Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana shareta, Koda yaushe yana nuna mata Baisan ta nayi ba, ita Kuma taqara shige masa, Daga qarshe sai tsintar kayanta tayi abakin gate

Ta biyar Kuma, sata take masa, idan yayi ajiya sai yaga babu, Daga karshe yakama ta, Saida ya nada mata shegen duka sannan ya koreta
Tun daga lokacin yace qannansa su dinga yimasa aikin, sukuma karatu yasa sun sangarce basu Iya komai ba

To yanzu de kece ta shida, shiyasa nace Miki kiyi Ahankali, Amma ni ganin farko Dana Miki naji kin kwanta min, nayaba da hankalinki
Ina Miki fatan alkhairi

Ajiyar zuciya Shalele tayi tace, to amma baba da wannan canje canjen meyasa ba zaiyi Aure ba yahuta?

Yace babu wadda yake so, Amma duk wannan halin nasa na masifa da miskilanci yanada temako, zaiyi wahala yaga kana cikin halin buqata yarabu dakai

To Allah yasawaqe

Baba Hanne tace amin, Bari nakawo Miki abinci kici kihuta Zuwa goben

Tace to baba nagode

********
Gidan Alhaji bukar shazali Kenan, babban gidane Mai dauke da part biyu dakuma Dan qarami guda daya, babban shine na Alhaji da yaransa, madedecin shine na Haneef, sai Kuma Dan qaramin na ma'aikata maza

Daga can Baya wajan part din Haneef akwai Swimming pool me shegen kyau, Saikuma gidan gaba daya dayasha adon fulawa ja da green

Acan gefe kuma motocine birjik Kamar wanda ake saidawa
Babban gida ne sosai

Bangaren Alhaji da Hajiya, anan yaransu mata suke, sai dakin baba Hanne inda akace ta dauki Shalele su tafi tare

Alhaji bukar yanada yara bakwai, babbar yarsa itace anty jiddah, sai Haneef, sai Fadila, sai iklas, sannan twins mata, Safah da Samah, sai Dan qaramin su huzaifa

Anty jiddah tana zaune a Abuja, da yaranta biyu mace da namiji, duk sunkai sa'annin Shalele, sai anty Fadila danta daya namiji, sai iklas tana goyan yarta mace, Dukansu Suna nan Abuja a zaune da mazajen su, yanzu gidan yarage Daga Haneef sai Yan biyu da huzaifa

Rayuwar su Suna gudanar da ita cikin jin dadi, matsalar su daya masifar Haneef, yacika fada dayawa

Shekarunsa 33 miskili ne na gaske, idan ya harde awaje yana bada order kaika rantse Dan wani Sarkin ne, bayasan raini kokadan, dogo ne ba gajere ba, idanunsa a lumshe suke always, saikayi tunanin bacci yake idan yana zaune Yarufe idon, nan kuwa Sarai yana Kallan ka, ahankali yake magana, yamafi wata macen magana cikin sanyi, idan ku biyu ne awajan saika nutsu sannan zakaji maganar sa, idan kanaso kaji yana magana sosai da Daria , to da momy ne sai daddy, Saikuma abokinsa Ajmal,anan Kam zakaga Daria harda dimple sai sun futo, rashin son raini yasa bayama kula qannan nasa

Wannan Kenan

*******

Washe gari da asuba Suna idar da sallah Shalele tafara karatun alqur'ani dawani data gani a dakin
Baba Hanne tanajin ta, Saida gari yayi haske suka gaisa, baba Hanne tace ashe kema kin Iya karatun yarinya

Na'iya mana baba, meya faru?

A a kede Tunda kin Iya zaki dinga Ko yamin, da jikata ce take koyamin Kuma tayi Aure, Amma yanzu Tunda gaki Kinga aina huta

Zan dinga yi miki baba, duk lokacin dakike so

To Aikuwa zansa me gadi ya siyomin wasu littafin ma kidinga yimin

To baba, yanzu yaushe zaki rakani wajan aikin nawa? Ba yanzu zamu jeba?

