suka kawo masa, Har qasa ta tsugunna tazuba masa, ta kalleshi to uncle gashi
"bazaki Bani ba?"
Murmushi tayi tatashi tabar wajan, Afrah na kallan su daga gefe, kome yace Mata? Shide komai nasa a hankali cikin sigar rada, inba kana kusa dashiba, ba lalle bane kaji meyace
Cikin nutsuwa yakeshan a binsa, saiyaaji kamar baba Hanne ce taayi
(renon baba hannen cede🤣🤣🤣)
Shi Yana gefe Yana shan kununsa Yana kallo itada Afrah suna gefe a zaune, Har aka Kira sallar magrib, yaje yayi sallah yadawo, ya kalli Afrah qanwata ku shirya mana muje ku rakani unguwa
Afrah Dama Zaman ya isheta, kullum mutum Yana gida ba yawo tace to Yaya, sukayi daki suka shirya cikin sauri, Dakin Mami sukaje sukayi Mata sallama sukai fice, afraah na baya, su kuma suna gaba
Har yakaisu wajan shan ice-cream, su kasha, ya lodo musu wani, Yana ganinsu sau murna suke, Shide kawai kallan su yake, yarintama da dadi take 🤣🤣daga zuwa wannan wajan shine abin murna, sude Yara kullum basa gajiya da Abu, inba hakaba jiya jiyan nanfa sukazo🤣🤭
Daga nan sukaje yasiya musu shawarma dasu boga sannan suka tafi gida, a harabar gidan ya ya tsaya, Afrah ta kwashe musu kayan tayi cikin gida, Shikuma ya dubeta yace kada ki manta fa, kibude wayarki
Saida ta sunkuyar da Kanta qasa sannan tace to uncle insha Allah
Saida safe
No bawani Saida safe, first kifadamin maganar dazanji dadinta sannan kitafi
Cikin shagwaba tace to uncle ni mezance
Wani irin yanayi yashiga sakamakon wannan shagwabar data masa, Har baisan lokacin daya kwanta da kansa a jikin seat dinba
Yace ko Maima kice
Shiru tayi, can de tace masa I luv you uncle, thnks you for everything Tabude motar tafice da gudu, murmushi yayi, sannan yaja yarufe yayi gida, Yana hanya saiyaaji kamar ansauke masa wani nauyi a kansa
********
Washe Gari takama weekend, Mami takira Dr Bilal yazo Har gida, suka dunguma gaba dayansu suka tafi kuje, suna tafiya ahanya sunata fira abin gwanin birgewa Mami da shalele da Afrah Abaya sai Aududu dake cinyar Mami, Shikuma Dr Bilal suna gaba shida ameer
Basu tsaya ko'inaba saide kofar gidansu shalele
Ta kalli gidan, aduk lokacin data zo kuje babu mutumin dayake fado Mata irin baba
Rayuwarfa Kenan, Har anzo anyi antafi
Suna futowa sukaga gidan akulle
Basu tsayaba suka shiga gidan baba malam, Inna sabuwa tana Daka sai ganin baqi tayi
Da gudu taje ta rarumi shalele tace, shalelan baba? Wai kuwa kenake gani?
Shalele taayi murmushi tace nice Inna
Inna sabuwa tabisu Mami da kallo tace wannan ai hajiya ce dasukazo kwanaki, sannunku da zuwa
Tashinfida musu tabarma, suka zazzauna, aka sake gaisawa, sannan tace gashi kunzo malam baya nan yatafi kewaya, Amma bar atura yaro yakirashi
Nan da nan tatura danta yatafi Kiran baba malam, shalele tace Inna sabuwa baki gane wannan bane? Tanuna Mata Aududu
Inna sabuwa ta kalleshi tayi shiru, shalele tayi daria Inna Aududu nefa
Laaa Wai Aududu ne ya girma haka? Kekiga yaro yayi bulbul jajir dashi Dan Allah 🤣🤣
Duk saita Bawa su Mami daria
Tace hajiya ai ba abin daria bane, yaro duk ya sauya kamanni, tatashi tafice saigata yadawo da ruwa pure water 💦me sanyi
Dukansu kuwa suka Sha, akaci gaba da fira, malam yahai na zuwa yace a a a a kice yau shalelan baba ce dakanta, Dukansu Saida yabasu daria
Mami tace Dama haka kuke fada Mata ne?
