Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta dannawa Umma kira! Ko gaisawa bata bari sun yi ba ta fara magana “Umma, Huda aure zatayi! Ya Arshaad zata aura. Umma wallahi mutuwa zan yi in ya aureta Umma dan Allah kiyi wani abun, wallahi ina sonshi.” Cikin katseta Umma tace “Dalla malama ki tsaya ki nutsu kiyi min magana yanda zan fahimceki” Cikin kukan jalilan ta hau yi mata bayani tiryan tiryan akan yadda taji Gwaggo Asabe suna maganar auren ita da wata mai aiki satin baya daya wuce data tambayeta kuma ta gasgata mata hakan sannan yanzu ma Arshaad d’in ya sake tabbatar mata. Cikin b’acin rai Umman tace “Kece ai Jalila da shegen son abunki! Nace miki ki kawo kud’i kin k’i ki bayar ya kikeso in yi? Babanku ma yanzu haka baya nan ya gudu saboda ba zai iya rayuwa ba Maryam ba! Ga Ja’afar ba lafiya! Ga Junaidu ya b’ata! Matsalalo gasu nan burjik sunyi mana yawa ke kuma kin matse bakin aljihu ya kike so inyi???. Ni kaina sai na mutu dan bak’in ciki in dai Huda ta auri Arshaad d’innan ba ke kad’ai ba! Haba dan Allah mana sai kace su kad’ai Allah yake so?? Baban ta mai kud’i sannan ta auri mai kud’i! Inaa, ba zai yiu ba gaskiya!” Umman ta k’arashe maganar cikin tsananin tashin hankali. Cikin kuka Jalila tace “Umma yanzu meye abun yi? Dan Allah karta aure min shi wallahi Umma ina son Ya Arshaad sosai.” Ajiyar zuciya Umman ta sauk’e kafin tace “Ki bani kud’i! Ki turo kud’i! Ki zuba mini ido kawai, shine abun yi.” A hankali Jalila ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace “Tam shikenan, Ta accnt d’inki ko?”. “Eh” Kawai Umman tace saboda tsantsar tashin hankalin da take ciki ba zai iya barinta tayi magana sosai ba. “Tam” kawai Jalila tace ta kashe wayar daganan ta tura mata ragowar kud’in accnt d’inta da ta ishi Auwal, ya tura mata da kyar.............. Bayan Arshaad ya tafi sun d’an tab’a hira tukunna Gwaggwo Asaben tace “itama bara taje ta bawa Mommy maganin nata ta sha ta shaafa dan yanzu ita take yi da kanta” Har ta yi gaba sai kuma ta juyo tace “Ka zo muje kaga jikin nata mana”. Ahankali ya girgiza kai kafin yace “Gwaggo na san da sauk’i tunda gamu waje d’aya amman lafiya, kuma kin ce tayi garau yanzu to ai Alhamdulillah! Inaga ba sai na je ba, kar muje a samu matsala.” Shiruuu, Gwaggo tayi.. Ita har ga Allah so take Aslam d’in yaje ya ga Mommy watak’il In ya ga ta warke shima ya samu ya rage damuwar da ta hau kanshi. Amman tunda taga baya so bara kawai ta kyaleshi. Ganin dayayi kamar bata ji dad’in musun da yayi mata bane yasashi mik’ewa kafin yace “muje to” Murmushi ta saki tace “Yauwa d’an albarka, muje.” Itace a gaba shi a baya Haka suka nufi saman ba don ranshi yana soba gashi k’irjinsa In banda dukan uku uku ba abunda yake yi. Wutar parlourn a kashe suka tadda, suna k’ok’arin kunna flash d’in wayoyin su haske ya gauraye ko Ina! Bata lura da shi ba tace “Yanzun fa nake shirin kiranki na jiki yau duk shiru! Sai kuma nace bara in yi wanka kafin ki zo, kin ga banma ida shiga d’akin ba naji motsinki.” Tana maganar tana tahowa garesu. Aslam mutuwar tsaye yayi! Dukda a cikin zuciyarsa hamdala yake yi na ganinta a hakan, amma kuma bayaso suyi ido biyu dan bai san ya zata kaya ba! Hakan ne yasa shi fara ja da baya dan barin wajen Ita kuma