Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dubu a gogi naga ashe shida ma tayi ban lura ba kai da Azumin nan nasha wahala mara misaltuwa. Duk na rame na lalace na fige sai ido a waje na bakin shi yana cewa kamar na mujiya haka hr sallah tazo shi kadai ya tafi kaduna kan ita zuba ido ya ce in shirya shiru sai ma gurin direba naji ya ce Madam Ke ba ki bi oga kaduna ba?Sallah a garin nan ba dadi duk Hausawa sun gudu garin su na ce eh sai ya dawo zan je kai ranar nayi kuka hr na gaji dan nasa rai. Kwananshi 2 ya dawo ina kwance ina jin shi ya turo kofata ya jeho wata leda baka mai dan girma ya juya, na tashi na dubu ledar kayan miyan ne irin kuka, Ku6ewa, da garin yaji da daddawa. Sai Kuma wata ledar mai dauke da wasu tarkace kamar magani sai wasu wasiku guda 2 daya daga momy daya daga Rahma, na rungume wasikun ina kuka na soma duba ta momy. 'Yata ina fatan kina lfy? Na yi kokarin jin Muryarki amma soja ya ki, Sai ina ganin kamar yana wahalar da ke ne kada ki damu ina nan zuwa cikin watannan zan sa Aliyu ya rako ni in ganki. YA JIKI? Ya ce Kinyi 6ari kwanaki Allah ya ba da mai amfani sannan ga dan tarkacen mata nan duk kisha da madara sai na zo. Momynki. Shiru nayi ina mmkin Ya Umar,wai nayi 6ari? Kai namiji sai a barshi na ji dadi in Momy tazo kafarta kafata, ba zan zauna ba. Bayan na krnt ta momy, na kuma warware ta kawata Rahma domin itama naga abn da ta kunsa. Sis.....Asma'u Nayi Yi kewarki da zaton ki, Musamman a mkrnt Malamai sun kewarki hr gobe na kan yi kuka idan na kalli gurin zamanki a cikin ajin Islamiya,sai dai na ka ji dan dadi in na tuna Ya Umar mutumin kirki ne rike ki amana. Munyi jarabawa yanzu muna SS1 kuma ni da Ya Usman mun shirya don hr iyaye sun shiga ciki.A kwai labari da yawa sai kin zo bikin su anty Aina'u sauran sati 4,nasan kin sani. Aminiyarki, Rahma. Haka wasikar ta zamar min tamkar Kur'ani, kullum sai na karanta ina kuka ina fadin nima ina kewarki Rahma, ina kewar mkrnt.Rayuwa ta haka ta ci gaba da tafiya hr ranar wata Jumma'a na zauna kenan a falo sai ga shi ya shigo tamkar an jeho shi na tashi da sauri zan gudu dan ya min gargadin kan zaman falo,wata rana ya same ni ina zaune ya min duka sannan ya ce duk randa ya same ni sai ya harbe ni tunda bai hada falonshi da sunana ba. Don haka yau ma na ruga daki ina kokarin rufo kofa sai gashi ya banko na tsaya jikna na 6ari shi kanshi yasan ina matukar tsoronshi sai dai ya ce haushen da nake bashi ko zai kashe ni ba zan ce yayi hkr ba sbd tsabar taurin kai,ya ce ke da karfi na dube shi ya ce bari kiji ina ma dai zuwa ya fita can sai gashi da wata 'yar bindiga nan na soma sakin fitsari sbd tsoro nasan zai iya harbina, ya saito ni sosai,sannan ya kauce ni ya harbi bango nan na dauke numfashi na na fadi tare da salati ga zatona ni ya bindage ashe bango ya harba suma nayi sai da ya debo ruwa ya zuba min na farka ya san na kara tsorata dashi ina da daga kwance ya ce tashi na tashi da sauri ya ce Momy zata zo gobe kinga bindigar nan?na kalleta ta cikin tsoro ya ce yanda kika ga na harbi wannan bangon ya huje haka zan huda cikinki in har kika yi kuskuran gaya mata halin da kike ciki. Hawaye na zuba na ce bazan gaya mata ba,ya ce ke ki ka sani dai ya fita kai Soja babu imani. Duk da haka nayi murna da zuwan Momy da wuri na gama aikina ya ce yau ban da wankin mota,nayi