Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawai danta ganshi, Amma Kuma baba Hanne tace saiya fita ake gyarawa, Kamar Yanda tayi jiya,baba Hanne ta kalleta tace Kekam yar nan bakya kwalliya ne? Tunda kikazo banga kinsa Ko kwalli a idon ki ba, babu ruwanki da irin kwalliyar dasu Samah sukeyi

Murmushi tayi baba yanzu ni danazo aiki wacce irin kwalliya zanyi? Ai Gara nayi abinda yakawo ni

Toke yanzu Yarinya aigara kiyi kwalliya, kokya samu miji, kiyi auren ki, Kinga kinhuta da wannan aikin, Amma yanzu hankalin iyayenki ma bazai kwanta ba, tun kina qaramar ki Gara kisamu Miji kiyi auren ki

Baba Kenan, ai banda iyaye, ni marainiya ce, mamata tarasu tun Ina qarama, babana yarasu baima Dade da rasuwa ba, yanzu kishiyar mamata ce takawo ni aiki, abinda yasa nasaka araina Cewa zanyi aiki tsakani da Allah, saboda in samu kudi ne inyi karatu in zama lauya inje inkamata

Baba tayi daria, yarinya duk Bawa mumini da yafiya aka sanshi, gaskiya na tausaya Miki, tun kina qaramar ki kina fuskantar matsalar rayuwa, Amma komai me wucewa ne, kiyi hakuri

Tagaji dajin wannan hakuri hakurin inde Marka ce babu maganar hakuri atsakaninsu, Dan bataji abinda ta mata bane, danhaka takatse maganar da Cewa baba yaushe ne yake fita aiki ne? Karfe nawa?

Um wani lokacin karfe Tara, wataran Kuma Tara da wani Abu

Haka ta zauna tana jiran lokaci, ajima ta kalli agogo, asake jimawa ta kalli agogo

Har karfe goma tayi, ta miqe tace baba natafi, to saikin dawo yata

Su Samah Suna falo itada Safah, ta wuce su Ko kallansu batayi ba

Samah tace wannan yarinyar kanta yana rawa, Kuma zan sauke mata shine

Safah tace Kekuwa Samah me yayi Miki zafi da ita? In fact ma ba matsayin ku dayaba, nikuma wallahi Kinga Tunda naganta naji tana birgeni, babu ruwanta, komai cikin nutsuwa

Ke ai kowama birgeki yake, ai saikije kiyi tayi, ta tashi tayi dakinsu, Safah tabita da kallo

********

Yauma Ahankali ta shiga falon, tataka tayi hanyar kitchen, Saida ta qare masa kallo taga babu abinda akai aciki, dozbin din kitchen din ta kalla, taga sai goran ruwa dayawa aciki, sama sama ta Kade kitchen din ta goge shi, tafitar da sharar waje

Sannan tasake gyara falon, hijabin ta na jiya tagani akan kujera, tace oww ashe ya dauke min, awajan ta barshi tashige dakin, gadon tafara lelayewa, sannan ta share tayi mopping, a tsakiyar dakin ta tsaya tana dube dube
Daga wajan labulen dakin taga wani Abu Kamar photo, tana dubawa kuwa taga photunansa ne, Ko meyasa ya juya su? Aikuwa saide yayi hakuri saina futo dasu, guda uku ne, manya manya, daya yasa manyan kaya, daya da suit daya da qananun kaya

Duka photon tasa agaba tana kallo tana zuba Murmushi, tarasa meyasa idan taganshi take tsintar kanta cikin farin ciki

Daya Bayan daya ta ajiye photunan a inda yadace, Aikuwa Hakan datayi saiya qarawa dakin kyau


Toilet ta shiga domin wankewa, saitaga kayansa aciki, dasauri taduba taga singlet ce guda biyu da gajerun wanduna guda biyu, zama tayi tasaka su cikin ruwa ta wanke su tass🤣😃

Sannan tafara neman inda zata shanya tarasa, to su ba wanki sukeba bare kasamu igiya a gidan, saide akai wajan wanki kokuma abawa ma'aikata su wanke shi da machine

Aikuwa ta futo ta shanya su akan fulawoyi, sannan Takoma ta wanke toilet din, yauma Saida ta fesa turare a ko'ina

Sannan tafice taje inda ta shanya kayan ta zauna, Saida suka bushe sannan ta dauke tadawo dasu dakin tasaka masa cikin wardrobe