kamar ance ta d’ago karaf! Suka yi ido biyu da ita...... Ta k’uraa mishi idanu ko kiftawa bata yi tana kallonshi kamar da mamaki akan fuskarta… Lura da hakan da Gwaggo Asabe tayi ne wadda itama ba k’aramin firgice ta shiga ba ya sanya ta daure taje ta fara jan hannunta tana “Muje ga tofin naki kisha In kin fito wankan sai ki shafa ko?” A hankali suka ji Mommy tace “Aslam!” Aslam wanda already ya juya da niyyar tafiya har ya d’aga k’afar shi jin ta kira sunanshi ya sanyashi dakatawa ba tare da ya sauk’e k’afar shi ko ya juyo ba! Sai da ta sake cewa “Aslam” Tukunna ya ajjiye k’afar ya juyo yana kallonta da idanuwanshi da suka rine lokaci guda!. Dafe kanta tayi da k’arfi, ta runtse idanuwanta kamar mai son tuno wani abun… Ganin haka yasa Gwaggo Asabe ta sake kamo ta kafin ta ce mata “Muje ki huta dan Allah” Sannnan ta baya ta yiwa Aslam d’in alamar ya tafi da hannunta. A hankali Mommy ta bud’e idanunta tana sake kallonshi kafin tace “Asabe me ya faru da ni? Kin ce nayi rashin lafiya meye ne ya sameni? Na shekara nawa?. Kinga fa Aslam kina ganin abunda nake gani kuwa? Shekara ta nawa a kwance? Dan Allah kimi.....” Gigitacciyar rungumar da Aslam wanda ba suba tahowarshiba yayi mata ne ya sanya ta kasa k’arasawa… Tana shirin yin magana taji Gwaggwo Asabe ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi cikin kukan banda kalmar “Alhamdulillah!” Ba abunda take ta nanatawa. Da kyar Mommy ta iya b’amb’aro Aslam daga jikinta, a hankali da hawaye sharkaf akan fuskarta ta shafa fuskarshi wadda ta koma jajir kafin tace “Loosing memory nayi ko?” Ta fad’i hakan tana mai fashewa da kuka. Rasa wanda zai rarrashi wani akayi tsakanin ita da Gwaggo Asabe.. Aslam kam banda ajiyar zuciya ba abunda yake sauk’ewa! Shi kanshi yau so yake hawaye ya zubo ta idanunsa amman abun ya gagara! A hankali ya cika mata hannunta dake cikin nashi ya dan jaa da baya kafin ya seseta gabas ya durk’usa yayi sujjada! Da sauri itama Gwaggwo Asabe tayi sujjjadar, ita kam Mommy tsayawa tayi tana kallonsu tana hawaye da mamakin abunda ya sameta haka… ….Wani abun mamakin still shine yanda ta kasa tambayar inda Aslam d’in yake har sai da ya baiyyana a gabanta! Wanne irin loosin memory tayi haka ita kam? Aslam wanda ta san shekarunshi basu wuce 12 ba shine yanzu haka wanda ta tabbatar yafi 30! Daman tun kwanaki 7 da suka wuce tayi noticing yanda Gwaggo Asabe tayi aging da kuma ita ma kanta! Mai ya faru? Wanne irin ciwo tayi haka? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun Allahumma ajirni fi musibati… Take ta maimaitawa cike da rud’ani da alajabi gaba d’aya kwanyarta ta cunkushe............ A hankali Aslam ya mik’e ya kama hannunta suka shiga d’akinta ya zaunar da ita kafin yace “Ina yake miki ciwo, yanzun?” Murmushi tayi ta shafa fuskarshi a hankali tace “Ba ko ina” Sai kuma ta sake fashewa da kuka. Hugging d’inta kawai yayi yana tapping bayanta. A hankali ya d’auko wayarshi, ya hau kiran Dad video call, bai damu da time ba. D’auka Dad yayi suka gaisa yana tambayarshi “ya shirye shirye na bikin su Arshaad?” A hankali Aslam yace “Alhamdulillah” Sai kuma ya gyara zamanshi ya matsa kusa da Mommy ya kamo hannunta cikin nashi ya d’an kalleta yayi murmushi yana ganin yanda ta k’urawa Dad