Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Allah Toshikkenan Allah yakaimu Tashi yayi, be Iya cemata komai ba, yatafi part dinsa Har dare de magana tana cinsa Arai, Daga qarshe yaje wajan momy yace momy dama inaso zamuyi magana ne Tace inajin ka, wacce iri? Momy Tunda daddy yace bazai sake samomin me aiki ba, kifadawa anty jiddah tadawomin Dame aiki na🤣 Yanzu Kai Alhaji shazali Ina kataba ganin anyi haka? Itama fa Acan din aiki yarinyar take mata Hade hannayen sa yayi waje daya 🙏🏻 please momy nah Tace to shknn, tadauki wayarta takira anty jiddah Bugu daya ta Daga, Bayan sun gaisa momy tace jiddah babu me gyarawa Haneef dakinsa fa yanzu, yakamata ki dawo da yarinyar Nan haka, taci gaba da gyara masa, yaro duk yanata mita anbar masa dakinsa da datti Anty jiddah najin haka cikin ranta tace wannan ba aikin kowa bane saina Haneef Shegen yaro ni zaiyi wa wayo? Tanan ya bullomin kenan🤣 Sharhi, comment, share, Dan Allah 🙏🏻 Amnah El Yaqoub ✍🏻 💕SHALELAN BABA💕 (Romance) Writing by Amnah El 27&28 Amma momy yarinyar nanfa school nakesan maidata tareda Sajida To yanzu jiddah Tunda shi wanda yayi silar zuwanta yace a dawo masa da ita basai abar magana ta wuce ba ita Kuma yarinya tadawo bakin aikinta Momy meyasa kikesan biyewa wannan Yaron ne Dan Allah? Ba biye masa nakeba jiddah kawai quruciya ce take damunsa 🤣 Quruciya de momy, yanzu Haneef dinne me quruciya? Yaron da kuke shirin liqa masa mata biyu Yanzu de jiddah Kinga babu wani tone tone Dan Allah kihado mata kayanta tadawo gida, sai anjima, qit takashe wayar saboda kada ma anty jiddah tasake Cewa komai Yanajin Yanda wayar ta qare wani farin ciki ya mamaye Zuciyar sa, yace yawwa momy to yanzu ba shikkenan ba, kema Yan biyunki sun huta Kallansa tayi, to kaima Kuma Haneef saika kiyaye gaba, banasan wannan kore koren dakake wa masu aiki "nikwa momy inani Ina korarta? " Kallan rashin fahimta Tayi masa me kake nufi? A a momy babu komai, Bari inje daki na huta, sum sum yatashi yayi part dinsa yana gudun karyaci gaba da zama Kuma momy ta harbo jirginsa Yana Zuwa part dinsa yafada kan gado, ya janyo computer sa yafara aiki cikin kwanciyar hankali, haba ai Gara haka, Gara tadawo insata agaba ina kallanta San Raina, yafi ace kullum Ina zarya a gidan anty, Tunda inada ikon dawo da Mai aikina, (tofa kaga masu yar aiki😃🤣) ******** Sister Kinga wannan brezia din na siyo mana su a school dazu da safe, Kinga wannan babbar zata Miki Sajida wacce irin brezia Kuma? Kofa candy ba muyi ba To brezia sai anyi candy ake sakawa? Nikam saka abata zanyi wallahi Shalele tace a a nikam babu ruwana, bazan sakaba, aisai inji kunya ma, kowa Yana ganinka yasan me kasaka Au kunya Ko? To shikkenan ai sai ki zauna da Abu turu turu babu Rigarsa Anty jiddah ta turo kofar Dakin nasu ta shigo, gefen gadon ta nema ta zauna, tace Haneefa kinason Zuwa gidan su momy? Mama gidan su momy Kuma? Aiken mu zakiyi? Ba aikenku zanyiba Haneefa, inaso ne kikoma can gaba daya, dazu munyi waya da momy tace Haneef dakinsa yana zama da datti, shikuma Kinga Baisan qazanta, shiyasa tace kikoma Sajida tace Amma mama karatun dazata fara fa? Wannan babu damuwa akan haka, zanyi magana da Haneef yasama mata lesson teacher din dazai dinga yimata karatun, kokuma shi yazauna yayi Mata, Bayan wata daya sainayi masa maganar karatun inji Yanda zamuyi dashi Ahankali Shalele