ba?
Ahankali sukaja kofarsu suka rufe, gudun kada yagansu
Cikin ranta tace bakin gate, ni wannan gayen zai Kora?
Cikin masifa ta qwace Jakarta tayi gaba ko momy batayiwa sallamaba
Shima murmushi yayi yazauna Yana shan lemo, abincin dabai qarasa ciba Kenan yatashi yayi part dinsa, hajara ta cika damuwa da yawa wallahi 🤣
********
Saida suka gama shan dariyarsu sannan shalele tace baba dama haka yake?
Ai inde haneef ne zaiyi yafi haka ,itama narasa dalilin bin saurayi gidansu,hakan ba mutuncin mace bane ga me hankali
Tashi muje muyi girkinmu kinji
Tashi sukai suka shiga kitchen, cikin ranta tana tunani yaushe ne lesson teacher din zaizo ?tayaya zataje ta tambayeshi ?
Tana wannan tunanin baba tace kinga wannan kunun gyadar karbi kiyi da kanki yau nagani
Yauwa baba kullum saikin dama kunun gyada wai waye yakesha ?Alhaji ne?
A a yata haneef ne,ai shi yanasansa dayawa
,yanzu ma dazan samu mekai masa sai akai masa yasha
Shiru tayi tana tunani ,kota karba ne ?wannan ce kawai hanya mafi sauqi dazata kaita gareshi
Cikin kunya tace to baba ki aikeni mana
Baba tayi murmushi dama ta manya tamata🤭😃
Tun dazu taga tana tunani, tasan Kuma tunanin haneef take, tasan sarai tana sansa tun lokacin datayi mata wannan tambayoyin
Zubawa tayi ajug tasaka mata akan try da qananun kofuna ,tace to dauki kije yata
Aikuwa tayi wuf tadauka tatafi🤣😂
********
Kadan kadan gabanta yake faduwa harta tura kofar falon nasa ahankali tashiga
Adede lokacin yayi shirin motsa jiki ,dagashi sai farar singlet da gajeren wando 🤭🤣
Sau daya ta kalleshi tayi sauri tasauke idonta Qasa
Bata taba ganin namiji azahiri ba ahaka saide ko yan ball kokuma a TV
Wannan wanne irin jiki gareshi duk a mummurde ?kalli qirjinsa duk gashi
Lokaci daya taji tsoro duk ta diririce ,ita kuwa meyakaita San wannan qaton ?Ina zata kaishi?
Shima yana dago kansa yaganta yakafeta da wani irin kallo
Shi saida yaganta ma yatunada maganar karatun su
Dakuma kayan daya siyo mata jiya🤣🤭
Ahankali ta qarasa wajansa tace Uncle ina yini
Gashi wai inji baba
Kallanta yasake yi,cikin ransa yace"wai"
Sude yara kullum suna cikin aikata yarintarsu
Inba hakaba zatayi magana menene saitasa wai aciki ?🤣
Bece mata komai ba yazauna a kujerar ,itama ahankali ta tsugunna agabansa tafara zuba masa kunun acikin cup (🤭to ita kuma wannan me za'ace mata kenan ?)
Tadauka ta miqa masa
Yana kallanta yasaka hannu ya karbi kunun ,ahankali yafurta "thank you so much"
(Tab gaskiya shalele kinyi sa'ah yau Haneef shazali ne dakansa yake gode miki😃)
Zama tayi aqasan kujerar shikuma yana kai azaune,yana satar kallanta Qasa Qasa
Wasa take da yatsun hannunta ,cikin ransa yace masha Allah dogaye dasu
Yar yarinya da ita me hankali hartasan takawowa babba abu tazuba masa da kanta
🤣🤣
Yaga tazauna bata tafiba ,shikuma dai bazai koretaba ,inda zataci gaba da zamama anan beqi su tabbata ahakanba🙈
Ganin baida niyyar yimata magana cikin ranta tace maganina kenan ai da shegen cusa kai 🤣🤣qilama ya gane sansa nake shiyasa yake manna min🤣
Tana jan yatsun hannunta tace uncle dama maganar karatun
Cikin sigar rada kamar me tsoron wani yajisu yace oh karatunki ko ?