Ajiyar zuciya tasauke tace yawwa, Bari intafi wajan baba
Tafito tarufe masa falon, tayi part din momy

********

Sai yamma lis yadawo gidan, direct part dinsa yanufa, yanaso ya watsa ruwa yaje wajan momy
Yana shiga falon ya lumshe idonsa, dama Abu a lumshe 🤣
Kallan falon yayi yaganshi very neat, aranshi yace "yauma tazo Kenan"

Dakin nasa yaqarasa, still wani Qamshin yaji, ya kalli pictures dinsa data ajiye waje daban daban, dasauri yaqarasa wajan yasa hannu zai dauke Saikuma ya fasa, ya cire kayansa, yashiga toilet yayi wanka, Saida yagama wankan tsaf yatuna dazufa da safe yabar qananun kayansa a toilet dinnan, dubawa yayi Bai gansu ba, Allah yasa de ba yarinyar Nan ce ta sake dauke masa ba (🤣😂)

Yafuto dakin daure da towel a qugunsa
Saida yagama shafe shafen turarensa sannan yabude wardrobe domin daukar kayan dazai saka , kawai sai yaga kayan a ajiye waje daya, tabbacin batasan inda yake ajiyewa ba Kenan shiyasa tasaka masa su anan, dasauri yadauki kayan, yana dubawa yagansu a wanke tas

Innalillah... 😳wannan yarinyar ita Kuma da salon datazo dashi Kenan?Ina korar wadda ta nuna tana sona ashe ita wannan me kankat ce?
Jiya Ina fada ta dauke dogon wando, ashe yau Har gajeren wando na zata dauka ta wanke?
Afili yace Gara nayi maganin yarinyar Nan tun kafin abin nata Kuma yadawo kaina, tana dauke dogon wando tadawo wanke gajeren wando, to tun kafin tsaurin idon nata yadawo kan me kayan, Gara nayi maganin abin

Cikin sauri yasaka qananun kaya yafuto Daga part din yayi nasu momy

********
Yakusa Zuwa part din yahangota a zaune awaje, Kamar ance ta waigo sai ganinsa tayi yana nufo inda take
Lokaci daya tafarajin faduwar gaba
Shima anasa bangaren haka yake, afili yace ai zuciya ki dena bugawa nakusa yin maganin komai 🤣🤣🤣

Shalele kuwa ganin da gaske ita yake nufowa yasa tayi sauri tashige ciki, momy na zaune Afalo ita kadai, ta russuna tace Hajiya sannu da hutawa

Yawwa inji momy

Dakinsu tashige itada baba Hanne, baba na ganinta tace yawwa yata, gobe zaki fara biyamin karatun kinji? Nabawa megadi saqo dazu yasiyomin littafin

To baba Allah yakaimu, Wai baba in tambayeki?

Inajin ki 'yata

Baba Wai gidan nan ba'a dauke musu wuta ne?

Murmushi Baba tayi, ba'a dauke wa yata, Ko an dauke wuta agari Sunada solar, ai kinsan solar Ko,?

Daga Kai tayi tace nasani baba

Agogon dakin ta kallah taga biyar da Rabi na yamma, Tome zaizo yi nan part din yanzu? Ko abinci zaici? Meyasa nake murna ne danna ganshi?

Ajiyar zuciya tasauke ta dubi baba Hanne tace baba dama akwai tambayar danake so namiki

Baba tasake Murmushi, gaskiya tanajin dadin Yanda yarinyar Nan take kiranta baba, tace Inajin ki yata, fadamin tambayar Taki nabaki amsa

Wai baba yanzu misali idan kaji gabanka yana faduwa idan kaga wani mutum menene Hakan yake nufi?
Kuma idan ka ganshi saikaji Kanata murna Kai kadai, menene Hakan baba?