Baba malam yace ai hajiya Kowama anan Garin shalelan baba yake cemata, saide Yan makarantar su ne suke kiranta da haneefa
Amma kinga malam surajo, tunda nake dashi zaiyi wahala kiji yace haneefa, saide yace Shalele nah, komai de Shalele nah
Lokaci daya qwalla tacika idonta, tace hakane kam baba malam, ni tunda nake da baba ma bantaba ji yakira sunana ba, saina ranar dazai rasu
Tana fadar haka tafashe da Kuka
Gaba dayansu jikinsu yayi sanyi, barinma Bilal da agabansa akai komai, shi kansa yaji mutuwar mutumin, suna wannan halin shiyasa a lokacin yayi mamakin Ina shalele tasamu wannan kudin aikin da akayiwa babanta, yaga alokcin Yana fada babu ko dar tace zataje tabiya, ashe Shikuma wannan ta dalilin haneef tasamu, Dama can Allah yariga daya tsara komai, Shiyasa ya aiko Mata shi a lokacin daya dace kuma akayi sa'ah ya temakesu Akan kudin
Allah yajikaan malam surajo
Baba malam yashare qwallarsa yace naje wajan liman nayi masa magana Akan gidanku da kuma gonakin malam surajo, akwai gonakinsa na shinkafa guda biyu saiwata gonar dayake shuka ayaba, dakuma wasu guda biyu dayake shuka kayan gwari aciki saikuma fili guda daya, sai kuma Yan kudadensa dasuke wajena gaba dayansu, ansanar aagari idan akwai Wanda yake binsa bashi to yazo yasameni yayimin bayanin komai, to Alhmdlh babu kowa, ko mutum daya babu
Saikuma amfanin gonarsa yafuto ancire, nakaishi kasuwa ansiyar, Shima duka kudin Yana nan a ajiye
Liman yace nabar takardun a hannu na idan kika zo sai ahada da kudin Araba muku keda dan'uwanki Aududu
Jin wannan bayanin na baba malam saiya Sakata Kuka riris, shi kansa baba malam din hawaye yake, sai sharewa yake da babbar rigar jikinsa
Afrah Kam tuni takasa tsaida hawayen ta, Kai Allah yaqarawa iyayenmu lafiya da nisan kwana, ta tausayawa shalele, haqiqa taga rayuwa, itadin abar atausayawa ce
Mami ce tayi karfin hali tace malam yahai ai baza'ai hakaba, Har gobe Kai ubane a wajan haneefa, kunyi zama na Amana atsakaninku, babu maganar Rabe Rabe anan, haneefa de macece, kuma duk Daren dadewa gidan wani zata, kuma abune dayake a baiyane duka dukiyar za'a Raba gida uku, shi Abdallah yadauki kaso biyu ita Kuma tadauki daya, kamar yanda ubangiji yafada acikin aqur'ani, cikin suratul nisa'i ayata goma, saboda haka Kaci gaba da amfani da gonakin nasu, Har Allah yaraya Abdallah saiya riqe musu gaba daya shida yar'uwarsa, duk da tafishi shekaru shi namiji ne, zuwa gaba shine zai jagoranci rayuwarta, batada kamarsa, Shima haka
Maganar kudi kuma kasa ayi bohol dashi a makaranta, kokuma acikin masallaci al'umar annabi sudinga diban ruwa, Duk Wanda yayi amfani da ruwan Allah yakai ladan kabarin malam surajo
Gaba dayansu suka amsa da ameen, baba malam yace hajiya ai duk da haka kudin sunada yawa
Tace karka damu malam yahai, kasa ayi bohol din kawai
Yace to toshknn hajiya, daga gobe zan Nemo ma'aikata ayi famfouna da bohol amakarantu Dama masallatai gaba daya insha Allah, abinda yayi Saura kuma za'a yi masa sadaka dashi
Shalele tace baba malam kadage kabarshi kawai
A a shalelan baba, ayiwa malam surajo, Shima yayi mana lokacin dayake Raye
Shakeran jiya sha'aban me kaiii makaranta kuwa yazo yakawomin machine dinki, nace masa a a yaje saikin zo saiya dawo
Daria tayi tace kawai kace nabar masa baba malam, yace to za'a fada masa
Mami tace malam yahai yarkafa zuwa mukai musanar dakai ansaka Rana
Yace a a a a Waye angon? Ya nuna ameer yace koshine?
