Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ina yace ta za..za su ji. Ya fita da gudu gudu sauri sauri. Ta dube ni tace 'dan yata ne. Na taba baki ba tare da nace uffan ba, na shiga daki ina mamaki. Ba wani da zai zo ta kai shi bedroom in har gaskiya za a bi ko yaya suke. A raina nace biyu kenan, dama na taba jin hirarsu da kawayenta. Ya umar da ya dawo ya sha mamakin yaran nan. Sayyida har yi take tamkar ya tashi daga zaune ta kamo shi, sai daga mishi hannu suke yi. Niko na share su. Yau kam ko sannu da zuwa ban mishi ba, nace in shi yasa hajjo take cewa ina sonshi to na daina daga yau. Tsaraba kam yara sun sha ta, washe gari ya fara hutu. Nan ya shirya mana fita ban ma sani bani da hajjo da yara, tunaninshi daya farida. Amma ga mamakin shi da yace yana son ya kai yara check up turai sai ta nuna yardarta. Tare da fatan khairan. Nan ko itama dana tana da fita da alhaji jamilu. Tafiyar da take saka ran shakar kudi masu kauri, har million ashirin. Alhajin na sonta musamman yanda take yadda yayi luwadi da ita son ranshi. Auzubillah. Ce min kawai yayi shirya zamu je kd, munyi musu tsaraba na kura kowa yaji dadin ganin yara bul bul, can na samu labarin fita zamuyi a bakin antyn shi, ban nuna mata ban sani ba. Zaune nake a falo ina kallo su sayyida suna ta guje gujensu, sam dama ba sa zuwa gurina tunda ko kare gurin mai kula shi yake zuwa. Hajjo tana kicin tana tuwon masara, tace ta gaji da ciye ciyen nan, nace nima zanci. Ta mana kuka dama muna da su duk momy tana bamu. Farida ta shigo yara suka nufe ta da gudu, suka rike ta. Kinga wani ball da tayi dasu tayi ciki abinta, wani irin kuka mai cin rai suka saki sannan suka shide. Wani abu naji yazo ya tsaya min a raina, ina kallon su tare suka mike a gigice suna kallona suka nufi dakin hajjo. Na mike da sauri na bi su na kama su na rungume sai naji hawaye yana zubar min, na kwashe su zuwa dakina. Na lallashe su suka kwanta a cinyata sai ajiyar zuciya suke yi. Baccin wuya ya kwashe su na tsura musu ido cikin jin tausayinsu, nan ko sai naji wani son yarana yana ratsa ni. Jin motsin hajjo sai na zame jikina na kwantar dasu na tashi bakinsu duk ya kumbuta. Ai ko hajjo ban ba labari ba, don ni zata ma fada. Ranar dakina suka kwana, na rungume su yau ce rana ta farko da suka ji dumin jikin uwarsu. Da safe ni na musu wanka har hajjo tana min tsiya. Yau kuma ana yi da 'ya'yan nawa ne? Sai da ya umar ya shigo ya same ni ina gyara ma sayyida gashi na raba mata gida biyu, na kama mata da ribbon kalar rigarta da takalminta. Ranshi kar amma baiyi magana ba yana Tsoron in yayi magana zan fasa gyaran, yace babyn baba me ya same ku a baki? Nace sunyi karo ne. Yace iye! Sorry zo nan yarinya na kinyi kyau. Ta tafi tana murna tare da fadin dady sweet ata, na soma shirya sayyid shima kayan shi masu kalar ja da fari tamkar nata. Ya umar yaji dadi, don har kama su nayi suna gulmata shi da hajjo yana gaya ma hajjo don Allah kada ta min tsiyar abinda nayi ma yara kada ma daina dan yasan halina. Mun dawo da kwana uku muka tafi, england muka fara sauka. Dakin hajjo daban namu daban. Ya umar da mukayi cikin wannan kasa nakan manta wai ba son shi nake ba. Kananan kaya ya kai ni na jibgo abin son raina. Kullum ya sani in tsuke mu tafi shakatawa, a raina na kance ina malumtar? Guraren wasanni mu