Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jin Gabansa yana faduwa, ahankali tace masa "Ina yini?"

Yasake kallanta yace "lafiya"

Juyawa tayi zata koma kitchen Sajida ma tabi bayanta tace uncle bye bye, yace ok my daughter

Yabi bayansu da kallo, Amma azahiri hips din Shalele yakafe da kallo, yana ganin yanda suke Juyawa

Anty jiddah na lura dashi, tace mekake ganine?

"no anty babu komai fa, wacece wannan din? "

Au Wai baka gane taba? Haneefa cefa yarinyar datake gyarama daki, harna taho da ita

Yace ok, yasake bin hanyar kitchen din da kallo

Anty jiddah tanaso ta qureshi Tace Wai kalau kuwa?

Oh Allah anty nace Miki babu komai, kawai de Naga tanada komai ne, like yar tsana haka, shiyasa nake kallanta

Haneef me kace? Yar tsana?yar ta wace yar tsana?

Murmushi yayi dimple dinsa yafuto yace Kinga anty ni sai wani lokacin ki gaida doctor idan Yazo, Daria tayi tace to zaiji, Shima dasauri yafice Daga gidan, anty jiddah Tace mataki na farko Kenan, zakaga yar tsana😃

********
Washe gari gida ya kaure da Qamshin girki, kowa yaci kwalliya Ana jiran Zuwan baqon Abba, sun jera komai a dining, sun dawo falo Suna zaune Dukansu

Tsayawar motar Abba sukaji, hakanne ya tabbatar musu da Cewa Abba Yazo shida abokin nasa
Da sallama suka shigo cikin falon, Dukansu suka maida hankalinsu wajan kofar falon

Lokaci daya Shalele ta miqe tsaye tace Uncle Bilal !!!

Cikin tsananin mamaki yace Haneefa

Dama Kaine baqon Abba?

Ai kafinma yayi magana tatafi da gudu ta rungume shi

Lokaci daya Anty jiddah Taji kishi, yauga yarinyar datake so qaninta ya Aure ta tana qirjin wani daban ba Haneef ba

Dasauri yafara janyeta Daga jikinsa gudun kada tasashi a wani Hali uba yayi abin kunya😃🤣
Wayarsa yadauko Daga Aljihun wandon jeans dinsa, yayi kira yace hello inspector zaku iya sakin matar nan yanzu

Daga hannunsa yayi sama, yace alhamdulillah, Allah nagode maka, Haneefa jeki dauko jakar ki, yau qafarki qafata








Anya kuwa anty jiddah zata yarda tabar Shalele?

Toshi kima Bilal me yarinya Anya yau kuwa zai iya barin Shalele tasake subuce masa?

Yaya makomar Haneef Shazali?


Muhadu Zuwa gobe idan Allah yabamu lokaci



Masu Cewa nayi 2pages kuyi hakuri, babu lokaci, kowacce mace Bata rasa ayukan gida, shiyasa yau nayi dayawa saboda ku😃😃😃Amma da tun lokacin da anty jiddah tajisu Suna sirri zan tsaya, saboda ku naqara masoyana, ku kasance tare Dani, Nima Ina sonku sosai





Sharhi, share, comment, Dan Allah 🙏🏻




Amnah El ✍🏻

💕SHALELAN BABA💕
(Romance)

Writing by Amnah El

25&26

Doctor Sulaiman yace a a doctor Bilal me kake nufi ne? Wai shin dama kunsan junane?

Anty jiddah tayi Ajiyar zuciya tace haba doctor, me kake nufi da qafarka qafarta? Ina ne zaka tafi da yata?

