yarda ka kaini mak’ura!!”
Yana gama fad’an hakan ya koma wajen dpo ranshi a mugun b’ace…
Da sauri Mom ta sake rik’o hannunshi duka biyun ta matse gagam sannan ta fara magana
“Kayi hak’uri ka sauk’a daga kan wannan dokin zuciyar Auwal, dan babu inda zai kaimu, idan ma za a hukuntasu to bata haka za a yi ba, kaji??
Yanzu na tabbatar kana yin wani abun laifin ka za a gani, kuma nima kaga dai gani da nawa issue d’in, sannan ga matsalar ka da Granpa abun zai yi mana yawa.”
Cikin yin k’asa da murya tace
“Kana gani ai Arshaad da ya fika wayo tun jiya bai zo ba, kuma na tabbatar yana cikin gidan, shi kuma Aslam dayake babu uwar shi a ciki ta sama ya mak’ale yanata kallonmu bai ce ko yayi komaiba, bai san ba ganshiba.
Don haka inaso kayi hak’uri ka danne zuciyar ka, tukunna sai mu san abun yi, kaji ko?”.
Da k’arfi ya sauk’e ajiyar zuciya yana bin hannun Mahaifiyar tashi da yayi jajur ya kumbura ga borin jini kala kala, da ido. A haka har gara ita nata da d’an sauk’i akan Ummi, dan ita nata har fuska…
“Kaji ko?”
d’in da tace mishi ne ya sanya yayi mata nodding kai kawai sannan ya koma ya zauna, itama ta dawo ta zauna.
A Chan teburin dpo kuwa
Babu yadda Daddy bai yi da shi ba akan “zai biya ko nawa ne a ware musu office d’in wani d’an sandan a gyara musu toilet su dinga amfani da shi su uku kawai zuwa nan da 2 months d’in”!
Amman furr!! Dpo d’in yak’i, yace
“Jiya bayan na dawo sojoji Mahaifinta ya aiko suka kaini har gabanshi da daddare
ya ja mini warning akan in tabbatar na basu horo mai tsanani, kuma ya shaidamin yana da cid’s da yawa, muddin na k’etare umarnin shi to a bakin aikina.
Tsabar yanaso ya tabbatar min idanunsa suna kaina, yau da safe ya kirani, duk wani abinda ya faru a nan daga dawowata zuwa tafiya ta gida da zuwana nan yau da safen kaff! Babu abinda bai gayamin ba, har na cikin dare wanda bananan a bakin shi na ji.
Hatta abinci yace sau biyu kawai za a dinga basu…
So, dan haka dan Allah ka rufamin asiri ina son taimakonku tabbas amman ina jin tsoron rasa aiki na. Da kuma hukunci da yayi alk’awarin yanke min, wanda ban san meneneba.”
Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e, sannan ya juyo ga su Ummi….
Idanuwa yaga sun zuba mishi alamun suna sauraron komaai.
Tausayin su ne ya kamashi, hakan yaasa yayi saurin d’auke kanshi yana shirin yiwa dpo d’in magana Mom ta matso ta katsesu ta hanyar cewa
“Tou dan Allah idan ba zaka iya komaiba, ka raba mana d’aki da matan nan, basu da mutunci kwata kwata, gara a kwashesu a zuba mana wasu”
Jijjiga kai dpo d’in yayi sannan yace “zan gwada in gani.”
Abinci Daddy ya bayar aka je aka siyo musu da alk’awarin zai dinga zuwa dubasu kullum sannan ya yiwa Mammy da Ummi sallama yace “Mom ta tsaya yana da magana da ita.”
Suna fita ya cewa Auwal “ya matso”, ba tare da b’ata lokaci ba ya zayyano mata abinda ido da kunnuwanshi suka jiwo mishi daga Auwal d’in da Jalila yau da safen nan, kafin ya k’ara da cewa
“Kina tausayin Yarinya kin d’auko ta zaki bata kud’in kayan d’aki!
To ga d’anki nan zai lalata mata rayuwa gaba d’aya
tun kafin ta samu kud’in da zata yi auren da shi.