tace Amma mama ni Bansan rabuwa dake Kiyi hakuri Haneefa Nima akwai dalilin dayasa zan barki kikoma can din, insha Allah zakiga ribar Hakan agaba, yakamata ku kwanta yanzu dare yafara yi Taja musu kofar tayi dakinta, dalilin dayasa zatabar Shalele tatafi guda daya ne, tanaso yarinyar ta kusanta da Haneef, yakasance a kullum tana kusa dashi, ta hakanne zaisa ta cimma burin ta akansu Doctor Sulaiman ma dayaji dalilin nata sosai ya gamsu Wajan sha biyu saura Sajida ta dubi Shalele data fara bacci tafara tashin ta Cikin magagin bacci tace Sajida lafiya? Tashi sis magana zamuyi Haneefa ta tashi zaune, tace meyake faruwa ke baki fara bacci ba? Sister shawara zan baki, duk lokacin dakika koma gidan momy, kada ki yarda ki nunawa uncle kina sonsa Kinsan halin maza, idan sukaga mace tana sansu tofa babu zaman lafiya Daga ranar zasu dinga tashin Kai (🤭 nikam ba ruwana Sajida ce tafada) Sannan koda wasa kada kisa aranki Cewa Wai bazai Iya sanki ba, a kullum anaso Bawa yasa aransa Addu'ar dayake yi ta riga da ta karbu Kawai kisa aranki uncle nakine ke kadai Maganar kina sonsa kuwa kiyi biris ki share shi, kiyi Kamar bakisan komai ba Ajiyar zuciya ta sauke, gaskiya Sajida maganr ki Hakan take, Kuma naji dadin shawarar dakika bani insha Allah zanyi amfani da ita, Amma yanzu please ki kwanta, dare yafara Sajida tace to shknn gud 9yt, Daga nan sukaja bargonsu suka kwanta ******** Washe gari da safe anty jiddah da Sajida suka tayata tahada kayanta, momy tace ta turo iliya direban yara zaizo ya dauke ta Iliya dayazo Shima waje yasamu yazauna yana jiransu Anty jiddah ta dubeta, Haneefa kiyi hakuri kinji, insha Allah zansa Haneef yana kawomin ke da kansa, Sajida ma Ko weekend ne zansa ta dinga Zuwa Miki idanunta suka cika da qwallah, ni mama banasan rabuwa dake, Dan Allah kice musu nide su barni awajan ki Haneefa nafada Miki inada dalilin dayasa banyi musu ba akan komawarki gidan, nan gaba kadan zaki gane dalili na, tashi muje iliya tun dazu yana jiranki Haka suka futo Har wajan motor sa, Suka sake sallama, sannan ta shiga suka tafi, Sajida ta zauna tayi Shiru Kamar marainiya, dama haka ne sabo yanada dadi rabuwa babu dadi Suna shiga gidan ta harari part din Haneef, aranta tace a kanka gashinan ansa narabu da Sajida ta Momy da yara Suna falo, huzaifa yana cinyar Samah yanayin game awaya, tayi sallama tashigo gidan Momy tace sannunki da Zuwa Ahankali tace Yauwa momy nagode A a babu komai, kije kihuta kici abinci, da yamma kyaje kiyi masa gyaran, yanzu Kam jeki huta Cikin girmamawa tace godia nake momy, tayi cikin dakinsu itada baba Hanne 🤣 Samah tace oh momy kuwa radau abakinta, Kamar ita tasaka Miki Safah tace to laifi ne danta fadi Hakan? Kede da neman magana kawai Tana shiga dakin tafada jikin baba Hanne Cikin murna baba Hanne tace wanake gani Kamar yata? Baba nice, Allah yadawo Dani Baba tace Kai amma naji dadi alhmdlh, sannu yata, sannu da Zuwa Tace amin baba, tana ajiye truly dinta yar qarama Daga gefe Baba wallahi nagaji, Kuma wai momy Ina shigo wa Wai inzo in huta anjima naje nayi masa aiki Ni wallahi aikin nan ya isheni, gidan mama jiddah yafi nan dadi wallahi Baba tayi Murmushi to kiyi hakuri mana yata, nan dinma abinda yasa bakya jin dadinsa saboda Yan biyu basa janki ajiki ne, can Kuma akwai Sajida, Sajida Kuma sauqin Kai Gare ta Kiyi hakuri zakiji dadin nan