Jeki dauko littafin
Batace masa komaiba tatashi tafice,kenan shine zaiyi mata karatun ?to Allah yasa de yasaka kayansa kafin tadawo🤣🤣
Tana zuwa part din Momy ko kallan kitchen batayiba tashige dakinsu ta dauko littafin nata tatafi,baba hanne kawai sai gilmawarta tagani da littafi ahannu tayi murmushi tadaga hannunta sama Allah kasa abinda nake tunani yazama gaskiya,tacigaba da aikinta
Tana komawa falon nasa, taganshi da baqar jallabiya ,ahankali tasaki ajiyar zuciya ,taje gabansa tamiqa masa littafin tace gashi
Karba yayi yabude ya dudduba sannan shima yadawo kasa yazauna yana fuskantarta
Cikin qwarewa yakeyi mata explain din komai ,yanayi yana Watso mata tambayoyi Tana bashi amsa ,suna karatu yana nazarin yarinyar
Yalura batasan kallansa kome yasa ?
Abinda ya fahimta ga yarinyar shine tanada ilmi amma meyasa iyayenta basu sakata a makaranta ba suka barta Tana aiki ?meyasa ?
Har suka gama karatun bata kalleshi ba ,tatashi zata tafi yace "kinga"
Juyowa tayi ta kalleshi
One minute ina zuwa
Tsayawa tayi shikuma yashige dakinsa,yanzu ne yakamata yabata wannan abun nasu🤣🤣
Saida yadauko yatsaya yakasa fita ,yanzu me zai fada mata ?
Wata dabara ta fado masa ,yasaki ajiyar zuciya yafuto
Tana nan atsaye,ya miqa mata ledar "gashi inji qawarki"
Kallansa tayi "sajida?"
Yes ita
Tasaki murmushi tasa hannu zata bude yayi sauri yace no kibarshi idan kinje ciki kya duba
Tace to ,tareda ja masa kofar
Saida yaga fitarta sannan yayi ajiyar zuciya,yana ganin hakan yafi ,wayarsa ce tayi qara dasauri ya duba yaga abokin karatunsu ne daga kano Abbas
Yana dagawa yace shazali Allah yasa de baka manta da maganar taron nanba gobe
Wanne taro Abbas?
Taron da za'ayi a Russia mana na qarawa juna sani dakuma habbaka harkar kasuwanci,kada kacemin ka manta
Kansa yashafa yace Abbas wallahi na manta
,kawai nahakura bazan samu zuwaba
Mekake nufi ne shazali?
Taron nan dakai aka hada meeting dinsa da yanda zai kasance ,tayaya zakace bazakajeba?
Abbas banyi visa ba,yaushe zan samu viza ayau zuwa gobe?
Haba shazali meyasa kacika damuwa ne ?waya daya zakai kayi magana zance yawuce,nidama zan fadama ne nariga Dana tura musu sunayen mu ,sun tanaji hotels da abubuwan daya dace,kuma kada ka manta kowa da matarsa zaije idan bakada ita saikaje da budurwarka
Budurwa Abbas😳
Yes haka qa'idar take ,menene abin damuwa shazali dama kowa ya matsu yaga yarinyar dazaka Aura, kaga shikkenan saiku tafi tare ,nima daga nan zan dauki matata
Amma abbas ni.....
Dan Allah karkace komai shazali saimun hadu ,qit yakashe wayarsa
Innalillah....wayyo Allah na,meyasa Abbas zai masa haka ?meyasa ?
********
Tana zuwa dakinsutafara duba ledar hannunta ,brezia ce aciki masu kyau,kai sajida da jaraba take saida ta biyota dashi kenan🤣🤣amma ina tasamu kudin dazata siyo wannan ?dan daga gani kasan zasuyi tsada
Nunawa baba tayi,baba kinga kayan da sajida ta aikomin dashi
Yanzu uncle yayimin karatu shine yabani yace injita
Baba tace kai amma sunyi kyau sosai yata,yauwa baba bani aron wayarki nakirata nayi mata godia🙆🏻🤭
Baba tabata wayar me tocilan
Aikuwa tasaka number sajida aciki tayi kira ,dama ta riqe number
Sajida na dagawa tace mata sis naga saqo nagode,gaskiya sunyi kyau kuma kamar kin gwadani wallahi zasumin Dede
Wanne saqo kenan Haneefa ?
Saqon brezia mana dakika bawa Uncle yakawomin
Zaro ido sajida tayi tace brezia😳
A a ni wallahi ban bashi komai ba,ke rabona da uncle tun kina gidan
Innalillah...sajida me kike nufi ?
