zata dawo.
Taho muje, ko kayana ba zan d’auka ba wallahi Auwal yaa zo ya d’auka anijima, k’afata
k’afar ki, mu tafi.
Ashe alkhairin ganin ki ne yasa naji ina kwad’ayin lek’owa nan
dan tunda naji Gwaggwo Asabe tace ana biki anan na kasa sukuni.”
Lumshe ido kawai Mom tayi,
sai da ta tabbatar da zuciyar ta ta dedeta tukunna ta bud’e idanuwanta da sukai ja ta zubasu akan Jalila wadda tayi mata k’urr! da ido.
“Muje”
Shine kawai abunda Mom d’in tace, ba tare data sake bi ta kanta ba tayi gaba
Jalilan ta bita a baaya
daman neman wanda zata k’untatawa take yi ta san watak’il ta samu tashin hankalin da take ciki ya d’an ragu!
Duk da Umma ta bata assurance d’in ‘ba matsala an tabbatar mata da babu aure tsakanin Huda da Arshaad
dan haka kar ta damu da wani bikin da suke ta yi’
Amman ta kasa nutsuwa kuma zuciyarta ta k’i ta daina tafarfasa……
Sannan zata fita daga estate d’in nan, da Auwal ya maida mata shi kamar kurkuku.
Murmushi tayi aranta tace
“Zan jefi tsintsu biyu da dutse d’aya!”
Driver ne ya jasu su duk biyun a baya, kamar yadda tayi zato kuwa masu gadin da kyar suka bari aka fita da ita....
Sai da Mom ta nuna mata d’akin da zata zauna a sama, daganan ta wuce nata d’akin.
Sai da Ummi ta tabbatar kowa ya watse tukun tabi bayan Mammy Sisters d’inta( Mammyn) kuwa ko sallama basu yi mata ba suka wuce suka rabu da ita.
A d’aki ta sameta sai faman safa da marwa take yi ta hana zuciyarta sukuni sam!.
Ta ganta sarai taga shigowarta
amman sai tayi banza da ita taci gaba da kai kawon da yake yi.
A hankali Ummi ta nemi waje ta zauna tukunna tace
Mammy
Da sauri Mammy tace
“Zainab tashi ki fita!
In dai shawararki kika san zaki sake bani
to
tashi ki fita tun kafin raina ya b’aci!”.
Murmushi Ummin tayi sannan ta fara magana
“Dama ai in dai kinga mutun yana farin ciki idan ana bashi shawara in yayi ba daidai ba to ki tabbata ba gaskiya ake fad’a mishi ba!
Nazo in baki shawara ne Mammy kuma zan yi matuk’ar farin ciki idan naga kina jin haushin shawarar tawa dan na san gaskiya ce nake fad’a.
Bari kiji in fad’a miki abunda na San Baki sani ba..
idanuwanki ne suka kulle ba kya ganin komai ba kya ganin kowa sai k’iyayyar Huda da
Aisha wadda kika gani abkan k’afafuwanta!”
Da sauri Mammyn ta kalleta kafin tace
“Magana zaki fad’amin?
Me kike nufi?
Use your words!
Ta fad’i hakan tana me k’arasowa daff da ita.
Mik’ewa Ummin itama tayi
sannan tace
“Ba zan yi using words d’ina ba Mammy dan na san kin san me nake nufi!
So yanzu ba lokacin tashin tashina bane ba, yanzun lokaci ne wanda ya kamata ace kin farka idanuwanki sun bud’e sannan kin kalli rayuwa da idon gaskiya da basira.
Bari in baki wani d’an misali , watak’il ki gane abunda kowa yake son fahimtar da ke
wanda kika kasa nutsuwa ki fahimta..
For instance ace,
ki samu kare ki kulle shi yayi kwanaki baki bashi abinci ba!
Rana d’aya ki samu dogon lungu, a k’arshen lungun ki ajiiye nama da k’asusuwa da ruwan sha
sannan ki kawo zarto k’usoshi da wuk’a ki ajjiye a daidai ta saman lungun a saman wannan naman
sannan ki d’ana mishi tarkon da in dai yabi ta kai ya taka to wannan wuk’a da zarton zasu sauk’o su chakeshi su kasheshi murus har lahira ba tare da ya ci wannan naman ba.”
