Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ajiyar zuciya Kallanta yayi, "kitashi kiyi alwaya ayi sallah ko" Daga masa Kai tayi, tatashi tashige toilet din Ga mamakinsa saiya tsinci kansa da jiranta, haka yatsaya Saida tafuto sannan yajasu sallar Saida suka Rama duk sallolin dake kansu sannan yaita karanta musu addu'oi suka shafa saika rantse wasu sabin amare ne🤣 Dubanta yayi yasaki Dan qaramin murmushi,haka kawai yakejin wani irin nishadi na shigarsa, Anya kuwa Ajmal ba gaskiya yafada masa ba?gaba daya ko tunanin gida ma bayayi tunda yaganshi tareda ita Ajiyar zuciya yasauke kinajin yunwa ko? Cikin sigar shagwaba tace eh uncle inaji Wani yarrr yaji ajikinsa, Allah yaso sallah suka idar, Toda ansamu matsala gaskiya🤣 Abincin yadauko musu yasaka musu agaba, shinkafa ce wadda taji kori, da gasashiyar kaza aciki Yakalleta cikin maganarsa ta sigar rada yace Mata taso kici Abincin Aikuwa hajiya shalele babu musu ta matso tasaka hannu tafara cin abincinta (hoo yunwa ba dadi 🤣🤣 ) Tagumi yayi Yana Kallanta, shi baifara ciba, ta kalleshi uncle Kai bakajin yunwa ne? Cikin nishadi yace kedin yunwa kikeji? Emana sosaima No ban yarda kinajin yunwaba Ta kalleshi meyasa? Da idanunsa ya nuna Mata Abincin datakeci Sannan yace inda kinajin yunwa dasauri Zakici ai Murmushi tayi, tace haka nakeci ai Innalillah... Kalli murmushinta, yarinyar nan kada takashewa momy ni🤣 Matsowa yayi dab da ita, Har gabanta yadan fadi, jikinsa Yana gugar nata, atsorace ta kalleshi Shima yaga Hakan kawai saiya share, yasaka hannunsa acikin Abincin ya karyo kazar babba yakai Mata bakinta Yanda ya matso tan Kamar zaiyi Mata kiss, ahankali yace "eat" Jikinta yayi sanyi, kasala ta Kamata, ta kalleshi, Shima ya Kalle ta yace ci mana Ahankali ta Bude bakinta yasaka Mata naman takaryi kadan taci Yanda takecin abincinma kadai abin kallo ne, yazubawa pink lips dinta ido, komai nata me kyaune Haka yayita dura Mata Abincin, hartace uncle na qoshi Cikin sanyin jiki yace da gaske? Ta daga masa Kai OK jekishiga kiyi wanka ki kwanta kiyi bacci Tace to Saida yaga shigarta toilet din sannan yasaki ajiyar zuciya, meyake damunkane shazali? Wadannan abubuwan dayakeji na menene? Karfa maganar Ajmal ta tabbata, Innalillah... How? Wannan qaramar yarinyar? Sannan ma yar aiki, yar aikinsa Idan yagama tabbatar wa kansa gaskiya, tofa da an dafka abin kunya🤣😃Aida kunya ma yatunkari Ajmal da wannan maganar bare Kuma su momy, Kai Allah yasa Bahaka bane Bama (to zamu gani de🤣) Kadan yaci Abincin, yasake tafiya duniyar tunani, daga karshe ma saiya fice daga Dakin domin yabarta tashirya Ita kuwa Tana Gama wanka taga babu towel, dube dube tafara sai can taga wata rigar fara, Jikinta Mai laushi, tadauka tasaka, rigar dukanta iyakarta gwiwarta, hakade ta Kalli kanta, tasake kallan kanta, Anya kuwa zata Iya fita ahaka? Kai bazata iyaba Dan kwalin datai rolling na rigarta tadauka tabazashi akanta sannan tafuto cikin Sanda Tana futowama taga baya nan, tasaki ajiyar zuciya taje takashe wutar Dakin ta kwanta Akan gadon, tashige cikin bargo tayi adduah tarufe idonta Saida yadau lokaci sannan yadawo Dakin, Yana shigowa yaga duhu, kunna wutar yayi yahangota ta makure akarshan gadon,Koda wanne