Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dasu agida

Yaron anty fadila namiji kyakykyawa dashi taji tana son Yaron, afalo tazuba musu ido tana kallan su Yaron Yana sakawa haneef ice-cream abaki, sai nishadi suke

Anty iklas kuwa mace ce yarta ko zama batayi

Har yamma suka Kai sannan suka tafi, da daddare tana falo tana kallo duk da ba dabi'arta bane, Shima yashigo falon yazauna

Ruwa tatashi takawo masa, Takoma qasan kafet tazauna Shikuma yanakan kujera, Kallanta yayi

Kinason Yara ko?

Murmushi tayi, Ina sonsu Sosai uncle, musanman ma namiji

Meyasa kikeson yaro namiji?

Saboda insa masa sunan babana

Murmushi yayi, insha Allah kema wataran Zaki Samu naki

Murmushi tayi masa kawai

Kinga shikkenan saimu Samu me sunan baba

Daria sukasa gaba dayansu, Safah tafuto falon alokacin zatai kallo

Kallan tuhuma tahau yi musu, yaushe Yaya yafara sakewa masu aiki haka?

Anya kalau yake kuwa?

Kallanta yayi yace ke mekika zoyi nan?

A a Yaya Dama... Dama kallo zanyi

Wuce kikoma daki bazakiyi ba ko bakiga mutanene a zaune a wajan ba? 🤣🤣

Saida ta kalli shalele sannan tace kayi hakuri Yaya Tajuya ciki

Yau Kam ta yarda da maganar Samah, gaskiya Yaya yafara son wannan yarinyar me zubin fulani

********
Washe Gari yashirya tsaf cikin shirinsa na fita office
Qananun Kaya yasaka dasukai mutuqar karbar jikinsa
Gabansa ne yake faduwa idan yatuna yau yakeson fadawa su momy maganar haneefa

Kai tsaye yatafi part din nasu Yana adduah cikin ransa
Saida yabari suka Gama yin break sannan yakalli momy da daddy yace daddy Dama inaso zanyi magana daku kafin nawuce office

Daddy yace OK Bari mugama to

Aikuwa suna gamawa daddy yanuna masa hanya yace muje ko

Suka tafi falon daddy gaba dayansu

Yana zaune aqasa kansa a sunkuye, yakasa magana

Daddy yace muna jinka haneef

Dama zan sanar daku ne, nasamu wadda nake so, nida ita muna kaunar junanmu, kuma nayi Mata alqawarin aure

Mekake fada haka haneef? Tokuma maganar yar abokinafa? Da yar qawar momynku?

Daddy Danaga Dama rashin wadda zan aura ne yasa zaku hadani dasu kuma yanzu nasamu

Cikin fishi momy tace to baka isaba, aiba Kaine ka haifemu ba

Lokaci daya idanunsa yacika da qwallah, abinda basu taba ganiba a wajan haneef
Ya kallesu, yace momy daddy, yarinyar nan itace bugun zuciya ta, wallahi idan ban auretaba mutuwa zanyi

Cikin masifa momy tace Wai Kai haneef ba kada Aiki da anyima Abu saikace zaka mutu zaka mutu to wallahi wannan Karon saide Allah yaji qanka🤣🤣

A a hajiya, meyayi zafi haka,? Inji daddy

Ya kalli haneef yace wacece wadda kakeso din?

Ahankali yace haneefa

Wacece haneefa?

Tanan gidan yarinyar datakemin Aiki

Lokaci daya momy tafara tafa hannu tana salati, karasa wazaka so sai me Aiki haneef?

Daddy yace Dan Allah hajiya kiyi shiru yasake kallan shazali yace jeka turomin yarinyar inyi Mata tambayoyi

Ahankali yatashi yafuta daga falon, kansa namasa mugun ciwo, dan kada tagane yanayin dayake ciki saiya Dan nutsu

Ya tura dakinsu, tana zaune itada baba Hanne suna karatu, yace Mata haneefa zo mana, Gabanta ne yafadi, tasan kuma shikkenan magana ta qare
Saida suka futo yaqara kwantar Mata da hankali sannan suka shiga Dakin

Gabanta Banda faduwa babu abinda yake, kallan da momy take binta dashi kadai ya Isa ya tabbatar Mata da cewa babu hairu alamarin🤣

Daddy ya Kalle shi yace haneef jeka Dakin momynka kabaamu waje

Saida yajuyo ya kalli haneefa sannan yatafi, suna ganin fitarsa daddy yace yarinya meyasa kikeson haneef? Dan kudinsa ko? Kokuma wani ne yaturoki aboye Bamu saniba?