dinma wata Rana, harma ki zauna din din din Baba me kike nufi? Yata nifa Tunda naganki Naga kinfi dacewa da Haneef, Amma iyaye duk sunje sun hadashi da wasu yanmata masu budadden ido, to baka Isa kayi magana ba, kinsan Yan boko Baba Kenan, nikam inani Ina shi? Bari inyi Dan bacci baba, idan ankira sallar la'asar ki datani Daga bacci To yata a tashi lafiya Momy dake falo wayarta tayi qara, tana dauka tace Haneef Ina jinka Momy yarinyar Nan tazo kuwa? Wacce yarinya? Kansa ya shafa yace Ina nufin me aikin nan Cikin ranta tace meyake damun Yaron nan ne? Afili tace tazo Haneef, tana dakinsu tana hutawa, nace taje tahuta, anjima saitaje tagyara ma dakin, kokuma abarta sai gobe? Dasauri yace a a a a momy, tana hutawa taje tayi aikinta, yawwa Takoma bakin aikinta 🤣 Momy tace yaushe zakaje wajan yarinyar? Lokaci daya annurin fuskarsa ya gushe, yace yanzu ma Ajmal nake jira Yazo Daga office dinsu saimuje Yauwa to Allah yayi ma albarka Sai da ta idar da sallar la'asar sannan tatafi part din nasa Tana saka kafarta aciki taga duk yayi wani iri, ita kanta tasan gyaran be gamshe taba Kujerar falon tahau tayi kwanciyar ta, wannan uban aikin wallahi bazan Iyaba saina huta, Dade da Bansan ciwon jiki naba nayi 🤣 Aikuwa Kamar a gidan anty jiddah tayi kwanciyar ta, Bata tsoron ma yashigo ya sameta ahaka ******** Suna hanyar Zuwa gidan su qawar momy wayarsa tayi ringing Anty jiddah yafuto baro baro ajikin screen din Dasauri yadaga yace anty nah ya gida yayarana Yara lafiya Haneef, yau ba za'a zominba? 🤣 A a anty Zuwan nan de da sauqi OK da sauqi Ko, to shikkenan dama nakira ne infadama inada niyyar saka yarinya a school momy tace a dawo ma da ita, Dan haka alhakin karatun yarinyar Nan yana kanka, idan anshiga sabon term ka tabbatar ka maidata makaranta Sannan akwai lesson teacher dayake Zuwa gida yayi musu karatu Yace to yanzu anty me kike nufi Kenan? 🤔 Kamarya menake nufi Haneef? Tanaso taqara tabbatar da abinda take zargi Dan haka dasauri tasake Cewa Nifa Haneef aikin nan ba dole, yanzu saina sa hijabi na inzo in dauke yarinyar Nan, babu zafi Dasauri yace a a anty, basai kinzo ba, za'a nema mata (🤣) Meza ka nema mata? Kince asamo mata lesson teacher, shine nace za'a samo mata Babu wanda zaka samo mata Haneef, Kai zata yiwa aiki, danhaka Kaine zaka koya mata karatu Har Zuwa lokacin dazaka sakata a school Amma anty.... Dasauri ta katse shi, Kaga Haneef nifa abin nan babu zafi, Ada kun dauke ta ne batada uwa, yanzu kuwa tanada ita, aiki zata maka me lasisi Cikin damuwa yace shikkenan za'a mata Za'a mata Ko zaka mata? "zanyi " Tace ok sai anjima takashe wayar, Murmushi tayi Wai zanyi, bazai cede zanyi mata ba, saide zanyi, wannan miskilanci na Haneef yana Bata mamaki Yanzu ne tasake tabbatar wa Haneef ne yasa momy ta kirata akan Haneefa, afili tace Haneef kakira wa kanka, Kuma Nima ka ragemin aiki, domin kuwa zamanku waje daya, zaisa yarinyar taqara shiga ranka fiye da yanzu Kafara son yarinya baka saniba, sannan ka gagara baiyyana kowa, ba irin wannan soyaiyar nakeso ba Haneef, nafison kaso Haneefa ta Yanda zakaji aranka Cewa zaka Iya baiyyana wa kowa, ciki harda iyayenmu, rashin budurwa ne yasa suka hadaka da wannan yaran, aganina kawo musu Haneefa zaisa su janye wannan maganar yanmatan Ajmal yana ganinsa Kuma yaji duk wayar da sukai, Amma be tambayeshi akan menene ba, yanaso