kayan ta kwanta? Basu taho da kayantaba ko daya murmushi yayi yasake kashe Mata wutar sannan Shima yashiga toilet yayi wankansa cikin nutsuwa, jallabiya yasaka yafuto, yadauki fillon dake gefensu yasaka shi atsakaninsu 🤣sannan ya kwanta batare daya rufaba Cikin dare yaji sanyi, yaja bargon yaci gaba da baccinsa, itama tana bacci taji anjanye bargon, dasauri ta matso tasake shigewa ciki Da asuba, shine yafara farkawa, ahankali ya Bude idonsa yaganta, sai yanzuma yatuna tare suke, fillon dayasa atsakaninsu Yana nan, tana kwance tana baccinta, gashin kanta duk ya barbaje Sunkuyawa yayi zaiyi kissing dinta🙆🏻🙈saiya fasa, yasaka hannu yashafa gashin nata ahankali sannan yashige toilet yadauro alwala Yazo gabanta yasaka hannu yana bubbuga fillon nata "ke" Yaji shiru Yasake cewa "qawar sajida🤣" still yaji shiru Kawai saiya share ta yatada sallah, yasan baccin gajiya take saboda Bata sababa Saida ya idar sannan yakoma wajanta ya sunkuyo dab da ita yace " Haneef" (zakayi bayanine🤣) Yasake cewa "Haneefa" Juyi tayi hadeda hamma tabude idonta, sannan ta karanta adduah tatashi daga bacci Kallansa tayi da idanunta dasuka cika da bacci, batace masa komaiba Shima ya kalleta yace ki tashi kiyi sallah fa Cikin shagwaba tace uncle Allah ni baccin be isheniba Tarufe idonta Innalillah... Sufa mata matsalarsu kenan🤣😃 Yace am Kinga, asuba tayi, yakamata kitashi, kinji Taja bargon harkanta tace um um Toshi yanzu yazai Mata? Bargon ya janye, yasaka hannu yadago kafadarta, yazaunar da ita Dab da kunnanta yace tashi kiyi sallah kinji? Anjima za'a fara taron Daga masa Kai tayi, shikuma yafuce daga Dakin dasauri Jikinta ta kallah, tashafa Jikinta, aranta yace um uncle baimin komaiba 😃Dama anty zeey tace bazaimin komaiba Tatashi tayi alwala tayi sallah sannan tayi wanka tasaka kayan ta na jiya Saida Gari yayi haske sannan yadawo Dakin da Kaya ahannunsa, yace gashi, kije da wannan wajan zainab tana jiranki Saida ta gaisheshi sannan takarbi kayan tafita, tana zuwa daki wajan anty zeey suka gaaisa, ta kalleta tace dafatan lafiya ko? Murmushi tayi tace babu komai anty, wallahi baimin komaiba Tabawa anty zeeey Daria yanda tayi maganr 😁, Sosai zaka Fahimci da gaske take Shiryawa sukai anan, anty zeey akwai gayu lokaci daya ta sauyawa shalele kamanni Tayi kyau Sosai acikin doguwar Riga, light blue, harda jakarsu da takalminsu, takalmin yayi tsini dayawa, tana sakawa tace gaskiya bazan Iya tafiya da wannan takalmin ba Kiyi hakuri haneefa haka Zaki zaka, shine yasiyo Miki su, yazakiyi Haka tasa takalmin tana turo baki gaba, suka zauna suna fira kadan kadan Sai wajan karfe Tara sannan Abbas yashigo Dakin Shima yasaka suit baqa yayi kyau, yace ku tashi mutafi Shalele ta gaidashi ya amsa Mata cikeda fara'ah, ahankali shalele take tafiya anty zeey ta kamata, Yana harabar hotel din yajuya baya Yana waya sai Daria yake, tana hangoshi tace kodawa yake waya? Juyowa yayi yaga sun futo, cak ya tsaida idanunsa akanta, tayi masa kyau Sosai, tafiyarta ya kallah yasan Dama daqyar zata Iya tafiya dashi Ahankali Shima yataho Yana fuskantarsu, Saida sukazo dab dashi sannan yayi sallama awayar yace to anty sai anjima Anan tagane da anty jidda yake magana Babu kunya yasa hannu