Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
last two weeks ba (Tym d’in da suka dawo. A Abuja), shiyasa ai na hanata dawowa nan, da kyar fa da addu’o’i tukunna abun yayi sauk’i ta dawo hakan.” Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauk’e kafin tace “nima dai gaskiya na dad’e da lura, magana ce kawai banaso.” Cikin d’an fad’a Dad yace “Ai kuwa ta gama theraphy! Dan a gaskiya, ko ance za aje, sai dai In kaita Abuja kawai muyi sati mu dawo, abu ba fad’ar Allah ba amman an maidashi kamar dole!?” Kwalla Gwaggo Asabe ta share sannan tace “Ai shima Granpa d’in naji yana cewa ‘daga wannan an gama’.”Cikin katseta Dad yace “ai tun last year yake cewa ‘daga wannan an gama daga wannan an gama’! Amman an kasa gamawa da gasken.” Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauk’e ranta duk ba dad’i da yanayin y’ar uwarta ta…. A hankali ta durk’usa ta fara serving abincin cikin mutuwar jiki. Hudan itama duk jikinta yayi sanyi dan haka tace “Allah ya bata lafiya”. A hankali Dad ya d’an juya ya kalle ta sai kuma yace “Ameen” cike da jin dad’in adduar tata. Juyawa yayi ya kalli Mommy, gani yayi har yanzu Hudan take kallo, kamar tanaso ta tuna wani abun.. Bai gama fahimtar yanayin ta ba yaga ta d’aga hannunta sannan tayi amfani da yatsar ta manuniya wajen sai da Huda! Gaba d’aya hankulansu kanta ya koma, cikin rawar murya kamar ta mai koyan magana sukaji tace “Aaa-sllam, ttanna kama ddda Aasllm d’Ina” Ba Dad ba hatta Gwaggo Asabe sai da gabanta yayi wani irin mahaukacin fad’uwa!!! Rabon da Mommy ta kira sunan Aslam, tun kafin ta fad’o daga bene! Gaba d’aya rawa jikin Dad ya d’auka, a hankali ya sa hannu ya juyo da fuskarta, ya kalli cikin idanunta sannan yace “Kina so kiga Aslam d’in naki?” Da sauri ta hau d’aga mishi kai, sai kuma hawaye, shaaarrrr suka zubo mata. “Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!” Shine abunda Dad ya dinga maimaitawa, cikin kid’ima ya mik’e ya fita yana cewa “su Gwaggwon su tsaya gashi nan zuwa, kar kowa yaje koina.” Ba ayi minti goma ba sai gashi ya turo k’ofa, rik’e da hannun Aslam Abba yana binsu a baya! Cikin zumud’i yace “Ga Aslam d’in naki” ya fad’a yana tunkarar ta, yana cewa su Abba “komai yazo k’arshe in shaa Allah, Aslam yau da kanta ta kira sunank.........” Razananniyar k’arar da ta fasa ce ta hanashi k’arasa maganar tashi, ta kuma rud’a duk wani wanda ke a cikin d’akin!! Basu ida dawowa haiyyacinsu ba ta kuma sakin wata k’arar! Wadda kusan rabin estate d’in sai da aka ji!. Cikin tsananin tashin hankali firgici kid’ima da tsoron da ya baiyyana k’arara a kwayar idanunta take nuna Aslam d’in tana kururuwa! A kid’ime Dad wanda duk ya rud’e ya sake nufota still yana rik’e da hannun Aslam wanda ya sake shiga tsananin tashin hankali da rud’ani don shi Dad ce mishi yayi “yazo Mahaifiyarsa tana nemanshi yau da kanta!” Gashi yanzu kuma ya tarar da haka!