Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[8/24, 10:07 AM] SHALELAN BABA: 💕SHALELAN BABA💕

(Romance)



Story about luv❤

She is a very very poor girl HANEEFA, who fell in love with one person, he is rich man, nd beautiful, miskilin gaske, duk inda kake tunanin masifa tashi ta wuce nan

karku Bari abarku Abaya wajan Jin Yaya wannan story zai kasance

💕SHALELAN BABA 💕

💕SHALELAN BABA 💕

COMING SOON





Mrs Usman ce ✍🏻
[10/8, 10:31 PM] SHALELAN BABA: 💕SHALELAN BABA💕

(Romance)



To wannan karan alqalamin nawa zai fara tabo muku qauye ne

Ina Fata da burin kasance war mu tare my fan's, Allah Kuma yabani ikon gama wannan labari lafiya Kamar Yanda nafara 🙏🏻



Daga marubuciyar :



🌱DANA SANI🌱

(Ahmad&Feenah)



💞BURINAH💞

(Amal&Daddy)



💖WAZAN ZABA?💖

(Iman & Aliyu)



And now 👇🏻



💕SHALELAN BABA💕

Is loading...











Writing by Amnah El Yaqoub



Bissmillahir-rahmanirraheem



1&2



Tsugunne yake agabanta,hannunsa riqe da Kambos na yara Yan makaranta fari qal dashi Mai kyau, yayinda ita Kuma take atsaye, tayi tsananin kyau cikin uniform dinta na makaranta,wandon dark blue ne, yayinda rigar ta kasance white blue, Dan qaramin hijabi ne ajikinta fari wanda ya Qawata kyakkyawa fuskarta aciki

dago kansa yayi yadubeta da tsananin soyaiya da kulawa yace Shalele nah saka takalmin naki mana banaso kiyi latti wani malamin ya tabamin lafiyarki



Bubbuga kafafunta tafara aqasa cikin shagwaba tace Allah baba ni Bansan wannan Kambos din, baba yaufa zamu gama makaranta, nide saide ka daukomin wannan sandal din daka siyomin jiya, wannan dinfa satinsa daya baba, taqarasa maganar tana turo masa baki gaba



Murmushi inna Marka tayi, ta dafa kafadarta tace haba Shalele, yanzu menene laifin wannan takalmin,?



Rau rau tayi da ido alamar kuka

Murmushi Baba yayi yace "Kinga Marka dauko mata wancen din saita saka"



Duban ta inna Marka tayi tace to jeki cikin kwabet Dina zaki ganshi aciki saiki dauko

Da gudu ta juya tashige dakin inna



Ungo wannan takalman Marka, ki ajiye mata su a'inda yadace

Karba tayi takai shi cikin yar qaramar barandar datake gaban dakinsu, sannan ta nufo wajan baba da wani Kofi ahannunta



Daqyar tagano takalmin nata ta futo dashi, Kai tsaye wajan babanta ta nufa



Baba gashi



Yace to Shalele, Ina safar Taki?



Safar tabashi, ahankali yakama farar kafarta da yatsun kafar suke dogaye Zara Zara dasu gwanin sha'awa, saka mata safar yayi tana Daga tsayen saide ta Dora hannayen ta akafadarsa, Saida yagama saka mata sannan yasaka mata sandal dinta



Yace inyeee yanmatan babanta shikkenan sai hankali ya kwanta Ko?



Tafin hannunta tasa tarufe fuskarta alamun kunya 🙈



Murmushi yayi kawai, cikin ransa yana yaba tsananin hankali da nutsuwa dakuma uwa uba kunya da Allah yabawa yartashi qwaya daya jal



Kinga Shalele karbi wannan kwastadin naki Kisha, kada kitafi da yunwa, inji inna Marka



Babu musu tace to inna, tsugunna wa tayi, ta karbi kofin zata sha, baba yace a a Shalele nah, kawo nabaki da kaina



Daria tayi sannan tabashi kofin

Cikin nutsuwa yake Bata, Saida takusa shanyewa sannan tace baba naqoshi



A a Shalele nah, bakyason cin abinci, daure ki shanye shi duka, bazaki dawo gidaba sai Bayan sallar zuhur



Bata musu da mahaifinta, dole haka ta karba ta shanye da kanta, domin yaji dadi, suna gamawa, sukayi wa inna sallama tace to Maigida a dawo lafiya



Ya amsa da ameen, suka fice, suna Zuwa bakin kofar gidan, taci uban tuntube da bakin kofar gidan, dasauri baba yace yi Ahankali Shalele



