suka fara had’a ido dan haka ya yafitota da hannu.
A hankali cikin nutsuwarta ta nufi dogon dining d’in mai kujeru kusan ashirin
inda taga sun nufa
kamar an tsamota a ruwa a haka ta k’arasa wajen,
Abba ne da kansa ya jaa mata kujera ta zauna, ita har kunya take ji yadda ake wani lallab’a ta ana janta a jiki musamman ma Abba yadda yi mata kamar ya goya ta yayita zagaye garin da ita.
Cikin ladabi ta shiga gaidasu suka amsa, su Aslam kuma tayi musu jimla tace “ina wuninku”
Aslam ne kawai ya amsa mata,
a hankali ta d’ago ta kalle setin da Arshaad yake taga ya wani had’e rai ya d’auke kai ko inda take bashi da niyyar kalla ma!
Nan kuwa ta k’ule, tana mamakin shi, a ranta tace “tabarmar kunya yake son nad’ewa da bori!”
A take ta d’auke kanta itama bata sake kallonshi ba, tana jin haushi da wani tuk’uk’in kishin dake sake taso mata.
Tana cikin wannan tunanin taji Daddy yace,
“Sorry dota mun barki ke kad’ai ko?
Za kini shiru kam, gashi Aaima na school, ya kamata a nema miki Abokiyar hira gaskiya!in ba haka ba bazaki ji dad’in zaman ba kwata kwata
tunda su Sudais suma islamiyyarsu da boko a had’ene sai pass 5 suke dawowa.”
Da sauri cikin tarar numfashinsa Auwal yace
“ai daman da ace Ummi tana nan ba a kaita cell ba to da zata ji dad’in zama sosai, gashi Gwoggwo Asaben ma da naga kamar sun d’an saba itama ta saka an baro inda take!
Dole ta sha zaman shiru kuwa ai!.”
Dakatawa Abba yayi da zuba mata abincin da yake yi ya rik’e serving spoon d’in kawai still yana kallon plate d’in!
Yana mamakin Auwal!!
Wato rashin kunyar tashi yau ta hauro kanshi kenan, a gabanshi haka yake zuba mishi magana…..
Yana shirin yin magana yaga Daddy ya taso ya nufi Auwal d’in a zuciye, da sauri Abba ya mik’e ya rik’e shi haka ma Aslam ya mik’e yana cewa
“Daddy dan Allah kayi hak’uri ka kyaleshi.”
Arshaad kuwa ko motsi bai yi ba dan shi kam tasa kad’ai
ma ta isheshi, ba k’aramin k’ok’ari yake ba wajen share Hudan da yake yi, gashi tunda ya zauna yake d’an satar kallonta amman yaga kamar ma ko inda yake bata son kalla!.
Cikin fushi Daddy yace
“Dan uban ka iskanci naka yau a kanmu zai k’are?
Auwal wallahi zan yi mugun sab’a maka fa!!”
Cikin katseshi Abba yace “ya isa haka Daddy ka kyaleshi kawai! Dan Allah”
Cikin rashin jin dad’i Aslam ya cewa Auwal d’in “you can leave, tunda ka ganta gashi har kun gaisa ma.”
A fusace Auwal ya kalleshi, yana shirin yin magana Daddy ya daka mishi tsawa yace
“Get out akace!! Stupid boy kawai!!!”
Fuu!! haka ya tashi ya fita kamar zai tashi sama.
Daddy da kyar ya koma wajen zaman shi ya zauna gaba d’aya guiwanshi a sace! Ya so ace a kusa da Auwal ya zauna yau da sai ya sauya mishi kamanni ya nuna mishi still da ragowar k’arfinsa shima har yanzun, dan yaga alamun Auwal d’in ya kawo k’arfin da yawa shiyasanya yakejin kanshi a sama kamar yafi kowa!.
To dai dinner d’in haka ta wakana babu dad’i,,kowa da abunda yake damun ranshi.
Sai wajen 9 Aslam da Arshaad suka yi musu sallama suka tafi, bayan an yanke yin wata sauk’ar gobe amman sai dare za a kammala,
kowa zai yi izu biyu bayan sallar farilla sai su tafi da ruwan addu’ar a shafa mata .
