Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yayi kissing forehead d’inta tukun yace “Welcome home Mammy, we miss you.” Murmushin takaici tayi kafin ta mike tsaye, cikin tsananin b’acin rai tace “Ba kayi missing d’ina ba Arshaad, da kayi missing d’ina to da ba zaka yi min yaji ka daina zuwa inda nake ba” Kamar zai yi kuka yace “Mammy bana son ganin b’acin ranki, abunda kike so inyi ne ba zai yi ba, kiyi hak’uri please.” Cikin katseshi tace “Ka san cewa Aslam baya yin kwana uku bai lek’o mu ba? Haka Auwal shima! Daddy kuwa kullum sai ya kira waya an had’ashi da Adama Ummi kam daman kowa ya san Mijinta ba zuwa zai yi ba tunda shi ne ya kulle mu! Kai fa? Arshaad da kai da uban ka laifin me nayi muku, a rayuwa? Anya ni na haifeka kuwa Arshaad?” Da sauri ya matsa sosai inda take idanuwanshi har sun cicciko kamar zai yi kuka ya d’aura hannunsa ya rufe mata baki kafin yace “Mammy pleas...” Bai k’arasa ba ta buge hannun cikin tsananin b’acin rai tace “Kar ka yi mini ‘please’ bana son ji! Kun riga kun nuna min matsayi na da kai da ubanka! Naji nagani kuma na fahimta, akwai lokacin da na ware muku kai da shi zan waiwayeku amman ba yanzu ba dan wallahi sai kun san kun wulak’anta, hak’urina ya k’are a cikin gidan nan! Amman yanzu akwai boss d’in da ya kamata mu fara kashewa ni da kai a yau kafin komai.” Bata jira jin me zai ce ba taci gaba “Naji labarin za kayi aure! Jibi ko? To wallahi bari kaji In dai sunana Rukayya kuma nonona ka sha to wallahi muddin ka auri wannan Yarinyar ni kuma a ranar zan tsine maka......................” “Innalillahi wa innailaihirrajiun” Itace kalmar da Arshaad yake ta nanata wa a ranshi! Ya kasa motsi ya kasa cewa komai…… A ranshi yace “Wannan shine abunda nake gudarwa since day 1, ya zan yi da Mammy, ya zan yi da zuciyata wadda na san muddin aka fasa aurena da Hudan tabbas tarwatsewa za tayi”. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 51 Mammy tana gama fad’in haka ta wuce sama, haka Aaima itama ta bi bayanta tana jin kamar an tsundumata a Aljannah! Suka barshi shi kad’ai a tsaye. A hankali ya nemi kujera ya zauna ya sunkuyar da kai sannan yasa hannu ya dafe kan da hannu biyu.. Yafi minti ashirin a haka, chaan! Ya ji an dafa shi, yana d’agowa suka had’a ido da Dad. Kallon shi Dad d’in yake yi trying to fassara yanayin da yake ciki. Da sauri Arshaad ya mik’e tsaye ya fara k’ok’arin saita kanshi, cikin k’ok’arin danne abunda ya tokare mishi k’irji yace “Ina wuni Dad” Sai da Dad d’in ya d’an k’uraa mishi ido tukun yace “Lafiya kake kuwa?” Murmushi kawai Arshaad d’in ya k’ak’alo kafin yace “Alhamdulillah! All is fine na gaji ne kawai, bara inyi freshening off in kwanta” Ya k’arashe maganan da k’ok’arin barin wajen dan ya lura da kallon da Dad d’in yake mishi so yake ya gane yanayinshi ne. Har ya d’anyi gaba yaji Dad d’in yace “Arshaad” Tsayawa kawai yayi ba tare da ya juyo ba. Ajiyar zuciya Dad d’in ya sauk’e kafin a hankali shi ya taka ya k’arasa inda yake ya tsaya a gaban shi yasa hannu ya dafa kafad’ar shi, cikin kulawa ya fara magana “Son, irin haka is normal! Most a times couple basa tashi samun matsala sai ya rage y’an kwanaki kad’an aurensu.. Ka kwantar da hankalin ka kar ka sa komai a ranka, za