To babana muje





Kekensa yadauko yahau sannan itama tahau kan kariyar keken, yaja suka tafi, basu zame ko'inaba sai makarantar su, dalibai dayawa atsaye afilin makarantar wasu Kuma a zaune, Daga saman ginin makarantar Naga an rubuta Government day junior school kuje local government



Tana sauka sukayi sallama dashi tayi wajan sauran daliban, yana tsaye yana kallanta, tareda jiran yaga shigarta ciki sannan yajuya yatafi gida Kamar Yanda yasaba duk ranar Allah



Tana tafiya tana waigensa ta nayi masa bye bye, mutane da yawa dasuke wajan ba qaramin birgesu sukai ba, irin wannan soyaiya ta 'ya da uba



Saida yaga shigarta sannan yaja Kekensa yatafi gida, yana shiga gida ya ajiye Kekensa agefe, inna Marka tana masa barka da Zuwa, ya amsa yana tambayar ta, Marka Ina tsohon gatarin nan nawa?



Tsananin mamaki ya Kamata tace gatari Kuma Maigida? Mezakayi dashi kaida bame faskaren itace ba?



Marka banasan surutu Dan Allah, tashi daukomin shi



Batace uffan ba tatashi ta dauko masa tabashi



Karba yayi, sannan yayi hanyar kofar gida dashi, binsa tayi Abaya domin taga mezaiyi dashi



Yana Zuwa wajan yafara saran kofar gidan nasa da gatarin, duk wani tudu da gangare Saida ya sai tashi yabaje qasar wajan



Haba Maigida, yanzu fisabilillahi kofar gidan nan kalau da ita Amma haka kawai kasa gatari kadinga saran kofa Kamar Allah ya aikoka?



Dagowa yayi, yana goge Dan gumin daya Tara yace, Shalele nah ce tayi tuntube da wajan dazu, shine nake baje qasar wajan, saboda kada naje Garin shige da ficenta, tasake wani tuntuben (😳🙆🏻)



Yanzu Maigida saboda Allah akan wannan shine kake ta haqilo kaida gatari?



Wato Marka Naga alama bakisan Yanda Shalele take arainaba shiyasa kike wannan maganar, to dazu datayi wannan tuntuben jinsa nayi Har cikin Raina, abin baimin dadiba



Um to Allah yabada sa'ah Maigida, tajuya tayi cikin gida



Wani wajan yasake kaiwa duka da gatarin yana fadin ameen Marka, batare daya kalleta ba



** *** **



Su HANEEFA manya, wato de Har yanzu ke bazaki hutar da babanmu ba Ko? Kinsa bawan Allah kullum saiyazo daukar ki Bayan ya kawo Ki da kansa



Wata Daga cikin qawayen ne tace majidah ba HANEEFA zaki Ceba, Shalele zakice, Wai Shalele saikace wata yarinyar goye maishan mama



Cikin damuwa da kalaman nasu tace yau naji jaraba, babanku Ko babana, Shalele shi nakeso danhaka dashi zaku kirani, bawani Haneefa, haka kawai ga sunan da babana yake kirana, Shima yanajin dadin sunan ne shiyasa yake kirana dashi, ai yasan da haeefan



Wata Daga cikin su maisuna nasiba tace, to maji magani, yarinya Gara ma kidawo da ainahin sunanki, bawani Shalele ba, Tunda girma kike kina qara zama yanmata, inba hakaba samarin Garin nan wallahi Raina ki zasuyi

Saikace wata jaririya Wai Shalelen baba



Itama tace eh naji Shalele na nakeso, ai ni Har yanzu inde awajan babane, to a yarinya ta nake, nida zai maidani ciki ma saboda tsabar yarinta da bazan qiba



Sabira tace wanne irin yarinya kike magana Haneefa? Ga qirgen dangi nan akirjinki zaki dinga kawo wa kanki yarinta, to ai kuwa Ana kaiki gidan miji zama zakiyi daram yarinya



Kafin tayi magana Taji saukar Dan karamin duka abayanta, dasauri tajuya, tana ganin fuskar me dukan nata tace Kai Kai kai fadila sani miye Hakan?

Gani tayi duka qawayen nata Suna Daria, nasiba ce tace Rabu dasu Haneefa, Wai so take Taji kokin fara saka breziya shine ta wayance da dukanki Abaya, ashe ke bakisan wannan sarar tasuba



Da mamaki Shalele tace wacce irin brezia Kuma Ana zaune lafiya?