Suna fita Abba ma yace mata “ta d’auko hijabinta ya kaita ta duba Mama”
Murna a wajen Hudan ba a magana dan da gudu ta haye benayen, bata yi minti uku a saman ba ta sauk’o sanye da hijab har k’asa wanda ta gani a cikin kayan da aka bata.
Ya lura da yadda jikinta har karkarwa yake yi, shiyasa bai b’ata mata lokaci ba yace “suje”.
Da sassarfa ta shige motar.
Shi dai Abba kallonta kawai yake yi, tabbas Hudan da shi take kama komai da komai amma idan tana wani abun sai ya dinga ganinta kamar Maryam!!!
Wani d’an murmushi ne ya sub’uce mishi, a hankali cikin sanyin jiki ya murza key ya tada motar ya nufi gate.
Masu gadin gidanjensu na chan estate su suka d’auko suka taho dasu..
Suna Isa gate d’ayan ya ajjiye rediyonshi a kan dogon bencin da suke zaune su wajen biyar harda driver da mai wankinsu da gyaran fulawar, yaje ya bud’e musu makeken gate d’in, suka fice.
Tunda suka fita Huda ta kasa sukuni, tsabar zumud’i, gani takeyi kamar Abba baya gudu, har d’an tasowa take yi ta d’an lek’a gaban titin ta gaban glass d’in motar..
Dariya ta bashi sosai dan haka yace “Gani kike kamar bana gudu ko?”
Ya fad’a yana dariya sannan ya k’arawa motar wuta…
Itama murmurshin tayi ta koma ta zauna da kyau a mazaunin ta.
Tafiyar minti ashirin ce ta kaisu AKTH emergency, dan ma sun d’an tarar da go slow a hanya.
Tana shirin fita taji yace
“You promised Hudan, right?”
A hankali ta d’aga mishi kai, sannan tace
“Na gode sosai Abba”
sannan ta fita.
Da kyar security suka barta ta shiga bayan tayi ta nacin ce mishi Mamanta ne a kwance, Allah ya taimaketa, wanda yake gadi ne a wajen ranar da suka kawota ita da Aslam, kuma d’azu tabbas yaga Maman nata an fito da ita tana d’an zagaye, shiyasa ma ya barta ta shiga, don ya tunata tun ranar da suka zo ita tana kuka shi kuma yanata mamakin had’uwar Yarinyar, hakanan yaketa ganin hoton fuskarta a zuciyarshi amman ya san ko hauka yake ba zai ma yi tunanin tunkarar ta ba.
Dube dube ta hau yi bayan ta shiga, da kyar da sid’in goshi ta hango su…
Mama da Ummu a kan gadon a zaune suna magana da alamun mai matuk’ar mahimmanci ce sai Sakina ita kuma a gefe kan kujerar mai jinya da waya a hannunta.
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
41
Basu ga tahowarta ba, kawai suka ga an afka kan Mama da gudu an rungumeta!
Kukan da ta fashe dashi ne yasa suka gane itance, da sauri Sakina ta d’ago ta, ai
kuwa tana ganinta tayi hugging d’inta tana dariya.
Ummu itama murna kamar tayi me, Mama kuwa ba a magana.
Ummu ce ta zare Hudan daga jikin Sakina sannan ta d’an muskuta ta ajjiyeta a tsakiyar su ita da Mama.
A hankali Mama tasa hannu ta shafa fuskarta tana hawaye, da sauri itama Hudan ta goge mata hawayen tace “ki bar kuka Mama, i missed you so much, kwana biyun nan ji nayi kamar shekara wallahi”
Ta fad’a tana sakin wani kukan, sannan ta kwanta jikin Mama.
Sakina ce ta d’aka mata duka a cinya kafin tace “dalla Malama d’agata, kin wani zo sai kuka kike yiwa mutane salon ki karya mana zuciya muma mu biye ki! To Mama dai ance a daina sakata a damuwa dan haka sai kiyi k’ok’arin tashi ki ware garau ki bar wannan tab’arar.”
Da sauri ta d’ago tana goge hawayen da suka k’i tsayawa, da kyar kuwa ta tsaidasu, ta d’an harari Sakina tana murmushi
sannan juya tace “ina wuni Mama, ya jikin ki?”
