Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ma ta mike suka fita,ni kam jikina ba karfi amma duk da haka na yunkura zan tashi jiri ya kuma yardani,ya ce min ke wace irin macacciyar yarinya ce??? Ki bari a daura auran mana kafin kizo ki tare, na mike sbd nan take naji karfi, na dube shi kamar zanyu mgn,ya zabga min harara,na duka da kai na fita ya rakani da dogon tsaki,dakin Momy na shige ina kuka tayi-tayi in gaya mata dalili naki,duk da kuruciyata ina jin nauyin gaya mata abin da ke tsakaninmu da ya Umar yanda take dawainiya dani an daura aure misalin karfe 2 gidn su Momy tankam da mutane,ni ko na kule can uwar dakin Momy ta shigo ta zauna kasa dani tasa hannu a wuyana,zafi taji rau ta ce haba 'yar gidan Momy wane irin zazza6i kenan? Ta shi kiyi wanka mana?Na ce Momy bakin ce baki gayyaci kowa ba?ta ce ai bn san wanda ya gaya musu ba ne,na ce ni sanyi na ke ji ba zan iya tashi ba,Momy ta yi tayi naki tashi dole ta barni na sha magani na koma na kwanta. Can zufa ta rufe ni da kaina,na tashi nayi wanka a bayi Momy na cikin daki ta shigo ta same ni nayo wanka ta ce yauwa ga Soja nan ya ce kizo ga abokan su na gurin aiki da su Al-Amin suna jiranki,ta tsaya na saka wani lallausan leshi fari mai fulawa blue ta bani farin takalmi da gyale da jaka na ce bar jakanan Momy. Momy tasa min zinari kirar Dubai ta feshe ni da turaruka duk da kasancewar ban shafa komai ba sai hoda ina fitowa mutane suka soma fadin kai Amarya ta hadu fuskata murtuk babu fara'a na ce Momy ina suke? Ta ce dakin shi ne ko falon baki ne je ki duba su Rahma suka shigo ashe 'yan iskan hr anko suka yi,kallon banza nayi musu, Shema'u ta ce kinyi kyau Asama'u na ce lallai Rahma kema kin shiga layin makiya na ko? Ta ce dana yi me? Na ce ga shinan hr da yin anko ko? Ta ce ayya don Allah yi hkr nayi mama ta dinka min zuwana kenan ko wanka da na kinayi Mama ta matsa min Shema'u ta ce mune kenan Makiyanki? To kije gida ki gani cike da 'yan uwana ne sa dana kusa,wata motar ma yanzun ta iso batun anko da kike yi namu dabn na su Mama daban,dn haka sai ki san makiyan naki suna da yawa naja tsaki a raina na ce kwaji da shi Momy ta leko ta ce Asma'u ba ki je ba yana ta waya wai suna falon baki na tafi tare da Rahma a kofar falon naga Al-Amin ya ce yawwa 'yar Amaryarmu kin 6oye ki zoga bakinmu suna son ganinki na ce gsky ba zan zhiga ba ya gaya min mgn a gabn mutane Allah zan rama na gaji, Al-Amin ya ce a'a ya Mafita muka daine abokan shi ne na can gurin aikin su, Na ce to ni wai ina ruwa na da abokan gurin aikinsu? Amin ya ce dan Allah ki taimaka in mun gama bikin nan lfy an fita kunyar mutane a san yanda za'ayi na ce ni dai in zaka taimaka min ya sake ni to,Al-Amin ba tare da wani tunanin ba ya ce to naga sun kalli juna da Rahma sunyi Murmushi na ce menebe na dariya?Harsuna hada baki gurin fadin babu komai. [1:44PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----13 Suka shige gaba ina biye dasu muka shiga falon kato ne falon abba amma cike da mutane suna ta ciye-ciyen kaji da abinci ga kalolin juce naji kunya sosai da ganinsu kadan kadn ko ina a hankali al- amin ya ring zag ywa dni yana gabartarw muna gam gaisawa ban tsaya jin wani dogon turanc ba nayo waje ina jin sanda dayan da akace sunanshi suleman yace amarya