yakamo hannunta, Abbas ya kalleshi yayi murmushi Kai shazali Dan duniyane wallahi Yakalleshi, shazali ni baka fadamin sunan babyn takaba, yasan da biyu yayi masa wannan maganar saboda kowa yasan cewa shazali bayasan qaramar yarinya Shiyasa Wai baka fadamin sunan babynka ba🤣😃 Kallansa yayi yace "baby haneefa" Kafahimta? Cikin Daria yace ai dole na fahimta🤣 Hannunta Yana cikin nasa suka qarasa cikin Mota, zeey na gaba abbas na driving Itadashi Kuma Abaya, yaqi sakin hannun nata, ahankali yake murzawa, laushi hannun nata kamar Bata aikin komai shiyasa yaqi saki Ita kuwa duk wani iri takeji, idan Yana murzawa saitaji wani iri haka ajikinta, ahankali tafara zare hannunta, Amma saiya sake riqewa Yajuyo ya kalleta cikin rada yace Mata why? Kasa tayi da idonta,batace masa komaiba, Shima saiya kawar da kansa zuwa kallan titi Amma Bai saki hannun nataba, Har motarsu ta tsaya Su zeey suka fita, mutane damqam a wajan, Yan Nigeria dakuma sauran qasashe turawa, Kallanta yayi yace Mata "wait" Dakatawar tayi kuwa yayi sauri yafita ya zagaya yabude Mata motar dakansa, abinda yayi ba qaramin birge mutanan wajan yayi ba, ita kanta zeey Saida tace gaskiya yarinyar nan tayi Dace da samun shazali Kafarta daya tasakko sannan tafuto gaba daya, masu camera kuwa me zasuyi dauka, Yan jarida da sauran gidan TV kasancewar ansanshi bane mu'amala baane da Mata, duk taron dazaai shi kadai yake zuwa, Amma abin mamaki yau gashi ga budurwa mace sai Hakan ya birgesu Hannunsa ya miqa Mata, Saida ta kalleshi sannan tadora nata Akan nasa, yariqeta suna tafiya ahankali Sun kusa shiga wajan takalmin Kafarta yagurde kadan, 🤣🤣Allah yasosu hankalin mutane ba Akan takalminta yake ba😅, a kansu yake Cikin sauri ya saketa ya tsugunna a gabanta, yakama Kafarta ta Yana dubawa kamar me neman wani Abu, yadago kansa yace Mata sorry, sannan yakai kafar bakinsa yasakar Mata wani zazzafan kiss Zeey de yau tana ganin ikon Allah, takalli shalele ta kalli shazali, gaba daya sun birgeta🤣 Yan jaridafa ansamu abinda akeso, tun lokacin daya tsugunna suka fara daukarsu photo Shikuwa ko ajikinsa Bai dauki Hakan dakomaiba Kamata yayi suka shiga wajan, wajan yatsaru matuka, abinci nan agaban kowa da ruwa da lemuka Kamar yanda suka fada haka aka tsara kowanne mutum bibiyu Cikin kwanciyar hankali aka fara Kiran sunayen mutane suna gabatar da kansu, Har akazo kansu suma suka fadi nasu😍 Sannan aka fara taron, Wanda suka dauki tsawon awa uku Ana wayarwa damutane Kai wajan habbaka harkar kasuwancinsu Kallanta yayi, baya ganin fukarta Sosai, saboda gashin ta daya Dan saqqo yarufe Mata fuska Yace kinsan me? Kallansa tayi tace a a uncle Pls kidan janye gashin nan ki, Yana bani tsoro, ya qarasa maganar cikin sigar wasa Daria yabata, Saida tayi Daria Sosai sannan tasaka hannunta ta janye gashin ta Text ne yashigo cikin wayarsa yabude "" Shege abokina wato kana zaune Ana gyarama gashi, gaba daya ka rikicewa yarinya qanqanuwa"" Murmushi yayi, Kai Abbas, abbas bashida damuwa wallahi, kana wajan zamanka Amma hankalinka Yana Kan wasu🤣 Suna zaune Har aka Gama taron, inda suka yiyyi photuna, kowa sai tayashi murna yake Akan samun shalele, harda masu cewa sai sunzo biki Shikuwa Yana amsawa kamar ya