Da murmushi Maman tace
“Alhamdulillah”
Sannan Huda ta juya ta gaida Ummu, wadda itama ta amsa mata cikin kulawa
sannan tace “ya mutanen gidan naku?”
A hankali Huda tayi k’asa da kanta tace
“Alhamdulillah”
Sakina ce tace “a estate d’in kike? Family house d’in nasu kamar estate ne kowa da kowa ko?”
Numfashi Hudan ta fesar tukun tace “Eh, nan aka kaini da farko, amman yanzu dani da Abba da Daddy da Ya Auwal mun tashi mun koma wani gida a baya.
Saboda Granpa yace ‘Abba sai dai ya zab’a, ko ni ko su!’.”
Cikin mutuwar jiki Sakina tace
“Shine ya zab’e ki kuka tashi?”
Da “eh” ta amsa, kafin tace “Har da d’an uwanshi ‘Daddy’ shima muka tashi, sun yi fad’a sosai jiya da Granpa d’in.”
Tana shirin sake yin magana Mama tace
“Kuka tashi as in how??
To ai yayi ta banza ne, dan ke kam kin zo kenan!!
Ya aka yi kika fito? D’azu su Kaka suke gaya mana kalar rashin kunyar da yayi musu ai!
Yanzu haka takardun shiga kotu ake had’awa!…”
Cikin rashin jin dad’i Ummu tace “Mama dan Allah ki daina biyewa su Abba Modu kina k’ara tunzurasu!
Kina ji fa bawan Allahn nan har gidansu ya bari, saboda ita!.
Ko fa anje kotun nan na fad’a miki bamu da nasara saboda
kamar yadda Abba Madun yace d’an uwanshi( Daddy) ya fad’a musu d’azu ‘ko a iya case d’in Baba aka tsaya dole a bashi Hudan!!’
Ballantana kuma idan aka duba yanayin standard of living! Shi (Abba) yana da aikin da zai iya kula da ita ke kuma.....”
Shiru Ummu tayi ta kasa k’arasawa ganin yanda Maman ta kafeta da idanuwa.
Cikin jan numfashi Maman tace “Ki k’arasa mana! Ni kuma bani da aikin yi, bani da komai ko?.”
Sai kuma tace
“Bari kiji idan su sun yi amfani da Baba to ni kuma zan yi musu amfani da Granpa!
Ai har gara Baba shi bai tab’a korar Huda a gidanshiba, Granpa fa?”
Cikin katseta Ummu tace
“Amman ai yanzu ko me Granpa yake ji dashi bai isa yayi mata ba! Saboda Abban ma ya d’auketa a kusan shi gaba d’aya!
Dan haka Kotu ba zata duba wannan bama a matsayin reliable.”
Cikin d’an fad’a Mama tace
“Wai Ummu kina nufin in barta kenan a wajenshi ko me kike son gaya min?”
Cikin kwantar da murya Ummu tace “ba nufi na kenan ba, ki fahimceni Dan Allah…
Maganar shiga kotun ne bana so saboda idan anje mune za muji kunya!
Kuma In dai Abba yaga anbashi custody d’inta gaba d’aya to fa ba lalle ya dinga barinta tana zuwa mana ba!
Mama, Hudan y’a mace ce! Makaranta ma zata shiga yanzu university wanda idan kika kwantar da hankalinki ma wata rana a wajenki za tayi Hutun ta! A hankali a hanakali zakiga zata iya dawowa wajenki gaba d’aya wata rana.
Abunda nake so dake shine yanzu ki barshi (Abba)
Zafin zuciya ne kawai yake damunshi..
Ni a nawa ganin banga amfanin a shiga kotu anata kace nace ba k’arshe kuma na san mu ne da kunya!.
Kuma Hudan aure zata yi
nan ba da dad’ewa ba, daga k’arshe fa dole ta bar gabanku gaba d’aya daga ke har shi.
Dan Allah Mama ki fahimceni ki tayani fahimtar da su Kaka.”
Cikin tsananin b’acin rai Maman tace
“Eh!! Ai shiyasa ya turo mata da Arshaad, kuma abunda basu saniba na riga na gama yanke hukunci ‘In shi kad’ai ne Namiji a duniya to Hudan ba zata auresaba!’
