Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nayin Hakan Dr haneefa itace tafara son haneef, naji hakaanne lokacin dasuke fira itada sajidata Nan ta bashi labarin komai Sannan taci gaba da fadin nabarta Takoma can dinne saboda shaquwa tashiga tsakaninta da haneef Har Shima yasota, saboda a lokacin anriga da anyi masa Matan dazai aura Kuma sai gashi alhmdlh yafara yimata sonda ita Kanta tasan Bata sonsa Har haka, likita cewa yayi zuciyar sa zata Iya samun matsala idan ba'a bashi abinda yake soba Bilal tace subhanallah Anty jidda tace to wannan ne dalili na, Amma ban karya alqawarin Dana dauka maba kayi hakuri Aikomai yawuce anty, tunda anriga da ansa musu Rana ma Rana kuma Dr? Yaushe? Yace a a Wai baki saniba? Dazu fa su Alhaji Tahir suka kirani Wai naje manema auren haneefa sunzo Ai anma Saka Rana nanda wata daya biki, itada ameer da Safah Yanzu hakama zuwa zanyi gidan inji menene za'a fara shiryawa Cikin mamaki tace to aikuwa su momy basu fada ba, kuma da alama ma yanbiyu basu saniba Yace ansaka wallahi, inajin mu kadai ne iyaye muka sani🤣🤣 Tace a a doctor muma ai iyayene🤣 Yace to anty Bari natafi Kituromin wadannan yaran Tace to Tana zuwa Dakin tace yanbiyu tahowarku kuwa daddy Yana gida? Samah tace a a gaskiya yafita Tace to kuje Dr Yana jiranku awaje Duk suka futo, sajida da Samah Da Safah Suna zuwa wajan motarsa sukaga Yana waya, aikuwa suka Bude suka shiga baya Dukansu, Aududu Yana hannun Samah Yana Gama waya, yashiga yatada motar, yajuya ya kallesu, waiku driver Kuka samu kome? Duk kun shige baya 🤣🤣 Yakalli Samah data riqe Aududu, yayi tunanin Safah ce, saboda yasan cewa Samah bazata karbi dansaba, dan haka tunanin sa yabashi Safah ce yace, Shiyasa nace Miki banason damuwa😣 Cikin fishi ta kalli sajida da Safah tace Aidama Saida nace muku karmu shiga karmu shiga Kuka nace, aiga irinta nan Tabude murfin motar tafice ko rufewa batayi ba Owk Dama kece? Cewar Bilal Sajida da Safah suka kama Daria qasa qasa Sukaja murfin suka rufe Ita kuwa tana tsaye, yaleqo ta window yace idan bazaki shigo ba kifadama na muwuce Tace kuwuce kawai Yace OK to Bani Dana inyaso saiki tazama awajan Tace wallahi bazan bayarba, kuje kawai, driver anty jidda yakawoni Nifa bance kishigo ba, cewa nayi Bani Dana,sai driver yakawo ki, Nima ai banqi Taki ba🤣🤣 Batace masa komaiba tajuya tafara tafiya da Yaron ahannunta 🤣 Kut lalle yarinyar nan, nizata maida mahaukaci Ina Mata magana ta kyaleni tatafi Burum yabude motar yafuto, yanufeta gadan gadan, yasha gabanta yatsareta da ido, lokaci daya yayi Mata kwarjini taga yacika Mata ido Idonsa cikin nata yace Bani Dana Lokaci daya qwalla tacika idonta cikin muryar Kuka tace Allah bazan Baka Shiba Iska ya firzar daga bakinsa, yau yaga karfin hali Yanuna Mata hanya yace to wuce mutafi Babu musu Tajuya tashiga motar suka tafi Suna tafiya ahanya ta kawar da Kanta can gefen window, Bama ta kallan inda yake Har sukazo gidan C.P, (commissioner of police) Gidan hajiya hafsat Kenan Yansanda basuda yawa yau a harabar gidan, yanayin parking su sajida da Safah suka futo, shikuwa ya dannawa motar lock 🔒 Samah