Still nasiban ce ta dubi wadda tayi dukan tace fadila to kinji de abinda Shalele tace, babu ita ba brezia yanzu, inajin sai anyi auren mijin nata zai aunasu da kansa, idan yaji adadin girmansu saiya siyo mata wadda zata mata









Shalele zata sake magana aka kada musu qararrawar shiga aji, danhaka Bata Cewa nasiba da fadila komai ba sai harara data bisu dashi, suka miqe Dukansu suka shiga aji



Suna zama malamai suka fara Raba musu questions paper, sannan aka basu umarnin farawa, daliban na kalla Dukansu bazasu wuce 14 to 15 ba



Suna gamawa kowa yafara futowa, kowa kagani yana dauke da Murmushi a fuskarsa

Kowa nagama futowa Aka fara photuna, maza da mata wannan yakira wannan ayi musu photo wannan ma yakira wannan

Suna murna Ayau sun gama junior



Sai can gab da la'asar suka fara watsewa, itama itada qawayenta suka futo, suna tafiya Ahankali, yayin da suke fira cikin nutsuwa,



Sunyi Nisa sosai akafa ta hango baba yana tunkaro su, cikin Murmushi tace to nide babana Yazo, sai anjimanku dalibai



Dukansu sukayi mata caaa kowa Yana tsokanarta, Daga me Cewa to Shalelen baba sai munkawo Miki ziyara, sai Mai Cewa to Haneefa sai anjima, Sabira cede ta Daga murya tace Yarinya ba sai anjima ba kihau keken nan de Ahankali wallahi kada kiyi wa angon ki asara, Dan me rabaki dashi sai Allah ehe mude ba ruwanmu



Gaba dayansu suka kwashe da Daria, itama murgudawa Sabira baki tayi, sannan tayi wajan babanta, ta Dane keken suka nufi gida, suna tafiya baba yace,Shalele nah ya jarabawar?





(wannan page din na farko zan tura shi akowanne group, duk group din dasuke so naci gaba da sambado musu, sai sumin magana 💁🏻💁🏻💁🏻💁🏻💁🏻)






Mrs Usman Ce✍🏻
💕SHALELAN BABA💕
(Romance)


Writing by Amnah El

3&4

Tayi dadi baba

To Shalele nah yanzu Kuma sai hutu Ko?

Eh baba sai mun gama hutun sannan zamu shiga ss1, a lokacin exam dinmu ta futo

Hankalinsa yana kan tuqin keken dayake yace Ai jarabawarku na futowa kokari zanyi in sauya Miki makaranta Mai kyau ta kudi, ke inda Hali ma makarantar kwana zan kaiki

Dasauri tace a a baba, nikan banaso nayi neda dakai da inna

Murmushi yayi yace to ya zamuyi Shalele nah, neman ilimi aiya zama dole, keda kikeso kiyi ilmi me zurfi kizama lauya, Ko bakyason ki ganki acikin wannan babbar rigar baqa, wadda lauyoyi suke sakawa,?

Inaso baba, Amma ni Bansan yin nesa dakai Ko kadan baba, sannan baba bakada kudi, Kawai zanci gaba dayin day din

Yace Shalele nah

Ta amsa na'am baba

Kiyi wa babanki Addu'ah, Allah yahore masa kinji?idan inada Hali zan Iya kaiki Har qasar qetare, kije kiyi karatun ki, nasan bazaki bani kunya ba, saboda nasan irin tarbiyar Dana baki

Murmushi shimfide asaman fuskar ta tace to baba Allah yahore

Amin Shalele nah, suna tafe Suna firar su Har suka je gida
Suna Zuwa gidan tashige da gudunta ta rungume inna, itama cikin Daria tace oyoyo Shalele nah, to Yaya jarabawar? Allah yasa de kinyi da kyau
Nayi inna, yaude gashi mun gama junior, saura Kuma senior insha Allah

To Shalele Allah yasa adace, Allah ya dafa Miki, kinji yata?
Bari nakawo Miki abincin ki

Tashi tayi ta dauko mata abincin ta, ita Kuma ta shinfida tabarma a birandar tasu ta zauna akai domin taci abincin

Baba ne yashigo ya jingine kekensa agefe, inna tace maigida ga abincin Naka fa, abude shi yanashan iska ne?