wanka nasa sabon kaya wani yalon leshi mara nauyi,dama tun da nazo kayana uku ne, daga jallabiya sai atamfa da wani matarial wannan yayi datti in sa wannan,to wace kwalliya zanyi tunda nazo ko bakin gate ban taka ba,ban na ta6a ganin kowa ba daga shi sai masu gadi suma in sun zo daukan abncu,inazaune a bakin gado ina tunanin yanda zanga Momy,oh Allah yau zan ga na gida. Kiran Ya Umar na ji "'Ke!" Na taso da sauri ya dube ni na dan lkc sannan ya ce to haka yayi saura ki je ki saka sarka da dankunne kiyi shafe-shafen ku na mata,bana son ki yarda Momy ta gano halin da muke ciki za ki koma kwana dakina hr ta tafi na dube shi da sauri ya ce kada ki zata ko na soma sonki ne ba zan ta6a sonki ba,ya ci gaba zan daure in ci jagwalgwalonki hr ta tafi sannan yanzun in kin gama ki zauna nan falo zanje na dauko su,zan kara tuna miki kada kiyi ka sadar sanar da Momy komai dan nasan kanki zata yi fushi dani kamar yanda kema zan ha da ki da naki iyayan duk da ke baki dama d fushin su ba,amma ki sani in ba kya gidana sai dai ki shiga dny ce war Mahaifinki,ko fa da ki ka yarda Momy tayi min Allah in ta tafi zaka gane kuskuren ki,ya tafi dauko su haka nayi jigum a gabn madubi ina kallo kaina ni Asma'u wannan shi ne a dake ka a hana ka kuka,lallai ban da ya ki ina ganin har da sharri ake koya ma Sojoji, Da na yi kwalliyar sai naga nayi kyau,na juya kwayar idunana da Ya Umar ke kiran su na Mujiya irin idanun nan ne da kwayar su ke da girma kuma sun fito na sha jin mutune na cewa suna son idanuna,haka Suraj na saka sarka da dan kunne na koma falo na zauna ko in ce nadofanu ina kallon tashar Aljazira ina zaton ahi ne yake kallo ya tashi ya tafi dauko su. Sallamar Momy da Aliyu da Ya Umar ce ta dawo dani daga kallon,da gudu na taso ina tsalle na rungume Momy,itama cikin farin ciki ta ce 'yata Asma'u oyoyo 'yata,sai kyma naga ta ciro ni daga jikinta ta tsaya tana dubana, ta kai hannu wuyana ta shafa ramin kirjina ta ce wannan kashin wuyan fa? Na dubi Ya Umar ya 6allo min harara nayi saurin fadin tun da tunda ya Umar ya amshe tunda tayi 6ari ne nima na kakaro 'yar fara'a na ce eh mana ba?tun lkcn ne kuma bani da lfy ne ai Momy ta dube shi sannan ta dube ni kin zubar da jini ne?Daga ganin jikin nan naki babu jini na ce eh na zubar na kama hannunta zo muje ki zauna,Momy na ce ya Aliyu sannu da hanya ya ce yauwa Asma'u Ya umar ya ja shi suka zauna Momy ma ta zauna naje da sauri na soma loda musu abnci da na sha kala-kala ga.farfesun kaji ga na kan rago ga farar taliya da miyan kwai ga jalof din shinkafa momy fadi take sannu 'yata da aiki duk namu ne? na zuba ma Ya Aliyu komai ga mamakina sai naji ya Umar yana cewa Madam sbd yau kinga su Momy watan kin manta da ni ko? Na yi dan yake na ce to me zan zubo maka? Ya ce sa min Farfesun kannan na zubo Mashi na koma kusa da Momy nima na saka cokali cikin nata.... Muna ci na kalli Ya Umar ya harare ni,Momy ni,Momy ta kalle shi sai abu yake kamar hararar wasa yake min yana yi yana murmushi,Momy ya ce me ki ka gani? Ta ce Harararta naga kana yi, ya ce ai ita ta sani Momy da da ni ta ke cin abncin yau gulma ta tashi wato ta gan ki,ai Momy za ta ta fine .Ni dai sai naji abn wani banbarakawai wai namiji da Suna Hajara. Yanda na lura ya ji dadin naman kannan sai da ya kara,kun san yin girki yau da gobe kan sa mutum hannunshi ya goge, don