d’in ido, kafin ya juyo ya kalli Dad shima yace “Alhamdulillah Dad..” Bai ida rufe bakinshi ba, yaji Dad d’in ya saka kuka, cikin kukan shima yace “Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!” Sannan yace “Aslam ganinan zuwa yanzun nan, in shaa Allah” Da sauri Aslam d’in yace “No dad, kabari sai gobe yanzu dar....” Kit! Dad ya kashe wayar ba tare da ta tsaya jin maganar Aslam d’in ba. Anan aslam ya zauna, ya rik’e mata hannu gam kamar ance za a kwace mishi ita! Sai kallonta yake yana murmushi yana sauk’e ajiyar zuciya in yaji hakan bai mishi ba yasa hannu yai hugging d’inta. Ita ma Gwaggo Asabe a daren ta kira Yaranta duk biyun ta fad’a musu halinda ake ciki, murna a wajensu ba a magana, suka ce “in shaa Allah, za su tambaya. Za su taho suma in shaa Allah.” A haka Mommy ta sha addu’o’i ta shafa da hannu d’aya dan Aslam yak’i cikata, Gwaggo Asabe tana musu dariya tana kuka at the same time. Ko cikakkiyar awa biyu Dad bai yi ba, sukaji tsayawar mota. Aslam ne yace “Oh Dad, dana sani da ban fad’a mishi ba. Waye ma ya d’auko shi a airport d’in sai Allah tunda gashi bai kira ni ba.” Murmushi Gwaggo w tayi kafin tace “ai ko kaine a matsayin shi na tabbatar sai ka zo” Murmushi shima yayi kafin yace “Kuma fa hakane” Cikin minti goma ya iso cikin d’akin! Yadda ya gansu a zaune ne yasa hawayen da yake ta koma run yaga ya danne suka samu nasarar zubowa. A hankali ya k’araso ya had’asu waje guda ya rungume .. Shi kuka Mommy da kanta ya d’aure da komai kuka Gwaggo Asabe ma kuka Da kyar Aslam wanda duk ya fi su son yin kukan ma ya samu ya lallashesu, daga nan aka hau murna k’arshe dai ba wanda ya runtsa a cikinsu har asuba. Kafin gari ya gama wayewa kuwa, labari yaje kunnuwan kowa a estate d’in, har su Abba. Daga masallaci Arshaad ya biyo Aslam suka zo tare dan ya ganewa idanuwanshi, ai kuwa shima har da kukan shi na tsananinfarin ciki. Haka shima Auwal yazo da daddare tare da Daddy da Abba duk a b’oye kar e ya gansu. Sun ji dad’in ganinta kuwa, sukayi barka suka tafi . Mommy kuwa tunda aka bata labari sannan taga su Arshaad da Aaima yadda suka girma da shi kanshi Aslam d’in, ta shiga alhinin ‘shikenan tayi missing teen age d’insu, da yanda suka taso kenan har abada?’ Gaba d’aya tausayin kanta da Aslam d’in sai ya lullub’eta.. Da kyar ta iya cin abinci, in banda kuka ba abunda take yi, tun ba ma da Dad ya gaya mata irin abubuwan data dinga yiwa Aslam d’inba, da irin rayuwar da yayi, gaba daya sai ta sake birkice musu, tana kuka tana cewa Aslam do yayi hak’uri ya yafe mata. K’arshe dai barin gidan ma yayi dan ba zai iya tsayawa tana kuka haka tana neman gafarar sa ba bayan ya san ba laifinta bane ba. Dad kanshi kasa zama yayi sai gidan su Abba yaje, ya d’an zauna yana dana sanin fad’a mata d’in da yayi. Sai dare aka samu damar kaita wajen Granpa, dan Gramma ita tunda taji labari ta taho itama suna tare ranar har dare. Ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwarta ya yi mata ya jiki. Ba abunda yake b’ata mishi rai irin yanda Gramma take ta faman yayatawa cewa “Ai Hudan ce ta bada shawarar yi mata sauk’ar Qur’ani kullum”. Har sai da ya kwab’eta ta hanyar cewa “Ta daina cewa ‘Huda’! Kawai ta dinga cewa Allah ne ya bata lafiya ya warkar da ita.” Gramma ta so yi mishi bayani, amman ganin kamar ranshi a d’an b’ace yake kuma ta son ba ya son jayayya yasa kawai tace “In sha Allah, Granpa. Zan gyara.” Tun daga kan Gramma har Aaima ba wanda bai bada zakka da sadaka ba na ban mamaki! Sauk’a kuwa ba su daina ba ana kan yi dan Dad cewa yayi “zuwa k’arshen watan nan ma in Allah ya yarda aka kammala na Mommy to ba dainawa za ayi ba duk sati sai an yi sauk’a a cikin eatate d’in a tsakanin su, in shaa Allah”. Yau kusan sati d’aya da warkewar Mommy, har su Hudan sai da suka zo suka yi mata sannu da barka a b’oye da daddare. Mommy tayi matuk’ar murnar ganin Sudais da Shuraim ita daman tana son twins, kuma tunda taji labarin suna da twins a family d’in taketa so ta gansu da su da Huda. Tunda Mommy taga Huda Allah ya d’aura mata k’aunarta, especially ma da taji gudummawar data bayar akan rashin lafiyarta.. Tayi mata godiya yafi a k’irga! Ita kam Hudan wani tsoron Allah da girman zatin shine ya sake shigarta, tana tunawa ko 2 month ba ai ba ta ganta a hargitse amman kalleta yanzu garau! Tabbas a rayuwa, in dai mutum yana neman sauk’i! Waraka! Taimako! To kuwa ya nema a wajen Ubangijin Talikai wanda bashi da kishiya. Da kyar ranar ta barsu suka tafi, ita Huda mamakin ma yanda matar take mata take yi, kamar ta santa tun daa chan amman da ta tuna yanda Mommyn ta bata labarin shak’uwarsu ita da Mama sai tayi tunanin ko saboda Maman ne yasa take yi mata haka.... Sannan itama a lokaci d’aya taji girma da k’aunar matar ya shige ta. A b’angaren Mommy kuwa, kawai tsintar kanta tayi da tsananin k’aunar Huda, dan koda bata kasance y’a ga Maryam ba tabbas Ubangiji ya d’aura mata k’aunar Yarinyar a ranta. Ba abunda yafi sosa mata rai irin da taji cewa ‘an sa ranar ta da Arshaad!’ Saboda ita har ga Allah tun da ta d’aura idonta akan Yarinyar ta fara kwad’ayin ganinta da Aslam d’inta a matsayin maaurata! Amman kuma da ta duba taga abunda yayi Aslam shi yayi Arshaad sai ta hak’ura ta barwa Allah komai sannan ta bisu da fatan alkhairi......................... BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 50. Yau saura sati biyu auren su Hudan, sai shirye shirye ake yi. Yayinda jikin Mama yayi sauk’i sosai abun har mamaki yake bawa jamaa kamar ba wadda ta karye ba, follow up kawai take zuwa abunta. Abba da kanshi yaje ya siyowa y’arsa kayan d’aki na gani na fad’a, hatta cokali bai bari ba sai da ya siyo mata komai bayab ya tambayeta taste d’inta, wasu kuma yana daga chan d’in yake turo mata Sakina ta tayata zab’a. Sannan ya had’a mata gara nan ma na gani na fad’a. Lokacin da bikin ya rage saura sati d’aya already kayan gara da kayan d’akin amarya suna gidanta. Duk da ba wai zama za suyi anan d’in ba, kai ta kawai zaayi gidan daganan su wuce karatunsu amman hakan bai sanya an k’i yi mata kayan d’aki ba saboda time to time za su ke zuwa hutu. Shima Arshaad a nasa b’angaren hakan bai hana sa siyan gida ba! Daa a cikin estate d’in zai zauna amman da yake Granpa ya san Hudan zai aura haka nan k’iri k’iri sai ya hana sa gida! Da farko Granpa d’in cewa ma yayi ya bar mishi estate d’inshi, tun kafin auren! Da kyar Aslam ya lallab’ashi ya hak’ura amman dukda haka sai faman neman fad’a yake yi kuma fa sai da Dad ya tambayeshi tun farko