatan ya tafi gida zuwa wannan lokacin.
* . °•★|•°∵ TAURA BIYU ∵°•|☆•° . *
®𝓐𝓼𝓱𝓪𝓷𝓽𝔂 𝓵𝓸𝓿𝓮
18+
【Pg3&4】
Tun suna yara suka san halin mahaifin su na dukan mahaifiyar su. Mutum ne shi mai karancin hak'uri. Mai iko da san komai ya tafi yanda yake so. Yana so ya yi control komai na rayuwar su ita kuma mahaifiyar su tawali'u macece dake tsananin rauni bata iya ja dashi ta bashi dama ya juyata duk yanda yaga dama. Babaah ya auri Mom ne ta hanyar auren had'i. Auren su babu soyayya, aure ne na dole domin Measha Begum tana da wanda take so sai kuma Khalid ya shiga rayuwar ta lokacin daya je can Saudiya sauke farali. Sud'in yan uwan juna ne Measha an haifeta ne a Saudiya saboda can iyayen ta suke. Mahaifiyar ta asaĺin bahaushiya ce taje karatu Saudiya karshe a can tayi aurenta. Kunsan labarawa babu ruwansu mahaifiyar Measha ita ce ta jawo family nata cikin dangin mijinta har ya kasance suna kallonsu kaman y'an uwa ne, duk wani abu daya shafi family nasu to da nata family za'ayi koda kuwa rabon gado ne. Ganin ta samu dama kaman haka ta dinga jawo danginta suna aure cikin wannan family kafin kace me sun zama one big family gaba d'aya . A irin yawace-yawace da suke zuwa ne Khalid d'an wan mahaifiyar Measha yaga Measha yace yana sonta lokacin tana da shekara 17. Measha tayi tsalle ta dire ita sam bazata auri wani daga can wata duniya ba ta rabu da danginta ita tana da wanda take so. Khalid bai hak'ura ba saida ya shiga ya fita ta k'arfi ya auri Measha ya dawo da ita Nigeria nan garin Bauchi. Lokacin gaba d'aya ta rabu da dukkanin wasu tushe na rayuwar ta. Tana ganin ta rabu da farin cikinta shi yasa ta bar Khalid yake mata dukkanin abunda yaga dama tana ganin bata da wani sauran amfani a duniya.
Babban abunda kuma yake k'ara assasa wuk'ancin Khalid a kanta saboda rashin haihuwa kuma duk mata. Yaranta biyu ne kawai Suliem da Ajwaah. Suliem ita ce babba tana da shekara 21 cif a duniya. Kaman mahaifiyar su itama Suliem bata da hayaniya gata da rauni. Duk abunda mahaifin su zaiyi bata iya d'aga kai ta kalle shi bare ta kare kanta kaman Ajwaah. Saboda haka ne Ajwaah a d'aya b'angaren ta tashi kaman dutse. Babu abunda yake affecting nata . Lokacin da take yarinya a koda yaushe Babaah na dukan ta komai kankantar laifi idan tayi ko ya yi ta mata fad'a kaman zai ari baki har yasa ta kaman mai tsarguwa da komai(paranoid). Babaah yana yawan kiranta da yarinya mai sakekken baki. Saboda wannan sunan haka take tsayawa gabansa ta fad'i duk abunda yazo bakinta babu shakku babu tsoro.
Kaman k'aramin bakinta mai babbar murya ,tana jure marin mahaifin ta da zafin ransa ba kaman Suliem ba dake jin maganan sa babu question.
Kaman koda yaushe yanzu ma abunda ya faru kenan bayan hanashi marin mahaifiyar su da tayi.
“Me zakayi haka Babaah?.”
Ta sake jefa masa tambaya har zuwa lokacin tana riƙe da hannun sa. Wane irin kyau ne da wannan suna BABAAH?. Suna da zaka kira cikin tsananin soyayya, ya kamata kariya da kulawa su fito daga wajen wanda suka kira dashi. Tana kishi idan taga yanda k'awayen ta basu da magana sai na mahaifin su ya musu kaza,ya musu kaza. Mahaifin su shine mutum da suka fara fad'awa soyayyar sa a rayuwar su. Amma ga Ajwaah kaman ne tsinuwa ce . Ta tsani ta kirashi da sunan uba respectfully. Lokacin da sauran yara suke girmama mahaifinsu, ita ta tsani nata saboda dodo ne a wajenta.
Ita shedace kan ciwokan dake jikin mahaifiyar ta tun basu mallaki hankalin kansu ba suke gani ciwo jikin Mom. Wani baya warkewa zai sake jimata wani. Babban abun bak'in cikin shine yanda ya lalace wajen shaye-shaye. Mutane ana masa kallon mutum mai dattako, kamala da kuma tausayin na k'asa dashi, amma kuma a gida ba haka yake ba. Zai dawo gida da daddare a buge ya yi ta ihu yana fasa kaya daga baya kuma su dinga jiyo ihun mahaifiyar su daga d'akin ta. Sai dai su zauna suyita kuka basu da wata dabara ko abunyi. Suliem ita take k'arfin hali ta rarrasheta tanace mata mafarki take ba ihun mahaifiyar su bane. Tun tana shekara biyar ya fara dukanta saboda tace ya siyo mata alwala .Da suka fara mallakan hankalin kansu ne ya daina shigowa a buge amma su sunsan har yanzu yana shan giya kuma sunsan cewa bayan hakan har mata yana bi.
wani irin fisge hannun sa ya yi daga cikin nata ta tafi taga -taga zata faɗi tayi saurin danne k'afafuwanta. Daga Mom har Suliem saida suka saki y'ar kara sobada data fad'in sosai zataji ciwo. Yana zuba uban huci da gurnani yace
“Har kin isa zan yanke hukunci ki riƙe ni?. Matsamin daga nan kona kakkarya ki”
Ya wani nufeta da zafin rai ya hankad'ata da k'arfin gaske saida ta zube d'in dai a k'asa.
“Ajwaah . Maza ki tafi d'aki ”
Mom tayi magana desperately kaman zata shid'e bata son yawa ya'yan ta wani abu. Aikuwa Babaah ya k'ara harzuƙa ya juya da zafin rai wajen Mom, Ajwaah dake yashe a k'asa ta yi wani irin kukan kura ta miƙe ta k'ara shan gabansa tana cewa
“akwai wani abu ne cikin abincin ?ni na dafa miyar Babaah ,na saka gishirin kad'an saboda nasan kana da blood pressure. Likita ya hanaka cin gishiri da yawa Babaah ka manta?”
Tayi saurin d'aukan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 15