dakansa yayi masa maganar, idan abinda yake damunsa yakai intaha dakansa zaizo yayi masa magana Har suka je gidan qawar momy, Shima gida ne Dan madaidaici haka, Amma bazaka kirashi da gidan talaka ba, Afalo akayi musu iso suka zauna Snacks aka kawo musu da lemuka da ruwa Da sallama tashigo falon, fara ce Amma ba sosai ba, gaba daya haka tatafi babu wani shape, siririya ce sosai Kuma doguwa, dasuka gaisa, sai tayi Shiru Ajmal yace to ita Kuma wannan nata tsarin kenan🤣 Gyaran murya yayi yace, Hajiya barka da futowa, ni Sunana Ajmal, abokin Haneef Shazali, tun muna yara Wannan shine angon naki, munzo mu ganki ki ganmu, Ko za'a samu fahintar juna Murmushi tayi tace Sunana hajara, Allah ya tabbatar mana da alkhairi Baku sha ruwa ba A a karki damu babu komai Shide Haneef babu um bare um um, kallansa tayi tace Kai baka magana ne? Inayi mana, kawai de dake dinne banasan... Ajmal ne ya zungureshi Daga gefe jin baran baramar dazai musu Ya Kalle ta yace to Mungo de mu zamu tafi, ga katin sa na waya, Ko zaki Iya nemansa Tace a a barshi, yanzu zaku wuce ne? Wannan karan shazali da kansa yace eh To kujirani awajan Dan Allah minti uku Basu kawo komai ba suka ce to shikkenan Suka fice, Ajmal harda Cewa kya gaida hajiyan Suna fita harabar gidan Ajmal yace Allah sarki, wannan saliha ce wallahi 🤣 babu ruwanta, hajara duniya ba zafi Haneef yace nikaina nayi mamaki wallahi, qila itama bataso Kamar ni, shiyasa Ko katin ma Bata karba ba Suna wannan maganar suka hangota tana Jan truly qatuwa Ajmal yace Bari muga Ko gift ne takawo maka Tana zuwa wajan tace kuyi hakuri fa na tsaida ku, kayana naje nahado kawai zan bishi gida, Dan muji dadin fahimtar juna, shiyasa ban karbi katin ba🙆🏻‍♂🤦🏻‍♂🤣 Yanda kasan an doka masa guduma haka yaji, ashe ita Naga abin na gaske ne, ita harma tafi waccen Ajmal kuwa kasa magana yayi 😱 Ganin sunyi Shiru yasa ta bude Bayan motar ta shiga tasaka Jakarta ma, tace ku shigo mutafi mana 🤣 Ajmal ya kalleshi Shima ya kalli Ajmal, babu damar magana Suna shiga motar yakasa hakuri yace aida kinyi hakuri kin koma idan kina buqatar ganina sainazo, tace a a my Haneef, nida gidan qawar mamata kada kadamu muje Haka suka taho, ahanya babu me magana acikinsu saide ahada ido ayi shiru🤣😃(maganinku Kenan, yau kun hadu da wadda tafi ku tsiya) Suna Zuwa gida cikin bacin rai yayi part dinsa, Ko kallanta Bai sake yiba itama kuwa taja Jakarta tayi part dinsu momy ******** Saida tagama hutawa sannan ta tashi tafara gyara falon, riga da sket ne ajikin ta Yan kanti Yana shigo wa falon yaganta tana mopping Ahankali yasauke Ajiyar zuciya duk da yana cikin bacin ran wancen jarababbiyar Saida yaji sanyi aransa Zuba mata ido yayi yana Kallanta, Yanda take mopping din yake kalla saide ko'ina ajikin ta rawa yake, musanman qirjinta Dasauri yadauke idonsa akansu Masha Allah manya dasu, Zuciyar sace tasake bashi shawara, babu wata wata kuwa yabi shawarar Zuciyar sa yasake maida idonsa kansu Dama haka nakowa yake atsaye? Alamu Taji Kamar Ana kallanta, ahankali ta dago kanta ta kalleshi, suna hada ido duk da duburbuce Amma tana tuno shawarar Sajida saita saki jikinta Tace uncle sannu da Zuwa, Ina yini? Fuskar nan atamke yace lafiya, Daga nan yashige dakinsa yafada kan gado, niktile dinsa yacire yayi wulli dashi qasa, Allah yasa de yarinyar Nan bataga abinda yake Kallan mata ba ta Raina shi (um kagama kalla sannan kazo kahade rai? 