lokacin kafin ma a saka rana amma sai ya nuna irin shi ba ruwanshi d’innan su yi abunda sukeso.. Yanzu kuma da bikin ya taho sai neman rigima yake yi yana neman abokin fad’a! Shiyasa kowa ya sha jinin jikinshi dan duk wanda yayi rashin sa’a ya yarda ya samu matsala da Granpa a wannan yanayin da yake, tou tabbas kashin shi ya bushe! Wannan dalili yasa Arshaad ya sayi gidanshi da kanshi daman kuma shi har ga Allah ya ma fi son ya yi komai da kanshi, dan da kyar ma ya yarda ya bari Daddy ya bawa Mommy mak’udan kud’ad’e take had’a mishi zazzafan lefe.. Gida kuwa da Abba yace zai siya mishi yi yayi kamar zai yi kuka, shi kuma Abban ya dage! Sai da Mommy ta saka baki tukunna Abban ya hak’ura ya bar Arshaad d’in ya sayi gidanshi mai hawa biyu d’aki bakwai da parlour hud’u har da d’an k’aramin bq a gefe a nan cikin Nasarawa sai dai da d’an tafiya tsakaninsu da gida da estate.... Su Ummu da Mommy ne suka je suka yi mata jerenta tsaf! Wanda yanzu kawanchen Mama da Mommy ya dawo sabo fil! Dan har gida Mommy taje ta dubota, duk da Dad ba wani son yawan fitar tata yake yi ba amman indai abu ya shafi Maryam to ya kan bari saboda Mommyn tana yi musu campaign a lamarin Abba, sai ita kuwa Mama duk maganganu da Mommy take mata akan Abban amsa d’aya zuwa biyu take bata kullum ‘Allah ya zab’a mafi alkhairi’ ko kuma tace ‘ita fa ta riga ta hak’ura da Abba har abada! Ba akan dalili d’aya ba sai akan dalilai barkatai’. Amman duk hakan bai sanya Mommy ta hak’ura ba, haka nan suke fama kullum......... Yau sauran kwana uku d’aurin auren! Su Hudam basu samu komawa wajen Mama ba sai a yau d’in. Kafin su wuce Abba ya nemi ganinta.. Kamar ko wanne uba haka nan ya zaunar da ita yayi mata nasiha mai ratsa jiki! Yana hawaye tana kuka haka su Sudais suma da suka zo yi mata sallama… A haka dai ba dan suna so ba suka yi sallama Abba ya sanya mata albarka. Mommy da kanta ta kaita har gidan Shuwa gaban Mama Hudan tayi mamakin ganin baki y’an Maiduguri da suka zo dan gidan a cike tap! Suka tarar anata hada hada. A yau d’in zasu fara event! Dan haka suna isa suka tarar har mai kwalliya ta k’araso tana jiransu, waensu a cikin friends d’in su ma duk sun zo, da yake mai kwalliyar da tayi mata ita ce za tayi musu saboda Arshaad Maiduguri style yayi..duk shi ya biyawa friends d’inta kud’in makeup da anko. M T Tunda Mommy ta warke kullum itake ce take yiwa Aslam girki… Wani special kulawa take bashi amman ta rasa dalilin damuwarshi dan ko jiya ma sai da Doc ya zo ya dubashi kuma ya tabbatar musu jininshi ya k’i sauk’a instead ma k’ara hawa yayi! Sannan ga zazzab’insa shima ya dawo. Gaba d’aya hankalinsu duk a tashe yake, dan sun rasa gane kan Aslam kwata kwata. Arshaad tun yana kulashi, yana tambayarshi meke damunshi yana lallab’ashi, har ya zo ya hak’ura kawai ya watsa shi a kwandon shara Dan Arshaad d’in gani yayi kamar ma Aslam d’in haushinshi yake ji! Idan ma yana waje Arshaad d’in ya shigo kawai sai dai ya tashi ya fice ya bar mishi wajen, ko magana baya so ta had’asa da shi! Kamar ma wanda yake k’ok’arin yin gaba da shi ta k’arfi da yaji! Shiyasa Arshaad d’in kawai ya rabu da shi amman a chan k’asan zuciyarshi mamakin abubuwan da Aslam d’in yake mishi a wannan lokacin da ya kamata yafi kowa tayashi murna, yake yi. Hatta Dad Abba da Daddy sun lura da hakan, basa son shiga tsakaninsu tunda sun fi kusa shiyasa kawai suka zuba musu ido a ransu suna mamakin mai ya had’a best friends haka??