Tace a a bashi bane, wani dan'uwanmu ne Shima, nanda kwana 38 za'ayi insha Allah
Alhmdlh, to hajiya ai wannan babban albishir ne, Allah yakaimu lokacin, ya kalli Dr Bilal yace to likita ya zatayi aure, Shikuma baban sai yaushe? 🤣🤣
Bilal yace za'a yi insha Allah
Mami tace to idan Allah yakaimu angama biki lafiya, sai kayi shirin tafiya umara kaida hajiya sabuwa
Ai Inna sabuwa najin haka tasaki Buda, Dukansu Saida sukai daria Sosai
Haka sukaita zubawa Mami godia, daga nan tace suje wajan Marka, akai Mata danta taganshi
Baba malam ne yayi musu jagora, sukaje Har gidan, ahalin dasuka ganta, sun tausaya Mata, tana Kuka tanemi yafiyar shalele, tace babu komai Inna nayafe miki, aka Bata Aududu saide kuma babu idon gani
Dakanta tasake roqarsu alfarma su riqe Mata shi, kada su duba abinda tamusu, suduba halin ubansa malam surajo kawai
Haka suka bar gidan cikin sanyin jiki, gaskiya dan'adam ba'a bakin komai yake ba, anan Garin kuje suka wuni, sannan suka tafi gida yamma liss
********
Washe Gari Dr Bilal yashirya cikin manyan Kaya, yayi mugun kyau, yadauki hajiya da sady da Abdallah sukayi gidan mami
Mami tace a a baban haneefa wannan wankan haka sai Ina?
Hajiya tayi murmushi tace Kema de kya fada, Wai gidan surukai zaije 🤣
Mami tace a a kace neman auren yayi Nisa, Gara de anema Kam, kowa sai yayi masa yace zaiyi auren ya, shi baiyi ba
Hajiya tace ato ai Gara kidinga fada masa, qanwarsa ma sadiya jiya Bayan kuntafi kuje manema aurenta sukazo, Wai zasu kawo gaisuwa nace suhado Har kayan Saka Rana kawai babu maganar wata gaisuwa, ita bikin Nata sai nanda wata biyu
Mami tace a a lalle, gaskiya zamusha bukukuwa, Allah yakaimu
Shikam Dr Bilal sallama yayi musu yace zaije yadawo saiya daaukesu sutafi
Yana zuwa gidansu momy yakira daddy awaya yace Yana da baqo
Daddy ya yi mamaki wanne baqo kuma? Haka de yafuto, Yana ganin Bilal yace a a Dana ashe Kaine, yamiqa masa hannu
Dr Bilal yabashi haannu aamma saiya tsugunna bai tsaya a tsaye ba🤣🤣shide daddy mamaki
Yace Dr Bilal ko kazo wajan mijin yar taka ne haneef? 🤣
Ya Sosa qeyarsa yace a a daddy ba wajan haneef nazo ba, wallahi yau zuwan nakane, wajan ka nazo, 🤣🤭
Daddy yace masha Allah, to ko daaga wajan daurin aure kake Naga Kaci manyan Kaya harda babbar riga🤣.