ku hirya soon komai ya wuce kamar bai faru ba. Wannan duk aikin shed’an ne so karka bari yayi galaba a kanka. Allah yayi muku albarka.” Cikin sigar zolaya ya ci gaba da cewa “Nan da jibi fa ka zama magidanci, a nan ne zaka fara facing real life da real issues So garama ka shirya! Kar ka bari small things irin haka suyi breaking naka.” Da k’arfi Arshaad ya taune lip d’inshi na k’asa, yana jin yadda zuciyarshi take tafarfasa! Ba k’aramin kokawa yayi da makogwaro da harshenshi ba kafin ya samu su bashi had’in kai wajen furta kalmar “In shaa Allah Dad, thanks a lot.” Murmushi Dad d’in yayi kafin ya d’anyi tapping kafad’ar shi da hannunshi ke a kai yace mishi “good night” daga nan ya nufi hanyar side d’inshi, ya bar Arshaad tsaye a wajen… In banda ajiyar zuciya babu abunda Arshaad yake sauk’ewa a jere a jere. Ganin ya fara ganin duhu duhu, kar yaje ya fad’i a wajen yasa ya lallab’a ya nufi side d’inshi shima dake nan a k’asan. Da kyar ya kai kanshi toilet bayan ya ajjiye suite d’in hannunshi akan gadon. Ko agogon hannunshi bai samu ya cire ba ya yana shiga toilet d’in ya sakarwa kanshin shower ta ko’ina da ruwa mai mugun sanyi! Ya dad’e a haka kafin da kyar ya samu ya fito kayan jikinshi na d’igar ruwa.. Dai dai nan ya ji wayarsa ta hau ringing, hannu yasa a aljihu kafin ya zaro wayar k’irar iphone 13 ya kalla screen d’in! A take damuwar da ya samu ta d’an ragu ta dawo mishi sabuwa ta sake hauhawa sakamokon ganin mai kiran nasa.. Har ta tsinke bai d’aga ba kuma bai daina kallon screen d’inba! Yana a yanda yake wani kiran ya sake shigowa… A hankali hannunshi na rawa ya d’auka ya kai kunnenshi kawai yayi shiru bai ce komai ba. Cikin sanyin muryarta yaji tace “Ya Arshaad.” Ajiyar zuciya ya sauk’e ya lumshe idanuwanshi da suka yi jaaa wanda hakan ya bawa hawayen da yake ta addabar zuciyarshi daman zubowa ta ido d’aya! Kafin d’ayan idon shima ya samu damar zubo da nashi hawayen... Ajiyar zuciya kawai taji yana sauk’ewa a jejjere Hakan yasa a d’an rud’e tace “Ya Arshaad ka yi mini magana pls, baka da lafiya ne yanzu? Mai ya faru” Da kyar ya iya k’arasawa bakin gadonsa ya zauna dan ya fara rawar sanyi ba kad’an ba! Yana zama wata wawiyar atishawa ta kece mishi wanda yasa Hudan mik’ewa daga kwancen da take, kafin tace “Mura ko? Sorry sannu ka sha magani tou?” Sai a sannan taji yayi magana “Hudan!” “Naam” tace da sauri dan daman so take taji ya furta wani abun dan shirun nashi ba k’aramin tsoratata yayi ba. A hankali ya d’an yi tari kafin yace “Do you love me??” Ta d’anji kunyar tambayar amma jin yanayin shi da kuma muryarshi wata iri yasa tace “Yes, a lot” A hankali yace “Say it” Shiruu, ta d’anyi kafin a hankali yaji tace “I love you” Sai da yad’an lumshe idanuwansa kafin yace “To what extent??” Ya sake jeho mata wata tambayar. Zuwa yanzu kam yad’an fara birkita mata lissafi hakan yasa tace “Ya Arshaad meye ne yake damunka?” Tayi masa tambayar kamar zata fashe da kuka. Cikin tsare gida yace “Just answer me! How much?? To what extent za ki iya zuwa domin kiga mun mallaki junan mu??” Ita dai ba abunda take fahimta daga shi zuwa yanzu, gashi tana jin yanda numfashinshi yake seizing sama sama! Daurewa tayi tace “Kamar yaya?” Dan da gasken bata fahimta