tafara kici kicin budewa taji Mota arufe,tasan Sarai shine yarufe, Tajuya ta kaalleshi cikin mamaki Safah tace sajida muje mana A a Safah, Kinga mujirata mana saimu shiga gaba daya Me zamu Jira? Da niyyafa yarufe motar, kibarsu su kashe kansu Taja hannun sajida sukai cikin gidan (da alama de hajiya hafsat tadauki fishi dayawa, abin yamata rauni🤣Dan yafi karfin ciwo) Wannan page din nakune masoyan wannan littafi, nabaku shi kyauta🤗 Masu sharhi wallahi kunfi kowa birgeni, dan Allah adinga sharhi tahanake zanji dadi Har insamu qwarin gwiwar yin wani typing din 😊, sharhi Yana temaka wa Sosai, Amma wasu basayi saide acema tnx, wasu kuma suce godia, Wanda sukafi Bani Daria ma sune masu cewa t, Wai t , nide dakacemin t Har gara kacemin sannu wance😃😃, nasan ka kulani Posting din yau zakuga baida yawa wallahi zazzabi nake, tun Daren jiya, dan yau banmayi tunanin zanyi posting ba, to Amma nasan za'a jirani, ajini shiru, Shiyasa nace bari naayi ko yayane yafi ace anji shiru din, babu sanarwa Koda ace kunjini shiru to wallahi zazzabi ne yahanani typing, idan kuma kunjini shikkenan Dama haka akeso, gani nande under probability Ngd Sosai 🙏🏻 Amnah Muhammad El yaqoub✍🏻💕SHALELAN BABA💕 (Romance) Writing by Amnah El Jinjina gareku Rabiat Mafida ibrhm Khadeeman Othman Khadeeja Bilal Sirdeeq Zaenerb Abouberkhar Bashirma Halima Ayshat Abdulkharim Fateemah Zarah Muhammad Khadeeja fasih Feenah Alwasa Hafsat Aliyu Abdurrahman(mmn mama novel) D prince Abba Princessiko Maman maama Samira Aliyu Nawara Ahmad Maman Ja'afar Maman mee'ad Fatima salihu Maman Yasmeen Samira Yahya(gaisuwarki tana samuna) Ummu farouq Kai bazaku lissafu ba, Amma Sarai nasan kowa😃🤣Har masu cewa T, nagode Sosai da yanda kuke bibiyata, dakuma Jin lafiya ta, Alhmdlh nagode da addu'arku agareni dukanku masoyana baki daya, zamu Dora daga inda muka tsaya🤗🤗 43&44 Zuba Mata ido yayi, ta kalleshi da tsananin mamaki a Fuskarta Malam lafiya zaka rufeni amota? Yaushe zakiyi aure? Abazata maganar tasa tazo Mata, aure Kuma? Ta kalleshi, menene hadinka da aure na? Meyasa ne ke kincika rashin kunya da yawa? Tambayarki nayi, saiki amsa min Dan Allah kabudemin kofa na fita, wannan wacce irin tambaya ce ta qwa qwa? Tambayar yaushe zaka mutu na auri maatar ka? Dan kaga budemin infice, inba hakaba... Katseta yayi inba hakaba me? Nide kawai abudemin kofa zaki aureni? Yasake jifanta da wata Tambayar Kallansa tayi ido cikin ido tace Aure de? Ni in aureka? Allah yasawaqe ko maza sunkare 🤣budemin kofa nafita Malam Aikuwa aure dole, da kinqi da kinso saikin aureni, a Hakan kuma mazan basu qare dinba kinaji kina gani dolen dolenki ki zama tawa Batace masa komai ba tafara kici kicin Bude kofar saide abin takaicin yaqara Bude Mata Kanta tadafe 🤦🏻‍♀sai hawaye, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, yace sorry, yamiqa Mata hannu yace Bani Abdallah na saina Bude Miki kifice Tayi banza ta kyaleshi🤣 Yace, kibanishi mana, tasake shareshi, yasaka hannu zai daukeshi da kansa, Tariqe Yaron gam 🤣 Cikin fada yasake cewa nace kibani shi nabude Miki kifice kinqi Bani, kinzo kin tisani agaba kinamin