Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kafin ya fara magana “Shikenan zamu gwada mu gani, amman idan mun yi nasara kin dawo wajen Maman naki to inaso kisan cewa Ba a inda take zaki zauna ba sai dai ki zauna a gidana! Saboda Usman ba zai tab’a bari ki ci gaba da zama nasa a gida ba sannan na san ba zai dinga barin itama Maman naki tana zuwa inda kike ba kwata kwata kinga kenan baki zauna da Abba ba kuma baki zauna da Mama ba!” Cikin kuka Mama tace “Abba dan Allah ka dai na, za ka karya mata guiwa” Murmushi ya sake yi kafin yace “Maryam hakan shine gaskiya! Kuyi hak’uri, for the first time nayi miki alk’awari ban cika ba! In dai zan fad’a miki ki ji, tou inaso dan Allah ki bar Yarinyar nan ta koma wajen Mahaifinta kamar yadda ya buk’ata, ko munje kotu ya fimu gaskiya, kuma rashin hankalin da Usman ya sake yi yau d’innan ma wata shaida da point ne Abba ya sake samu. Ki barta ta tafi, za ku dinga waya sannan yace anytime kike son ganinta kije ki ganta, idan ma bakya son zuwa gidan nasa to zai saka ko driver ne ya kaita ko wani park ko restaurant, ku had’u achan amman yace ba zai sake barinta tazo inda kike ba! Har ga Allah Maryam, Abba is trying to be just here.” Da sauri ta d’ago tana kallonshi da jajayen idanunta. D’aga mata kai yayi alamar gasgata mganar shi, kafin Baba Bashir ya d’aura da cewa “Maryam har yanzu zuciyar ki a k’ulle take da zafin abunda Abbas ya aikata miki, shiyasa ba za kiga abinda mu muka ganiba, wanda muma a da bamu ganshiba sai bayan da muka yi k’ok’ari muka goge takaicin shi daga idanuwanmu.” “Mune muka haifeki, baki da masu fad’a miki gaskiya sama da mu, ki tashi ku tafi suyi miki kwatance ki kaisu ki dawo, dama haka rayuwar take, ba komai kake kwallafawa rai kuma ka samu ba, ki bari ko nan da wata biyu ne haka, sai a san abun yi kinji? Yanzu kuje kawai.” Hudan ke kuma idan kin koma, ki san yanda za kiyi mishi magana a samu ya saki Babanku Usman kinji?” Cewar Shuwa. A hankali Mama ta rintse idanuwanta wasu zafafan hawaye suna zubo mata! Ta manta rabon da Shuwa tayi mata magana mai tsayi haka. Bata dawo daga duniyar tunanin da ta tafi ba, taji Sakina ta furta wasu maganganu da suka girgizata matuk’a! Wai “An saka ranar Huda nan da wata biyu da Arshaad!!” Ba Mama kad’ai ba, gaba d’aya parlourn shiru ya d’auka! Chaaan! Shuwa tace “Allah ya sanya albarka” Da sauri Mama ta kalle ta da idanunta hawaye shab’e shab’e! Kasa jurewa Shuwan tayi kawai ta mik’e ta kama hanya ta fice… Baba Bashir ne yace “ku tashi kuje Maryam, za muyi wannan maganar wata rana!” Cikin kuka Mama tace “Kaka, Abba Naji zan barta ta koma amman dan Allah kar ku saka na maida ita, ba zan...” Kukan da ya kufce mata ne yasa ta kasa ci gaba da magana ta mik’e ta fice tayi cikin gidan… Baaba Talatu ce ta bita domin lallashin ta. Wannan shi ake kira isa da mallaka!!! Tayaya zaka sa ranar Yarinya ba tare da tuntub’ar Mahaifiyarta ba? Saboda Allah fa!. Shiruuu, parlourn ya d’auka, chaan Kaka yace “su mik’e su kai su” Ita Sakina tausayi ma y’an tsofaffin suke bata, sun tsufa amman har yau basu huta ba, bayan jigilar case d’in y’an unguwa ga na family…ta tabbatar yanzu suna maida su, police station zasu wuce, akan case d’in Baba……….. A k’ofar