ba. Da kyar ya dedeta numfashinshi kafin yace “Idan Mama tace ki hak’ura da ni, za ki hak’ura?? Sai da ya sake maimaita mata tambayar tukunna tace “Maama ba zata tab’a cewa In hak’ura da kai ba! Meyene ya faru na kasa gane komai” Bai bata amsar ba sai cewa yayi “Idan Maama tace ki hak’ura da ni, za ki hak’ura??” Ta kasa fahimtar inda ya dosa, kawai sai ta yanke shawarar ce mishi “Ya Arshaad ai albarkar iyaye shine abinda ake buk’ata! In basu da niyyar sakawa meye amfanin auren da za ayi babu albarka?” Rintse idanuwansa yayi da k’arfi! Tuni numfashinshi suka fara korar juna… She can feel it dan haka duk sai ta sake rud’ewa ta hau kiran sunan shi amman yak’i kulata, k’arshema wani irin tari taji yana yi, yayi kusan 3 minutes yana tarin Hudan tana kuka tana kiran sunanshi amman shiru wanda hakan har sai da ya farkar da Sakina da Khadijah amarya y’ar Anty Zainab da suke d’aki d’aya da ita daga bacci. Ganin yanda duk ta rud’e ne yasa Sakina ta shiga tambayarta…. Karb’ar wayar Sakina tayi itama ta shiga kiran sunan shi tana “Are you there? Are u okay??” Amman tsit kake ji ko tari babu. Rikicewa suka yi… Da kyar idea ta fad’owa Sakina hakan yasa da sauri ta d’auki wayarta ta danna kiran Aaima! Sai da kiran ya kusan tsinkewa tukunna aka d’auka, cikin gigita Sakina tace Aaima ina wuni, sorry na tashe ki, Ya Arshaad ne bashi da lafiya, dan Allah ko zaki gayawa Dad in yana gida a duba shi ko kuma ki tura wani wanda yake kusa….” Shiruuu, Sakina taji anyi! Hakan yasa ta sake cewa “Aaima” Ajiyar zuciya taji Aaiman ta sauk’e sannan ta fara magana “Ki turo Hudan mana ta zo ta duba shi! Daga nan ma sai su yi sorting out decision d’in da ya kamata su yanke.. Besides a nan ba wanda zai kulashi saboda rashin lafiyarshi ba zamu iya yi mishi maganinta ba. Spoiler alert!! Bara kiji abunda na san ya jawo mishi ciwon...... Mammy ta dawo d’azu at last ita da su Mom! And tace masa ‘ya hak’ura da auren Huda ko kuma ta tsine mishi!’ Wannan shine abunda ya janyo mishi rashin lafiya na riga da na sani.” Tana gama fad’in haka ta ajjiye wayar. K’amewa Sakina tayi ta kasa cire wayar daga kunnenta! Sai da Hudan ta tab’ota tace “Ya ake ciki Sakina?” Tukunna tayi firgigit ta dawo daga tunanin tashin hankalin data fad’a na y’an sakanni.... ….Dama da ita bata tab’a fadawa kowa ba ne amma haka kurum idan ta tuna Mammy bata san dalili ba sai taji gabanta yana ta fad’uwa! Dan bata san ya tsakaninta da Huda zai kasanceba. Kuma ta lura kamar Arshaad d’in yana ta saurin ayi ayi ai auren su samu su bar k’asar! Tabbas sai yanzu ta fahimci dalilinshi.. To amma mai yasa Ya Arshaad zai so ya had’a ta da surukar da ba zata amsheta ba? Duk kuwa da tsananin k’aunar da suke yiwa juna ai da sun hak’ura!…… “Sakina, akwai matsala ne?” Muryar Hudan cikin rauni, ta katse mata tunaninta…. Juyawa tayi suka had’a ido! A take wani tsananin tausayinta ya rufeta dan bata jin a cikin shekaru ukun nan akwai lokacin da take hango tsantsar k’aunar Arshaad a idanun Hudan kamar wannan lokacin. Da kyar ta iya ce mata “Aaiman bata gida, bara in kira Auwal kawai.” Ta fad’i haka tana me mik’ewa ta fice daga d’akin gaba d’aya. Hudan kwata kwata bata gamsu da maganar tata ba dan haka ta mik’e ta bi bayanta. Suka