Wai wanne irin rainin wayo ne ma wannan Abba yake yi wanda kika kasa fahimta???
Kina ganifa yadda muka taso muka sha wahalar rayuwa tare, bai tab’a ko da lek’en ta ba, sai yanzu data zama mutum tukunna shine zai nuna ya santa? Inace daa cewa yayi ‘kar ma in fad’a mata sunanshi?’.”
Dafe kai Ummu tayi
tana shirin yin magana Huda tace
“Mama da gaske yake tun ranar anan ya fad’a miki ‘bai san da ni ba!’
Kuma dagaske yake.”
Cikin jin haushi Mama tace “k’arya yakeyi!! Na fad’a na sake maimaitawa ‘k’arya yake
yi!’
Kinji mai uba!
To nuna min shine ya haifeki kinji Huda, hakan yayi kyau!
Wato d’an kwana biyun da kika yi tare dasu har an juya miki tunani akaina ko?
Bilkisu kinga irinta ko?
Ina kuma ga in na barta ta zauna dasu gaba d’aya?
Hudan fa ita kad’ai Allah ya bani, amman kalli mugu Abba abinda yayi a cikin kwana biyu kawai!!.”
Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka.
Da sauri Hudan ta hau lallashinta sannan ta fara basu labarin yadda akayi da Mom
da su Ummi da Mammy, har cell d’in da suke ciki a yanzu….
Ummu wani sanyi da proud na Abba take ji, kuma ta sake amincewa zai kula da Huda iya iyawarshi kuma zai yi duk iyakar bakin k’ok’arin shi wajen bata kariya.
Amman wani abun mamaki furr!! Mama tak’i amincewa da zancen tace “Makirci ne suka k’ulla da shi da y’an uwan sa, aka yi komai a gaban Huda dan ta yarda dashi asa ta juya mata baya!”
Ba Ummu ba hatta Sakina da Huda da basu da shekaru sosai, sai da suka tsorata da lamarin Mama, ga gaskiya nan ana nuna mata amman ta kafe! Tak’i ji taki gani..
Ummu har ce mata tayi “zata je suyi maganar fahimta ita da Abba, ba sai anje kotu ba! Kawai Huda za ta dinga sati sati a hannunsu, har Allah ya kawo mata miji tayi aure
Ma’aana taje Gandu tayi sati d’aya sai ta koma Nasarawa tayi sati daganan ta sake dawowa Gandu….haka dai.”
Amman nan ma furr!! Mama nace akan ‘attakafur!! Ita sai dai a bata Huda gaba d’aya!’
K’arshema cewa tayi “idan Ummun ba zata tsaya mata ba ta daina yi mata kwana kwana kawai ta fito fili ta fad’a!
Ta samu ta fara neman wani lawyer d’in, tun kafin lokaci ya k’ure mata.”
Da jin hakan ne yasa Ummu taja bakinta tayi shiru bata sake cewa komai ba!
Daganan shiru ya wanzu a wajen….
Hudan ce ta kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa
“Ya Jalila ma tana gidan”
Da sauri duk suka zuba mata idanu…
Cikin In Ina tace
“Ciki ne ma da ita”
A firgice Sakina ta rafka salati haka ma Ummu
Mama kuwa daman ta riga ta Sani, amman abunda ya bata mamaki shine ‘me take yi a gidan su Abba’.
Ummu ce tace
“Me take yi kuma a gidan?”
Shiruuu, Hudan tayi, bata san daliliba amman sai ta kasa ce musu cikin na Arshaad ne
kawai tace “itama bata sani ba”
Tana goge wani hawaye mai zafi daya zubo mata ba tare data bari sun gani ba, kafin
ta k’ara da cewa “A gidansu Ya Auwal dai ta ganta, kuma yanzu da suka tashi, Ya Auwal d’in ya kaita wajen Gwaggo Asabe.”
Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e kafin tace
“Sadiya ta cuci Yarinyar nan har abada wallahi…”
Cikin sanyin murya Huda tace
“Ummu nace mata ta kwantar da hankalinta zan nema mata mafita, ya za ayi yanzu?
Dan wallahi naji tausayinta..”
Da sauri Mama tace
“Wacce mafitar za ki nema mata??
Meye naki a cikin lamarin ciki, iye?”