ihu, mekikeso namiki? Yamaida hannu Kan Aududu Yana kokarin daukeshi Itama tafara kici kicin rikeshi 🤣, Garin kokarin qwatar yaro hannunsu ya sarke da juna, lokaci daya wani irin shock ya kamasu, cikin sauri kowa ya janye hannunsa Ta Dora Kanta a jikin Aududu tasaki Kuka, wallahi ka budemin Yaya zaiyi? Yahadu da wadda tafishi masifa 🤣ai dole yabude Bude Mata yayi, tasa kafa kuwa tafice da d'an ahannunta 🤣 Ajiyar zuciya yasauke yabisu da kallo cike da birgewa, kuma wallahi saita aure shi, azuba agani🤣 ******** Suna shiga falon sai Mami suka gani ita kadai, cikin fara'ah ta kallesu tace a a yau yanbiyu ne a gidan Namu? To wacece ne acikin ku Samah ce ko Safah? 🤣 Safah aka sunkuyar dakai qasa, alamun anzo gidan surukai, 🤣 (um kuma da kinji ansa Rana fa 😲😲) sajida tace Mami wannan Safah ce, nikuma sajidan anty jiddah A a, sajida sannunku da zuwa, ta kalli Safah, kuma ke Banda abinki sai kiyi shiru🤣, aini ba sirikarki bace maminki ce, taso kidawo nan ki zauna, ta nuna Mata waje kusa da ita Cikin kunya ta girgiza Kanta, murmushi Mami tayi tace tokushiga Dakin nasu, suma su Haneefan suna ciki Sajida tace to Mami, suka miqe sukayi ciki Mami tabi Safah da kallo, ita kunya ameer kunya, ko Yaya za'ai wannan Zaman aure 🤣🤣 Samah ce tashigo da yaro ahannu, mami ta kalleta taga alamun kamar tayi Kuka, ga kuma yaro a hannun ta, Amma Sai tayi shiru, Har qasa itama ta gaisheta cikin fara'ah Mami tace Samah sannunku da zuwa, wannan din Yaron Waye ahannunki? Bilal ne yayi sallama yashigo, ta kalleshi, anan Mami tagane Kenan Dan nasane, Samah tatashi tayi hanyar Dakin da batasan ma ko shine nasu haneefa ba, sai tayi dace shine 🤣 Mami tace a a likita bokan turai, Saida yashafa sumar kansa yagaishe ta cikin murmushi Tace lafiya kalau muke baban haneefa, Ina kasamo mana yaro ne? Ina Tambayar Samah Naga tana kallonka, ga idonta kamar tayi Kuka Mami Abdallah nefa, qanin haneefa, nakawo Mata shine, rannan munyi magana da ita tace tana so naganshi, nakawo Mata shi, shine Samah ta karbeshi Kuka kuma saboda nace ta aure nine, shine take Kuka, waai ko maza sun kare🤣 Murmushi Mami tayi, Kai Bilal wannan fadan naku babu ruwana aciki, yafi karfina😃 Tatashi tsaye Bari naturo Maka abban afran Yana ciki Shima yabita cikin murmushi yace to Mami ******** Tana shiga Dakin duk suka bita da kallo, sajida tace kaga masoya Ku futowarku daban ce Qyaleta tayi tanemi waje a gefen gadon ta zauna, ta ajiye Abdallah, shalele tasa hannu ta daukeshi cikin murna, ya kalleta yaga baisan taba aikuwa yafara Kuka Takalli Afrah tace Kai kiga Yaron nan Afrah nizaiwa qiwa, Afrah tace ato Ina yasanki Sajida tace wallah muma bai sanmu ba, Amma damuka daukeshi baiyi Kuka ba Shalele tace aikuwa wallahi saide kayi, saina daukeka🤣 Yaro kuwa yasaki Kuka Ta Kalle shi tace Kai Aududu, tsabar rashin m karasa wa zakayiwa qiwa saini?