amman abun ya faskara!.
Baaba Talatu ce ta k’arasa ta ja wannan tsohuwar gefe suka had’u ita da Shuwa suna mata magana k’asa k’asa…
Ganin kamar ana shirin fara traditional event d’in
cikin kwanciyar hankali ne yasanya Umma ta sake cewa
“Nima fa kamar uwa nake a wajen Hudan!
Dan haka ba zan bari kowa ya tab’a ta ba har sai Angon nata ya k’araso..
idam kuma fasawa yayi ne to kawai a fito a fad’a wa mutane sai a fasa sakata a lallen,
dan ba girman mu bane mu tsaya muna yiwa mutane wasa da hankali!
Ko ya kuka gani?”
Ta k’arashe maganar tana kallon cousins d’in Ummu waenda suke gefen ta! Ba su kad’ai ba kusan kaff wajen babu wanda bai ji abinda tace ba hatta su Shuwa.
“Ga Angon nan”
Muryar Mommy wadda suka fito su uku yanzu ta daki dodon kunnuwansu!
Da sauri Mama da Aslam suka kalleta!
Ba tare da ta kallesu ba ta
kama hannun Aslam ta fara janshi
Mama na binsu a baya kamar rak’umi da akala shi kuma yana binta!..
Bata cikashi ba sai da ta kaishi gefen Hudan sannan ta zaunar da shi.
Da sauri Ummu ta matso k’asa k’asa tace
“Mommy a Al’ada fa dole sai Angon zai....
Cikin katseta Mommy tace
“A addini fa?”
Bata jira Ummu ta bata amsa ba ta sake ce mata
“Kalla nan kinga”
Tayi maganar tana
nuna mata Huda wadda sai a lokacin Ummu ta lura da yanda mayafinta ya jik’e sharkaf!
Wanda kana gani ka san ruwan hawaye ne…
Mommy bata jira jin me zata ce ba ta ci gaba da yi mata magana k’asa k’asa irin na masu hankali,
tace
“Saboda ita kawai ki bari ayi a gama!
Na tabbatar ba wai rashin zuwan Arshaad kad’ai bane ya saka ta kuka ba! Har da maganganun matar nan! Tun muna parlourn bayankun nan muke juyo komai.
Dan Allah kar kice a’a!
Kalla kiga mutane kowa ya zuba ido an fara k’ananun maganganu, na tabbatar in dai ba Angon suka gani ba to haka za a tashi ana gulmace gulmace shima kuma sai idan an samu waenchan matan sun bari anyi d’in kenan.
Na tabbatar mutane k’alilan ne kuma na jikinku sosai suka san ba Arshaad bane wannan, ba kowa ne zai gane ba
so dan Allah ki kwantar da hankalinki ayi abun nan a gama without any more dramas.
Saka lalle ai ba d’aurin aure bane ba, ba komai kawai bidi’a ce so mu bisu kawai ayi a gama.”
Tana gama fad’an haka ta juya ga jamaar wajen tace
“Kuyi hak’uri mun yi latti wani d’an uzuri ne ya tsaida mu!
Sunana Hajiya Aisha
Maman Ango, mun gode kwarai da zuwanku dan taya mu farin ciki.”
Daga nan ta juya ta cewa
Ummu
“Ni zan fara ko ke?”
Da murmushi kwance akan fuskarta.
Kallonta kawai suke yi
daga Ummu har Mama.....……
Mama da Ummu sun so hana mai video coverage da pics d’auka amman ganin yanda hankalin kowa yake a kansu
da kuma Mommy wadda tace ‘su bari kawai tunda ga wasu ma a gefe suna ta d’auka da waya’ ne ya sanya
kawai suka hak’ura.
K’awayen su Huda kuwa abun ba k’aramin d’aure musu kai yayi ba dan tabbas sun san wannan ba da shi akayi cocktail jiya ba, kuma ba shine a pre wedding ba!
A haka dai suka bar maganar akan in an tashi za suni komai a bakin Sakina....
Aslam kuwa so yake ya mik’e amman sam ya kasa!
Ya rasa dalili..tun da yake bai tab’a jin fargaba irin wadda yake ciki a halin yanzu ba!