bar Khadija wadda itama bata wani yarda da maganar Sakinar ba dan ta lura da yanayin da ta shiga tun fara wayarta da wadda suka kira da ‘Aaima’. Tana fita ta samu damar zubar da kwallar da take ta k’ok’arin rik’ewa! Yanzu Ina mafita? Meye abunyi ? Sune tambayoyin da suka toshe mata kwanya sannan ta kasa samun mai bata amsar su. Daman y’an layi har sun fara k’ananan maganganu suna cewa ....Allah dai yasa tarihi kar ya maimaita kanshi Ita maryam bata daddara da family d’in Abba da abunda shi kanshi Abban yayi mata ba shine zata aurawa Huda nephew d’inshi dan kawai taga yana da masifar kud’i! Ga dai Ummu ita da ta auri saffa saffa hankalinta a kwance rayuwarta gwanin ban shaawa amman ita har yau bata samu kwanciyar hankali ba a ta dalilin So da Buri! Ta mannewa mutumin da yafi k’arfin ta nesa ba kusa ba.... Jin k’arar bud’e k’ofar d’akin nasu ne ya sanya Sakina goge hawayenta da sauri, sannan ta lalubo number Auwal ba dan ranta yana so ba ta fara kiranshi…. Bacci bai dad’e da d’aukarsa ba dan bai dad’e da kwanciya ba amman yana fara baccin ya hau mafarkinta............. Yana cikin mafarkin nata k’arar wayarshi ta katse mishi mafarkin…. Kamar ba zai juya ba bayan ya farkan sai kuma yayi tunanin ko Granpa ne dan haka yayi tsaki ya lalubo wayar akan bedside ya amsa ya kara a kunnnen shi ba tare daya duba mai kiran nasa ba. Jin shiru yasa tace “Ya Auwal” A hankali. Bude idanuwansa yayi da kyau kafin ya zaro wayar daga kunnenshi ya kalla sosai ya tabbatar itan ce tukunna ya mayar da wayar kan kunnensa ya mik’e zaune yana adduar ‘Allah yasa lafiya’ dan ya san ba k’aramin abu bane zai sanya Sakina ta kirashi kuma cikin daren nan ba. Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “How far” Dan lokaci d’aya ranshi ya b’aci bayan ya tuno ta Ita da Ashraff d’azu. Ba tare da b’ata lokaciba tace mishi “Ya Arshaad ne suke tunanin bashi da lafiya dan yanzu ma kamar suma yayi suna cikin waya da Hudan.” Ta san maybe Hudan ce ta fito d’azun kuma maybe tana tsaye a bayantata dan haka sai ta tak’aita maganar tata sannan tace “Dan Allah yaje ya dubo shi” “Okay” Kawai yace daga nan ya kashe wayar ya mik’e ya fad’a toilet yad’an d’auraye fuskarshi ya chanja zuwa jallabiya tukunna ya fita.......... Sai da ya daddannawa gate man d’in zagi, tukunna ya barshi ya fita A cewar shi (gateman d’in) Daddy ya hana a na barinshi yana fita cikin dare. Sai mita yake yi shi kad’ai a mota haka ya isa gate na estate d’in MT ..a ranshi yana aiyyanawa ‘Da mutane sun san halin da yake ciki to da ko kallonshi ba zasu dinga yi ba! Komai b’ata mishi rai yake yi tun d’azu...’ Allah ya so shi bai samu matsala da mai gadin main estate d’in ba, sai dai ya rok’esa akan ‘ya bi a hankali kar ya bari Granpa ya ganshi dan zai iya cewa a bakin aikin shi’ Jinjina kai kawai yayi ya wuce ciki. Ya dad’e yana knocking jin shiru yasa ya yanke shawarar kiran Aaima yace mata ‘ta kira layin wata a cikin masu aikin gidan tazo ta bud’e mishi k’ofa.......’ Tunda Sakina ta kira ta bacci ya k’aura daga idanunta, tana cikin chatting kiranshi ya shigo wayar tata. Ta dad’e tana kallon number, kasancewar ta dad’e da goge numbershi amman ta na nan a kwakwalwarta bata gogu ba! A take jikinta ya mutu.. Sai da wayar ta kusan tsinkewa tukun ta samu damar amsawa, cikin sanyin jiki ta kara a kunnenta tace “Hello” Ba tare da ya amsa ba yace “Aaima Arshaad is sick, na zo duba halin da yake ciki kuma k’ofan ank’i bud’ewa.. Can you do me a favor ki kira wani wanda kika sani a cikin gidan yazo ya bud’e min? It’s an emergency” Tunda ya fara magana ta lumshe idonta har ya kai aya a hankali tace “to” kawai, ta tsinke kiran. Kamar 5 minutes yaji ana k’ok’arin bud’e k’ofar, ana bud’ewa ya kutsa kai ciki ba tare da ya kalli bayan k’ofar ba inda take, yayi hanyar side d’in Arshaad direct kawai. “Ina wuni” Yaji muryar ta. D’an juyowa yayi ya kalleta a ranshi yace “Ashe ta dawo.” Ba yabo ba fallasa yace “Lafiya” Kawai ya juya ya nufi hanyar part d’in Arshaad. “Ya k’ara haske, sai dai yad’an rame kad’an! Ya k’ara kyau.” Ta fad’a a k’asan ranta! Bata san dalili ba amman taji zafin yanda yayi mata, taso ta koma sama kawai abunta amman sai ta tsinci kanta da kwad’ayin bin bayanshi, dan haka ta rufe k’ofar ta nufi side d’in Arshaad. Direct main bedroom d’in dake side d’in Auwal ya nufa. Yana shiga ya ganshi yashe a k’asa da jikakkun kaya. Da sauri ya k’arasa wajen ya durk’usa ya hau jijjigashi yana kiran sunanshi…. Dai dai nan Aaima ta shigo, duk da fushin da take yi dashi hakan bai hanata fashewa da kuka ba da ganin halin da yayan nata ke ciki. Da sauri Auwal ya juya gareta yace “Yi maza Aaima d’ebo ruwa a toilet yi sauri plss..” Ya fad’a cikin gigita da kid’ima. Da gudu ta nufi toilet d’in ta d’ebo ruwan ta fito ta na zuwa Auwal ya amsa ya hau yayyafa mishi…. Sai da suka fidda ran ma zai farfad’o tukunna yayi wata wawiyar ajiyar zuciya wadda ta taho mishi tare da tari! Auwal ne ya d’an d’ago shi kad’an yahau bubbuga mishi baya yana jera mishi sannu. Da kyar ya samu tarin ya tsaya ya shiga jejjera ajiyar zuciya.... Sai da Auwal ya kamashi ya kaishi kan gadonshi, tukun ya zaro waya ya fara k’ok’arin kiran family doctor d’insu…. Kamar Arshaad d’in ya san me yake shirin yi, yace nasa “Kar ka kira kowa Auwal, i’m fine. Please.” Kallonshi Auwal d’in yayi kafin shima yace “Dan Allah kar ka gwada yin wannan taurin kan! Ka bari a kirashi ya duba ka kawai.” Cikin d’an fushi Arshaad yace “Auwal zamewa nayi na fad’i na buga kaina! Yanzu kuma na farfad’o… Ka gaya min in akwai abinda Doc zai yimin idan ya zo d’in bayan wanda kukai min.” D’an k’uraa mishi ido Auwal d’in yayi kawai ya tsaya yana kallonshi. A hankali Arshaad d’in ya koma ya jinjina a jikin gadon sannan yace “sorry” Ajiyar zuciya Auwal ya sauk’e kafin yace “Are you sure that’s all?” Jinjina kai kawai Arshaad d’in yayi. Auwal bai wani gamsu da maganan shi ba but yaga kamar he wants to be alone shiyasa yace “Shikenan, Allah ya kare gaba, ka kira su Hudan hankalinsu ya tashi sosai. And dan Allah ka sauya kayan jikin nan naka, sai da safe.” “Ok” shine abunda Arshaad yace sannan ya k’ara da cewa “Thanks a lot” Murmushi yayi kawai yace mishi “Good night” Daganan ya nufi hanyar fita. Kallonshi (Arshaad) itama Aaima tayi tace “Ka kira wayana if you need anything” Jinjina mata kai kawai yayi sannan ya fara k’ok’arin mik’ewa dan chanja kayan jikinshi. Ganin haka yasa Aaiman yi mishi sai da safe itama ta juya tabi