🤣 Afraah tace Dan Allah ki ajiye Yaro yaje gun Wanda yakeso anan,kawai kin matsa masa Sajida tace kawoshi, takarbeshi, aikuwa yayi shiru, suna zaune Yana hannun sajida saiya koma wajan Samah, Kodan yaga ita tashigo dashi ne oho Ita Kuma tana cike cike da haushin Bilal, kuma tashigo ma ba Wanda ya kulata🤣, saita shareshi, kawai tasaka Kanta acinya tasa musu kuka Kunsan Yaro, idan yaga babba Yana Kuka Shima kukan yake, dan haka Shima Aududu yasaka Kuka Duk suka juya suna kallan su, Safah tace a a me aka musu ne, dagake Har Yaro kuna Kuka Afrah tace Samah meyake faruwa? Tayi musu shiru Shalele tace Samah kode keda uncle Bilal ne? Duk tayi shiru ta Qyalesu Safah na ganin haka tafara hawaye, tace Samah Wai miye na kukan,? Wallahi idan baki daina kukan nanba Nima bazan Dena ba, ai kinsan de abinda Hakan yake jawo mana Sajida tayi murmushi tace um yau munga Yan biyu🤣🤣, wato muda ba Yan biyu ba, mune kukan baya jamana komai 🤣 Afrah tace sajida Dama haka suke? Haka suke wallahi, daya na Kuka yanzu dayar ma zata fara koba dalili, aide yanzu kingani, tunda bataji komai ba tahau kukan itama🤣, idan jinya daya takeyi to itama dayar yanzu zakiga ta kwanta, Dama can haka suke, karku damu Shalele tace haba sis sajeey yazakice karmu damu Tatashi ta dawo kusada Samah tace Samah, dan Allah meyake faruwa? Cikin Kuka tadago Kanta tace Wai cewa yayi wallahi saiya aureni, nace masa banaso banaso Amma yace shi wallahi saiya aureni, nikuma wallahi bazan yardaba yaje ya aureni yakaini gidansa yaita jibga🤣🤣 Shalele tace Waye? Wai uncle Bilal din kike nufi? Ta daga Kanta alamun eh Aikuwa suka kwashe da daria 🤣 Safah ta share hawayenta ta harari Samah, tashige toilet domin wanke idonta 🤣 Afrah tace kuma yanzu menene abin Kuka Samah?gayen baida matsala, kawai de kunsamu sabanin fahimta ne, ni banga aibunsa ba Shalele tace nikam nayi murna, zanyi farin ciki idan kika aure shi, sannan ta kalli Afrah kekuma Afrah karki sake cewa babana Gaye, saikace wani Yaro? Afrah tace to sister haneey tsoho🤣Kema Naga alama zamanki dashi yafara shafa Miki son girman Tace eh naji Sajida tace yanzu de Samah kiyi hakuri, Kinga dukanmu muna San abin nan, idan kika amince shikkenan zance ya qare Safah data futo daga toilet itama tace ku kurabu da ita, tana Sansa gulma ce, gashi nan ta riqe masa da, idan Bata Bata Sansa ai bazata so Yaron saba Afrah tace laaa waiji kuke dansa ne?qanin haneefa nefa, Yana son Yara ne kawai shiyasa ya riqeshi Samah da sai yanzu tayi magana tace au dama ba dansa bane shine yaketa nuna min wani iko? Harda cemin nabashi dansa ni driver yakawo ni? Wallahi DANA SANI tun a lokacin zan ce masa yabari saiya Haifa tukunna Dukansu suka hade Mata baki sukace saikun Haifa de, 🤣🤣 Sajida tasake cewa Dama yanzu ga sister haneefa nan🤣 ******** Yayi shiru a office dinsa shi kadai, ga ayyuka agabansa nan yakasa qarasawa, yarinyar nan tana so ta kashe shi,🤦🏻‍♂tun ranar dasukazo gidansu Har yau taqi Bude wayarta, Yaya takeso yayi? Hauka takeso tasashi kuma Bayan jinyar daya kwanta adalilinta? Wayarsa tayi qara, yadauka yakara akunne, yallabai anturo design din takalman dakayi magana a kansu tun jiya Amma bakayi maganar meeting din da za'a yiba "Zan nemeka Bayan naduba" abinda yace Kenan, daga daya bangaren akace Okey sir Turo kofar office din nasa akayi, wani ma'aikaci ne, yace yallabai ga wadannan takardun