Ajiyar zuciya Ummi ta sauk’e kafin tace
“Ki gaya min in akwai mahaluk’in da ya isa ya hana wannan karen cin naman nan?
Ko kuwa shin wannan karen zai iya hankalta da wannan tarkon da yake a gaban naman?
Amsar anan itace
‘a’a’, sai dai In d’auke shi za ayi ta k’arfin tsiya a sama mishi sabon nama a bashi yaci.
Sannan ne za a samu sauk’i.
Wannan karen ba kowa bace face, ke.
Naman nan kuwa, Hudan ce da Aisha waenda k’iyayyarsu haushi da takaicinsu ya sanya kika kasa ganin komai da kowa hatta tarkon dake gabansu wanda in dai kika taka to tabbas wuka zata fad’o kanki ta kashe ki har lahira ba tare da kin tab’a su ba!
Waennan tarkon da wuka’ak’e ba komai bane Mammy face Dad da Arshaad da auren ki da mutuncinki da k’imarki, da kike k’ok’arin lalatawa
ki kashe rayuwarki jin dad’in ki kwanciyar hankalinki da farincikinki da aurenki,
duk akan rashin hak’uri.
Second option kuma da na baki na ‘sai dai a d’auke karen a bashi sabon nama’
Shine wanda ni, y’an uwanki da Aaima muke ta k’ok’arin fahimtar da ke!.
Idan kika yi hak’uri kika sawa kanki da zuciyarki salama, zaki samu peace of mind
za ki samu farin ciki
amman fa sai kin yi tunani irin na mutane bawai irin na karnuka da basa ji basa gani idan suna jin yunwa ba.
Ki daure ki kwantar da hankalinki, wata rana sai labari. Kar kije maybe akwai babban rabo a tsakanin Hudan da Arshaad ki kashe kanki ba tare da kin hankalta ba...”
“Attakhbir!
Allahu akhbar!
Mai k’aramar kwakwalwa da zuciya.
Naji na gode reformed Zainab!
Na lura tunda kika ji azabar cell shikenan zuciyar ta mutu.
To bari kiji in gaya miki
Wallahi! Kin ji dai na rantse gara rabon dake tsakaninsu ya kashe ni! Akan in zauna a gaban idona a d’aura musu aure inaji ina gani
dan na tabbatar bak’in ciki ne zai k’arasa ni
muddin Arshaad ya auri wannan Yarinyar!.
Kinji dai kankat! Kenan, ko?.
Oya jeki na gode
duk ranar da fargabar cell ta bar jikinki, kya iya zuwa mu yi magana.”
Cewar Mammy.
Bak’in ciki ne ya hana Ummi sake ce mata komai,
dan haka kawai ta juya ta fita
cike da takaici da tsananin mamakin Mammy.
Da harara Mammyn ta rakata, sannan tayi tsaki ta koma kan gadonta ta zauna.
Ummi na fita suka had’u da Daddy da alama d’akin shi zai yi
amman yana ganinta yace “ta zo suje ya kaita kawai ya gama tukun ya huta.”
Ba ta san taya zata fuskanci Abba ba, bata san taya zata fara bashi hak’uri ba!
Hakan yasa tunda taje ta yiwa su Granpa sallama suka d’au hanya zuciyarta take ta faman tsitstsinkewa.....
Ba kowa a parlourn dan su Shuraim tun safe suka tafi gandun albasa.
Basu dad’e da gama waya da Dad ba yace mishi yana gida
don haka suna zama ya kirashi yace “ya sauk’o gashi ya kawo Ummi”
Wallahi Abba har ga Allah har cikin zuciyarshi shi mantawa ma yake yi da wata Ummi.
Mike’wa yayi kawai ya je jikin drawer inda yake ajjiye important documents d’inshi ya d’auko takardar da ya dad’e ajjiye da ita, ya fice yayi k’asa.
Da kyar ya iya daurewa suka yi cikakkiyar gaisuwa shi da Dad.
Ummi na shirin gaidashi da fara sake bashi hak’uri har da
d’am zamowarta daga kan kujera taji yace
“Ke! Zo ki karb’a nan”
Ganin ya mik’a mata farar takarda ya sanya gabanta ya hau dukan uku uku!
Ba ita ba hatta Dad sai da ya shiga rud’ani.
