Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi wanka ko alwalla sai taje bakin k’ofar ta lab’e mishi har sai ya fito sai kace wani wanda akace mata zai b’ace! Dagashi har ita ba wanda ya samu bacci jiya Idan ka gansu duk a gigice. Ko da Aaima ta kawo musu breakfast ma ba wanda ya tab’a har yanzunnan Tun jiyan da ta shigo har yanzu ba wanda ya cewa wani uffan a tsakaninsu. Amman duk wani motsinshi idanunta na akanshi. Ba abunda yafi d’aga mishi hankali kuma ya bashi mamaki irin yanda ta kasa tashi ko sallah tayi Yanzu haka yana lura da yadda ta kasa zama mai kyau sai faman mutsu mutsu take yi wanda ya tabbatar fitsari take ji amman gudun kar ta shiga ya gudu ta gwammace ta zauna a haka!. Suna a haka Dad ya shigo cikin d’akin. Yayi mamamkin ganinta a zaune amman sai ya d’auke kai kawai ya maida hankalinshi ga Arshaad, ransa a d’an b’ace yace “Ka san fa k’arfe 11:30pm ne d’aurin auren, uban me kake yi a zaune a haka?” A hankali yace “Ina kwana Dad” “Lafiya” kawai yace masa, daga nan ya nemi waje ya zauna kafin yace “Mik’e maza, yanzun nan Aslam zai kawo maka kayanka” A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya yanayin k’asa k’asa yana kallon Mammy wadda ta d’auke kai tana kallon gefe. Mik’ewa yayi jikinshi ba kwari ya fad’a band’aki! Ya kai kusan 20 minutes tukunna ya fito sanye da bathrobe a d’akin ya tarar da Aslam sanye cikin sky blue d’in rantsattsiyar shadda aikin gaban rigar white da d’an ratsin blue ya murza farar hula mai asalin kyau da tsada sai kyalli take yi da farin takalmi hatta agogon hannunshi white ne. Yana rik’e da babbar rigarshi a hannu wadda take a ninke, k’amshinsa gaba d’aya ya cika ilahirin d’akin…. Suna had’a ido ya sakar mishi murmushi a hankali yace “Ango” Murmushi shima Arshaad d’in yayi sannan ya wuce jikin wardrobe d’inshi ya na mamakin ta yanda zai shirya a gaban waennnan body guards d’in! Inner wears d’inshi ya kwasa ya d’auki jakar kayan da yaga an ajjiye akan gadon ya juya ya wuce toilet. Bai yi minti biyar cikakku ba ya fito! Murmushi Dad yayi yana kallon shi yana mai jin wani sanyi a ranshi! Kana ganinshi kaga Ango.. A hankali jikinshi a mugun sanyaye ya k’arasa gaban mirror ya d’an shafa mai sama sama a hannu da fuskar shi sannan da k’afa, ya fesa perfumes ya d’auko takalmin da ya fito da shi a jakar kayan nashi ya sanya… Farar shadda ce k’all! Mai babbar riga sai bak’in takalmi hula da agogo.. Yana gyara d’aurin agogon suka ji knocking Aslam ne ya juya ya d’an bud’e k’ofar dake a kusanta yake. Da mamaki yake kallon Abba da Daddy da Auwal a bayansu. Dad Abba da Daddy duk ankon shadda ruwan goro light suka yi, aikin rigar ciki da babbar rigarsu kuma na kalar kayan amman dark sosai Sai hulunansu zannah bukar d’in da suka amsa sunansu ZANNAH bukar! Amman kowa da design d’inshi, takalmansu kuma na fata kalar ruwan goro masu mugun kyau da tsada iri d’aya. Yayinda Auwal ke sanye da maroon shadda shima ya murza zannah bukar d’inshi mai asalin kyau da tsada. Cikin girmamawa Aslam ya gaida su Abba Daddy ne yayi dariya yace “Kaga yau har da mu a y’an sneaking a shigo estate ko?” Murmushi kawai Aslam d’in yayi. Kallonshi