😱) Itama kafada ta dage tace kome aka masa oho, taci gaba da aikinta Saida tagama gyaran falon sannan Takoma tagyara kitchen dinma Hanyar dakin ta nufa, kafin ta shiga Saida tace nutsu Shalele, karki ji tsoro ki nutsu kishiga ciki kawai Ahankali ta tura kofar Dakin ta shiga, yana kwance akan gadonsa Amma kafafunsa Suna qasa, idanunsa a lumshe, Amma Sarai yana ganin duk abinda take, ita kuwa tayi zatan bacci yake, ta wuce toilet ta wanke shi, tasaka abin Qamshi Sannan tadawo cikin dakin, kallansa ta tsaya yi, taga bacci yake sai kawai tafara aikinta Harta gama shara, taje wajan data ajiye masa photunansa tadauka ta goge su sannan tasake gyara musu zama Shide yana kallanta, yana ganin irin wannan baiwa Tata, gata qarama Amma tana wannan uban aiki saikace inji🤣 Wani iri takeji hau gata gashi a daki daya, duk Bata cikin hayyacinta dande ta dake ne kawai🤣 Mopar ta ta dauko tafara mopping dakin, cikin sauri, tanaso tagama tafice tabar cikin dakin nan Duk yana kallanta, cikin ransa yace to ai Gara haka, Gara tadawo nan din Yanda zai sata agaba yayi ta kallo Garin saurin datake wajan mopping santsin tiles yajata zata fadi qasa, da karfi tace Auch!!! Asukwane yatashi zaune yace lafiy... Kafin Yarufe baki tasowar dayayi zaune ita Kuma zata fadi qasa yasa jikinsu ya hadu Aikuwa lokaci daya tafada kansa Wadannan abubuwan guda biyu dasuka sauka akirjinsa yasa jikinsa yasaki yaji baida kuzarin dazai tareta haka yanaji yana gani suka fada kan gadon Atake ya lumshe idonsa, wannan karan Kam bawai yana ganin nata bane, da gaske lumshe idon yayi Ita kuwa tsoro yasaka runtse idonta,tana tunanin faduwa aqasa, jin ajikinsa tafada yasa tafara bude idonta Ahankali, harta bude shi fes akansa, taga ya lumshe ido, ta sauri ta janye jikinta Daga nashi Shima sai a lokacin yabude idonsa yace "are you OK? Daga masa Kai tayi, tazari Mopar dazata fice Daga dakin Ahankali yace" bakiji ba " Juyowa tayi ta kalleshi Yace ki shirya gobe za'a fara yi miki karatu inji anty Qasa tayi da idonta tace to, sannan taja masa dakin tafice dasauri gabanta na faduwa, yau itace ajikin Haneef? Oh ya Allah Tana fice wa cikin ransa yace meyasa Bata saka wannan abin ne? Yanzu Kuma inda wanine tafada kansa haka Shima fa zaiji irin abinda yaji yanzu Ko? Nan da nan kishin Yan maza yatashi 🤣🤣 Key din motarsa ya Zara yafuto waje, a lokacin Ana Kiran sallar magrib, Saida ya tsaya akai sallah sannan yashiga mota da kansa yafice da gudu ******** Tana shiga dakinsu tafada duniyar tunani, meyasa bataji Haushin abinda yafaru tsakaninsu ba yanzu? Kodan San datake masa ne? Haka taita murmushi Baba Hanne tana kallanta, tasan Kuma Sarai Daga part din Haneef yarinyar take, Ko menene ya wakana take wannan farin cikin oho musu, yaran zamani de ba'a iya musu 🤣🤭 ******** Wani babban boutique yaje, yayi parking yadauki ATM dinsa yashiga ciki Wadanda suka sanshi sai kallansa suke Ana nuna shi, haka yafara zagaye wajan yana dube dube, to abinka da mutumin dabai sababa, saide yayi waya yabada umarni ayi Daqyar yagano wajanda kayan mata suke, wata budurwa yagani awajan yaqaraso wajanta "sannu fa" Tana Juyowa taga Haneef Shazali, ai tuni tafara fara'ah, tayi tunanin ko zaice yana sonta ne, tace yawwa, yace am Dan Allah inane ake Saida vest na mata, tace laa kaga wajan can, gashi can Yace