sai kinzo zamu yi namu bikin a can ban dai tanka ba. rahma ma data rako. ni nan baya na barota . sanda na iso tsakar gidan nannaga momy suna tsaye da ya umar da wsu kannanta yana mata baynin shi zai tafi tare da abokin shi sbd akwai abubuwan da zasuyi kila karin girma ne.momy taace Allah ya taimaka kaga abbanku? yace yaana tare da mutane ne amma xan gnsh yanzun tace to amaryar fa? yace ai zamuyi sallama tana can gurin abokan nawa , momy tce gta can ta wuce ya faga sanda nazo na wuce su amma sai yace bai kula ba, ya dubeni har kun gaisa kaina na daga yace to shi kenan ni zan wuce a raina nace kafi ruwa tafiya ,momy tace amma dai ba sallamar kenan ba ko? kai da kace sai wani satin za'a kaita ai ka bar mata wani abun sannan ku dan zanta. yayi shiru canyaace ko ina cike yake,momy ta harare shi dakin ka babu kowa ai. Ya dube ni sai kije ina xuwa na tsaya momy tace jeki dakin nashi ki jira shi kinji yar momy? hawaaye na nazuba shar na tad, ina zaune kan kujera na bar hawayena su zuba son ransu tunda ni nama rasa me zanyi inji dadi kamar yaqi ya shigo dakin ya dube ni, har da sauri nace kije ganinan sbd son maza. Allah yay wadaran mace mar kamun kai mara aji, to bari ma in shaida miki bana ga kanki yana rawa ba, tsautsayi ne yasa kika aure ni gabana ya shiga faduwa, yaci gaba shawarar da zan baki itace kada ki soma gangancn yarda a kawo ki gidana,domin in har kika yarda kaddara ta sa kika zo yayi dan murmushin mugunta , sunanki sorry kada ki manta kn tab watsa min ruwan dai fasiqa ba, sallah 5 rana aikn hajj da ummura shida duk bana mance rokon mace ta gari nasan Allah ba zai barni ba, zai amsa minute na dube shi idona jajur nce ka sakeni nima ai naga ba sonka nakeyi ba da kace kar na yarda nazo inda kake mezai hana baza ka fadawa su momy da kanka ba? yayi murmushin mugunta , ni inaso na gama da mahaifana lfy ba zan basu kunya ba , kuma bazan ki jin maganar suba kuma abu na karshe da xan gaya miki shine,zan aiko da komai kuma xan tanadar miki masauki zan bada motocin da zasuzo daukan amarya amma duk dan na faranta ran iyaye na amma inkin yarda kn shiga motor nanhar kika kai kanki inda nake ? yaja wani tsaki tare da fadin hum-hum yayi wani guntun murmushi Ya saka hannu cikin aljihun wandonshi ya ciro rafar yan dari biyar ya jefe ni a fuska da ita yace ga sadaka bance kada kije yawo ba, amma ki sani zina da aure babban laifi ne koda yake ke laifin gaba kikaa saka shi ba baya ba, zuciya ta ta baci nima cikin dacin rai nace ni di ba mazinaciya ba ce sannan in har ka kawo mata zan shiga kuma zanso don Allah kayi tsirena ba laifin ka bane, iyaye na suka jamini na saki kuka mai karfi yace kada kisake ki tara min jama'a nan gurin domin in har momy da abba sukaji abin da yake faruwa har ransu ya baci to saina kiyafi nasu baci domin ni nasan zafin bacin ran mahaifa duk karancin shekaruna nasan , habaici yayimin kuma kafin nace komai har yayi waje don haushi, kifa kaina nayi akan kujera ina kuka, is yaje yace ma momy wai gani can ina kuka bai san dalili ba, kuma ya rarrashe ni nakiyin shiru. momy tazo tana lallashina wai inyi shiru yace ya lallashe ni nakiyn shiru, ko dai zn bishi n? nace a'a kaina na ne yake ciwo muka koma dakinta na sha magani na kwanta. haka biki ya tashi ana ta son barka, amma