Ke kuwa inake Ina tafiya part din Haneef yanzu? Ai Yanzu be tashi ba yana kwance, aike yata aikin ki me lasisi ne, Kisha baccinki da safe, saiya shirya yatafi office zakije kiyi masa gyaran, Kinga baya nan kema zakifi jin dadin aikinki, ga kayan sakawa nan, su zaki dinga amfani dasu, wannan na jikin naki sun tsufa

Ni de zan tafi kitchen yanzu, saboda nahada musu break

A a to baba muje narakaki

Kiyi zamanki yata, aikin gidannan yawa gareshi, kada na gajiyar dake

Shalele tayi Murmushi, kada kidamu baba, muje wallahi Nima nadinga koya

Haka suka tafi kitchen din tare abinsu gwanin sha'awa

********
Daddy ne yadawo Daga masallacin gidan, da carbi ahannunsa, dama haka yake qa'ida idan yatafi sallar asuba sai gari yayi haske yake dawowa gida, direct part din Haneef yanufa
Yatura kofar falon yashiga,

Falon nasa yanada girma sosai, Daga gefe daya kayan motsa jiki ne masu yawa, wajan ya nufa Aikuwa yaganshi akwance da gashi sai wando three quarter, da baqar singlet, yana 'Daga wani uban qarfe muscle 💪🏻 dinsa sai motsawa suke, gaba daya jiki a murde qirar kakkarfan namiji, sai gumi yake hadawa
Daddy yace wato Kai bakada aiki sai Daga qarfe, da yamma gudu da safe Daga karfe
Ajiye karfen yayi agefe, yadauki handkerchief ya goge face nashi, yace morning daddy

Idan kagama abinda kake inasan ganinka kafin ka wuce office

Kasa yayi da kansa yace ok daddy

Yadauki goran ruwa faro me sanyi agefensa yakafa Kai Saida ya shanye sannan ya wullar ta awajan yayi cikin dakinsa

Acan part din su Hajiya kuwa, su baba Hanne Suna kitchen Saida suka hada komai itada Shalele, duk abinda Bata ganeba tambayar baba Hanne take, tana Bata amsa

Baba Hanne tazuba musu nasu tabawa Shalele tace gashi yata, kikai mana daki kizauna kici, Nima zan Kai musu nasu dining

Shalele ta karba tayi dakinsu dashi
Baba Hanne taje tasanar da Hajiya angama komai, sannan takoma dakinsu

********

Dukansu Suna zaune Suna break babu me magana acikinsu, yau Kam qananun kaya yasaka, wandon jeans da riga dark green saiya Dora wata rigar fara asama me hade da hula, kayansa Kenan dama, Daga suit sai kananun kaya, sai yar saman dayake dorawa me hade da hula, Kala Kala, duk kayan daya saka to yar saman dazai Dora itama kalar ta daban
Da wahala ka ganshi da manyan kaya
Daddy ne yamiqe yayi daki ya kalleshi yace kai inka gama Ina jiranku a daki kaida Hajiya, yayi dakinsa

Shima Haneef Bai zauna ba yatashi yabishi, momy ma haka, aka bar yaran awajan su kadai, adan qaramin falon daddy suka zauna Haneef yazauna aqasa, kansa aqasa yanaso yaji dalilin Kiran

Daddy yace my son

Dago lumsassun idonsa yayi ya kalli daddy na'am daddy

My son why bakasan yin Aure ne?
Gabansa ne yafadi, tofa yau ake yinta

Bai dago kansaba yace am.. Daddy ni Har yanzu... Dama.. Ban sa..

Dakata Haneef what's wrong with you? Haneef kanada lafiya kuwa? Kokuma insa doctor ya dubaka?

Innalillah... Me yayi zafi haka? Yafadi Hakan aransa

Afili saiya girgiza kansa yace daddy I am a good health, babu wadda nakeso ne

To Tunda hakane kaje gidan abokina Alhaji Sadiq akwai babbar yarsa tana nan, kaje ka ganta Hairat nasan insha Allah zatama

Haba Alhaji, wacce irin magana ce wannan? Kasan fa Qawata Hajiya Amina ta Dade tana qulafucin muhada zuria da ita, kawai de Dan yasamu mun Daga masa kafa ne, Amma idan akai haka ai Inaga Kamar ba'a yi adalci ba

Haneef kuwa kawai kallansu yake, ya kalli momy ya kalli daddy

Cikin rashin damuwa daddy yace to shknn, kawai ya Aure su su biyun, ya kalli Haneef tokai idan kasamu lokaci saikaje ka gansu