Ana cewa k’afafuwa da gangar jikin mutun suna sagewa ya koma kamar gunki bai tab’a yarda da hakan ba sai yau da ya faru a kansa dan hatta kwayar idanunsa ya kasa juyawa, so yake ya runtse idanuwanshi ya samu ya dedeta zuciyar shi amman sam ya kasa!
Yana nan a haka yaji Ummu na rufa mishi wata jibgegiyar alkyabba akan jamfar jikinshi
Akan hular kanshi
Ummu ta d’aura mishi wani jan kyalle mai tambarin moon a gaba golden colour
(Allah yaso suna da extra)
Daga nan ta mik’a mishi wata sanda wadda ta ci ado! Tace masa “ungo, rik’e”
Mommy ce ta kama hannunshi ta sanya mishi
sandar sannan ta had’a da nata hannun ta maste!
Sai a lokacin ya samu nasarar lumshe idanuwanshi
sannan ya d’an bud’e su kad’an yana kallon k’asa....
Ba tare da b’ata lokaci ba aka fara gudanar da alada……..
Bayan uwar Amarya da uwar Ango sun yi, ragowar jama a suma suka zo suka sanya musu suka basu gift
daga nan aka fara serving abinci.
Sai a lokacin Anty Zainab da Umma suka samu suka iya zama…Umma so take yi ta sake mik’ewa tsaye tace
“To Ina y’an unwan Ango!?” ta sake creating scene amman sam ta kaasa dan in banda
dishi dishi babu abunda take gani! A ranta ta shiga aiyyana
…..Tabbas sai taci uwar malan ado! Wallahi sai ta saka an yi mishi yasin mai walk’iya!
Ba Malami ba ko uban waye shi. Kuma sai ya bata kud’inta.
Jiya jiyan nan fa ta sake komawa wajenshi dan ta sake nanata mishi, shi kuma ya
tabbatar mata da “babu aure tsakanin Hudan da Arshaad
ya riga ya gama aiki
kuma ya buga k’asa ya tabbatar ba Mijin ta bane ba
sannan
ya ingiza zuciyar iyayen shi (Arshaad) ya rura wutar k’iyayyar Hudan a cikinta
ta yanda ba zasu tab’a bari ayi auren ba musamman ma Mahaifiyarshi (Arshaad)…”
Amman kalli yadda Maman nasa taketa jan Hudan a jiki,
anyi musu hoto yafi kala nawa tare sai faman fara’a take yi tana washe baki kana ganinta ka san tana cikin tsantsar farin ciki….Inaaaaa!!!!!
Taya ma zata tsaya ta yarda Hudan ta auri wannan
No1 kyakkyawan da ita tunda take a rayuwarta ko a telebijin bata tab’a ganin mai kyawunsa ba! Ga uban kud’i ga kyau kamar aljani
Allah sarki Jalilan ta
dole ta mutu akan soyayyar Arshaad, ai kuwa idan zata yi yawo tsirara wallahi sai ta raba auren Huda da Arshaad ko sama da k’asa zasu had’e
Wallahi sai dai in rabo ya kasheta akan dai ta zauna ta nad’i wannan abun takaicin da ta san k’arshe in dai bata d’auki mataki ba to shine ajalinta!
Kuma ko yana so ko baya so sai ya auri Jalila!
Wannan alkawari ne ta d’aukarwa Jalila da ita kanta!
D’an halal ka fasa……..
Anty Zainab ce ta tab’o ta
wanda hakan ne ya katse mata tunani.
Da kyar ta iya motsa wuyanta dan ji take kamar ba jini da rai a dukkannin ilahirin jikinta
Suna had’a ido taga itama Anty Zainab d’in idanuwanta sun kad’a sun yi jazir!
Kafin Umman tace wani abu
taji tace
“Sadiya taso mu tafi,
kai na ciwo yake yi min”
Suna shirin mik’ewa
suka fara jiyo gud’a daga parlourn Madu sai a sannan ma suka lura Shuwa da Baaba Talatu da wasu y’an tsirrun mutane basa wajen
A bakin matan wajen sukaji an fara k’us k’us d’in
“Ashe tun d’azu mazan gidan Ango suka zo sun kawo lefe yanzu suka wuce
da yake falon Madu yana da k’ofar shiga da fita ta waje, shiyasa har suka zo suka tafi ba wanda ya sani
Sai da suka tafi yanzu akace aje a fito da shi” Sunaji anata k’usk’us d’in “ai motocin da suka zo da su ma kansu abun kallo ne!