Hawaye ne suka zubo Mata masu dumi, ta girgizawa daddy Kai

Momy tace toki tattara yanaki yanaki kibar gidan nan yanzu basai anjimaba, kinji nafada Miki, akwai yaran damukeso danmu ya aura

Daddy ya kalleta yace kinji abinda aka fada Miki?

Cikin kuka tace eh, kuyi hakuri, tatashi tafuto tana share Hawaye, Dama tasan haka zata faru, tasan cewa haneef yafi karfin tunanin ta, kawai tana yaudaran kanta ne

Tana shiga dakinsu tafara hada kayan ta cikin jaka
Baba tana tambayrta Amma batace Mata komai ba, sai sharar Hawaye kawai datake

Truly dinta taja, tacewa baba kiyi hakuri baba zamana a gidan nan yaqare, sai wata Rana, tafuto falo tanajan jaka tana ruskar kuka

Samah na ganinta tace sai aqara gaba kuma, Safah kuwa batace da ita komaiba

Itama Bata Kalle suba, tawuce tafuto harabar gidan, tana tafe tana share hawaye
Dakanta tabude gate din gidan tafuto, kanta yasara Mata, afili tace tabbas kowa yabar gida... Allah yaji qanka baba, na tabbatar babu Wanda zai Soni aduniyar nan Sama dakai, zan koma kuje Koda kuwa Hakan Yana nufin Inna zata kasheni Dan azaba, zan zauna a gidan ubana, inda babu me korata bare ayimin gori

Jakarta tabude tasaka number Bilal takirashi, bugu daya yadauka, tace uncle Dan Allah kazo ka daukeni

Haneefa lafiya?

Lafiya uncle nide Dan Allah kazo, tafashe da kuka, yace subhanallah gani nan, kina Ina yanzun?

Ta kwanta ta masa wajan sannan takashe wayarta baki daya ta jefata acikin jaka, kallan gidan tayi, Bata marmarin qara shigowa gidan nan, su riqe dansu Itama ta riqe mutuncin ta

Tafiya tafarayi akafa, harta hango motar Bilal, Yana zuwa kuwa tashige suka tafi

Meyake faruwa haneefa? Kisanar Dani mana

Kuka tasaka masa, lokaci daya tabashi labarin komai
. Dakatawa yayi da driving, Kenan da gaske sadiya take ita din tagani

Cikin fishi yace, ke kinason haneef din?

Tayi shiru, Kenan tana sonsa 🤣yasake cewa shi haneef din Yana sonki?

Ta daga masa Kai

Yace to kunyi sa'ah kunason juna, wallahi dayau saiya gayamin shegen dayasa ya daukeki yafita dake wata qasa, ni tun farko ma Dakin sanar Dani halin dakike ciki a wannan gidan wallahi dabazakiyi kwana daya acikiba, Amma sai kika nunamin a gidan jidda Zaki zauna

Cikin hawaye tace uncle Dan Allah kayi hakuri

Rufemin baki ni, mezaki fadamin (tofa ran uba yabaci 🤣🤣🤣)

Motar yaja suka fara tafiya, tace uncle kuje zaka kaini

Mezaki yi a kuje?

Dan Allah uncle kada ka tambayeni dalili, natuna baba ne pls kakaini can

Tausayi tabashi Dan haka bece komai ba suka tafi kuje, suna zuwa kofar gidan kuwa sukaga wata danqareriyar Mota,dawata motar Abaya, da kuma yansanda kusan biyar suna tsaye

Bilal na tsayawa shalele ta futo, mekuma inna marka tayiwa Yan Sanda?

Mami kuwa tana hangota tace haneefa tah!!!