(Kai daddy Dan Allah 😃😒)
Saida yayi murmushi kin furucin daddy sannan yace a a daddy, Dama Samah ce taturoni wajan ka 😳😲🤭🙆🏻
Munyi magana da ita, to sai tace nazo wajan ka duk yanda mukai de, mun dedeta kanmu nida ita, ni inso saamu nema inaso ahada bikin danasu yar'uwarta da yayanta
Daddy yayiwa murmushin su na manya, ai sai yanzu yagane dalilin Saka manyan kayan🤣ashe wajan surukai za'a zo shine dalili
Amma fa yayi mamaki Jin sun dedeta kansu shida Samah, yaran da agabansa Saida sukai fada a asbiti lokacin dasuka je Bilal yarakasu wajan haneef? Koda yake yaran zamani ne qila sun shirya din
Ya kalli Bilal yace to Bilal babu damuwa zaaka Iya turomin magabatanka
To daddy insha Allah zan turo su, Amma daddy Dan Allah kada afamada Mata, inaso nayi Mata surprise
Daddy baice komai ba yayi murmushi gamida girgiza kai yajuya gida 😃
Dr Bilal na zuwa gidan mami yace su hajiya su futo su tafi, sady ta ware acikin su shalele sunata firarsu, tayi Mata murna Sosai Akan auren Miji kamar haneef shazali
Saida suka rakosu Har wajan Mota, shalele tace hajiya kinqi yimin kwalliya de kisamin kwalli🤣🤣
Daquwa hajiya Tamata, kede kin maidani kakarki wallahi
Sady tace hajiya Dama ai itace, dahaka sukai sallama cikin farin ciki
********
Washe Gari kuwa iyayen Dr Bilal sukaje akai komai aka Gama, aka tsaida lokacin biki danasu shalele, momy tayi farin ciki Sosai zata aurar da yaranta Dukansu
Dr Sulaiman ma dayaji wannan labari sai yace to tunda duka za'ayi wannan auren na dangi Shima Ajmal idan yashirya kawai yafuto, idan kuma bai shiryaba sai ayi nasun daga baya, to Dama gwanin naku kamar Akan qaya yake 🤣🤣baisha wahala ba wajan yiwa iyayen nasa bayanin komai, sukazo suma aka tsaida bikin lokaci daya
Anty jidda tayi murna Sosai, Gara tayi gajiya daya tahuta 🤣
Alhaji Tahir da daddy sunyi magana Akan zuwa siyaiyar kayan Yara
Daddy yace haneefa tazauna saboda karatunta babu inda zataje ta yanke karatunta
Mami taji dadin Hakan Sosai, Koba komai tasan idan yarinyar taxo gidan ma bazai Bari karatun Nata ya tabarbare ba
Sajida ma tazauna agida tunda ga jiddah nan zataje, yatura Mata kudin komai, furnitures na yanbiyu, da zata siyo musu, sai kuma na sajida ma dazata siyo duka Har ita, uku Kenan
Daga can wajan su mami kuwa itace da Kanta zata tafi, zata hadowa haneef lefe da Bilal data dauke masa nasa, 🤣tunda Yan biyu suka dauko Mata Gara taje dakanta tahado musu komai iri daya, sai kuma furnitures din haneefa, lefe biyu daa kayan daki daya
Ita Kuma anty jidda kayan daki uku, sai kuma lefe daya na haneefa, haneef yace zai tura Mata kudin tasiyo komai, haka ta dage tace wallahi sai yaje, bawani kudi dazai tura Mata zuwa zasuyi yahadowa yarta Kaya nagani nafada
Tayayama zaice zai Bata wani kudi, ai kawai ita shine kudinta suje kawai tana jidar Kaya ga ATM dinta haneef akusa🤣🤣
Idan taje tasiyo masa ma ai yadan samu sauqi, ita Kuma tafi so yaji a jikinsa yasan cewa mace Mai tsada zai aura
Dole sai sake daga tafiyar sukai zuwa Bayan kwana uku tajirashi🤣🤣 yagama ayyukansa sannan suka tafi Dubai ita dashi kafarta kafarsa
🤣
Saikuma Mami
Bataso suyi kwanaki dayawa a Dubai, tana so suyi sudawo tafara gyara yaranta ciki dabai
(gaskiya anty jidda zan turo Miki kidnappers 🤣🤣🤣irin wanna tafiya haka ai kinyi tsada dayawa)