Menake nufi koke me kike nufi ?ai dama nafada miki abunnan gasu nasiyo mana daga mkrnta kikaqi karba kisa
Kinga yanzu ai gashinan shi yasiyo miki
Shalele tace nashiga uku sajida meyasa ya siyamin?
Cikin daria sajida tace oho muku wayasani ko shima gani yayi suna tsone masa ido ?🤣🤣😃
Batace mata komaiba takashe wayar,karfa zancen qawayenta na kuje ya tabbata,mijinta ne zai gwadata yaji adadinsu sannan yasiyo mata
Wayyo Allah itakam yau tashiga uku,🙆🏻da wanne ido zata kalleshi?
Baba hanne tayi murmushi dan tagama jin komai,dama tasan yaran nan kamarfa sunfada son junansu,inba hakaba shi meyasa zai siyo mata idan ba sonta yakeba?
tace yata to menene abin damuwa ?ai Haneef kamar yayanki ne
Cikin shagwaba tace Kuma baba saiya siyomin wannan ?kinga fa
Baba tayi daria tace to ayi hakuri mana tunda anriga ansiyo ai sai kisa 🤣😂
aranar haka tawuni adaki ,taqi yarda tafuto danma kada taganshi
********
Washe gari tunda safe yayi report a office cewa zaitafi Russia wajan taro na tsawon kwana uku
Ajmal yayiwa waya yasanar dashi komai, ajmal yace to ai bawani abin damuwa bane,ni ina ganin kawai kaje kadauki Hairat kutafi,dan tadanfi hajara wayewa
Sannan ita tanaji da tashen boko, nakega bazaka samu matsala da itaba
Eh nima abinda nake tunani kenan, shikkenan duk yanda ake ciki zakaji
Daga haka sukai Sallama yawuce gidansu hairat ,yau saboda yana sauri dakansa yake driving dinsa🤣🤣🤣
Yana zuwa gidansu hairat yatura maigadi yayi masa magana da ita
Aikuwa tanaji ance haneef ne tafuto,dama datasu yakashe mata waya rannan🤣😂
Kallansa tayi tace inajinka
Daqyar Kamar anmasa dole yace am dama zaki rakani wajan wani taro ne
Daria tayi, tahada hannayenta tayi tafi,🤗tace taro ?ko ?
Wato duk da baka nemeniba ,sai yanzu da buqatarka tatashi zaka nemeni,?wato zakaje dani taro danna rufama asiri🤣😂
Cikin bacin rai yace kinga....
Katseshi tayi,Malam kajuya katafi babu inda zani ,kaje wulaqancinka ya nema ma wata
(yauwa hairat nuna masa de mata sunada daraja suma🤣)
Bece da ita uffan ba yaja motorsa yabar gidan
Haushi yaji dabai karbi number hajara ba ,yanzu dolensa yaje gidan baida wani zabi
Yana zuwa gidansu kuwa aka kaishi falo ,hajara tafuto, ta tsaya akansa takama qugu tariqe
Shima tsaye yatashi yace hajara akwai inda nakesan ki rakanine
Nice zanma rakiya haneef? Ina zakaje da mummunar mata?Aida kunya ,kaje de ka nemi sarauniyar kyau ta duniya🤣🤭😃🤣
Tana fadar haka tashige ciki tabarshi anan
Da bacin rai yataho gida ,ko Neman ajmal baiyiba bare yasanar dashi abinda yake faruwa 🤣🤣
Part dinsa yaje yadauki kayansa ,yawuce part dinsu Momy yayi mata Sallama itada daddy
Yafuto harabar gidan yasaka jakar sa amota,yadafe kansa da hannunsa🤦🏻♂
(tofa yau taqarewa maza😂🤣)
Wayarsa ce tayi ringing yana dauka yace Abbas ya ake ciki ?
Shazali gani nida madam zamu wuce ,saikunzo ko ?
Cikin damuwa yace gaskiya..Abba..bansamu...
Haba shazali ,dan Allah karkace komai,danni harna Riga nasanar da friend's dinmu cewa zakazo mana da matar dazaka aura😳🤣
Cikin damuwa yace Abbas kakasheni🤦🏻♂🤣
Acikin gida kuwa shalele suna kitchen itada baba ,tace baba nagaji zanje daki nahuta,baba tace to yata Dan Allah dauki wannan towel din kidan shanya min shi akan fulawa,saikije ki kwanta
Towel din tadauka zata futo
Tana futowa adede kofar lokakcin Kuma Samah takawo kai itama
Aikuwa sukai gware
Cikin masifa tace ke wacce irin kidahuma ce ?bakya kallan gabanki ne ?