Ko kuma ma ince ya gama lalata mata rayuwar dan na kasa fahimtar inda zancen nasu ya dosa!
Saboda haka it’s either kice mata ta koma wajen Inna ko kuma shi Auwal ya bar gidan, tunda na lura kamar ba kya son sallamar Jalilan.
Duk lokacin data tafi shi sai ya dawo.”
Hak’uri Mom tayi ta bashi da alk’awarin zata kira Innar taji, idan komawarta ba zai yiu ba, zata rok’i Gwaggo Asabe ta rik’eta a wajenta kafin ta dawo.
Da kyar ta lallab’ashi ya hak’ura, akan sai zuwa wani d’an lokaci In ta tuntub‘I Innaa da Gwaggo Asabe amman da cewa yayi a yau zata bar gidan dan shima jibi tafiya zai yi, so ba za’a bar daga ita sai Auwal ba.
Taso su d’an keb’e da Auwal d’in amman hakan bata faru ba, dan Daddy bai basu dama ba.
A haka suka yi mata sallama suka tafi, zuciyarta a cunshewa gashi babu daman yin waya don an karb’e tun jiya, gaba d’aya hnkalinta kuma sai ya koma kan yadda zata ci uban Jalila! Dan ta kaita mak’ura, so itace target d’inta in the next two months tana fita a cell zata yi maganin shegiya, tukunna Abba sai Aslam sai Maryam sannan Huda da Ummi….
Kmr yadda wannan Likita ya fad’a, da yamma sai gashi e da results ya bawa Granpa da duk wasu bayanai tukunna ya tafi.
Sai bayan sallar isha, tukunna Granpa ya nemi ganin Huda Abba Gramma Daddy da Dad wanda dawowarshi kenan ya tarar ana sallah dan haka ya kira Gwaggwo Asabe suka k’arasa cika ita da Mommy shi kuma ya shiga masallacin
ana idarwa Granpa yace “su wuce side d’inshi, ko gidanshi bai bari ya lek’a ba................
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
38
Sai da Arshaad ya dawo daga masallaci ‘sallar isha’
tukunna ya lura babu Mammy a gidan.
A bakin cook d’insu ya ji komai bayan ya tambayeta.
Da kyar ya iya controlling kanshi dan ya san idan yace zai samu Abba ko Daddy a wannan lokacin a yanayin da yake ciki to tabbas za a samu matsala….
Dafe kanshi kawai yayi ya sallami cook d’in.
Ya dad’e a tsaye!
Bai ma san ta ina zai fara ba!
Dan haka kawai ya sake komawa d’aki ya kwanta….
Da kyar kuwa ya samu ya iya rintsawa a daren ranar.
WASHEGARI.
Sai bayan sallar isha, tukunna Granpa ya nemi ganin Huda Abba Gramma Daddy da Dad, wanda dawowarshi kenan ya tarar ana sallah dan haka ya kira Gwaggo suka k’arasa cika ita da Mommy shi kuma ya shiga masallacin..
ana idarwa Granpa yace “su wuce side d’inshi”, ko gidanshi be bari ya lek’a ba.............
A tare su duka hud’un suka iso parlourn Granpa.
Ba tare da b’ata lokaci ba ya d’au waya yayi kiran Gramma yace “su zo ita da Huda!” Hijabin Gramma na salla mai hannu Hudan ta zumbula a kan abayar jikinta.
Bayan sun fito
Hudan ta bisu duk ta gaidasu..cike da kulawa duk suka amsa mata apart from Granpa wanda ya kauda kai gefe!
Tana k’ok’arin zama a k’asa Abba yayi saurin jawota ya zaunar da ita a kan kujera kusa da shi sannan ya hau tamabayarta “how is she?”
Tana shirin yin magana
Granpa yayi gyaran murya!
Sai da ya lura hankalin kowa ya dawo kanshi, sannan cikin serious voice d’inshi na tsoffi ya fara magana
“Na san kowa a nan ya san abunda ya faru! Da kuma wannan Yarinya da Abba ya kawo yace ‘y’arsa ce’!