Doctor Bilal yayi Murmushi yakamo hannun Shalele suka zauna akujera, Suma su anty jiddah duk suka nemi waje Suka zauna
Ya kallesu da kyau yace Haneefa yata ce, dama nemanta nake ido rufe, bansameta ba, mahaifin ta tun kafin yarasu yace nadauketa yabani ita halak Malak, nazama uba agareta, sharrin matar ubane yasa Har tazo gidannan domin yi muku aiki, Amma wallahi da gatanta, daddynta yana raye🤣😃(su daddy manya, Kai Bilal ka shige su da son girma)

Ahankali anty jiddah tasaki boyaiyar Ajiyar zuciya, sai yanzu hankalinta ya kwanta da Bilal, Amma da Kam gaskiya qaninta take tayawa kishi

Tace doctor Haneefa ba aiki tazo yi gidan nanba, a gidan mu take aikin, nikuma na dauko ta na riqeta tamkar yata, yanzu doctor idan karabata da yaran nan Suma kansu ba zasuji dadi ba, sun riga da sun saba, doctor ayi hakuri abar mana ita mana

Kallan Shalele Bilal yayi, da gaske kinason zaman dasu?

Duk su Sajida suka bita da kallo

Ahankali ta Daga masa kanta alamar eh tanaso

Yasake Cewa kina ganin nan din babu damuwa Ko?

Babu damuwa uncle, mama tana sona sosai, Abba ma haka, sun riqeni amana Kamar Yanda kayi

To alhamdulillah Tunda de yanzu nasan gidan da kike, to hankali na zaifi kwanciya

Ya kalli su anty jiddah, yanzu de matar aboki kin qwace wa uba yarsa karfi da yaji

A a doctor to yanzu saida muka saba zakace qafarka qafarta fisabilillah
Yanzu de Tunda nagama jin matsayar zance, babban baqon mu Kuma baban yata, yatashi abinci yana jiransa

Duk falon sukai Daria

Gaba dayansu suka rankaya Zuwa dinning, anacin abinci kowa nata fara'ah, wannan ya tsokani wannan, wannan ma haka, Har suka kammala
Suka dawo falon suka zauna anata kallo, Amma Shalele tana gefen Bilal Suna fira qasa qasa, cikin nutsuwa

Ya kalleta yace yarinyar uncle duk kin canja kin girma, ai Gara Dana ganki Dan inje gida infara Tara kudin da zanyi bikin yata

Cikin kunya ta rufe ido, Kai uncle Dan Allah ni bawani Aure da za'a min yanzu

Aikuwa Aure dole yarinya
Kina nufin haka zan zuba Miki ido Ina Kallan ki?

(tofa Kamar shidin yayi🤔😃) To garama ki shirya, Abdallah fa yana wajena

Cikin rashin fahimta tace Abdallah...

To yar qauye Aududu

Cikeda murna tace laaaaa uncle Dan Allah? Yaya akai inna tabaka shi?

Nan take Bilal yabata labarin komai, Aikuwa ta dinga Daria, itama tabashi labarin Yanda sukai da ladidi tijara Bayan sun taho

Yace ai Ko yaushe Naga wannan matar, saina nuna Nima Dan tijara ne, ba'a taba yata a zauna lafiya

Qasa qasa yayi da murya sosai cikin rada yace mata aide da gaske nan din babu wata matsala Ko? (tab wallahi Bilal idan anty jiddah tajika nide ba ruwana🤭🤣)

Shalele tayi Murmushi tace eh uncle babu komai fa wallahi, Ina anty Sady da Hajiya?

Duk Suna nan kalau, zance kina gaishe su, idan nasamu lokaci ma ai zanzo na daukeki muje

Doctor Sulaiman yace wato de yanzu baqon namu ya zama Iya baqon Haneefa ita kadai

Daria Bilal yayi yace to abokina tuba nake, sannan yajuyo sukaci gaba da firar Dukansu

Dazai tafi gida, Har wajan mota suka rakashi, yashiga motarsa yadauko ATM dinsa guda daya, yace wa Shalele ki riqe wannan ATM din, Ko zaki buqaci kudi aciki, ni inada wani, sannan ga kati na nan, duk numbers Dina Suna jiki, idan wata matsalar ta tashi, zaki Iya nemana, pin din ATM din qarshan number tane, kingane?