haka da ba ma yi a gida muna gani in su Anty Aina suna yi akan ce muje muna yi musu irin jajjage ko yankan albasa ko su Alayyaho,hakan yasa na riga lura tunda ina sha'awar girki shi ya sa yanzun ba ya ba ni wata wahala.Bayan mun gama na ja Momy dakin muna ta hira na tambaye ta Rahma ta ce ga ma sakonta nan na hotuna ta ce kema ki bata naki, da zumudi na amsa ina dubuwa ina fadin Allah Sarki Rahma ina naga hotunan da zan bata? Momy ta ce ba ku ta6a daukar hoto ba ne? nayi saurin tuna gargadin Ya Umar (Da har zan ce yaushe na samu 'yancin yin hoto)Amma sai na wayance na ce mu da ke cikin bariki anya ma muna da gurin hoto,ban dai sani ba. Momy ta tsuramin Ido ,Anya dai zamannan naku da soja Baya takuraki kuwa? Ni Naga lalacewar tayi yawa Ne Nace bakomai momy Ko mai yanamin daidai gwargwado, abincima sai yadda Naso zanci (A Raina Nace farin abinci bazan Kona namanshi ba; dakanshi yake duba store da firiza duk Wanda babu xai kawo haka drinks)tace shin kodai yana matsamiki ne? Nace a'a momy sai dai Ko Xaki rokarminshi yasani makaranta,Amma fa kadafa kice ninace fa Sabda namishi magana yace a'a yace to Xan mishi (a Raina Nace Allah dai kasa Yaya ya ambience). Munyi magariba da Isha'i tuwon semo na tuka mana da miyar kubewa busasshiya Ga man shanu dayazo dashi damuna cinema yake cewa momy baban farida nema yabashi sanda yaje yola.momy ta tabe baki haryanzu haryanzu kuna tare da farida? Yace to momy aydama ba matsalar tabace babantane kuma yasoma sakkowa, momy tace to kudai kuka sani nidai bazan yarda da batun wani Aure dai yanxuba, sai Naga kamun ludayin yata a gidan nan, ya cire hannu a cikin abinci Kamar ya'ya momy? Ta ce to ganin farko da zanyi Mata banga tasiriba,ta Kara baki ta rame sai idanu a warwaje .yace tonidai gatanan Ki tambayeta me nake Mata? Don ba a satina hudu da auranmu kikaxoba kafin tasamu cikin Nan Kinga Kyan datayi Ga kiba Kamar tafashe. Amma Tana samun cikin Kullum muna hanyar asibiti, kaina sunkuye anata keramin karya, momy tace kodai batacin abinci ne? Yace tanaci Badai Kamar daba momy tace itama haka tace Toh Allah ya kyauta sukace Ameen. A kitchen ya sameni Ina harhada wanke wanke yace ke dakina zakizo kuma karki soma zuwanmin da datti batare da yajira amsa taba ya fita. Bayadda zanyi haka nayyo wanka nashafa turare na dakko kayan Bacci nasaka dama bantaba saka rigar Bacci ba mai ya, na taje gashina danma Allah yasa gashina mai kyaune Amma da yadda ba kitso ba saloon din Nan ay da ya lalace na daure da ribbon na daura zani akan kayan nasaka hijjab na zauna kusa da momy tace tashi Kije gurin mijinki nima Bacci zanyi saida safe Haka naja Mata bargo nakara Ac najamata kofa daidai kofarshi Natasha duk tsoro ya cikani kilafa Yau nasha bakaken maganganu ,na tura kofar ahankali tamkar mai tura kwai na leka yace shigo mana cikin tsawa ya fada, nashiga na Maida kofar narufe natsaya Ina raba Ido Ina kallon shahararren dakin mai mutukar tsari komai nadakin sky blue ne, tundaga gadon har shinfidun xuwa kafet da labulaye zaune yake da Riga da wando na Bacci a gaban computer idanunshi sanye da glass, nazauna kasa gefen kofar Ina karema dakin kallo hoton wata kyakkyawa nagani Tana sanye da bakar jallabiya ta rufe kanta da gyalen, Nan kuwa na tsuramata Ido tamkar jinsin larabawa kusa da hotonta Shima nashine yayi kyau cikin kakin sojoji, bansan