manta da maganar iyayensa Hotel suka koma, tabi zeey dakinsu taqi komawa nasu dakin🤣 Sai can yamma Sosai abbas yashigo sannan tatafi, tabasu waje Tana shiga Dakin taganshi zaune Yana amsa waya dawata Leda akusa dashi, da Alama daga office dinsune Zama tayi, tayi shiru tana tunanin taron da akayi dazu Fatanta daya, Allah yabatashi amatsayin miji Saida yagama wayar Yajuyo ya kalleta, kina buqatar yawo,? Ina zamuje? Idanunsa cikin nata yace ko'ina Tace eh inaso OK ga rigar sanyi nan kisa, akwai sanyi yanzu, saimuje Dasauri tatashi, ta cire mayafin kanta, gashin ta ya kallah tayi fakin sai qyalli yake, tasaka rigar agabansa, sannan tadora mayafin Iya kanta, Shima yasaka tasa suka fice daga hotel din, Hannunsa Yana cikin nata Meyasa ne uncle yakesan riqe Mata hannu? (laushi yaji🤣🤣) Tafiya sukai Sosai akafa Yana nuna Mata wajaje daban daban, wani waje ma daya nuna nata ruwa Yana futowa ga fulawa masu kyau a wajan, ta kalleshi tace uncle kaimin photo anan idan munkoma na nunawa sajida da mama Wace mama? Tace mama de Oh Wai kina nufin anty? Ashefa ke mamanki ce🤣 Nikuma anty nace Tace nasani Kema idan kinso zata Iya Zama antynki Antyna Kuma tayaya? Yace ki tambayeta kiji, zata fada Miki ko ita ko qawarki,🤣🤣 tace masa to Photon yayi Mata, wani mutum daga gefe Yazo yakarbi wayar yayi musu su biyu, yanda ya rungumeta ajikinsa akayi musu photon Kai saika rantse Samah da Safah ne🤣🤣 Har dare Suna yawo, daga qarshe sukaje waani shago yasai Mata waya qirar sumsung Sannan suka dawo, dakansa yasaka Mata wayar acharge sannan sukai sallah sukaci abinci Zama tayi shiiru agefen gadon, yaje yadauko wayar dakansa yazauna dab da ita Yace ga wayarki Kallan mamaki tayi masa tace Uncle waya kasai min? Yes tayi Miki kokuma asake Miki wata? Tayi Sosai uncle nagode Nine yakamata nayi Miki godia, dakika boyoni batare danayi Miki bayaniba Kallansa tayi, babu komai uncle, yanzu zan Iya Kiran waya? Wazaaki Kira? Uncle Bilal Lokaci daya ransa yabaci, yanzu yanzu yasiya Mata wayar Amma tana cewa zata Kira wani? Waye Bilal? (um kaji manya wato Waye Bilal Bama Waye uncle Bilal ba 🤣🤣) Tace masa babanane Babanki? Tace eh, shine babana, banda kowa saishi, mamata tarasu babana yarasu, shine gatana banida wani uba saishi saikuma anty jidda Tana Gama maganr idanunta suka cika da kwalla Tausayinta ne yakamashi, yace sorry, Ina so kibani labarinki, wacece ke? Sunana haneefa suraj daga kuje,..... Tsaf tabashi labarinta kaf Bata boye masa komai ba Sosai ya tausaya Mata no wonder take aiki, yasan cewa ayanda tabashi labarin babanta babu yanda za'ayi yabarta tatafi aikatau wani gida Ajiyar zuciya yasauke, kiyi hakuri, insha Allah komai zai wuce Nasan kuje, akwai wata yar'uwarmu acan, Amma tarasu da dadewa Kwanaki ma nawuce ta Garin, munje gwagwalada Akan aikin company na da akeyi acan Murmushi tayi tace Aina ganka Cikin mamaki yace kinganni? A'ina? Tace acikin Mota zankai babana asbiti na tsaida motarku ku rage mana hanya kuka tsaya Amma Baka futo ba ka Watso min kudi kuka tafi, da wannan kudin nayi amfaani wajan biyan kudin aikin da aka yiwa babana Kansa ya dafe🤦🏻‍♂innalillah, kina nufin Babanki ne awata bishiya a zaune? Ahankali tace shine uncle Kiyi hakuri? Kiyafemin