Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a ciki ne ya ziyarceta a take, lokaci guda!. Akan kujerun suka nemi wajaje suka zazzauna. Sai da suka gama gaisawa da Abban tukun ta juya ta gaidasu A hankali Aslam yace “Lafiya Alhamdulillah” Arshaad kuma yana d’an murmushi ya d’aga mata gira d’aya yace “fine” a hankali. Murmushi tayi itama ta maida kanta k’asa. A hankali Aslam ya lumshe idanuwanshi kafin ya bud’e yace “Abba, Arshaad yace wai akwai meeting inzo kana son ganinmu” Murmushi Abba wanda ya fahimci Arshaad d’in yayi kafin yace “Ni shi kad’ai na kira, sai dai kuma na lura har kunyar surukai ta fara shiga tsakaninmu tunda gashi sai da ya nemo d’an rakiya.” Murmushi Arshaad d’in yayi ya sunkuyar da kanshi k’asa yana danna wayarshi dan gaskiya Abban ya fad’a sam bai san daliliba amman wata kunyarshi yake ji kwana biyun nan. D’an murmushi kad’an Aslam d’in yayi yana mai sauk’e ajiyar zuciya. A hankali Abba ya sauk’e ajiyar zuciya shima kafin yace “Mun gama magana da Huda saura kai” Har zai fara magana sai kuma ya juyo yace “Daughter akwai wani abun da kike son sanar dani ko shikenan?” A hankali tace “ba komai Abba duk na fad’a kawai dai maganar zuwa wajen Mama ne, k’arfe nawa?” Murmushi yayi yace “bayan isha zan kaiki ku shirya ko?” Da “to” ta amsa tana murmushi kafin ya sallameta tayi musu sallama, ta wuce. D’an gyaran murya Abba yayi kafin yace “Arshaad!” Jin yanda Abban ya kirasa yasa Arshaad d’in d’agowa yana kallonshi with full attention. “No need na In tsaya tamabayar ka ko kana son Hudan tunda gashi duk ka fad’a mana ko? But inaso In sake tabbatarwa tunda kaga shi aure ba abun wasa bane, sannan kuma inaso ka tsayar da kanka da hankalinka waje guda kafin a gama magana, dan naji Dad yana cewa 2 months kawai za a saka bikin saboda tafiyarka! So kaga kar aje abu ya taho kuma kuzo ku fara inda inda, bayan ba wannan lokacin.” D’an tari kad’an Aslam yayi, kafin ya mik’e tsaye yace “Abba Ina zuwa, i’m thirsty” Bai jira jin me zasu ce ba ya fice daga parlourn ya sauk’a chaan k’asa. Yana fita Abba ya ci gaba da cewa “Sannan magana ta biyu! Why do you hide Hudan away from me?? Meye shirinka? Bana so ka b’oye min komai” A hankali Arshaad ya lumshe shanyayyun Idanunshi, kafin ya bud’e su ya d’aura akan Abban sannan ya fara magana “Abba ba 2 months ba, ko nan da 2 days ne aka yanke ranar aurenmu, I’m ready in auri Hudan dan ita nake so, so na tsakani da Allah, Ita nake son aura in rayu da ita har abada, na yanke wa kaina wannan decision d’in 3 years ago and I don’t think akwai rana d’aya dana tab’a jin tunanin sauya decision d’ina. Magana ta biyu kuma Tabbas na fahimci wacece Huda, tun ranar da muka had’u da Mama a graduation d’inta saboda naga pictures d’inta (Mama) da yawa a locker d’inka da sunan ta and everything a time d’in da kace in tayaka, parking. But I’m really sorry Abba i was selfish back then, shiyasa na k’i fad’awa kowa har ita (Hudan) dan na san no mattarr how much I love her itama take sona muddin iyayenta (b’angaren uwa) suka fahimci waye ni to ba zasu tab’a yarda da auren mu ba duba da issues d’in da suke tsakanin families d’in kuma kaima it can cause problems for you daga Granpa