bayan Auwal wanda har ya kusan ficewa… Sai da ya kusan isa k’ofar fita ta main parlour tukun ta samu ta cin mishi ta wuce ta isa bakin k’ofar ta sa hannu ta bud’e. Ba tare da ya kalletaba dan shi har ga Allah ta fara k’ular dashi Ya sa kai zai fice. Daurewa tayi tace “Mun gode sai da safe” “Allah ya kaimu” yace daga nan ya fice. Ta jima a parlourn bayan ya fita.. Daga k’arshe ta nufi side d’in Arshaad har bedroom ta lek’a ganin yayi bacci yasa ta fito ta nufi sama ta koma d’aki. Da kyar ta samu bacci ya d’auketa. Shi kuwa Arshaad yanda yaga rana haka ya ga dare! Yana jinta lokacin da ta shigo, baya san ganin kowa shiyasa yayi baccin k’arya, ko Hudan text kawai ya iya tura mata cewar ‘he’s okay’. Kafin safiya ya gama deciding yanda zai yi da abunda zai cewa Mammy amman still yana d’an d’arr! Ga fargaba ga tunani barkatai shiyasa zazzab’i yace salama alaikom........... Zazzab’in da ya rufar masa ne yaasa da kyar ya iya mik’ewa yayi sallah a daddafe! Kafin 7 kuwa zazzab’in yayi masa rufdugu…. Ganin yana shirin mutuwa ya sanya shi kiran family Doctor d’in da baya so, dole! Ya kira fad’amshi yana zazzab’i mai k’arfi. Ba a rufe 30 minutes ba Doctor d’in ya iso.. Allurai yayi mishi bayan ya duddubashi dan ya san Arshaad ya tsani magani, daga nan ya jona mishi drip yayi mishi sallama… Sai wajajen 11 drip d’in ya k’are da kansa ya zare ya danne, bayan some minutes ya mik’e ya fad’a wanka. Yaji dad’in jikinshi ba kad’an ba kuwa. Yana fitowa ya d’an shafa mai da turaruka ya zura wata cream jallabiya mai gajeran hannu… A hankali ya k’arasa bakin gadon ya d’au wayarshi ya fara kiran Hudan dan tun da safe yaga message d’inta. Bata wani dad’e tana ringin ba ta d’auka! Bayan sun gaisa ya tabbatar mata da ‘he’s okay daman kawai dan zazzab’i ne’. Tace mishi “Anjima around 1 ana buk’atar shi za suyi traditional event d’insu na yaren Shuwa kuma dole sai yana wajen! Inda hali ya turo driver kafin nan, yazo ya karb’a mishi kayan tradition d’in da aka tanada domin shi (wanda zai saka a event d’in) Kayan ba su iso ba sai d’azu shiyasa bata bashi da wuri ba.” Da “to” ya amsa ta daga nan suka hau hirarsu dan yaga kamar hankalinta still a d’an tashe yake. Sun jima suna hira dan sun fi 30 minutes kafin suyi sallama. A hankali yayi shiruuu, yana y’an tunane tunane.. Chaaan! Ya turawa driver d’in da zai karb’o mishi kayan nashi message daga nan ya mik’e yayi kalmar shahada ya fita ya nufi sama wajen Mammy. A stairs suka had’u da ita tana k’ok’arin sauk’owa! Kamar bata ganshiba haka tazo ta wuceshi. Hannunta yayi saurin rik’ewa ya juyo a hankali yace “Haba Mammy.. Ki saurareni please mana.” Ya fad’i hakan kamar mai shirim fashewa da kuka. Ba tare da ta kalle shi ba tace “Ka bari idan Allah ya kaimu gobe naga kayi abunda nace sai in saurareka” “Meye abunda kike so yayi miki goben??” Suka ji muryar Dad a bayan su!. Da sauri Arshaad ya juya yana kallonshi gabanshi na tsananta fad’uwa! Ba tare data juyo ko ta damu da Dad d’inba tace “Ai gaka ga shi nan! Kana iya tambayarshi.” Tana gama fad’in haka ta nufi k’asa wajen bakinsa da take expecting dan sune ma suka ce mata sun kusan shigowa ba daban su ba da babu abinda zai sauk’o da ita k’asan! Tana buk’atar time ita kad’ai, dan