ok, yayi gaba, ganin yatafi baice mata komai ba Kuma tasan basake ganinsa zatayi ba saitasha Gabansa tace Dan Allah Ko zan Iya yin selfie dakai? Yace why not? Yatsaya sukai, baisake kallanta ba yayi gaba, ita kuwa tace jeka de, inma bakace kana sona ba ai de munyi photo 🤣🤣 Yana Zuwa wajan yadebi panties da brezia dozin biyu, yatafi yaje yabada ATM Dinsa suka ja kudin su, Daga nan yayi gida Yana Zuwa gida yayi parking motarsa yafuto da kafarsa daya yazuba wa ledar hannunsa ido, brezia din dake ciki ya kallah latest ne shegen masu kyau, aransa yace Ko zasu yi mata? To Wai ma tayaya zai iya Bata? Yace mata me? Karfa tayi masa wata fassarar, Kuma shi gaskiya idan yana ganin wadannan abubuwan ahaka gaskiya akwai babbar matsala 🤣 Haka de yafuto Daga motar, yayi part din momy, inyaso kawai ya ajiye mata ledar agaban ta yajuya, yana ganin kawai Hakan shine mafita 🤣🤭 ********* Hajara na zaune Afalo ta Dora qafa daya Kan daya tana kallo, a lokacin Shalele na daki tacewa baba Hanne baba Bari inje kitchen in dauko ruwa, qishi nakeji Tafito Daga dakin taga baquwar fuska a falon, wannan Kuma wacece yaushe tazo gidan? Kosu momy baquwa sukai? Dazu Bata ganta ba Hajara na Juyowa taga Shalele atsaye, ta miqe dasauri tace iyeee kece Anan gidan? Tafidda hannu ta wanka mata mari, tace dama nafada Miki inde nasake ganinki, wallahi sai jikinki yagaya Miki Rannan ma dakika ga na qyale ki, ba tsoron ki nake jiba 🤣🤣 Shalele Taji zafin mari tuni tafara hawaye tace Mena Miki zaki mareni? Au ni kike tambaya me kika min? Tasake Daga hannu zata sake mata wani Marin Cikin tsawa Hajara!!! Juyawa sukai Dukansu, Haneef ne atsaye abakin kofar falo, duk abinda yake faruwa akan idonsa Shalele ta juya tayi daki da gudu (nace jeki dama rabon shan mari ne yafuto dake🤣🤣🤣) Haneef yana Zuwa wajan Hajara babu tambaya babu komai, Kuma dama ga Haushin ta da yakeji tunna dazu Shima yadaga hannu ya watsa mata mari Tace nika mara Haneef? Kobe ishe ki ba? Meyasa bazaka tambayeni abinda tamin ba? Yarinyar Nan awajan shopping naganta tayimin rashin kunya, na qyale tane kawai saboda tana tare da bodyguard Yan Sanda Shine yanzu saboda na rama zaka mareni? Kansa yadafe da hannunsa 🤦🏻‍♂yayi gaba yabarta anan, Hajara tanason saka masa ciwon Kai (um ahakan zakayi mata biyune?) Itama cikin fishi tayi dakin da aka sauke ta aciki (wata sabuwa, mude asaninmu Shalele Bata taba Zuwa shopping da Yan Sanda ba Ko fans🤔 Wai Yaya makomar kyautar Haneef ga Haneefa? Taya zai Bata? Zaku samu amsoshin ku Zuwa jibi insha Allah, gobe babu posting 🤗 ranar hutu ce, Nima hutawa zanyi inyi karatun novel Kamar kowa ehe😃😃😃 Zan huta na kwana daya, muhadu jibin kawai my fan's 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 ngd sosai Sharhi, comment, share, Dan Allah 🙏🏻 Amnah El ✍🏻 💕SHALELAN BABA💕 (Romance) 29&30 Tana shiga dakin dakuka baba tace subhanallah yata keda wa daga fitarki yanzu? Jikinta tafada cikin kuka tace baba watace afalo ina fita ta mareni wai tataba ganina nayi mata wulaqanci Baba tasa hannu tafara bubbuga bayanta kamar qaramar yarinya kiyi hakuri budurwar haneef ce ,kina can part dinsa tazo dazu Baqin ciki goma da ashirin ya kamata ,lokaci daya taji batasan ta,daga kukan mari sai aka wuce Dana kishi(😂🤣) ******** Zama yayi aqasan kafet din dake malale afalonsa yadafe kansa🤦🏻‍♂,su mata akoda yaushe inde suka