dan na lura maganar kad’ai idan akayi ran kowa sai ya b’aci a estate d’in. Shiyasa na rok’i Baban Sakina akan ya b’oye identity d’ina har iya lokacin da za a d’aura mana aure, daga nan zan san yanda zan yi In shirya ku kaida su Madu, tunda kuma ga auratayya a tsakani, dole a na san za a hak’ura a sauk’o a yafewa juna… Na san nan ne side d’in Mahaifinta mun fisu k’arfin da iko da ita amma da nayi lissafi tabbas naga akwai possibility d’in suci galaba a kanmu, ni kuma issue ko case ne kwata kwata bana so har in samu cikar buri na shiyasa nayi k’ok’ari wajen ganin na danne duk wani abu da ka iya zama mini matsala wajen ganin na mallaki Huda a matsayin matata. I know I was wrong! Ban san taya zan fara baka hak’uri ba, but I did everything out of love! Dan to be honest a yanda nake jin k’aunar Huda a raina Abba wallahi I don’t think I can go on living idan aka yi tunanin raba ni da ita! Please try to understand and forgive me.” Ya k’arashe maganar cikin tsananin kalar tausayi kamar wanda zai fashe da kuka. Shiruuu, Abba yayi yana nazari kafin yace “Arshaad na san menene so, tbh a lokacin da nake tare da Maryam, ake k’ok’arin rabamu! Hakan nima nayi na zama selfish har naga mun mallaki juna… Amman abunda kai kayi is morethan selfish, Arshaad banji dad’i ba, ka k’i ka baiyanar mini da y’a ta.” Shiruu, Abba ya d’anyi kafin ya sauk’e ajiyar zuciya yaci gaba da magana “But, zan iya yafemaka! Zan yi k’ok’ari In manta da abunda kayi after all everyone deserves a second chance sannan naji reason d’inka and its not all bad. But Arshaad don’t ever try something like this again saboda i as selfish back then just like you and abun bai yi ending well ba! Although I was happy for good 10 years, but har yau Maryam is not in good shape with her parents because of my decision.” A hankali Abba ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace “And another thing thankyou so much! Hudan ta fad’amin yadda ka dinga d’awainiya da su har makaranta, Allah ya saka maka da alkhairi.” A hankali Arshaad yayi murmushi kafin yace “Ba komai Abba, thankyou” Murmushi Abban yayi kafin yace “A matsayina na Mahaifin Hudan! Na baka ita Halak Malak! Allah ya nunamin ranar da zan aura maka ita. Dan Allah Arshaad ka kula min da ita.” Ya k’arashe maganar, cikin nauyi da karyewar zuciya. Zamowa Arshaad yayi daga kan kujerar da yake kai kawai ya hau godiya, yana yi masa alk’awarin in shaa Allah zai bata dukkanin kulawar data kamata….. Sai godiya yake yi, har sai da Abban ya sallameshi tukun ya mik’e ya fita still yana godiya. Murmushi Abba yayi bayan fitar Arshaad d’in, ba abunda ya zo kanshi sai lokacin dasu Kaka suka bashi Maryam! Yanda Arshaad yayi exactly shima hakan yayi….. A hankali yayi murmushin da har sai da y’ar kwalla ta zubo daga idanunshi! Yana tuno ta (Maryam) da moments d’insu…. Chaan, ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya, a hankali yasa hannu ya sharce kwallar shi, sannan yace “Astaghfirullah”. BULAMA ✍️ So da Buri Free Book 45 Kiran sallah aka fara, dan haka ya mik’e ya wuce toilet ya d’auro alwalla ya sauk’a don zuwa masallaci. Arshaad yana zuwa k’asan, ya tarar da Aslam a tsaye jikin dispenser yana shan ruwa.. wanda jin sauk’k’owar tasa ne yasanya shi ya juyo. Fara’ar da ya ga yana yi ne ya sanya Aslam d’in fahimtar wani abu dan haka yad’an matsoshi yana shirin yin magana yaga yayi hugging d’inshi yana wani murmushin da yake baiyyana tsantsar farin cikin da yake a ciki! Cikin farinciki ya cika shi still yana murmushi ya d’ago ya kalleshi sannan yace “Call me Ango! An bani mata”. Ya fad’i hakan yana dariya. Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e, sannan yace “Congrats bro, i’m very happy for you.” Cikin zolaya Arshaad yace “na yi maka wayo! Kai ma kayi sauri ka nemo..” Murmushi Aslam d’in yayi kafin yace “ka yi mini wayo kam!” Shigowar da Auwal yayi cikin parlourn ne ya katse su. Bai kalli kowa ba ya wuce yaje ya zauna akan d’aya daga cikin kujeraun parlourn… Aslam ne yace masa “Auwal ya gida” D’an d’agowa Auwal d’in yayi ya kalleshi, har zai ce wani abu kuma sai ya d’auke kai kawai yace “Fine” yana mai kallon hanyar staircase…. Bayan kamar 2 minutes Abba ya sauk’o. Cikin girmamawa ya gaida Abban har da d’an rissinawa! Da d’an mamaki Abba ya kalleshi ya amsa sannan ya wuce, su Aslam suma suka nufi hanyar wajen ganin zasu fita yasa shima ya mik’e suka nufi mosque gaba d’ayansu....... A dining d’in suka tarar da Hudan, Sakina Sudais da Shuraim don haka suka yi joinin d’insu su uku, banda Aslam wanda ya wuce gida daga mosque d’in don kanshi yana d’an ciwo! Shiyasa kawai ya wuce bayan ya cewa Arshaad “ya karb’a tofin ya taho dashi in sun gama”. Babu kunya haka nan Auwal ya samu guri ya zauna dai dai gefen Sakina! Da mugun sauri tayi zumbur! Zata mik’e Hudan tayi saurin rik’ota tana nuna mata Abba da ido. Suna shirin farawa Daddy ya shigo, yana ganinsu gaba d’aya ya cewa Abba “Wato ka had’a kan y’ay’anka ni kuma ka manta da ni, ko?” Dukkansu dariya suka yi kafin su shiga gaidashi one by one.. Cikin kulawa ya amsa musu yana mai cewa “Na gaji da cin abinci ni kad’ai daga yanzu kawai a dunga yin dinner a chan side d’ina, breakfast da lunch ku dinga yin abunku a nan, in ba haka ba shirun ai sai yayi min yawa, daga ni fa sai Auwal shima kuma in yaga dama ma sai ya kwana biyu bai yi dinner d’inba, yau kuma kalleshi ja’iri ya gudo ya barni!”. Duk dariya aka sa sannan suka fara cin abincin cikin nishad’i….. A zaman su Auwal ya cewa Sakina ‘Hi’ Yafi sau ashirin amman har aka tashi bata amsashi ko d’aya ba! Ko arzik’in kallo ma bai samu daga gareta ba k’arshema juyar da kujerar tata ta yi kad’an ta karkatar da hankalinta a Huda gaba d’aya! Wanda hakan ya sanya duk jikinshi yin sanyi dan tunda yake a rayuwarshi tun yana secondary school mace bata tab’a yi mishi haka ba, wasu ma sune suke cewa suna sanshi, dan ko a yanzu haka kafin yace yana so sau d’aya sai ance ana sonshi sau goma!!. Daddy ne ya fara mik’ewa sai Abba…. Auwal yana shirin yi mata (Sakina) magana tayi sauri ta mik’e ta haye sama Hudan kuma ita da Arshaad suka koma cikin parlourn suka zauna, su Sudais ma suka yi mishi sai da safe suka tafi. Kasa mik’ewa Auwal yayi a wajen, dan haka har Abba ya dawo ya taddashi yana nan bai tafi ba!. Hudan daman a shirye take dan haka ta kira Sakina a waya tace “tazo su je” Arshaad yaso yace zai je amman