Kallansu yasakeyi da mutuqar mamaki yace momy daddy Ina zan Kai mata biyu? Daddy kubar dayar de, Amma Yaya zanyi da mata Har biyu? Gaskiya daddy akwai damuwa zasu kasheni wallahi, idan ma basu kasheni ba zan mutu, wallahi momy mutuwa zanyi

Momy ta kalleshi, bazaka mutu ba Haneef, zaku zauna lafiya tashi kaje

Tashi yayi yafuto ransa abace su Samah Suna dining sai ganinsa sukai yafuto ransa abace, duk suka bishi da kallo
Shikuwa yana fita saminu ya bude masa mota dasauri yashiga suka wuce office

Murmushi daddy yayi ya kalli momy, tace Alhaji yanaga kana Daria?
To ai al'amarin Haneef ne abin nasa akwai abin dariyar, Wai zai mutu, ni nasan yarona jarumi ne, Ko mata hudu na aura masa zai iya dasu

Momy tayi Murmushi itama, to Allah yasa de su dedeta kansu

*******
Suna tafiya ma sai tsaki yakeyi shi kadai, saminu de yayi Shiru babu damar tambaya, Dan yau uban gidan nasa akusa yake, suna Qarasawa company ma bejira yabude masa mota ba, dakansa yabude yafice dasauri cikin bacin rai saminu yadauko jakarsa yabishi da ita

Duk inda yabi kowa Cewa good morning sir
Saide yadaga musu hannu kawai, dahaka yaqarasa cikin office din nasa, agaban takardun dasuke Gabansa wani dan qarfe ne red colour qarami ansaka sunan sa ajiki, Haneef Bukar Shazali

Bedade da zama ba saminu yashigo masa da jakarsa, yace yallabai gashi, kayi hakuri... Daga masa hannu yayi alamar Baisan jin komai Daga gareshi, cikin sauri saminu yafice Daga office din

Wayarsa yadauko yakira Ajmal yace oga, yaufa akwai matsala, Dan nakawo yallabai office yanzu Amma da alama akwai abinda yake damunsa, dasauri Ajmal yace ok gani nan Zuwa saminu, godia nake

Ko 30 minutes ba'a yiba Ajmal Yazo office din nasa, ganinsa yayi ya Dora kansa akan tebur din Gabansa, ahankali yatako Yazo kansa yatsaya, abokina meyake damunka?

Yanajinsa yayi Shiru ya qyale shi
Murmushi Ajmal yayi, Haneef idan baka fadamin damuwar kaba, wazaka fadawa bayansu momy?
Sanin kanka nede bama boyewa juna sirrin mu

Ahankali yadago kansa yace Auren dole zasumin Ajmal

What? Are you serious?

Cikin damuwa yace yeah

To meyasa su momy zasuyi haka? Wacece wannan yarinyar?

Tagumi yayi 😱😱idan mutum daya cema aida sauqi, Har mutum biyu, Ajmal Ina nake da time din dazan Bawa mata biyu? Yau Ina can gobe Ina can, dayar ma dayaya, dole sai tayi hakurin zama Dani kokuma tabini mutafi tare

To su waye?

Yar abokin daddy, da yar qawar momy, sunce in samu lokaci inje nagansu, Ajmal banasan auren nan wallahi, nafison na auri mace Babba, wadda tahada komai danakeso ajikin mace...

Ajmal ya karbe zancen da fadin, yar boko, wadda zaka zaga, da ita ko'ina aduniya bakaji kunya ba, wadda ta goge da ilmi, idan aiki yayima yawa ta karba tayi ma, me manyan Boobs.... Haneef Bafa ma'aikaciya zaka dauka ba, mata zaka aura wadda zata haihu dakai ta kulama da yaranka, aganina kawai ka amince yafi ace koda yaushe kana dirkawa kanka tablet, Koda yaushe kana jin feeling yakama ta ace kayi auren

Shawarata biyuce Haneef, idan mukaje ka gansu ka zabi daya kawai, kabawa su momy hakuri kace musu zaka auri daya,fatanmu ta kasance yar boko ce Kamar Yanda kake buqata, shawara ta biyu kama cire maganar Cewa sai manyan mata ne suke da manyan Boobs, Haneef acikin yara ma akwai masu manya, kawai kayi fatan Allah yabaka me shi Tunda kanaso

Dan Allah Ajmal kadena min wannan maganar, tayaya qananan yara zasu samu wannan abun?

Ajmal yace saboda me zasu rasa? Abin ba baiwa bace?