Cikin fishi itama tace toke meyahanaki kallan gaban naki ?
Cikin masifa samah ta fardo rigar jikinta tace nikike fadawa magana ?wacece ke ?Yar wacece ke dazakimin rashin kunya ?
Cikin fishi shalele ta fizge jikinta tace bansaniba kiyi abinda zakiyi ,tafuto harabar gidan cikin bacin rai
Itama samah tajuya takoma daki tafasa shiga kitchen din🤣
Tafara shanya towel din kenan yaji alamar motsin mutum
Dago kansa yayi ya kalleta,doguwar riga ce ajikinta ta atamfa
Ahankali yace "bakijiba"
Sai akai dace kuma maganar tasa ta tabbba,batajinba🤣
Yo magana ce anayinta kamar ba'aso🤣🤣😂
Sake daga murya yayi yace "qawar Sajida"
Ahankali ta juya taganshi atsaye ajikin motarsa
Besan sunanta bane yace qawar sajida ?
Qarasowa tayi wajansa,tace Uncle gani
Ahankali yatako yazo gabanta ,yasaka hannu yabude mata mota dakansa (tab matsayi🤣)
Kallan rashin fahimta tayi masa
Shima yagane hakan,lokaci daya yasha kunu ya tamke fuska cikin Qasa Qasa da murya yace "shiga mota mutafi"
Yafada mata hakanne saboda yana tsoron itama kada yace tarakashi tace bazata ba ,dan haka yasha kunu yace tashiga sutafi
Ganin babu alamar wasa a fuskarsa yasa babu musu tashiga ,yarufe ,sannan ya zagaya yaja motar sukabar gidan
Tab wayaga shalele a Russian😱
To masu korafi banyi typing ba jiya shikkenan de magana ta qare gashi har yau din tazo 😃
Tunda nafara rubuta littafin nan bantaba fashin turo mukuba,ai yakamata nima amin azuri,na kwana daya de
Nidama namuku uzuri tunda nasan soyaiyarku ga SHALELAN BABA ne yasa kukai hakan
Sharhi ,comment,share ,dan Allah karku manta🙏🏻
Amnah El💕SHALELAN BABA💕
(Romance)
Writing by Amnah El
31&32
Tunda suka fara tafiya babu Wanda yayiwa dan'uwansa magana
Ita sai kumburi take saboda Samah ta bata mata rai
Juyo da kansa yayi ya kalleta yaga sai cika take tana batsewa ,toya zai mata ?yasan bacin ran baiwuce tace yadaukota daga gida batasan inda zasuba ,idan kuwa ya kuskura yayi mata magana tace yamaidata gida tofa shi shikkenan tasa taqare dan baisan kuma wazai kamaba🤣
Danhaka shima yashareta yaci gaba da driving dinsa kawai
Kai tsaye wajan passport sukaje ,yanayin parking ya kalleta yace "muje"
Kallansa tayi sannan ta kalli jikinta,batada ko mayafi
Shima bece mata komai ba sai zagayowa dayayi side din datake yabude mata kofar motar,ganin da gaske yake yasa ta warware dankwalin kaanta tayafashi ,dukda beje mata ko'inaba
Tun kafin sushiga cikin wajan taga mutane sai gaidasu suke
Suna shiga cikin office dinkuwa dasauri ma'aikatan dakansu suka tashi suka basu abin zama
Abinka da manyan mutaje,nan take yadauki kafa daya yadora akan daya ,sabanin ita datai zamanta normal
(🤣to su shalele ba'a sababa)
Ahankali suka bashi hannu suka gaisa,sannan yace akwai tafiyar da zamuyi ne very important, but batada passport
Tafiya zasuyi ?ina zai kaita ?aikuwa bari su fice daga nan ta tambayeshi
Haba yallabai haneef,ai yanzu za'ayi mata, photon ta suka dauka,nan take suka fara yimata
Shikuwa gogan ya harde akujera yana danna wayarsa
Daya daga cikin su ne yafara yimata tambayoyi tana bashi amsa
Sunanki ranki yadade
Tace Haneefa Suraj Adam
Shekaru fa
Tafada masa komai ,yabata wani Biro dayake daure da wata na'ura yace tazo tayi sign
Tatashi tayi ,sannan tadawo kusa dashi tazauna
Suna zaune kawai sai gani tayi dayan ma'aikacin yace yallabai an gama komai
Yataso yamiqa masa ,karba yayi yace godia nake
Sannan yadauko ATM card dinsa yabasu,suka saka cikin p.o.s dinsu ,dakansa ya karba yacike musu komai har adadin kudin sannan yazare abinsa
Fara'ar dataga sunayi kadai ya tabbatar mata da cewa kudin daya basu ya wuce Qa'ida
Futowa sukai,suka nufi wajanda motarsa take
Yanda yake bude mata mota kadai zaisa kagane tanada muhinmanci awajansa
Sun fara tafiya ,ta kalleshi taga fuska atamke
Amma dukda haka saida tace Uncle ina zamuje ?