yaxo kusa daniba sai dai jinsanayi ya shakoni cikin hijab ya ruko wuyana yajani har gaban gadon, yasaka hannu ya ciro hoton wannan matar yace rike na rike da sauri yayi kasa da murya. Matata kenan farida, yaki ka ganta? Gaya min? Da sauri Nace Tana da kyau Nace shigarfa? ta menene? Nace ta mutunci, yace to mutuncin ya mace kenan shigar musulunci ba irinkiba ya Maida hoton ya dauki filo ya wurga min can sakon gadon da bango je can Ki kwanta Sbda gadona bana kazanta bane. Na kwanta da hijabina sbd sanyin AC na shi yayi yawa.Can cikin dare na farka sai na ganshi yana ta nafilfilu daga gurin da nake ya juyo min baya ne,na tsura mishi ido.Ya Umar yana da kyau ashe yana da Ibada sai dai mugunta,o Allah ban koma baccu ba har sanda naga ya gama ya kwanta,ya dauki waya ina jin shi ya lalubo abar son tashi hira suke ta masoya ina zaton ana nema take gaya mishi zata je fatakot dan yin shawara da Anty Amina game da batun Auran su,shima ya nuna jin dadin shi da yin haka sunyi sallama in da yake ce mata ta yu mafarki mai dadi yana kashe murya tare da kwantar da ita,hr mmkn shi na riga yi, bacci ya sace ni naji an shure ni na tashi firgigit! Tashi kiyi sallah har naje Masallaci na dawo kina nan kina aikin bacci,tun jiya ko juyi ba ki yi ba,kina ma sallar kuwa? na daga kai alamar Eh. Na tafi ina mmkin ashe akwai Masallac ni dai bn ta6a jin kiran sallah ba,naje zan shiga bayin shi ya ce wa?Maza na ki yanda cututtuka suka cika gari? Na ta fi na yi sallah sannan na gaida Momy na shiga kicin.Satin Momy daya suka soma shirin tafiya,kan su tafi sai da ta ce lallai ya Umar ya nemar min mkrnt ya ce zan shiga amma sau mun koma Abuja,sbd nan duk sai a hankalu,mkrntn haka su Momy suka tafi suka bar ni da kewarsu,na koma kamar da uban aiki ga masifa in nai kuskur naci duka da gwale-gwale cikin haka rannan ina fashin sallah na kira masu gadi ta hanyar dannan kararrauwar kar6ar abinci su,daya yazo na bashi naira 500 na ce ya siyo min always,kudin d Momy ta bani dubu biyu,ya dawo kenan sai ga Ya Umar ya tambaye shi menene? ya zo nema ya ce na aike shi ne ya amshi sakon ya shigo dashi ya duba yaga always,ya ce dama su kike aiki siyan wannan abn? Na ce na'am ya ce ina wasa dake ni,ina ina miki mgn kin ji sarai ki dinga wani na'am sai kin sani na ce au ba da shi nake amfani ba tsumma ne nake amfani,ya ce to yanzy ina kika samu kudi ko kin soma sata ne? Da sauri na ce a'a Momy ta ba ni ya ce to bani su na ciro na bashi ya wuce,haka na zauna gidan nan kullum addu'ata Allah ya kawo karshen zamana a gidannan. Ni ban sani ba ashe tun da Farida taje gurin Antynta Amina ta mata fa da ta ce ki zauna rayuwarki ta kare abn maza su in ba ki sani ba da kin tsufa shekarun ki sunja shi kenab sun gama yayinki gara ki je ki bude wuta ta ce to ya zanyi da shi na gaya mishi halin da kuke ciki zai goya miki baya to ko je gurin Baffan ruga wane ga baban nasu kuma ya bata dama ta turo mai sonta nata don haka ta kira Sojanta kuma ya amsa sun gana da Baffan kuma an ce tura manya yaje ya samu Abba,Abba ya ce ba ruwanshi da wannan mgn,sai ya nufi gurin Alhj, Alhj kam ya goyi baya shi nema ya shirya ya nufi yola inda aka yanke mishi sadaki dubu dari nai ga tsadar ta ba tunda ya san zauki Amarya dal a leda ana mishi tunanin an saka rana wata 4 a lissafe september kenan biki zai kama. Duk da gargadin