ban dani da ango, kullum zai yau waya gidan yace a bani in amsa sai ya dinga gayamin bakaken maganganu, niko inba'a gabanmomy bane sai na aje in a gabanta ne sai na daure in hakura, har kwana 8 dinnan kowa yasan na rame matuka, ya aiko da kudin jirgi na kusan mutum 3 banda nawa yace a ciki har antyshi a cikin masu zuwa kai ni ranar tfiya da safe nasha kuka, tun ran sstters day sai yau na fito waje gdan mu kuma tun randa momy ta kaini asibiti ban kuma shiga ba sai yau su anty ne suka kaini amin fada, duk sunmin nasiha su umma da hajiya mama kam cewa tayi in naga dama in zauna in naga dama kada in zauna ita dai ai ta gaya ma ya umr in namishi rawar kai ya min dukan mutuwa. Alhaji ya min fada da nasha, kuma yace umar da yake namiji yayi na*am da wannan auran dan Allah kada ni in basu kunya, inko har na zama sanadin mutuwar auranbai yafemin ba duniya da lahira sannan kada na doso garin kd da sunan aurena ya mutu ko kuma yaji kai ganin gida ma baya nemana sai nan da shekara, ina ta kuka ak sani motar har filin jirgi rahma ta rakani da kyar aka rabamu. mun rungume juna muna kuka har sanda muka isa garin kuka nake, motoci ne sukazo daukar mu gud 2 duk sojoji ne drivers din, dma 'yan rakiyar anty amarya ne sa hajiyar gidnmu, sai kanwar mama inna shatu. Katon gida ne mai dauke da manyan flat guda hudu ginin iri daya ne ya tsaru, na farkon shine na ya umar nan muka shiga ta qofar cikin daga nan sai ka isa qatan falo mai masifar tsari da kayan alatu, yana dauke da dakuna biyu dayan a kulle danyan a bude,muka shiga na budan gado ne mai kyau da sauran tarkacan shi sai toilet da wordrop muka xauna ina ta lura wani yaro ne kirista dan qabilan ibo ya shigo mana da abinci ya ce oga yace ku jira shi ya fita.sun ci sun sha suka yi dani inci abinci naqi dole suka barni, inna shatu tace in sun tafi na ci nan muka kwana,sai washe gari da safe ya dawo ina jinsu yana ce musu legos yaje kuma bai samu gama abin da ya kai shi ba sai dare, shine yayo sammako jirgin qarfe shida suna karyawa suka soma shiri, kuka nasa suna ta lallashina shi da kanshi ya kaisu filin jirgi. farida ta xubama wayarta dake kan teburin gacnta ido,ga wani dogm tagumi da tasha, duk wanda yasanta yana ganinta yasan yau sai a hankali ba harka. Tunaninta daya yanxu sojanta yana can tare da yar iskan yarinyan da tsinannun iyayanshi suka xaba mishi,tana tsoro duk da yace sam baya qaunan ko ganin yarinyan tasan mace fa mace ce duk muninta musamman da ta tuna cewa ya sanar da ita yarinya karuwa ce bin maxa take yi danhaka baya sonta, inko xasu xauna tare tayi imani har ga Allah sai yarinyar nan tayi yanda tayi ta shawo kanshi ya saurareta. halama tana bin malamai, wani dogo tsaki da taja shi ya jawo hankalin alhj sambo dake ta amsa wayar shugaban masu kamfe dinshi yayi sallama da shi sannan ya dube ta yace na kula yau kina ciki damuwa farida,gaya min menene damuwar? kudine? ta ce a,a ta miqe tana cewa gida xan je yau ba xan dade a club dinnan ba. ya miqe shima xuciyarshi cike da yaudara idanunsa suna mata kallan sha'awa ya kama hannuwanta ya maida ta xauna, shin kin taba shan maganin damuwa? bai jira amsar ta ba ya balle hancin kwalbar giyar dake gabansa ya cika wani kofin glass ya miqa mata,amshi faridata duk wata damuwa ta duniya