bansaniba, kada ki qullaceni aranki pls bansaniba Murmushi tayi tace wallahi uncle babu komai, ni gode makama nayi, da Baka bani kudinba Aida bansan Yaya zanyi ba Kidena maganar kudin nan, nawa yake ma? Pls kin hakura? Uncle nahakura fa Yace toshikkenan Bari nakoya Miki yanda zakiyi amfaani da ita, matsowa yayi kusa da ita, Har jikinsu yahadu sannan yafara koya Mata wayar, tun suna zaune Har suka dawo tsakiyar gadon Saida yagama yace kingane? Eh nagane, nan danan tafara yi masa bayanin abinda yakoya Mata, yazubawa Dan qaramin bakinta ido Tana bayanin Yana kusantota, shiru tayi tazuba masa ido Ahankali yasaka hannu ya janye Mata gashinta, ya Matso da fuskarsa dab da Tata, burinsa kawai ya sumbaci wannan bakin nata Dasauri tace uncle... Firgigit yadawo daidai🤣mekake yine haka shazali 🤦🏻‍♂ Dasauri yafice daga Dakin yaja Mata kofar🤣🤣 (Haji shazalinmu🤣🤣🤣) Baidawo dakinba Saida tayi bacci, sannan yasaka musu fillo yauma, ya kwanta Shima, tunani yafaara Akan yarinyar nan, yanzu Kam zuwa wannan lokaci haqiqa ya tabbatarwa da kansu son yarinyar ya Kamashi Yanzu Yaya zaiyi dasu momy? Tayaya zai fuskancesu da wannan maganar? Yana wannan tunanin baisamu mafitaba bacci yadaukeshi Cikin dare fillo yayi gefe, babu Wanda yasani atsakaninsu, ga sanyin Gari Gana esi, kowa najin sanyi, hakanne yasa suka Matso jikin juna Dumin dayaji ajikinta ne yasa yasake janyota jikinsa ya rungume ta Sosai, itama batasan lokacin data sake rungume Shiba, sukaci gaba da baccinsu cikin Jin dadi 🤣 ******** Washe Gari suna farkawa da asuba sukagansu manne da juna, Dasauri suka rabu, kunya yakamata, shikuwa Yama kasa kallan ta, haka yashige toilet, baiyi alwalaba Saida yayi wanka🤣 ******** Mami! Mami!!! Dasauri tajuyo tace na'am Afrah Mami yakamata kidena wannan tunanin haaka, idan kina tunani Ina kikeso Musa kanmu ne? Afrah kalli wannan yarinyar da aka nuna atv yanzu daga gidan talavijin na Russia Afrah yarinyar nan kuwa Anya ba haneefan zainab bace? TV din ta kallah, taga sunyi kama da yarinyar Sosai, haka babu abinda zasu fadawa juna, wanima idan yaganta yaga haneefan zaiyi zatan yanbiyu ne Ajiyar zuciya tayi, Mami kidena wannan tunanin, haneefa datake kuje mezai kaita wata qasa? Afrah bakisan wannan Wanda yariqe Mata hannun ba? No bansanshiba Mami, tayaya zan sanshi nida nake nan India 🇮🇳 To haneef ne Yaron wajan momy, cousin sister dinmu nida zainab mahaifiyar haneefa Oh ashe shine Mami, ai bansanshiba kinsan kwanaki danaje Nigeria 🇳🇬, dahar zanje gidan, tokuma naje shopping super Market, wata yar'iska tabatamin rai, da niyyata insa yansandan daddy suyi Mata duka kuma Dai saina shareta (mekaratu dafatan kungane labarin hajara 🤣🤣, aikuwa wallahi afrah kindauki alhakin Marin shalele 🤣😃) To yanzu Mami ya za'ayi? Afrah tun lokacin Dana Kira Malam surajo yacemin zai kawota Har yanzu idan naakirashi wayar Bata shiga, Amma dazaran kungama bikin candy naku, dole zanje Garin kuje dakaina indauko haneefa Idan kuwa bansameta ba, to tabbas wannan yarinyar Dana gani tareda haneef din momy to haneefanmu ce, dole inje gidan momy nasamu haneef yanemomin haneefa (tab shazali kaga ta kanka🤭🙆🏻🤣) Afrah tace to Mami Allah yakaimu, tashi muje daki ki kwanta kihuta (barka