Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fatima , Aminu yana nafdac lagos , hadiza dai ina ganin Aliyun gidn Abba zata aura naga yana dan kiranta. Abba Aminin alhaji ne dan sun wuce abokai. abba dan bauchi ne mutumin azare , kuma tun a gombe suke abotarsu , har yau. Abba shine silar zuwan alhaji kd. Abbba yayi karatun boko mai zurfi kuma ma'aikaci ne bai dade da yin ritaya ba, saboda abota ne suka yi gidanjansu layi daya sabanin d abba 'yan unguwar sarki . Alhaji yana unguwar dosa sunan Abba Alhaji muktar , yana da mata 2 uwargida momy kawar mama ce kut da kut , babban yaronta soja ne umar yana port ya girmi yaya abubakaar din gidin mu sai aliyu dan bata haihuwa da wuri tsakanin umar da aliyu shekara 9 , Aliyu ma'aikaci ne. bnkin phb sai anti salima zak zata yar mamace saboda kusn ma a gidanmu take, sai nafisa sa'ata sai yan biyunta hassan da usaini, na manta da jamila daga itace sai nafisan jamila ce sa'ata koma nace kawata mama ce tace ta daina bina kar na bata ta , mamanmu [1:30PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1------4 Ya umar tunda mugu ne yanda naji su anty salima dasu anty aina suna lbr tun suna kanana, ysha basu wahala musamman inkn ci na 5 a makaranta zuwa sama, amma daga na 1 zuwa na hudu yana maka uzri inko kaci sama da haka ayya sunan ka sorry, zai zane ka tas ya saka ka kallon rana irin da mugancin su na sojoji. wata rana su anty fatma da anty aina sunjehutu gidan shi ma yazo hutun, ayya sun sha wuya , yana zaune a falo yana kallon kwallo. suma suka zauna yace bakun zaunaba saura naji surutu, dama ina ciki daku suka yi tsit suna ta kallon kwallo anty fatima tace ni dai nafi son masu fararen kaya su ko anty salima da anty aina'u suka ce sunfi son jajayen, ashe shima yafison fararen wato asnal.can jajayen suka ci, hu suka soma fatima sun ma manta da batun yaya umar yana ciki, haushi 2 ya kama shi ga haushin anci garin shi ga ihun su, nan ya had kan anty salima da anty aina'u ya gwara sannan yasa ka su zaman mashin da tsallan kwado sun yini suka kuka dan sun gaji a karshe ya musu bulala 20. ni kuma in sun bani lbrn shi sai ince ce ya rana ku ne ina ma lokcin ne da sai na nuna mishi nawa taurin kan, anty aina'u tace ai da yanxun ne shi ne maganin shegen taurin kanki in ce sai dai mu zuna shine yanzun ya soma nunamin? y jika ni sannan ya mre ni? zan rama. yau kusan watana dy da daina zuwa makarant kullum cikin roko nake har anyi jarabawa bana nan , ranar ko anyi kukan d dukmai sona sai ya tausaya min amma 'yan gidanmu ko a jikinsu. Alhji ma da mishi maganar yayi hakuri na daina sai yace ai ban rabu da suraj ba, saboda haka sai dai in suraj din ya fito ayi auran can naci gaba da karatun gidansu. na shirya zanje gidansu rahma kuma inason ganin suraj dan in san yanda zamuyi, tun daga abin da alhaji yace , cikin sa'a ina ftowa sai naga mugunnan ya umar, suna magana shi da wani abokinshi ne ko yaya suke oho, duk suna sanye da kaki, na koma cikin gda hadiza tana wanke wanke kwanuka, na suro an sannan nazo na antayamishi tsayawa sukayi suna kallona, nace kima kaji inda dadi, ya Aliyu kaninshi dake can bakn gate din su ya taho da sauri yana fadin ke karamar mara kunya shi tsaronki ne? nace ehdin kai kuma ina ruwanka?zai kai min mari ya umar ya rike shi yace barni da ita kada kayi fada da karuwa....mutuncin ka zai zuba na san maganin ta , kinga yanda kika jika kakin nan sai kin wanke su, so dari nace ba so dubu ba? ai sai