Ta k’arashe maganar cikin fad’a! Sannan taci gaba
“Kin san Allah Huda babu ruwan ki a cikin lamarin nan, mafita Sadiya ta nema mata, wannan maganar tafi k’arfin ki kar inji kar in gani! Ballanta a tsunduma ki a cikin lamarin a yi miki bak’in fenti ke daman mai bak’in jini a idonsu…”
Hawayen Hudan ne ya k’aru, ta sa hannu ta shiga gogewa..
Ita kad’ai ta san kalar tuk’uk’in da zuciyarta take yi mata, kawai tunowa da lamarin cikin da tayi
And
Tana mamakin masifar da Maman nata ta koya.”
Ummu ce tace mata “kin dai ji ko Huda? Ki bita da addua kawai, Sadiya ta fiki sanin kalar taimakon da zata yi mata, ba ruwan ki!
Dan yanzu za a goga miki fenti taki sai tafi ta kowa tsami!”
Cikin katseta Mama tace
“Ai gashi irin tarbiyyar Abban da kuke magana akai!! Yanzu kamar Hudan har tana shiga lamarin ciki tana alk’awarin zata nemawa mutum mafita sai kace wata nurse??!”
Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e sannan tace
“Ki kwantar da hankalinki, ai taji abunda muka ce mata ko Huda?
Besides ai basa tare ma yanzu, naji tace tana wajen Gwaggo Asabe ko?
Wacece Gwaggo Asaben?”
Nan Hudan tace “k’anwar Mommy ce” Sannan ta basu labarin halin da Mommyn take ciki.
Kaf a labaran da Huda tazo da su na Mommy ne kawai ya girgiza Mama. Ta ji ba dad’i sosai, gashi ta san matar sun d’an saba dan haka tayi ta jimami…ga shima Aslam wanda dukda kalar rashin kirkin da yayi mata ranar amman har yanzu tana jinsa har cikin ranta…..
Kamar ance ta kalli wayar Sakina da message ya shigo yanzu ta d’anyi haske!
Wayar na nan akan cinyarta don haka ta samu damar ganin time…
Mamakine ya kamata dan har ta shafe wajen awa d’aya da minti ashirin a wajen.
Cikin k’arfin hali ta d’an kwanta a jikin Maman, bayan kamar minti uku ta mik’e ta cewa Sakina “tazk ta rakata taje tayi fitsari.”
Kamar kuwa Mama ta sani dan tashi d’aya ta fara k’ok’arin mik’ewa tace “bari ta rakata da kanta!”
Da kyar Ummu ta lallab’ata, ta hak’ura ta koma ta zauna.
Daganan Sakina ta gyara mayafinta suka rik’e hannu suka yi gaba….
Har suka fita daga wajen tana d’an juyowa tana satar kallon inda su Maman suke…..tun kafin suje waje ta fashe da kuka mara sauti suna fita harabar asibitin ta sakeshi mai sauti ya fito, da sauri Sakina wadda tun d’azu taketa ce mata “bafa nan bane hanyar toilet d’in” amman tayi mata shiru sai janta kawai take yi
tace
“Lafiya Huda mai ya faru kuma?”
Waige waige ta hau yi, chaan ta hango motar Abba da suka
yi parking d’azu! Daman bata yi tunanin zai tafi ba.
Bata b’oyewa Sakina ba, nan ta fad’a mata komai akan yadda suka shirya da Abban nata.
D’an k’ura mata ido Sakina tayi….Chaan! Tace
“Yanzu sai yaushe kuma?
Anyways kinga dai 30 minutes ya baki yanzu kuwa kin kusan awa d’aya ma. Ki kunna wayarki kawai
za muyi magana.
Mai yasa kika kashe ko kwacewa akayi?”
A hankali tace
“Charger ne babu.
Amman d’azu na siya a online an kawo har na ma jona Ina so ya cika ne kafin In kunna.”
“Ok za muyi waya muje in rakaki”
Hannun ta Hudan ta ruk’o kafin tace “Sakina kina ganin Mama ba zata ji haushina ba?
Me za kice mata idan kin koma ciki?”