tafkeken mansion d’in da suka isa da taimakon kwatancen Sakina suka yi parking, daganan suka yi musu sallama, da d’an Guntun maganganu tukunna suka wuce, su kuma suka shige ciki. A parlourn suka tarar da Abba, Daddy har Dad da Arshaad! Da alamun maganganu suke yi masu mahimmanci. Yadda Hudan ta baro Mama tana kuka yasa ta d’an ji zafin Abba! A hankali suka gaidasu, bayan sun amsa bata tsaya ba kawai ta haye sama! Har sai da Sakina ta d’an yi mata magana bayan sun hau, dan taga kamar basu ji dad’in yadda tayi musu d’in ba. Ko lunch k’in sauk’a tayi, ba yanda Sakina batayi da ita ba amman tak’i sauk’a, gashi Abba sai kira yake a waya tana amsawa tana cewa “Huda sallah take” Kamar minti ashirin haka, suka ji knocking. Sakina ce tace “Come in” A tunanin ta ko maid aka turo ta kawo musu abincin. Turo k’ofar yayi ya shigo, Sakina bata san lokacin da ta fara dariya ba ganin Abba ya shigo har da hular kuku a kanshi da basket d’in abinci a hannunshi. Harararta yayi, ya d’aura yatsanshi akan lips d’inshi alamun tayi shiru! D’aga hannuwanta sama tayi tana gimtse dariyar tata, sannan ta mik’e ta fice da sauri. Sai da ya ajjiye kular, sannan yace “princess” Shiru tayi still tana kwance ta bawa k’ofar baya. Chan taji yace “Hudan” A hankali ta mik’e ta zauna ta juyo tana goge hawayenta, fuskarta tayi jaaa alamun taci kuka, over!! Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya zauna a bakin gadon, yayi hugging d’inta ya fara lallashinta ai kuwa kamar jira take ta saki kukan babu control. Bai hana ta ba, sai da ta gaji dan kanta tayi shiru tukunna a hankali yace “sorry dota, i’m really sorry, ok?” Cikin sheshshek’a tace “Abba Mama na da bp, yanda na baro ta tana kuka, Allah zai iya tashi?” Murmushi yayi yana sakinta kafin ya gyara zamanshi yana kallon k’ofar fita tukun yace “Hudan, na fiki jin zafin kukan da Maman ki take, please don’t question my decision, it’s the right thing.” Ahankali tace “Amman Abba pls...” “Shhhhhhh” Yace ba tare daya kalleta ba, kafin ya juyo ya fara k’ok’arin zuba mata abinci. Omelet d’in da ya soya mata ya saka a gefe, da pizza slice uku da ya d’auko. Da farko k’in ci tayi sai da yayi dagaske, tukun ta d’an karb’a. Bayan ta gama ta sha ruwa, ya d’an dunga janta da magana yana ta faman lallashinta. Hudan bata iya dogon fushi da mutum ba, don haka ta d’an sauk’o, hakan kuwa yayi matuk’ar ragewa Abba kusan 20% na damuwar da yake ciki shiyasa da ta rok’esa akan ya saki Baba ba don halinsa ba sai dam kakanninta da hankalin su yake a tashe! Abban ya amince, a take ma a gabanta yayi waya yace a sake shi. Ta ji dad’i sosai kuwa. Daganan suka d’an ci gaba da maganarsu. Hammar da yaga tanayi ne ya sanya ya fahimci bacci take ji, dan haka yace mata “ta kwanta” Bata yi 10 minutes da kwanciyar ba ta fara bacci…. Ahankali yake kallonta yana tunani kala kala… Sai bayan kusan 1 hour tukun ya rage mata k’arfin ac ya lullub’eta da bargo, sannan ya fita da kayan abincin............... A chan parlourn k’asa kuwa, sam Sakina bata lura da Auwal wanda ya daya dawo break ba, sai da ta kusan k’arasawa dining d’in! Tun kusan sauk’owarta yaji a jikinshi! Addua yake Allah yasa itance, don haka ya k’urawa stairs d’in ido… Ba a hankali take