ka sani na wanke, ya ce ayya ai baza ki iya ganewa bane , sai randa ki ka fara mara kunya , karamar karuwa , kalmar da tamin zafi kenan na kara tsanan shi, wai ni ce karuwa nace eh to karuwar ce naga dai ba jikin wani bane koh? na koma gid cikin takaici , abokinshi yace amma aminina yarinyar nan bata da kuny , yace barta zata gane kurarta,kasan mata ba abin fadan soja bane, zan azabtar da ita ta manta hanya. a daren ranar muna tare da suraj ya bani waya kirar kamfanin samsung yar mai kyau da layinta duk gidanmu su ya abubakar ne ke da waya sai alhaji sai ko landline da ke falon kowacce matar gidan boyeta nakeyi cikin wando suraj sai ya kirani musha hira inba kowa a dakin. gaskiya inason karatu na , don haka na matsa ma suraj inaso mu gana, muna cikin motar shi ya dube ni menene kike son ganina baby duk ya kosa menene kike son ganina baby duk na kosa dare yayi danna amsa kirar gimbiya? mata na dan hada rai yace bakiyi kyau ba,ya juyo da fuskata gayamini mana sweetynah, nace nifa na gaji da sauri yace dame? nace da zama babu karatu ba zan boye maka ba tunda alhaji yace ka fito, to ka turo kawai ayi auran in yaso sai naci gaba a gidanka , tunda yanxun yaki, 'yan gulma suna gaya mishi muna tare. yayi shiru na lokaci can yace kin san yanda muka yi ta kai ruwa rana dasu daddyna kuwa? ban gaya miki bane saboda banason hankalin ki ya tashi sun dage kan cewa ban isa aure ba wai 21yrs me zance ma matar? kinji fa yanda nake jina garau ko 4 suka zuba mini. ai zasu sha mamaki , nace ni dai yanxun ba wannan ba mafita nake nema, tunda nima ai da saurana , auran dan dai rashin gata ne yasa za'a min yace. to ko in canza miki makaranta? na a'a wai raba ni ai kilama sai su mama sun tsine min duk mukayi shiru , a ranar dai har kusa 10:30 babu mafita kafin daga karshe mukayi sallama akan kowanne zaiyi tunani Abba ya daga kofin shayi yana sha kuma gefenshi anty ce amaryar shi yace kiramin hajiya ta mike ta nufi dakin hajiya anty haka yaran gidan suke kiranta bata taba haihuwa ba tana matukar son 'yakyan mijinta dayake ance mai da wawa na ne yasa suke matukar zaman lfy da momy hakan nan ya umar dan dakinta ne yanxun nan zakaji suna hada plan akan wani abun in ba'a son Abba yayi fada bayan sun dawo sun zauna , abba yace hajiya Aisha kin san dalilin kiranki? tace a'a yace na gaji da zaman umar haka, na bashi dama ta farko na bashi na biyu , na kuma nashi na uku wannn karon na gaji xan nemar mishi mata. momy tace gara haka ni kaina nayi nayi yaki saurarena amma ga anty tashi nan ina ga ita ce zata fini sanin meke faruwa? tunda itace abokiyar shawarshi yayi murmushi ya dubi anty tasu yace to ke anty su yaya kuke ciki da dan gidan naki? ya zama tuzuru anyi karatun anyi course din har so nawa am kuma aiki sai me? momy tace sai aure, anty tace kada ku damu, yarinyar da muke so ce tana kartu da a son ranmy sai in ta gama ya zama daidai da mun kammala gininmu Abba yace a'a wannan katafaran gidan na umar ya mishi kadan? anty tace ba nufin mu kenan ba, abba yace to ku sake shawara na baku wata 2 in lokacin ya cika babu wani bayani zakuji nawa bayanin maganar yarinya tana karatu ba ayi da aure ne? momy tace yi kai yace to. donhaka wannn cekarshen magna, anty tayi dariya tace munji abb insha Allah zakaji mu kafin lokacin dakaba mu . Na samu da kyar da taimakon hajiya da umma Alhaji ya yarda na koma makaranta bayannasha tsauraran dokoki nace wa bani ba suraj ,bani ba kananan kaya sannan