Yace a a Marka, bani nafita dashi waje, Naga Malam yahai a zaune, saimuci tare

Dauka tayi ta meqa masa, Yadubi Shalele data bararraje atabarma tanacin abinci, yace Shalele nah Bana hanaki cire Dan kwalin ki bane?
Banasan barin gashi awaje fa

Cikin ladabi tace to baba,Saida takama doguwar kalbar datake yawo agadon bayanta da ribom sannan tadauki Dan kwalinta ta daure kanta dashi

Ficewa yayi daga gidan yana Cewa Marka Dan Allah kisata tashirya da wuri saboda kada tayi lattin islamiyya, banason abinda za'a zo Ana dukan nan nata Kamar sun sami jaka

Inna tayi Murmushi tace to maigida za'a shiryata

Ta dubi Shalele tace toke kiyi ki maida hankali kiqarasa kije ki watsa ruwa kutafi

Kanta aqasa tanacin abincin tace to inna

Tana gamawa tashige wanka, Bata batalokaci ba tashirya, cikin uniform dinta, wandon ruwan toka, sai farar riga wadda tsawon ta yakai mata Har gwiwa, dakuma farin hijab

Sallama tayiwa inna tace inna natafi saina dawo, inna tace to Shalele a dawo lafiya, ayi karatu da kyau kinji? To inna tah

Tana fita taga babanta da Malam yahai maqocinsu, Har qasa ta tsugunna tana gaida shi, tace baba Malam Ina yini?

A a Shalelen babanta an futo? Tace eh Wlhy baba

To Allah ya tsare, Allah yabada sa'ah awajan daukan karatun

Kanta aqasa tace amin

Baba ne yatashi yadauko keken sa, tahau suka tafi
Suna tafiya,sunyi Nisa sosai, Bata saniba by mistek tasaka kafarta awayar keken, nan da nan kuwa jini yake disa Daga kafar Tata, dasauri tace wayyo baba kafata

Yana kawo idonsa wajan kafar Tata yataka birki, lokaci daya duk ya rikice, subhanallah, Shalele kice naji Miki ciwo, kiyi hakuri kinji yata

Ganin duk yabi ya rikice ne yasa ta boye jin zafi da radadin da kafar take mata, tace baba babu zafi ba

Cikin ranta kuwa kukan zuci take, saboda ita Abu kadan ne zai sata kuka, babanta ya riga daya gama shagwaba ta, gaba da baya

Haba Shalele ya zakice babu zafi Bayan ga jini yana fita Daga jikin ki, Bari muje chemist, kinji

Kan keken sa yajuya Daga hanyar makaranta Zuwa chemist, suna Zuwa tasauko suka shiga ciki, tana dingisa kafar

Cikin damuwa baba yayi masa bayanin komai, mai chemist din ya nuna mata kan benci yace ta zauna

Babu musu ta zauna, shikuma baba yana tsaye, kayan aikinsa yadauko, yakama kafar Tata zai wanke mata
Yana zuba mata hydrogen tafara yarfe hannu, tace wayyo Allah na Baba zafi, nan da nan sai hawaye

Shi kansa baban dayaga Yanda wajan yake kumfa nan take ya runtse idonsa

Mai chemist din ya kallesu gaba dayansu, shi sai suka bashi Daria ma, wannan Dan ciwon akewa wannan abun, ita tana kuka shi yana runtse ido, to ciwo ma akai masa haka inaga haihuwa Kuma?

Saida yagama wanke mata kafar tass sannan yadago kansa cikin Murmushi yace Alhaji nagama, sai a sannan baba yabude idonsa yace to nawane kudin?

Yafada masa kudin, baba yabashi kudin sa, sannan yasai mata magunguna yazuba musu aleda, maimakon yabashi saiya miqa mata yace gashi qanwata riqe wannan kije waje kijirashi, ta karbi ledar maganin tafice tana dingishi

Tana fita, mai shagon Yadubi baba yace baba Dan Allah a kiyaye gaba kada tasake jin wani ciwon, kasan karfe bashida dadi, idan akwai datti tetanus zai iya shiga cikin ciwon nata, Kuma koba haka bama ita mace ce, Yawan Hawa keken bashida amfani

Ajiyar zuciya baba yasauke yace to likita insha Allah za'a kiyaye
hannu Mai chemist din yabashi suka sake sabuwar musabaha sannan baba yafuto Daga shagon

Suna Zuwa wajan keken, yace Shalele nah zaki Iya Hawa kuwa kona doraki?( 🤣😃)

A a baba karka damu zan Iya wallahi

Karka to mata yayi Bayan yahau yace to hau muje, tana Hawa yace mu tafi gida Shalele nah, yau Kam babu inda zakije, ke gobe ma haka, kiyi zaman ki a gida kihuta, zanje makarantar inyi musu bayani gobe insha Allah


Comment Anda Sharhi please 🙏🏻



Mrs Usman ce ✍🏻

💕SHALELAN BABA💕
(Romance)

Writing by Amnah El

5&6

Suna qarasawa gida ya tsaida keken, yakamata ta sakko suka shige ciki
Inna na zaune abakin wuta tana girkin dare cikin firgici tace subhanallah menake gani haka maigida? Meyasa meta?