Dasauri ta kalli matar taga suna mutuqar kama Sosai, afrah tatafi da gudu ta rungume shalele
Hajiya hafsat ma haka, gaba daya sukasa kuka, Bilal kansa Saida yayi qwallah, Hajiya hafsat tace nice mamanki haneefa

Bilal yace Hajiya hafsat ko?
Cikin hawaye tace eh nice yaro, Waye Kai?

Yace dogon labari ne, zanzo gidan kibani address dinki, aikuwa Mami agun tabashi, taja hannun shalele suka shige cikin Mota, ko gida Bata Bari tashigaba

Saida Bilal yaga tashin mortarsu yasaki ajiyar zuciya alhmdlh Allah nagode ma, haqiqa yau nacika alqawarin Malam surajo

********
Yaga zama zama su momy basu kirashi ba, dan haka Yakoma Dakin daddy yaana zuwa yaga Bata nan
Iyayen nasa ya kallah yace momy daddy Ina haneefa take?

Kai tsaye momy tace mun koreta, Gabansa yafadi yasaka hannu ya dafe qirjinsa yace momy Saida nace muku yarinyar nan I tace bugun zuciyata Ina sonta momy Ina son... Bai qarasaba yafadi a wajan sumamme

Lokaci daya Iyayen sukai kansa, momy ta Dora hannu aka tafasa ihun kuka tace munshiga uku alhaji🙆🏻

(keda kikace saide Allah yaji qansa 🤣)













(tofa shazali kana cikin dalala😱)

(congratulations shalelan baba, shalelan haneef shalelan Bilal, yanzu kuma shalelan mami💃🏻💃🏻💃🏻)

Shin momy zata yarda da aurensa da 'yar qawarta kokuma zatayi amfani da Karin maganar nan na wata kusan....?








Sanarwa
Nafarko Dama nafada cewa labarin shalelen baba yanada yawa, shiyasa nake kokari nake yin page me tsayi Dan muyi muyi mugama, Amma mutane suna fadamin cewa typing din danake yayi yawa, har wasu suna cewa wallahi sungaji da karantawa, imagine nida nake zama naabata lokaci nayi typing bance nagaji ba saiku da kawai riqe waya zakuyi a hannu Kuna karatu, 😣😣😣dan haka daga yau zan rage yawan page insha Allah, zanyi komai ataqaice kamar yanda nayi wannan, kamar kuma yanda kukeso, nimafa macece kamar kowa, inada ayyukan gida, Amma nake tsayawa Ina wannan rubuttun)


Saina biyu, wasu suna cemin Wai bekamata shazali yafita da shalele qasar waje ba, wannan ba al'adar bahaushe bace, jama'ah me kuka dauki novel ne?
Kudinga banbancewa tsakanin true life story dakuma qageggen labari, labarin shalelan baba qageggen labari ne Dana zauna nikadai nahada abina kuma na fidda mafita, Abu biyu kowannne novel yake daauka a Dunia, Abu Mai kyau da marar kyau, saika dauki Mai kyau ka watsar da marar kyau, bance Wai dole sai an dauki abinda narubuta acikin wannan labarin ba,


Sannan kuma shi shazali daya dauketa suka fita kun tsaya kunga sakamakon sa ne? Kun tsaya kunga naqare littafi na batare Dana nunawa shi shazali illar hakanba?
Idan kukaga nagama rubutu na batare Dana nuna rashin dacewar hakaba saiku yimin magana, Amma bawai ku katseni yanzu ba




DAN ALLAH naroqeku da babbar murya, kudenamin katsalandan acikin labari nah🙏🏻

Kamar yanda na roqeku tun farko kuci gaba da bibiyata Dan Allah kubini, kudena yanke hukunci sai kunga qarshan labari ngd 🙏🏻
























Amina Muhammad El yaqoub ✍🏻💕SHALELAN BABA💕
(Romance)

Writing by Amnah El

37&38

Ihun da momy tasa tana Kuka ne yaja hankalin su Samah dasuke falo
Aguje suka shigo falon na daddy, suna ganin yayansu akwance kamar Matacce suka fara Kuka sukai kansa
Yaya katashi! Momy munshiga uku ko Yaya yamutu ne?
Daddy ne yayi karfin Hali yace kurufa mana baki, wacce irin mutuwa kuma? Kutashi kubani ruwa