Eh uncle nagane, nagode sosai, Dan Allah ka gaisheda hajiya sosai, da Aududu, da anty Sady

Karki damu my daughter zasuji, Saida taga fitar sa, sannan ta juya cikin gidan itama, ayaz ne kawai Afalo, anty jiddah tana daki wajan Abba, sai kawai itama tatafi dakinsu ta adana katin da ATM din cikin jakar kayanta, a gado ta zabe kusa da Sajida Suka fara maida baccin gajiya, kasancewar sunsha aikin tarbar baqon abbansu

********
Juyi yayi akan gadon nasa, yasake Jan blanket dinsa fari qal qal dashi, akaci gaba da bacci
Azahiri ma maganar sa Ahankali yakeyi Kamar mace, yanzun ma hakance ta kasance dashi cikin baccin, ahankali yabude bakinsa yace "karki tafi"

Yaci gaba da baccin kadan, alamar mafarki yakeyi, da aka jima ma cikin sigar shagwaba yasake Cewa "nace karki tafi fa"

Ahankali yasaka hannu yaja Fillo din dake gefensa ya rungume shi aqirjinsa sosai yace "Stay with me please"

Yaci gaba da baccin sa cikin kwanciyar hankali, wayoyinsa guda uku dake ajiye akan bedside drawer ne daya Daga ciki ta dauki qara

Runtse idanunsa yayi, ahankali yabude idon nasa, lokaci daya yaji wani irin bacin rai, meyasa za'a kirashi akatse masa mafarkin sa? Waima da meyasa ya manta ne Bai kashe suba?

Yanajin wayar na ringing harta katse be Iya dauka ba, Saida aka sake kira akaro na biyu ne sannan ya meqa hannu yadaga, Ajmal ya akayi?

Kai Sarkin nawa, kazauna Kanata kwalliya kaiba budurwa ba, already anyi sadaka dakai, kaqi futowa office da wuri, mutane Suna nemanka wayoyinka duka a kashe, shine wani daga ciki yakirani yace idan inada wani layin Naka infadama Suna can Suna jiranka akan meeting din dazakuyi

Ajmal, kafada musu su dage meeting dinnan, banida lafiya bazan Iya fita ko'inaba

Dasauri Ajmal yace what? Ganinan Zuwa

Shima Haneef anasa bangaren ajiye wayar yayi yazuba wa saman dakin nasa ido, bagarama rashin lafiya ba akan wannan tsinannan tunanin dayake🤦🏻‍♂

Tun shekaran jiya yake Fama da tunanin yarinyar Nan, shi Kam wannan yarinyar inaga masifa take neman zame masa

Tashi yayi yafuto falo da kayan motsa jiki ajikinsa, Kamar kullum yauma Saida ya ajiye robar ruwa agefensa me sanyi, sannan yafara motsa jikin

Yayi Nisa da motsa jikin kawai ya tuno idanun nan nata, zazzaqar muryarta "Ina yini"?

Ya tuna gaisuwar datayi masa, lokaci daya jikinsa yasaki, gudun dayake yi yadena, ya sunkuya yakama gwiwoyinsa da hannayen sa, Kamar me ruku'u yana maida numfashi

Awannan halin Yazo ya riskeshi, dasauri Yazo yadago shi, subhanallah abokina Ko ciwon cikinka ne yatashi? Shazali shiyasa nace kadena durawa kanka wannan maganin, shikkenan Kai dakaji yar sha'awa saikaje kakama magani kasha, sannu...

Yaga alama idan Bai dakatar da wannan gayen ba, bazai daina zubaba, shi Ko gajiya bayayi da magana, qwace jikinsa yayi yace Dan Allah Malam cikani,yamiqe yadauki ruwansa ya kwankwada

Cikin mamaki Ajmal ya kalleshi, kaiiii, au Wai dama kalau kake shine kasa nabaro aiki na nataho wajan ka?