…. K’arar da ta sake saki ne ya kid’ima su dan tafi ta ko yaushe! Sai kuma ta saki jiki rigif ta fad’i sumammiya akan gadon….. Da sauri Aslam wanda idanuwanshi suka kad’a sukai jaa over, ya k’arasa inda take ya hau jijjigata yana kiranta amman bata motsi…….d’ago jajayen idanuwanshi yayi yana kallon Dad. Gaba d’aya sai Dad d’in yaji tausayin su, su duka ukun ya lullub’e shi.. Abba ne yayi k’arfin halin zuwa inda suke, yad’an kura mata ido kafin ya cewa Gwaggo Asabe “ta mik’o mishi ruwa!” A hankali yake yayyafa mata ruwan, har sun cire ran zata farka sai kuma sukaga tana motsi da idanunta alamun zata farfad’o…. A hankali Abba yad’an kalli Aslam wanda ke zaune a gefenta ya rankwafa kanta sannan ya kama hannunta gam!! Yana kallon idon da take k’ok’arin bud’ewa, alamun a kag’e yake yaga ta bud’e idanun nata! Da kyar Abba ya tattaro courage d’in da ya iya cewa Aslam “Aslam, ko zaka d’an je waje ko? Kar ta farka kuma ya zamana kai d’in zata fara gani.” Da sauri yace “No Abba, I think bata gane ni bane ba.” Sai kuma ya kalli Dad yace “Dad da kanta ai kace ta kirani ko?” Ganin da Dad yayi Aslam d’in na neman koma musu wani firgitachche ne ya sanya shi kawai cewa “Kaje wajen tukunna mu gani.” Jikinshi har wani karkarwa yake yi, sai da Dad ya sake cewa “I’m so sorry Aslam, ita tace a kiraka but ban san me ya sake faruwa ba kuma, for now just, ka d’an jira a waje ko?” A hankali ya cika hannun ya mik’e ba tare da ya yarda ya had’a ido da kowa ba ya fice, Dede nan Dad ya fashe da kuka, gaba d’aya sai hankalin su Abba ya sake tashi, saboda abune wanda basu saba gani ba! Don haka duk sai suka hau bashi hak’uri suna tausar shi, tare da adduar in shaa Allah Allah zai bata lafiya soon… A b’angaren Dad shi kuma Aslam yake ji, da ya sani da bai yi saurin kiranshiba, gaba d’aya duk sai yaji ya tsani kanshi….. Da kyar suka samu ya tsaida kukan ya k’arasa gurin Mommy wadda ta farka yanzun tanata faman dube dube a mugun tsorace alamun neman tsari take daga sake ganin Aslam d’in. Sai da komai ya lafa sannan Gwaggo Asabe suka fito ita da Hudan daga d’akin…. Ita dai Huda gaba d’aya kanta ya kulle, hakan yasa ta kasa hak’uri ta hau tambayar Gwaggo “meke faruwa? Mai ya sameta take haka? Tun yaushe? An yi mata sauka?” Dan ita Huda har ga Allah kawai ta fi jirkita akan lamarin na iska ne, tunda gashi dai ita da kanta ta tambayeshi but yana shigowa gaba d’aya ta firgice! Tayaya uwa zata dinga gudun d’anta haka?? Don ko ba a gaya mata ba ta gane itace Mahaifiyar Aslam ko dan yanayin kamar da suke yi da juna! But why him? Him alone?” Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e sannan tace “bani minti talatin, inje inyi wanka, Ina dawowa za kiji komai in shaa Allah.” Kamar yadda Gwaggo Asabe tace Sai da tayi wanka ta dawo ta zauna sannan ta fara bata labari………… Asalin sunan Mommy, Aisha ana kiranta da Humaira, k’anwarta d’ayar duniya Khadijah wadda ake kira da Asabe. Aisha da Asabe sun taso cikin yanayin k’unci na rayuwa ata dalilin babu.. Yahaya ya had’u da Aisha ne lokacin da ya kai ziyara Taraba, jalingo a wani d’an k’aramin k’auye. Ata dalilin, masallaci da makarantun addinin daya d’auki nauyin ginawa. A rafii yana zagaye ita kuma taje d’ebo ruwa suka had’u. Tunda ya kyalla ido ya ganta ya rikice, a lokacin Mahaifiyarsu ta rasu Mahaifinta kawai ya rage musu. Tun Aisha tana kauce mishi har itama ta fara kulashi sama sama. Tashi d’aya ba kwana kwana ya nuna mata yana k’aunarta kuma yana son aurenta, Bata bashi amsa