shiga motocin dake gudu kan kankara, mu hau dokin keke da dai sauran su. Ko ina ina manne dashi satinmu biyu mukayi america sannan mukayi dubai. Watanmu biyu na zubar da karatun da nake ikirarin so na kama bin miji yawo duk da ni ba haka nan na so ba. Muna dawowa na tada ballin saki, haka yayi ta lallabani yana cewa in bari yara su shekara. Cikin yardar Ubangjij watansu goma suka soma tafiya, nan fa nace na yaye su dama ba basu nonon kiriki nake yi ba. Ya umar yace to shi kenan. Na ta da tsiyar saki, yace dai a bari sai ranar lahafi. Dadi naji zan kuma nuna musu cewar ina son ya umar ba haka bane. Lahadi tana yi yace muje kaduna zai zo ya kawo min, sannan ya min godiya har da cewa aikin ma min kokari asmy, ni naja motar sabida a rayuwar mu ta england ya koya min mota, kuma ban sha wahala ba. Sai dai ban taba doguwar tafiya ba sai yau, yau ma don ya riga ya fita ne ni ko naki kiran direba. Cikin yardar Allah muka iso lafiya. Kwanan mu daya gurin su momy, ya aliyu yasa aka gyara mana gidanmu muka tafi can. Na zauan zaman jiran saki. Wata sabuwa! Ba sai ciwon kirji ya sarface ni ba? Baya, kirji abin babu arziki muka yi asibiti. Wani kayan takaici gwajin farko wai ina da ciki wata uku. Nace ciki? Wai ciki. Tun a asibiti na mishi waya nace sai kazo san yanda za ayi dan wallahi dacto yace ciki garan. Kazo sai dai a zubar...ya katse ni, kada ki zubar min da ciki, ki bar ni dai zanzo nace to gara kazo, na sha kuka tamkar wadda ta yi shege. Hajjo fada tayi ta min, washe gari yazo yace to gashi yazo yaya zamuyi? Ina kuka nace zubarwa ce zamuyi. Yace to daina kukan abi mai sauki, shirya muje. Ashe ya kira dr sun hada baki da muka je likitan ya dan dudduba sai cewa yai akwai hadari a cikin aikin wai zan iya mutuwa. Ya umar yace toh fa! Yanzun ya za'ayi kenan likita? Likitan yace mu bari sai nan da wata hudu, zai dai bani magani wanda zai sa abin dake cikin ya rasu, in yaso su sai su sa injin su markade shi. Ya tulo min kwayoyin magani ashe duk na karin jine ne ban sani ba. Naje gida nayi ta sha har da wuce ka'ida ni dole zan kashe abin dake cikina. Satinmu biyu yazo ya lallabani wai in dawo abuja kada su momy su kula ina da ciki su hana mu cirewa. Kai ya umar sai a bar shi. Tun daga sannan na kama 'ya'yana, nan na shiga yi musu hidima. Su kuma suka daina zuwa gurin farida koda tana zaune da babansu ne. Dan munafunci sai ta ringa cewa mamanku ta raba ni ku, shi kam sai yace sha'anin yaro ne yaya mamansu zata raba ki dasu? Sai tace toh ba gashi ba tunda ta ja su suka ki ni, nikam wata hudu yana cika na tada balli domin lokaci cikina wata bakwai naki zuwa kaduna don kada ma su ganni da ciki su min tsiya, nan ya shiga lallashina wai zamu canza wani asbiti. Muna cikin haka ranar sai ya shiga dakin shi don ganin shirmen yaranshi da na musu birthday baya nan. Ya tuna da na'urarshi mai dauko mishi komai kunne take. Tun daga can suna kanana ya soma kallon da shirmen kin da uwarsu ta musu ya kan sha dariya yanda take satar kallon yaran a lokutan baya da bata son su. Kwatsam sai dan duhu kan abin kallon can sai ga wani saurayi gabanshi ya fadi yace wanene wannan? Farida ta fito daga dakinta sanye da gajeren wando da kuma bireziya. Innalillahi yake ta maimaitawa, cinyar yaron ta zauna shi kuma soma shafa cibiyarta. Ba zai jure gani ba