da futowa hajiya hafsat 🙏🏻) ******** Tana zaune a dakinta tana kallo, kamar yanda tasaba bibiyar al'amuransa yauma haka, tazauna tasaka TV agaba tana kallo, tunda taji ance yatafi Russian 🇷🇺, tadinga dube duben tashoshin dazataga an Nuna shi, kamar wasa kuwa tana cikin duben taga wata Tasha tana haska haneef shazali da wata yarinya Tuni tatashi zaune, dede lokacin daya kama kafar yarinyar Yana kissing Ana hasko idon yarinyar tace kaiiiii wannan ai haneefa ce, Waye yahadata da haneef shazali? A'ina ta sanshi? Nashiga uku ni sadiya 🙆🏻😱 Cikin sauri tadau wayarta tafara neman number Bilal domin ta fada masa cewa toga yarsa can awata qasa da wani 🙆🏻🤭 (sorry sady😢) ******** Yau Kam a hotel suka wuni, kamar wasu surukai haka suka zauna a Dakin, ita takasa sakewa dashi, tana tuno yanayin jiya daya Matso zaiyi kissing dinta Shikuma Yana tunanin dumin jikinta nayau dayaji Gaskiya dole ma duk Wanda ya auri yarinyar nan yahuta, dan haka yazama dole shiya aureta, yarinyar tanada kayan more rayuwa Haka suka yi shiru shi sai amsa waya yake, ita Kuma tana game da wayarta, Amma kuma sun kasa kallan juna 🤣 Yauda dare yayi kuwa fita yayi daga Dakin sai can daya dedeci tayi bacci sannan yadawo Shima ya kwanta Washe Gari dasafe sukai shirin tafiya, yauma anty zeey ce tazo Har dakinsu ta shiryata, doguwar Riga tasaka yar Dubai Rigar nada fadi, sai mayafi qarami kalar adon dutsinan dake jikin Rigar Kwalliyar da zeey tayi Mata ta karbeta Sosai, girar nan Tasha gyara Zaunawa tayi abakin gado, tana daddanna wayarta, ai suna komawa Nigeria 🇳🇬 zata je Har gidan anty jidda tanunawa sajida Saide Tarasa dalilin wannan kyauta ta uncle haneef Shigowa yayi Dakin Shima cikin qananun Kaya, ta daga Kai ta Kalle shi Sai qamshi yake, yace tashi mutafi, yaje yadauko jakar kayansu, da wadda yasiya Mata dakuma tasa dayazo da ita Tashi tayi tsaye, tasake Kallansa Dan gaskiya yayi Mata kyau sosai Shima tana tashi yazuba Mata ido Yana kallan ta, zuciyarsa na tunzurashi Akan yasanar da ita abinda yakeji game da ita Takowa yakeyi ahankali Yana tunkarota, itade tana binsa da kallan mamaki Yana binta tana yin baya ahaka Har sukaje jikin bangon Dakin Cikin faduwar gaba tace un... Uncle... Lafiya? Bece Mata komaiba yasaka hannunsa yakama kyakykyawar fuskarta da duka hannayensa biyu, yamatso da fuskarta dab da tashi Cikin sauri ta runtse idonta ganin abinda yake shirin yimata Ahankali yadora bakinsa Akan nata, yanayi Mata wani irin kiss me zafi, dan qarami lips dinta yakama yanasha, Sun dauki tsawon minti biyar ahaka sannan yazare bakinsa daga cikin nata Tana Bude ido taga idonsa akanta dasauri tayi qasa da kanta Baisaki fuskarta da hannun nasaba, cikin rada yace "Haneefahhhh... Yaja sunan nata Kasa amsawa tayi Yasake Kallanta, cikin rada yace Mata" I really luv you so much, Zaki Iya aure nah "??? (yau kaam kasa nakasa magana shazali, wallahi ku soye harku qone, Nigeria tana nan tana jiranku☺) Yaya kuke ganin amsar haneefa zata kasance? Anya shazali kuwa Yana saane da maganr iyayensa akansa? To dafatan de yanzu kowa yasan matsayin momy da hajiya hafsat dakuma maman shalele Yaya zata kasance tsakanin Bilal da sadiya? Duk kubiyoni zuwa gobe domin Jin Yaya zata Kaya, Ina