"Unguwa"
Abinda yace mata kenan
Shiru tayi ta rabu dashi ,basu tsaya ko inaba sai wajan saloon, yana tsayawa ya kalleta yace "futo"
Saida ta kalleshi sannan tafuto ahankali,shagon suka shiga babba ne sosai da fadi ,ayi saloon ,ayi makeup, ga kayaiyaki dasuke siyarwa agefe
Suna shiga yasake qarewa wajan kallo
,matar yarece ba bahaushiya ba,saide tanada yara mata masu yimata aiki hausawa
Tana ganinsa tafara fara'ah ,itade shalele aranta tace ikon Allah shi ansanshi ako'ina kenan
Gefe daya suka koma yayi mata bayanin komai ,sannan ya dubeni yace kije,shikuma yafice
Zaije yakai passport's dinsu wajan visa dakuma nema musu ticket din jirgin dazai tashi anjima
Matar dakanta tafara aiki akaina bata bawa yarantaba
Gyaran gashi tafarayi sannan ,sosai aka gyara matashi sai qyalli yake,ta nade matashi abaya yayi donut
Sannan sukaje wajan kwalliya ,ta tsantsara mata kwalliya ,lokaci daya tasauya kai bazakace shalelan baba ta qauyen kuje kaganiba🤣dan qaramin lips dinta bata cika mata janbaki ba ,kawai pink din jambaki tasaka mata shima kadan
Alokacin yadawo ,ma'aikatan suka sanar dashi cewa suna ciki basu gamaba
Agogon hannunsa ya kallah,wannan wanne irin gyarane ,yadauki lokaci sosai
Wajan zama suka bashi,amma bai zaunaba ,a tsaye yake yafara zagaye wajan ahankali yana duban agogo
Aciki kuwa wajan kaya suka shiga ,matar tayi shiru tana tunanin wanne kaya oga yasaka
Jijjiga kai tayi bayan tagama tuno kalar suit din datake jikinsa ,milk colour
Tadauki doguwar Riga fitet gwon me kyau ,rigar batada ado sosai sai dutsina dake jikinta farare masu qyalli,kafadar rigar ayanke take ,irin me bulalliyar kafadar nan ,tabata tasaka ,aikuwa Riga tazauna mata sosai ,musanman hips dinta yabada tashi gudunmawar ,dan kwalin rigar babba ne danhaka tayi mata rolling dashi
Wow gaskiya wannan wanka koni nayaba ,takalmi tabata me tudu tasaka ,da Yar qaramar jaka ,suka futo
Yana aikin zagaye falon sukazo suka sameshi,matar tace yallabai shazali we are finish
Yana juyowa yaganta lokaci daya gabansa yafadi ,kasa dauke ido yayi akanta ,matar ta kalleshi ,ta kalli shalele ,gaskiya ya'iya zabe,sunyi mutuqar dacewa da juna
Gyaran murya tayi ,dasauri ya kalleta ,yace sorry fa ,yabats ATM dinsa suka saka,dakansa yatura musu kudin
Sannan yajuyo ya fuskanci shalele datake tsaye tana kallan ikon Allah, su Kansu maaikatan wajan sunyi bala'in birgesu
Ahankali yatako yazo wajanta yamiqa mata hannunsa
Hannunsa ta kalla ta kalleshi,yaza'ai yariqe mata hannu?
Sake kallansa tayi ,taga yakafe mata idonsa,ahankali ta Dora hannunta akan nasa,lokaci daya suka karbi wani saqo daya ziyarci cikin jikinsu
Hannta Yakama suka fita ,yabude mata motar dakansa tashige sannan yaja suka tafi ,suna tafiya yadauko wayarsa yayi dialling number Anty Jidda, tana picking yace Anty zamu danyi tafiya ne
Tafiya kuma haneef ?kaidawa ?