Mutara zuwa gobe yan'uwa, ngdi🙏🏻
SHARHI Dan Allah 🙏🏻🙏🏻
Mrs Usman Ce✍🏻💕SHALELAN BABA💕
(Romance)
Writing by Amnah El yaqoub
47&48
Kwanansu anty jiddah biyar suka Gama hada komai suka yo gida, ammafa jiki yaji, dan ba qaramin Kaya suka siyo ba
Nan gidansu momy tasauka, itama Mami tawuce gida
Sai washe Gari anty jidda tatafi gidanta
********
Mami na zaune afalo da yaran Nata maza Dr Bilal da ameer suna ganin kayan, ameer yace gaskiya Mami sunyi kyau Sosai, kamar safah🤣
Iyee lalle ameer wato nema kake yanzu kakoyi rashin kunya, sunyi kyau kamar matarka
A a Mami nifa Bahaka bane nufi ba
Tace kaika Sani ameer
Ta kalli Dr Bilal dayayi tagumi Yana kallan kayan😱
Dana kayi shiru Kai banji kace komaiba
Ajiyar zuciya yayi, ai Naga kin kashe kudi dayawa ne Mami, wannan marar kunyar yarinyar zaaki siyawa Kaya dayawa haka 🤣
Haba Bilal, kaida ameer ai duk daya kuke a wajena, kada ka manta kariqe yata Amana a lokacin data rasa Wanda zai tallafa Mata, tana nemanka a lokacin da take cikin tsaka me wuya
Zanyima fiye da haka Bilal, saide kuma in basu birgeka bane
A a Mami sunyi kyau Sosai wallahi
Yafadi haka Yana sake yin wani tagumin😱
Mami tasake Kallansa cike da damuwa
Wai meyake damunkane kazauna kayi jirim haka, ko ameer dayake min Dan kawaici yau kawar dashi gefe yayi Yana kallan kayan matar sa🤣🤣
Ameer yasosa Kai yakawar da fuska gefe
Dr Bilal yajanye tagumin dayayi, ai Mami bakisan rikicin Dana hadawa kainabawa,😣😣😣
Yaarinyar nanfa batasan komai ba, sannan nace daddynsu kada yafada Mata, nide kawai mun Riga mun dedeta kanmu😢😢
Tace wakake magana? Wai Samah?
Be Iya cewa komai ba sai gyada kai🤣🤣
Tace zancen banza, to me zatace kuwa Bilal, anriga ansiyo kaya an tsaida ranar biki kuma zasu ce sun fasa ne? Impossible 🙅
Zai iyu Mami 🤣🤣
Saboda me zakace za'a Iya fasawa?
Mami kemafa lokacin da'aka yanke ranar bikin yarki, da ranki yabaci, haka kika tubure kikace sai an maida musu kayansu 🤣🤣
To Kinga Nima zasu Iya fadar haka idan ran yarsu yabaci
Mami tai jimm🤣🤭takasa magana, Saida tayi tunani sannan tace eto babu dadi de gaskiya, Amma nide Dan Allah kasaki jikinka ayi farin ciki a lokacin da ake cikin sa, banaso Naga jikinka a sanyaye
Kaje kasameta kayi Mata bayani cikin fahimta, zata fahimceka idan kuma taqi sauraronka kahadata da Safah
Daga shi Har Bilal suka hada baki wajan fadin Safah kuma!!? 😳
Yace to me Safah zata Iya Mata Mami?
Tace Bilal Kenan, yar'uwata cefa, sufa Yan biyu ne, Safah tana son dangantakarka da Samah, tun suna Yara nasan halin Yara idan daya tanason Abu daya bataso, to zasuyi cece kuce dinsu lokaci daya, ammafa daga baya duk suna dawowa suso Abu dayane
Ina tabbatar ma kosu momy saisu Mata magana Tari biris sabanin Safah
Kaje ka gwada, ba'a shiga tsaakanin yanbiyu, idan mutum yashiga ma kunya zaiji, Shiyasa Yan gidan basa shiga sabgar su🤣🤣
To Mami zan gwada insha Allah
Kafin tace komai shalele tayi sallama tashigo falon, cikin murna ta qarasa wajan su, Mami kayansu Yaya ameer ne? Ba'a Bata amsa ba tafara dagawa Kai ammafa Mami kin Iya zabe, kayan sunyi kyau, kuma komai iri daya
Toba dole nasai ko Mai Iya iri dayaba haneefa, sun je sun dauko min yanbiyu🤣🤣
Dukansu sukai daria, Bilal yace ya makarantar?