yinku Sosai fans Sharhi comment share Dan Allah kada amanta 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻 Amnah eh ✍🏻💕SHALELAN BABA💕 (Romance) Writing by Amnah El 35&36 Fuskarta ta qwace daga cikin hannunsa tafice daga cikin Dakin dasauri Shima yabita da kallo, murmushin daya gani a Fuskarta kadai ya gamsar dashi wajan samun amsarta Murmushi yayi Shima yabiyo bayanta da jakar kayansu, haka suka futo harabar hotel din, tana gaba Yana binta Abaya, zeey da abbas suna tsaye awaje suna jiransu, zeey tace Kai Ina jambakin Dana shafawa yarinyar nan? Daria abbas yayi yace sun shanye abinsu🤣 A a haba de Kai kana ganin Hakan zata faru? Kinga uwargida wasa nake Miki, Bana tunanin Hakan gaskiya Adede lokacin suka qaraso wajan, babu Bata lokaci suka tafi, suna zuwa Airport jirginsu yatashi zuwa Nigeria ******** Tana samunsa awaya tace Yaya yanzu Naga haneefanka a TV wallahi Haneefa kuma? Meya hadata da gidan TV ita Kuma? Yaya wallahi yanzu naganta da haneef shazali, suna Russia shida ita Haneef shazali de Dan kasuwar nan? Eh shi Yaya, wallahi dashi naganta yanzu To ita mezai hadata da shazali? Tayaya ma ta sanshi? Kinga sady idan nagama aiki zanje gidan datake ingani Toshikkenan Yaya sai ka dawo, Ga Abdallah Yana gaisheka, OK tokishafamin kansa, bye ******** Jirginsu na sauka sukayi sallama dasu zeey, baima yi waya azo daukarsu ba, kawai taxi yatare musu suka wuce gidan jidda Kai tsaye, alokacin uku saura Suna zuwa gidan sajida ta rungume ta, sukayi ciki, Shima afalo ya zauna shida anty jidda, tace mutanan Russia, Yaya taro? Alhmdlh anty, mundawo lafiya, kuma nagode Sosai Ba godia zakamin ba haneef, fadamin zakai dalilin dayasa ka dauki yarinyar nan, haneef meyasa zakai haka? Idan wani ne yadauki yanbiyu zakaji dadi qanina? Ajiyar zuciya yasauke ya kalleta cikin serious voice yace anty kiyi hakuri nasan nayi laifi, Amma naje wajan hajara da hairat sunqi yarda mutafi, anty alokacin Banda zabin daya wuce hakanne, shiyasa nace tashiga Mota mutafi, Amma itama ba'ason ranta ba, saboda Dana dauketa ma da bacin rai muka tafi,Amma kiyi hakuri, insha Hakan bazai sake faruwa ba, ki yarda da qaninki anty, bazai yi abinda zai cutar da 'yar kowaba Anty jidda tace Toshikkenan, Allah yashige mana gaba, Allah kuma yasa kada wannan labarin ya Isa kunnan Wanda zaice Yana sonta zuwa gaba, domin kuwa bazaiji dadi macen dayakeso tafita da wani namiji daban qasar wajeba Anty wacce irin magana kike haka? Dama haneefa akwai Wanda zata aura ne daya wuce ni? Haba anty, duk da babu abinda yashiga tsakaninmu ai bazan yarda ta auri waniba, Bayan na dauketa na nunawa Dunia cewa itace wadda zan aura, idan naki aurenta ma ai sai Allah ya kamani Dadi yakama anty jidda, tace haneef kana nufin zaka auri haneefa ta? Zan aureta anty, wannan dalilin nema yasa nabiyo ta wajanki ban wuce gidaba, anty nasanar dake inason haneefa, itama nafada Mata Ina sonta Amma yanzu haneef Yaya kake ganin zamuyi da momy da daddy? Cikin sanyin jiki yace shine abinda bansaniba anty Kaga qanina ka kwantar da hankalinka, zanyima adduah, kawai kaje kasamesu kasanar dasu abinda yake faruwa babu maganar boye boye Toshikkenan anty, nizan wuce, duk yanda mukai dasu zakiji, to qanina sai