Yanzu de Anty tunda kikaji an nemi izni awajanki kigane mana
Bazan ganeba,naqi nagane din ,kafadamin kaida waye ?
Wayyo Allah Anty,Nide babu ruwana tunda nafada miki
Sarai tagane inda zancensa ya dosa ,yafuto fili yace da haneefa muka tafi,shine bazai iyaba,gaskiya haneefa saitayi da gaske inma auren wannan yaron tayi kafin ta saitashi
Murmushi tayi ,haneef, Ina zaka kaimin yarinya?
Anty zamuje Russia ,wajan wani taro ,kwana uku kacal Anty nah
Innalillah...haneef zaka dauki yata kutafi wata uwa duniya har tsawon kwana uku amma kanacemin kacal
Wanne irin kacal
To Anty yaza'ayi
Yanda za'ai kawai kadawomin da yata
Wata irin daria yayi Dabe shiryaba,yace Anty amisali?
Nikake cewa amisali?babu wani misali ,agaske,inna yankatanka ,meyasa bazaka tafi dasuba
Anty abinne yazo da haka
Kuma shi abinda yatashi zuwa sai yazo yasauka akan yata
Wayyo Allah Anty ,zaki sani ciwon kai ,yanzu ina driving zamu qarasa Airport bye ,yakashe wayarsa
Duk abinda sukai taji ,yanzu itace zataje wata Qasa ?
Itace zatahau jirgi ?
Tana wannan tunanin taji yaana magana da saminu akan yazo yatafi da wannan motar
Suna qarasawa cikin Airport din suka fita ,jakarsa kadai yadauka ahannu sai passport's dinsu
Suka tsaya saminu yazo wajan, shide sai kallanta yake,wannan ba me aikin yallaabai bace?
Haka de yakarbi key din motar ,sukuma sukai ciki
Basu Dade da zamaba jirginsu yatashi,itace agefen window, shikuma yana gefe yadauki jarida yana kallo kamar ba acikin jirgi yakeba
Ta leqa ta kalli window, taga gajimaren nan sun keta taciki sunyi samansa ,tadawo da kanta gefe cikin tsoro
Yana kallanta ta gefen idonsa ,yayi dan qaramin murmushi, yasaka hannu yadanna wani abu aqasan window din nan da nan jikin window din yayi duhu
TV din dake jikin kujerar gaabansu ya kunna mata ,sannan yamaida hankalinsa kan jarida kamar ba shiba
Kallansa tayi ,takawar dakai,ina ita ina wani kallo ana wannan halin,kafarka daya aduniya daya alahira 🤣😃ai saide adduah
********
Wannan karon da Yar qaramar jaka tazo ,tayi nocking falon nasu
Samah da Safah ne azaune afalon ,samah sai kumburi take akan abinda yafaru tsakaninta da shalele
Hakan yasa Safah tabude kofar,da hajara tayi tozali ,to kunsan dama tsakanin nasu ba dadi🤣😃ta tsaneta
Cikin ranta tace kai wannan da jaraba take ,tace tafiya?
Samah ce ko Safah?
Safah tace Samah ce ,tasan idan tace safah ce zata raina mata hankali ,amma samah datake da masifa ,yanzu za'a zauna lafiya
Tace OK ,ina yayanku ?
Wallahi Yaya yayi tafiya yanzu
Hajara tace yayi tafiyar da gaske kenan
Murmushi tayi,wallahi kuwa ,Yaya anacan sararin samaniya yanzu ,🤣,saide kiyi hakuri dabai sanar dake qasar dazai tafi ba ,may be yana fadawa mutane masu muhinmanci ne awajansa
Tana gama fadar haka ta rufe kofar ,hajara tace wannan yarinyar karya takemin ,ba samah bace ,safah ce,dukda samah tanada masifa ai tana sona
Ko sake nocking batayiba taja Jakarta takoma gida ,dama dan mamanta ta matsa matane akan tazo tabishi ko hakan zaisa su qara son juna 😃
********
Malam yahai katemaka ka kiramin wannan yaron dayasa aka rufeni,na nemi yafiyar shalele awaajansa
Sannan inji Yaya Dana yake?