Wlhy alhmdlh uncle munkusa zana exam ai
To ki dage da karatu de, abinda baki ganeba ga Ameer nan
Uncle ai kullam ma munayi da Afrah
OK to Allah yasa adace, tace amin
Ta kalli Mami, Mami Ina Afrah? Ita taga kayanne?
Afrah Tana bacci, idan tatashi zata gani itama
Wayar Mami tayi qara, tana dauka suka gaisa da anty jiddah, banji me jidda tace ba, Mami tace to shikkenan, kawai Saita dinga zuwa daga nan ba, eh, Toba damuwa, akwai wata Mata ma Dana Mata waya, zan turota nan gidan naki kawai sai tayi Miki bayani,
Dahaka sukai sallama
Ta dubi shalele tace haneefa jidda tace kidauki uniform dinki da sauran kayan amfani driver yakaiki can, zakici gaba da tafiya school ta gidanta
Tace to Mami meyafaru?
Mami tace Ina zan Sani haneefa? Abinda tacemin kenan🤣
Shalele tace to Mami, ta daga wani takalmi da jaka tace Kai wannan kuwa kamar kinsan kafar Yan biyu wallahi zai hau kafar nan tasu🤣🤣
Mami ta kalli ameer da Bilal tace kungani ko? Bafa zata Dena wannan sururin kayan ba, 🤣inajin idan taga Nata haukacemin zatayi, dan jidda Ina ganinta tana tisa qeyar Yaron nan komai siya Mata yake saikace Wanda zasu Bude shago
Ai tanajin maganar Mami taayi cikin dakinsu da gudu
Duk suka Saka daria Mami tace idan banmata hakaba bazata tatashi taje ta shiryaba 🤣
Suna nan a zaune hartaci abinci tafuto da yar qaramar Jakarta, Afrah tarakota sai hamma take da alama daga bacci tatasheta
Dr Bilal yace Mami Nima Bari inwuce wajan yarinyar nan duk yanda mukai zan Miki waya, tace to kawai kutafi da haneefa idan kasauketa gida jiddah saika wuce
Yace to, ya karbi jakar Tata a hannun Afrah sannan yayi gaba
Shalele Saida taje ta rungume Mami sannan taace bye bye Mami, tabi bayansa da gudu
Mami ta girgiza Kai, haneefa! Haneefa!! Um haneef zaisha fama
********
Anty mu kinsa andauko mu daga gida, kuma ni wallahi kallo nakema momy tasa saida muka taho
Anty jiddah ta kalli Samah, me yarinyar nan take nufi? Takirasu nefa gaba daya duk tahadasu ayi musu komai lokaci daya Amma kuma taga kamar ma ita batasan komai ba
Tace Samah, gyaran jiki fa za'a muku, sannan munyi waya da maminku yanzu tace akai wata Mata ma dazata turomin ita takanas kawai dantazo tayi muku komai Har gida, Amma Dan iskanci kina min maganar kallo, Waye yahanaki dauko system din Taki
Gyaran jiki kuma anty?
Name? Nida ba amarya ba wanne gyaran jiki za'a min, Anty Samah cefa ni ba Safah ba 🤣🤣Naga duk bakwa ganemu, Safah ce amaryar 🤣
Anty jiddah cikin ranta tace tirqashi!! 🙆🏻
Sannan tasake duban Samah cikin nutsuwa tace Samah, nasan kece Samah nake Miki maganar ba ganeki ne baanyiba, Samah kinaso kicemin bakisan dake za'a hada ayi auren ba?