Fridge din falon sukaje suka daukowa daddy ruwa, nan aka yaiyafa masa, Amma shiru kakeji babu wani bayani

Tofa al'amarin yafi karfin tunanin sa, fita yayi waje yakira ma'aikata, babu Bata lokaci akayi asbiti dashi

********

Cikin Kuka Sosai take magana, idanunta sunyi jajir da Fuskarta, abinka da farar mace
Haneefa ki yafemin, ban riqewa zainab alqawari ba, nayi watsi dake, kuma Hakan yafaru ne sanadin babanki suraj, yahana kowa daukarki, yace Yana so yarsa ta shaqu dashi fiye da kowa

Munyi waya dashi kwanaki yace zai kawoki, nace masa ni yabarni zanzo Amma yace nabari zai kawoki dakansa
Daga lokacin bansake jinsa awayaba, kuma Ina tsoron inzo yahanani tafiya dake, saboda bansan dalilinsa nacewa kada nazo ba

Mezata cewa Allah? Ai sai godia atsakaninsu, yau da ace Bata Samu yayar mamanta ba, ta tabbatar dazata Iya kamuwa da yawan jini, saboda baqin cikin abinda momy tayi Mata

Dan Adam ako'ina daraja ce dashi, idan sunyi Mata magana cikin fahimta ma dole zata rabu da dansu, bawai sai anhada da tozarci ba, na farko qannansa sunyi Mata ta shanye, shi yayi Mata da farko duk da ance halinsa ne fadan baya San raini tashanye,yadauketa cike da iko yatafi wata qasa da ita, ita ba'a Mata ba, ita ba'a budurwarsa ba, kuma ita ba'a karuwa ba
Duk ta shanye

Dama hakane, duk Dan da beji maganar iyayensa ba to tabbas zaiga ba daidai ba, baba yayi Mata nasiha kafin yarasu Akan ta riqe mutuncin ta na ya mace, Amma tayi watsi da Hakan, yanzu ga sakamakon data Samu nan

sannan mahaifiyar sa tayi Mata, ta koreta daga gida mama jiddah ta rufa Mata asiri ta dauketa, daga qarshe akaro na biyu tasake korarta, to ita kuwa kosan hauka take masa ai yaci ace tahakura dashi

Waya sanima koba San gaskiya yake Mata ba, kawai yanason wani Abu Natane, inba hakaba meyasa tunda farko baisanar da ita ba sai Bayan yagama kissing dinta ya shanye Mata baki🤣

Kai wallahi ma bazata yardaba saiya biya Mata bakinta, aiba Nasa bane natane🤣

Afili tace wallahi bazan yarda ba 😱

Hajiya hafsat tace nasan namiki laifi, kiyi hakuri haneefa, ke kadai zan gani yanzu naji kamar zainab nagani

Cikin sauri ta juyo ta kalli hajiya hafsat🙆🏻tab ashe Afili tayi maganar, 🤣

Ahankali tace babu komai hajiya

Wacece hajiya haneefa?
Kada kisake fada, ta kalli afrah tace fadawa sister ki sunan dakuke kirana

Afrah ta Kalle ta tace Mami, nikuma afran Mami, kekuma haneefan Mami, Shikuma Yaya ameer Banda shi

Daria tabasu gaba dayansu, hajiya hafsat taja haneefa da afrah jikinta ta rungumesu, tace Allah yajiqan Malam suraj, sukace amin gaba dayansu

********

Tunda sukazo asbitin suka kasa zaune suka kasa tsaye, momy Kuka yanbiyu Kuka, daddy ne yake kokarin kwantar musu da hankali, sunyi kusan 30minutes a wajan sannan doctor yafuto, cikin sauri sukai wajansa

Am hajiya, alhaji ku kwantar da hankalinku, yaronku Yana cikin matsanancin Hali gaskiya

Cikin Kuka momy tace doctor wanne irin Mu kwantar da hankalinmu kace Dana Yana cikin matsanancin Hali 😭

Doctor idan haneef Dina ya mutu Nima mutuwa zanyi

Hajiya kiyi hakuri, yayi doguwan suma ne, Amma yanzu munsaka masa oxygen insha Allah zuwa wani lokaci komai zaiyi daidai

Daddy yace zamu Iya ganinsa kuwa likita?