Bece dashi komai ba, yayi wajan kujerun sa yazauna, ya Dora kansa akan kujerar

Ajmal yace abokina what happen?

Bude ido yayi ya kalleshi, Ajmal meyasa me idan kaga wasu mutanan sai kaji gabanka yana faduwa haka?

Ajmal yace mutane Kuma? Kamar suwa?

"Ina nufin Kamar mace haka "

Zaro ido yayi😳mace kagani gabanka yafadi?

Ahankali yace" yes "ba sau dayaba, duk ganin Dana mata

Um tab, gaskiya abokina nide a Iya sanina, alamu ne na kamuwa da so

What? So? sofa kace Ajmal, ni inso wannan yarinyar? Yarinyar Dana haife.... Saikuma yayi Shiru yazari wayar Ajmal dake gefe yashiga danne danne

Tsayawa yayi ya karanta abinda yaduba, yayi cilli da wayar kan kujerar dasuke, yace "shirman banza"

Ajmal yadauki wayarsa yaga abinda shazali yaduba, ya kwashe da Daria, au baka yarda da maganar Dana fadama ba Saida ka duba a Google?
Yasake kwashe wa da Daria yace Allah sarki, ashe wannan ne rashin lafiyar dakake, shiyasa yau kaki Zuwa office, abokina wacece wannan yarinyar? Wacce me sa'ar ce? Daga fara kamuwa da sonta anqi Zuwa office Tokuma idan aka aureta Yaya za'ai Kenan? 🤣😂😃aikin za'a ajiye duka?

Ajmal kadena Daria mana, wannan abin fa ba abin Daria bane, da gaske banida lafiya, kullum naganta sai gabana ya fadi, kaga wannan ma ai babbar jinya ce, ni babu wani so danake wa kowa, Daga Kai Har Yan Google din duk qaryar banza ce, aikin banza aikin wofi 🤣

Me Ajmal zaiyi inba Daria ba, yace gaskiya ne abokina, wanan Kam babbar jinya ce

Tsaki Haneef yasaki yatashi yashige dakinsa, Daga nan yayi toilet domin watsa ruwa

********
Suna zaune akan gadon su, da daddare Suna fira, Sajida ta dubeta tace Wai kuwa sister Dan Allah jiya da uncle Yazo Yaya kikaji?

Ajiyar zuciya ta sauke tadauki Fillo ta Dora a cinyarta, ai wallahi bakiji Yanda naji dadi ba, Kamar karna bar falon, saide Kuma ba dama

Um ai sister Haneefa shiyasa danaji ance Yazo nace kizo muje kikaqi Zuwa

Ke gabana nefa yaje faduwa, Kuma ni idan Ina ganinsa sai Inga yamin kwarjini nakasa komai, Ko kallansa kasawa nake wallahi, ninarasa wannan wanne irin so ne

Lalle sis, wanne irin kwarjini? To tsaya anan yana Miki kwarjini wadancen yanmatan su kwace Miki shi(karfin Hali irin ya zama natan nan🤣🤣)

Toya zanyi sis Sajida, shi din wani irin mutum ne na daban, ga aji, jiya fa Wai nace Ina yini, akace min "lafiya" shikkenan fa bass
Bakiji Yanda yasake birgeni ba, Allah Kasa idan akwai Aure atsakanina dashi Toya tabbatar mana da alkhairi, idan Kuma babu Allah kaciremin Sansa araina
Dasauri Sajida tace akwai ma insha Allah sis, babu wani family dazaki tafi, kina nan a shazali's family insha Allah
sukasa Daria gaba dayansu

********
Yashirya kansa cikin qananun kaya, sai zuba Qamshi yake
Momy da daddy Suna zaune, ya tsugunna Har qasa ya gaishe su, ya kalli daddy yace daddy dama.. I want talk with you

Inajin ka Haneefa

Am daddy gyaran dakin da yaran nan sukemin bayamin, kwata Kwata Kamar ma basa taba wajan wallahi, shine nakeso asamomin wasu masu aikin please daddy

Murmushi yayi, yau shida kansa yace Alhaji shazali Kenan 🤣

Dasauri Haneef ya Kalle shi

Shima daddy yace yes, Alhaji shazali, bahaka suke fadama ba? Wato Kai bakada aiki sai akawo ma yarinya me aiki, Washe gari ka Koreta, shazali Anya kuwa? Anya zaka Iya riqon Aure kuwa?