Aure Kuma anty? Kai anty kinada abin daria wani lokacin wallahi 🤣🤣🤣to dawa za'a min wani aure?
Tamaida hankalin ta Kan wayar dake hannun ta tana dannawa
Anty jiddah tace da Bilal mana
Ai tanajin wannan maganar tayi wulli da wayar dake hannun ta
Anty me kikace? Bilal kuma? Yaushe? Yaushe mukai haka dashi? Yaushe nace masa Ina sonsa?
Anty jidda oho muku, Amma kinsan de aure babu fashi, tunda iyaye sun shiga maganar, bazaki maida mana daddy qaramin mutum ba
Kuka tafashe dashi, kukanta ne yaja hankalin Safah da sajida dasuke daki
Cikin kururuwar Kuka tace wallahi ni Bana Sansa, Allah bazan aure shi yaje ya kashe niba, Yaushe mukai haka dashi daza'ace za'a Bani shi, Bayan kullum cikin yimin mugunta yake, Allah bazan yardaba
Safah tace anty meyake faruwa
Anty jidda tayi Mata bayanin komai
Girgiza Kai Safah tayi, taqarasa wajan Samah ta dago ta, tace kiyi hakuri mana Samah, menene aibun Dr Bilal? Yana sonki, Samah bazaki gane hakanba sai nan gaba, fadan dakuke Bana komai bane sai soyaiya Samah
Cikin hawaye ta kalli Safah tace dayake ke anbaki Wanda kikeso ba dole kice hakaba, nafasan halin Bilal din, wallahi mugunta ce dashi, mutumin dayake budar baki yace zai zaneni tayaya da hankali na zan yarda naje gidan sa, nace Miki Bana Sansa ko dole ne?
Ran Safah yabaci tace shikkenan tatashi tsaye tadauki wayarta tana dannawa
Sajida tace Safah Wazaki Kira? Dan Allah karki fadawa daddy
Safah tace ba daddy zan kiraba sajida, Ameer zan Kira in fada masa nafasa aurensa, inyaso nisai na auri Bilal din
Samah tanajin haka ta miqe tsaye tafara kokari qwace wayar, Safah ta hanata, tace Samah wallahi bazan baki wayar nanba, bakince saboda zan auri Wanda nakeso ne yasa nafadi hakaba? To daga yau Nima nafasa auren ameer din, taqarasa maganar tana fashewa da Kuka
Itama Samah din cikin Kuka Safah nace ki Bani wayar nan ko?
Itama ta kalleta cikin ido tace Samah Abaya Kam duk na Miki biyaiya amatsayinki na yayata, Amma Banda yanzu, kije kiyi abinda kikaga Dama Nima zanyi abinda nagadama
Zan auri Dr Bilal, Kema kije ki auri ameer, Kinga anyi 50 50 kowa ya auri Wanda baya so, tunda haka kikeso
Cikin Kuka Samah tace Safah nikike fadawa haka ko?
Safah tayi shiru tana share hawaye
Anty jiddah tayi shiru tana kallansu, yau Kam tasan ran yanbiyu yabaci, Bata taba ganinsu suna sa'insa Har hakaba
Suna wannan koke koken Haneefa tashigo itada Dr Bilal, sun danna door bell sunji shiru Dan haka kawai sai suka shigo
Haneefa ta kalli kowa tace mama lafiya? Meyake faruwa? Naganku duk a tsaye?
Anty jiddah tace sannunku da zuwa haneefa
Sajida ta karbi jakar hannun Bilal tace uncle sannunku da zuwa
Ya amsa Mata idonsa nakan Yan biyu dasuke Kuka, yakasa gane wacece Samah dinma acikin su
Yace anty sukuma wannan me aka musu?
Harara Samah ta wullo masa, tayi cikin daki da gudu tana Kuka
Anty jidda tace itada yar'uwata ne, fada sukai saboda Kai
Yace subhanallah
Ya kalli Safah, Garin Yaya Safah?