ita kanta bata san daliliba amman komai ya kunce mata.. Kame kame Arshaad ya fara bayan ta sauk’a… Babu yadda Dad bai yi da shi ba amman yace mishi “ba komai! Kawai sun d’an samu issue ne shi da ita lokacin tana cell shine yake so suyi settling”. Sam Dad bai yarda da shi ba dan kwata kwata babu kamanceceniya a cikin maganar shi da tata!. Fahimtar da Dad yayi Arshaad d’in ba zai gaya mishi komai ba ne yasa kawai yace “to, shikenan ka samu ku shirya d’in kafin ka bar gidan nan.” Yana gama fad’in haka ya wuce shi shima yayi k’asan. Sai a sannan Arshaad ya sauk’e ajiyar zuciya He needs to talk to Mammy! Idan tak’i ta lallashi tabbas zai b’ullo mata ta hanyar da bata zata ba! Akwai abubuwa da dama waenda ya sani amma yayi shiru kuma ta san ya sani but it’s like kamar ta manta, so he has to remind her!. Sannan ya san ta inda zai b’ullo mata ta yarda dan yaga alamun ba lalle ta yarda cikin sauk’i ba gashi babu enough time!…. Ya jima a wajen kafin ya juya ya wuce sama da niyyar d’an bata time Kafin ya sake ganinta! Yana da full hope d’in zai yi nasara bi izinillahi. Mammy na sauk’a k’asan ta fara shan mamaki.. Kulolin abinci kala kala da su drinks ake ta shigowa da su! Bata ida fita daga wannan mamakin ba taga friends d’inta da sisters d’inta har da Mahaifiyarta suna ta shigowa har da ankon super d’in su da suka yi a jikinsu…. Da sauri ta k’arasa kusa da yayarta ta kamota tace “Me kenan? Wats the big idea?” Murmushi Haj Binta tayi kafin tace “Wunin d’an mu za muyi mana! Anjima kad’an kuma muje muga Amarya naji Dad yace za suyi traditional day d’insu suma daga nan mu bata kyaututtuka Naga ke baki son zancen shiyasa ma na zagayeki na kira Dad. Anko kuwa ni na fitar kuma gashi kowa yayi, ni da su Hajiya ( Mahaifiyar su) tun lokacin da aka sa rana dama muke ta shirye shiryen mu. Matsowa Mahaifiyar tasu tayi kusa da su ( ita da sister d’in tata ) kafin itama ta fara magana “Ki nutsu ki bari ayi komai a gama daga nan sai a san abun yi! Ni na hanasu su fad’a miki komai akan lamarin auren, gudun samun matsala dan na san halinki. In dai ni na haifeki to inaso ki kwantar da hankalinki kiyi hak’uri, ni kaina ba wai son had’in nake yi ba! Amman ki bar ni da su kawai ai in sun san wata basu san wata ba! Kuma kar ki bari kowa ya fahimci halin da ake ciki, ki nuna kina so inda hali ma ki shirya muje ki bawa ita Yarinyar kyauta da hannunki a gaban kowa…” Ganin friends d’in Mammyn sun tunkarosu ne yasa Mahaifiyar tata yin shiru ta fara yak’e.. Suna zuwa kuwa suka hau tayata murna kowa na farin ciki tare da yi mata ya jiki (dan ce musu aka yi ita da su Mom duk sun yi inhealing dangerous abu shine aka fitar da su k’asar waje suka yi jinya sai jiya suka dawo). Haka nan suka k’arasa tsakar falon aka zazzauna… Masu decoration suka shigo suka hau d’an gyaggyara parlourn Yayar tata ce tace “bara taje ta ajjiye abu daga nan ta cewa Arshaad ya shirya, su d’anyi hotuna a nan kafin a tafi event d’in su Hudan..” Sama ta nufa da niyyar ajjiye abu tukun ta je ta kira Arshaad d’in Tana shirin hawa suka had’u da Dad yana sauk’owa… Cikin mutunta juna da barkwanci suka gaisa daga nan yace mata “Ta kirawo masa Mammy, su sameshi su biyu a side d’in Arshaad.”

Chapter 23 of 28