saboda jininshi da ya hau. Nan take ya kashe sannan ya zube a gado, sunayen Allah ya shiga jerowa sannan ya samu sassauci lokacin ne wayar shi ta soma ruri kamar kada ya daga sai kuma ya duba aminu ne yace in da hali fito mu hadu nan area 23 zamu gwada maka wani abu mai muhimmanci. Kamar kada ya fita, sai kuma yaje ya dauko mota. Gidan shakatwar alhaji jamilu suka shiga inda aka shiga da farida da zuwan kamar minti talatin. Salisa yana aiki da wani kamfanin ne mallakar alhj jamilu shiyasa ya san shi kuma alhj jamilun yana sanyo salis cikin lamuranshu saboda yanda yake da amana. Shi yasa ake da ikon shigowa gidan shakatawar dan wataran anan ake lissafin ko shawara. Kai tsaye falon suka shiga inda suka leka dakin barcin inda ya umar yaga faridarshi haihuwar uwarta ana luwadi da ita. Wa iyazu billah. Faduwa yayi su salis suka fita dashi. [7:54PM, 17/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu 2----14 Faduwa yayi su salis suka fita dashi sai da yasha ruwa laida biyu a ranar amma da yake jarumi ne sai ya dake. Wata tsana da gami da kyamar faridar suka shige shi. Tsoron daya ko suna da HIV tun kafin ya bar asibitin yasa aka mishi gwaji babu komai tare dashi, don haka yayi ma Allah godiya. Tara saura ya shiga gida amma bata dawo ba, falo ya zauna gidan ma babu wanda yasan ya dawo sai ni ce na fito dakin hajjo naga mutun zaune tamkar gunki. Na shige tunda dama ba wai ina shiga sabgarshi bane. Don ko shi ya sani sai naga dama nake tanka shi. Tara da kwata ta shigo cikin hijabinta na sutura, har kasa a ranshi yace FUSKA BIYU. Ta nufo shi da fara'a. Sorry sojana kana ta jirana inzo in baka abinci. Ya daure yayi murmushi kada ki damu na sani harkar kasuwanci ce to ya kasuwa? Tace alhamdulillahi mun gode Allah. Ta nufi daki barina rage hijabin nan. Ya ce to, ta fito cikin leshi ja hannunta dauke da gwangwanin coke dayan maltina. Kusa dashi ta zauna ta mika mishi maltina, kasha naka in sha nawa. Yace yau nima naki zan sha. Tace toh bari na dauko maka wani. Yace bani wannan ma ya ishe ni. Ta mike bazan baka ba tana dariya wai ita wasa. Ya gane giya ce ta zuba, yace yau naga abin ala'ajabi. Ta zauna, a ina? Kuma me ka gani kai da baka cika damuwa da lamuran mutane ba, yace to ai yau nasha mamaki. Wani soja ne cikin wannan barikin ya kama matarshi da wani, ta zauna da gaske kake fada? Yace sosai ma kuma matar aure kace? Yace Allah matar aure mijinta kuma salihi ne dan tare muke. Tace innalillahi, kai wannan tayi asara. Ita ko ina zata kai zunubi, kina matar aure sannan kina bin wani? Sojana anya mutane sun san girman zunubin zina kuwa? Balle matar aure ga hakkin miji ga na Mahalicci? Tir da wannan mata. Kallonta yake cike da mamaki bai san tsawon lokacin da ta dauka tana cutarshi ba. Yace kinsani my farida yanzun ji nake in ni ne wane mataki ya kamata na dauka a kanta? Kashe ta zanyi ko hukuma zan hada ta dasu? Tace ai ba zancen hukuma in yana son ya more mata ko ya sake ta dama kaga ai in haka ta faru ba aure. In ya sake ta sai ya barta da Allah ya isar mishi sannu kan hankali sai Allah ya saka mishi da mata ta gari. Ita kuma zata ga karshenta. Ya mike cike da murmushi, shawararmu tazo daya my farida. ya mika mata takardar sakinta uku, yace gashi kinga karshenki, sannan tuni Allah ya min sauyi. Kije Allah ya isa Allah ya isa