kawai Abba yake yi… Ya manta when last da ya ganshi da manya kaya, ba k’aramin kyau yayi ba, har ga Allah Aslam ba wai favorite d’in Granpa bane kad’ai Har da shima Aslam ne favorite d’inshi! Kawai dai shi d’in baya nunawa ne Yaron akwai hankali da nutsuwa da sanin ya kamata “Ina ma inama! How i wish......” Ya fad’i hakan a ranshi sai kuma yayi saurin kawar da tunanin ya juya suka fara gaisawa da Dad. Daga shi har Daddy ba wanda ya kalli ko inda Mammy take Kuma sarai sun ganta dan har had’a ido suka yi da Abba! Hakan kuwa ba k’aramin sake ingizata yayi ba Tabbas yau sai ta nuna musu ta isa wallahi! Chap!! Arshaad ya shirya dan haka suma duk suka mik’e dan har an fara jera musu kira Abokanan su sun fara zxuwa venue d’in.. Ba tare da Mammy ta motsa ba tace “Arshaad!” Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna ya juyo yace “Na’am Mammy” Mik’ewa tayi tsaye tace “Koma ka zauna” Sannan ta dubi su Dad waenda suke kallonta gaba d’ayansu tace “Kuna iya wucewa ku tafi! D’a dai ni na haifa ko? To wallahi tallahi ba wanda ya isa ya yi mini iko da shi! Da kuka shigo kuka wani banzatar dani kamar baku ga mutum ba saboda ban kai ba har kai Abba! Kalla Auwal shima Aslam ne kawai ya gaidani ya kulani a kaff d’inku saboda ka riga ka nuna musu bani da mutunci bani da daraja a idanunka! To Yanzu ni kuma zan nuna muku na isa dan wallahi ba za a d’aura auren nan ba kaji dai na rantse!” Murmushin takaici Dad yayi kafin yace “Dole ba wanda zai kulaki mana Rukayya! Saboda kema baki kula wanda ya kamata ki kula ba, ko kin gaida ni tunda na shigo?” Ganin ta kauda kanta gefe ya sanya kawai ya girgiza kai kafin yace “Kaga Arshaad wuce mu tafi! Zan ga wanda zai hanaka fita yau” Mammy ya kalla, suna had’a ido tace “In dai kana neman albarka a auren nan to ka sani ba zan tab’a saka maka ita ba! Kuma wallahi Arshaad in dai ka fita a d’akin nan to ban yafe maka ba!” Da k’arfi ya runtse idanuwanshi yana ji kanshi na mugun sara mishi. A zafafe Dad ya yunk’ura zai yi magana da sauri Daddy ya katseshi ta hanyar cewa “Dan Allah dan Annabi ka kyaleta, Uwa ba abar wasa bace ba! Dole Arshaad da Huda suna buk’atar albarka ta Dole.” Yana gama fad’in haka ya juya ga Mammyn yace “Mammy mu tsaya mu fahimci juna, wannan maganar bata tasoba. Ki duba shi kanshi Yaron naki mana za fa ki cutar dashi saboda son zuciyarki sannan da ita kanta Hudan, babufa abu mafi gorantawa a rayuwar y’a mace kamar azo aurenta a fasa!..” Cikin katseshi Mammy tace “Yi mini shiru Yusuf!” Sai da Daddy da Auwal suka d’an zabura jin yanda ta kirashi . Bata damuba taci gaba “Babu maganar sulhu fa a tsakaninmu! Maganace na riga na yita na gama, babu kuma uban wanda ya isa ya sanya ni in chanja wallahi!” Cikin tsiwa da masifa tace “Kuma kar ka wani ce mini In duba rayuwar wata Huda dan babu abunda ya shafeni da ita! Allah Ubangiji yasa a yi ta mata gori a had’a har da kyama da hantara daganan har k’arshen rayuwarta wannan ba damuwa ta bace ba.” A hankali Aslam ya lumshe idanuwanshi. Ba tare da Abba ya kula kowa a cikin su ba kawai ya juya ya fita, da sauri Aslam ya bi bayanshi. Takawa Dad yayi ya tsaya a gabanta sannan yace “Rukayya bani da ishashshen lokaci! Ki nutsu ki shiga hankalinki kiyi abunda ya dace, for the last time ina mai shawartarki ki ajjiye wannan haukar ki bari a d’aurawa Yaron nan aure.” Cikin katseshi ido cikin ido ta kalleshi kafin tace “Yahaya! Ko da ace ka bar nan ka tafi kai kad’ai ba tare da Arshaad ba Wallahi muddin ka d’aura mishi aure da Huda wallahi tallahi billahilazim sai na tsine mishi!” Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauk’e kawai ba tare da yace mata uffan ba ya juya, har ya kai bakin k’ofa sai kuma ya juyo yana kallon Arshaad wanda shima shi d’in yake kallo Wani mugun tausayinshi ne ya lullub’e shi lokaci guda, a hankali yace masa “ka zauna, kar kaje koina bara muje mu dawo .” Yana gama fad’in haka ya juya ya fita, su Daddy ma suka bishi a baya. Abba ko Aslam bai tsaya jira ba ya shiga motarshi suka yi gaba tare da su Shuraim, dama suna ciki anan suka barsu. Aslam na shrin shiga motar shi shima yabi bayan Abba su Dad suka fito “Wuce mu tafi masallacin” Haka kawai Dad yace mishi daganan kowa ya shiga motarshi sukai gaba. Aslam ya dad’e a tsaye so yayi ace ya bi bayan Abba dan ya san definately gida ya koma, saboda yaga yadda ranshi yake a b’ace! Ga shi daman shima so yake ya zille maybe he can use this as an opportunity. Har zai bishi sai kuma kawai ya yanke shawarar bin bayan su Dad d’in. Da kyar ya iya tada motar dan yafi minti goma a ciki a zaune bayan ya shiga d’in, daga k’arshe dai ya tada motar ya fice daga estate d’in….. A hankali yake driving, babu nisa sosai dan haka mintuna k’alilan ne suka kaishi masallacin. Da mamaki yake kallon motar Abba a parke a harabar masallacin! Kokwanto ya hau yi akan anya kuwa motar tashi ce? Sudais da ya gani ya nufo shi ne ya tabbatar mishi da Abban nan ya yo.. Chan kuma ya hango suna gaisawa shi da su Madu cikin tsananin farin ciki da nishad’i. Auwal ne ya dafa shi dan haka yayi saurin juyowa Kwata kwata in banda k’unci da firgici ba abunda ya hango a shimfid’e kan fuskar Auwal d’in! Yana mamakin abunda ya sanyashi a wannan yanayin yaji yace “Aslam dan Allah idan sun zo kace......” “Ku wuce muje mana! Ya naga kun tsaya anan?” Muryar Dad ta katsesu. Kallon Auwal d’in yayi ya kalli Dad sannan yace “Ok” Kawai, ya juya ya yi gaba…. Duk taku d’aya ji yake kamar yana kusanta kanshi da kabarinshine! Tabbas badaban Mommy ta rok’e shi akan ya zauna a garin nan ba to da tuni baya nan! Babu yadda bai yi da ita ba d’azu amman nan ma furr! Ta ki yarda, ta nace ta tilastamishi dole sai da yazo wajen nan! He might look calm but tabbas ya san ba lalle k’afafuwan shi su iya fitar dashi daga masallacin nan ba! Wannan wacce iriyar k’addara ce? Mai yasa yake jin hakan har yanzu? Mai yasa yake jin haka? Garin yaya ya bari hakan take faruwa da shi…..? A hankali yaji Abba yace “Aslam” Firgigit! Haka yayi hankalinshi ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi, sai a sannan ne ya ga yana daff da yin karo da bango ashe, da sauri ya ja burki! Sannan ya juyo da kanshi yana kallon Abba wanda yake matsowa daff da shi sosai. A hankali ya kama hannunshi ya d’an jashi gefe.. Da d’an murmushi akan fuskarshi