Gasu kana ganinsu kaga manyan mutanen da kud’i ya zaunamawa”
Da kyar Umma take iya jan numfashi, dan ji take yi gaba d’aya iskar wajen bata isarta!.
Ummu ce ta d’an matsosu kafin tace
“Umma kuzo muje a fito da lefen nan kowa ya gani ko?”
Anty Zainab ce ta iya ce mata “eh”
Itanma da kyar,
daga haka ta mik’e ta d’an dafa Umma kana tace
“Muje Sadiya”
Da kyar ta iya mik’ewa k’afafun ta suna rawa suka jera ita da Anty Zainab suka bi bayan Ummu suka yi parlourn b’aki.
Mutane kam wasu basu ma samu damar shiga ba
dan akwatunan sun cike parlourn tap!
Ganin kowa cirko cirko a tsaye iya y’an k’alilan kuma na a ciki suna mik’owa ana fitowa da shi ne yasa suma suka ja suka tsaya a gefe
kai kana ganinsu ka san basa cikin hayyacin su..
Ta gabansu aka fara wucewa da akwatuna
nan kuwa suka maida hankali suka hau k’irgawa!
Ana wucewa da goma
Umma ta nemi d’an dakalin slop ta zauna dan jiri ne taji yaana d’ibarta ba na wasaba!
A tunaninta su kenan
amman ga mamakinta sai taga ana ta sake fito da wasu!
Ganin ta k’irga ashirin da d’aya basu k’are ba ya sanya
ta janyo Anty Zainab wadda itama tayi mutuwar tsaye kafin tace
“Zainab zo mu bar wajen nan,
tabbas kwakwalwa ta ta d’an samu matsala sannan bana gani sosai!
Gani nake yi anata wucewa da akwatuna fa har yanzu basu k’are ba.”
Da sauri Anty Zainab d’in tad’an dafa ta
dan yanda take magana da sauri kuma da k’arfi kamar wata zararra ya sanya mutane har sun fara d’an juyowa ana kallonsu. A hankali tace mata
“Ba idonki bane!
Ashirin da hud’u ne cass! Gasu chan ragowar ukun
Sai kuma waenchan baskets d’in da ban san na menene ba”
Bata ida rufe bakinta ba aka fara fito da na Gwaggo da Kawu.
Ai kuwa
Umma bata san lokacin da ta mik’e tsaye ba tace
“Amman dai Maryam sayar da y’ar nan tata tayi ko!?
Haba mana wannan abu kuma ai ya zama hauka!
Meye hakan? Me sukeso su nuna?”
Cikin takaici Anty Zainab tace
“Wallahi Sadiya za kiyi hanyarki nima inyi tawa har a tashi daga bikin nan gaskiya!
Maganar Allah kenan, haba mana! So kika mu zama abun kwatance?
Sai wasu abubuwa kike yi kamar tab’abb’iya?
Kiyi controlling kanki mana
Haba?”
Ta fad’i hakan tana mai wucewa ta barta a tsaye nan dan a yanda take jin zuciyarta yanzu, tsaf zata iya sauk’e ruwan bala’i da fushinta akan matan dake k’ok’arin maidasu telebijin….
Sai da Umma taga an gama fito da kayan an watse daga wajen sannan ta samu da kyar taja y’an k’afafuwanta ta isa harabar tsakar gidan.
Banda gud’a da hayaniyar mata ba abunda yake tashi
A lokacin har an bud’e akwatunan farko an fara dubawa….
Sai a sannan ne Aslam ya samu ya tatttaro nutsuwar shi da d’an ragowar kuzarinsa ya mik’e tsaye!
Yana mik’ewa Ummu da Mommy suka k’arasa wajensu..
D’an b’ata rai yayi kafin yace “Mommy zan wuce
wannan bidi’ar bada ni ba gaskiya”
Murmushi Mommy tayi ta shafa kanshi kafin
ta juyo ta cewa Ummu
“Zai iya tafiya?”
Murmushi Ummun tayi kafin tace “eh, zai iya ai an gama komai”
A hankali yace mata
“Sai anjima”
Cikin kulawa tace
“Mun gode kwarai Aslam,
mun gode.”