Wanda zaka duba ne kafin a shiga meeting, anriga da angama aikin komai, saide dubawarka dasaka hannun ka da ake jira Sannan akwai turawa dasuka turo mana appointment latter daga Singapore 🇸🇬 Karbar takardun yayi yace OK munir zan duba, sannan meeting asanar za'a zauna gobe insha Allah Yace ok sir sannan yafice daga office din Saida yaga yaci karfin aiyuka dayawa sannan yatafi gida yamma lis ******** To Bilal kaji abinda ita hajiya ta yanke, nikuma da hankalina da girmana, da matsayina bazan je nayi wannan aika aikarba, dubafa kagani, Yara ma sun sa aransu anzama daya, tunda gashi suna zuwaa Har gida ganin ita haneefa Mami tace Alhaji bazaka fahinceni bane, bakasan inda magana ta ta dosa bane Cikin zafi yace aikuwa inde ban Fahimci inda maganar ki ta dosa ba, to bazan fahimta ba kuwa hafsat, nide nafada Miki babu inda zan maida Kaya, saboda me? A wanne dalili? Sunyi laifi anbaku hakuri, yaran nan daga haneef Har haneefa yaranki ne Bilal yayi murmushi yace Mami kiyi hakuri, tsakanin da kunya ace Ana maida abun Saka Rana, sannan sunasan junansu, kawai ayi musu adduah abarwa Allah komai Kallansa tayi, Bilal haneefa batasan haneef, jinake a gabanka tace ita batasan shi, to saboda me za'a takurawa yarinya, a Barta tayi karatunta Alhaji Tahir yace, hafsat anriga angama magana Akan karatun yaran nan, zasuci gaba da zuwa school dinsu, sannan Alhaji bukar yace zai hadata da yaransa su shiga University tare, hafsat me kuma kike buqata Bayan haka? Tace Shikkenan Alhaji, Amma Bari na Kirata naji ta bakin ta, hankalina zaifi kwanciya Tatashi taje Har Dakin nasu ta Kirata Aqasa ta zauna Kanta kasa Tace Abba gani Alhaji Tahir yace haneefa, ki fadaamin gaskiya kinason haneef? Lokaci daya gabanta yafadi Tace a.. Abba.. Nifa.. Am Nifa Abba Dama abinda yasa nake Sansa saboda yabani kudi ne nakai baba asbiti Hajiya hafsat da Bilal dabasusan da wannan magar ba sukace kudi kuma? Yaushe ? Tace akuje Nan tabasu labarin komai, sannan tace shiyasa nake Sansa amma saisu momy suka Koreni, shine nace nafasa Ajiyar zuciya Mami tayi, tace tashi kije Tatashi tatafi, tana tafiya Alhaji Tahir yace to ai kinji, to yanzu hafsat Kodan wannan abun ai Yaron nan yasamu sassauci daga wajanki, ke hafsat karma kiyi masa danki ne ai, Yana fadar haka yayiwa Bilal sallama yakoma ciki 🤣 Saida Bilal yasake Bata hakuri, tanuna masa komai yawuce, sannan su Afrah suka futo suka rakosu wajan Mota zasu tafi Da Aududu yakoma, Saida yakai su Samah haar gida sannan ya karbi number ta a wajan Safah, data Daddynsu, yaja motarsa yayi gida baiko kalli Samah ba🤣🤣 ******** To Alhaji kunje gidan Alhaji Tahir Amma kazo kayi shiru bakace mana komai ba Daddy yace a a hajiya Kenan To ansaka ranar yaranki, nanda wata daya biki Momy tace alhmdlh, Allah nagode maka, yanzu kuma saide in Kira hajiya laraba nabata hakuri Akan hajara Daddy yace eh yakamata Kam, Shikuma Allah yasawaqe masa Momy tace amin Alhaji, ai banga tazama ba Bari inje daki indauko wayata inkira jidda da sauran yan'uwa afada musu, tatafi tana Kiran baba Hanne domin tasanar da ita itama (anty jidda Kam tarigaki ji🤣🤣) Su Safah ne suka Shigo, daddy yace a a daga Ina kuke? Samah tace daga gidan anty jiddah Yace kafin ku shiga kuje kuyimin Kiran yayanku a part dinsa Suna zuwa suka dawo dashi, daddy yace to Dama magana ce Akan aurenka, dazu munje mun nemama auren haneefa a wajan Alhaji Tahir, kuma anbamu harma ansa Rana nan da wata daya biki, dakuma na Safah da Ameer Safah najin haka tashige dakinsu da gudu Wayyo tasan da haka meyasa zataje gidan dazu? 