Bata gama gigicewa ba sai da ya daka mata wata uwar tsawa!
A take jikinta ya d’au rawa.
Gudun kar ta b’ata mishi rai ya sa ta mik’e da kyar ta k’arasa inda yake tasa hannu biyu ta karb’a….
Dad ne yace
“Abba meye wannan ka bata?”
Yana mai tsareshi da idanu.
Cikin nuna halin ko in kula yace
“Ta karanta za ta gani”
Da kyar Ummi ta iya bud’e takardar, jikinta na karkarwa tana adduar Allah yasa ba abunda take tunani bane…
Zuwa yanzu ran Dad ya soma b’aci da attitude d’in Abba
dan haka cikin b’acin rai ya yunk’uro da niyyyar fara zazzzage mishi ta cikinshi
dan yaga alamun da renin wayo ya sauk’o k’asan
shi kuwa yadda Mammy ta gama chaza mishi kai wallahi ba Abba ba ko waye ya shigo gonarshi yau sai ya ci ubansa!
Ya bud’e baki kenan, yaji k’arar fad’uwa! Da sauri ya maida hankalinshi a direction d’in Ummi, ya ganta zube a k’asa.
Dan haka ya mik’e a mugun firgice ransa na k’arasa dagulewa.
Abba kuwa ko gezau bai yi ba
Yana nan zaune a yanda yake ko motsi ma ba shi da niyyar yi.
A gigice Dad ya mik’e cikin sassarfa ya k’arasa inda suke yana cewa
“Subahanallah, Abba suma tayi ko me?
Duba ta mana, tashi mana, ya kamar baka ga abunda ya faru ba ne?”
Ya fad’i hakan yana mai durk’usawa a inda Ummin take.
Cikin nuna halin ko In kula ya mik’e tsaye ya karkad’e farar jallabiyar dake jikinshi, kafin yace
“At least na sakata tayi mai dalili ai yanzu ba fake ba.”
Yana gama fad’in haka ya juya zai hau sama..
Da sauri Dad ya mik’e
ya sa hannu ya juyo da shi, bai yi wata wata ba ya d’auke shi da wani mahaukacin mari
dan tun lokacin daya durk’usa akan Ummi idanuwanshi suka sauk’a kan takardar saki biyun da Abba yayi mata.
Da sauri Auwal wanda ya shigo yanzun ya k’araso inda suke yana cewa
“Subahanallah, mai ya faru?
Dad wace..?”
Maganarsa ce ta katse sakamakon Idanunshi da suka kai kan fuskar Ummi,
da sauri ya durk’usa ya hau tattab’ata yana tambayar mai ya same ta?.
Cikin b’acin rai Dad yace
“Maida ita yanzunnan ko ka fuskanci fushina Yakubu!”
Da mamaki Abba yake kallonshi jin yana yin yanda Dad d’in yayi mishi magana da kuma yanda ya kira sunanshi haka!
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace
“I can’t Dad, I’m really sorry
Wallahi baz..”
Wani marin ya kuma sakar mishi kafin yace
“Kar ma ka rantse!
Dan ko ka rantse sai kayi azumi saboda Ummi sai ta koma d’akinta a yau wallahi!
Kaji dai na rantse.”
Bai ankara ba yaji hawaye yana zuba ta idanunshi..
Cikin kuka yace
“Dad bana son ganin fuskar matar nan, tayi ruining komai nawa saboda selfish reason d’inta!
Ba zan b’oye maka ba
wallahi Ina having second thoughts akan auren Hudan da Arshaad saboda
kwata kwata bana son yin nesa da y’ata
because i just knew her,
all because of ummi.
Ka san irin azabar da Hudan ta sha a hannun Usman kuwa?
All because of Ummi.
Ka san yadda nake jin Maryam a cikin zuciyata? Amma ba yadda na iya dole haka inaji Ina gani ta auri wani ta rayu da shi for almost 20 years!!
All because of ummi
Komai fa Yaya ita ce sila!
Itace silar ciwon zuciyana!
Itace silar bak’in cikina!
Itace silar lalacewar soyayya ta!
Haba haba dan Allah..
sannan yanzu kace In maida ita?
Gaskiya kayi hak’uri Yaya, ban tab’a maka gardama ba amman kam yau zan yi maka!.