ba tace “yaje ya samu Mahaifinta”. Yahaya bai yi wani jinkiriba yaje ya samu Mahaifinta da maganar sannan yayi mishi alk’awarin ‘bayan auren zai barta tayi karatu har sai tace bataso’, dan ya lura burin Mahaifin nasu kenan. D’an guntun bincike akayi akan Yahaya, a lokacin, daga nan Mahaifinta ya bashi aurenta yace masa “duk lokacin daya shirya yazo da iyayenshi a d’aura” To fa!! anan ake yinta, dan k’iri k’iri Granpa ya nuna k’iyayyar shi muraran akan Aisha da inda ta fito, acewarshi “sam ba a jin auren d’ansa bace ita d’in!!!”. Buwayar Ubangiji, rabon Aslam, da soyayyar Granpa a matarshi ne suka tabbatar da auren Yahaya da Aisha wanda aka d’aura a k’auyen Jalingo ba tare da halartar Granpa ba. Tabbas anyi rigima ba k’arama ba, kafin, da kuma bayan auren!. Zan iya cewa ban taba ganin macen da ta sha wahala a hannun suruki kamar Aisha ba! Sauk’in ta d’aya Gramma tana mugun sonta ba kad’an ba, dan tun lokacin da Yahaya yaje mata da labarin Aisha farat d’aya taji Yarinyar ta kwanta mata, ita ta dinga lallab’a Granpa har aka yi auren. To bayan auren ma haka tayi ta fama, in tak’aice miki labari hankalin Granpa bai kwanta da Aisha ba har sai da ya aurawa Yahaya ajin nashi da yake ik’irari! Wanda ranar d’aurin auren ana d’aurawa Yahaya yana hawaye kamar k’aramin Yaro, dan zan iya cewa ban tab’a ganin Mijin da yake matuk’ar so da gudun b’acin ran matarshiba kamar Yahaya ba. Sauk’i d’aya da Aisha ta samu a gurin Granpa shine haihuwar Aslam da tayi, zan iya ce miki ko y’ay’an da Granpa ya haifa a cikinshi bayayi musu kalar son da yake yiwa Aslam, ko dan ya kasance jikansa na farko ne? Allah kad’ai ya sani. Tun ranar da aka haifeshi da ya d’auke shi aka tabbatar da hakan, domin kuwa kalar farin cikin da yayi kowa sai da ya gani ya tabbatar da ‘Granpa na cikin farin ciki’!. Zakkah da sadakar da ya bayar kuwa bana jin har yau a tarihin kaf garin Kano an tab’a bada irinta. Aslam ya taso cikin gata, duk wani abu da kika sani Granpa ne yake yi mishi… A tunanin kowa, Granpa zai kasance irin kakannin nan masu shagwab’a jikokinsa ne, sai dai kuma shekarar Aslam biyar a duniya aka haifi Arshaad amman kwata kwata Granpa bai yi wani murna sosai ba ma balle aje ga maganar shagali da jan shi a jiki kamar yadda kowa ya d’auka… Tun ranar da aka haifeshi da ya d’auke shi bai k’ara d’aukar sa ba, Aslam kuwa kullum suna tare, hatta abinci tare suke ci, takanas ya nemo wani bature yake yi mishi lesson a gida, da yamma kuma wani balarabe ne yake koyar da shi addini! Sai da Granpa ya fahimci loneliness da rashin wasa da Yara agemate d’in Aslam d’in kan iya jawo mishi wani ci baya a rayuwarshi tukunna ya nemi makarantar da tafi ko wacce tsada a kaf Nigeria ya turashi a Abuja wajen mahaifinshi, tare da kwakkwaran warning a me makarantar na “kar a tab’a mishi jika ko me kuwa zaiyi! Kuma kar a bari aci zalinshi.” Duk da yana da wayo sosai dan, a lokacin shekararshi tara Arshaad hud’u Auwal kuma uku wanda shima Granpa bai wani nuna farinciki ko tunanin janshi a jiki ba tun sanda aka haifeshi. A lokacin ne kuma Yahaya ya sake tadawa Granpa maganar yana so ya tafi da Aisha Abuja , daman ya tab’a nunawa Granpa son yin hakan amman fur k’iri k’iri Granpa ya nuna mishi sai dai ya tafi da Mammy saboda itace tayi karatu bayan k’iri k’iri babu irin artabun da baayi da shi ba amman fur haka ya hana Aishan yin karatu acewarsa ‘irin su In suka yi karatu gagarar mutum suke yi!’