Ajiyar zuciya kawai ya sauk’e
daga nan ya ajjiye sandar hannunshi a gefe ya juya
dai dai nan su Sudais suma suka mik’e
Shuraim yana ta b’ata rai shi ala dole ya gaji..
Ummu da Mommy ne suka yi musu rakiya har waje, shi da Sudais da Shuraim bayan ya kira drivern da zai maida Mommy gida yace masa ya taho yanzun…
Mutane in banda kallonsu ba abunda suke yi sunata yaba kyawun Angon
Gashi bai wani zak’e ba irin yanda Angwayen yanzu suke yi! Instead shi ya kama kanshi matuk’a, hakan kuwa ba k’aramin burge jamaar wajen yayi ba.
Su Mommy suna komawa
suka tarar anata ware lefe an yi filla filla ana gani…
Tun daga kan atamfofi Umma ta raina kanta…
Zata iya cewa tunda Laraba ta kawota duniya bata taba shiga tashin hankali irin na wannan lokacin ba!
Hankalinta bai gama tashi ba sai da aka zo kan akwatunan jewelry’s
kit kit
waenda aka ware guda biyu aka shak’e taff da sark’a da y’an kunne
Na farkon fashion ne
Na biyun kuwa gold ne zalla!
Matar dake gefen ta ce taji tana cewa
“Ai dama su family d’in MT haka suke lefe duk matan gidan da aka tashi aurar su ko wacce sai da aka yi mata kit d’in gold!
Yanzu kuma wannan kinga shine jika na farko da yayi aure.
Kaii ammanfa wannan Yarinyar ta tako, gaskiya tayi goshi
Allah yasa y’ay’anmu a danshinta. Zata sha gata ba kad’an ba!
Naji ma kamar ance wai k’asar zai bari ma da ita gaba d’aya!”.
Tabbas zuwa wannan lokacin Umma ta daina ganin komai in banda duhu! Maganar ma sama sama ta dawo ji
daga nan kuma jinta da ganinta suka d’auke d’iff!!
Mutanen wajen kowa hankalinshi yana kan kallon lefe mai abun mamaki da alaajabi
Saboda kaff cikin su babu wadda zata ce ta tab’a ganin lefe kwatan kwacin wannan....
Dimmm!!!
K’arar fad’uwar Umma ta sa jamar dake kurkusa da ita zabura suka jujjuyo…..
“Subahanallah!
Mai ya sameta!!
D’in da aketa maimaitawa ne
ya janyo hankalin mutanen gurin kaff kowa akayi kanta akai mata rumfa......
A zaune Auwal ya tadda shi,
a d’akinsa. Ya jinginar da kanshi a jikin gadon ya lumshe idanuwanshi fuskar shi tayi jajawur! Kana ganinshi ka san yana cikin tashin hankali.
Auwal bai damu da yanayinshi ba dan shi ganinsa ma da yayi a zaune ko shirin tafiya bayayi shi yafi komai b’ata masa rai!
Cikin muryar b’acin rai yace
“Haba Arshaad!
Ka sa mutane sun tara jama’a kai kawai ake jira kazo ka wani zauna anan, me kake jira?
Gaka nan dai a shirye tsaf!
Mai kuma ya hana ka tafiya tun d’azun?
Nace maka ina zan taho karka jira ni.
Ka san yanda hankalinsu ya tashi kuwa?
Dagajin muryar Sakina ka san ba lafiya ba!
Taso mu tafi da sauri dallah”
Wata nannauyar ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e kafin a hankali ya samu ya d’an bud’e lumsassun dogayen idanuwanshi, sai da Auwal ya d’an zabura
sakamokon had’a ido da suka yi da Arshaad d’in!
Da kyar ake iya hango maroon eye balls d’inshi da suka b’uya cikin jajawur d’in idanun nasa.
Sai a lokacin Auwal ya lura da yanda jijiyoyin kanshi suka fito sukai rud’u rud’u!
Da sauri ya k’arasa ya zxauna a gefen shi kafin yace
“Lafiya kake??
Me ya sameka haka?”
Ya jera mishi tambayoyin
duk ya rikice.
Banda ajiyar zuciya ba abunda Arshaad yake ta faman sauk’ewa yama kasa yi mishi magana
Da kyar ya samu yace
“Mammy ce ta….”
Sai kuma yayi shiru.