kinga maganita Cikhn xafin nama ta amsa ba tare da wani tunani ba, ta daga kofin sai data gama sannan ta aje ido ta tsura mishi tana ganinshi ya koma mata sojanta.murmushi ya ke mata irin wanda yake qayata sojan ya miqe ya kamata sannan ya dauki jakanta da kuma wayarta sai mota, tana ta mishi sambatu har suka isa gidan shaqatawarsa suka ci gaba da masha'ansu yanda suka saba,wal iyaxubillah.da safe ko sai gurin tara ta farka,jinta tayi wasai sai yar damuwar dan kadan, tayo wanka ba batun sallah ta sami alhj sambo yana karyawa dama shi mutun ne wanda ya ba ciki gsky da amana dan haka ga lodin abinici nan kala kala yaci wannan yaci wancan ya dube ta yar kyakkyawa ta kin farka? ta xauna da dan murmushi na tasg ya kk? yace lfy ba lau ba,da me ya faru kace ba lau ba? yace da farko wanene sojanki? kuma wanenf umar? ta mishi wani duba sannan tace menene? yace jiya na shiga gurare da yawa wanda ada baki bani damar shiga sosai ba,saida giya ta gaya miki qarya cewa ni sojanki ne tayi tsaki malam banasam binkice. Tunda dai ni ba matarka bace, kuma umar inka damu kasan shi to,ina mai farin cikin shaida maka shine xan aura. alhj sambo ya tsura mata ido.a ranshi yana raya aiko Allah bai qaddaro aure tsakaninsu ba, ta auri wani, baxai so su rabu ba, allah ya kaimu tace amin cikin isa.kuma daidai lkcn wayarta ta soma tsuwa alamar saqon waya ne ya shigo, ta ciro sai taga kiqan sojanta har guda ashirin da takwas tun jiya xuwa yau, koda ta duba sakon sai taga ban hakuri yake tare da lallashi yasan fushi ne ya hanata daga wayar amma ta saurari isowarshi yola nan da qarfe daya. ta dubi lkc qarfe goma ta soma tattara yanata yanata ya dube ta menene? tace babu komai gida xanje, yace bari inyi waya akaiki dan bai dace a matsayina na dan takara a ganni da mace ba, xai iya kawo min matsala ta gefen abokan gaba, tace bama sai ka kira kowa ba bari in tafi,ta gama shirya komai sannan taxo gabanshi yasan nufhnta dan haka ya soma neman inda ya ajiye check dinshi ya miqa mata, farida na yaba jiyan. [1:46PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----14 Dan haka gashi rbt duk yanda yayi miki ta tsugunna ta rbt dubu dari biyar yace sun isa, tace i, yace to nidai bana san abin da xai sa mu rabune, ko kinyi aure, tace dan wannan ai babu ji.Ina daki sanda ya umar ya dawo daga kai su anty amarya. nasan hakan ne ta hanyar jin danayo yana cewa yaran mai suna emeka yaje but din motarshi ya kwaso plantain, sannan yana son ganin shi tare da duk masu mishi aiki ma'ana sauran yan aikin su biyu,mai ba fulawa ruwa da kuma mai wankin motoci da shara ban da sojojin masu gadin shi.ban kuma jin duriyarsa ba har nayi sallar isha na kulle qofata na kwanta. sai fa da safe nayo wanka na gama shafa mai raina a cushe ga wata shegiyar yunwa da nakeji ta tun jiya raina bai gama baci ba, sai da na bude kayan sawana kaf babu nawa na gida, duka na lefe ne na dai dauki wani material mai taushi fari mai bulun fulawa na saka ina daura dan kwali naji wata irin dukan qofa tamkar xa'a karyata,tsoro ne ya kama ni na soma tunanin ko wani ne ya shigo ya umar baya nan? Amma sai naji muryanshi ce take fadin ke! ke! malama xo nan ki bude ma mutane qofa, kamar dakinta,da sauri naje na bude qofar yana tsaye da wando 3kwata,na kakin soja sai