Baba tayi Murmushi tace yata wannan alamomi ne na kamuwa da so

Gabanta yabata Dam lokaci daya, zaro ido tayi tace baba so Kuma? 😳😳

Qwarai kuwa yata so de dakika sani, me girma ma kuwa, Tunda kince idan kika ganshi kinajin farin ciki, to wannan so ne

Dade ace Iya faduwar gaba kikeji kawai Toda sainace Miki kina da wata alaqa ne me girma tare da wannan mutumin

Yata Bari inje kitchen ingano girkin dare, Ina zuwa, baba ta tashi tafice

Shalele na ganin fitar baba tafashe da kuka, ta shiga uku, 🙆🏻 Ina ita Ina son mutumin dayafi karfin ta? Yau inda ace wata alaqar ce tsakanin su ma Toda sauqi akan ace sone
Zuciya ta meyasa zaki kamu dason wanda Bai sanki ba? Yafi ki komai da komai? Kudi, kyau, aji, ilmi,? Innalillahi... Taqara rushewa da kuka, tasan Ko giyar wake Tasha wannan mutumin bazai taba sonta ba

********
Yana shigowa falon yaga momy a zaune, kusa da ita ya zauna, yace momy gaskiya akwai damuwa

Wacce irin damuwa Kuma Haneef?

Akan wannan yarinyar me yin aikin nan da kuka tura part Dina

To ita Kuma ta shidan meta maka? 🤣

Shiru yayi shi kadai, yanzu me zaice mata? Gajerun Wandunan sa take dauka ta wanke?🤣🤣🤣 Kokuma cemata zaiyi Gabansa ne yake faduwa idan yaganta?

Tace inajin ka Alhaji shazali

Momy kawai de ni batamin bane yarinyar, please 🙏🏻ki sallameta









Tofa😌Yaya makomar karatun inna Hanne?

Shin idan aka sallameta hankalinsa zai kwanta ne Ko Kuma akasin haka?

Shin momy tasan hajiya Hafsat ne? Ko tanada alaqa da ita?

Mutara Zuwa gobe domin jin amsoshin wadannan tambayoyi

















Amnah El ✍🏻

💕SHALELAN BABA💕
(Romance)

Writing by Amnah El

23&24

Salamu Alaikum

Daga shi Har momy suka kalli kofar

cikin kunya ya sunkuyar da kansa qasa yana shafa qeyar sa
momy tace a a jiddah kece a gidan da wannan magrib din?
Saida ta zauna akujera tace wash, wallahi momy nagaji, naje gidan sunane shine nabiyo naganki ke kadai keda daddy nah saina wuce gida
Momy tayi Murmushi tasan Haneef ta fadawa magana saboda bayasan Zuwa gidan ta, shiyasa tace ita kadai tazo gani sai daddy Murmushi yayi dimple dinsa yafuto, yace anty jiddah Kuma ni Banda ni? Ni nefa Dan qaninki da kike kama hannu na mutafi school

Hararar sa tayi, sannan tace babu ruwana da Yaron nan momy, bayasan Zuwa gidana

Momy tace tsakanin ku

Shima Murmushi yayi, yanzu momy ya ake ciki?
Bakace bakason taba Haneef, ai shikkenan saita tafi

Anty jiddah Tace momy akan me kuke magana?

Wai meyi masa gyaran bangaren sa ne bayaso, shine Yazo yake fadamin

Yanzu momy shikkenan shi baida aiki sai korar yara masu aiki? A Iya sanina ankawo wa Yaron nan masu aiki sunkai hudu

Momy tace wannan itace ta shida jiddah

Momy ma'aikata Har shida, Kuma kuka zuba masa ido yana abinda yaga dama, gaba daya kun gama shagwaba shi

Tashi yayi yace Bari inje masallaci momy, anty saina dawo
yaga alama anty jiddah bazata dena cemasa yaro ba idan ba fita yayi ba, yanzu shi Har yanzu awajan ta a yaro yake? Shi yana can yana Cewa yazama babba baligi Amma ita tana qara maidashi baya 🤣

Anty jiddah Tace toka dawo da wuri Nima Ina idar da sallah zan tafi

Yana fita, ta kalli momy tace yanzu momy Ina yarinyar zata idan tabar nan?

A a jiddah gidan iyayen ta mana

To momy ni kibani ita, dama Ina neman me shara

Momy tace
Toki dauke ta a sauka lafiya

Mutumin naki fa anyi masa mata

Mata Kuma momy? Bama guda daya ba Kenan?

Wallahi Alhaji yace yaje yaga yar abokinsa, Nima Kuma nace yaje yaga yar Qawata

Momy mata Har biyu? 😳Yaya zaiyi dasu? Momy ai saisu kashe shi

Waike jiddah bakida aiki da anyi wa Haneef magana saikice zai mutu zai mutu, to zabin nawa zai Bari kona ubanku?