🙆🏻 Haneef yayi murmushi yace to daddy godia nake, Amma daddy ya maganar hairat? Hairat tunda kace bakaso ai shikkenan, Alhaji shazali ai munfi San lafiyarka Akan jinya, yaqarasa maganar cikin barkwanci 🤣🤣 Sumar kansa yashafa yatashi yatafi cike da farin ciki Yana fita yakira Ajmal yace kana inane abokina? Lafiya najika kamar kana cikin farin ciki haneef? Ai farin cikima daaya Kenan Ajmal, daga yau kawai ka kirani da angon next month Aaaa haba Dan Allah abokina? Yace wallahi, Nima yanzu daddy yake fadaamin, Amma fa yarinyar nan sainayi da gaske, wallahi taqi Bude wayarta, gaba daya ta toshe kafar da zan sameta Ajmal yace, to muje gidan mana mu sameta OK to kazo kadaukeni mutafi Sai Bayan sallar magrib sannan Ajmal yazo suka wuce gidan Mami Suna zuwa, suka zauna afalo, Mami tana ganinsu tace a a su haneef ne a gidan Namu, sannu ku da zuwa, Alhaji Tahir yadawo daga masallaci Shima suka gaisa sannan yayi ciki yanayiwa hafsat kallan maganin ki kenan🤣🤣tunda gashi anfara Mata sintiri agida, baga Mata ba, baga maza ba🤣🤣 Mami ta kallesu tayi hamdala da yaran Nata basa falo, tace haneef saide fa kuyi hakuri, mutuniyar Taku yanzun nan suka fita, sunje zasusha ice cream sudawo, yanzunnan suka fita, da kunzo kafin minti biyar ma Dakun samesu 🤣😲🤭🤣 Kansa yadafe🤦🏻‍♂, to Mami idan nakirata wayarta a kashe, kuma taqi nemana, Mami metake so namata ne? Kayya shirman haneefa ne kawai🤣🤣, idan ta dawo saina fadamata kunzo No Mami zan jirata Dasauri tace a a haneef, kada kuzauna Kuma su Bata muku lokaci, zansata takiraka idan sun dawo, yace toshikknn Mami, mu zamu wuce Tace to ku gaida Hajiyan🤣 ******** Washe Gari momy takira Mami Akan kayan lefen Yara, tace hajiya hafsat Yaya kike ganin za'a tsara kayan nasu? Mami tace hajiya ai kece babba, duk yanda kikace, Yara ai duk na kine Momy Taji dadin furucin hajiya hafsat tace to nida cewa nayi haneefa sutafi da jidda da haneef saisu siyo abinda takeso da Kanta Ita Kuma Safah saisu wuce da ameer da Afrah Mami tace eh hakanma yayi, babu damuwa, abinda basu siyoba sai ayi ordering nasa, momy tace to shikkenan wannan de duk maganar mu ce, bamusan Yaya su alhajin zasuceba, duk de yanda Kuka yanke keda Alhaji Tahir din naji, Nima nan idan Alhaji yadawo saina fada masa naji yanda zaice Dahaka sukayi sallama ******** Da yamma Yana dawowa daga wajan aiki yayi wanka, yashirya cikin Qananun Kaya, meeting suka Gama Yagaji Sosai, key din motarsa yadauka ko abinci baici ba yayiwa momy sallama yatafi gidan hajiya hafsat🤣 Yaarasa gane maganar wa zai yarda da ita acikinsu? Ita Afrah ranar dasuka zo, tace zata yi Mata magana ta Bude wayar, ita Mami jiya tace dasun dawo zata sata ta