singilet itama ta kakin ce saidai mai santsi ce, fuskarshi murtuk tamkar hadarin magariba, ya daka min tsawa kallan me kike min? nayi maxa na kauda kaina.yace ta mara kunya yau Allah ya shigo da ke hannuna, xaki gane kuskuran da nace kada kiyi, gashi kin qiji kinbi san xuciyarki ta xaki sha wahala.duk masu aikin nan xan sallame su sbd abu 2,na farko kema ai yar aikince, sannan inma na barsu tunda kin riga kinsan dadin maxa to xaki kafa min xina a gida, dan haka na sallame su sai ki fito in nuna miki aikin ki,in kinyi kuskure daya ki sha duka. haka xaki yi ta bauta har my farida taxo kin dinga mata aiki, oya see your eyes lk a mujiya kina kallona a gurin,qaryan masifa kikeyi, na fito yayi gaba na bishi daga kitchen ya fara, gashi nan xaki dunga maku abinci keda masu gadi kada kisa dani dan baxan ci jagwalgwalonki ba. Sannan bana san qaxanta kada a barmin kitchen da datti falo a share agoge komai wanke toilet da gyara duk dakunan gidannan.sharangefanmu xuwa mota,sannan kakina dakika jiqa duk dadai basu bane yanxu suna cikin aikinki kina jina ko? hawaye yana xubo min nace to,yace in kin yarda na kamaki da wani kuskure sunanki sorry, ya juya ya fita. a raina nace azzalumi ya xanyi dole inyi tunda iyayana sune suka bada ni dole na haqura. da abinci na fara duk da cewan ban soma sakar mana girki ba ina ganin yanda su anty aina suke yi, dan haka na dafa ruwan tea na soya uban dankali sbd nasaba ganin na gidanmu da yawa,da makunsan ance duk abin da iyaye suke yi ko kuma nace ya mace duk abinda ake yi agidansu krt ne itama shi xata yi a gidan auranta.na gama na soma da dakina sannan falo na shiga kitchen ina gogewa ya umar ya shigo fuska tamke yace ina abincin masu gadin? na bude kula shaqe da dankali da qwai ya xuba min ido cikhm takaici baki da hankali dama nakula da haka,wannan uban abincin fa? Na xuba mashi ido cikin tsoro yace bar kallona da idanun mujiyanki a gun, na sunkuyar da kai yace ke da wanene wannan dankalin? na ce ta to to ban san yawan masu gadin bane, yaja tsaki ba xan dauki almubaxxaranci ba, dan haka sai ku cinye rar dare ga gun da xaki danna nan xasu xo su amsa ya fita na bishi da kallo yau ne na soma ganin shi da shadda ba kaki ba yar garke ja sai maiqo takeyi. araina nace ga mutun har mutun amma a cikin xuciyarshi mugu ne a mugunta bashi da abokin tarayya. na ci gaba da aikina na gama na fita na share cikin gidan sannan na hau wankin motocin guda uku ne duk na wanke, ban taba wanke mota ba sai yau a gajiye na koma kitchen na danna gun daya nuna min, sannan na xuba musu cikin wata kular na xuba musu komai cikin jug wato tea dana hada, na basu kofuna ya leqo ta windo ya ce gud mrng madam, na danyi fara'a kadan na ce, mrng naci gaba da aikina ya miqo hannu na bashi ya tafi.na xauna falo na soma karyawa kenan, na dubi agogo sha biyu a raina nace lailai na sha aiki. A raina nace lalle na sha aiki inko haka xanyi kullun aiki ya same ni, ni asma'u, ina cin abincin nan ina hawayen tausayama kaina,ina gamawa naje na kwanta, wani wawan bacci ne yayi awon gaba dani sbd gajiya ban farka ba sai karfe 2 da rabi ina ganin lkc na duro daga gado na shige toilet wanka nayo tare da alwala na idar da sallah na saka doguwan bakar riga na daura dan kwalin ban ko shafa mai ba sbd bashida