hadu su biyu tofa ransu bayayin fari harsai sun saka mutum cikin damuwa ,yanzu ita wannan banda Neman fitina me wannan qanqanuwar yarinyar zatayi mata hartayi mata irin wannan hukuncin ?ai marin yayi mata yawa irin haka ai sai yataba lafiyarta(😃) Kuma koba wannan bama ai shi duka kangarar da yara yake,bawai ya shiryasu ba Ledar hannunsa ya kallah ,yanzu damuwarsa daya tayaya ma zai fuskanceta yabata wannan abin nasu🤣? Shiya koreta saboda ta wanke masa gajeren wando ,yanzu yaje yasiyo mata brezia ,shikuma ayaya yake kenan ? Allah yasoshi bai futo fili yabaiyana dalilin dayasa yace tatafi ba Dakinsa yashiga da ledar yaboyeta,daga nan yashige toilet domin watsa ruwa ****** Washe gari yana fita aiki shalele taje tagyara masa part dinsa sosai sai qamshi yake da daukar ido,tadawo daki tayi zamanta tana jiran yadawo taje ta tambayeshi maganar karatu ******** Yana tsaka da aiki wayarsa tayi ringing, new number yagani ,baiyi picking ba ya ajiyeta yaci gaba da abinda yake Aka sake kira ,yayi rejecting ,bai amsa kiran number dabai saniba ,akaro na uku da aka sake kira cikin masifa yace wai waye? Hairat is my name Cikin taqaici yace OK ya'akayi ? Haneef nakiraka kana cemin ya akai ?sai wani abu yafaru ne sannan zan kiraka ? Am dan Allah kinga hairat yanzu I'm very busy ,kit yakashe wayarsa Wayar tabi da kallo,ita wannan gayen zai kashewa waya? Itada take kashewa wasu?🤣 Gaskiyane ,idan yasan bayasan kiran meyasa zasu bata Katin? Cikin bacin rai take jijjiga kai tana cewa gaskiya ne,gaskiya ne (🤣😃😂to tsaya nan kina gaskiya ne kin kasa daukar mataki) ******** Saida yagama dukkan ayyukansa sannan yataho gida Saida yaje part dinsa yayi wanka yashirya sannan yatafi part dinsu momy domin cin abinci Yana zuwa kuwa yaga momy da hajara afalon, Bayan sun gaisa momy tatashi tayi cikin dakinta cikin farin ciki Safah ce takawo masa abinci,, ko kallan hajara batayiba tayi cikin dakinsu, ita Dama ta tsani wannan matar wallahi tafison anty hairat , ita Kuma Samah San hajara take 🤣 Ahankali yasa hannu zai dauki spoon yafara cin abincin, hajara tayi sauri ta riqe haannunsa Haba my Haneef Ina zaune? Kawo nayi saving dinka mana Kallanta yayi, yasake kallan hannunsa data riqe Ahankali yace waike wacce irin mashirmaciya ne ce? Sakemin hannu To laifi ne danna riqe hannunka? Jikinka na riqe? Tsaki yayi yagirgirza kansa sannan yazare hannunsa daga nata yace mummunan tunani daga mummunar Mata Nikake cewa mummuna Haneef? To sainayi qarya nace kinada kyau Bayan baki dashi? Cikin fishi tasake cewa nikacewa mummuna de? Ahankali yace yes Bata sake cewa komai ba tayi cikin data sauka, Shima cikin nutsuwa yafara cin abincin sa Shalele da baba Hanne suka futo zasu Dora abincin dare, suna Bude kofar sukaga hajara ta futo da qatuwar truly dinta Sai suka dakata daga Nan bakin kofa Haneef na ganin hajara da wannan uwar jaka yatashi ya nufeta, bece Mata komai ba yakama jakar ya riqe Cikin tsananin masifa tace kaga Haneef kasakar min jakata, wallahi yau yau dinnan gidanmu zan kwana Still baiyi Mata maganaba yafara Jan jakar Dasauri ta riqeshi ta qwace Jakarta, nace ma bazan zauna ba bakaji ne? Ajiyar zuciya yasauke, metake nufi dashi ne? Afili yace hajara me kike nufi ne? Damafa Naga jakar tayi Miki nauyi ne shine zan Kai Miki ita bakin gate 🤭🤭🤣 Baba Hanne da Shalele me zasuyi inba Daria

Chapter 9 of 17