tafiyarta ba ba kuma da sauri ba! Da d’an murmushi a kan fuskarta. Gaba d’aya ya shagala da kallonta, har wani lumshe ido yake yi yana bud’ewa. Jikinta ne ya bata kamar ana kallonta, sai kuma mayen k’amshin turarenshi da ta fara ji a jikin shi tun ranar farko ya daki hancinta! Dan haka da sauri ta d’ago ta kalli dining d’in.. Suna had’a ido yayi saurin rintse idanuwanshi kafin a hankali ya bud’e su a kanta! Doguwar riga ce a jikinta Ashape y’ar kanti bak’a mai ratsi ratsin sky blue sai d’ankwalinta wanda tayi simple d’auri da shi.. Rigar bata wani kamata ba, amman kasancewarta mai garin jiki yasa ta d’an fiddo mata surar jikinta kad’an!. Ranta ne ya b’aci ganin yanda yake wani rufe ido yana sake bud’ewa yana k’are mata kallo! Da sauri ta sa hannu ta warware d’ankwalinta ta yafa a jikinta sannan ta doka wani uban tsaki, wanda yayi sanadiyyar dawo dashi cikin parlourn. Har ga Allah abinda take tunani ma shi Allah bai bashi ikon lura da nan d’in ba, kawai shi dai yasan ya tsinci kanshi cikin tsananin farin ciki da shauk’i na daban, sannan yanda ta yi d’aurin ya sake fito da ainahin kyauwun fuskarta dan yawanci cikin hijabi yake ganinta, ga wani lallausan saje dake shirin had’ewa da gashin girarta, na gefen kunnenta ma ya sauk’a sosai kamar zai had’e da gashin k’eyarta, sannan tunda yake bai tab’a ganinta tana murmushi irin yau ba! Bai ida dawowa dede ba yaga ta juya da sauri zata bar wajen. Da sauri ya mik’e ya k’arasa ya sha gabanta kafin yace “Sakina, please, listen to me dan Allah.” Wani kallon tsana tayi masa kafin tace “mallan dalla matsa In wuce” Tayi maganar babu alamun wasa a tare da ita…. Zagayeshi take k’ok’arin yi amman yak’i ya bata damar yin hakan, da alamun ma in ta biyeshi to a yadda yakesa hannayenshi wajen k’ok’arin kareta daga wucewa tsaf zai tab’ata! Don haka ta tsaya ta fara aika mishi da harara kafin tace “Malan ni ba Jalila bace ba! Ka bar ganin wai a gidanku nake wallahi Idan baka bani hanya na wuce ba, zan zabga maka mari!” Ga mamakinta sai taga yana dariya, sai da yayi mai isarshi sannan yace “Na yarda! But duk mari d’aya zaki bani 10 minutes d’inki, kawai ko d’an hira ne muyi…..tbh i can do anything to get your attention” Ya k’are maganan yana kallonta da murmushi akan fuskanshi sannan ya d’anyi k’asa da kanshi….. Yanayin zanen flower d’in da aka yi na sky blue akan kayan jikinta yayi mishi kyau sosai! Zanen ya bi da kallo, har ya sauk’e idanunsa akan yatsun k’afarta! , Gaba d’aya ya shagala da kallo yaga ta janye da sauri cikin b’acin rai tace “D’an iska kawai!!” k’asa k’asa, ita kanta bata yi tunanin zai ji ba, sannan tayi sauri ta nufi d’akin da ke kusa kusa, tana shiga ta datse k’ofar ganin yana shirin biyo ta. Tunda Auwal yake a rayuwar shi, har snake friends d’insa wani lokacin suke kiranshi da shi, ko master, ko danger sunaye dai na rashin d’a’a kala kala but bai tab’a jin ba dad’i ba! Amman yau da Sakina tayi mishi wannan kallon har ta furta, gaba d’aya duk sai yaji babu dad’i! He hates it. Kasa ci gaba da lunch d’inma yayi don haka ya mi’ke ya fita ya koma office da tunani barkatai a ranshi! He just wants to talk to her, yana so ya sake ganin smile d’in nan nata! D’an 5 minutes d’in da suka yi shi da ita d’azu tare zai iya cewa ‘it one of the best moment of his life.......’ BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 46 BAYAN WASU Y’AN KWANAKI. Tun ranar da su Hudan suka koma Nasarawa gra, malaria da mura suka yi mata ram!Bata iya komai hatta karatunta ma Sakina ce ta karb’a take yi. Gaba d’aya hankalin Abba a tashe yake, kwananta d’aya a asibiti aka sallamosu aka had’o su da nurse wadda zata dinga yi mata allurai da chanjin drip. Shi da kansa (Abba) yake jinyar ta, da kyar yake yarda yaje yayi bacci amman da sassafe shi da Arshaad ne suke tashinsu a bacci. Babu abunda yafi d’aga musu hankali irin yanda bata iya cin abinci dan ta samu lost of appetite! A rana sai a girka abinci kala nawa amman da kyar zata iya tsakular d’aya, gaba daya duk ta zabge ta rame tayi wani irin fariii! Sai dogon hanci wanda ya sake fitowa tubarkalla, idanuwan nan daman ya lafiyar kura sun sake lumshewa kamar na mashaya. A cikin kwana biyun nan ba Hudan ce kad’ai ta rame ba har Auwal!! Dan kwata kwata Sakina ko a waje ta ganshi to ta bar wajen kenan sai in ya tafi tukun zata koma, k’iyayyar k’iri k’iri take nuna masa babu ji babu gani. Ranar da aka kwantar da Hudan a asibiti kuwa, da Auwal d’in yaje dubota akai rashin sa’a Sakinar ce a wajen Abba ya d’an fita ita kuma Huda tana bacci dan haka ya samu chance! Ganin da Sakina tayi abun nashi ba na k’are bane yasa ta fito mishi a Sakinar ta ta wankeshi tass!! Sannan tace “Ta tsaneshi, ba zata tab’a iya yin rayuwa da mazinaci mak’aryaci kuma mayaudari ba! Ya fita a harkar ta tun kafin ta sauya mishi….” To dai tun daga ranar ta samu ya d’an sakar mata mara, dan ita yau kusan sati d’aya ma amman bata saka shi a idontaba. Abunda bata sani ba ashe rashin lafiya shima yayi na kwana biyu..gaba d’aya duk ya rame, office kawai yake iya zuwa, Daddy yayi tambayar duniya har ya gaji ya kyaleshi….. Yau Hudan ta d’an tashi jikin da sauk’i tun safe, dan yau through out batayi amai ba kuma ta d’an ci abinci ba laifi Abba sai murna yake yi, don haka yace “idan zata iya tazo suje k’asa suyi dinner da kowa (cikin mutane)”. Sudais ne ya ruk’o hannunta na dama Abba kuma na hagu, Sakina sai murmushi take yi, dan ba k’aramin burgeta suke yi ba sai wani lallab’a ta ake yi kamar kwai! A haka suka sauk’o gwanin ban sha’awa. Tayi tunanin a nan za suyi dinner d’in amma sai taga sun nufi side d’in Daddy, Sakina ba dan taso ba ta bisu dan kwata kwata bata son abunda zai had’ata da Auwal, sam!. A chan suka tarar da Aslam da Arshaad… Basu samu Daddy a wajen dining d’inba amman an kammala jera komai. Ba suyi 5 minutes da zama ba, su Daddy suka sauk’o shi da Auwal! Bai yi wata wata ba ya nemi kujerar dake gefen Sakina ya zauna Allah ya taimakeshi babu kowa a wajen. A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yana jin wata nutsuwa ta musamman…. Sakina kuwa kamar ta tashi haka taji, kawai dai ta san su Abba za su d’an iya fahimtar wani abun shiyasa ta zauna saboda itafa ko a labari bata k’aunar a sako sunanta kusa da na Auwal! Cikin kulawa aka shiga exchanging greetings.. Sai da aka gama gaggaisawa tukun Daddy yace “sorry i kept you waiting, Auwal ke hunger strike kamar wani baby abincin ma wai sai naje na lallab’ashi