Yana riqe da ita yace Marka babu lokacin amsa, yanzu de muje ki bude min dakinta ta shiga tahuta
Dasauri taje takama qyauren dakin sannan ta dage labulen tace shigo da ita Malam
Shiga sukayi dakin, abinda yabani mamaki shine duk da dakin qasa ne,Bai rasa kayan kallo da wata dundumemiyar katifa ba, agefe Kuma ga yar tsana nan ta wasan yara manya guda uku
Kan TV din Kuma Fina finai ne na cartoon dayawa akai
Banda wayarin din da aka ja mata a dakin Kamar wata yar kansila

Akan katifar ta kwanta, tace baba zanyi bacci yanzu

Yace a a ga magungunan da likita yace abaki, karbi Kisha saiki kwanta
Babu musu tasa hannu takarba tana runtse idonta ahaka Tasha maganin

Tanasha ta kife da nufin bacci

Inna tace Kinga hijabin naki ma jini yataba gefensa, kawo aje awanke Miki shi

Dasauri baba yace a a, karbi de kibayar dashi, Ko maqotane karbi kibasu, ita sai asake mata wani
Dama ai ya tsufa hijabi aka saka shi Har tsawon wata daya Kuma ai yaci duniya, sai ayi hakuri dashi

Inna tace to maigida tana fita Daga dakin, Shima fita yayi yace mata zanje wajan Malam yahai yarakani can cikin kasuwa, insha Allah yanzu zamu dawo

Inna tace to maigida a dawo lafiya
Yana fita Bai zarce ko'inaba Sai gidan maqocinsa Malam yahai, ya daukeshi suka wuce kasuwa, wajan masu Saida machine yaje yasiyo Sabo dal dashi, sai daukan ido yake, Daga nan suka juyo gida, inna na alwala taganshi yana kiciniyar shigowa da machine (😃😃)

Tsaye ta miqe tana daura Dan kwalin kanta daya kunce saboda shafar Kai datayi wajan daura alwala
A a Malam lafiya naganka da machine? Mezakayi dashi Ko acaba zaka koma ja? Yanzu Malam saboda Allah duk Yawan gonakin da Allah yabaka basu ishekaba saika siyo mashin kafara kabu-kabu?

Kansa yadafe da hannunsa alamun maganar Tata harta gundureshi (🤦🏻‍♂)
Haba Marka! Haba Marka!
Yanzu wannan tambayoyin dakika jeromin tayaya zan fara baki amsa?
To wannan mashin dakika ga naje nasiyo, bani zanyi kabu-kabu dashi ba, Shalele nah nasiyowa shi, saboda adinga kaita makaranta Ana daukota, munyi magana da Likitan daya wanke mata kafa dazu yace ita mace ce, yakamata tadena Hawa Keke hakanan, saboda gudun matsala
To shiyasa naje nasiyo wannan mashin, nadauka mata Yaron dazai dinga kaita makaranta yana Zuwa yana dauko mana ita, shikuma zan dinga bashi dubu biyar duk Watan duniya (😳🙆🏻 fan's)

Inna da mamaki yagama kashe ta atsaye tace Anya maigida? Anya maigida turbar dakake Dora Shalele akai kuwa me dorewa ce? Yanzu Malam duk gidan nan baka saka mana kayan kallo ba, Amma ita kasaka mata, katifar damuke kwanta haqarqarinmu akai ta tsufa, baka sake manaba Amma ta Shalele Bata shekara, Malam itafa mace ce, duk Daren dadewa gidan wani zata

Ajiyar zuciya yasauke yace, eh lalle Marka sai yau ta tabbatar da abinda nake zargi, Marka zarginki nake akan kulawar danake Bawa yarki ta tsaye Miki a maqoshi ya qarasa maganar yana Dora hannunsa awayansa
Wai shin, Shalele tarbiya ta rasa Ko nutsuwa? Addini tarasa Ko ilmi,? Tataba yi miki rashin kunya? Marka abinda nakeso ki Gane shine, zan Iya sadaukar da komai nawa saboda Shalele nah, ita kadai Allah yabani, Dan haka Marka, yakama kunnansa guda daya yace Iya gani....?