da momy ta yi ma Ya Umar ya barni in zo bikin su Anty Aina sai ya ce mata to tana tafiya ya ce in dai ban yi kiba ba ba zan je ba.to ban ma san takamaiman lkcn bikin ba shi dai nasan yaje.A kwna a tashi gashi mun shiga October shekara daya da wata kenan da yin auranmu kuma lkcn ne ya Umar ya gama course din shi tun dare ya ce min na shirya kayana washe gari muka dauki hanyar Kaduna a mota.Direba ya jamu ya mu gun ja min kunne kan cewa kar na sake aji wata mgn a bakina,ni dau farin cikina zan je gida.. [1:53PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----16 Duk da ba sona iyayena suke yiba,hakan ba xai hanani shiga na gaishe su ba.mun cika mota da tsaraba sai gurin isha muka iso duk da shegen gudun da mukeyi tare da sammakon da muka yi amma sai da mukayi dare.wannan gari da shegen nisa da gudu na shiga gidan momy ta idar da sallah kenan na fada mata ina ta murna nayi sallolina kenan ina cin abinci yau dai jina nake tamkar na fito daga kurkuku.sai ga rahma ta muka rungume juna sai kuka, momy tayi tayi in shiga gidanmu naqi nace saina huta ai suma basu damu dani ba, da yanxu ko yara ne sun turo, in ina wannan maganan momy dry take min tace quruciya ce, haka sanda taje tana ji ina tambayar kowa ban tambayi yan gidanmu ba, tace baki tambayi su mama ba, nace bayan qilama basuce a gaishe ni ba? momy tayi dry tace sunce a gaida ke mana,dakin antx amarya na kwana ta ciromin sababin dunkuna wai inji ya umar kada nayi kada nayi amfani da kayana, na gane hikimarshi dan kada ace baya min dinki.washe gari na shiga gidanmu bayan na karya. Hawaye taf idona bansan ko kunan menene ba, haka suka xagaye ni suna min sannu dana shiga dakin mama ina ganin ta na saki kuka, ita dai kallona take nasan raman da bakin dana qara take kallo, yan gidanmu duk sunyi qorafi kan ramata, nidai bakina qanin qafata inji yan iya magana,ina can har dare na tashi na dawo.momy ke cemin ashe ya umar xai yi aure? duk da ba xaman dadi muke ba saida naji daban,nace ai banma sani ba, shine take ban rabarin sunqi yarda alhj ne mai shige mishi gaba nace Allah sanya alheri kada ki damu momy danni babu matsala,nidai ki mishi xancan krt na tunda ynxu abuja xamu koma ni konan kd ne ma ya barni.momy tace a'a babu batun kd yaxo dai ya min magana daya in baxai saki mkrt bane yamin bayani. ya umar ya sha fada gun momy na cewa bai gayan xancen auranshi ba, duk da yayi qaryar cewa baya ran raina ya baci ne,shi yasa yaqi gaya min haka nan tasa shi ya sai min waya mai kyau bansan yana qera gida a kd ba saida momy take cemin ai yanxu an yanke shawara inya gama gininshi na badarawa. In ya gama gininshi na badarawa nan xa'a min daki,nace au momy dama xa'a min daki? tace xa'a a miki man cae dinma ai shine yaqi,yace a bari sai kun dawo nan arewa naje gidansu anti aina da gidan salima da fatima. rahma ce ta rakani,randa xamu gaida momynta mun ba ta guri layinsu suraj ance tunda kika yi aure iyayanshi sun rasa gane kanshi, amma sun maida shi krt malesia, nace xaije ya qara lalacewa kenan, agaban suma ya bi mata bare wata qasa? tace lallai kam, nace ai ni inda ya suremin daya nuna yanasan jikina, kinsan fa nan duniya na tsani namijin da xai nuna yana san jikina. rahma tayi dry tace da kenan yanxu ai dole ki sakarma saja.na dubeta wane wai ya umar um ayi sha'ani dai kawai, tace da fatan ba gudun