Eh zaku Iya shiga, Amma Dan Allah Banda surutu, anyi masa allurar bacci, idan yatashi zamu saake dubashi, yawuce office dinsa

Dukansu zama sukai a Dakin sukai jugum jugum dasu, abin tausayi 😢😱

********

Suna zuwa gida, aka wangale musu gate, still harabar gidan ma Yan Sanda ne,itade shalele cikin ranta tana cewa ko meyasa suke yawo da yansanda?

Momy ta riqeta afrah ta riqeta haka suka qarasa cikin falon, gaskiya gidan yahadu ba qarya

Ameer na zaune afalo ya tusa computer agaba Yana typing yadago kansa ya kallesu, da tsananin murna ace a a Mami sannunku da zuwa, ya kalli shalele yace inye Mami kinga yanda haneefan baba ta girma, Yara duk sun girma sai aure 🤣

Daquwa Mami tamasa, ungo nan Ameer, Kai basu ce kayi aure ba sai Kaine zaka fada musu haka? Sosa kansa yayi yamaida hankalin sa Kan computar, yace sannu da zuwa haneefan baba, murmushi tayi tace yawwa sannu

Afrah ta kalleta tayi Mata rada, haka yakefa, kullum cikin aiki kamar computar, ba shida magana yanda kikasan damo🤣

Kallansu yayi, afrah Har anfara Halin gulmar ne?

Cikin nutsuwa tace a a Yaya, taja hannun shalele sukai daki, Mami ma tabi Bayan yaranta, Saida sukai wanka taci abinci sannan suka baje kolin fira, lokaci daya tasake dasu, Mami babu ruwanta hada Kan yaranta take ta rungume 🤣

Shalele tabasu labarin komai Nata, Amma Bata basu labarin aikin datayi agidansu shazali ba, fatanta daya ta manta da ahalin gidan ayanzu

Mami azuciyarta tace toba haneefa bace suka gani atv ba rannan

To Amma meyasa Bata basu labarin abinda yarabota da gidan jiddan datace ta zauna ba? Haka kawai zata dawo gida ne? Kai dole akwai abinda yake faruwa Amma ta Barta tasake sakewa dasu kadan kafin ita da kanta tasanar dasu komai

********


Haka suka zauna shiru a Dakin, Har dare bai farkaba, yanbiyu sun fara gyangyadi daddy yace sutafi gida, badan sunso ba driver yazo yatafi dasu

Momy da daddy suna zaune agefensa babu abinda yake tadasu sai sallah


********



Shalele kuwa afrah Nata Bata labari da daddare, sun ware sai zancensu sukeyi, afrah tace Wai haneey bakida boyfriend ne?

Banda shi afrah, mutum daaya de yataba cewa Yana sona kuma mun rabu🤣

Ayya sorry sister haneey insha Allah, ubangiji zai kawo wasu

Shalele tace afrah Ina abbanku ne?

Wallahi yatafi arewa, Amma may be yadawo jibi, dagani sai Mami sai Yaya Ameer ne a gidan dakuma security

To shi Yaya ameer din a wacce ma karanta yake?

Afrah Tai Daria, aiya Dade da Gama mknrta, yanzu yana aiki ne dawani company na qera computar, shiyasa zakiga kullum Yana cikin sarrafata, bashida magana, haka yake shiru, babu ruwansa yanada hakuri Sosai

Shalele tace Allah sarki

Haka sukaci gaba da firansu Har afrah tayi bacci, ita Kuma tafada tunanin haneef

To meyasa ma zatai tunanin sa? Mutumin daya cuceta yagama tsotse Mata lips, ai wallahi tana sane Kuma saiya biya Mata abinta tunda iyayensa basuda mutunci 🤣😱🤭


********


Washe Gari Dr Bilal yaje gidan, ta hanyar adress din da Mami tabashi, ankarbeshi Sosai, Shima kuma ya ware kamar Dan gida, Yana basu labarin irin gwagwar mayar dayasha da Marka Akan neman hajiya hafsat 😄
Sai Daria suke yi abin gwanin birgewa

Ya kalli shalele, to shalelan baba yanzu Kuka ya qare ko?

Afrah tace au uncle da Kuka take?