Although ga kamanni nan na gani kuma su Ummi suma sun tabbatar da hakan, but dukda haka i need proof! Saboda ko dan abinda akace su Ummi sun yi jiya ya sa na saka jin ba zan iya trusting family members d’ina ba ma akan komai talkless of Maryam!
Na lura ba zata iya hak’ura da Abba ba so she can do anything, zata iya tricking su kansu su Ummi d’in ta jira for years tukunna ta aiwatar da plan d’inta.
Wannan dalili yasa jiya aka d’au sample d’inta da kuma na Abban wanda ya nemi yayi mini rashin kunya bayan na kirashi za a d’auki jinin nashi!
He looked at me yana cemin ‘ko da ace The girl is not his, shi already ya riga yayi accepting nata, so tests d’ina babu abunda zasu saka ko su chanja!’.”
Shiru Granpa yayi ya d’an sauk’e ajiyan zuciya sannan yaci gaba
“Idan nace muku na tsani Maryam!!! Sai ku dinga ganin laifina….. jiya kawai ya ganta suka had’u amman har ya zama mara kunya mara mutunci!!!
I’m pretty sure inda ace bai ganta ba to da ba zai iya gayamin maganar da ya gaya mini ba!!
He even hit his wife! Saboda kawai giyar ganin wannan matar yana yawo a jikinshi….
Anyways duk ba wannan ne ya zaunar da mu anan ba!.
Abba, inaso ka sani ko da ace zan yi disowing d’inka kamar farko, i’ll make sure Maryam bata lik’a maka y’ar da ba taka ba! Shiyasa na saka aka yi DNA and results d’in sun fito positive, so she’s your daughter, although na san you don’t need it!.
Magana ta anan itace ….
29 years ago!!! Na fad’a maka na fad’awa Maryam cewa ‘I’ll never accept her and her children!!’
Dan haka wannan Yarinyar”yayi maganan yana nuna Huda, sannan yace
“Kasancewarta y’a ga Maryam hakan ya sa she cannot live with us in this estate!!!!.
Kana da two options
Either
ka mayar da ita wajen Maryam
Or
You are free to leave this estate and family, with her
Forever!!!.”
Yana gama fad’in haka ya koma yayi lamooo, a kan luntsumemiyar sofar da yake kai.
Shiruuuu, parlourn ya d’auka, baka jin komai sai sheshshekar kukan Huda.
A hankali Abba ya mik’e rik’e da hannunta har yanzun..
Gaban Granpa suka je suka durk’usa sannan ya fara magana
“Granpa bani da bakin da zan yi maka godiya akan irin abubuwan da kayi mini tun haihuwata har kawo yanzu, ba zan tab’a iya biyanka ba sai dai In kamanta!
Ko da ace kai ka cire Ni a cikin y’ay’anka Ni ba zan tab’a iya chanja uba ba! You’ll forever remain my Dad that same Dad that loves me so much!
Wanda son zuciyata ya sanya a yanzu bana jin akwai 10% out of 100 na son da yake yi mini. Na san ba lalle ka iya finding place a heart naka kayi forgiven d’ina ba, but i’ll keep on apologizing till the end of time, I’m sorry, so sorry, very sorry! Dan Allah kayi hak’uri ka yafe min.”
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya mik’ar da Huda itama sannan yace
“Hudan and I are leaving!! Good bye.”
Da sauri Huda tace
“Dan Allah kayi hak’uri, ka zauna da su, ni zan koma wajen Mamana, na ma fi son wajen ta akan nan, kar kuyi fad’a saboda ni dan Allah!”.
Abba bai saurareta ba sai ma k’ok’arin janta da yake yi, dan so yake yayi sauri ya bar parlourn baya so su had’a ido da Gramma.
Ya juya kenan yaga Daddy a tsaye! Bai gama tunanin me ya mik’ar da shi ba yaga ya k’araso inda yake ya rik’e free hand d’inshi!