Kaga ni yanzu ba wannan ba, damuwa ta daya yanzu shine duk su biyun narabu dasu, bazan Iya ma auren suba

Karka ce haka abokina, muje de mugansu din

Ajiyar zuciya yasauke, ya hargitsa sumar kansa, Yace Mata biyu!!!

Ajmal yadanne dariyar sa, yaga alama shi Haneef mata biyun ne suka tsaye masa Arai

Dan haka yaqara tunzurashi yace may be su momy sunga alama kaidin jarumi ne shiyasa

Becewa Ajmal komai ba yadauki wayoyinsa da brief case dinsa yace nabarka lafiya
Yanda yakejin bacin rai acikin Zuciyar sa, bayajin zai iyayin wani aiki yanzu, Gara yaje gida yahuta

*********
Yauwa yata, Dan Allah kingane komai?
Murmushi tayi tace eh nagane baba, insha Allah zan yi duk Yanda kika gwada min
Baba Hanne tace yawwa to zanje nadan huta, saikin zo

Baba Hanne nafita, takalli falon, taganshi tangameme, wajan dayake Jim ta kalla, ahankali tataka taje wajan, tasa hannu zata Daga karfen dayake dagawa Taji nauyi, tace Wai, wannan Ina zan Iya, barin wajan tayi, ta dauki tsintsiya tafara share falon, babu wani dattin kirki, sai tarkacen kwalayen lemuka, da goran dayasha ruwa dazu da safe, duk ta tattara tazubar
Takalli kujerun falon afili tace wannan tsarin su beyiba, hijabin jikinta ta cire taci damara dashi, duk ta juya kujerun falon, tasake musu wani design din

Sannan tayi mopping, tashige qaramin kitchen dinsa, tagyara shi tsaf, ta goge ko'ina Har jikin lokokin Bata barsu ba, fridge din dayake ciki ta bude, babu lemuka aciki sai ruwa, cikin frizar din ta bude taga lemo na kwali qwaya daya

Dube dube tafara a kitchen din harta ga lemuka da ruwa agefe katan katan, Aikuwa ta fasa takwasa tazuba wasu acikin fridge din sannan tarufe ta nufi dakinsa

Kitchen din ta kalla da falon, tayi Ajiyar zuciya afili tace Karo na farko, nagode inna Marka, domin kuwa da baki horar Dani akan aiki ba, inajin Dana kafa tarihi a gidan nan, nazo ata shida, to kuwa zan bar tarihin Cewa ma'aikaciya ta shida ankoreta Washe gari🤣🤣😃😂

Dakin tashige duk furnitures din dakin nasa farare ne, gadon dakin ta kallah taganshi wani Kala me round ga radio a manne Agefen gadon kusa da bedside drawer, agaban gadon an shinfida wani kafet me mutuqar kyau
Da table irin jikin gadon Dan qarami akan kafet din shikuma andora masa computer akai qirar apple

Saida tagama Kalle kallenta tace tab, wannan ai dole kace ayima gyara, kaya duk farare ba baqi🤣😃🤣🤣

Dressing mirror ta kallah, taduba taga turaruka birjik babu wanda tasani , tace um, wannan Ko waye duk Yanda akai Dan qarya ne 🤣🤣 inba hakaba wannan uban turare saikace wani maceToilet din tashige, taganshi kalau, Amma haka tazage tasake wanke shi tas, mirror din dake jikin bangon toilet din ta kalla, taga nanma turaruka ne, karanta wa tayi taga na wanka ne sai Kuma Air freshener, cikin murna tace yawwa, ta dauko guda daya Mai Qamshi, tadawo falon tayi ta fesawa saida Taji Qamshi yabaza ko'ina sannan Takoma toilet din, ta goge jikin mirror din, nanma tasaka wani turaren Mai wani qamshin daban, dakin tadawo ta share, duk kayansa aqasa riga a gado wando aqasa, haka ta dauke su, tayi mopping ta kalli gadon, taga Bedsheet din ansaka ja, girgiza kanta tayi afili tace inaaa wannan Beyi ba

Labulen dakin ta kalla taganshi light green, Aikuwa Kamar Yanda baba Hanne ta nuna mata komai, haka ta bude wardrobe din tadauki wani bedsheet din green and white, tasaka a gadon, ta cire dayan