Mayafinta tacire ta miqe tsaye tana cire agogon hannunta, momy, yanzu nawa yake da zaku Dora masa nauyi tun yanzu? Yaro tun Bai tafasa ba zai qone

Toke jiddah dakike wannan haqilon ke Hakan ba shagwaba shi kike ba?

Tafiya tafara yi Zuwa dakin momy, tace ade duba momy

Saida tayi sallah, sannan taje gaban mirror din momy tasake gyara fuskar ta, sai tayi Das da ita Kamar ba itace yayar wannan qaton ba
Falon tadawo tadauki handbag dinta tace to momy zan tafi, Ina yarinyar take?
Su Samah ne suka futo Daga daki da sauri suka rungume ta, tace Yan biyu ai saiku kadani
Ina kukaje kuka bar min momy nah Afalo ita kadai?
Anty muna assignment nefa

Toku je kukiramin me aikin Haneef zamu tafi, kasancewar sun sanshi da sauye sauyen me aikin, shiyasa basu damu ba, Safah ce ta tafi taje dakin baba Hanne, a lokacin Shalele na zaune asallaya, baba Hanne tana gefe akwance
Tayi sallama ta dubi Shalele, Wai kizo inji momy zakibi anty jiddah gidan ta

Gabanta ne yafadi, Ina za'a kaita Kuma? Shikkenan yanzu tadena ganinsa?

Baba Hanne tace me zatayi Safah?

Momy tace zata koma canne, tana fadar haka ta juya tafice

Baba Hanne tace Kash Amma gaskiya banji dadi ba, yanzu yata Yaya maganar karatun mu?

Baba kiyi hakuri, wataran inda rabo zanyi Miki, ni kadaina nagaji da wannan yawace yawacen

Ledar da kayanta suke ciki tadauka ta futo da hijabin datayi sallah ajikin ta, kyakykyawar fuskar ta tayi kyau acikin hijabin nata me hula, tayi fayau babu wani tarkace a fuskarta Baba Hanne tarakota Har falo, suka gaisa da anty jiddah Tace baba zan dauke Miki me tayaki aiki Ko,kiyi hakuri insha Allah zata dinga Zuwa Miki lokaci Zuwa lokaci

Ta kalli Shalele taga yarinya batayi kama da masu aiki ba, tace zomuje

Sallama Shalele tayi musu sannan suka fice Zuwa harabar gidan

Inda anty jiddah tayi parking suka je, anty jiddah ta bude mata kofar ahankali ta shiga, sannan itama ta shiga, tadauki wayarta ta kirashi
Tace to Kai ango zamu wuce

Gabanta yafadi, waye ango? Kafin tagama tunanin nata ta hangoshi, dasauri kawar da idonta tana Kallan wani wajan daban

Anty jiddah ta kalleshi, cikin tausayawa tace ashe su daddy sunyi maka mata

Cikin damuwa yace wallahi anty

Duk maganar dasuke tana jinsu wannan Karon Kam Bata Iya tsaida hawayen idon taba, lokaci daya suka zubomata masu dumi, tasa hannu ta share, anty jiddah Bata gantaba, duk abinda tayi akan idonsa

Why Take kuka?

Anty jiddah Tace to yanzu yaushe suka tsara yin bikin? Kai wanne lokaci kakega yayi ma?

Any time anty, zanje shan ice cream yanzu, I will call you back ok?

Yafadi hakanne saboda yanaso yabar wajan, Baisan kukan mace Ko kadan

Tace To shikkenan qanina sai munyi waya, taja motar sukabar gidan, dazasu fita Daga get din gidan Shalele ta rushe da kuka, yanzu shikkenan Hakan fa yana nufin ta rasashi Kenan? Ya Allah gani gareka, dole ta cire shi Daga ranta, Allah ka Temakeni nadena tunanin wannan mutumin, insha Allah Daga yau zansa araina Cewa banma sanshi ba, dole zan cire shi Daga Raina

Anty da batasan kukan da biyu ba, tayi Murmushi tace kiyi hakuri, insha Allah zan dawo dake wataran inde bakyajin dadin zaman gidana kinji? Zan dawo dake wajan baba

Daga Kai tayi, ta share hawayen ta, haka anty jiddah taci gaba da driving cikin qwarewa, Har sukazo gidan, tanayin parking suka futo, anty jiddah takama hannun ta suka shiga ciki

Mutum biyu ne a zaune a falon mace da namiji Suna kallo,namijin zaikai 25, sai Sajida me 16 years, sa'ar Shalele