Itama tayi qwafa cikin fishi tace masa Iya qyalewa

Kallanta yayi yace Yauwa ashe kin fahimta, yasakai yabar gidan domin Zuwa masallaci sallar magrib

Tana Daga cikin dakinta tana jiyo maganganun iyayen nata, inda Sabo yaci ace tasaba da irin wanan fadan nasu, Murmushi tayi Ahankali tace baba da inna ta Kenan

Shikuwa yana idar da sallar magrib yadawo gida shida wata yarinya Amma ta girmi su Shalele sosai, inna Tana rumfa ta idar da sallah tana lazimi tagansu sun shigo, da mamaki tace a a Ramatu kece a gidan namu?

Tana Daria Kasa kasa tace eh Wlhy innar hanifa, nazo ganin jikin Shalele ne

Kafin inna tayi magana baba yace a a Ramatu ki fada mata gaskiya Cewa Zuwa nayi wajan mahaifinki Malam yahai na dauko ki, ki kula da Shalele Tunda ita uwarta tafara gajiya da ita

Murmushi inna tayi tace Malam Kenan, sannan ta dubi Ramatu tace Ramatu wuce ki koma gida kinji, kice Ina babar Taki, Ramatu Saida ta kalli inda baba yake taga yadaga Kai sama alamun akusa yake, sannan tace to inna natafi, Allah yaqara kiyayewa gaba

Amin, inji baba

Ramatu na fita inna tace yanzu maigida saboda Allah kaje Har gida kasako yarinya agaba saboda kawai tazo ta kula da Shalele? Koka manta zawarci take? Kabarta Taji danata yaran mana
, inde akan Shalele ne kayi hakuri insha Allah zan kula da ita, nayima wannan alqawarin

Sai a sannan yasakko Daga dokin naqin dayahau, suka cigaba da firar duniya

Da daddare Yan makarantarsu Shalele sukazo dubawa Ko lafiya yau basu ganta a Islamiya ba, malamai Sai tambayar ta suke, kasancewar yarinya ce ita Mai kokari da hazaqa, kokarin ta ne yasa dayawa Daga cikin malaman nasu take mutuqar birgesu

Bayan sunga ciwon dataji ne suka mata sannu tareda tafiya gida

*******
Shalele kafa ta warke sosai, taci gaba da Zuwa makaranta, Daga bangaren baba babu wani Abu daya sauya wajan Yanda yake nuna mata kulawa
Yau inna ta tashi da zazzabi sosai, akwance ta wuni, Shalele duk ta damu, baba ne yadauki machine din daya siyowa Shalele yakai inna qaramin asbitin Garin, suna Zuwa kuwa likita ya tabbatar musu da Cewa inna nada ciki harna tsawon wata uku da Rabi, baba Kamar yayi hauka Dan murna, itade inna Murmushi tayi, domin kuwa ta riga da tasan dama tana dashi, haka suka dawo gida da wannan daddadan labari, Shalele naji ta dinga ihu da tsallan murna, itama zata samu kanwa Ko Kani

Ko a Islamiya data Bawa qawayenta labari, mamaki sukai tayi, ganin yanda take murna, Kodan Bata ganin yaran ne a gidan su oho

*******
Tilin kayan wanki ne a hannunta ta futo dashi Daga daki, Daga murya tayi ta qwalawa Shalele kira
Shalele!
Shalele!!
Da gudu ta futo Daga daki kanta Ko Dan kwali babu tace na'am inna gani
Watso mata kayan wankin tayi tace gashi nan maza dauke kije ki wanke minsu gaba daya, ta Cilla mata nera hamsin, taci gaba d Cewa ki dauki kudin nan kifita waje shagon ubaliyo ki siyo kilin kiyi maza ki wanke su ki shanya

Shalele Bata kawo komai aranta ba dasauri ta dauka tace to inna, asalima ita murna take akan wankin da aka Bata kasancewar bayi take ba, Bata wani aikin fari bare na baki

Hijabin ta tadauka zunbulele ta fita taje ta siyo kilin din tadawo tahau kan wanki, ta nayi Ahankali harde ta ware tafara dirzar kaya, rana tazo tatarar da ita Har inda take sunkuye tana wankin, gumi sai zirarowa yake Daga kanta

Inna Tana kallanta

Please Login or Register in order to submit comment