Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
hannun Mom d’in ya wuce sama. Tabbas Jalila ta d’an sha jinin jikinta kuma it’s like kamar akwai abunda yake damunshi sannan tanada buk’atar kud’i daga hannunshi da kuma alfarmar ya barta ta je wajen Umma dan she can’t afford to loose Arshaad, duk da kuwa Umman tace mata akwai nasara amman tana son zuwa yau ta bita ta je da k’afafuwanta, shiyasa ta barshi kuma bata sake yiwa Mom wani yunk’uri ba ta hak’ura kawai ta barshi akan idan ya d’an huce kamar nan da 20 minutes haka zata kirashi ta zayyane mishi buk’atun ta. Hira sosai Mom da Aaima suke yi, Jalila kuwa tana gefe tanata hura hanci. Chan Mom ta cewa Aaiman tazo suje suci abinci. Haka suka mik’e suka isa dining d’in sukai lunch d’insu cikin kwanciyar hankali. Sai a sannan Aaima take tambayar Mom wacece jalila? Murmushi kawai Mom d’in tayi sannan tace mata “no one” kawai, daga nan tace “Ta mik’e ta je ta jirata a parlourn sama. Hakan kuwa akayi, Mom na ganin wucewar Aaima ta mik’e itama tayi kitchen….. Dama tun d’azu ta sallami cooks da masu goge gogen gidan! Tace musu “su tafi part d’insu In akwai wani abun zata neme su!” Har ta shiga ta d’auko abunda zata d’auka ta fito hankalin Jalila yana kan kallo. A dai dai stairs na bakwai ta tsaya ta zuba abunda zata zuba tayi sama abunta da cup d’in cikin sand’a. Kamar minti biyu ta dawo bayan ta ajjiye abun hannunta a d’an gefe kad’an a nan saman ta tsaya a saman bata sauk’o ba kafin ta d’an fara sauk’owa sai kuma ta tsaya tana lek’en parlourn k’asan kafin tace “Jalila ga Ummanki tayi miki message, ungo wayarki, tunda na hau nake ta jin k’arar wayar shine na duba d’akin naga misscalls da messages Za ki zo ki karb’a? Ko kuma ma kawai bara in karanto miki kina daga zaune dan na san mik’ewa yanzu aiki ce a gareki saboda yanayin da kike ciki.” Ba tare da b’ata lokaci ba Mom ta fara karantowa “Aslm Jalila ya gidan, yau banjki....” A zabure Jalila ta mik’e tayi hanyar stairs tana masifa “Adama bana son rashin mutunci! Yanzu ke inda ace uwarki ce tayi miki message zaki yarda a karanto miki….?” A fusace take maganar tana tahowa da d’an cikinta wanda ya d’an fara tasowa! K’arfen stairs d’in ta kama cikin sassarfa ta fara taka stairs d’in har da d’an gudunta, tana zuwa kan na bakwai kuwa ta zulme santsi ya d’ebeta a take ta hantsila ta gangara ta koma k’asa ta fad’a ruf da ciki a kan cikinta! Wata azababbiyar k’ara ta saki daga nan ta saki jiki bata sake motsi ba!. Da sauri Mom wadda daman da tsummanta har biyu ta ajjiye a gefe farkon stairs d’in dan haka ta d’an juya ta d’auka ta sauk’o, dai dai wajen na bakwai d’in ta saka wet one d’in da ta jik’a a ruwan omo ta goge wajen tass kafin ta saka dry one d’in ta goge wajen sosai shima. Dai dai nan Auwal da Aaima waenda k’arar Jalilan ya janyowa hankali suka taho a tare… Da sauri Mom ta d’ago ta kalleshi a rikice kafin tace “Yauwa Auwal zo ka duba inaga jiri ne ya kwasheta kaga ta fad’i kamar ma ta suma bara in d’ebo ruwa.” Ta fad’i hakan tana mai sake duk’unk’une tsummokaran a hannunta Yayinda su kuma gaba d’aya hankalinsu ke a kan Jalila… Idan idanuwansu