amfani in tsaya yin wata kwalliya. na danna kiran maigadi sai gashi da sauri ya ce wldn madam ban ma tanka shiba na miqa mishi dankalin cikin wata kular ya miqo kayan daxun nima na diba na bude fridge, ina neman ruwa, sai naga ashe frixer ne shaqe da kifi,nama, kaji dadai sauransu na komo falo, can soqon tsakanin kujera da kujera naga wani dan mitsilin abu kamar fridge naje amma na kasa budewa.ina xaton ya umar dan kanshi ya aje wannan fridge din tunda daga gefen kujeran xamanshi take, na gane kujeran xamansa ne ta hanyar ganin jaridu da sauran takacan shi a kanta. Hatta phone landline a gefen kujerar take na koma kitchen na taro a gun wanke wanke na dawo haka na yini iar dare muka cinye wannan dankalin da qwai gyatsar magwas ta dame ni shi dai bansan shigowar shi ba ban kuma damu da in saninba. suna tare da abar sonshi,wanda ta canxa shiga xuwa atamfa yar holan da qaton hijabi maimakon riga da wandon da ta fita dashi, yayi lallashi tare da qara nuna mata tsananin tsanar da yayi ma amaryan tashi tare da qara karanto mata mugayan halayan amaryan,sannan ya labarta mata irin matakin da yayi niyar dauka na axabtar da ita, har sai wuya tasa ta kama gabanta.farida taji dadin hakan amma bata nuna ba sbd iya bariki, sai tace kar dai a tsananta fa,yace ke dai ki ta mana addu'a baba ya sauko duk randa kika shigo gidan xata bari.farida ta ce iyayanku fa? yace ko ban sake ta ba sai dai ta koma gun su da xama kiyi qoqarin shawo mana kan baba mu samu ya yarda kafin na koma abuja dan Allah ya sani baxan koma abacha barrack da wannan yarinyan ba.ya je yanemi masauki.. Da safe ya zo sunyi sallama in da ya cika su da kudi ya tafi jirgi ya biyo zuwa gida. Tun tuni ya dawo amma bai shigo ba sai 5 ni ko a wannan lkcn na gano wani dan fili can baya gurin da yalwar iskar Ubangiji ba kamar sanyi falon nan ba abu kamar hauka, AC 2 ga fankoki hr 3 bayan ko wani dan couredor na gani kusa da dakina na bi sai naga kofa ina budewa sai naga fili hr da 'yan fulawowyi da kujeru 2 tun da na gama abnci rana dama jalof din taliya nayi,ina gama wanke-wanke na dau abncina na nufi can. A can na yi azahae haka La'asar na kwanta kan sallayar na saka filo sanda ya shigo ya bi ta garejin shi na aje Mota anab ranshi ya soma 6aci sdb yanda yaga motarshi duk jirwaye duka 3n ashe 6acin rai na gaba sai da ya bude motar yaga yanda na lafge motocin da ruwa takaici ya ishe shi ya shigo ta kitchen bai ganni ba ya nufi dakin,shi ne hr toilet bana nan,ya dinga fadin ke ina ki ka shiga ne? Ke sam ni ban ji ba,bam san duniyar da nake ba,ina ta shara baccina ya ce lallai kenan hr ta soma zuwa yawon gulma a mokata don yasan ba za a bar ni fita ba sai da izininshi wato masu gadi hr zai fita sai kuma ya tuna da baya nan take ya zagayo ya fito bayan. Saukar Marin da naji ita ce ta katse min mafarkina da nake yi wai gani ga Rahma a mkrnt muna ta lbr. Firgigit na tashi tare da rike kumatuna tsananin tsoro ne ya ratsani.... Na zaro ido jikana yana rawa ya ce uban wanene ya saka ki ki jika min mota? Cikin in-ina na ce na na na wanke ne,hk ake wankin mota a garinku? Fuu!ya fita sai ga shi ya dawi da belt ya zane ni ya hana ni kuka sannan ya ce in yi ta tsallan kwado,ya fita ya saka direba da maigadi suka kai motocin gurin wanki ni ko nasha kuka