Wallahi ko sunanta ba na son ji
kwata kwata..”
Ya k’arashe maganar cikin d’acin zuciya sannan yana gama fad’in hakan ya wuce sama ya barsu shi da Auwal wanda yake ta yayyafa wa Ummin ruwa yana son yaga ta farka.
Da kyar Dad ya iya juyowa ya kalli Auwal d’in, sannan yace
“Kamata mu kaita asibiti,
Allah yasa ba wani babban abun bane ya sameta......”
Gandun albasa
(2:30 pm)
A tsakar gidan Madu,
akayi decoration na traditional kaulu!
Wajen yayi masifar yin kyau.
Taken wak’e wak’en Shuwa Arab ne ke tashi in a very low tone.
Su Sudais da wasu Yaran sai y’an tsofaffi tsilla tsilla ne a zazzaune a kan kujerun da aka k’awata tsakar gidan da su.
Gaba d’aya y’an mata da manyan matan suna ciki,
wasu suna had’a takeaway da souvenirs wasu kuma suna shiryawa dayake mostly family ne sai na jiki sosai suka zo
dan Mama ba wani taro tayi ba
Ita dama ba wani sanin jama a ma tayi sosai ba, sai y’an unguwa da suke ta zirya tun safe waenda rabinsu duk munafurci ne yake kawosu
dan an san yau za a kawo lefe.
Umma bata da lafiya tana fama da hawan jini amman tun sassafe suka zo ita da Baaba Laraba da yayarta Hansai,
kuma wani abun mamaki tunda tazo d’in tak’i kula Mama dan wani mugun zafinta take ji, sun dai gaisa da Shuwa da Ummu
Ita kuma Mama sun gaisa da Hansai da Baabaa Laraba
amman Umma kam tama k’i bari su had’u dan tana hango ta zata kauce hanya
ko ta fad’a d’aki ta shige band’aki. Da Mama ta fahimci hakan kawai sai ta tattarata ta watsar ta shiga sabgar gabanta dan ita mamaki ma Sadiyar take bata duk tabi da d’aurawa kanta wahala
gaba d’aya a takure ma kamar ta ganta ga kuma rashin lafiyar Bp da take ta fama.
Sai da Anty Zainab ta zo tukunna ta d’an samu ta ware.
Itama Anty Zainab d’in da kyar ta iya daurewa suka gaisa da Maman wadda tayi wani irin fresh! Sannan idan ka kalleta ba zaka tab’a cewa sa’ar su bace ita da Sadiyar
Sai dai kace Antys d’inta ne
dan ba za ma ka ajjiyesu a matsayin yayunta ba!
Musammam ma Sadiya wadda ta zama kamar wata mahaukaciya kwana biyun nan!
Tun lokacin da taji labarin maganar auren Huda
har yau bata san inda nutsuwarta take ba………
Mama na gama gaisawa da Anty Zainab ta juya ta wuce abunta.
Anty Zainab kuma ta nufi wajen Umma! Nan kuwa
suka hau hassada da zagin Mama har da suna cewa wai “bazawari take nema shiyasa taci wannan uwar kwalliyar”.
Laffaya Maman ta nad’a itada Ummu, kalar laffayar ja sai blue d’in flowers,
sun yi kyau sosai dan
har d’an light makeup sai da Sakina ta tirsasa su suka tsaya aka yi musu.
Itama Sakina laffayar ce a jikinta, amma bata nad’a ta har ka ba, instead sai tayi d’aurin Zahra Buhari da mandil a kan nata shi kuma mayafin layyafar ta nad’a a kafad’ar ta.
Amarya kuwa ta sha traditional kaya abunta!
Hatta hair style d’inta ma irin nasu aka yi mata,
daga sama ta nad’a wata had’add’iyar blue black d’in laffaya, aka yafa mata mandil akai.
Tun daga kan sark’ok’in k’afarta har na wuya da y’an kunneta da wanda ta sa a kanta na sisin gold duk na asalin gold ne!
Wanda Madu ya bata kyauta jiya da daddare, yace “tun na mahaifiyar mahaifinsa ne!
Maryam yaso bawa Allah bai yi ba.
Ashe rabon ta ne..”
D’akin isu isu ne ita da k’awaye ta, anata d’aukar hotuna
amman kallo d’aya za kayi mata ka san hankalinta baya ma gidan gaba d’aya!