Kansa ya sunkuyar qasa bece komai ba

Daddy yaci gaba, toka bace kabani waje, babu wata yarinya da za'a sake kawoma, aiba Haifa ta kayi ba, sannan munyi waya da Alhaji Sadiq yace bakaje kaga yar tasaba tsawon wannan lokacin, ba shawara nake bakaba, umarni nake baka, yanzu basai anjima ba kanemi Ajmal kuje ku ganta, zanyiwa babanta waya nasanar dashi

Gobe Kuma kakoma wajan dayar itama ka ganta

Ajiyar zuciya yasauke, baicewa iyayen masa uffan ba, yatashi yafice Daga falon idanunsa jajir, shifa Yama manta da batun wadannan yaran, ashe su daddy Har yanzu abin yana ransu

Wayar Ajmal ya kira, yace masa gashinan Zuwa
Ajikin motarsa ya tsaya yana jiransa, Yaji massage yashigo wayarsa, yana dubawa yaga daddy ne ya turo masa da address gidan

Tsaki yasaki Bayan yagama karanta wa, Daga gefensa yaji ance Yaya gashi Wai inji momy, kakai mata

Kallanta yayi, yaga wata Leda ahannunta , baisaniba Samah dince Ko Safah, Harara yabi yarinyar dashi, yace ajiye anan

Ta ajiye ledar Agefen sa ta juya ciki

Ajmal nazuwa ya miqa masa wayarsa, yace kakaimu wannan address Ajmal, bazan Iya driving ba, daddy ya matsa akan naje Naga yaran nan, wallahi banasan maganar auren nan

Kafadarsa ya Bubbuga kayi hakuri abokina, insha Allah Allah zai kawo mafita

Daukar ledar dake qasa Ajmal yayi, suka shiga motar sukabar gidan

Aharabar gidan suka tsaya, babban gidane na gaske, da alama itama mahaifinta yana dashi sosai
Wani ne Yazo yayi musu iso, Zuwa dakin baqi
Dakin yayi kyau, ga sanyin esi dayake tashi

Ma'aikata ne suka fara shigowa da girke girke, Kala Kala, Saida suka ajiye girki yakai kusan Kala takwas
Sannan aka ajiye musu lemuka

Ajmal yayi Shiru yana Kallan ikon Allah

Qamshin turaren dasukaji ya taso ne ya tabbatar musu da Cewa tazo

Kallan su tayi tace hi

Suka Daga Kai Suna kallanta, baqa ce ba fara ba, saide mayukan datake shafawa yasa tadan Washe, babbar mace ce sosai, shi kansa da kadan zai girme ta

Mayafin jikinta Dan qarami ne, saita yafashi Iya kafadarta daya
Zama tayi a kujerar datake fuskantar su tace Sannunku fa

Shi dakansa ya amsa yace "yawwa"

Tace am Haneef Shazali Ko?

Yace "yeah I am"

Munyi magana da dad Dina, yacemin za'a turo min Kai in ganka kokamin, well nide awajena banda matsala, Tunda naganka yanzu naji kayimin, zaka Iya Zuwa kasanar a gida, mun dede ta kanmu, kawai ayi maganar Aure

Lumshe idanunsa yayi, shi aka turo mata tagani Ko yamata? Hmm

Ahankali yace ba damu

Ta kalli abincin gabansu, meyasa bakuci komai ba?