in daina tsiwa na yarda duka zan bari amma banga zan iya ba, na koma makaranta cike da murna da farinciki.surajkam muna tare sai dai a waya, waya cikin sirri na rage saka wanduna sai dai riga da siket suma din damammun ne sai dai yan dan fi wandon haka yasa wasu sakar min fuska ganin su na shiryu. ya kishin gida bayan ya aje kofin gilashin da ya gama shan juice yanxu ya ciro wayarshi ya soma neman antynshi ringing na 2 ta daga yace Allah ya bar min antynah ya gidan? tace lfy ba lau ba , ya gyara zama me ke faruwa a gidan? tace abba ya bamu lokaci yace wata 2 in mun wuce haka za'a mana auren dole , ya saka dariya auren dole anty ai na wuce nan, ta sak. dariya da gaske Abba keyi har momy fa, yace ai momy ita ce ta zuga shi anty tace menene lbrn farida saboda gara asan nayi fa? yace tun wancan satin muna tare babanta ne matsalar yace bai yarda tsarin ana aure ana karati ba, ni kuma gaskiya inason yarinyar sai kinganta antyna , tana da kyau ga ilimi ga hankali, ga kamun kai samun kamar farida sai an tona Anty tace guri yayi nisa ne shiyasa ban ganta ba , yace hakane amma kinsan yanda zamuyi? tace a'a zan kirata a way,inji in har tana nan port din zanje mu ga yarda za'ayi Anty tace ya kamata ka sani ne? yace a'a tace kace manyanka zasu zo in yaso in sai a saka lokaci zuwa sanda zata gama makaranta yace kin kawo shawara antyna saidai nazo karshen wata suka ajiye waya tare da fatan alkhairi ga juna ina cikin saba sabulu naji wayata dake gefe ta soma ringing nayi sauri daukar zanina na goge hannuna jikina kam duk kumfa na daga wayar ina tsoron kar wani ya jiyo ni , nace suraj yaya ne? yace zakije party dinne? nace wanne kuma? yace na faisal kin manta ne? nace oh birthday din faisal kake magana? yace eh, zanje mana yace yauwa har naji dadi saboda kinsan in an tashi daga na gidan su akwai wanda muka shirya mishi iyaka mu friends da beb dinmu, a maharaja hotel nace duk a yau? yace eh na gidansu xa'ayi 3 zuwa 6 mu kuma 8 zuwa yanda ya samu nace zanje is dai kasan yanzu an samin takunkumin yawo kuma an amshe min wanduna na yace dan wannan karki damu zan sai miki wasu in mun hadu sai ki saka nace to zan san yarda zanyi in fito ko ban samu zuwa na gidan su ba sai muje chasun , yace haka ne tawn me kike yi ne yanzu? nace wanka fa nakeyi yayi driya kiyi da kyau babynah , nace take care, da sauri na karasa wankan na fito ina shafa mai ina tunanin irin karyar da zan sheka dan na samu fita da dare, gani da son party. [1:31PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1-----5 Gani da son party rawa dama sai kace indiya ta haifi ni, ranar dai na rasa mafit hour magrib, can dabara ta fadomin na samu mama a daki nace mama zanje in gaida momyn su rahma bata da lfy , ta dube ni zani da riga na saka ga wani zumbulelen hijabi na shema'u ne ma nasaka fuskarta ta nunamin taji ddin hak , sannan tace ki gaida ta nim zanje na dubata , nace to ina fitowa suraj na min waya, na dauka yace kin samu fitowa kuwa? nace eh ynxun na fito amma zanje gidan su rahma kasan da ita nayi karya, yace to in kin fito gidan su ki same ni a karshen titin laynsu nace to, mun gaisa da momy sannan naje gun rahma mun dan taba hour inda ta nunamin jin dadint da ganin shigar da nayi cewarta wai na fi kyau, nace zan tafi tace da sauri haka? nace ina note ne fa kika fadomin a raina naji ina son ganinki shi ne akace kar in dade, kin san an samin takunkumi, tayi dariya sannan tace bagashi ba ana ganin cin