Cikin firgici da tsoro
Auwal yace
“Ta hana ka zuwa??
Lumshe ido Arshaad yayi kafin a hankali yace
“Har ma auren! Tace idan aka d’aura sai ta tsine min!”
A zabure Auwal ya mik’e
kafin yace
“Innalillahi wa innailaihirrajiun!
Shine kuma ka zauna za ka kashe kanka haka?
Zama ai bai ganmu ba!
Bara in je in samu su Dad in yi musu bayani, idan ta kama har Granpa sai a sa a case d’in.
Mai yasa Mammy zata yi mana haka?”
Ya k’arashe maganar kamar mai shirin fashewa da kuka.
A hankali Arshaad d’in yace
“Ba wanda bai sani ba.
Kowa ya san da case d’innan.
Har mamanta da sisters d’inta duk an bata hak’uri amman tak’i hak’ura.”
Wata kakkausar ajiyar zuciya Auwal d’in ya sauk’e kafin yace
“Ya aka yi Mammyn ta sani?
Last time da naje na dubasu naga kamar duk basu san da zancen ba..
Na san dama suna iya causing problems shiyasa nima ban yi gigin fad’a musu komai ba!
Ko maybe Ummi da aka kawo ce ta kirasu ta gaya musu?”
Da d’an mamaki Arshaad d’in yake kallon shi kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yace
“Baka had’u da Mom ba hala?
Sun dawo jiya.
All of them”
Da mamamki shima Auwal d’in yake kallonshi ya ma kasa cewa komai.
A hankali Arshaad ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“Auwal do me a favour..
Ka kira Sakina, inaso kayi mata bayanin komai
amman kace kar ta fad’awa kowa kawai a san yanda zaai a gudanar da event d’in ba tare da an jira ni ba!
Yanzu na san Mammy idonta a kaina yake dan tun d’azu nake lura tanata turo Aaima tana mata patrol so ba zan iya fita ba.
Sakina is smart she’ll know what to do yanzun
In shaa Allah ni kuma anjima da daddare za mu je
Ina son ganin Hudan
na san abunda zan yi.
For now amman kawai ka lallab’a mun Sakina tayi handling komai, kafin nan da anjima.”
Cike da gamsuwa Auwal d’in ya d’aga kai alamar to
sannan ya zaro waya ya fara kiran Sakina.
Tun lokacin da aka fara rangad’a gud’a taji
dan haka ta mik’e ta lek’a ta windown d’akin Shuwa..
Ji tayi kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha sakamokon hango su su biyu a zaune da ta yi!
Bata ganin fuskar su especially Huda da har yanzu tata fuskar a lullub’e take sannan windown a rufe ne kuma sun yi mata nesa..
Bata san lokacin da hawayen farin ciki suka zubo mata ba!
Tana gani yanda mata suke zuwa suna d’an d’aga mayafin kad’an suna shafa mata da hannuwanta shi kuma a tafukan hannunshi da goshinsa ake shafawa
sannan su ajjiye musu gift a cikin d’an kwanon da aka ajjiye wasu kuma kud’i.
Ba k’aramin burgeta suka yi ba, banda kalmar ‘Alhamdulillah’ ba abunda taketa nanata
a ranta tana mamakin dalilin da ya sanya Aaima karkacewa ta gilla mata wannan uwar k’aryar haka
Wata zuciyar kuma tace maybe an gyara abunne Mammyn ta sauk’o
cikin kawar da tunanin a ranta tace
“Chan ta matse musu”
Sannan ta hau raya yanda zata yiwa Arshaad in sun had’u na k’in d’aukar wayarta da yayi.
K’arar wayarta dake kan gado ce ta katse mata tunani
dan haka ta isa ta d’auki wayar..
Kamar ba zata d’auka ba
ganin sunan Auwal ne sai
kuma ta d’anyi murmushi a ranta tace
‘Kar In zama kaza mana’
dan haka ta d’auka ta kara a kunnenta kafin yace komai tace
“Gashi chan Ya Arshaad d’in yazo suna zaune ana saka su a lalle.
Thanks for your time”
Tana gama fad’in haka ta katse kiran.
Da mamaki suka kalli juna shi da Arshaad dan a hands free wayar take
Shiruu, d’akin ya d’auka chan kuma Auwal yace
“Bara inje wajen maybe ko fushi suka yi shiyasa tayi min gatse”
Cikin katseshi Arshaad yace
“Kaje wajen Mom mana.