Ajmal daya Dade da mamakiin wannan uban girki yace, to ranki yadade wannan abubuwan ai sunyi yawa, ruwa ma kawai ya wadatar, saide fa kiyi hakuri kinsan manyan mutane basu cika cin abinci ba awajajan da aka gayyacesu, musanman ma shi angon naki

Murmushi tayi, to aini aganina wannan ma yayi kadan, a kullum Ana girka min abinci fiye da ashirin arana

Ajmal yace Kuma duk ke kadai kikeci? 😳😳

No zanci wanda zan Iya cine, sauran na zubar dashi

Shazali ya kalleta, baice komai ba

Ajmal ya miqa mata ledar dasuka zo da ita, yace to ga wannan amarya, kyauta ce Daga ango

Ledar ta karba, ta bude ta, turare ne aciki, guda uku, masu tsada, aqalla Ko wanne daya acikinsu zaikai dubu hamsin

Yatsina fuska tayi, tace Haneef wannan wanne irin turare ne? Ai sunyi araha dayawa Kamar fiyawota🤣😃🤣
Masu tsada nake shafawa, na dubu Dari biyu, Suma duk wata saina sake wasu koda kuwa basu qare ba
Amma babu damuwa, ngd, kuyi hakuri ban fada muku Sunana ba, ni Sunana Hairat Alhaji Sadiq dala, Haneef abinda nakesan fadama shine, arana Ana girkamin abinci kusan ashirin

Ina zuwa gyaran gashi duk Bayan kwana biyu, Amma Tunda zan auri Haneef Shazali zaka dinga kaini wajan gyaran gashi kullum 😳🤣

Duk wata babana yana kaini yawon bude ido qasashen qetare, Bana girki, zaka samomin ma'aikata Kamar Yanda kagani a gidan mu
Bafa anan abin yatsaya ba🙆🏻‍♂duk wata dubu dari tana shiga account Dina Daga bankin babana wannan ta Zuwa shan ice cream ce

Kai meyasa ma zan Bata lokaci na wajan yima bayani, nasan banda matsala dakai inde wajan kudi ne, duk da mom Dina tana Cewa Yan kasuwa su a kullum burinsu shine Yanda zasu samu riba, basu yarda da rashin riba akan kasuwanci ba

Huci Haneef yafara 🤣😃

Ajmal yana Kallan yanayin sa aransa yace wannan tun kafin ya wankawa yar mutane mari, babanta yadauki mataki akanmu Gara najashi mutafi

Cikin sauri yace to hajiya Hairat, ga kati nan me dauke da numbers din angon naki, zaki Iya kiransa idan kinsamu time, mu zamu wuce, sai Kuma next time idan mundawo

Tace ok, Bari na rakaku

A a aike gimbiya ce, ki zauna ki huta Mungo de

Haneef baiko kalli inda takeba suka fice

Suna shiga mota, Yadubi Ajmal, meyasa kace zamu tafi baka Bari nayi mata shegen duka ba 🤣😃
Meyasa zaka hanani?

A a Haneef nifa dama Tunda Naga yanayin ka nasan idan na qyale ka, to bazamu Rabu da yarinyar Nan lafiya ba, shiyasa nace mutafi

Huci yaci gaba da yi, matsiyaciya harni zata kalla tace Wai anturo mata ni taga Ko nayi mata? Talla nake dakaina?

Ajmal yayi Daria, au Kai wannan ne damuwar ka? To maganar data fadawa Yan kasuwa fa? Bata duba dukanmu Yan kasuwar neba, yaci gaba da Daria

Haneef yayi tsaki, Wai gyaran gashi duk Bayan kwana daya Kai kaji wani bala'i

Ajmal ya qara da dubu dari tashan ice cream 🤣😃

Tsaki kawai Haneef yake ja, turaren jikinta Ko nawa baikai tsadaba, shine zatace wanda aka kawo mata yayi araha dayawa, ni batasan ma bada kudi na nasiya mataba

Ajmal yaqara tunzurashi, araha Kamar fiyawota, haka tace
, yanzu Kuma sai goben idan Allah yakaimu idan munje wajan dayar saimuji, ita Kuma menene nata qa'idojin 🤣🤣