yana mai kallonshi sannan ya fara magana “Watak’il yau in yi maka laifi! Amman dan Allah Aslam ko menene ya faru karka bad’a mini k’asa a ido” Da mamaki yake kallonshi zuciyarshi tana dukan uku uku! Dan a take a yanzun tunani d’aya ne kawai ya fad’o mishi daga jin furucin Abba na yanzun! Da mugun sauri ya fara kokawa da zuciyar shi yana k’ok’arin kawar da tunanin dan jiya ma ba k’aramin artabu ya sha ba! Ko rintsawa bai yi ba ata dalilin false hope d’in da Mommy ta sa ya d’aurawa kanshi. Dafa shi Abba yayi sannan yace “mu shiga” Yana gama fad’in haka ya wuce ciki. Da kyar Aslam ya iya jan k’afafuwan shi, ya shiga ya nemi waje ya zauna kusa da Abba daff da liman da su Daddy Opposite Auwal. Kana ganin Auwal tashi d’aya zaka gane bashi da nutsuwa kwata kwata! Ko zaman kirki ya kasa yi a wajen, sai zaro waya yake da alamun kira yake yi amman kuma ba a d’auka! A fili sannan da k’arfi yace “damn it!!” Sannan yayi jifa da wayar tashi wanda hakan ya janyo hankulan mutane kanshi…. Suna had’a ido da Daddy ya zabga mishi harara. A hankali ya sunkuyar da kanshi ya d’au wayar sannan yace “Sorry”. Hannu Dad ya mik’a mishi alamun ya bashi wayar!. Ba musu ya mik’a mishi shi kuma ya sa hannun ya karb’a ya saka ta a aljihu daga nan aka fara gabatar da d’aurin aure…….. Auwal k’ok’ari yake yi su had’a ido da Aslam sai dai kuma Aslam d’in yak’i d’ago da kanshi kuma kamar ma idanuwanshi a rufe suke. A bangaren Aslam kuwa zai iya cewa ya jima bai shiga irin wannan tashin hankalin a rayuwarshi ba! Mai yasa ya yarda yazo nan? Wanne irin heartbreak zai yi facin? Yanzu kenan a gaban idanunsa yana ji yana gani za ayi komai.... “Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun....” Ya furta a hankali sosai! Baya ganin komai zuwa yanzu shiyasa ya runtse idanuwanshi kawai yana jiran lokacin da zai farka ya ganshi a gadon asibiti ko kuma yaji ance mishi Man rabbuka?!….. Yana jin su sama sama Daddy ya gabatar da kanshi a matsayin waliyyin Amarya Dad kuma a matsayin waliyyin Ango! Da k’arfi zuciyarshi ta buga jin limamin yace “Waliyyin Ango yana nemawa Yakubu Aslam auren Maryam Huda!” Bud’e idanuwansa yayi tarr!!! Ya fara ganin komai. Kaii inaa bai ji da kyau ba! Ko kuma dai sunan waliyyin Amarya aka ambata dai ko wani abun daban…. Da sauri ya d’ago jajayen idanuwanshi yana kallon Daddy jin yace “Mun bayar” Limamin kuma yana cewa “sun yarda cinta shanta suturarta komai ya koma hannunsu? Hannun Yakubu Aslam.” Bai gama fita daga shock ba Yaji Dad yace “Mun yarda! Mun karb’a!” Zuwa yanzu gaba d’aya jikin Aslam in banda karkarwa ba abunda yake yi gashi ya had’a wata uwar zufa! Tashi d’aya. Tun daga nan kanshi ya kulle jinsa ya d’auke! Binsu kawai yake yi da ido suna gudanar da d’aurin auren!. Yana kallo Dad ya zaro kud’i ya mik’awa Daddy! Limami ya sanar shedu suka shaida… Jin shi bai tashi dawowa ba sai da muryar limami ta fara tashin amo a cikin masallacin “Alhamdulillah!!! An d’aura auren Yakubu Yahaya Umar Faruku MT Aslam Da Amaryarsa Maryam Yakubu Huda akan sadaki naira dubu d’ari biyu! Lakadan ba ajalan ba. BULAMA ✍️ An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 28 of 28