Kace bama ka san ta dawo ba
bayan a gida d’aya kuka kwana.
Kaje wajenta daga nan
ka d’an lallab’ata
may be in tasa baki Mammy ta hak’ura.”
Har ya d’anyi gaba sai kuma ya juyo yace
“Su kuma fa?”
“Kar ka damu na gama tsara komai, zuwa anjima da daddare za muje in shaa Allah.
Zan sameka a gida.”
Cewar Arshaad yana mai maida kanshi da lumshe ido dan kanshi ba k’aramin ciwo yake yi ba amma kuma har ga Allah y’ar maganar da ya samu suka yi da Auwal ya d’an ji sassauci a ranshi.
“Allah ya kaimu”
Shine kawai abunda Auwal yace yana me fita daga d’akin
da waya kare a kunnen shi still yana sake kiran Sakina
sai dai har ya tsinke bata d’auka ba.
A tsakiyar main parlourn suka kusa yin karo da Aaima,
kasancewar hankalinshi naga wayarshi yana turawa Sakina message.
D’agowa yayi yana kallonta
itam ma shi take kallo kafin da kyar ta iya cewa
“Ya Auwal Ina wuni”
“Fine”
kawai yace yana me wuce ta.
Da sauri ta sha gabanshi kafin tace
“Am dan Allah gida zaka je?”
Maida hankalinshi yayi a wayar kafin yace
“Eh”
A hankali tace “Owk, d’an jirani plss
Mammy ta bani sak’o wajen Mom ina so zan kai mata.
Bara in d’auko vail d’ina”.
Ba tare da ya kalletaba ya k’arasa kan d’ayan daga cikin kujerun parlourn ya zauna still yana danna wayarshi.
Ta fahimci yaren kuramen nashi dan haka ta wuce sama da d’an sauri …
Bayan 5 minutes ta sauk’o!
Ta chanza kaya daga atamfar ankon dake jikinta
ta d’aura bak’ar abaya tayi rolling, ta sanya lipstick da powder. Ta yi kyau kuwa ba laifi.
Gabanshi tazo ta tsaya sannan tace “muje”
Tun kafin sauk’owarta daman ya san ta taho sakamokon k’amshin turarenta da ya karad’e parlorn! Tana sauk’owa kuwa ya lura da ita amman sai ya kawar da kai…
Wai me Aaima take nufi ne?
Ya kasa gane kanta kwana biyun nan! Har magana take mishi ta WhatsApp yanzu.
Yana tunawa lokacin da suke tare yasha gaya mata yana matuk’ar son yaga mace da black abaya tayi rolling abun yana burgeshi shiyasa
kusan duk lokacin da zasu fita tare takan yi irin wannan shigar kuma ta san baya son native cloth kwata kwata
Inba riga da wando ba to abaya…..
“Mu tafi, na shirya”
Muryarta ta katse shi.
Kallonta yake yi tun daga sama har k’asa! Hakan kuwa ba k’aramin dad’i yayi mata ba.
A hankali taji yace
“Ina sak’on??”
Diriricewa tayi kafin da kyar tace
“Yana cikin purse d’innan”
Tayi maganar tana nuna mishi purse d’inta wadda ta saka iya wayarta da lipstick a ciki.
Ajiyar zuciya ya sauk’e
kafin ya mik’e yayi gaba….
Shi fa har ga Allah kunyar ta yake ji a halin yanzu..idan
ya tuna irin yanda ya fito mata k’iri k’iri ya fad’a mata abunda yake buk’ata daga gareta da kuma yanda ya furta mata kalmar ‘ba ya k’aunarta’
Wasu abubuwan da yawa da ya yiyyi idan yana tunasu a yanzu sai ya dinga ji kamar k’asa ta tsage ya shiga!
Tabbas Daddy yayi gaskiya daman ya tab’a gaya mishi
‘’’Akwai ranar dana sani!Ranar da zaka ji inama ana yin reverse ayi maka domin ka samu ka aikata alkhairi ka kuma goge duk wani abun da kayi marar kyau.
Ranar tana nan zuwa, ko bayan raina za kace na fad’a maka‘’.