D’agowa yayi yana kallonshi da jajayen idanuwanshi, ganin Daddyn shima shi yake kallo ya sanya shi cewa
“Don Allah kar ka ce komai, ka san ba zai tab’a chanja decision d’inshi ba, ni kuma ba zan iya barin y’ata taci gaba da zama a gidan wani ba!
Please don’t stop me.”
Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e, kafin yace
“I’m not trying to stop you Abba. I’m coming wit you!!.”
Da sauri ya kalleshi sannan ya juya ya kalli Granpa wanda ya lumshe idanunsa yana nan kishingid’e kamar mai bacci.
Shima Daddy juyawa yayi still rik’e da hannun Abba yana kallon setin Granpa sannan ya fara magana
“Granpa! Laifin Maryam da Abba bai kamata ace ya shafi Yarinyar nan ba!
Bafa mu ma santa ba, bamu san ma tana existing ba, ta taso ba tare da kulawar d’aya daga ciki mu ba. I think yanzu lokacine da ya kamata ace mun yi welcoming d’inta warmly + mu nuna mata gatan da bamu nuna mata ba a baya!
Bawai a hukuntata a kan laifin da iyayenta suka aikata ba
wanda yaci ace yanzu ka yafe tunda Abban da Maryam d’in sun dad’e da rabuwa!!.
To be honest Granpa
What you have been doing is not right!! Kawai muna yi maka biyayya ne because we respect and love you as a father!
But it’s like abun yana neman yin yawa! Tunda gashi kana k’ok’arin kai Abba wuta! Ko baka tunanin Allah zai tambayeshi hakkin y’arsa akanshi ranar gobe k’iyama??
What you are about to do is wrong! Very wrong!! Dan haka i think it’s about time da ya kamata mu fara fad’a maka gaskiya!
But na san ba lalle ka yarda ba, kamar yadda Abba ya fad’a nima na san ba lalle ka chanja decision d’inka ba So idan ka kori Abba, nima zan bishi, that’s it!!!”.
Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin ya bud’e idanuwanshi, bai kalli ko inda suke ba, ya sauk’e idanunsa a kan Dad, a hankali yace masa
“What about you Yahaya?? Wat’s your decision?”
Ahankali cikin mutuwar jiki Dad ya mik’e, muryarshi na d’an rawa dan shi kwata kwata abun nan da ake bai yi mishi dad’i ba!
Bayason tension kwata kwata..a halin yanzu shi
ko da matsalar matarshi aka barshi ta isheshi, but he has to do whats right, dan haka yace
“Na zab’i side d’in brothers d’ina Granpa.
I’m sorry, but whatever Yusuf just said is the truth.”
“Ok “
kawai Granpa yace, kafin ya juya wajen Gramma ya kalle ta itama yace
“Ke fa??”
Hawayenta ta sa hannu ta share, sannan tace
“Sun fika gaskiya!! Na rok’eka da girman Allah for once a rayuwanka kayi hak’uri kayi abunda suke so dan Allah”
D’an murmushi Granpa yayi kafin yace
“If not kema baki da choice d’in da ya wuce ki bisu ko???”
Shiruuuu, tayi bata ce komai ba, har sai da ya sake cewa “ke muke jira, your decision is important.”
Tukunna,a hankali cikin kuka Gramma ta hau d’aga kai alamar ‘eh’.
Da sauri Abba ya durk’usa ya fara yi mishi magiya
“Dan Allah kayi hak’uri ka barni In zauna da ku!
Ka yi accepting Huda
plss karka....”
Hannu Granpa ya d’aga mishi kafin ya mik’e tsaye!
Yaje inda yake shima ya mik’ar dashi tsaye sannan ya fara magana
“Already na riga na gama magana Abba, kai ka sani.
And please stop pretending dan na san this is wat you want! Kana so inyi regretting akan abunda na yiwa Maryam
Tunda inda ina shiri da ita tun farko ai da duk haka bata faru ba, right?
But inaso kan san 1 thing
Ko d’aya, hakan bai sa naji ba dad’i ba, infact I’m happy because i’ve and i’m punishing the devil!!!