ban taba zina ba, nagode Allah da bai bani haihuwa dake ba. Yayi daki ya bar ta nan cikin mamakin wannan lamari. Bansan hidimar da suke yi ba sai dai washegari naga ya shigo da wasu zaratan sojoji sun fita da kayan farida sai kangon dakin. Ga zatona sabon gida ya gina mata ta tare tun da naga itace matarsa. Sai dai ganin ko yaushe yana gida na soma zargin ko sun rabu ne? Wata kulawa yake mana wacce tafi ta baya. Kullum yana lallashina ni kam kara botsare masa nake. Yau dai da muna kwance yace ya min alkawari na karshe da zasuyi ya dawo zai sallame. Cikin satin tafiyan wata biyu zasuyi wata haihuwata zai dawo. Suka tafi dan kwantar da tarzoma tare da runduna karkashinsa. Ranar tafiyar tamkar kada ya rabu da 'ya'yansa. Nima ya rungume ni sannan ya durkusa gabana wai in yafe masa laifukan da yayi min wanda ya sani da kuma wanda bai sani ba. Cewarshi ko ba zai dawi ba, jikina yayi sanyi nace tunda kace in ka dawo zaka sake ni na yafe maka. Yace kina sona? Na girgiza kai alamar a'a. Ya fita sai wata zuciyar ta ce kilan tafiyar kenan. Sai kuma hankalina ya tashi. Kaduna muka koma kowa ya sha mamakin ganina da tsohon ciki ga yarana dake bibiyata ko ina na shiga. Yanzu nima gaban kowa nuna musu so nake balle ma da babansu yayi wannan tafiya sai naga tamkar sun zama marayu. Su rahma da jamila suna min tsiya kai matar nan da gulma take, bana son miji bana son miji sai shegen hadama, har kin kunso wani cikin. ban da ta cewa wai barawo hannun mata, kowa haka yayi ta min tsiyar nan ni damuwata ta dame ni tunanin mijina. Sai yanzun na yarda da batun su hajjo na cewa ina son mijina domin yanzu na kasa kuzari ko yaushe ina kwance da tsohon cikina ina tunanin mijina tare da tuno tafarkin rayuwarmu har zuwa yau. Waton yadda na dauki ya umar ba haka yake ba, ba mugu bane wancen karan yaki halina ne da yake zaton ina dashi. Ko zaman mu na kudu bai taba hanani ci da sha ba. Kuma yana horani ne in nayi masa laifi. Sannan bakaken maganganu da na aikata maganganu ba laifi bane dan ya gaya min su, tunda ya gane zaton shi ba haka bane fa? Yana kyautatamin, yana tausayamin kuma yana nuna yana sona. Ya umar yana da alheri, sadaka, kyauta, zumunci da kuma adalci. Na tuna sanda ya ba farida jari haka ya siyo min gold na daidai kudin da ya bata yace in ajiye. Na tuno irin soyayyar da yake min a lokutan da muka kadaita don auratayya. Nayi juyi na rungume pillow na saka dayan hannuna ina shafa cikina wanda muka same shi muna tsaka da soyewa a london. Ina son cikina, na tuno sanda ya umar zai bar gida yaso in fada mishi kalmar so na kasa, in bai dawo ba ba fa? Nan kuka ya kwace min cikin kukan nake fadin ina son ka ya umar don Allah ka dawo zan gaya maka kaji, ina tsananin sonka. Na fito daga wanka na koma ban shafa mai ba na saka kayana ban daura dankwali ba na xari hijabina .tunanina ya sha kaina tun gun wanka nake kuka,yau fiye da wata ya umar babu waya in na kira tashi sai ace min tana rufe, ni kam bai ta ba min irin wannan tfy ba,na fito falo hajja da su sayyada suna kallo catun.. Na xari key din mota,dama motocinshi duka ya xube min keys,ban da tawa, sayyida ta dube ni anty an biki,anty suke kirana dan sunji hajjo tana ce min, na kalle ta xo to muje, na dubi sayyid yaran akwai haquri nace xaka? ya daga kai alamar eh, nace to xo muje, hajjo