kunyar Abba sai ta hanashi yin maganar, dan haka ya yi musu sai da safe ya tafi bayan ya karb’i ruwan Addu’an Mommy. Auwal ma ganin yanata zama shi d’aya yasa ya yiwa Abban sai da safe ya tafi, bayan yaga sauk’owar Sakina. A tare suka fito shi( Auwal ) yayi part d’insu su kuma suka wuce mota Sakina na baya Hudan na gaba a haka har suka isa bakin k’ofar gidan Baba. Ba Hudan ba hatta Sakina zumud’i take yi.. Cikin rawar k’afa suka fita a tare suka shige gidan. Basu tarar da mashin d’in Baba a soro ba, da alamun bai kai ga dawowa ba. Gidan shiruuuu, sai d’an hasken fitulu da suke hangowa ta d’akin Umma da Mama. A hankali Huda tasa hannu ta d’an tura k’ofar kafin su shiga a tare da sallama… Kendir d’in dake kan dressing mirrow ne ya taimaka wajen haskaka d’akin! Tana zaune a k’asa gaban gado kan sallayarta, da charbi a hannunta, da alama bata tashi daga wuridin bayan Isha ba dan ga hijabinta ma a jikinta, a gefe guda kuma ta kunna maganin sauro yana d’an tashi da kad’an da kad’an. D’ago fuskarta tayi ta kallesu, kafin ta maida idonta k’asa kamar bata ga kowa ba!. Gaba d’aya jikinsu sai yayi sanyi, amman suka aro jarumta suka k’arasa inda take! Sakina ce tayi k’arfin halin hugging d’inta kafin tace “Mama Ina wuni ya jiki?” “Alhamdulillah” kawai tace Maman tace mata. Itama Hudan ta gaisheta ta bita da “Alhamdulillah” Sannan ta mik’e ta cire hijabin jikinta ta ninke da sallayar, ta mik’e ta haye gado ta kwanta abunta. Duk kasa cewa komai suka yi, d’akin ya d’auki shiruuuu. Wajen minti goma ta tashi taje ta kashe kendir d’in ta dawo ta tofa addua ta kwanta, harda d’an jan abun rufuwa. Sheshshek’ar kukan Huda ne ya sa Sakina kunna flash d’in wayarta! Itama Mama jin kuka yasa ta mik’e ta zauna daga kan gadon tana kallonsu a inda suke. A hankali Sakina ta cewa Mama “Mama dan Allah ki yi hak’uri mana.” Cikin katseta Maman tace “Hak’urin me?” Dibi dibi Sakina ta hau yi kafin ta samu damar cewa “Naga kamar kina fushi da mu ne” Murmushi Maman tayi kafin tace “ba fushi nake yi ba Sakina, ko kad’an bana fushi daku Kawai kun zab’i abunda kuka ga ya dace ne Nima kuma na zab’i wanda naga ya dace!” Ajiyar zuciya ta (Mama) sauk’e kafin ta juya kan Huda tace “Na san abunda kika yi ranar da kika zo duba ni a asibiti! Dukda Ummu taso b’oyewa amman naji kuma na fahimta! Na gode Hudan, Mahaifin ki ya fini ko? Ba komai.. Amman abunda nake so ki fahimta shine Tunda shi kika zab’a, to ki zauna a iya shi kad’ai kar in sake ganin k’afar ki a inda nake! In ba hakaba wallahi sai ranki ya b’aci! Na bar masa ke! Tunda naga a ganin ki yanzu ban dace ki zauna da ni ba, kin girma ko? Kin mallaki hankalin kanki, so bani da wani amfani a wajen ki, tunda ba abunda zan iya miki ko zan iya baki..” Wani irin kuka Hudan ta rushe da shi, tana shirin yin magana Mama ta katseta ta hanyar cewa “Haka ne mana, kar ki min kuka gaskiya na fad’a! Kinyi girma ai yanzu tunda har kika iya yankewa kanki decision..” Sakina ce tace “Mama dan girman Allah kiyi hak’uri, wallahi kin yi misunderstanding d’in mu ne Please Mama ki tsaya ki fahimcemu” “Hmmmm” Maman tace, kafin tace “Nima kun kasa fahimta ta Sakina ba wai haushi naji ba fa, kawai ina baku space d’in da