Ita kanta gadon Saida ya birgeta, Murmushi tayi tare Ajiyar zuciya tace yawwa nagama aikina nayau alhamdulillah, saura turare, tasake shigewa toilet domin dauko wani kalar Air freshener din, ta dauko ta fesa, Shima dakin yabada nasa kalar qamshin daban

Tunda yashigo gidan Ko part dinsu momy Bai kallah ba ya wuce part dinsa, Dan yau Kam fishi yake da kowa a gidan, Tunda akace za'a masa auren da bayaso
Direct part dinsa yanufa

Tun Afalo wani irin Qamshi ya ziyarceshi, cikin ransa yace masha Allah Yan biyu sun fara hankali 🤭😌
Dama ai yasan yaran zasu Iya aiki, kawai de Dan momy Bata sakasu ne, kujerun falon ya kallah, duk da yana cikin bacin rai Saida yayi mamaki, yaga an sake musu tsari, yace toooo 🤗
Kace yau aikin nayi ne, dasauri yashige dakinsa, Adede lokacin ita Kuma ta futo Daga toilet din, Dama ta shiga ne ta maida Turaren datayi amfani dashi

Karaf akai sa'ah idanunsu yahadu, lokaci daya faduwar gaba ta ziyarcesu

Cikin ranta tace dama shine?







Sharhi Sharhi Dan Allah 🙏🏻






Amnah El

💕SHALELAN BABA💕
(Romance)

Writing by Amnah El


Tab ashe haka SHALELAN BABA yake da masoya ban saniba? 🤔🤔
gaskiya nagode sosai jiya Naga ruwan comments da sharhi 😃Ina yinku sosai masoyana




21&22

Lokaci daya wani irin farin ciki da batasan dalilin sa ba ya ziyarceta, yau gata ga mutumin daya temaketa ita da babanta a lokacin da suke buqatar temako
Inama ace tanada number uncle Bilal, data fadawa anty Sady ga rayuwar ta taganshi a araha yauma🤣😂
Saitin inda Zuciyar shi take bugawa da karfi yasaka hannu, why yakejin faduwar gaba me tsanani haka?
Ya kalli yarinyar datake Gabansa ta tsaya masa qiqam tanata fara'ah
Cikin bacin rai da tsawa yazaro mata ido yace ke😳, mekike yi adakina!!!?

Runtse idonta tayi cike da tsoro, ita Kam Kuma shikkenan ta shiga ukunta yau dama ance mata masifaffe ne

Zuba mata ido yayi, ganin yanda ta runtse ido cikin tsananin tsoro

Wata tsawar yasake daka mata yace get out of my room, da sauri taraba ta gefensa ta fice Garin gudu ta yarda hijab dinta aqasan dakin, batabi ta kansa ba tafice Daga falon ma da gudu baki daya
Shi kadai yake huci cikin bacin rai, meyasa ake barin Ko wanne yara Suna shigo masa part ne? Shikkenan yanzu haka taga wandon sa aqasan dakin 😳
Wajan daya yar wandon ya kallah, yaga wayam babu shi

Saiga Haneef jagwab yazauna asaman gado, shikkenan Kuma yarinyar Nan tagama ganin komai🤦🏻‍♂🙆🏻‍♂
Innalillah...


Idonsa ne yafada kan gadon, anan yaga gadon ma ansake masa sabon bedsheet, Saikuma yafara Kalle Kalle a dakin yana ganin yanda kamarsa ta canja

Kwantawa yayi a gadon yanaji Zuciyar sa na bugawa da sauri da sauri, what is wrong with me ne? Na Dade rabon danaji wannan abin, Kuma sai yau zai dawo? Bayasan faduwar gaban nan wallahi😔 🤣🤣

********

Duk da atsorace ta futo Daga part din nasa, haka kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki, still gaban ta Bai bar faduwa ba
Turus tayi ganin momy dasu Samah a zaune a falon, lokaci daya ta nutsu, ta tsugunna Har qasa tace Hajiya Ina kwana? Kallanta sosai momy tayi, ita sai yau ma ta qarewa yarinyar kallo, lokaci daya tagano tsananin Kamar datake da Hajiya Hafsat
To ai Kuma wannan ba haneefan baba bace, babu ma abinda zai kawo Haneefa gidan aiki, Ko gidan sarki ne tasan baba bazai Barta ba (tofa wata sabuwa 🤣😃, ashe de baba kowa yasan hali)

Safah tace momy tana gaishe kifa
Firgigit tadawo Daga duniyar tunanin data fada, tace lafiya yarinya, kinfara aikin ne?