Tabbas kuwa tun kafin aje ko Ina gashi ranar ta zo
Ya san dalilin da ya sanya Sakina take gudunshi ta kuma k’i sa! Bai wuce akan tunanin da take yi na alak’ar shi da cikin jikin Jalila ba ne…..bai san
wanne kalar kallo zata yi masa ba idan taji tabbas cikin nasa ne!
Ballantana kuma azo kan maganar halayyarshi
da baya fatan Allah yasa Sakina ta sani!
So yake ya gyara komai
ya zama mutumin da ta ambata tana son kasancewa tare da! Gashi already yana da competition, yanzu ahaka ma ta riga ta nuna mishi ta zab’i Ashraff a kansa
ina kuma ga idan taji wata magana akanshi!
Ya kenan?….,
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Itace kalmar da ya ambata yana mai dafa motar shi
dan har sun iso bakin motar.
Da sauri Aaima tace
“Subahanallah Ya Auwal mai ya faru?”
Tana mai matsowa inda yake.
Sai da ya d’an runtse idanunsa kafin ya dawo dai dai tukunna ya samu yace mata
“Ba komai, shiga mu tafi”
Yana mai zagayawa ya bud’e mazaunin driver ya zauna.
Tana shigowa ya tada motar yaja suka fita.
Har suka isa mansion d’in nasu babu wanda ya samu damar furta kalmar ‘a’ a cikin su.
Shi ya fara fita daga nan itama ta fito suka nufi ciki.
Suna shiga parlourn suka tarar da Jalila ta d’aura k’afa d’aya kan d’aya ga remote a hannunta tana ta chanja channel…
Lumshe idanuwanshi yayi a hankali ya shak’i iska ya furzar sannan ya bud’e idanuwan nashi
a hankali a fili yace
“My worst regret!!”
Ya kasa gaba ya kasa baya.
Aaima ce tayi k’arfin halin k’arasawa tsakiyar parlourn inda Jalilan take
tana kallon ta da d’an mamaki dan kamar bata tab’a ganinta ba.
Fitowar Mom daga kitchen ne ya katse mata tunani har shi Auwal d’in
Uwa mai dad’i suna had’a ido yaji wani sanyi a ranshi…
Takawa yayi har inda take yana zuwa ya sa hannu yayi hugging d’inta.....
Tun a cell Mom take aiyyana kalar abubuwan da zata yiwa Auwal kala kala
In Allah ya maidota gida lafiya dukda kuwa tana shakkarshi,
babu yadda bata yi mishi shi da Arshaad akan su basu kud’i su samu su fito ba
amman suka hana su
saboda suna shakkar Granpa sannan basu san darajar su uba and sun rainasu!
Sannan ta dawo amman tun jiya take zuba ido but bataga k’eyarsa ba.
A hankali yace “welcome home“
Ta manta rabon da Auwal ya nuna wani affection a kanta irin haka, ba ta san lokacin da wata kwalla ta zubo mata ba,
a hankali tasa hannu ta share
tana jin duk wata wutar masifar da ta shirya juye mishi tana sauk’a daga k’irjinta.
Muryar Jalila ce ta katsesu jin da d’an k’arfi tace
“Adama ina shayin nawa??”
Da mamaki Aaiima take kallonta sai kuma ta juya tana kallon su Mom.
Da sauri Auwal ya cika Mom ya yunk’ura zai yi wajen
yaji ta rik’e mishi hannu
yana juyowa ta girgiza mishi kai daga nan ta koma kitchen ta d’auko tea d’in daman ta gama had’awa waya take so tayi shiyasa ta manta ta fito d’aukar wayar.
Zata nufi wajen Jalilan amma ga mamakinta sai taga Auwal ya tare, yace
“Ba zata kaiwa Jalilan ba wallahi!.
Idan tana son sha to tazo ta d’auka anan d’in!”
Ya fad’a hakan yana mai karb’ar tea d’in ya d’aura akan dining sannan yaja hannun Mom d’in za suyi sama.
Da kyar mamakin Auwal ya barta ta iya ce mishi
“Ban ci abinci ba,
Bara in na gama sai muyi saman dukkanmu ko?”
Ajiyar zuciya ya sauk’e ya watsawa Jalilan wata uwar hararar da sai da y’an hanjin cikinta suka kad’a!
Daga nan ya cika
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 28