. A lokacin ya nace akan sai dai ya tafi da Mammy ita zata iya zaman Abuja wata k’ilan ma ta d’an dinga taimaka mishi ta fannin aiki, shi kuma Yahaya yace ‘ba zai tafi da ita ba! Ko da ace Aisha bata kasance uwargidanshi ba tou tabbas da ita zai tafi’….. Mistake d’aya wanda Yahaya yayi kuma yake kan yi har yanzu shine ‘k’iri k’iri yake nuna fifici a tsakanin matanshi’ (k’iri k’iri yake nunawa kowa ba tare da shakkar wani abu ba ‘ya fi son Aisha a kan Mammy’. Da kyar a wannan lokacin dan sai dai Gramma ta shiga tsakani tukunna case ya mutu, dan daa Granpa cewa yayi sai ya tafi da Mammy dole! Shi kuma yak’i. Tou kuma da Aslam ya koma chan ma da ya sake yin maganar Aisha ta bishi, still magana d’aya irinta farko shima Granpa ya maimaita mishi ‘sai dai ya tafi da Mammy’ shi kuma yak’i, Shiyasa har yau shi kad’ai yake zaune a Abuja, yanzu haka shi da Aaima ne kawai a gidan. K’in tafiya da Mammy da Yahaya yayi ata dalilin Aisha yasa Granpa ya rufe ido ya dinga keta mata ruwan rashin mutunci kala kala, ga Adama da Ummi suma basu barta ba, Mammyn ce ma ita bata shiri da ita kuma bata fad’a da ita. A lokacin ne kuma Mahaifinta ya rasu, Allah yaso ni nayi aure don da ban san ya zan yi ba saboda shi kanshi Mahaifin namu su uku aka haifa biyun duk sun rasu, Mahaifiyar mu kuma daga gidan marayu ma aka aurota, balle inyi tunanin zuwa gidan y’an uwa! Dan a lokacin halin da Aisha take ciki a gidannan, ko mage bata isa ta d’auko tace zata rik’e ba. Aslam shekara biyu kawai ya iya yi a Abuja ya d’agawa kowa hankali Akan shi fa ‘Mahaifiyarshi yake buk’ata’ Dan ba kad’an ba suna mugun k’aunar juna, kuma yana da k’ulafucin uwa ba kad’an ba, itama kuma haka, komai Aslam, shima komai Mommy. Saboda tsabar tsananin shak’uwar dake a tsakaninsu yasa har kusan zarewa tayi lokacin da aka kaishi Abuja, Idan nace zan tsaya fasalta miki kalar soyayyar da sukewa junansu sai mu kai jibi anan.......... Ba yadda Granpa ya iya haka ya tarkatoshi ya dawo dashi kano gurin Mahaifiyarshi, akan dai ya bari a tafi da ita d’in. Sai dai kuma daya dawo d’in abun bai yi dad’i ba sam! Dan k’iri k’iri Granpa ya dinga nuna banbanci k’arara ba tare da shakkar komai ba! Abun mamaki hatta driver d’in da zai kai Aslam makaranta daban ne da nasu Arshaad. Tun abun baya damun mutane har aka fara k’us k’us, su kansu Yaran suma suka fara fahimtar waensu abubuwan….dan shi Arshaad ma a tunaninshi Aslam d’in d’an Granpa ne shiyasa a lokacin yake kiranshi da ‘Uncle Aslam’ a lokacin. Ranar 12th birthday d’in Aslam ne Granpa yayi wani abun da ya girgiza mutane! Gida guda ya d’auka ya bawa Aslam as birthday gift, a Dubai! Wanda su kansu y’ay’ansa basu ma san yana da shi ba, kar ki ce k’aramin gida fa mansion ne mai zaman kanshi! Dan ko a jikin takardar wajen d’akuna ashirin ne suka fito a cikin gidan, iya d’akuna kawai!. Mutane basu dawo daga shock ba ya cewa Yahaya “ya yiwa lawyer d’inshi magana a fara had’a takardun MT! yana so zai mallakawa Aslam su tun yanzu, in yaso shi (Yahayan)sai ya rik’e mishi idan ya kai 18 years ya bashi abunshi.” Cikin nuna k’in amincewa Dad ya d’an fara k’ok’arin fahimtar da shi akan shekarun Aslam d’in da kuma gudun abunda hakan ka iya janyowa K’asa k’asa ba tare da ya bari kowa yaji ba. Amman Granpa maimakon ya fahimceshi sai ya birkice mishi, ya fara magana yana fad’a kowa yana ji! Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba! Fad’a a ranar ba kalar wanda bai yi mishi ba a gaban taron y’an birthday… Sai da Aslam d’in yayi kamar zai yi kuka yana bashi hak’uri tukunna aka samu ya hak’ura. Jiki a mace haka Dad ya fita ya kira lawyer ya hau kora mishi bayani…… Kusan minti talatin tukunna ya dawo ya sanar mishi lawyer d’in yace zuwa nan da jibi in shaa Allah komai zai kammala. Kaf a wajen! Y’an tsirarrun mutane da Granpa ne kawai suke farin ciki amman kowa a family d’in in ka kalli fuskarshi ba zaka iya tantance me ke wakana a cikin zuciyarshi ba, sai dai tabbas tashi d’aya zaka hango damuwa binne a k’ark’ashin komai. Ana i gobe takardun zasu iso, wato washegarin birthday! Wani mummunan al’amari ya afku.” Ajiyar zuciya Gwoggwo Asabe ta sauk’e kafin ta kalli sama hanyar staircase ( parlourn k’asan da yake da matattakalr staircase d’in biyu anyi tsarin wajen ne irin me high ceiling dinnan, mutumin da yake falon sama wanda ya had’a staircase d’in dama da hagu yana iya hango komai na k’asa, shima na k’asan haka, sai kuma hanyoyin dogon corridor biyu da suke kallon juna, d’aya yana a right staircase d’ayan yana kusa da left one. Sai d’akin special guest guda biyu da yake a main parlourn sama da kuma hanyar da zata had’a ka da benen da zai kaika chan sama). Sannan ta cewa Huda “kinga chan wajen?” Tayi maganar tana kallon falon saman, kafin taci gaba da cewa “Mommy tana tsaye tana waya a jikin k’arafunanan taba d’ab lek’o k’asa…… Ganin shigowar Dad Aslam da Arshaad a tare yasa gaba d’aya hankalinta ya dawo kansu tana yi musu murmushi, Arshaad ne ya hau kawo mata k’arar Auwal tun daga k’asan yana yi yana hawa benen, dan haka ta mayar da hankalinta a kanshi tana ce masa ‘ya taho a hankali kar ya fad’i..’ bata ida rufe bakinta ba dai dai Arshaad ya kusan k’arasawa inda take kawai kamar wadda aka turo sai k’ara akaji timm!!!A take kuma ihun Aslam ya karad’e gidan gaba d’aya… Da gudu ya k’arasa inda take kwance dukda cewa ta fad’o ne bisa wasu tumtum da suke kan kafet d’in k’asan, hakan bai hana kanta zubar da jini ba! Saboda ba duk jikinta ne yayi nasarar sauk’a a kan cuision d’inba!. Da kyar Dad ya iya k’arasawa wajen ganin yadda take kallon sama tana karkarwa yasa kawai ya yanke jiki a take ya fad’i sumamme dan shi a tunaninshi ma mutuwace zata yi. Banda ihun kiran Mommy ba abunda Aslam yake yi, wanda hakan ne ya jawo hankalin mai gadi ya iso.. Ya dad’e ya na knocking yaji shiru ga Aslam yanata rad’a ihu dan ita Mommy a lokacin mai aikin ta zuwa takeyi tana tafiya, kuma lokacin har ta tafi , so ita kad’ai ce sai su Dad da suka shigo wanda yake a sume! Kuma akai rashin sa a suka tura k’ofar bayan sun shigo ta shiga lock!. Arshaad kuwa, mutuwar tsaye yayi, ya k’ame k’am! In banda kallon wajen da take