miji kike yi ba? nace rahma dama ina so mu kebe kiji damuwata,sbd anan duniya kece mutum daya dana ke fadama damuwata, kamar yanda kema nasan duk damuwarki, tace hakane, na kwashe komai tsakanina da ya umar na gaya mata sai da tayi kuka,dan tausaya min sannan tace cabdi yanxu tao ke a wace tuqa kike, Kada fa kije gashi yanxu shi da matar shine suyi ta cin xarafinki? nace ai ina ganin xan gaya ma abba ne qila ya kashe auran nan tunda sam baya qaunata, bakiga yanda na dawo bane? tace yanxun ma aikin danyi kyan gani,amma batun gaya ma abban shi ba ita bace mafita,sbda yana nuna yana kula da ke sannan yana nuna sanki gaban mutane, ta ki barshi shi da Allah ba azzalumin bane,akwai ranar qin dillanci yanxu dai ki sa krtn ki samu ko can abujan ne,in kin tafi ka kya gidan ma bare kiga haushi,in kin dawo kina daki,nace Allah na tuba rahma haushin me xanji naga nifa ba sanshi nake ba ina ruwana da matarshi? tace to sai abu nagaba.addu'o'ikin shagala da yin nafilfilu,nace acan ina san tashi amma ba xan iya ba naci aiki na gaji kamar jaka, tace yanxu sai ki tashi kiyi ta addu'a,Allah ya kawo miki sauki Nace hakanne magani na gode. tace,ai ni ma xan dinga taya ki addu'ar, Allah ya sani ina sanki da ya umar saidai kuma yanda Allah yayi ba makawa, na harare ta sannan nace dube ki kema xaki shiga layin masu cewa yana birge su ko kuma yana da kirki ne? tayi dry sannan tace baxa ki gane abin da ake nufi bane.momy ta matsa mishi da maganar mkrnt, hakan yasa shi nema min ta kwana gayamin yake wai shi ba xan je in hana shi sakewa da amaryanshi ba,gara in tafi ta kwana.sannan yace turkish na kaiki, in har baki tsaya kinyi krt ba Allah ba xanyi asaran kudina ba, wuya xaki sha kin sanni,kuma kika yarda kika yi wani abu na bata suna ko kibi maxan da kika iya dan akwai maxa a mkrnt saina saka bindiga na dauke ragowan nunfashinki duk mu huta,saura kuma idan momy tace kina san mkrnt kice a'a ki gamu dani.shi ke surutunshi amma ni ina maimaitawa ne a raina ina qarawa turkish ni asma'u a turkish? cab! komai yana da hanya,amma da kamban sa rai ba.momy kam tayi fadan yaya xaikai matar aure mkrnt kwana? nace nidai zanje momy inason ta Allah.momy ta yarda cikin kwana kalilan ya gama min komai yace ya aliyu ya kaini momy taki yarda ta matsa mishi saida ya bar komai ya kaaini. da duk abin da dangata yake tafiya dashi makarantar saida komai ya kammala sannan suka tafi don haushina ko sallama bai min ba, ya alyune muka yi sallama dashi na zauna bakin gado ina kallon dakin namu kato ne mai dauke da gado 4 mu 4 kenan . dakin ga kafet labulaye ga ac ga kumafankalafyayyun gadajantamkara gidan uwarkaniko gidanuwatama ban da kamar shi saurn 'yan dakin suna gurin wasanninsu domin yau lahadi duk daliban na. ga suna gurin wasanni. cangurinsha biyu da rabi saigasu sun shigo duk sa'nninane gasu masu kyau, suka bi ni da kallo nima sunake kallo,suka kalli kayana dake lode gefe daya suka kalli juna. dayar ta taso ta zauna gefena tace sannu da zuwa turkish, dyar dake can itama tazo sannu da zuwa wannan dakin namu, itako dayar gabana ta tsugunna tace shin 'yaruwa yaya sunanki? nace ni asma'u ahmad , kufa? ta gabana farar ciki itsce ta soma fadin sunana Amina turaki, mahaifina mataimaki nega shugaban kasar nan, ta gefen dama tace ni ko sunana bilkisu salis marfa, mahaifina shine ne gwamnanjigawa a