Ka duba fa kaga yadda Ummi ta koma, abunda suka yi ita da su Adama, duk saboda matar nan( Maryam), which I’m pretty sure ba halinsu baneba! Laifinta ne she push and made them act that way!!
And now look! Abunda dukkan ku ku kayi mini, all because of her!!
Abba How? Tayaya kake tunanin zan yi accepting y’ar matar nan? Matar da ta mayar mini da family haka?
Tunda nake da mahaifiyarku gata nan ku tambayeta bata tab’a yi min koda yaji ba nima ban tab’a tunanin tura ta gidansu saboda wata matsala ba amma yanzu kalli, she’s ready to leave..
Because of Maryam! Maryam bad luck ce! Amman ka kasa fahimta kwata kwata. Ka duba kaga fa, tun lokacin da ka had’u da ita baka samu peace of mind ba har yau d’innan!
Iya jiya( just yesterday) da kayi spending time da ita kalli abunda ya janyo, bu.....”
Mahaukacin kukan da Hudan ta fashe da shine yasa su kallonta gaba d’aya, dukkanin k’arfin da Allah ya bata tayi amfani da shi wajen fincike hannunta a cikin na Abba, sannan ta d’iba a guje tayi waje……a ranta tana ayyanawa “wallahi ba sojoji ba ko barrack ne a bakin gate d’in estate d’in yau sai ta fita, yadda ta kwasa a gujen nan ba zata tsaya ba sai ta ganta a titi sai dai ayi mata kallon mahaukaciya.
Shiyasa ashe Baabaa Talatu take rok’on ta akan karta kuskura ta yiwa Mama maganar Mahaifinta (Abba) ashe wannan ne dalilin kenan…Tunda take bata tab’a ganin hatred irin wannan ba, dan ko k’iyayyar Shuwa garesu bata kai ta wannan tsohon da ake kira da Granpa ba, gashi har yana k’ok’arin danna musu tambarin ‘bad luck’, kuma duk wanda yaji labarinsu tabbas zai yi musu kallon hakan, tunda gashi ita kanta iya kwana d’aya kawai tayi a estate d’in but familyn yana neman hargitsewa! What type of daughter will she be idan ta yiwa Mahaifin da yake k’ok’arin making up to her sanadin tarwatsewar family d’inshi? Besides tanaso taje taga halin da Mama take ciki, so she has to leave, ta ko wanne hali a yau sai ta gudu daga estate d’innan!”
Da wannan tunanin ta dinga zabga gudu.
Cikin ikon Allah ta hango k’ofar gefen gate d’in gidan a d’an bud’e kad’an dan haka ta k’ara gudu ta bi ta k’ofar ta fice…
Tun tana jin muryar Abba wanda ya biyota yana kwala mata kira har ta daina.
Fitulu ta ko ina tarr!! Kamar rana, shiyasa ta samu damar ganin gabanta cikin sauk’i!.
Gudu kawai take tun iyakar k’arfinta…
Tana gudu tana kallon baya taga fitowar Abba daga gidan Granpa inda ta fito.
Mai gadin ya tsaya yana tambaya taga yana nuno masa direction d’inta, hakan yasa tayi saurin b’uya a bayan motar data gani a gefenta jikin wani gida, tana d’an lek’owa kad’an ta jikin glasses d’in, gadan gadan taga yayo inda take dai dai aka bud’e k’aramar k’ofar shiga gidan dake jikin gate d’in da alamun fitowa za ayi,
Allah ya taimaketa Daddy ya biyo Abba yana mishi magana dan haka ya juya gareshi…
Wani wawan tsalle tayi da mugun sauri ta afka gidan.
Da sauri yasa hannunshi ya dafe bango d’ayan kuma ya dafe bayanta, wanda
hakan da yayi ne ya taimaka musu basu zube a k’asa ba!
K’amshin turaren shi da tun ranar da suka fara had’uwa ta sanshi da shi ne ya tabbatar mata da waye!!
K’ok’arin barin jikinsa take yi amman bata san dalilinshi na rik’e mata baya ba!..