a tsaye kafin ta fad’o d’in ba abunda yake yi, dan har lokacin da mai gadi ya nemo mutane aka b’alla k’ofar aka shigo, Arshaad yana nan a yanda yake, dakyar aka iya janyeshi a wajen aka kaishi wajen Mammy, dan kurma ya koma musu, sai da yayi kwana biyu baya magana….. A asibiti kuwa da kyar aka dedeta numfashin Dad, bayan awa biyar Allah ya bashi ikon farfad’owa, garau ya tashi dan haka hankalin mutane ya d’an kwanta, saboda a yanda jinin shi yayi mugun hawa ba wanda bai yi mishi zaton stroke ba. Mommy kuwa da kyar aka tsaida jinin aka kuma samu ta farfad’o bayan kwana biyu sai dai kuma scan d’in da aka yi mata na kwakwalwa ya tabbatar da cewa jini ya shiga kwakwalwarta, wanda sai anyi aiki an kwashe an kuma d’inke inda ya samu rauni. Dad bai yadda anyi aikin anan ba, waje ya fita da ita aka yi komai, sai dai kuma tun kafin ayi aikin dama sun tabbatar da cewa ba lalle inta farfad’o ta dawo kamar daa ba sai dai a hankali, wasu kan iya d’aukar 1 year wasu 10 wasu 20 wasu kuma 4eva ma basu dawo normal d’in ba! But ita case d’inta minor ne so ana saka ran ma ba lalle ta d’auki 1 year d’inba in shaa Allah komai zai dawo normal. Granpa yayi mugun sauk’owa, ko dan ganin yadda hankalin Aslam ya tashi yasa shima nashi hankalin tashi, Allah kad’ai ya sani, dan tare ma suka tafi har shi da Mammy wadda itama ta d’aga hankalinta da ganin halinda Abokiyar zaman nata take ciki, dan da Dad yak’i biya mata kud’in jirgi ma da kanta ta biya ta bisu daga baya. Tunda aka yi aikin kuwa ita take kula da Mammy sai Dad yayi da gaske take yarda taje hotel ta d’an huta, tayi bacci. Aslam, tunda aka yi wa Mommy aiki, yake azumi kulli yaumin, har ranar data farfad’o. Da farko b’oyewa yayi dan ya san za a hanashi, dan har yi yakeyi kamar yaci abincin sai daga baya aka fahimta, ba yadda ba ai ba amman yak’i ajjiyewa, ganin haka yasa Granpa yace a barshi, sanadiyyar azumin da yayi tayi a jejjere gashi da k’arancin shekaru ya sanyashi kamuwa da cutar ulcer. Kamar yadda Likitocin suka fad’a, haka Mommy ta farfad’o amman a iya rayuwarta Aslam kawai ta iya ganewa, bata magana sannan komai sai an nuna mata sai an koya mata! Abu d’aya ta sani ta gane take iya fad’i, shine ‘ASLAM’. Anji ciwon hakan sosai, amman kwarin guiwar da ake ta samu a wajen manyan Likitoci ne yad’an kwantar da hankalin Jama’a, dan suna ta bada assurance d’in ‘zata dawo normal!’ Sai dai kuma ana yin wata d’aya komai ya burkice!!! Dan Aslam d’in da ta fara fahimta sai ya dawo ya zame mata dodo!!! Da farko yana shigowa zata fara kuka!! Sai kuma ta dawo ihu!!! Daga k’arshe dai ko asibitin in Aslam ya shigo tun kafin ya k’araso inda take zata hau kururuwa tana kuka kowa ta nan ne yake gane Aslam ya iso! Wani abun mamaki shine ta warke garau ta fara magana ta gane kowa amman fa ko a labari idan aka sako Aslam tou yanzu hankalin kowa zai tashi!! Ba k’aramin kid’ima Likitocin suka yi ba dan su kansu sun zama confuse..A iyaka sanin su masu irin wannan matsalar basa haka amman duba da suka yi da shi ta fara ganewa a lokacin data farfad’o ya sanya suka yi y’an bincikensu, iya abunda tunanin su ya basu ne ya sanya su dangantata da psychiatric. Allah sarki Aslam, a lokacin sai