……. Da yamma, Mommy na d’aki tana jera kaya a wardrobe Dad ya shigo.. A bayanta ya tsaya yayi hugging d’inta. A hankali tayi murmushi kafin ta juyo still yana rik’e da ita tace “ina wuni Dad” Murmushi shima yayi mata yana jin tsananin k’aunarta tana nunkuwa a cikin zuciyarshi, a hankali yace “Bayan waennan akwai wasu kuma da kike buk’ata??” A hankali ta girgiza mishi kai alamun ‘a’a’. Ajiyar zuciya ya sauk’e, kafin ya jawo hannunta suka nufi gadon dake d’akin. Sai da ya zaunar da ita shima ya zauna a daff da ita tukunna yace “Aisha, magana nake so muyi dake ta gaskiya da gaskiya” Da sauri ta mik’e tana k’ok’arin kawar da kanta daga gareshi kafin tace “Not again Dad, na gaya maka ban tuna komai ba, please Dad ka bar maganar nan.” Mik’ewa shima yayi ya sake rik’o hannunta kafin yace “Look at me kice mini ‘wallahi Dad ban tuna komai ba‘.” Hannunta ta fara k’ok’arin kwacewa a cikin nashi ta had rai sosai cikin fushi tace “Tunda baka yarda da ni ba, shikenan!” Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace “Jiya da yamma kin manta wayarki a d’akina kin tafi kitchen, naje kai miki wayar saboda a nata kira.. I didn’t mean to eavesdrop but i have no choice! Naji komai maganan ku da kuka yi ke da Asabe!.. Mai yasa kika b’oye min?”. Gabanta ne ya yanke ya fad’i! A hankali ta tsaya tayi tsit ta nutsu ba tare da tace komai ba, sannan ta kasa d’agowa ta kalleshi… Hannu yasa ya kamo hab’arta ya juyo da fuskarta ya d’ago fuskar, da sauri ta runtse idanuwanta. Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sake sauk’ewa kafin a hankali yace “Maimaita min abinda ya faru that very day da kika fad’o, waye ya turoki?! Ina so inji daga bakinki, don’t lie, kin san naji komai.. Kawai i want you to tell me.” A hankali tace zan fad’a maka amman sai ka yi min rantsuwar ba zaka fad’awa kowa ba sannan ba zaka nuna ko da a fuskarka ne ba.” Cika fuskarta yayi cikin fad’a yace “Ba zan iya ba Aisha! Ya zama dole in fad’a sanann in nuna fushi kuma in d’auki mataki! Dole ne in hukunta mai laifi! Kin san irin ciwon da kika yi kuwa? Kin san irin wahalar..” Cikin katseshi tace “To kaga dalilin da ya sanya na b’oye maka ko?” Cikin karyewar zuciya taci gaba da cewa “I have lost a lot, shekaru sun jaa.. Na ci burin yiwa y’ay’ana tarbiyya especially ma Aaima da ta kasance mace amma kalli fa duk nayi missing Mai ya rage yanzu?. Ni za kayi wa abun nan ko? A kaina kake so ka hukunta me laifin ina? To ni d’in nace ‘na yafe har abada har gaban abada!’ Meye kuma na dawo da abunda ya riga ya wuce??. All i need to do now shine ibada dan kwata kwata ban gamsu da sallolina da kuka ce inayi ba, Nafilfili da ibada su kawai nake buk’atar inyi a halin yanzu, ba wai case da holding grudges ba! I want peace.” A hankali ganin ya d’an nutsu yana kallonta kawai, ta kamo dukkannin hannuwanshi biyu ta rik’e tace “Dad, duniyar ma duk nawa take? Idan fa mukayi hak’uri ma duk mutuwa za muyi! Yanzu idan kace zaka d’auki mataki wallahi square one zamu koma, mutane ba za su tab’a duba laifin da aka yi mini ba