ba gizo suke musu ba kamar jini ne yake fitowa ta k’asan ta! Shiyasa ma kwata kwata basu lura da Mom d’in ba suka fara sauk’owa har suna y’ar rige rige, ita kuma ta wuce wuff!! Tayi kitchen tana mai cewa “bara in kawo ruwan” Hankalin Aaima ba k’aramin tashi yayi ba ganin kamar ma ta mutu ne! Ga kuma jinin da taga yanata kara b’ulb’ulowa, shi kanshi Auwal duk da cewa babban burinshi a halin yanzu yayi getting rid of Jalilan ne amman sai da ya firgita ba kad’an ba. Suna a haka Mom ta fito, ruwan da ta zo da shi a jug gaba d’aya sai da ta juye mata shi amman ko gezau Jalilan bata yi ba! Ganin haka yasa Auwal yin sama da gudu ya je ya d’auko makullin motarshi ya dawo ya zo ya kinkimeta yayi waje su Mom suna binshi a baya…. Yana gama sakata a bayan mota motocin su Dad na shigowa ganinshi a d’an firgice yasa suka tsaidashi suka hau tambayarshi.. Da kyar ya iya ce musu Jalila ce ta fad’o a bene ta suma ya shige ya tada motar ya fice a 70 ya bar su Mom suna sake yi musu bayani “Allah ya sauwwak’e” suka ce. Shi kam Dad bai ma san wacece suke magana akai ba daga haka suka nufi side d’in Abba dan Dad yad’an yiwa Daddy bayani a mota So ya kamata su sameshi ya maida Ummi first kafin granpa ya tsine mishi, sannan kuma ayi maganar ta yanda za a b’ullo wa haukar Mammy dan sun yi alk’awarin in dai sune mazan mt masu fad’a aji to tabbas gobe sai an d’aura aure bi izinillahi! Babu fashi….. GANDUN ALBASA “Ku bata iska mana ya duk kuka lullub’eta haka ne??!!” Cewar Baaba Talatu wadda take k’arasowa wajen da kyar. Da sauri duk aka fara matsawa gefe. Hansai da Anty Zainab da wasu mata Baaba Talatu ta umarta da su d’auketa a kaita parlourn da ga nan ta cewa Maryam “ta kirawo Likitan da take zuwa tana dubasu.” Hakan kuwa aka yi Nan tace mata “gata nan zuwa tana ma kusa dama, su bata nan da minti goma.” Ko da Likitan ta zo da kyar ta samu Umma ta farfad’o amman ta bada shawarar a kaita emergency a take dan jininta ba k’aramin hawa yayi ba! A motar Abba k’arami wanda suka iso yanzun nan shi da iyalinshi da Mahaifiyarsa da Baban sa aka kaita asibitin. Duk da halin da take ciki da suka had’u da Ya Jamilu a waje bakin motar sai da ta tambayeshi “ina Baba?” “Yana nan” kawai ya iya ce mata daga nan ta shige ita da Anty Zainab wadda ta zauna a gaba suka wuce asibitin. Da kyar Mama ta iya tsayawa aka gama kallon lefen da ita daga nan ta wuce ta shige tayi sama… Tun a corridor d’in d’akin Shuwa ta saki kukan da take ta k’ok’arin dannewa. Da sauri ta tura k’ofar ta shige tana wani matsanancin kuka a tunaninta ba kowa amman tana shiga suka yi ido biyu da Sakina. K’ok’ari take yi ta danne kukan ta wayance amman ta kasa dan haka kawai sai ta durk’usa ta sake sakin shi a wajen da dukkan k’arfinta tanayi kamar ranta zai fita......... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 54 Da sauri Sakina ta k’arasa wajenta ta hau tambayarta “mai ya faru?” Bata iya bata amsa ba, sai da ta d’an dedeta kanta da kyar tukunna ta d’ago jajayen idanunta tana kallon Sakina tace “Kina da number Abba? Baban Huda.” A hankali Sakina ta hau girgiza mata kai..kamar wadda ta tuna wani abun kuma sai ta mik’e ta isa gado inda ta ajjiye purse d’inta, tana cewa “Amman ga wayar Hudan, bara in kira miki shi ta nan” Da sauri Mama ta mik’e ta isa inda take dai dai Sakina ta fara dialing number Abban, Mama ta sa hannu ta karb’a wayar ta kara a kunnenta. Sai da kiran ya kusan tsinkewa tukunna ya d’auka! A hankali taji yace “Princess, how was your day?” Sai da Mama ta lumshe idanunta na sakanni wasu zafafan hawaye suna zubo mata tukunna tace “Horrible, Abba! Her day was horrible!”. Da sauri ya gyara zamanshi kafin yace “Maryam” Cikin son sake tabbatarwa. Cikin kuka tace “Lalata mini rayuwa da farin cikin da kayi bai isheka ba sai da ka had’a da Huda ko? A haka sai faman ik’irari da pretending d’in kana k’aunarta kake yi!.. Abba in dai har kana son ta mai yasa ka jefa ta a irin wannan relationship d’in??? Da ka san mahaukaciyar matar yayanka ba zata so auren Arshaad da Hudan ba mai yasa tun farko kuka had’a? Saboda ku maidamu abun kwatance ko me?? An tara mutane k’iiri k’iri Ango yak’i zuwa! A Ina aka tab’a yin haka? To bara kaji in gaya maka Tunda har Mahaifiyar Arshaad da kanta ta furta cewar bata son y’ata a matsayin suruka To Wallahi ko ta dawo tace tana so, Ina so ka san cewa ‘maganar aure babu ita!!’ Sak’o ne wannan na baka, ka gaya mata ka gayawa Arshaad da wakilin shi! Dan ba zan tab’a yarda in kai Huda gidan da ba’a k’aunarta ba wallahi. Saboda na san zafin k’iyayyar surukai” Ta fad’i haka tana fashewa da wani matsanancin kuka. Da sauri Abba wanda yakejin zuciyarshi tana wani mahaukacin racing yace “Maryam listen to me dan Allah ki bar wannan kukan” Cikin tsananin b’acin rai tace “Abba kuka yanzu na fara! Na san zan yi kuka especially idan Allah ya kaimu gobe aka yi calling off auren y’ata na ganta a cikin tashin hankali dole zan yi kuka.....” Kasa cigaba ta yi da maganar dan haka ta yi jifa da wayar akan gadon ta durk’ushe a k’asa tana kuka. Sakina na shirin yin magana Ummu da Mommy suka shigo. Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e tanaji itama kamar ta fashe da kukan, a hankali ta d’an matso Maman sannan tace “Wannan dalilin fa shiyasa nak’i gaya miki tun farko, kin yi min alk’awarin ba zaki d’aga hankalinki ba yanzu menene haka? Ki kwantar da hankalinki ni na san Mammy bata isa ta hana komai ba! Dad ba zai barta ba.” Cikin katseta Mama tace “Wallahi ko Dad ya barta ko bai barta ba babu maganar aure tsakanin Huda da Arshaad Idan ita ta hak’ura to gobe ni zan hana! Ta yaya kuke tunanin zan bar y’ata ta rayu da surukar da bata sonta? Mommy na san mecece k’iyayyar surukai! Kullum addua ta Allah ya had’a Huda da surukan da zasu k’aunaceta. Taya za ki yi tunanin yanzu zan amince ta auri Arshaad??” Cikin katseta Mommy tace “Kar kiyi haka dan Allah, kawai mu zuba ido amman kar kice zaki shiga tsakanin kaddara! Idan kika yi hakan ai kun zama d’aya ke da Mammy kenan.” Cikin katseta tace “In zuba ido y’ata ta tafi inda ba a k’aunarta kome kike nufi? In zuba ido rayuwar Huda ta lalace kamar yadda tawa ta lalace?” Cikin rashin jin dad’i Mommy tace “Haba Maryam, rayuwarki bata lalace ba, da ni da ke fa kusan mataki d’aya muka taka a