Tun da gari ya waye take jin fad’uwar gaba, gashi yanzu kuma sai kiran Arshaad take yi baya d’auka…..
Shuwa ce ta shigo
ita da Baabaa Talatu sanye cikin wata rantsatsiyar milk laffaya sun yi anko su biyu suma abun su ita da Baabaa Talatun.
Basu dad’e ba wasu mata suka shigo su biyu, daga nan suka umarci Hudan da ‘ta mike
a fita da ita’
Aranta ji take kamar ta tambayesu ‘Ya arshaad ne ya zo? Sai kuma taga rashin kunya da zak’ewarta
Kuma ta tuna jiya Sakina tace mata
‘Ta bar nuna mishi ta damu sosai fa, idan ba haka ba tabar ganin wai yana sonta
Wallahi wahala zata sha....’.
Lumshe idanuwanta tayi
ta dedeta nusuwarta
sannan ta bawa Sakina wayarta ta mik’e, ta jaa
mandil d’inta ta rufe kaf fuskarta, su kuma
suka tik’eta sukayi waje.
Suma su Sakina suka take musu baya.
Hudan, so take ta yakice tunanin Arshaad a kanta amman ta kasa!
K’arshema bigewa tayi da adduar Allah yasa tana fita ta ganshi amman yanayin yanda taji an zaunar da ita a doguwar kujerar da aka k’awata domin ita da shi ne yasanya ta fahimci bai zo d’inba.
Ummu ce ta fito ta bud’e taro da addua sannan ta fara gabatar da al’ada a Huda,
A matsayin uwa.
Mama suna parlourn Madu, tun lokacin da Mommy da Aslam suka zo suka buk’aci ganinta har yanzu bata samu damar fitowa ba.
Wata distant relative d’in Shuwa wadda zata d’an girmi Shuwan kad’an ce
ta k’arasa wajen sannan
cewa Ummu “Ina uwar Angon?
Ta zo ta zauna a kusa da ke
yadda kina gamawa zata karb’a.
Sannan ba ayi welcomin Ango ba kuma ba aga shigowarsu ba besides ai dole sai yananan ma tukunna za ayi komai.
Na ga bai riga yazo ba
amman kin yi wuff kin fara abu haka bayan kuma akwai abubuwa da yawa before wannan.”
Karaf! A kunnen umma. Daman neman abun yi suke yi ita da Anty Zainab shiyasa
suka zo suka zauna a k’asa gefen kujerar Amarya. Da sauri sannan da d’an k’arfi yadda ta tabbatar kowa zai ji
Umman tace
“Eh kam tabbas!”
Sannan ta mik’e tsaye
kafin tace
“Uwar Ango! Tana Ina?
Ana buk’atar Uwar Ango a nan yanzu yanzu”
Da k’arfi ta yadda kowa ya iya jiyota tunda daman wak’ar da aka kunna a low tune yake
kuma iya murya ne kawai babu kid’a.
Da sauri Ummu tace
“Umma meye haka?
Idan kin yi min magana ba zan je In kirata baneba?
Ko hakan da kika yi kina tunanin shi zai sa ta fito?”
Still da k’arfi Umma ta sake cewa
“A’a, ai ji nayi kamar kince bata zo ba!
Gashi shima Angon shiru.
Duk da dai ni ba Shuwa bace ba amman Tabbas na asan cewa Ango da Amarya a tare ake shafa musu lalle, manshanu, da ragowan abubuwa! Dan har yau ina tuno naki, a tare aka shafa muku ke da Muhammadu wanda ya zo wurwuri
bai tsaya b’ata lokaciba,
Ita kuwa yayarki daman ba a yi mata ba
shiyasa gaba d’aya auren nata duk biyun suka tab’arb’are!
To kuwa kinga ai ba zan so auren Huda itama ya samu matsala ba ko?
Dan haka gara mu jira Angon ya zo ko nan da k’arfe taran dare ne mu masu iya jiransu ne
har sai shi da uwarshi sun zo an yi alada yadda ya kamata!”.
Ta k’arashe maganar har wani karkarwa jikinta yake yi, wanda kana gani ka san bala’ine kawai yake cinta.