kirashi, Yana tunanin akwai abinda Mami take boye masa, to Gara yaje wajanta Kai tsaye yaji dalilin wannan shariyar, yafi sauqi, yau Kam inta kama ko kwanane saiyayi a gidan Mami, Amma bazai taho ba saiya ganta, 🤣🤣 Yana zuwa kuwa yayi parking yashiga falon, Mami na zaune cikin ranta tace yau Naga idi🤣🤣 Tace sannu da zuwa haneef, Bari nakawoma ruwa, tashige kitchen tana tunanin irin dabarar dazata masa yau 🤣 Yana ganin shigarta kitchen yatashi yayi wuf yashige dakinsu Afrah Suna zaune suna karatu itada Afrah sai ganinsa sukai yashigo Dakin da sallama Afrah tace Yaya Ina yini Ya kalleta yace lafiya qanwata Mami na futowa daga kitchen hannun ta daukeda ruwa da just taga falon Wayam babu kowa🤣 Ta tsaya, to Ina Yaron nan yatafi daga shigarta kitchen? Adede lokacin Afrah tafuto daga Dakin nasu danta basu waje Mami tace ke kokinga haneef anan yanzu? Afrah tace Yaya haneef ai yanzu yashiga dakinmu🤣 Dakin ku? Afrah tace eh Mami, meyafaru? Ruwan hannun ta ta ajiye tanufi hanyar dakin🤣🤣 Afrah ta riqe ta Mami Ina Zaki? Kallanta tayi Afrah Zaki sakeni kokuwa? Afrah tace, Haba Mami Dan Allah karki shiga🙆🏻 Sharhi Comment Share Dan Allah🙏🏻 Mrs Usman Ce✍🏻💕SHALELAN BABA💕 (Romance) Writing by Amnah El Yaqoub 45&46 Bazade ki sakeniba ko Afrah To yanzu Mami in kinshiga me zakiyi? Haba Mami Yaya haneef nefa? Dan Allah ki zauna Zama tayi Akan kujera tace to Afrah bari nazauna Naga da idon dazai futo ya kalleni Uwa tana zaune kashiga Dakin yarta Mami ai Shima danki ne, duk daya suke a wajanki Mami de batace Mata komai ba ******** Saida ya qare Mata kallo, Yana tsaye, uniform ne ajikinta da alama daga school tadawo Kanta babu dankwali Amma akwai kitso manya, sai littattafai dasuke gabanta Ita Kanta taji kunyar ganinsa, saboda tasan tayi masa laifi, but mazan ne Sai ka Dan gwarasu wani lokacin za'a daidai ta duk da kana sonsu, Hakan bazaisa ka zaqe ba Dasauri taja dankwalin ta tarufe Kan, tace uncle sannu da zuwa Ajiyar zuciya yasauke, yatako yazo gar gaban gadon ya zauna daga gefe Yazuba Mata ido Kallansa ta sakeyi, tace uncle Ina yini "meyasa kikeson kasheni? Why? Uncle kisa.. 🤭 Yes, gashi kin hanani ganinki, kin kashe waya, bakya nemana, ke ko ajikinki, jiya munzo kunfita kuma dakuka dawo baki nemeniba, kuma Saida nace zan jiraki Mami tace Baku Dade da fitaba Shiru tayi tana tunani, unguwa kuma? Itade tasan suna gida, to may be Mami ce tafada masa haka🤣 Kanta ta sunkunyar qasa tace kayi hakuri Baice Mata komai ba yatashi daga inda yake yadawo gabanta ya tsugunna daga kasan gadon, hannayensa duka biyu suna zube Akan gadon Yayi qasa da murya yace ba hakuri Zaki banida, ni bakimin laifi ba, kuma nasan bazakimin insha Allah, kawai nide ki Bude wayarki, rashin Jin muryar ki zai haddasa min damuwa fa, yanzu ma kinsa duk na kasa aiki a office, duk kinbi kin susutani Kinshiga cikin zuciya ta kin zauna haneefa, bazan Iya rayuwa batare dake ba Wata irin kunya ce ta kamata, Wai yau haneef ne a tsugunne a gabanta Yana fada Mata wannan kalaman, tasa hannun ta tarufe idonta 🙈sannan tace Kai uncle please nide katashi Dogayen yatsun hannunta ya kalla, a hankali