tace anty ina xaku je? nace gun su momy tace to sai kun dawo, na riqe musu hannu muka fita sayyid yace anty banbino aje, nace a'a sayyid yace dady mun je ko?na kalle shi kana san ganin dady ne babana? ya ce um sayyida tace nima ,sabon hawaye ne ya xubo min ina yin parking a qofar su momy ya aliyu tsaye shi da wani suna magana.sayyid ya ce anty ga uncle suna sauka gunshi suka nufa ni kam ciki nayi da sauri. na tasa momy ina kuka tace me ya faru? hankalinta tashe,cikin kuka nake gaya mata halin da nake ciki tace min dama yacd mata inda xasu je daji nd inyi haquri in Allah ya yarda lfy xai dawo, aliyu ya shigo da yara nan suka yi ta lallashina har na haqura muka yini sannan muka koa gida. Yau watanshi 2 cur na xuba ido shiru har dare wasa wasa har sati duk na fita hayyacina ga ciki ina gani tsabar tension ne ya sani naqudan dole, naqudan ma ta jini, tunda EDD dina saura kwana 10, kwana na 3 a asibiti na haihu yaro namiji qato, sai dai na xubar da jini sai da aka min qarin jini, aliyu da usman suka bani, an sallame ni duk da ya bar komai hannun aliyu, cewa nayi baxanyi taron suna ba, abar ni inji da kaina, da kuma damuwata, suna kuwa da su abba suka tambaye ni nace susaka sunan ya umar nasan mun rabu kenan yanda nake yi suma duk na karya musu xuciya hankalinsu suka tashi, kai wasa wasa har muka yi arba'in su aminu ma suna xuwa suna kwantar min da hankali shine mai kawo min lbrn halin da suke ciki yace har an qara tura su wata rundunar sbd abin yaci tura, sai da qar ya kwantar min da hankali ya kance wai shi suna waya,inma musa sai hajjo tace kada kiyi musu anty kin san fa shima soja ne sai ta yuwu hakanne. Kwatsam rannan ya aliyu yaxo min da lbrn sun dawo suna abuja,amma an riqe su sbd xa ayi muru qarin girma.murnan dana ringa yi har mamaki tayi ta ba mutane. sai kuma ahanyan su ta xuwa lagos jirginsu yayi hatsari, mafi yawa sun mutu,ina xaune ina kallan lbrn CNN da misalin 12,sai ga lbrn da duminshi,wai jirgi mai dauke da man yan sojojin da xa'ayi ma qarin girma ne ya fadi,jirgin yata so ne daga lagos xuwa abuja,ai ban gama jin xance ba na saka ihu,ashe gida sunji ance kada a gaya min domin hajjo tana musu waya tace gani nan na fadi sume bata san me ya faru ba,nan momy ta saka kuka tace shi kenan wani ya gaya mata,farkawa nayi na ganni a gadon asibiti kuka nake sosai musamman dana ga daukachn yan uwana su momy ne ke lallashina ita da mama,mama tace asma-u ai shi bai rasu ba, nace ya mutu ba kwasan in sani ne,lkcn ma su kansu ba sani sukayi ba,jinina ance ya hau dan haka sukaimin alluran bacci na samu ya dauke ni xuwa yamma sunji bai mutu ba suna asibitin sojojh dake can abuja. Su abba sun dugunxuma can ina farkawa na samu lbr nafa ce saina je aka yi ta lallashina kan in naje hankalina xai tashi ne sbd ko su an hana su gani shi.da qar nayi sati tsabar kukana da rashin cin abinci yasa aka ce su barni inje.da qar suka barni na shiga gun shi.na sha kuka ganin yanda kusan duk jikinshi an nannade shi gidanmu na abuja muka dawo,cikin satin ya soma motsi na liqe a asibitin nike kuka dashi addu'oi jama'a sai yi suke masallata har da isalamiyu sbd ya umar mai jama'a ne ga alheri shi yasa kowa ya damu da ya fara jin sauqi, sai me? duk damuwa da kuma hidiman da nake yi dashi sam baya min walwala ko sakin fuska. da farko na ce ciwo ne