Daria yayi ai Tasha kukanta, kawai Marka takawo wata Mata Wai maqociyar kice zata kawota wajanki, shine yarinyar nan saboda tsabar shirme tabita

Mami tace Toya za'a yi tanaso taga namanta

Sukayi murmushi Dukansu, Saida yadade agidan sannan yayi musu sallama zai tafi
Mami ta dubeta ki tashi ki rakashi mana

Tace to, tatashi tabishi cikin kunya, Mami fa kada tayi tunanin wani Abu ne atsakaninta da uncle, 🤣wannan me shegen son girman a'uba yadauki kansa

Suna zuwa wajan motarsa ya dubeta, idan nasamu lokaci zan kawo Miki Abdallah ya wuni, but dashi zan koma, bazan barmiki shi ba

Oh uncle da son Yara kake wallahi

Kinga laifi na dannaso Yara?

Sosai ma

To menene laifin? Ya kafeta da idanuwansa

Saida tayi qasa da kanta cikin kunya tace to uncle kayi aure mana, tana Gama fada Takoma gidan da gudu🤣

Bayanta yabi da kallo, tab to tunda yarinyar nan tafara maganar aure Gara yasamu wata ya aura, yarinya me kunya tana ganin girman sa to me akayi kuma idan tafara futowa qarara tana cewa uba yayi Aure 😱🤭🙈

Murmushi yayi yashige motarsa ya koma wajan aiki, Dama daga asbitin yake yafatse ayyukansa yataho

********

Doctor yazo ya dubashi, aka cire masa oxygen din da aka aka Saka masa, sai ruwa daya daura masa yayi masa Yan gwaje gwaje , ya kalli su momy yace hajiya, Alhaji maganar gaskiya danku Yana cikin matsananciyar damuwa,Har Hakan yaso taba zuciyar sa

Atare momy da daddy suka ce zuciya doctor 😳🙆🏻

Qwarai kuwa, zuciyar sa Amma yanzu babu wata damuwa
Idan Har zaku kiyaye yimasa abinda ransa baya so, kukuma bashi abinda yake so, haka ne kawai zai rabashi da damuwa, bare aje ga samun matsala

Hawaye momy ta share, Dama yace yarinyar nan itace bugun zuciyar sa

Cikin mamaki ya kalleta, yanzu hajiya Dama kunsan damuwar Dan naku?

Daddy yace wata yarinya yakeso, mukuma munriga munyi masa Matan dazai aura, dalilin hakane yafadi yasuma

To gaskiya Alhaji shawarata agareku itace kode kubashi wadanda Kuka zaba masa ya auresu Shikuma ku rasashi, kokuma kubashi wadda yakeso ku zauna da danku

Daddy ya zabga uban tagumi😱

Momy kuwa kallan haneef take cike da tausayi, gashi takori wannan yarinyar, Ina zasuje su nemeta ta Ina zasu fara?

Jidda ce tafado Mata, batazo da wayarta ba, ta kalli daddy tace Alhaji ko zaka Kira mana Jidda muji ko yarinyar nan can tatafi

Daddy ya Kira anty Jidda

Tana dagawa tace daddy Ina kwana?

Lafiya jiddah, nace wannan yarinyar tazo gidanki ne?

Wacce yarinya daddy?

Yarinyar datakewa haneef aiki

OK daddy Wai haneefa?

Ok haka sunanta Kenan,?

Tace eh daddy haka ne sunanta, Amma shalelan baba ake fada Mata

Daddy yace um aijinake karyar haneef ce Bahaka sunantaba, sunan ma Ara Mata yayi shiyasa yace mana haneefa🤣🤣

Daddy meyake faruwa? Ni batazo nan ba, wani abun haneef din yace akanta?

A a jidda qaninki de gashinan akwance rai a hannun Allah, tun jiya muna asbiti Har yanzu Bai farfado ba, Amma likita yace zai Iya tashi kowanne lokaci, yace yanason yarinyar ne, mukace bamu amince ba

Shine yafadi yasuma, Wai itace bugun zuciyar sa🤣🤣🤣ke kinji fa wani shirme jidda, yaushe zaka tsananta son mace Har haka?

Innalillah... Yanzu daddy haneef din Yana kwance a asbiti Amma Baku fadaamin ba?