yasaka hannu yajanyesu daga Fuskarta Yariqe hannun cikin nasa, sannan yatashi ya zauna dab da ita, ya kalli takardun gabanta yace meyasa kikamin wannan abubuwan? Uncle karatu ne yasa, kayi hakuri Saida yadan murza hannunta sannan cikin sigar rada yace to zakiga Bude wayar? Wani iri takeji ajikinta, dazai gane daya sakar Mata hannu,ahankali tace eh Kinyi alqawari? Nayi uncle Littafi daya yaja Gabansa , still hannunsu na sarqe Dana juna Ya kalleta kina gane karatun? Ta gyada masa Kai, Ina ganewa abinda ban ganeba Afrah tanamin bayani Yanzu ma itace take sakemin Ok inci gaba dayi Miki? Tace eh, sannan tafara zare hannunta daga nashi Yanajin abinda take yasake riqe hannun, hannun Nata very soft, Shiyasa yakejin dadin riqewa Karatun yafara yimata, yanayi Yana murza hannunta, hannunsa na yawo acikin tafin hannunta Kanta a sunkuye takasa Kallansa, shikuwa duk bayanin da zai Mata idonsa akanta yake, basuyi da yawa ba ta dauke littafin tace uncle ya Isa, tayi hakane hakane danta qwace hannun ta, taga alama bazai gane irin yanayin datakeji ba, wani iri haka duk ba dadi Kallanta yayi yasaki murmushi, yace Toni bai isheniba, yakai hannunta bakinsa ya lumshe idonsa, sannan yasakarwa hannun Nata wani irin zazzafan kiss Sannan yasaki hannun, ya gyara zama Sosai, Yana fuskantarta, yasaka littafin atsakaninsu, sannan yayi gyaran murya yabude muryar sa Sosai yafara yimata karatun dalla dalla 🤣 Cikin ranta tace Dama da niyya Kenan Mami afalo taji shiru, tace um Afrah bakida hankali ke yarinya ce, Bari kiga na dubo yaran nan🤣 Afrah na chting a wayarta, ta girgiza Kanta kawai batare datace komai ba Mami na zuwa tagansu a zaune a gadon, ga littafi atsakaninsu Yana yi Mata karatu 🤣 Tace a a haneef ashe karatu kuke? Saida yadan Sosa kansa sannan yace wallahi Mami Ina tayata ne Har cikin ranta taji dadi, haka kuma lokaci daya tasaki sisiyar ajiyar zuciya 🤣tace to idan kungama haneefa kizo ki hada masa abinci Tace to Mami Sannan tajuya tafita, Bata zauna afalon Bama tawuce dakinta Afrah ta bita da kallo tana daria Sai wajan biyar da wani Abu suka Gama karatun, tagane Sosai yanda batayi zato ba, tashi tayi ta ajiye book din yabi bayanta da kallo, wannan yarinyar ai dole ma tayi nauyi irin wannan uban hips din Nata 🤣 Ita kuwa Batasanma yanayiba, ajiyewa tayi tace muje uncle, nazubama abinci Da lumsassan idonsa ya kalleta, saide kiyimin kunun gyada idan kin Iya Laaa uncle na Iya mana Um um fa kada kije ki qone, Mami takamani Murmushi tayi masa tace Bari inje inyi maka, tayi gaba, Dasauri yasa hannu yariqo Nata, sannan yace muje Ta Kalle shi, uncle agidan Mami muke fa Saida yadafe kansa 🤦🏻‍♂sannan yasaki hannun, yace sorry muje Falo suka futo, shiya zauna Yana canja Channel din kallo zuwa labarai Ita Kuma taja Afrah suka shiga kitchen Suna aikinsu suna fira, Afrah tace nikam Yaya haneef soyaiyarsa taana birgeni, babu ruwansa dawani boye boye, kinsan Mami fa Nina hanata shiga dazu🤣wallahi cewa tayi saita shiga Shalele tace Mami na Kenan, aigara tazo tasani ko yankewa yarta Kai zaiyi? Dukansu sukayi daria, Har suka kammala sannan

Chapter 14 of 17