Dukkanin k’arfinta tayi amfani da shi wajen ganin ta raba kusancin nasu amman hakan sai ya gagara! Don ruk’on da yayi mata bana wasa bane, as if his life depends on it.
Gaba d’aya sai ta sake firgicewa, kukanta ya k’aru barema yadda taji zuciyar shi na wani kalar mahaukacin bugawa....
So yake ya cire ta a jikinshi amman ya kasa, idan ana maganar over racing to shine abinda zuciyar Aslam ke ciki a halin yanzu, tun daga lokacin da yaga tayo tsalle ta shigo da gudu tana kallon baya, har kawo yanzu da take a jikinshi....
Tun lokacin da Arshaad ya fara kiran sunanta taji, dan haka har d’an dukan Aslam take tana kuka akan ya barta! Amman kwata kwata babu chanji a yanayinshi sam, it’s like yama k’ame a hakan ne ko yaya ne ita dai ta kasa ganewa.
Sai da Arshaad ya k’araso ya kama hannunshi wanda ya rik’eta gagam, da kyar ya iya b’amb’areta daga jikinshi..
tukunna hankalinshi ya fara dawowa jikinshi a hankali abhankali…
Sannan da kyar ya cika bangon ya d’an seseta tsayuwarshi kafin ya kalli Arshaad wanda kafeshi da manyan dogayen idanuwansa.
He looks calm ammanfa idanunsa sun mugun chanja kala.
Gaba d’aya kuma sai abunda ya faru ya dawo mishi, take yaji wata kalar kunya ta lullub’e shi, da kyar ya Iya tattaro y’ar ragowar jarumtarshi, yana shirin yin magana suka jiyo muryar Abba da Daddy suna dumfaro su, Daddy yana cewa “ga k’ofar a bud’e maybe nan ta shiga, dan na san ba lalle an barta ta fita ba lets check.”
Da sauri Hudan wadda har yanzun gaba d’aya ilahirin jikinta ke rawa ta juya tana kallon Arshaad kafin a hankali tace
“Ya Arshaad dan Allah ka b’oye ni dan Allah.”
Tayi maganar tana had’e hannuwanta waje d’aya alamun rok’o, tana kuka.
Ganin sun kusan isowa ne yasa Arshaad d’in da sauri ya jata yasa a d’akin mai gadi sannan yace mata “ta shige toilet d’inshi(mai gadin) tayi shiru.”
Tana rufe k’ofar toilet d’in su kuma su Abba suna shigowa gidan, dai dai Arshaad yana shirin fita shi kuma, suka yi kicib’is!.
Kallon kallo aka tsaya yi,
kafin Daddy yace
“kunga Hudan?”
Aslam yana shirin yin magana Arshaad yace “No” da sauri sannan ya d’ora da
“Neman ta ake? ina tayi? Mai ya faru?”
Aslam kawai Abba ya k’urawa ido..ganin yak’i had’a ido da shi yasa ya cewa Daddy wanda yake shirin yiwa Arshaad bayani
“Mu koma kawai, inaga wajen Gwaggo Asabe tayi. Ma duba ta anjima, lets take care of Granpa, na tabbatr biyotan da muka yi yanzu ma case ne.”
100% Daddy ya yarda da hakan dan haka ya cewa Aslam “ya ci gaba da duba musu Hudan za suyi musu bayani anjima, shi kuma Arshaad yaje Gate yayi confirming in bata fita ba daganan ya sa curfew a estate d’in har su samu su gama meeting da Granpa su fito.”
Da “to” suka amsa musu daganan su Abba suka wuce.
Suna fita shima Arshaad ya fara k’ok’arin fita a gidan
“Kace mata zata iya fitowa.”
Shine kawai abinda ya iya cewa Aslam ba tare da ya yarda sun had’a ido ba.
Har ya juya yaji Aslam d’in ya ruk’o hannunshi…
Da sauri ya runtse idanunsa da k’arfi, sai da ya d’an dedeta fushinsa kafin ya juyo yana kallonshi.