yanxun ta gefen hagu tace fatima shehu, ni daya ce daga cikin jikokin shehu barno mahaifina shahararren dan kasuwane. da fatan zaki saki jikinkidamu tare da bamu goyon baya mu zama aminai,nce hakana fiso kun tabajin inda zaman makaranta yafina gida? is gurina kan na hada watana maida jikina nayi kyau red house duk muke dasu mina haka muke. kiranta tuni house captain ta zabeni a saurauniya, duk da kyawawan makarantar kokarina yasa kawayena like min, har ma da yan class ss1 n shiga lokaci guda sunana ya koma sarauniyar , duk cikin mkaranta muna da abokai maza yan class duk da bana shigemusu amma muna taimakon juna. zama da su mina yasa na goge har na manta da duk wani bacin rai,ban taba tunann akwae ranan da zatazo har inyi dariya ba, dana zata dariyata takare . ashe bahakabane, yau gashi masifataa ta dawo yanga da tsiwa duk sun dawo,dama gasu mina 'yan jan aji sai nace mana group dinmu yan jan aji mun cika girman kai. bana mantaa lokacin inter housee na yarda naci sunan queen.wayyo Allah shigar da yan red housesukayi da shirin da captain dinmu ta min zuwa farentinmu, mun burge mu nemuka zo na daya.ya aliyu da ya usman ne sukazo min su kansu sun yaba da shigar queen. mune mukazo na daya sunce min ya umar ne ya turo su dan an mishi waya ana son iyayenmu suzo muyi a gabansu, shine ya turo su, don shi suna ta shirin biki yana zarya tsakanin yola , kd da abuja sunyi kayatccen biki irin na masoya , amarya tasha kayan matsi duk dan ta hade kada ango ya gane wani ya riga shi bin hanyar. akwatina 12 dam da kaya masu tsada haka aka diba zuwa yola, a ranar jajibarin daurin aure suka shirya wani shegen lunchin kusan duk wani saurayin ta ko nace abokin shashashancintaya halarta in ka dauke alhaji sambo wanda kishi ya hana shi zuwa, kuma yace to zo suyi na ban kwana kafin nan da ta tare gidan mijinta, inko taki zaiyi yanda mijnta zai gane. haka nan duk ya daga mata hankali gurin lunchin din sai waya yake mata . ango ya damu da tambayar wake ta kiran haka? tace mutane , ta kashe wayar. da dare suna tare da sojan ta har zuwa sanda ya tafi masauki sannan ta kunna waya. alhaji sambo ya kira yace ta rufa ma kanta asiri tazo yanzu inko ba haka ba zai shirya mata tuggu, dole taje gareshi cikin wannan daren ya kwashi garar da akayi wa ango tana ji sai da safe ta dawo gida, bataso haka ba duk da yawan kudin da ya bata , haka daai ta kara wasu 'yan shirye shirye , an daura auren bayan sallah azahar kasancewar ranar asabar ce, ya umar jin shi yake yau tamkar sallah sunyi dinner katafariyar dinner da abokanshi suka c burn shirya mishi tun bara yace musu auran ya mutu su bari sai zai yi wani su al-amin manyan abokai sai yanxun suka shirya da ya umar sbd yanda yayi mishi tonon silili lokacin. auran mu, yayi ta tura wa yayita turawa abokan su na ko ina da batun auran. son ya umar lokacin ayi komai a boye .amma sai alamin ya yayi ta mishi tallata a waya wannan ya kawo musu dan sabani sai fa yanxun daya wanke kanshi gurin bingimbyafi, yayi duka d aeso boki yayi agun. sai dai farida bata kwanta mishi ba, duk kyanta nashi gurin kyawu in ya cika yawa hadari ne. *amma sai al-amin ya yayi ta mishi tallata a waya wannan ya kawo musu dan sabani sai fa yanxun daya wanke kanshi gurin bikin gimbiya , yayi duk abin da akeso aboki yayi aagun. saidai farida bata kwanta

Chapter 6 of 16