nasara? nace haka ne zan tafi in kinzo gidanmu mama tace ya jikin momy , kice da suki tace naje na ma momy sallama ta rakani ni hanya Ta rakani hanya nace ta barni nan tace to mukayi sallama na sameshi yana jirana cikin nota na shiga sai gidansu yau ce rana ta farko dana taba zuwa gidan su suraj dake badarawa. tangamemen gida mai matukar kyau, gefenshi daban ne yace bari muje ta can kusa da dakina kada a ganmu nace to na rude da kayan da suraj ya sai min, kaya ne hadaddun babies duk kala hudu ne amma babu riga dake da hannun arziki , wata ma iya cibiyata, ya soma cire min hijabi yana fadin gwada mu ga wadda zatafi yi miki kyau, kin san zanfi so ki fi bebs din gurin kyau, nace nima zanso haka na kwashi kayan nace bari na shiga nan in na saka sai nazo in nuna maka ko? yace in kinfi son haka shikenan amma inkn gwada a gabana cinye ki zanyi? nace a'a bana son kallo ne. (kawata ta birgeni) duk sun min kyau amma suraj yace na saka wanda tafi matse ni , tun da shi rigarshi tana da hannu daya kuma yafi son rigar nace suraj duba fa cibina a waje haka duk kirjina a waje yake yace ai shi ne hadewar nan na yarda nace gashi ba takalmi d kayan makeup yace karki damu bari na sato miki na mom dina kiyi makeup din Takalmi da jaka in mun fita sai mubi ta wani store din ki zaba, ya fita da sauri sai gashi dasu munata dariya , nace amma ka iya sata naga kana fita har ka sato, yace ai tana dakin dad shiyasa, na taje gashina yayi kyau na kama na dubi madubi nayi kyau matuka saidai nayi kama da 'yan iska (Allah ya shirya) haka nace ma suraj yayi ta mun dariya yace in anyi auranmu kayan da zan dinga saka mishi kenan yana gani nace na yarda kai tun a cikin akwatuna kada kasa atamfa ko leshi zaka zuba, yayi dariya yace kinga munzo da sabon salo kenan ko? nace za dai musha surutu ne, yace ayi tayi muka fito ya canja mota glass dinta mai duhu ce 'yar kucila toyota ce, muka fita sky store muka shiga na zabi wasu shegun takalmi masu tsawo da jaka bakake nan na kara fitowa na zabi sarka da dan kunne fashion na yan gayu sannan muka dauki hanya San da mukaje guri yayi guri zuwan mu sai ihu ga bigboy ya iso haka abokanshi suke kiranshi, nan fa naga bebs 'ya'yan masu kudi sai dai nasan duk da sunfi mu kudi ba mai nuna min kudi da body, da iya ado.don haka nima sai naji kaina yayi sama ai nima wata ce kuma suraj din suna da kudi fiye da suran ashe ma shine shuganan hada partyn. don haka sai na shiga duban su da dai bayan kyar gabatarwa da dan abin da ba'a rasa ba sai aka shga casu, nan fa da yawa 'yanmata suka sallama min samban san dare yayi ba ashe sha biyu, kuma na soma tsorata da yanda naga wasu yarinya da saurayi anyi cikin wani daki, suna manne da juna. kuma a dakin dundum da duhu duk sai na tsargu don ni iskancina bai kai nan ba, don hka sai nace suraj zan tafi gida, yace ki dan bari mana dare gurin ya gauraye da duhu an kashe wuta. suraj ya rungume ni babyna nefa sun dauke wuta, nace muje ka kaini gida don Allah kasan fa da wayo na fito, kmin na karasa sai naji hannu a kirjina da saur nace menene haka suraj? na bige hannun sai nake jin nishin mutanan gurn wani gurnanina fahimci wato masha'a akeyi Nan na soma laluban hanya, suraj yana rike dani nace sake ni tafiya xanyi nan ya soma min korafin banason shi, shi yasa banason yana tabani nace wace irin tabawa ce baka yi min suraj? sa rai fa nason Allah ya hana amma saboda son da nake maka da kuma yanda banason bacin ranka na barka