kuke buk’ata ne, tunda gashi ta nuna min k’iri k’iri abubda ranta yake so ai kinga sai in barta in daina kutsa kaina cikin rayuwarta ko?? Ku tashi kuje dare yayi, na san yau ma yana waje yana jiranki! And maganar zuwa kotu itama na daina yi! Tunda gashi k’iri k’iri kin riga kin zab’i abunda kikeso, so ba amfanin zuwa kotun tunda babu amfanin inje inata yak’i ni kad’ai. Sai kuje ku yi ta rayuwarku mai dad’i cikin daula ke da Mahaifinki.” Tana gama fad’in haka ta koma ta kwanta abunta. Kusan 20 minutes suna bata hak’uri, amman tak’i kulasu Sai da suka kaita bango ta tashi ta balbalesu da fad’a tace “wallahi In basu fita ba zata dake su! Su bar ganin wai sun girma.” Mik’ewa Hudan tayi kamar zata fita, sai kuma ta koma da gudu ta je ta kanainaye Maman tace “Ni ba inda zan je, dan Allah ki daina fushi dani haka, ba zan sake komawa ba, anan zan zauna.” Kasa cewa komai Mama tayi.. Suna a haka wayar Hudan ta fara ringing, har ta tsinke ba wanda yayi yunk’urin d’aukar wayar… Sai da aka sake kira, tukunna Sakina tayi k’arfin halin d’auka ta d’an fita waje, ta fad’awa Abban halin da ake ciki “Sai da safe” kawai yace mata, daga nan ya kashe wayar! A chan d’aki kuwa, da kyar Mama ta d’an kulasu.. Sai da Hudan tayi mata alk’awarin ta bar zuwa gidan Abba har abada sannan ta d’an sauk’o…. Daga Hudan har Sakina, gabansu fad’uwa yake yi dan basu san ta inda zasu fara yi mata bayanin baikon Hudan da sa ranar da aka yi ba! Chaan dare! Kowa ya kasa bacci sai juyi suke yi, Mama ta hango kendir d’in d’akin Umma a kunne, ita tama yi tunanin ko tana d’akin Baba ne tunda ita ke da girki, gudun kar ya k’are ya kama wani abun yasa ta cewa Sakina “taje ta kashe mata kendir d’in, in k’ofar a bud’e take.” Tun daga bakin k’ofar d’akin Sakina fara jiyo gwarti! Tsaki tayi ta d’anyi sallama kusan sau uku, jin shiru yasa ta d’an tura k’ofar ta shiga… Kendir d’in saura kad’an ya k’are, dan ba don ta je ba ma to da babu abunda zai hanashi kama kan mudubin katakon d’akin, dan Umman bata d’aurashi akan komai ba kamar yadda taga Mama tayi ba. Kallonta tayi dariya taso kufce mata, da sauri ta hure kendir d’in ta fito ta maida k’ofar ta rufe ta wuce a ranta tana mamakin rashin hankali jahilci da rashin sanin ciwon kai irin na Umma! Ace y’arki tana nan da ciki a chan wani gidan da baki san ko su waye ba! Amman kalli yanda ta barrarraje tana shek’a uban bacci kamar wata jaka! Da wannan tunanin Sakina ta k’arasa d’aki ta tarar bacci yayi nasarar d’auke Hudan, daman ita bata da wuyar bacci. Itama Sakinan bata wani dad’e ba baccin ya d’auketa cike da tunanin rashin man kai irin na Umma…inda ace su Ummu ne akace d’aya a cikin ita ko Huda bata gida ta tabbatar ko gigin yin bacci ba zasu yi ba!