rayuwar aure. Tabbas mun jigatu kuma mun sha wahala amman a ko da yaushe idan na kalli Aslam wallahi ji nake gaba d’aya wahalar it’s worth it! Dan Allah yayi mana kyauta. Kuma dama a rayuwa dole akwai jarabta da kuma gwajin imani. Ni dai shawarar da zan Baki itace Dan Allah kar kiyi interfering ki zuba ido ki barwa mazan komai, su sun san me za suyi.” Cikin sharar kwallah Ummu tace “hakane tabbas! Mama dan Allah ki gwada yin hak’urin da kika saba wata rana sai labari.” Da sauri Baaba Talatu wadda bama su san ta biyo su ba ta k’araso tace “Taya zaku ce mata haka? In dai uwar Yaro tace batayi to muma ba zamu kai jikarmu mai tsada inda ba’a k’aunarta ba wallahi! Allah na tuba maza da yawa a gari.. Ga mai sunan kakan ta nan, d’an wajen Jamilu, idan Arshaad d’in zai kawo matsala ana iya d’aura musu aure gobe in sha Allah. Na san ba zai tab’a cewa a’a ba, saboda daman ni na d’an so in fahimci take takenshi tun ba yau ba.” Gyaran murya Shuwa wadda ta shigo yanzu tayi, dan haka duk suka juya suna kallonta. A hankali ta k’araso cikin tafiyar ta wadda ke nuna tsufan da ya rufar mata. Sai da tazo gaban Maryam tukunna ta kama hannuwanta duka biyu ta fara magana “Dan Allah dan annabi kar ki yi komai kar ki yi kuka kar ki d’agawa y’ar ki hankali. Ki bar komai a hannun Ubangiji, tun kafin ki haifi Huda already an riga an gama rubuta k’addararta da komai nata. Kar ki yi interfering wai dan kina tunanin zaki iya kub’utar da ita! ki zuba ido ki yi mata addua komai zai tafi bisa yanda Ubangiji ya riga ya tsara. Bamu isa mu saka ko mu hana komai ba. Kin ji y’ar albarka?” Ta k’arashe maganar tana mai sa hannu ta share mata hawayenta duka biyu. Kuka Mama ta sake fashewa da shi ta fad’a jikin Shuwa suka rungume juna. Ita kanta Shuwan k’arfin hali ne kawai da dauriya suka hanata kukan Ta rasa gane wachche iriyar k’addara ce A rayuwar Maryam da Huda, Astaghfirullah..... Shigowar ta tare da matan da suka ruk’o ta ne ya sanya d’akin yin shiru. Har yanzu fuskarta a rufe take amman kana gani ka san kuka take yi. Sakina na ganinta taji kuka na shirin kufce mata dan haka da sauri ta fita a d’akin. Suna zaunar da ita a bakin gado Mama ma ta saki Shuwa ta fice. Shuwan ce tayi k’arfin halin cewa “Mommy da Ummu da kuma mata biyun da suka shigo da ita “Su je akwai motoci a fara kwasar kayan Amarya ana kaiwa gidanta, dan ba zata yarda da ajjiye wannan dukiyar a gidanta ba, tunda kowa ya gani kawai su kai mata abunta gidanta.” Murmushi Mommy tayi kafin tace “Ni kam gida zan wuce.. Ina a matsayin uwar Ango ina ni ina ziryar gidansu Ai nayi jere sai kuma in ta haihu nan da wata tara in sha Allah ni da in koma.” Da sauri cikin raha ragowar matan suka ce “In shaa Allah” Ba a wani dad’e ba suka fito dukkansu a tare Mommy ta d’anso ta sake ganin Mama amman kuma kawai sai ta rabu da ita, a cewarta ‘in ta d’an sauk’o zuwa anjima zata kira ta a waya’….. A tare suka fito da Ummu, su suka fara yin gaba da akwatuna ita kuma ta shiga mota ta nufi MT estate dan already drivern ya zo tun d’azu. NASARAWA g r a. Daddy da Dad na zaune sai zazzagawa Abba fad’a suke yi akan ‘ya mayar da Ummi tun