kana tabani na fit waje kafin na fitan ma sai karo akeyi da mutane. suraj ya biyo ni yana ta faman bani bak ya sha gabana ya rike min hannuwa, lallashina yakeyi har da hawayenshi wai yana cikin wani hali in taimaka mashi nace gaskiya suraj ba zanyi zina ba, na kwace hannuna na tafi , ya tsaya yana kallona, can yace baby in nayi da wata baza ki damu ba? ko juyowa banyi ba bare in bashi amsa gabana ke mugun faduwa ganin hanya shiru, lallai dare yayi na ciro wayata ina duba lokaci 12:30 na dafa kirji nace na shiga 3 ! na kara sauri titi na mika babu kowa sai motocin dake wucewa jifa jifa. Wata mota ta tsaya da sauri na isa gurin dan neman taimako samari ne guda 2 a ciki suna shan sauti na bayanne yace shigo mana baby nace taimako nake so sabon kawo zanje , suka ce shigo mun kai badarawa sunata min surutan banza, hardai na bayan ya soma dagamin kafada tare da fadin baby ko zamuje mu dan huta na awa 2 kacl ni awa 1 abokina awa1 ? na dube su cikin takaici nace, ni ni ba 'yariska bace da zaka ce muje a huta , sai naga sun hada ido sun kwashe da dariya. direban ya ce haba yarinya duk wanda ya dube ki yaga cikakkiyar karuwa sai dai in zaki mana rowa takaci ya kamani nace kune dai yan iska bani ba, suka ja suka tsaya ke 'yar bariki kada ki gaya mana magana, sauka nace sai me in an saukan na fita suka ja motor nace 'yan iska kawai. Tafiya nake har ma bansan gurin da nake jefa kafa ba, sai jin taka birki nayi quuu a bayana kan in kauce har motar ta bangaje ni sai gani a kasa, fitilar motar ta dallare ilahirin gurin da haske, ban tashi dga kasan ba naji taku tafiyar mai motor tsoro ne ya kamani a raina nace kilama dan yankan kai ne, takalmin shi na fara kallo gabana ya fadi na dubi wandon soja ne , na fada a raina shi kenan zai kasheni da duka, yce ke na dube shi da sauri saboda muryanshi dana ji gabana yayi mummunar fadywa na'am na ambata ya umar jikina ya soma bari yace ke me sunanki ma? nayi shiru ya dakamin tsawa ya sunan ki nace? nace asma'u , yace tashi da tsawa yakemin magana na tashi yana dubana tamkat yaga kashi cike da tsana yace lallai yarinyar nan kin fita daga sahun kananan karuwai kin koma cikin manyansu, lallai an jibga asarar haihuwa wannan ai gwara barinki da haihuwarki, amma bakiyi halin mama da alhaji ba kai kaf gidanku kece fitinanniya banma san sanda aka haifeki ba, amma har kin kware da bin maza yaja tsaki tare da tsirtar. da miyau ya wuce ya shiga motar shi Hakika naji zafin zagin da ya umar ya min, amma hakan bai hana ni yin saurin zuwa kusa da kofar motarshi nace ka taimaka min ya umar don Allah gida zani ya mini wani kallo sannan yace god for bid in dauki najasa cikin motta? bani ba ban kasance mazinaci ba ba zan dauki mazinaciya ba ya tada motarshi tare da fadin ba kwanan gida zaki je ba? dan rashin imani irin na soja haka ya uwar ya tafi ya barni . ina tafe ina kukan bakin cikin zuwana gurin partn nan nayi nisa da tafya naji wata motar na kauce kar a buge ni, ashe suraj ne haushinshi ya kama ni ya tsaya yana baby zo muje in kai ki gida nayi mishi banza naci gaba da tafiya, yayi parking ya fito haba baby yi hakuri nima sai daga na gane ban kyauta ba, na tsaya danaji haka ya iso zo muje nace kaje kayi da wata dinne? yace iye, a'a haba dai ya shiga 'yan kame-kame naje na shiga motor na ce dubi time suraj kai baka damu ba ko kashe ni za'ayi kashe yi ko? yace a haba yanzun dai ya zamu yi? nace ina kayana , yace gasu can gidanmu, can muka wuce