tukunna zai yarda yazo yaci” Murmushi Aslam yayi, Abba kuma yace “gashi kuwa duk ka rame, what’s wrong with you?” Yayi maganar referring to Auwal d’in. “Nothing” kawai ya iya cewa yana sunkuyar da kanshi k’asa. Murmushi Abban yayi, dan kamar yad’an gano Auwal d’in amman sai ya basar kawai aka fara cin abinci. Arshaad ke zaune a kusa da Aslam Abba kuma na ata gefenshi (sun saka shi a tsakiya) Duk su biyun suna lura da yanda yake kallon Hudan wadda ke opposite d’insu akai akai! Gaba d’aya Arshaad sai yaji ya damu sannan bai ji dad’in hakan da Aslam d’in yake yi ba kwata kwata! Amman sai yayi ta k’ok’arin kawar da duk wani negative thinking a kanshi. Ita kanta (Hudan) a takure take, gashi zuciyarta ta hanata sukuni. Loma biyu kawai Sakina ta iya yi cikin kwanciyar hankali dan tunda Auwal ya fara mata ‘Hi’ ‘How are you?’ D’insa taji wani malolo ya tokare mata mak’oshi! Bata san lokacin da ta ajjiye spoon d’inta da k’arfi ba wanda hakan ya janyo hankalin kowa kansu… Dariya Abba yayi dan tun d’azu yanata lura da su, cikin dariyar yace “Ya takura miki ko?” Da sauri tace “Eh wallahi Abbac kace mishi....” Kasa k’arasawa tayi sakamokon zungurinta da Hudan tayi, k’asa k’asa tace “kinga Daddy fa yanda yake kallonki, ki yi shiru” Kallon inda Daddyn yake tayi, karaff! Taga itan yake kallo yana d’an murmushi, gaba d’aya sai kunya ta lullub’eta tayi k’asa da kanta. Y’ar guntuwar dariya Daddyn yayi kafin yace “K’arasa mana Sakina… Ace mishi ya daina takura miki ko?” Cikin dariyan ya kalli Auwal kafin yace “Auwal, Allah har a gama cin abincin nan kar inji ta sake kawomin k’arar ka!” Shi dai Auwal shiru kawai yayi kamar ruwa ya cinye sa.. Arshaad kuwa dariyar mugunta yake yi mishi a ranshi yace “Allah mai had’i!” Don ya tabbata Auwal sai yaci kwal ubanshi a hannun Sakina. Daddy kuwa kallonsu yake ta yi lokaci zuwa lokaci….tabbas daman ya d’an fahimci akwai abunda yake damun Auwal kuma yake kaishi side d’in Abba! Kenan wannan Yarinyar ce, but yaga kwata kwata Yarinyar bata da interest a kansa shi kuma gashi ya fahimci tsakani da Allah Auwal d’in nasa yake son Yarinyar. A zuciyar shi ya hau adduar ‘Allah ya karkato da hankalinta ga Auwal d’in a samu yayi aure ya bar wannan tsalle tsallen, dan tabbas ya hango nutsuwar d’an masa a tareda Yarinyar……. Har aka kammala, Auwal bai sake yi mata magana ba. Sai da aka d’an tab’a hira tukunna aka watse. Arshaad na son ya gana da Hudan amman Abba yayi kane kane! Har d’aki suka rakasu shi da su Sudais kamar d’azu… Sakina ce ta kawo musu tofi suka yi sallama suka tafi shi da Aslam..... Suna shiga d’akin, suka hango wayar Hudan dake kan gado tana kyalli, da sauri Shuraim ya k’arasa yaje ya d’auko dan yanayin tafiyar tata kafin ta isa kiran zai iya tsinkewa, amman dukda hakan kafin ta kai ga amsawa kiran ya tsinke. Gabanta ne ya fad’i ganin 20 missed calls d’in Mama akan screen d’in, tana shirin kira wani kiran ya sake shigowa…. Tana amsawa taji Maman ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Duk hankalina ya tashi na d’auka jikin naki ne ya motsa.” Murmushi Hudan tayi tana k’arasa zama a kan gado kafin tace “Da sauki Alhamdulillah, ai na fad’a miki na warke fa Mama ki daina d’aga hankalinki.” Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e sannan tace “Gobe zamu zo mu dubaki ni da Ummu in shaa Allah.” Hudan, cikin d’an zaro ido na murna tana murmushi tace “Na gode kuwa sosai Mama zan ji dad’i, sai kin zo.” Murmushi itama Maman tayi kafin tace “take care, kina dai shan maganinki ko? Na sanki da k’in shan magani.” Cikin yin y’ar dariya Hudan tace “Maama kin manta Sakina na tare dani.” Y’ar k’aramar dariya taji itama Maman tayi kafin tace “Hakane fa, sai mun zo goben in shaa Allah, Hajiya ma tace a gaida ke!” A hankali Hudan tace “kiran ki tayi? Kun shirya? Na ga rannan ma tayi miki magana a gida lokacin a gaban kowa.” Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace “Kirana tayi takanas Hudan dan taji jikinki da kuma yanda nake” ta k’arashe maganar tana share hawayenta. Murmushi Hudan tayi itama kwalla ta zubo mata, kafin tace “Alhamdulillah” Tana share hawaye sannan tace “Sai kun zo Mama” Tana murmushi, itama murmushin tayi sukai sallama ta kashe wayar. Cike da nishad’i Abba dake tsaye a kanta yace “Y’ar gidan Mama” Cikin yanayin zolaya. Cikin d’an murmushi tace “Wai hankalinta ya kasa kwanciya gobe zata zo ta ganni” ta k’arashe maganar cike da zumud’i. Murmushi Abban yayi sannan yace “Allah ya kaimu goben” ya shafa kanta tukun ya juya ya fita. “Sai da safe” Shuraim yayi mata, Sudais ma haka, yayi pecking cheek d’inta sannan ya fita. A hankali ta kwanta ta lumshe idanunta ahaka Sakina ta shigo ta sameta. Nan take fad’a mata good news d’in! Ta kuwa yi murna, sannan tace “Ai daman lokacin dana ce mata har a asibiti kika kwanta baki ji yanda hankalinta ya tashi ba, daman na san ba lalle ta iya hak’ura ba, sai tazo. Allah ya kaimu goben ya kawosu lafiya.” A hankali Hudan tace “ameen” tana hamma...... Tun da suka tashi da safe suke expecting d’in su Mama, har girki suka d’anyi musu dukda rashin k’arfin jikinta sai shirye shirye suke yi. Suna cikin setting dining Abba ya shigo, murmushi yayi a ranshi yana yaba irin k’aunar da y’ar tasa take yi wa Maman ta. Sai da yazo ya dafa kanta tukunna ma ta fahimci ya shigo. Gaishesa suka yi ya amsa musu cikin kulawa kafin yace “Suje da Linda (mai girki) ta bata kayan wankinsu da suka tara, masu wanki zasu fara. Da mamaki yake kallonta, jin tace “Ai su kullum In suka cire kayansu a washing machine suka sakawa su wanke” Sannan ta k’ara da cewa “Akwai fa washing machine a toilet din nawa Abba” Murmushi yayi ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace mata “Na wanke inners ne wannan dota. Next time ku tara akwai masu wanki da guga da suke yi, time to time. Yanzu ku bata kayan ta kai musu sai a goge” Da ‘to’ suka amsa ya wuce Sakina ma ta kira Linda suka wuce domin ta bata kayan, ta bar Huda anan tana ci gaba da setting dining. Sai bayan sallar azahar, Ummu tayi musu waya tace “su fito, suna waje.” Sai da suka gayawa Abbas tukunna suka fita…. Babu yadda basu yi da su ba akan su shigo ciki amman suka k’i shiga gidan. Sun d’an jima a wajen, dan ma unguwar ba mai mutane da yawa bace ba dan babu k’afa a layin, shima titin shiruuuu. Daga baya Mama ta bawa Hudan ledar su tsami gayen da tace ta taho mata dasu. Aikuwa taji dad’i sosai, ta dinga murna, nan Mama ta cewa Sakina “kar