kafin zance ya isa kunnen Granpa’ shi kuma ya tubure ya k’i!. Suna a haka wayar Mama ta shigo… Tsaf! Duk sun ji abubuwan da ta fad’a, dan wayar a high volume take kuma suna kurkusa da juna. Yana gama wayar Dad yace “Abba ka mayar da Ummi yanzunnan in dai na isa da kai.” Haka shima Daddy same thing ya fad’a mishi. Ba yadda ya iya haka ya maida ita yana ji kamar yayi ta kurma uban ihu!. Daganan Dad ya mik’e! Kamar Daddy ya san meye a ranshi yayi saurin mik’ewa shima ya tsaya a gabanshi sannan yace “Dan Allah kar ka yi haka. Ka tsaya zan yiwa Adama magana, na san kafin zuwa gobe in sha Allah zata nutsu.” Cikin fad’a fad’a Dad yace “Ba zata nutsu ba! Sam ba zata nutsu ba. Da ace zata nutsu da tun tuni ta nutsu, ku bar ni kawai!!” Ya fad’i haka yana k’ok’arin zagaye Daddy ya wuce. Da sauri Daddy ya kuma tareshi sannan yace “Ya abunda muka gama gyarawa yanzu! Da girman ka kake k’ok’arin aikatawa?” Cikin tsananin b’acin rai Dad yace “This is a different case..” Cikin katseshi Daddy yace “Ba wani different case anan duk abu d’aya ne! Idan kayi mata haka ma ai ka ji haushi kenan, wato ta ci riba ma kenan tunda har kaji haushi ka hukuntata, ai idan mata suna haukarsu ba a biye musu. Tabbas na san dole ana buk’atar albarkar ta amman ka b’ullo mata ta bayan fage. Wani abun fa dole sai ka sauk’o, ka san yadda za ayi a d’aura auren shine ka ci riba! Amman yanzu idan ka biyeta ka saketa aka zo ta sake birkicewa Wa gari ya waya? Abunda ya kamata kayi shine ka san ta inda zaka b’ullo mata ka bawa iska ajiyar ta ka nuna kamar bama ka san me take yi ba! Ka d’aure ta da jijiyoyin jikinta Tana ji tana gani a d’aura auren gobe kamar bata existing a duniyar! This is the best punishment da tayi deserving, amma yanzu idan kayi haka( ka saketa) ai jagula komai za kayi, kuma itace zata yi nasara at the end of the day tunda Uwa ce. Ka ga dai ga Granpa a gefe wanda a yanzu haka jira kawai yake yi a tab’a shi! Kai da kanka kace yayi mana warning a kansu duk mu ukun I assure you wallahi idan kayi wani abun ba zai duba laifintaba zai bi takanka......” Sannu a hankali Daddy ya samu ya shawo kan Dad da kyar! Ya hak’ura. Shi dai Abba yana nan zaune bai ce musu uffan ba! Dan ba fahimtarsu yake yi ba har yanzu ba abunda yake yi mishi yawo a kunne sai kukan Maryam da tashin hankalin da ya jita a ciki. Tabbbas sai ya gasawa Ummi aya a hannunta! Hakan ba halinshi bane ba kuma bai kamata yayi mata hakaba a matsayin ta na mahaifiyar su Sudais amman ba yanda ya iya…Dole ta san waye Abba! Ba ita kad’ai ba har su Mammmy, kasancewar su yayu a gareshi ba zai hanashi ya ja musu fasali ba. A hankali ya mik’e ya yiwa su yaya rakiya, daga nan shima ya fita ya bar gidan. Dad da Daddy direct asibitin da aka kwantar da Ummi suka je, an samu ta farfad’o sai dai har yanzu jikin nata ba kwari. Likitan ne ya ke gaya musu “jininta ne ya hau sannan tana da buk’atar rest mai kyau. Za su iya tafiya da ita gida idan suna ganin gidan will be more comfortable for her dan ba abunda za suyi mata anan (asibitin) sai y’an drip da y’an allurai da maganin bp d’inta. Hutun ta da kwanciyar hankalinta shine abun buk’ata