Eh nafara, harma nagama yanzu

Yarinya Yaya sunan kine?

Kallan momy tayi tace SHALELAN BABA
Yan biyu dasuke zaune Suna sauraren su, atare suka fashe da wani irin Daria

Samah tace tofa kaji wata sabuwa, Wai Shalelen baba

Momy tace hakane sunanki?

Itama Shalele cikin jin Haushin dariyar da wadannan yaran suka mata tace eh haka Sunana

Toshikkenan tashi kije

Ahankali ta tashi tayi cikin dakinsu tarufe kofar, baba Hanne tana kwance tana bacci, saita zauna Agefen gadon tafada duniyar tunani
Menene yasa ne take wannan farin cikin? Ita kanta takasa Bawa kanta amsa, ashe dama shine wanda zata yiwa aikin? Aikuwa inde aikin wannan kyakkyawan ne kullum saitaje tayi Kodan ta ganshi, shida anty Sady tace ba'a ganinsa saide a video Ko jarida? Wallahi saide Nima ya koreni Dan kullum sainaje na ganshi (nikwa nace ai kuwa wataran zaki ci duka awajanx sa🤣😃)

Tanata tunani ita kadai tana zuba Murmushi

********

Futowa yayi daga dakin zai dauko ruwa Mai sanyi yasha, yayi hanyar kitchen nanma yaga irin gyaran dayasha, yabude fridge din yaganshi ansaka komai da komai, haka yazuba wa lemuka da ruwan daya gani aciki ido Kamar yana tsoron dauka, Daga qarshe yadauki ruwa yayi dakinsa
Saida yasha ruwan yadanji ransa yayi masa sanyi, abinda be sababa yau yafara wato chtting, duk Dan yadena tunani, Amma tsabar massage din dasuke shigo masa lokaci daya saboda an ganshi online ne yasa dasauri nanma yasauka, ya runtse ido duk bayajin dadin Garin

Baba Hanne ta tashi Daga bacci taga Shalele na zaune agefe, hamma tayi tace yar nan bakya tashina in Dora abincin rana?
Murmushi tayi, to ai Naga bakiyi bacci ba da safe shiyasa

Yar nan inani Ina bacci, Bari inje kitchen yanzu, itama dasauri ta tashi tabi bayanta suka shiga kitchen din, suna tsaka da aiki Samah tashigo kitchen din tana waya, Saida tagama sannan ta kalli baba Hanne tace am baba Hanne yau inason farfesu, adafamin shi da wuri please

Baba Hanne tace Samah, insha Allah za'a Miki, Shalele ta kalleta, itama ta kalli Shalelen ta sakar mata harara hade da tsaki tafice Daga kitchen din

Tana fita Shalele tace Amma baba Yaya ake kike Iya gane wadannan? Ba Yan biyu bane?

Murmushi tayi, abinda yasa nake ganesu dayane yata, Kuma sudin yanbiyu ne Kamar Yanda kika fada, Samah itace babba, Amma batada kirki, tacika masifa dayawa Kamar yayansu, itace Hassana, Ko ina ansan Hassana nada hakuri Hussaina Kuma fada, to banda nan gidan, ita babbar itace me fada, ita Kuma qaramar Safah Kenan tacika tsokana, haka zatayi ta tsokanarta sunayi,duk Ina gidannan aka haifesu, ita Samah tana cemin baba Hanne, ita Kuma Safah kawai baba take Cewa

Tota hakanne nake ganesu, inde kinji ance baba kawai, to qaramar ce itace Bata fadin Sunana , idan Kuma baba Hanne akace to babbar ce

Ajiyar zuciya tayi, ai baba tun dazu da safe Naga daya acikinsu tanamin wani irin kallo, dazu ma hajiya tana tambaya ta Sunana Wai saboda nace Shalelen baba shine sukamin Daria

Zasuyi, wallahi yata inde wadannan yaran ne zasuyi yafi hakama, musanman ma Samah
Shiyasa dan'uwan nasu baya raga musu, Shima kansa baya banbance su, saboda Shiba shiga sabgarsu yake ba

To Allah ya shiryemu baki daya

Baba tace amin

********

Da yamma yasaka gajeren wando fari qal dashi, da singlet fara, yafara motsa jikinsa Amma na gudu, yana kan injinsa na motsa jiki kawai yana gudu

Da sallama yashigo part din nasa, yayi wankan manyan kaya, kallo daya yayi masa yadauke Kai yaci gaba da abinda yake

Ajmal ya qarasa wajansa yace sannu abokina anata Fama de😃

Yana hada gumi ga haki yanayi yace wallahi...