Ummu bata ga k’arasowar Sakina ba sai tayi tana cewa
“Eh tabbas kam Hajiya Umma kya zauna ai kiyi ta jira tunda daman kallon kwaf da munafurci ne ya kawo ki!
Mu nan dukkannin mu munada aikin yi kuma ba mu da lokacin zaman jira har k’arfe taran dare!
In dai Ango kike son gani to ki bada nan da awa biyu zaki ganshi sun iso tare shi da iyayenshi maza da za su kawo lefe wanda na tabbatar abunda ya tsaidasu kenan
ba wai abunda makirar zuciyarki ta shirya miki ba!”
Umma na shirin k’arasowa inda Sakinar take taga Ummu ta d’auke ta da mari!
Cikin yaren Shuwa Ummu ta hau yiwa Sakinar fad’a k’asa k’asa yanda ta tabbar ba kowa ne zai ji su, tace
“Baki da hankali ashe?
A cikin dangi da y’an uwa za ki bud’e baki kina yiwa babbar mata rashin kunya haka?
So kike a tafi dake a baki?
Wuce!
Wuce ki tafi chaan sama d’akin Shuwa ki rufe!
Idan ba ni na neme ki ba wallahi kika fito sai ranki yayi mugun b’aci!”.
Juyawa kawai Sakina tayi ta wuce tana ji kamar ta had’iye zuciyarta!
A kan Umma aka mareta a gaban mutane haka!?
Kuma ta tabbatar tunda Umma ta fara wannan maganganun to fa idan taka mata burki aka yi ba ko kuma Arshaad d’in ta gani ba tabbas ba zata
tab’a barin mutane su sha ruwa ba.
Ita daman tun d’azu da ta ganta tazo da sassafe ta san ba alkhairi ne ya kawota ba.
Ita da take da abun fad’a a gindi amma shine har take da audacity d’in yin magana!
Wallahi yau da Ummu ta barta da sai ta yiwa Umma zazzagar kwanyo....
Da wannan tunanin ta k’arasa d’akin Shuwa, sai a lokacin hawayen bak’in ciki suka samu nasarar zubo mata…
Daga Shuwa sai Baabaa Talatu ne a d’akin suna
shirya tukuicin da za a bayar in an kawo lefe.
Baaba Talatu tana ganin ta shigo tana kuka ta mik’e tana
“Subahanallah, mai ya
faru?
Ke da waye?”
Da sauri ta k’arasa ta hau shafa fuskarta inda hannun Ummu ya fito tarr!! Ya kwanta akan farar fuskarta
Cikin fad’a Baaba Talatun tace
“Wanne d’an iskan ne ya mare ki??”
Fashewa tayi da kuka
cikin kukan tace
“Umma ce take ta abubuwa a waje, shine Ummu ta mareni
wai dan....”
Ai bata tsaya jin k’arshen ba,
tayi waje.
Shuwa ce ta iya daurewa ta tsaya ta ji labarin Sakinar
tukunna ta mik’e itama tace mata “ta zauna a d’akin, kar taje ko ina .
Bari taje taji ba’asin abunda yasa Angon bai k’araso ba...........”
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
53
Shuwa ce ta iya daurewa ta tsaya ta ji labarin Sakinar,
tukunna ta mik’e itama tace mata “ta zauna a d’akin, kar taje ko ina.
Bari taje taji ba’asin abunda yasa Angon bai k’araso ba.”
“To”
Kawai Sakina tace,
tana mai sake goge fuskarta
sannan ta koma gefe ta fara warware laffayar jikinta da d’aurin d’ankwalin dake kanta..
Sai da ya rage daga ita sai long camisole d’inta wadda ta saka a ciki mai dogon hannu yayinda dogon gashinta ya kwanta a gadon bayanta sannan ta fara k’ok’arin kiran Arshaad...
Tayi mishi misscalls sun fi ashirin amman shiru. Dan haka
nan da nan hankalinta ya sake tashi…. Tun jiya take danne zuciyarta take k’ok’arin kawar da maganar da Aaima ta gaya mata a cikin kwakwalwarta
amman kuma attitude d’in Arshaad da k’in zuwanshi a yanzu ya yi matuk’ar bata tsoro.