a yanzu.” Dad ne yayi signing discharge papers d’in daga nan suka nufi gida da ita. Tunda aka kamo hanya Ummi take ji inama mutum zai iya kashe kanshi babu zunubi, wallahi da ba abunda zai hanata commiting suicide a yau d’innan! Atime d’in da ta farfad’o taso a ce mutuwa tayi.. Tun da ta taso tayi wayo ta san kanta Soyayyar mutane biyu zxuwa uku ta sani Abba Gramma sai Granpa! Yanzu kuwa da ta kawo yanzu ta san menene so ta san tabbas muddin babu Abba a rayuwarta to mutuwa ce tayi saura! Shiyasa kawai ta koma kamar mutun mutumi Ba abunda ya cika zuciyarta sai d’umbin dana sani Ita inda Abba zai yarda wallahi ya auro Maryam uku! Ya kawo ya had’a da ita su zama su hud’u, ta san za tayi kishi tabbas amma kuma zata hak’ura ta daure ta danne zuciyarta su zauna lafiya…… Tana cikin wannan tunanin taji su Dad suna danna horn! D’ago kanta tayi ga mamakinta sai ta gansu a mansion d’in su Abba instead of estate, addua ta fara yi a k’asan ranta ‘Allah yasa su Dad su saka Abba ya mayar da ita’. Ba wanda yace mata komai. Sai da suka shiga cikin parlourn suka zauna tukunna Dad yace mata “Ummi sai kin yi hak’uri da Abba a yanzu. Kar ki damu In sha Allah zai sauk’o. Kin ji. Ki tashi kije d’akinki ki huta. Ya gyara abunda ya b’ata d’azu. Ki kwantar da hankalinki Naki biyayyane, kin ji?” A hankali take jan numfashi tana share hawayenta tana jin wani farin ciki yana ratsa ta. “Tam Dad mun gode” Tace. Sannan ta fara k’ok’arin mik’ewa dai dai nan su Sudais da Shuraim da Aslam suka shigo! Suna ganinta suka yi kanta da gudu suna Ihun murna Shuraim harda y’ar kwallar shi Itama sai da tayi kwallar murnar ganin gudan jininta. Daga nan suka gaisa da Aslam ta wuce tayi sama ita da su Sudais. Tun a hanya Sudais ya fara zuba surutu yana bata labarin event d’in, da kalar hotunan da suka yi da kuma yanda Ya Aslam ya zauna a kusa da Huda…. Gaisawa kawai Aslam yayi da su Dad daga nan suka fice gaba d’ayansu.. Basu yi mishi zancen event ba shima daman hakan yake so.. Iya kar abunda suka sani shine Arshaad bai yi attending ba!. Shi da Dad suka yi gida Daddy kuma yayi side d’inshi. Sai dare Jalila ta farfad’o! Ba kowa a d’akin sai ita kad’ai. Jiri da ciwo a mararta take ji ba na wasa ba! Tana so ma ta mik’e ta d’an zauna amman ta kasa… A hankali kwakwalwarta ta shiga tariyo mata abunda ya faru da ita d’azu. Da sauri ta zabura ta dafa cikinta, dai dai nan nurse ta shigo. Cikin kulawa ta hau gwada ta tana mai tambayarta “ina da Ina ne suke yi mata ciwo?” A hankali Jalilan tace mata “Mai ya sameni? Marata tana yi min ciwo.” Cikin kulawa nurse d’in tace “I’m sorry ma’am, kin yi loosing baby d’inki ne” “L lo Loosing, me?” Cewar Jalila. Ganin kamar bata fahimceta ba ya sanya tace mata “Kin yi miscarriage! Cikin jikinki ya fita.” Da mugun k’arfi ta mik’e ta zauna sai kuma ta fashe da kuka! Dai dai nan Mom ta shigo. Tana ganin tana kuka tayi sauri ta k’arasa ta fara bata hak’uri sai kuma ta juya ta rufe nurse d’in da fad’a, tana cewa “Ba ance jinin ta ya hau sosai kar a d’aga mata hankali ba? Shine amma lokaci guda zaki zo ki fara zuba mata wannan mugun labarin? Asibitin gwamnati ya