Aslam tunda yake bai tab’a jin nervousness irin na yau ba, dan haka ya fara kame kame
“Um, I’m sooo sorry a b bout”
Da sauri Arshaad ya katseshi ta hanyar cewa
“It wasn’t your fault, tayi laifi, so ko baka yi abunda kayi ba dole na san wata rana gaskiya zata fito, kuma za ayi punishing nata. Kawai dai i was disappointed in you ne that’s all”
Sai da ya d’anyi shiru yaji hucin da yake yi ya d’an ragu
tukunna ya ci gaba da magana
“Ko sabon mai aiki aka chanja a gidan nan baka nan Aslam kana Uk but sai na kiraka na fad’a maka!
Ya kamata ace lissafinka ya baka ‘if Abba yana da y’a and bai san da ita ba, to dole akwai wani abu a k’asa’!.
Da kayi finding out about Huda you should have talk to me first mu samu mu fara bincike first!
Because that is wat i’ll definitely have done if i were in your shoes.
But you just went ahead and ruin everything.
Yanzu because of you Mahaifiyata is there a cell da anty Adama su da basu da laifin komai, they just help a friend.”
A hankali yace
“i tot we were brothers, best friends.”
Cikin katseshi Aslam yace “and yes we still are, yana matsowa kusa dashi da rik’eshi”.
Murmushi kawai Arshaad yayi ya zare hannunshi
sannan ya zagayeshi ya fara k’ok’arin shiga d’akin mai gadi.
Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e kafin yace “Ok, I’m sorry”
yana mai sake ruk’o hannunshi.
Sai da Aslam d’in ya maimaita sannan Arshaad ya juyo ya kalleshi na y’an seconds kafin yace
“Apology accepted.”
“Thankyou “
shine abinda Aslam d’in yace kafin ya d’aura da
“And about what you just saw, i’m..”
Cikin katseshi Arshaad yace
“Aslam we’re good fa, komai ya wuce, let me check on her, ta shiga toilet d’in mutumin nan barefoot kuma i don’t even know ko yana ciki dan ban ganshi a d’akin ba.”
Yana gama fad’in haka ya zare hannunshi sannan yayi cikin d’akin ya isa bak’in k’ofar toilet d’in yana cewa
“Hudan open the door, it’s me, su Abba sun tafi.”
A hankali take bud’e k’ofar tana d’an lek’owa..
Sai da ta tabbatar da shi d’inne tukunna ta k’arasa bud’ewa.
Murmushi ya d’anyi mata..
Gaba d’aya ta had’a gumi tayi zuru zuru!
A hankali yace “matsoraciya kawai”
A hankali tayi k’asa da kanta sannan ta fito, Allah ya taimaketa ba kowa a toilet d’in kuma mutumin yanada tsafta dan band’akin tass yake gashi tiles ko ina kuma a bushe. Amman dukda haka sai da Arshaad yayi amfani da ruwan butan da ya gani bayan sun fito ya zuba mata akan k’afafunta.
Suna fitowa ya cire takalminshi ya bata ta saka sannan yace “ta zo ta rakashi ya saka takalmi.”
A hankali ta fara kuka kafin tace masa “Ita wajen Mama zata je”
Gaba d’aya sai yaji wani matsanancin tausayinta ya kama shi. Shiruuu, yai yana tunanin ta yadda zai fita da ita bayan shi aka d’orawa alhakin curfew.
Dole ya lallab’ata ta d’an hak’ura ko zuwa gobe ne sai su je.
Matsowa yayi yana shirin lallashinta wayarshi ta hau k’ara, ganin sunan Sakina ya sanaya shi ce mata su k’arasa ciki akwai maganar da yake ai suyi da ita, dama. Tukunna sai ya kaita gurin Maman.
Ba tare da musu ba ta bishi suka yi hanyar shiga parlourn gidan, Aslam har zai bisu dan still ya lura Arshaad d’in is still mad, saboda da suka fito ko inda yake bai yarda ya kalla ba..
Sai kuma kawai ya chanja shawara
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 28