….. Abunda Sakina bata sani ba shine Umma magani mai k’arfin tsiya ta sha, dan yau kusan kwananta uku bata iya bacci tun lokacin da Jalila ta gaya mata Huda cousin d’in Arshaad ce! Ga kuma Mahaifinta yana son ta harma sun bar gidan kakan da shi da yayanshi duk akan Huda! Yau kuwa da Jalila ta kirata take shaida mata irin daular da Hudan take ciki sai da ta kusa hauka! K’arshema dishi dishi ta fara gani! Ga zuciyarta tana ta bugawa da mugun k’arfi ga zazzab’i. Don haka ta lallab’a taje wani Chemist a chan bakin titi babba da aka bud’e sabo! Matar(mai chemist d’in yare mai mutunci) Anan ne bayan an gwadata matar ta tabbatar mata da jininta ne yayi mugun hawa…dan haka ta samu ta sha magani ta rage damuwa tayi bacci.. Tun achan chemist d’in ta nemi matar ta bata maganin da zai sakata baccin dan itama tana buk’ata, saboda ta san in ta samu baccin at least zata huta da tashin hankalin da take ciki na y’an awanni, kafin kuma ta farka. Mai chemist d’in taso ta hanata, but ganin halin da take ciki yasa kawai ta siyar mata saboda tayi mugun tausaya mata dan a yanda jininta ya hau ita kam tama yi mamaki da ta ganta tsaye akan k’afafunta. Hakanan ta bata ta sallameta sai faman sannu take jera mata zuciyarta cike da tausayinta, har ta tafi a ranta tace “Maybe halin mazan zamanin nan ne yake neman hallakata, Allah sarki mata! Allah ya baku ladan hak’uri da maza........” Washegari da safe Umma bata samu tashi da wuri ba, har sai da Baba ya lek’a d’akinta ya tasheta tukunna saboda shima yaji shirun nata yayi yawa dan jiya yayi ta jiran ta amma yaga shiru bai ganta ba, yauma kuma gashi har ya shirya amma babu abun kari ba k’amshin shi babu alamun shi! Ba yadda bata yi da shi ba akan ya tsaya ta d’an dafa mishi abu mai sauk’i amman ya k’i yarda a cewarshi ya makara! Don haka tayi mishi a dawo lafiya ya amsa ya juya ya fita. A bakin rijiya ya hango Huda tana jan ruwa zata yi wanka saboda jiya cikin dare period d’inta yazo, gaba d’aya ya b’ata mata jikinta… Suna had’a ido dashi gabanta ya fad’i! Dan wani irin kallon mamaki taga yana yi mata. A hankali ta sunkuyar da kanta kafin tace “Baba ina kwana” Bai amsa mata ba, yace “Me kike yi a nan?” Tambayar tayi matuk’ar bata mamaki, dan duk tsawon zamanta da shi bai tab’a yi mata haka ba! Sai dai ya nuna tsana da kyamar ta k’iri k’iri, ko lokacin da take boarding ma sai dai ya cewa Mama ta hanata zuwa nasa gida in an yi hutu, ita kuma Maman ta gaya musu… Tambayar ya sake maimaitawa a d’an hassale!Don ya k’agu yaji dalilin zuwan nata sannan kuma yaji waye ya kawota. Cikin d’an rawar jiki da murya tace “Jiya da daddare nazo, ni da Sakina” “Da wa kuma? Waye ya kawoku?” Yai mata tambayar ba alamun rahama a fuskarshi. A hankali tace “Abba” “Ma shaa Allah” Baba yace Har yayi hanyar d’akin Mama a zuciye sai kuma taga ya juya ya fice fuuuu, ko mashin d’insa bai tsaya d’auka ba. Har tayi wankan ta fito duk ranta ba dad’i, dan a yanda taga Baba yau ta san ba za a kwasheta lafiya da shi ba! Su mama da Sakina sarai sun ji duk abunda ya faru, dan haka da ta shigo suka tambayeta “Ina yayi?” tace musu “Waje, ba mashin” kawai, ta fara shiri. Mik’ewa sakina itama tayi ta je tayi wanka.. Basu samu breakfast daga Sadiya ba, itama k’osai ta siya ta ci, tunda mijinta ya riga ya fita. Wankan itama Mama tayo ta d’an shirya, sannan ta basu kud’i dan suje su siyo musu abunda za suyi kari da shi Y’ar tsala suka siyo ta d’ari biyu, suka tafasa ruwan Lipton suka soma karyawa….. Hudan tana jan Mama tana ta shige mata a hankali a hankali dai tana d’an kulata. Suna cikin karyawa wayar Mama ta hau ringing Ganin number Kaka, yasa ta d’auka da sauri! ko gaisawa bai