To jidda muna cikin wannan tashin hankalin wama muka fadawa? Babu Wanda muka fadawa wallahi

Daddy yanzu kuna wanne asbitin?

Yana fada Mata, tace to ganinan zuwa


********

Afrah Ina wayatane zan Kira hajiya Amina

Tana wajan haneey, may be game take

Kirata takawomin kuma tafuto zamu fita akwai inda zamuje

Afrah ta daga murya tace haneey!
Haneey!!

Gani nan zuwa Afrah

Toki futo da wayar Mami

Futowa tayi falon dawata doguwar Riga ajikinta ta bacci, Me kauri, da kadan rigar tawuce Mata gwiwa

Zama tayi akusa da Mami ta Dora kanta akafadarta, afrah kuwa tana kwance,tace gashi Mami

Kiran hajiya Amina tayi

Salamu alaikum, hajiya momyn Yara, yagida ya yanbiyu?

Zuciyarta ce ta tsinke lokaci daya, wacce momyn? Wanne Yan biyun?

Daga daya bangaren momy tace hajiya hafsat lafiya wallahi, yaushe kika dawo qasar?

Shekaran jiya nadawo hajiya, Dama zan fada Miki ne jiya naje kuje fa nadauko haneefan baba

A a hajiya hafsat kuma kikama hanya kitafi wajan baba Amma kikasa sanar Dani, haba hajiya gaskiya banji dadi ba
Ina haneefan take yanzu?

Mami ta kalli haneefa tace gatanan hajiya, yau zamuje nayi Mata shopping ne, gobe zata koma makaranta , Amma insha Allah gobe zamuzo nan dinma gaba dayanmu Har su ameer yarama suga junansu

Toshikenan hajiya, Allah yakaimu goben Amma inaga mukam saide ku samemu a asbiti, haneef ne a kwance bashida lafiya

Subhanallah, meyasami haneef din hajiya

Shalele naji ance haneef gabanta yafadi, meyake shirin faruwa ne?


Momy tace wallahi hajiya
Wata yar aiki ya gani Yana so, shine muka hanashi, to daga nanfa sai suma, wallahi yau kwana mukai bamu rintsa ba hajiya

Mami tace yar aiki kuma? Me wannan Yaron yakeso ya nuna mana ne? Yarasa wazai kwaso mana viking family sai yar aiki duk ajin haneef shazali da kudinsa?hajiya Meyakeso muce ranar auren?
Toma wacece wannan yarinyar?🙆🏻

(gatanan agabanki 🤣)

Momy tace bar matsiyaciya hajiya, nakoreta ai jiya, yanzu de Allah yakaimu goben sai kunzo

Mami tace to hajiya, insha Allah gobe zamu zo idan ameer yataso daga wajan aiki

Idanunta ta rufe, kamar me bacci, yanzu Kam tagama fahimtar komai, ko tantama batayi wannan momy ce akai waya da ita

Amma meyasami uncle haneef? Meyasameshi?

Saide kuma zata so sanin menene hadin Mami da momy

Kallan Mami tayi, tace Mami wannan din wacece?

Haneefa Kenan bazaki santaba, Amma gobe zamuje ki ganta

Da mahaifinta da mahafinmu nida zainab yar"uwata, iyayensu daya, babanta ne babba, sai babanmu, Dukansu Allah yayi musu rasuwa, saimu uku kadai, tokuma itama zainab Bata Dade da haihuwar Kiba tarasu

Ban cika zama aqasar bane shiyasa Bama ziyartar juna

Cikin ranta tace Tab Kan bala'i🤣🙆🏻Kenan cousin din namanta ce ta koreta?

Aikuwa babu inda zataje, tariga datayi fishi dasu, suje su riqe dansu


Itama ta riqe mutuncinta,wallahi gobe batada lafiya, kawai gobe ba lafiya Dan haka tun safe ma zatayi kwanciyarta adaki cikin bargo 🤣ba ita ba gidansu momy

********


Momy tayi shiru tayi tagumi adaki ita kadai, tana kallan haneef dake kwance Yana bacci, yau da ace haneefan baba yace Yana so ma Aida yafi, shikkenan sai ayi tuwona maina, 🤣



(ai momy ko shinkafata miyata za'ayi mun fasa muma bamayi😏😏ki riqe danki mu riqe mutuncinmu 🤣🤣)


Anty jidda na zuwa tafara tattaba jikinsa, jikinta sai rawa yake, momy yanzu yaza'a masa?