da ta kai ga shima aka bashi gado a asibitin tsabar tashin hankalin daya shiga. Yaro ne shi a lokacin amman kasancewarshi mai kaifin basira yasa ya fahimci komai. Dan zan iya ce miki har yau ban tab’a ganin Yaro mai wayo tarin ilimi da kaifin basira irin Aslam ba, har gobe in da wani d’an ajinsu da suka yi makaranta zai zo gidannan to ba zaki tab’a ji ya kirashi da aslam ba , sai dai suce mishi ‘gifted’ Dan wani abun time d’in a makaranta ba sai an koya mishi bama yake iyawa, in kuma ya iya to ya zauna kenan! Ga wayo kamar wani d’an shekaru dayawa.” Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e sannan ta ci gaba “A lokacin hankalin kowa a tashe yake, ni kaina da nake nan da ban ganta ido da ido tana haukan ba sai da naji a jikina, abu yak’i ci yak’i cinyewa har aka shafe wata biyu a haka, ga Aslam a kwance… Tausayin shi da ya lullub’e Granpa gashi yana ganin yana neman mutuwa ne yasashi fara nemawa Aisha magani gadan gadan ba kama hannun Yaro, duk inda yaji labarin Likitan kwakwalwa nan zai tarkata su su nufi k’asar! Cikin shekara biyu zan iya ce miki sun kusa zagaye duniya dan ba k’asar da ba a je ba, in dai kinajin ta kuma sananniyace. Amman dukda haka Allah bai kawo sauk’in ba, saboda lokacin samun sauk’in bai yi ba. Daga karshe dai hak’ura suka yi suka dawo gida Nigeria. Ai ana dawowa abun yafi na daa, ba k’aramin tsorata muka yi ba dan nima nazo a lokacin…Idan Aslam baya gidan nan to k’alau amman ko bakin MT yazo yanzu zata birkice, abun tausayi In kana nan dole kayi kuka, don Aisha mahaukaciya tuburan ta koma. Shawara d’aya Granpa ya yanke shine na ‘kai Aslam boarding school’ don samun sauk’in kowa and ya kamata yaci gaba da karatu kuma ya maida hankali saboda an barshi a baya sosai… A lokacin shekarunshi sun haura 14. Da kyar Aslam d’in ya yarda, ya tafi bayan Granpa yayi mishi alkawarin ‘duk inda magani yake a duniyar nan in dai akwaishi to zai nemawa Mommy d’insa, ko nawa ne kud’in ba zai gaji da biya ba, koda kuwa zai k’arar da duk abunda ya tara ne!!!’. Haka nan aka tarkata Aslam aka kaishi boarding cikin tsananin k’unci, yana kuka muna kuka ba dan munso ba. Wani abun takaicin ko hutu Aslam bai isa ya zo ba, sai dai In kana buk’atar ganinshi kai kaje ka ganshi a inda yake, k’iri k’iri zaman estate d’innan ya gagareshi… Ganin abun na Aisha bana k’are bane yasa suka kira wani babban Likita daga k’asar waje har gida Nigeria ya dinga kula da ita, shi ne ya bada shawarar a kulle su ita da Aslam a d’aki d’aya su kad’ai, for 24 hours, to kuma abun bai yi dad’iba don shi yayi sanadiyyar da Aslam ya bar k’asar nan wanda sai yanzu ne Allah ya dawo mana da shi! Da farko an tsara akan zai d’an dinga lek’owa Hutu sai yake sauk’a gidan Abba, yadda ba zasu had’u da ita ba, har zuwa lokacin da Allah zai kawo sauk’i Amman abunda ya faru a wannan rana ya sanya Aslam yin yaji mai mugun tsayi ya tarkata komai nashi ya tafi sai dai waya, shima wani lokacin sai yake gudun d’auka!. Arshaad da su Abba suna yawan zuwa duboshi, Auwal ne ma yaje sau d’aya, amman Arshaad a shekara ma yakan je sau biyu shi da Abba..saboda shi Aslam ko hutu idan anyi na makaranta baya iya dawowa sai dai yayi

Chapter 9 of 28