anjima Yana tafiya takira haneefa tazo tazauna agabanta, tabita da kallo Ahankali tace mama Dan Allah kiyi hakuri, wallahi shine yace nashiga mutafi Tokuma haneefa danyace Kishiga saiki shiga? Idan yace Kishiga wuta ma Kenan saiki fada? Hawaye ne suka zubo Mata zirrr, tace mama kiyi hakuri Dan Allah Haneefa duk da haneef qanina ne, bazanso ya cutar dakeba, dole zanyi kokari Naga na qwato Miki yancinki awajansa, yasanar Dani cewa Yana sonki, sannan zaije yafadawa su momy komai Dasauri ta kalli anty jidda Anty jidda tace eh haka yafadamin, kada kidamu kiyi muku adduah insha Allah babu komai kinji? Daga Mata Kai tayi, anty jidda tace tashi kitafi, da yamma sai nasa driver ya maidake Tana tafiya, anty jidda tadaga hannu ta godewa Allah, wani farin ciki Yana qara ratsata ratsata, alhmdlh addu'arta ta karbu Wayarta ce tayi qara tana amsawa tace hello Bilal Na'am antunmu kuma amaryarmu ya gida? Gida alhmdlh doctor Dama nakirane ki hadani da haneefa Godia tayiwa Allah, yanzu dabasu dawoba me zata fada masa? Tasan da daga yau Zaman yarinyar yaqare agiidan su, shikuwa Bilal da biyu yayi Mata wannan tambayar domin ya tabbatar da mgnr sadiya, shin tana wata qasar dinne kokuma tana gida Anty jidda ta kwala Mata Kira sannan tabata wayar tayi cikin dakinsu tana magana dashi Da yamma kuwa anty jidda tasa driver da sajida suka rakata gidan momy ******* Tunda suka dawo daga Russia yau tsawon kwana biyu Kenan, tadena zuwa gyara masa daki saide intaga bays gidan zatayi sauri tagyara masa tadawo, Shima anasa bangaren Bai nemetaba, yasanar da Ajmal komai Shima kuma yadada karfafa masa gwiwa Akan Hakan, saide Har yanzu tunanin yanda zai fuskanci iyayensa yake da maganar Kwanansu uku da dawowa tana falo tana goge goge tana Taya baba Hanne, dan gyaran part din momy Dama baya daga cikin aikinta, kawai yau din ne take Taya baba Hanne Shigowa yayi cikin Shiri zaiyi tafiya shine zai sanar da momy Kawai ya ganta tana goge goge, Dasauri ya qaraso wajanta yariqe towel din, meyasa kike aiki? Bata bashi amsaba sai qasa datayi da kanta Yace kada kisake aiki agidan nan kowanne iri ne, Nima na part Dina nahanaki, banaso naqara ganin kina komai kinji? Daga masa Kai tayi, ya Matso da bakinsa saitin kunnan ta yace zamu tafi England yanzu nida Ajmal zamuje kallan gasar premier Insha Allah idan muka dawo zan sanar dasu momy komai, kinji? Qaran kofin dasukaji abayansu ne yasa suka kalli wajan dasauri, daya daga cikin yanbiyu ne, basu gane ko wacece ba acikinsu Kallan haneefa yayi yace saina dawo OK? Yakalli yanbiyu yace mahaukaciya koma wacece acikinku🤣🤣 Yashiga dakin momy yayi Mata sallama yatafi ******** Tun lokacin daya tafi, tafara yiwa baba Hanne karatu Sosai, Amma idan tatuna maganar da uncle yafada Mata sai jikinta yayi sanyi, Tasan cewa rabuwarsu tazo, yanbiyu kuwa idan sun ganta harara ce take rabasu, Tasan kuma Hakan baya rasa nasaba da ganinta dasukai afalo itada haneef duk da batasan wacece tagansu ba acikinsu Haka take kokarin sharesu Har suka dawo daga England shida Ajmal, da yamma suka dawo, Bata Samu ganin saba, sai washe Gari dasafe da akai baqi agidan Anty fadila da anty iklas ne qannansa dasuke binsa sukazo, sai hidima ake

Chapter 11 of 17