Sajida tataso da gudu tace oyoyo mama

Anty jiddah Tace Sajida sannunku da gida, me kika dafa mana ne, wallahi yunwa nakeji

Batace komai ba tace mama baquwa mukai ne? Anty jiddah Tace eh a gidan momy nadauko ta, kinsamu qawa, ta kalli Shalele tace wannan shine babban Dana ayaz, sai Sajida, da na dauko ki ne kidinga temaka mata da aiki, Amma Tunda naganki naji Ina sonki, naji Kamar yar'uwa ta ce ke, ki daukeni amatsayin uwa Kamar Yanda Sajida zatayi, kiyi duk abinda kikeso, nan Kamar gidan ku ne, sannan ta kalli yaran nata tace, ga yar'uwa nakawo muku, shikkenan Sajida kin huta da fada keda ayaz, kinsamu qawa kema,
Ayaz yace mama Yaya sunan ta? Anty jiddah ta kalli Shalele tace, kifada musu sunanki

Kallansu Sajida tayi tace Sunana Haneefa, Amma Shalelen baba ake cemin

Sajida tace a wanne gari kike?

Kuje local government

Dasauri anty jiddah Tace Aikuwa akwai wata yar'uwar su momy akuje, namanta sunanta, Amma zan tambayi momy

Ahankali tace to mama

Anty jiddah tayi Murmushi jin dadin sunan da Shalele ta kirata dashi

Ayaz yace to mama sannun ta da Zuwa, Amma kifada musu banasan raini, Sajida tace jishi Ko mama saikace me shekara talatin

Nikam kun isheni, Daga dawowata, banasan hayaniya Dan Allah, kuje ciki Sajida, kuyi sauri kufito muci abinci

Jan Shalele tayi suka shige daki, haka ta dinga janta da fira, tun tana noqewa harta ware, sai gashi sune harda yin game awayar sajidan

Saida ayaz Yazo yakirasu sannan suka futo falo Dukansu suka fara cin abinci, suna cin abinci tanata nuna mata Abu awaya, abbansu yashigo, sukayi masa sannu da Zuwa, yace baquwa mukai ne? Anty jiddah Tace eh doctor, yace to sannu da Zuwa, yashige dakinsa, ahankali Shalele ta amsa, anty jiddah ta tashi tabi bayansa, Sajida tace wannan shine abbanmu babban doctor ne

Ayaz yace oh uwar gulma harta fesa, tace eh nafesa din, Murmushi kawai Shalele tayi, wannan drama tasu saisu

Acan daki anty jiddah Tace doctor nayima laifi nadauko yarinya a gidan momy banyima bayani ba, Amma kayi hakuri, yace haba jiddah Ko mutum dari kika kawo ai bazance Miki komai ba

Allah yabamu zaman lafiya, tace amin doctor nagode

Yace yanzu de matso kiji wata magana, Hararar wasa tayi masa, ta tashi Ahankali taje ta rungume shi

Washe gari weekend Suna zaune Afalo Suna kallo, Sajida tace mama anjima zamuje da Haneefa wajan qawayena su ganta

Babu inda zaku, Nima Ina gama Kallan wanna episode din zaku tashi mufita shopping abbanku yabada kudi ayiwa Haneefa shopping, ta kalli Shalele tace ke Kuma kicire wannan hijabin, haba tun jiya kina Fama da Abu, dasauri tacire hijabin tun kafin itama ayi mata fadan 🤣🤣

Suna gama kallon suka fita

********

Kai tsaye wajan shopping suka je, Shalele sai Kalle Kalle take, ayaz da Sajida sai janta suke Ana selfie
Saida anty jiddah tasiya mata, atamfofi masu kyau, materials, takalmi, jaka, kayan kwalliya, kayan bacci, sannan suka wuce wajan me dinki, aka Bawa ayaz tip din ya gwada ta, sannan tazubewa me dinkin kudi tace express takeso, basu koma gida ba suka wuce wajan saloon
Manyan kalbar datake kanta aka tsefe, aka wanke mata kanta, nan da nan gashi yaji gyara yaqara tsawo, dama dayaya bare Kuma aka gyara shi, ita kanta sai takejin wata irin iska na shigarta, da akayi mata parking saita dawo Kamar yar turawa, to gashi ne da uban tsawo, gata da fari, nan da nan tafara sauyawa