bari sun yi ba yace “ki zo yanzu nan ke da su Sakina! Muna gidan Abban ku.” Gabanta ne ya fad’i ras! Tana shirin yin magana ya kashe wayar… Mik’ewa tayi ta d’au hijabinta sannan ta rarumi purse d’inta kafin tace “Ku taso muje, Kaka yana kira.” Hijabansu suma suka sanya, suka fito, gaba d’ayansu. A tsakar gidan suka tarar da Umma tana bawa Ya Ja’afar koka a baki! Ya dalalar da wani ya zxubar da wani…. Da tsoro Hudan ta kallesu, sai kuma ta k’arasa! Sai da ta d’an rissina tukun ta gaida Umma. Da kyar Umman ta iya amsawa Ya jafar d’in kuwa da ta gaidashi, kallonta kawai yake tayi bakinshi na zubar da yawu da d’an ragowa ragowar kunun, ya kasa cewa komai. Daga d’an nesa Sakina tace “ina kwana” bata jira jin amsawar su ba ta wuce tayi waje abunta. Itama Mama d’an matsawa kad’an tayi suka gaisa sama sama kafin tace “Ya jikin nashi?” “Da sauk’i” Umma tace, tana wani b’ata rai irin ita an dameta d’innan… Ajiyar zuciya Maman ta sauk’e kafin tace “Bara muje Kaka yana kiranmu.” Wannan karon banza Umman tayi da it. Guiwa a sace suka fice daga gidan ita da Huda Umma tana jin kamar ta bisu ta shak’e su! K’arshe dai haushin akan Ya Ja’afar aka sauk’e, dan kokon da bai sha ba kenan tace wai “yana ta b’ata mata lokaci”. Jikinshi ta bashi tsumma ya goge, da kyar! Daganan ta mik’e ta fice ko wanka bata yi ba. Su Mama kuma bayan sun fita ne, Hudan take tambayar “mai ya samu Ya Ja’afar?” Sakina ce ta iya amsa mata da “Fad’a suka yi! Nasu na y’an shaye shaye Wani ya d’au makeken dutse ya buga mishi a kai. A haka ma ya d’anji sauk’i….” A babban parlourn Madu suka same su dukkansu, Shuwa Baaba Talatu Madu da Kaka! Kana ganin fuskokinsu ka san ba lafiya ba! Dan haka su Mama suka sha jinin jikinsu suka gaidasu suka nema waje suka zazzauna. Baaba Talatu ce tace “Maryam yaushe Yaran nan suka zo?” A hankali Mama tace “Jiya da daddare” Jingina kai tayi tukunna tace , “Shi Abban ne yace su kwana?” A hankali ta girgiza kai. D’an shiruu ne ya biyo baya kafin Kaka yace “Maryam mun yi miki magana akan ‘ki d’in jira tukunna’ amma ko? Mai yasa kike da taurin kai ne? Kinsan me taurin kan naki ya haifar yanzu?” Bai jira amsar taba ya d’aura da cewa “Kinga na farko yanzu haka Usman yana hannun hukuma! Yanzun nan aka kamashi bayan ya wanke k’afa yaje ya kwashi y’an sanda ya kaisu wai su d’aure Abba saboda yana bin matar aure!! Ban san dai ya aka yi ba amman reshe ya juye da mujiya, yanzu haka yana d’aure a station! Sannan kema Abban yace ya baki minti 40 ki maida masa Yarinyar shi da hannun ki, in ba hakaba kuma to duk abunda ya biyo baya ke kika ja! Kuma yace gaishe kin ma ta daina zuwa yi daga yau!. Cikin kuka Mama tace “Kaka dan Allah kar ku ce in yi abunda yake so.. Wannan wanne irin son kai ne Abba yake gwadawa? Na ji na yarda da maganar ku da kuka ce bai san da itaba tun farko na yafe mishi wannan amman dan Allah kar ku bari ya raba mu! Kawai ni ya fita a harkar mu gaba d’aya, bama buk’atar shi.” Murmushi Madu yayi kafin yace “Hudan kema ba kya buk’atar Mahaifinki??” Sai da ya sake maimaita tambayar tukunna ta d’aga kanta alamar ‘eh’ sannan tace “Zan zauna a wajen Mama” A hankali, Madu yazo ya zauna a gefen su da kyau

Chapter 16 of 28