hr na gode Allah da na gaji na fadi a raina ina tuba uwar wuyar da na sha gurin wankin motocin ban ta6a wanke mota ba ban san yanda zanyi ba,shi yasa nayi ta maka ruwa ko ta ina ina sa6o omo,jiya ma haka nayi na zata gida ya kwana yaga sun yi ne shi yasa yau ma na sheka musu ruwa ashe bai ma dawo ba tunda sanda ya fita ban riga na wanke ba. Bai kuma biyowa ta kaina ba hr bayan magriba na rarrafo na shigo ruwan dumi nasa na gasa jikina sannan nayo alwala.A zaune nayi sallah sbd kafufuna sun gaji, nan na kwanta kan abn sallar ina kuka,ni dai ban zo duniya cikin sa'a ba,bn d Suraj da Momy Da Rahma bani da mai sona ina nan hr 8 tayi nayi Isha'i tunda daji ne cikin Inyamurai ban ta6a jin kiran Sallah ba sai dai ka aduba agogo. Asuba ma dan dai jiki ya sa ba da tashi duk gajiya asubahi tana yi zan farka,na idar na koma na kwanta can naji tsawa a kaina,na tashi shegiya ba ki ba masu gadi abincin dare ba? an gaya miki gidana ana yinwa ne ko rowa? See translation [1:52PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----15 Nan fa gabana ya fadi na tuna bamma yi girkin dare ba,da sauri na tashi da gani sai zani da hijabin sallah Makaroni na dora nan na zauna a cikin hr tayi na juywe musu na kira su suka dauka na koma daki sanda zan wuce yana zaune kan kujera da dama na zargi cewa tashi ce yana waya da Gimbiyar tashi suna Syy Na gane hakanne ta hanyar kiran sunanta da yayi ya ce Farida my sweet heart kada ki damu na ce ban ta6a ganinshi yana fara'a ba sai yau na wuce daki a raina ina fadin bakin mugu. ************* Haka rayuwata ta kasance cikin wahala da bauta tun ban iya wanke mota ba har na iya, don ya ce ni zan ci gaba da wanke mota in nayi kuskure insha wuya wankin kaki ma na kware hr Azumi yazo ina jin shi ranar wata Asabar da aje saran ganin watan na Ramadan ina goge -goge a falo shi kuma ya na zaune yana shan tea. Da kanshi ya dafa, wayarshi ta soma ringin ya dauka,naji ya ce Momy ina kwana? Na juyo da sauri tunda na zo nan gidan sai yau naji ya ambaci sunan wanda na sani.tun da ba zama yake ba kamar in amshe wayar in ce Momy ki zo ki cece ni don Allah amma babu hali naji ya ce tana lafiya. Ai tana bacci bata tashi ba na sanni aka tambaya ya 6ulla min harara na ci gaba da aikina hawaye ya ce duk san da za ki kira Momy bana gida yau kuma bacci take kada ki damu Momy ai zamu zo da sallah in na samu hali amma zaku ga aike na Azumi a raba ma makota naku da na gidan Baba Alhj,kudi zan turo Aliyu ya je ya cire sai a sai komai hr na hidimar Sallah ko? Haka Momy tayi ya nacin son Magana dani amma ya Umar ya ki. Ranar Mndy ko ba ya nan na dauki landline din falo zan kira amma abn haushi ban rike number momy ba, sai fa gidanmu su kam kiran me zan musu suna Murna sun rabu da kaya.Don haka tsabar mugunta ranar Azumin farko dore nayi don ya ki tashina da yake ban san anga wata ba sai da safe na jiyo yana jin Radio ana fada a labarai shine na kama baki duk da ban ci komai ba. Haka Azumin yayi ta tafiya ban san in da yake shan ruwa ba haka sahur. Masu gadi ne kullum sai na musu da rana da safe direba ne kadai ke Azumin shima bn san inda yake Sahur ba,ni dai dama sai dai in na tashi akan lkc in dan hada tea insha in ban tashi ba inyi dore,akwai ranar da har na hada tea saina

Chapter 5 of 16