amma da yaji sauqi fa? sai dake min tare da shan qamshi, watan shi daya aka sallame shi kuma cikin satin wanda suka yi saura suka samu qarin girma, harda ya umar a cikin wadamda suka samu prmt, kowa nata murna abokai sun shirya dinner mi kam tsoron shige mishi nake, shi kam yana yine sbd kada na mishi xancen saki. Bayan duk wadannan bidirin yau na fito wanka bayan sallar isha'I yara suna gurin hajjo har da junior. Kwalliya na zauna na soma tsarawa. Yau kam na dauki aniyar nuna ma ya umar ina sonshi. Zan gaya mishi baki da baki kuma zai gani a aikace. Sosai nayi gayu, dakinshi na shiga abin da ban tabayi ba shine zuwa turaka. Sanda na shiga yana sanye da gajeren wando fari sol haka singiletin jikinshi. Yana rubuta wata 'yar takarda. Ina shiga ya hada rai tamkar yaga mutuwarshi, yace yawwa gashi. Jikina ya soma bari nace me zan gani ya umar? Ya dubeni duban wulakanci abin da kika dade kina so ne na baki. Kasa na zube gwiwa biyu ka min rai yaya zaka yi da yarana? Yace ki amsa yaran da dama ba wai kina son su bane ko dama da kika wulakantasu me ya same su? Na rike mishi kafa kada kamin haka. Yanzu ina sonka ina kaunarka. Yace karya ne ke da kanki kin fada. Bakin da yace ki, ko yace so karya ne don haka amshi ni tuni na samu matar aure. Kingama hoton ta nan, ban kalli hoton ba na amshi takarda na fita ina kuka, na dauki gyalena tare da key din mota yana zaune falo nazo wucewa yace au na manta batun karatu in kina bukata zanfa taimaka. Cikin kuka nace banaso ka cuce ni ka koya min yadda zan soka a karshe ka tsunduma ni cikin kogin sanka sannan ka sake ni, ban yafe ba. Yace haka kika min. Na tafi na rasa inda zan nufa. [7:59PM, 17/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu 2----15 Karshe Gidansu naje a tsakar gida na saka ihu da gudu su momy suka fito dasu anty cikin kuka nake fadin ya umar ne ya sake ni. Saki? Inji momy. Shiru abba yayi, anty tace me ya hadaku? Nace ni ban mishi komai ba shine yace wai ba ya sona yanzun ya samu wata. Momy tace anya bai samu matsalar kwakwalwa ba hadarin nan? Abba yace ku shiga daki bari na neme shi a waya. Muna daki sai kuka nake ba ran ma da nonuwana suka soma zuba wannan alamace ta junior ya tashi, nace momy dan Allah ku bashi hakuri ban san me nayi mishi ba yaace ya sake ni, in ma auren zaiyi ai ban hana shi ba, momy tace to ya isa haka yi shiru, abin da kara firgita ni shine duk wayoyinshi a rufe. Ya kira aliyu ya kai shi gidan ya umar amma maigadi yace musu ya dauki mota ya fita, kwana nayi kuka damke da takarda a hannuna. 143-Da safe kam labari ya kai gidanmu. Abba da alhaji a falo suna tattauna yadda za'ayi. Abba yace anty amarya ta kira ni suji ko saki nawa ne. Ta same ni momy tana ta min fadan kukan da nake ta ce ai yazo ma sai ya kara raina miki wayo. Gara ma ki daure ki nuna bai dame ki ba. A raina nace momy ba zaki gane bane, samun kamar ya umar zai min wuya. Anty tace su abba suna kirana shima ya umar din sunci sa'a ya kunnan wayarshi kuma sunce suna neman shi yanzun nan. Kizo da sakin saki nawa ne? Fuskata duk ta kumbura cikin kuka nace bansani ba. Na dauko takardar kan madubi da zanyi sallah na aje ta don hannuna ta kwana muka tafi har momy tana cewa muje zai ga fushina yau. Muna shiga yana shigowa, wani kyau naga ya kara min shigar kananan kaya ta kara maida