Ajiyar zuciya Sakina ta sauk’e sannan tace
“Haushin ki kam za taji, ba d’aya bama kuwa! Kuma yau Allah yasa ta bar Ummu ta rintsa dan ni ba anan zan kwana ba Baba nake jira yazo ya d’auke ni sai gobe tukun zan dawo. Amman na san yau rikici zata yi tayi, Mama ta zama mai fad’a sosai!.
Maganar da zan fad’a mata kuwa, gaskiya ce zan fad’a kawai ba wani abun ba.”
Rau rau Huda tayi da idanu.
A hankali Sakina tayi murmushi tace
“Kije ku tafi, tabbas Mama za taji ba dad’i amman kije kawai kin ji?”
A hankali ta share hawayenta ta matso ta rungume Sakina,
dai dai nan Baban su Sakina shima ya k’araso wajen.
Abba ma haka wanda tun fitowarta ya gansu ganin da yayi kamar bata ganshiba ne yasa ya fito ya k’araso inda suke tsaye.
Kusan a tare suka k’araso wajen, Baban su Sakina yana ganinshi ya gane shi ne baban Hudan dan haka yayi saurin mik’a masa hannu
(wani aiki ya tab’a had’ashi da Abban kuma ya samu alkhairi sosai!
Har gidansa ma sukaje suka yi mishi godiya. Yanata yaba alkhairin mutumin, shiyasa
da Arshaad ya rok’esa akan ‘ya rufa mishi asiri kar ya fad’awa kowa daga family d’in daya fito yet saboda gudun matsala’
Shi kuma ya yarda yayi shiru bai fad’a d’in ba
Don yaga sun san mutunci
kuma shi kanshi yana so Hudan ta had’u da Mahaifinta a samu a dedeta komai!
Amma Arshaad yace
baya nan yanzu ya tafi wani aiki kuma akwai issue har yanzu a k’asa, but a hankali a hankali za suyi settling in shaa Allah, komai ya dawo normal .
Shi kanshi a lokacin ya yarda da hakan saboda ya san wani part na case d’in su Madu da family d’in Abban…
To kuma suna k’ok’arin ganin komai ya koma normal d’in
tukun
a samu a daidai sai shi kuma
Aslam yazo yayi musu mai gaba d’aya!)....
Shima Abban kallon sani yake yi masa, sai da Baban su Sakinan ya tuna mishi ‘ya tab’a basu wani contract kwanakin baya’ Tukunna Abba ya tuna shi, Hudan kuma ta gabatar masa dashi a matsayin Baban su Sakina mijin anty d’inta.
Sake gaisawa suka yi sakina itama ta gaidashi cikin girmamawa… kallon Abban take yi tana sake maimaitawa!
Tanaji Ummu tana cewa ‘Baba kishi yake da Abba shiyasa yake yin wasu abubuwan’ tabbas kam dole Baba yayi kishi da wannan mutumin!
Dukda cewa shima Baban ba mummuna bane kuma fari ne shima amman ko makaho In ya shafa yaji ya san babu had’i kwata kwata tsakanin Abba da Baba, Abba ya tsere mishi a komai da komai..
Gashi wani abun mamaki ba zaka tab’a cewa ma ya haifi Hudan ba dan kamar wani d’an 33 haka yake, jikinsa san bai
nuna tsufa ba kamar dai Mama,
Ita kam tunda take a rayuwarta bata tab’a ganin perfect match irin na Abba da Mama ba……
Da kulawa ya amsa gaisuwar tata yana tambayarta “ya school” a hankali tace “muna jiran results ne har yanzu”.
Sun d’an tab’a hira da Baban Sakina daga nan sukayi exchanging numbers suka yiwa juna sallama.
Abba ya lura da yadda Huda ta shak’u sosai da Sakina dan
har suka isa mota tana waigawa tana waving d’inta kamar wata Yarinya
itama Sakinan haka dan ita kam har sai da taga fitarsu tukunna suka shige ciki don su d’auko kayanta.
Tun kafin Mama ta gama gaisawa da Babansu Sakinan ta san yanda tayi ta zulle ta gudu, daman itama k’arfin haline kawai zata yi wajen yiwa Maman bayani
kuma yanzu ga mafita Allah ya kawo mata.