Ina aududu na,tunda suka sakani adakin duhun nan har yanzu idanun babu🤣😱bana gani,bana ganin komai
Malaam yahai yace marka kiyi hakuri,amma wannan yaron likita dakike gani dan boko ne ,bazaima kula kiba ,yafi karfinki marka
Fashewa tayi da kuka ,innalillahi...wai yanzu ni marka nice bana gani nice awannan hali
Malam surajo ka yafemin,hakika na karya alkawari
Yanzu Malam yahai dan Allah kakaini gidanmu wajan murja ,ko zata dinga temaka min,zamana anan gidan nikadai bazai iyuba,babu Malam surajo,babu shalele,babu Aududu
Haka Yakama mata sandarta ,sukayi gidansu markan
Rayuwar kenan😢
********
Jirginsu na sauka ,suka futo a gajiye ,tafishi galabaita saboda akwai nisa,Abbas yana ganinsu yaqaraso suka gaisa ,haneef ya harareshi
Yace eh naji de ,inba haka nayimaba ai bazakazoba
Kallan shalele yayi, masha Allah gaskiya abokinsu ya Iya zabe
Tace ina yini ?
Lafiya qanwata ya rigimar wannan gayen ,nasan kina shan shagwaba ko ?
Murmushi tayi,ta sunkuyar dakanta Qasa ,uncle dayake babba ina zaiyi wata shagwaba
Shazali yace dan Allah Abbas muje ,mungaji wallahi
Kafadarsa Abbas Yakama yace kai shegen gaye,ina kasamo sweet 18 ne ?
Yarinyar tayifa
Shalele de tafiya suke amma batajin me suke fada
Shazali yace nima haka naganta
Karya kake shazali,yaushe kadena ra'ayin manyan yanmata ?
Har yanzu ina ra'ayi
Abbas yace OK dakaga ta mallaki komai ko ?
Abbas kadena wannan maganar kada taji ta rainani
Dukan wasa yayi masa yace shege shazali🤣😃
Motar suka shiga ,suka wuce hotel din da ake saukar baqi
Motarsu na tsayawa matar Abbas ta qaraso dasauri cikin fara'ah ta rungume shalele
Bawata babba bace ,bazata wuce 26ba,tanaji da gayu dakuma yanmatancinta
Sannuku da zuwa ,sannunku,sai da suka gaisa da shazali sannan Abbas yace kuje ciki sweety tahuta gamunan zuwa muma
Ciki suka shiga itada shalele, zama sukai agefen gadon,dakin yayi kyau sosai babu tarkace dayawa kamar de yanda hotel suke
Tace sannunku
Shalele tace yauwa Anty
Dadi taji,lokaci daya taji son yarinyar, daga gani badata raini,tace sunana zainab,mijina kuma Abbas
Abokin haneef dinki ne ,suna kasuwanci tare🤣🤣
Cikin ranta tace haneef dina,to Allah yasa🤣
Zainab tace kekuma menene sunanki ?
Sunana haneefa
Wow nice ,wato shazali saida yajemo kyakykyawa kuma me irin sunansa sannan yafara soyaiya,shiyasa yadade bai samu budurwa ba
Shalele tace amma Anty..ni babu soyaiya atsakaninmu🤣🤣wannan tafiyar dakikaga anyima...
Murmushi Zeey tayi,takama hannunta duka biyun ta riqe
Haneefa ,azamanin nan na yanzu ,bakowanne mutum ne zai bude baki yace wance ina sonki ba
Kawai idan ya nuna mata a aikace ya wadatar
Kamar shazali ,na tabbata kallan dayake binki dashi naso ne,tunda kikaga ya zabeki yadaukoki yataho nan dake to yana sanki ne,bazai iyu ya nunawa abokan kasuwancinsa wata wadda ba ita zai Aura ba
Kiyi kokari kiga kin mallake zuciyarsa,tahakanne zaki tabbatar da abin danake fada miki
Inaji awajan mijina yanmata dayawa suna sonsa ,suna kai masa hari ,harkokinsa ne kawai dasuke dayawa yasa baya samun lokacin saurarensu
Bude kofar akayi ,Abbas ne da shazali ,Abbas yace mata kenan ,memakon kikaita dakinsu tayi wanka tahuta a a ,sai kuka baje kolin fira
Toga abinci ,Ku sauko kuci
Shazali yace no Abbas, sainayi wanka tukunna
Anty Zeey tace a a to itama ai gara tayi wankan kawai dakunci abinci saita kwanta tahuta
Daga kansa yayi yace OK yayi kofar fitadaga dakin
,yace Abbas
Abbas yatashi yabishi wajan kofar ,kallansa yayi yace abbs yaza'ayi ne
Kamarya ?