shi matashin yaro ya zauna. Momy dake zaune kusa dani ta zungureni ta baya alamar wai in daina kallonshi. Na sunkuyar da kai can na kara kallonshi sai ya min gwalo. Abba yace yanzu umar abin da kayi yayi daidai kenan? Yace me nayi abba? Momy cikin fada tace ina fa zaka sani, shiyasa nace a caji kwakwalwarshi. Alhaji yace duk ba haka ba, yanzu ta kawo takardar saki nawa ne? Na mika musa. Abba ne ya fara dubawa, tsaki yayi sannan ya ba alhaji. A raina nace shi kenan uku ya min. Na kalle shi ina sabon kuka shi kam dariya yake yi. Alhajin ya mike sun maida mu 'yan iska ne ma yaran nan. Momy tace saki uku ne ko? Alhaji ya bata gashi ki gani itama ta mika ma anty amarya ta fita. Dariya naga anti tana yi ta fita duk sun bar mu. Na dauki takardar a hannun kujera in da anty ta ajemin na soma duba ko saki nawa ne? Sai naga ya rubuta: 144 “Ni Umar faruk na kara nunka igiyoyin aurenmu, ba saki ba yaji. Ina son matata shin tana sona?” Na mike ina kallonshi yana min dariya nima dariyar nakeyi fuskata ga hawaye. Ya iso gurina ya rungume ni na dan mihsi dukan shagwaba a kirji nace kai ko? Yace sorry kin son umar ko? Nace ina sonka sosai. Ta kofar waje muka fita ba tare da na koma cikin gidan ba muka je muka bude sabon shafin soyayya da rayuwa mai dadi. 145 Na fito daga cikin mr biggs ina tare da yarana, sayyida da sayyid 'yan shekara biyar suna dauke da kayan kwalama. Junior yana da saurin girma don ya kamo 'yan uwansa, sai yaron cikin da nake dauke dashi muka nufi gidan rahma. A hanya ya umar ya min waya ina dauka yace kin zama matar general gobe za'a tabbatar damu, sai ku shiryo kuzo akwai shagulgula. Murna ba'a magana. Ya umar yana da sa'a duk cikin wadanda suka samu wannan mukamin ya umar ne mai karancin shekaru. Gurin dinner ne mata suka so su minkwace don haka na manne mishi. Munsha dauka gurin 'yan jaridu da kuma tambayoyi. Ranar muna kwance wata number sai kiran min miji ake yaba dauka sai naga yana kallona. Ana sake kira na dauka muryar mace naji tana cewa don Allah ka taimaka min ciwon sonka yana damuna, nace sai dai ya kashe ki, miji nawa ne ni daya. Yace haba asmy yaya zaki kashe min kasuwa? Na harare shi na tashi xan fita ya kamo ni Allah ni naki ne ke daya, da ace ina kula mata da nayi goma yanzu. Na dube shi bana son kishiya fa kaji mijina? Zo muyi wata hira mai dadi ki bar batun kishiya ke kina wadatani baki hanani abin da zai sa inji sha'awar wata. Kina wadata ni, zokiji wani story kanwata. Yau asibitoci muka nufa don kai taimako ga marasa lafiya. Ya umar kan ware kudi duk wata uku dan taimaka ma al'ummar annabi. Yace yau zan rakaki asmy nima ina son samun ladan ziyara. Kai fa ke bada kudin gurin 'yan HIV, muka soma a bakin gdon wata mata na tsaya jin tana cewa soja, baiji ba nace ya umar, farida ta fita hayyacinta ta koma kwarangwal. Duk wannan kyan babu shi ya gudu, ta soma kuka tana neman gafara. Yace yau ga sakamakona kuma kinga yadda Allah yayi dake, dama kince da sannau zanga yadda Allah zaiyi dake. Ya fita nima na bishi. Ina dukiyar da ta tara? Ina iyaye da 'yan uwanta? Duk sunki ta da ko itace ma shanawa a dangi. Mu kam soyayya akalar rayuwa, dan iyaye sun miki zabi kada ki ki. So da yawa yana zama alheri. Tammat bihamdulillah. THE END!!! An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Chapter 15 of 16