instead gani za suyi kamar ka fifita ni ne wanda fifita Aslam da Granpa yayi tun farko ni na tabbatar shiyasa aka zamo silar zabgemin kusan rabin rayuwata haka nan na yi ta a wahala! Please dan Allah let it go, for me..” Mommy ta dad’e tana kwantar mishi da hankali, da nuna mishi ita kwanciyar hankali kawai take buk’ata yanzu, tukunna da kyar da mugun kyar ya yarda da buk’atarta akan ba zai yi komai ba, kuma ba zai nuna ba ko a fuska! Tukunna a hankali ta hau fad’a mishi abunda yaji tana fad’awa Gwaggwo Asaben..... In banda ajiyar zuciya ba abunda Dad yake sauk’ewa a jejjere… Ji yake kamar ya mutu dan tashin hankali da takaici gashi ta saka shi yayi mata alk’awari. A haka Aslam ya shigo ya samesu.. Tabbas ya lura akwai abunda suke tattaunawa but yadda Dad yayi ta k’ok’arin ganin ya danne ne yasa kawai ya basar dan ya fahimci koma menene to bai shafesa ba. Gaidasu yayi ya nemi waje ya zauna a k’asa kan kafet yana kallonsu k’aunar iyayen nashi tana sake shigar mishi zuciya yana jin wani farin ciki yana taso masa ta k’asan zuciyarshi just by looking at them. Suma d’in shi suke kallo wanda tashi d’aya In ka kalleshi zaka hango tsananin damuwa da k’uncin da yake a ciki... “Ya baka shirya ba? Yanzu muka gama waya da Arshaad, yace yanzun za a tafi gudun kar ayi dare, kai da Aaima kawai ake jira. Na kira Aaiima tace min ta shirya tun d’azu, a tunanina kun wuce ma.” Ajiyar zuciya Aslam d’in ya sauk’e kafin a hankali yace “Am, daman sallama nazo in yi muku.” Da mamaki suke kallonshi. Bai jira jin me za su ce ba yace “Inaso zan wuce Uk! Akwai ayyukan da nake so In k’arasa a chan. K’uraaa mishi ido kawai yaga sun yi, har ya fidda ran za suyi magana yaji Mommy tace “Mai yasa? Ka fad’i mini gaskiya dan na san akawai dalili Aslam” Murmushi kawai yayi kafin yace “Please ku barni in tafi, dan Allah” Mik’ewa Dad yayi ya nufi hanyar fita kawai ba tare da yace mishi komai ba, ya fice. Hannu Mommy ta mik’a mishi, a hankali ya sa hannun nashi cikin nata ya mik’e ta dawo dashi kan gadon inda Dad ya tashi. Cikin kulawa ta kallesa tace “Aslam meye damuwar ka? Ko har yanzu kana jin zafin abubuwan da nayi maka ne?” Ta fad’i hakan muryanta na d’an rawa kamar wadda zata fashe da kuka. Da sauri yace “Mommy please mana, ki daina tunanin hakan sam a haka bane, ai ba laifinki bane ba.” Cikin katseshi tace “To yaya ne? Menene? Talk to me dan Allah! Ko kanada wadda ta fini? Talk, kai kanka za kaji nauyin zuciyarka ya ragu. Waye ya b’ata maka rai? Ko kana da masaniya akan abunda ya faru ranar dana fad’o? Fad’a kukayi da Granpa? Ko Daddy ko wani? Ko Arshaad ne? Ko company d’in ne? Naji Dad yace it was successful kun bud’e kai da Abba, akwai wani abun ne?” Duk ta rikice tambayoyi kawai take jero mishi barkatai. A hankali ya lumshe idanunsa, sannan ya d’auko Dayan hannun shi ya d’aura akan hannayen nasu! Ganin haka yasa itama ta d’auko Dayan free hand d’inta ta d’aura akai ta bashi dukkannin attention d’inta a hankali tace “Talk, I’m your mother, I can help you.” Bud’e idanuwanshi da suka yi jaa yayi, a hankali ya fara magana “I know I’m trying to be selfish here, but.......................... .” Wata k’akk’arfar ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e bayan ta

Chapter 21 of 28