Tunda suka kama hanya Hudan take tunanin abunda tayi sam bata kyauta ba! But ya kamata shima Mahaifinta ta d’an kwantar mishi da hankali tunda ga halin da yake ciki da family d’inshi….
Ya lura da ita sosai, don k’arshema har da y’ar kwalla yaga tana gogewa. Shiru yayi mata kawai…..har sun kama hanyar gida sai kuma ya juya yayi hanyar dominos.
Suna zuwa yayi parking ya shiga bai dad’e ba ya fito da Ledoji nik’i nik’i
dangin su ice cream da milk shake da pizza…..
A baya ya saka ya zagayo ya zauna yace “gashi ita da su Shuraim, in kuma sun yi bacci by the time da suka gidan sai ta sa musu nasu a fridge.”
Godiya tayi masa, daga nan
suka kama hanya, yana ta d’an
janta da hira kad’an kad’an, yace if “she’s bored gobe ta shirya Arshaad ya kaisu munjibir park”
Kamat zata ce masa a’a sai kuma tace “to” kawai.
A haka suka karasa gida.
Shi ya taya ta d’aukar kayan sai da suka isa chan sama tukunna ya ajjiye a parlour yayi hanyar d’akin shi bayan ya rarrage fitulu yana ce mata “ta duba su ta shafa musu addua idan sun yi baccin, itama tayi kafin ta kwanta.”
Kamar yanda tayi tunani, ko da taje su Shuraim d’in har sun yi bacci dan haka tasa a fridge d’in sama dan ita tsoro take ji ba zata iya sauk’a k’asa ba, a
Iyaka saman ma itakam duk a tsorace take!.
Tana jera kayan tana mamakin uban yawansu….
Ice cream d’aya ta Iya d’auka, dan gaba d’aya bata da laka a jikinta tunanin Mama take tayi..duk jikinta a sanyaye yake, ta san tayi laifi babba a Mama, bata san ma ta ya zata sake facing d’inta ba!
Cokali biyu kawai ta iya yiwa ice cream d’in duk dad’in shi amman sai ta kasa sha, da kyar ma ta iya had’iye biyun a mak’oshinta
don haka ta rufe ta saka a d’an mitsitsin fridge d’in gefen gadonta ta mik’e tayi wanka.
Tana fitowa ta rarumo waya ta danna kiran Sakina
Ita kuwa Sakina tunda suka fita tana zama a mota ta kashe wayarta ma gaba d’aya
dan wallahi ta gaji dayawa tana buk’atar isheshen bacci, in yaso duk fad’an da za ayi mata ayishi gobe!.
Shiyasa Hudan tayita kiranta amma taji a kashe…. daga k’arshe ta hak’ura tayi cilli da wayar, ta kwanta, gaba d’aya ranta ba dad’i, bata san ya Mama zata kwana ba yau! Kuka ta fara yi, ta dad’e tanayi kuma daga baya ta share hawayenta….
Wayarta taji tana k’ara dan haka ta lallab’a ta d’auka, gabanta ne yayi wani irin mugun fad’uwa ganin sunan Ummu, sai da wayar ta kusan tsinkewa tukunna ta iya d’auka
tana karawa a kunnenta Ummu tace “kina gida ne?”
“Eh” ta bata amsa.
“Waye ya mayar da ke?”
“Abba” ta sake bata amsa.
“Daman tare kuka zo?”
“Eh!”
“Tam! Sai da safe.”
Hudan tana shirin yin magana taji kit!! A yanke kiran.
A daren ta kira layin Ummu yafi sau ashirin amman bata d’aga ba!
K’arshema dena shiga tayi.
Gaba d’aya hankalinta sai ya sake tashi, sai wajajen 2 tukunna ta samu tayi d’an baccin ta rabi da rabi,
kiran sallar farko ta farka.
Tashi tayi tayi Nafila ta jira aka kira tayi sallar Asubah…
Bata kwantaba sai da tayi azkar d’inta ta fara karatu.
Sai bayan gari ya d’anyi haske tukunnna ta d’an iya yin bacci shima nisanshi iya awa d’aya!
Wayar Sakina ta sake gwadawa tana tashi but still a kashe.
Tana zaune taji kamar ana knocking chan waje k’ofar
falo, mik’ewa tayi ta fita taje ta bud’e…
Tana bud’ewa taga
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 28