To inka gama nikam Ina Daga ciki, yayi hanyar dakinsa, Yazo wajan da kujerun sa suke, yatsaya yayi turus, yadaga murya yace yau Kuma sakewa falon Naka tsari kayi?
Haneef Bece masa komai ba, ya share shi

Ajmal dinma yasan Tunda yaji Shiru to bazai samu amsa ba, Dan haka yayi hanyar dakinsa, yaci Karo da hijabi a yashe aqasa, dauka yayi yadaga harda warashi da kyau danya gani sosai, ahankali yace wallahi hijabi ne 🤣

Da hijabin ahannunsa yanufo wajan Haneef yace abokina Ina kasamu hijabi Kuma? Kona yanbiyu ne suka manta shi?

Cikin damuwa yace "natane"

Who?

Dena motsa jikin yayi yataho yanufi kujerun falon yazauna yana maida numfashi yace, sabuwar me aiki

Daria Ajmal yayi, yanaso yaji Yaya akai me aiki tabar hijabi a dakinsa Dan haka yace ikon Allah ita Kuma da cutar mantuwa tazo Kenan

Haneef yayi Shiru ya qyale shi

Yasake Cewa Allah sarki inajin mantawa tayi, ta barshi (Dan jaraba 🤣🤣)

Tsaki yayi yace, no Garin gudu ne

Gudu Kuma? Ita Kuma meya hadata da gudu?

Shi Haneef duk be gane abokin nasa zurashi yake ba, Zuciyar sa daya yace "ta tsoratane kawai"

Ido Ajmal ya zaro 😳yace tsoro? Tome tagani Taji tsoro, Kai masu aiki ma wani lokacin da shirme suke 🤣🤣

Wallahi kuwa, in banda shirme meyasa zata dauki wando na a daki Har tasa hannunta tadauka, shiyasa nayi mata tsawa nace tafice, shine ta yarda hijabin Garin gudu

Wannan Karon Kam Daria sosai Ajmal yayi, Haneef ya kalleshi, why kake Daria? Wannan ba abin Daria bane

Ajmal yace abokina Anya kuwa Iya wando ta dauka?

Zama yagyara ya kalli Ajmal sosai, Tome kake nufi?

A a ni bance Ina nufin komai ba, gani nayi Dan kawai yarinya tadauki wando ta sauya masa wajan Ajiya duk kabi kadamu kanka

Nadamu kaina fa kace Ajmal, yarinya tasa hannu tadauki wando na, wandon namiji, baligi

To Menene aciki danta dauke? Kaide kafadamin gaskiya Ko akwai abinda tagani Bayan wandon, kawai katsaya Kanata wani kwane kwane

Wannan Karon shida kansa Saida ya ware idonsa😳, Ajmal mekake nufi? Ai babu macen da za'a yi taga komai, ba'a haifeta ba

Ni wannan cika bakin Naka batamin rai yake Haneef, lokacin dazaka nuna mata ma waya sani, lokacin kashiga Daga ciki, Amma yanzu a tuzurinka kake, ni kaga ba wannan ba, tashi karakani,zanje zance wajan Sajida, my Sajeey

Mutsws yasaki tsaki, dawa zakaje wajan Zancen? Dani? Inrasa inda zan rakaka zance sai wajan wannan tatsitsiyar yarinyar, Kuma saita ganni gidaiyya Dani na rako abokina zance wajanta, Daga nan tasamu kofar rainani

To Menene aciki danka rakani zancen? Kaiba abokina bane?

A a Ajmal, Dade wajan wata ne zani, Amma banda 'yata, yarinyar yayata, anty jiddah

Zaman hularsa ya gyara yace Toni kaga tafiya ta, zanje wajan tatsitsiya ta 😃, Kai saika zauna anan kana neman masu bigi

Yace eh naji, babu inda zani


********

Washe gari ma da safe, tare suka shiga kitchen itada baba Hanne
Saida suka gama suka shiga dakinsu, wanka tayi tashirya ta zauna Allah Allah take taje part dinsa

Please Login or Register in order to submit comment