su durfafi mand’on suyi ta sha fa dan in suka sha da yawa zai kunche musu ciki.” Mama, tunda sukazo dama taga wata adaidaita sahu tayi parking, sai yanzu taga mai mashin d’in yana juyowa, kamar ance ta kalli cikin napep d’in suka had’a ido da Baba! A take gabanta ya yanke yayi wani irin fad’uwa! Sannan zufa ta hau keto mata ta ko wacce b’ular gashin dake jikinta… Daman tun da safe da tace masa “za su fita ita da Ummu” taga kamar rashin yarda a fuskarshi. Laifinta d’aya da tak’i fad’a masa gaskiya wanda ita kuma dalilinta shine ‘Ta san ba barinta zai yi ba’ ita kuma har ga Allah tana so tazo taga Huda. Dafa ta d’in da Ummu tayi ne yasa ta d’anyi firgigit ta dawo cikin haiyyacinta, tana mai k’ak’alo murmushi. Cikin d’an k’arfin hali ta cewa su Huda “su koma gida, kar a ga sun dad’e.” Sai da suka d’anyi y’ar kwallar su, tukunna suka rabu bayan ta sake tambayar Hudan akan “tana son Arshaad d’in?” Hudan kuma ta amsa mata da ‘eh’ sannan suka wuce… …Tunda Ummu da Madu suka zaunar da ita( Mama) suka fahimtar da ita sosai ta d’an dawo saita, tana k’ok’ari taga ta jaa y’arta itama a jiki su zauna lafiya wata rana sai labari…fushi da turjiya ba inda yake kai mutum sai garin dana sani, In Allah yayi auren yanzu shine mafi alkhairi kuma sai anyi a yanzun to fa idan ta dage tace zata hana tsaf rabo zai iya kasheta! Shiyasa tun ranar farko a waya bayan su Hudan sun dawo da ta tambayeta ita kuma Hudan tace mata ‘eh, tana sonshi’ shikenan Mama ta shafe komai, ta rungumi abunda Allah ya k’addaro da hannu bibbiyu……. Da kyar suka samu adaidaita sahu, Ummu dai ta lura akwai abunda ya firgita Mama amman ganin tayi tanbayar har ta gaji bata bata amsar komai ba ya sanya kawai ta kyaleta, a tunaninta maybe ko Abba ta gani. Mama aka fara ajjiyewa, sannan Ummu suka wuce ita da mai napep d’in ko shiga bata yi ba dan yau week end so tana son yin kwalema, saboda tun da Sakina ta tafi aiyuka duk sun yi mata yawa sun ch’ab’e mata. Tun a soro taga machine d’in Baba kamar yanda ta fita ta bari, amman k’ofar d’akin shi a rufe da kwad’o! Tunani ta fara a ranta tace “kenan bai dawo ya d’auka ba ko dai aiki ya wuce a napep d’in? Mai yasa ma ya bisu a napep in the first place?….” Da wannan tunanin ta k’arasa k’ofar d’akinta ta zaro makulli a y’ar purse d’inta. Gidan shiruuu, ba kowa. Tana d’aura makullin a ramin shi taji k’ofar tayi motsi! A take gabanta ya yanke ya fad’i. A hankali ta d’an tura k’ofar, ga mamakinta sai ta ga ta bud’u! Cikin rawar murya tayi sallama tare da kutsa kai ta shiga ciki. Turus! Haka ta ja ta tsaya sakamokon ido hud’u da suka yi da Baba wand yake a kwance a kan gadon nata yayi pillow da hannuwanshi akan pillows d’in da ya d’aura kanshi, ya d’aura k’afa d’aya kan d’aya yana d’an jijjigawa…. Ba abunda yafi d’agawa Mama hankali sai yanda taga idanun Baba sun sauya kala! Idan aka ce mata tunda ya dawo yake kuka tabbas ba zata musa ba domin kuwa idanunsa sun yi jaaaaa!! Sun k’ank’ance hatta fuskarshi sai da ta d’an kumbura. Bata gama fahimtar yanayin da yake ciki ba taji yace “Ai nayi tunanin ba zaki dawo nan ba!” Yayi maganar yana mik’ewa ya isa k’ofar d’akin, kawai taga ya sa key ya juyo yana kallon ta. A take wani mugun tsoro

Chapter 17 of 28