Ba wadda take jin fargabar taji wannan batu irin Hudan
shiyasa jiya ta kwana Sallah akan Allah yasa maganar Aaima ta zama k’arya
idan kuma gaskiyace Allah yasa su Abba su gyara lamarin cikin sauk’i…
Gaba d’aya hankalinta a tashe yake dauriya ce kawai take yi, tana kuma k’ok’arin taga ba wanda ta bari ya ma ji zancen har a samu a gyara lamarin in sha Allah.
Ganin arshaad d’in bashi da niyyar amsa ta ne
yasa kawai ta kira Auwal
dan taji me ke faruwa
a ina aka tsaya..
Shi sai a bakinta ma yake jin wai ‘Arshaad d’in bai je ba’
Saboda shi suna asibiti.
Ganin kamar bai san me yake faruwa ba ya sanya taja bakinta tayi shiru
saboda ance yawan yayata magana kan iya tabbatar da gasgatuwar ta. Dan haka kawai sai tace mishi
“ya duba musu Arshaad din pls”
Daga haka suka yi sallama.
Daman shima yana da shirinshi zai je wajen
So yanzu zai duba Arshaad d’in sai su wuce tare kawai
dan haka ya cewa Dad
“Bara yaje gida,
Sakina ta kirashi wai har yanzu Arshaad be k’arasa ba.”
“to” kawai Dad d’in yace masa.
Yana fita shima Dad din ya d’au waya ya kira Gwaggo Asabe yace
“Dan Allah tazo ta ji da Ummi.
Zai yiwa drivern da zai kawota kwatancen asibitin da suke....”
Drivern da ya kawota (Gwaggwo Asabe) shi ya maidashi mansion d’in.
Yana zuwa ya tarar da Daddy
ya shirya chap yana jiranshi
da akwatuna dozen biyu sun sha decoration
sai kuma basket na gift guda biyar, da akwatunan uwa uba gwaggwo da kawu..
Duk sun had’a. Tun sassafe Mommy ta aiko da kayan
shi kuma ya duba ya tabbatar komai dai dai.
Sai da aka gama loda kayayyakin a motoci wajen goma tukunna Abba ya fito da shirin shi shima da alama rakasu zai yi!
Dad, yana shirin shiga mota har driver ya bud’e mishi k’ofar motar ya hango tahowar Abba!
Wani takaici ne ya d’ebesa
bai san lokacin da ya daka masa tsawa ba! Yace
“Idan ka k’araso nan wallahi sai mun kwashi y’an kallo ni da kai!
Kaji dai na rantse
wallahi!!”
Ya k’arashe maganar yana mishi nuni da yatsar shi manuniya yana nuna sama.
Ajiyar zuciya Abban ya sauk’e kafin yace
“Dad nimafa rakaku zan y....”
Cikin fushi Dad d’in yace
“Kaga mota nan, zo ka shiga!
Amman direct
Asibitin da aka kwantar da Ummi zaka je
Idan kuma ba haka ba to ka koma ka zauna a ciki.
Zab’i d’aya!”
idanuwa direbobin da masu aikin suka tsura musu..Ganin da Abba yayi har sun fara kwasar y’an kallon kamar yadda Dad d’in ya ambata ne yasa kawai ya juya ya koma ciki ranshi a mugun b’ace!.
Tsaki Dad yayi ya shige motar
yana mai cewa
“Ba za ku haukata ni ba,
wallahi!”.
Shi dai Daddy
shiga yayi ya zauna a kusa da shi, yana son tambayarshi
wata zuciyar kuma sai ta bashi shawarar ya bari ya Dad d’in ya d’an sauk’o tukunna sai suyi magana…
A haka drivern ya ja su suka nufi Gandun Albasa
Daddy yana mamakin meye haka yake damun Dad??
Dan tabbas ya san akwai abunda aka yi mishi......
GANDUN ALBASA.
Baaba Talatu tana fita harabar gidan ta tarar gurin har ya fara kachamewa!
Dan bayan Sakina ta bar wajen Umma da Anty Zainab kan Ummu suka dawo
wai “ai itace bata yi mata tarbiyya mai kyau ba shiyasa ta raina manya har haka...”
Ga kuma wannan tsohuwa ita ma ta kafa ta tsare tace
“Sai Ango ya fito tukunna za a fara gabatar da komai!”
Yayinda Ummu da wasu cousins d’inta suke ta k’ok’arin ganin sun yayyafa wa lamarin ruwa
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 28