Ina haneefan take? Ina tatafi?

Wayasan inda take jidda, nikam jiya na koreta ai

Innalillah... Momy meyasa Zaki haka?

Haba jidda kuma de haneef yarasa wa zaiso sai yar aiki? Haba jiddah

To momy tunda shi yagani Yana sonta Kuma shi zai zauna da ita ba shikkenan ba?

Ajiyar zuciya tasaki tace hakane, yanzu a"ina zamu ganta jiddah?
Ke yar dakinki ce Bata fada Miki inda taakeba? 🤣🤣

Momy tacemin daga kuje take, yar can ce

Cikin tsananin mamaki tace kuje!!!? Sannan kuma haneef yacemin sunanta haneefa, lokaci daya gaban momy yafadi

Innalillah... Jidda kadafa tunani na yazama gaskiya, nashiga uku ni Amina 🙆🏻

Momy sai cewa kike kinshiga uku, Wai meke faruwa ne?

Kanta da Dora daga gefen gadon da haneef yake zaune, tace Barni jiddah, jiri nakeji wallahi 🤣🤣

Saida tayi kusan minti uku a kwance, tadena Jin jirin tace jidda Ina tunanin yarinyar nan yar wajan baba ce

Wanne baba Kenan momy

Cikin fada momy tace baba de, mijin zainab qanwata me rasuwa ta kuje ha'a, Ana Miki magana kina ta dawo min da Abu baya🤣

(tab momy fa zata huce Akan anty jidda 🤣🤣🤭)

Anty jidda tayi murmushi tace momy kefa kika kori yarinyar Naan kuma ni yanzu momy saiki huce akaina?

Hannu ta daga Mata ✋🏻dakata Dan Allah jidda, kibarni da abinda nakeji 🤣

To momy Kinga ni Bana tunanin haneefa itace wadda kike nufi

Wai jidda tayaya Zaki fadi haka, ke bakiga yarinyar tana kama da hajiya hafsat ba?

Anty jidda tayi jimm sannan tace gaskiya ne momy, suna kama gaskiya Amma ita wannan tacemin babanta yarasu, namanta ma haka, Amma akwai uncle dinta wadda take gidansa, nikuma abokin babansu sajida ne, inama da number sa, zan Kira shi yanzu, sai kuje ku sameshi yakaiku inda za'a Samu haneefa, idan kuma Bata wajansa to sai kuje can Garin nasu, kuduba nasan bazata wuce waje biyun nanba

Nikuma zan zauna da haneef nakula dashi, insha Allah, Allah zai tashi kafadunsa, Allah kuma ya baiyana ta

Haneefa!

Haneefa!!

Haneefa!!!

Daga momy Har jidda suka juya wajan haneef suka bishi da kallo, lokaci daya qwalla tacika idon momy, Kinga ni ko jiddah, farkawa ma da ita yake farkawa abakinsa

Mukam mun shiga uku jiddah, taqarasa maganar tana Kuka

Anty jidda ta matsa jikin gadon ahankali tace haneef, Bude idonka nice jiddah

Cikin muryar rashin lafiya yace anty su momy sun koreta, sun koreta anty, wallahi Nima binta zanyi, Allah bazan zaunaba🤣

Anty jidda ta dafe Kanta, 🤦🏻‍♀haneef, kayi hakuri mana, tashi nahadama tea kasha

Anty ni bazan Bude idonaba, banasan ganin kowa, tunda suma basason ganinta

Kayi hakuri nacema, yanzu zasuje su taho ma da ita

Cikin sauri yabude idonsa yace da gaske anty?

Saikuma yaga momy, lokaci daya ya kawar da kansa gefe yayi shiru

Momy takama hannunsa tace haneef tunda kanason haneefa yaya zamuyi, zanje nakawo ma ita da kaina kaji? Kadena damuwa Dana

Momy da gaske kike?

Da gaske nake haneef, Amma fa katashi kasa wani Abu

Please Login or Register in order to submit comment