Haneef de Haushi ya cika shi, yace no bakwa gobe ba, saide jibi Ko gata, ai babu wajan wadda zan sake Zuwa gobe, saina huce da wannan baqin cikin

Ajmal yace to shknn, babu damuwa Allah yakaimu

********

Washe gari yana zaune a qayataccen office dinsa, takardun dasukai meeting akansu yake dubawa, yaduba yaduba yakasa fahimtar komai
Ya tattara su ya ajiye agefe, yazuba tagumi
Meyasa ne Tunda yaga yarinyar Nan tunanin ta yahanashi sakat?
Shide yasan baya sonta, to meyasa zaiyi tunanin ta?
Yasan Ajmal kawai fada yayi, Amma shi yasan babu wata yarinya dayake so
Kawai de yanaji aransa yanaso yasata agaba yanata kallanta, kawai tana birge shi ne yarinyar gata yar qarama Amma tanada abubuwan hutawa masha Allah, shiyasa yake ganinta Kamar yar tsana
Toshi de yanzu idan yakoma gidan anty jiddah yau, dole zata masa wata fassara, dama rannan Daga Dan Kallan yarinyar tafara Watso masa questions

Murmushi yayi lokaci daya yace yessss, wayarsa yadauka yakira Ajmal
Hello abokina yaushe zakaje wajan Zance ne?

Ajmal yace Anya kuwa zanje Haneef?

Mezai Hana saina rakaka ma idan zakaje 🤣

Ajmal yace, Haneef Anya kuwa ba wani Abu kake qullamin ba? 😃kaine yau zaka ce zaka rakani wajan yarka zance?

No serious fa abokina da gaske nake, Naga Nima jiya kana yin aiyukan ka na katse ma nace kazo ka rakani, shiyasa Nima yau zan rakaka, idan zakaje Nina gama aikin danake, kawai ka futo mutafi

Ajmal Bai kawo komai aransa ba yace to shikkenan, ganinan Zuwa, zanje Naga my sajeey

(besan Shima yau ta manya akayi masa ba 🤣🤣)

Saida Yazo kamfnin su Haneef sannan sukabar motar Haneef awajan saminu, yace saminu zaka Iya wucewa gida, akwai inda zamu
Saminu yace to yallabai asauka lafiya
Suka shiga motar Ajmal suka tafi
Saminu yabi Bayan motar su da kallo
Yarasa Ina su yallabai suke Zuwa su kadai kwana biyu, kokuma yakusa samo musu uwargida ne? 🤣😃

Ajmal na driving Amma Haneef gani yake Kamar bayasan tuqa motar, haka de yadan ne komai aransa Har suka je gidan anty jiddah

Nocking sukayi, Amma Shiru ba'a zo anbude ba

Anty jiddah yau tana kitchen da kanta, sukuma su Shalele Suna daki, Sajida tace Kamar fa Nocking nakeji

Shalele tace Bari naje nabude, may be wata ce tazo

Riga da sket ne ajikinta English wears, takama gashin kanta tayi parking, jelar gashin nata tanata bin bayanta
Tatashi ta nufi kofar falon, Zuciyar ta daya ta bude
Sai ganin sa tayi agabanta, Zuciyar ta ta tsinke, Shima anasa bangaren ido yazuba mata yakasa dauke wa

Ajmal ya kalleta, wacece wannan Kuma?