Washe gari Sunday gidan gyaran jiki takai su,
(ah lalle anty jiddah kin dagewa yanmatan naki 😌😌)
Basu suka dawo gida ba sai yamma, jiki yasha gyara saikace wasu amare anyi musu qunshi

Cikin sati daya yarinya ta sauya

********
Yadawo Daga office ya kalli dakin nasa duk yahada datti, rabon da ayi masa gyaran daki Mai kyau harya fara mantawa
Tun yarinyar Nan tana nan, tsaki yasaki, yanufi wajan momy

Tana dakinta zaune yace momy, yau kwana biyu Kenan yaran nan basa Zuwa Suna share min da kina

A a, dazufa suka dawo suka cemin Daga part din Naka suke,sun gyarama shi

Tab yanzu momy ahakan anyi gyara?

Eh sun gyara wallahi, haka suke ce

Zama yayi Agefen ta yadafe kansa 🤦🏻‍♂cikin ransa yace gaskiya akwai damuwa

(tukunnama yaro 🤗)

********
Bayin Allah yanzu ashe bakuda Imani? Kukama ku tsareni awaje daya? Nabaku hakuri Nabaku kunqi ku Rabu Dani? Tafashe da kuka tace Dan girman Allah ku qyaleni, wallahi Daga yau babu ni babu Shalele
Hanyar datake Bima bazan sake biba, wallahi idan naqara kwanaki awannan dakin me duhu mutuwa zanyi

Ke Dalla malama kiyi mana Shiru, babu me sakin ki, sai oga Bilal yabamu dama, inna Marka tafashe da kuka

********
Yau Tunda lesson teacher dinsu yatafi ta lura sister ta tana cikin damuwa, Bari tayi Saida suka shiga dakinsu sannan tace sister meyake damunki?

Cikin damuwa tace babu komai sis

A a Haneefa, kada ki boyemin Dan Allah, idan damuwar ki karatu ne ai mama tace kiyi hakuri mu gama wannan term din idan zamu koma first term tare za'a maidamu, muyi zamanmu ajinmu daya, mu dawo gida ga mama, to Menene Kuma abin damuwa? Yau Watan ki daya a gidan nan, Ina lura dake kina Yawan tunani Haneefa, meyake damunki?

Kafin Shalele tace wani Abu wayarta tayi qara, tana dubawa tayi Murmushi, ta Daga tace Yaya Ajmal, zan kiraka, I am busy now
OK Yaya bye

Kashe wayar tayi tace, inajin ki sister, cikin damuwa tace sister nakasa cire shi araina, tana fadar haka tafada jikin Sajida tasaki wani irin kuka

Jikin Sajida yayi sanyi, tafara Bubbuga bayanta Ahankali, tace kiyi hakuri sis, waye shi din? Fadamin waye?

Batace uffan ba ta dauki wayar sajidan ta shiga gallery takamo photon sa ta nuna mata

Dasauri Sajida tace Innalillah.. Wai uncle Haneef?

Anty jiddah dataji su Shiru, ta biyo su dakinsu domin ganin ko kalau suke?
Takama handle din dakin zata shiga saita fasa, ta tsaya Taji me Haneef yayi? Me qaninta abin sonta yayi?

Cikin daki kuwa Shalele tana hawaye tace eh shi Sajida, Ina sonsa wallahi, nayi nayi nacireshi Daga Raina nakasa

Amma sis Haneefa Yaya akai kika sanshi hakika fara sanshi? Kokuma awannan Dan zaman dakikai ne a gidan momy?

Ba anan bane Sajida, tun aqauyanmu nafara ganinsa, tiryan tiryan tabata labarin komai

Ajiyar zuciya Sajida ta sauke, gaskiya sis kinyi kokari, na tausaya Miki, Nima fa haka infada Miki lokacin Ina zuwa gidan momy nake ganin Yaya Ajmal shida uncle Haneef din, wallahi sis tun daga lokacin naji inata tunaninsa, Amma ni da Allah ya rufamin asiri sai akai dace Shima yace yana sona, to kinji inda nadanji sauqi

To Amma matsalar uncle Haneef dinne baya Zuwa gidan nan bare muyi masa Yan dabaru Ko zamuja hankalinsa, Amma kiyi hakuri wannan girman kan nasa da miskilancin dayake ji dashi zamu sauke masa shi tas🤣😃, Yanda nakeso Yaya Ajmal ya Aure ni, kema sai uncle Haneef ya aureki, Kinga shikkenan mun auri abokai Ko?
Shalele tayi Murmushi suka rungume juna