Kafin Safah ta bashi amsa anty jidda tace saboda munyi Mata magana Akan auren ku shine taketa Kuka Wai bataso, shine itama Safah din tace to itama zata fasa Nata auren tunda haka takeso
Yace kash🤦🏻♂Aida kunyi hakuri anty, karkuga laifinta laifinane daban sanar da itaba, kuma wallahi yanzu haka Dama niyyata idan na ajiye haneefa anan inwuce can gida inyi Mata bayani
Ya dubi Safah, yace kiyi hakuri kinji Safah, nasa kinsamu sabani da yar'uwarki Amma insha Allah komai zai wuce kinji?
Ta daga masa Kai
Yace nemi waje ki zauna, anty Dan Allah kuma ku zauna
Safah tatafi wajan shalele tazauna, shalele tafara Bata hakuri
Yadubi anty jidda yace anty zan Iya ganinta? 🙈
Tace Dr shiga mana
Babu kunya kuwa ya tsallake yarsa yatafi lallashi🤣🤣
Yana zuwa yaganta takifa Kanta a cinyarta tana Kuka
Ya zauna dab da ita, Har jikinsu na gogan juna
Ya sassauta murya yace kiyi hakuri, nasan namiki laifi, but sabanin fahimta ne yakawo Hakan, Amma wallahi Ina sonki
Samah tun lokacin Dana Dora idona akanki naji nakamu da matsanancin sonki, Amma kuma sai fada yahadamu a lokacin, na lura idan nasakar miki rainani zakiyi, nikuma babu abinda na tsana arayuwata irin raini, inada son girma Samah
Shiyasa zakiga Ina Miki wasu abubuwan Wanda basu da dadi, Nima ba'a son Raina nake Miki ba, dole ce tasa Samah
Dan Allah kada kice bazakice aure niba, zan Iya fuskantar damuwa Akan haka
Kalamansa sun ratsata, kuma ta gamsu Sosai, sai yanzu ne tagane dalilin sa naayi Mata wani abun
Yace kiyi hakuri ki Dena Kuka haka kinji? Kanki zaiyi Miki ciwo, karkiga ni doctor ne rikicewa zanyi nakasa baki Koda pracitamol ne🤣🤣
Hawaye suka sake zubo Mata, Yana ganin haka yasa hannu yadago ta, ya rungumeta a jikinsa
Yana bubbuga bayanta a hankali, kiyi hakuri kinji
Mutsu mutsun kwace Kanta tafara, bai hanataba yasake ta, dan Shima dole ce tasa yayi Hakan, taqiyin shiru, Shiyasa zai lallasheta ta wannan sigar, Amma Banda haka babu abinda zaisa yayi abinda zai daga masa hankali
Hannu tasa tana goge sauran hawayen Nata
Yace kokinga Dena wannan hawayen kokuma yanzun nan na shanyesu anan
Hararar wasa tayi masa, tace saikace wani maye
Yes ni mayanki ne Samah
Maganarsa tabata daria, tasake murmushi tadauki fillo agefe ta buga masa
Cikin daria yace yanzu shikkenan kin huce?
Ta gyada masa Kanta, yace toshknn kice kina sona Nima
Cikin shagwaba tace nide Dan Allah kafice.....
Yace to naji, kiyi murmushi saina tafi
Babu musu tayi masa murmushin, yace yawwa kokefa, saina kiraki zuwa anjima kinji?
Ta gyada masa kai, Shikuma yafuto daga Dakin
Yana futowa yaga duk sun zuba masa ido🤣🤣🤣
Qasa qasa ya kalli anty jiddah yace anty nikam na wuce
Daria tayi tace Dr yazaka tafi bakayi mana bayani ba? Tahuce ne?
Yace Wayyo anty ked sai anjima mana, yayi sauri yafice daga falon
Duk suka Saka daria
Samah kuwa haka kawai taji wani irin farin cikin ya mamaye ta, Kenan Dama tana Sansa kawai rashin fahimta ne yakawo haka, yanzu da wanne ido zata kalli anty da Safah?
Tab wallahi Gara tayi baccin qarya kawai🤣🤣🤣Aida kunya tafita falo
Anty jiddah tatashi tashiga Dakin nasu, taga Samah a kwance ta rufe
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 17