Cikin in.. Ina tace sannunku da Zuwa, tajuyo cikin falon da sauri
Idanunsa Bai tsaya ko'inaba sai akan dogon gashinta

"masha Allah, me irin wannan gashin itace zata ce akaita wajan gyaran gashi kullum aciki umarni akaita "

Cikin daki tashige da sauri, ta Cewa Sajida ke wallahi su uncle Haneef ne, shida wani

Sajida tace haba? Kode Yaya Ajmal ne? Bari naje nagani

Falon ta futo, tana ganinsu tatafi da gudu tafada jikin Haneef, uncle sannunku da Zuwa

Yace yawwa my daughter, Ina anty takene? Kiramana ita mana, tace to, sannan ta kalli Ajmal tace Yaya sannu da Zuwa

Yawwa my sajeey

Yana ganin tafiyar ta, yace gaskiya Haneef bakamin kara wallahi
Agabana yarinyar Nan sai rungumarka take😃

Ya kalleshi, Ajmal mekake nufi? Yarinyar nanfa muharrama tace

To Dan tana muharramarka saikayi ta rungume ta? Ina zaune agefe

Haneef yace shikkenan Ajmal kaima rungume ta, rungume ta inka isa, wallahi Daga ranar bakai ba ita

Kawar dakai kawai Ajmal yayi, sai can Kuma yace kai abokina wacece wannan yarinyar data bude mana kofa?

Yana sane Sarai yace a'ina?

A kofa mana yanzu, wata yar fara me ido irinna Aishwarya

Tsaki Haneef yaja, yanzu Kai harka zuba mata ido kagane wanne irin ido ne da ita?
To yarinyar datake min aiki ce kwanaki

OK Wai me hijabi?

Cikin gatse yace a a

Ajmal yace kome gajeren wando? 😳

Shazali cikin fishi yace a a me uwar gajeren wando😃

Ajmal yasake Kallan abokin nasa, qarara yaga kishi a idonsa, toko itace wadda yace masa yanajin faduwar gaban? Wato kawai Daga yabon yarinya Har kishi yakamashi, shikuma Kenan yamutu shida ya rungume masa budurwa? 🤣kenan da shine hauka zaiyi

Shiru sukai ganin anty jiddah tazo, aranta tace dama nasan zaka dawo yaro 🤣
Gaisawa sukai Ajmal sai sunkuyar dakai yake, waishi me suruka
Su Shalele suka futo itada Sajida suka ajiye musu ruwa da lemo, Har qasa ta tsugunna ta gaida su

Sajida ta nemi waje ta zauna, ita Kam hanyar daki ta nufa

Anty jiddah Tace Ina zaki Kuma? Waike bakya gajiya da zaman daki ne?

Baisan dalili ba cikin ransa yace Alhmdlh, jin furucin anty jiddah

Dawowa tayi ta zauna tayi Shiru, hankalinta yana kan TV
Qasa qasa yake kallanta, wallahi sai yau yasake tabbatar wa kansa Cewa yarinyar Nan kama take da yar tsana, wallahi Har gashin 🤣😃🤣

Garin satar kallanta anty jiddah ta kamashi, dasauri yace am anty dama na rako Ajmal ne, shine nace Bari Nima nazo naganki

Aikuwa Gara haka, nasan badan Shiba aida bazaka zoba 🤣

Gudun kada tace masa meyake kallo irin rannan, tasa yaji kunya saiyayi fuska yace anty zamu wuce, sai wani lokacin

Tace to Allah yakiyaye qanina, ka gaida momy nah

Sajida de Saida tabi bayansu suka Dan zanta da Ajmal sannan tadawo gida

Suna tafiya amota Ajmal na kallansa sai fara'ah yake shi kadai, lalle akwai ayar tambaya akan abokinsa

Shikuwa Haneef tunani yake Yaya za'ai yadinga zarya a gidan anty jiddah? Wannan ai saita dauka ma son yarinyar yake, Bayan Kuma shi yasan ba haka bane 🤣
Kawai de yanaso yana ganin yarinyar ne, sha'awa take bashi wallahi Kamar yar baby 🤣
Gaskiya dole ya nemi mafita

Ajmal na sauke shi a gida, Bai wuce part dinsa ba, part din momy yaje, yanaso yayi Mata maganar Amma saiya kasa
Zama yayi suka gaisa sannan tace yaushe zakaje wajan yar qawar tawa ne? Yace gobe zamuje insha

Please Login or Register in order to submit comment