Anty jiddah datake tsaye abakin kofa Daria ta Kamata, lalle yaran nan wato dan'uwan nata ake hadawa tarko tana zaune bonono

Barin kofar Dakin tayi, ta shiga duniyar tunani, yanzu Haneefa Nason Haneef, ga Haneef Kuma a gida anhadashi da manyan mata, Yaya zatayi ta temaki yarinyar Nan, tanajin Haneefa aranta Kamar itace ta haifeta, dole zata temaka wa yarinyar tasamu abinda takeso (to gafa second Bilal 😃🤣😃)

Zama tayi akan kujera ta dauki wayarta takira Haneef yana dagawa babu alamar wasa atare da ita tace sai yaushe zaka zo gidan? Kokuma Sai nan da wasu watanni? Haneef nakusa Yin wata biyu rabon Dana ganka fa, aiki hauka ne? 🤣

Oh anty jiddah Kin cika damuwa wallahi 🤦🏻‍♂, yanzu natashi Daga wajan aiki, zan shigo kafin natafi gida

Batace masa komai ba takashe wayarta

Qwala musu kira tayi, dasauri suka futo falon, ta zuba musu ido tana qare musu kallo, babu abinda yaranta suka rasa, musanman ma Haneefa, zaman datayi a gidan tana hutawa, tana abinda takeso, hankalinta kwance, yasa komai nata yasake futowa musanman hips dinta, yaqara bajewa, sai shining yarinyar take, insha Allah zatayi duk Yanda zatayi taga Haneef ya Aure ta, wannan ai bazai Iyu ace Haneef yayi rashin taba

Qawancen su ya birgeta, basa boyewa juna komai, gashi yau dalilin Haneefa itama tasan damuwar Tata yar

Mama gamu, inji Haneefa

Anty ta jiddah ta kalleta, riga da sket ne ajikinta, dinkin yayi bala'in karbar ta, rigar me breas cup ce sai tayi Kamar tasaka brezia, nan kuwa Bata sakaba

Tace dama zan fada muku ne abbanku yace gobe yanada baqo da safe, kunga yanzu yamma tayi, inaso ku shiga kitchen kufara Har hada abubuwan dazamu girka masa, abinda babu sai nayi masa waya yataho dashi kafin yashigo da daddare

Atare suka ce to, sukayi kitchen din, anty jiddah tabisu da kallo, tayi Murmushi, su Sajida masu tarko😃Wai Har sunyi girman dazasu San wani Jan hankalin samari, oh zamani

Suna aiki a kitchen, saminu yayi parking motarsu, dasauri yafuto yace saminu minti biyar, zanga anty jiddah na futo mu wuce gida

Cikin girmamawa saminu yace to yallabai afuto lafiya

Kai tsaye falon nata yashiga, Kamar kullum yana cikin suit, light blue, yayi bala'in yin kyau
Anty jiddah na ganinsa tace hmm ai wallahi nakusa fishi

Murmushi yayi, banda rikicin anty ya za'ai naqi Zuwa, ai dole ne inzo de in ganki, yanzu ba shikkenan ba?
Ina yaran suke ne?

Ayaz yatafi ball tun dazu Bai dawo ba, sai su Sajida Suna kitchen, ta Daga murya tace Sajida, ga uncle dinku Yazo kuzo ku gaisa

Sajida najin ance uncle taja hannun Haneefa tace laaa kinji uncle dinma Yazo, zo muje

Um um sister jeki, ni wallahi gabana faduwa yake

Au bazaki ba? Aikwa saina fadawa mama, ta juya ta fita, tana zuwa falon tafada jikin Haneef tace uncle sannu da zuwa
Uncle bakasan Zuwa why?

Saida ya lakace mata hanci yace to my daughter yanzu gashi nazo

Anty jiddah Tace a a Ina HANEEFA?

Tazo su gaisa mana, ta Daga murya tace HANEEFA! HANEEFA!!!?

cikin ransa yace HANEEFA, suna me dadi, wacece wannan me irin sunansa?

Yanda anty jiddah take Qwala mata kira yasa ta futo dasauri, gabanta yana faduwa, Har falon taje, Amma takasa kallansa, saita kalli anty jiddah Tace mama gani

Bakiga baqo bane?

Sai a lokacin ta Kalle shi, idonsu yahadu, dasauri ya janye idonsa

Please Login or Register in order to submit comment