Ina nufin tazauna su kwana da zainab, saimu tafi dakai dayan dakin
A a shazali gaskiya ina buqatar matata ,kadauki abarka kutafi 🤣🤣
Haba Abbas...
Haba shazali,babu abinda zai faru insha Allah
Yadubi zainab yace ke zainab rakata dakin su, Anty Zeey tayi murmushi takama hannun shalele da takeaway dinsu na abinci suka tafi dakin da aka tanada domin su
********
Cikin tashin hankali tace hajiya wallahi naduba ko ina bangantaba
Momy tace a a to ina yarinyar nan zata shiga ?Tun safe ana nemanta
Safah tace Momy samah tacemin sunyi fada dasafe,saide in zuciya tayi tatafi garinsu
Momy tace kai Samah ,samah kincika matsala wallahi
Zaiyi wahala tatafi garinsu
Ta kalli baba hanne tace baba bari nakira Jidda naji ko can tatafi
Ana kiran Anty Jidda Momy tace Jidda yarinyar nan kuwa tana gidanki?tun safe muke nemanta bamu gantaba
Wacce yarinyar Momy?
Yarinya de datakewa haneef aiki,shalele take kowa?
Tuni Anty Jidda tadau haske😃hakan yana nufin babu sanin yan gidan ya dauketa kenan
Tace eh Momy tana nan ,sunma fita itada sajida
To alhamdlh tunda tana wajan naki,wai fada sukai itada samah shine tayi fishi tataho nan wajan naki
Kuma yanzu Jidda komai na duniya ba dan hakuri bane ?🤣
Idan taqi dawowa shi kuma yana dawowa daga tafiyar nan zai sani agaba ince kidawo da ita
Anty Jidda tasha daria tace to Momy zansa tadawo
A a Jidda yanzun ki barta,idan haneef din yadawo itama saida dawo,tunda shima yanzun baya nan
Anty Jidda tace toshinn Momy sai anjima
Wayar takalla tasake daria kai,Momy kenan,wani bikin sai agidan momu kina zaune agida ana wani budirin baki saaniba🤣😃🤣
Momy ta kalli baba hanne tace to baba kinji tana gidan Jidda
Baba tace to alhamdlh tayi kitchen
********
Suna shiga dakin Zeey tabata abincin nasu ,tamatso kusa da ita tayi mata rada akunne
Ki kwantar da hankalinki qanwata ,nasan halinsa babu abinda zai miki,tana fada mata hakan tace musu saida safe tafice
Yana ganin fitar Zeey ya kalleta ,duk tatakure kanta ,girgiza kansa kawai yayi cikin ransa yace yarinta kenan🤣
Bece mata komai ba yafara cire suit dinsa ,yajefata kan gadon ,niktile dinma ya cireshi ,agogon hannunsa ya kunce ya ajiyeshi daga gefe yakalleta atsaye ita bata zaunaba ita bata fitaba
"Idan kingama tsewar zaki Iya zama,nizanyi alwala nayi sallah"
Yana fada mata haka yashige toilet, tabi bayansa da kallo tasaki murmushi wannan mutumin yana birgeta ,zama tayi agefen gadon tana jira yafuto itama tashiga tayo alwala,tagumi tayi hannu bibbiyu😱 tana tunanin yanda zata kwana dashi daki daya
To mutara zuwa gobe domin jin yanda zata kasance ☺
Sanarwa
(Wannan sanarwar ta fan's dinane na Facebook kadai,har yanzu ban bude group nawa nakaina a facebook ba
Ku fahimta niba admin bace akowanne group na Facebook, nima member ce kamar yanda kuke members aciki
Idan naturo muku littafi bazai iyu Ku ganshi alokacin Dana turoba,dole sai admin sungani saannan sukuma su sakeshi,kowa yagani ,dafatan kun fahimceni ,ina jin dadin comment dinku sosai wallahi hakan yana qaramin qwarin gwiwa akan yin typing kullum nagode🙏🏻🙏🏻
Amina Muhammad el Yaqoub✍🏻💕SHALELAN BABA💕
(Romance)
Writing by Amnah El
33&34
Tana nan zaune harya futo daga toilet din, sannan tasaki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 17