kamata ki koma ba private ba! Tunda baki iya tausar patient ba. Ai inda kin bari da mu da kan mu za mu gaya mata idan mun koma gida....” Hakanan dai Mom ta wanke nurse d’in tass!! Ta inda take shiga bata nan take fita ba dag nan tayi signing discharge papers taja Jalila suka nufi mota driver ya jasu….. Ita dai Jalila in banda kuka ba abunda take yi… har ga Allah bata son cikin nan ba taso ta haihu amma kuma yanzu da cikin ya fita ta san tabbas ba abunda zai shiga tsakaninta da komawa gandun albasa!! Sannan ta daina samun kud’i daga Mom da Auwal kenan har abada! Amman kuma yadda Mom take lallab’ata sai ta d’an ji zuciyarta ta d’an yi sauk’i! Maybe tausayinta take ji amma duk da haka ta san ba zai wuce na sati ba zata tarkatata! Dan haka a take ta yanke shawarar nemawa kanta mafita.. Zata lallab’a Mom ta bata hak’urin abubuwan da ta dinga yi mata Idan ta kama ma sai tayi k’aryar aljanune da ita tace mata su ne suke sakata yiwa mutane rashin kunya. Ta samu dai Mom d’in ta ara mata ko da sati uku ne daga nan ita kuma da ita had’a y’an kud’ad’en hannunta ta sake turawa Umma a san abunyi ta auri Arshaad ko ta halin yaya ne da wurwuri cikin gaggawa! Itafa wallahi yadda ta d’and’ana daular nan to kuwa batajin zata iya minti uku a cikin gidan Baba!…. Tanata sak’e sak’e a ranta a haka suka iso gida! Sai wani nonnok’ewa take yi gudun abunda Mom zata yi mata, amman suna shiga sai taji Mom d’in tace mata “ta tafi d’akinta ta huta Coook zata kawo mata abinci yanzu.” A hankali tace “Na gode Mom” Wani kalan murmushi Mom d’in tayi wanda Jalilan ta kasa ganewa.’Daganan Mom d’in ta juya ta nufi hanyar kitchen a ranta tace “Yarinya kenan! Sarai na san zaki iya yi mana bori, kice ba zaki tafi ba ki tada mana hankali Kuma ko yanzu na san idan akai test a jikinki positive za a gani.. Ki jira nan da kwana uku In sha Allah za ki san wacece Adama.” GANDUN ALBASA Tun da garin Allah ya waye Huda take kuka Idan zaka titsiyeta ka tambayeta ba zata tab’a iya gaya maka menene tak’amemen abinda ya sanya ta kukan ba! Ita dai ta san bata da nutsuwa sannan a mugun tsorace take amman tabbas ba wai shariyar Arshaad kad’ai ne dalilin tashin hankalinta ba. Sakina da Khadija sun yi lallashin sun yi har sun gaji sun rabu da ita. Hankalinta bai sake tashi ba sai da k’awayenta suka zo sannan mai makeup itama ta zo ta fara shiryata! Tayi alk’awarin ba zata sake kiran Arshaad ba amman haka ta daure ta kirashi wannan karan kam a kashe ma taji wayar tashi gaba d’aya dan haka hankalinta ya sake tashi! Ba abunda yafi d’aga mata hankali irin kar azo d’aurin aure yace ya fasa! Ita gara ya fito ya fad’a mata gaskiya akan yayi mata hakan... Nasarawa gra. A b’angaren Arshaad kuwa jiya ya gama shirya plan d’inshi amman ga mamakinshi kamar wani ya gayawa Mammy bayan Magrib nayi ta shigo d’akin nashi ta kafa ta tsare! K’arshema a d’akin a kan couch ta kwana tsabar bala’i. Tun jiyan da ta shigo har yanzu k’arfe 10 bata fita ba! Ko wanka ko brush bata yi ba, har gara ma shi yanata watsa ruwa saboda zazzab’in da yake jikinshi.. Yana lura da ita ko mik’ewa yayi ya shiga shiga toilet zai

Chapter 27 of 28