na can za sannan ya kuma dauko ni har maigidansu Har maigadinsu yana ce mishi surajo ina zaka da dare nan yace yana zuwa. tun kafin mu kai gidnmu muke ta neman mafita a karshe ya kaini wani kemin aka dan sa min bandeji a ciwon da naji na kafa sakamakon bigeni da ya umar yayi sai ya kaini gidan wata kawar mama dake rafin guza yace wai ya buge ni ne shi ne na suma to ban farfado ba da wuri sai yanxun shi ne yace ina ne gdanmu na ce rafin guza , na nuna mishi nan gidan nayi shiru na sunkuyar da kai ina mamakin yanda suraj yake tsaro karya . hajiya rabi ta kama dama ta mijinta ya rasu daga ita sai 'ya'yanta shi yasa nace ya kaini can, ka bugu biyu zuwa na uku ta bude gnina yasa ta shiga rafka salati tare da tambayar ko lfy? kafin nayi magana suraj yace ko kin san wannan yarinyar? tace kwarai 'yata ce nan ya shga koro mata karya ta hau kai ta zauna musamman da ya nuna mata plaster kafata . ta shiga gero mishi godiya sannan ta jani cikin gida, kafin na kwanta sai da hajiya rabi tadafa ruwan zfi a kettle ta gasa min kafar da nake ta dingishin karya , nayo wnkasannan Nayo wanka sannan ta tambaye ni yanda abin ya faru, nan na karkacr na sharaara mata karya da cewa ina tafiya n dwo gidan kawata kawai sai naji taka birki ko kafin in ankare har motar ta bugeni, daga nan ban kuma sanin komaiba sai a kemis ni fa ma bansan sanda nace mas a rafin guza gidanmu yake ba, sai da naga mun shigo unguwar sai kuma Allah yasa na nagane nan gidan barka da arziki hajiya rabi ke ta yi min. kafa 'yar albarka dana dinga liliyata cikin dare don ta kumbura kan safe har ta tashi gurin ciwon yayi fushi ya kumbura , don haka nayi murna sosai sanda muka isa gidanmu tuni hankular 'yan gidanmu ya gama tashi banda maama wacce ta ce yawon iskancina na tafi, har umma da hajiya suna cewa ta bar cewa haka yanxun duniya ta lalace. bayan an gama karade unguwa da nemana sai gamu mun iso ina ta dingishi . hajiya rabi tana min sannu.'yan gidanmu suka biyo mu dakin mama suna tambayar meya faru? na yarda da haj. rabi in dai gurin bada kanu ne, domin yand take rattafo zancan babu mahalukin da zi ce ba' gabanta abin ya faru ba, [1:33PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----6 Su anty aina'u da umma da hajiya sun tausya min sabanin mama wacce tace ita wannan zncen bai shige ta ba, na dai tafi yawon iskancina ne. jin hakan yasa naa fashe da kuka tare da rantse rantse cewa mota ce ta buge ni, umma tace haba mama yarinyar tsautsayi ya same ta, mma kice haka? hajiya rabi kuma mikewa tayi tana fadin ni kinga tafiyata don na kula bamma miki gwaninta ba . mama tace haj.rabi ba nufina kenan ba , nagode hajiya rabi tace dama tun jiyan take min kukan tasan kila ace karya ne. hajiyan gidanmu tace wani irin karya? nan dai mama tayi shiru ba don ta yarda ba sai don ganin babu wanda ya goya mata baya. haka makota suka yi ta zuwa jaje amma da yawa gulma ce ta kawo su, lbrn ma sa canza shi akeyi har da masu cewa an sace ni ne, dayawa dai sunce party naje yan sanda suka kawo hari gurin gudu mota ta bige ni, nace kowa dai yayi ya gama ni dai dama Alhajinmu nafi ji kuma tunda ya yarda har da kaini asibiti a duba ni ko na bugu a wurin gurin mama ko haushin maganar takeji domin ta hakikance karya ne. Momy da anty suka gaisa da mama tare da mata jajen kade ni, tsaki mama taja sannan tace kema hajiya aisha kin yarda? wannan zancen karya ne momy tace haba ke ko maman su aina'u me yasa zaki dinga biye ma surutun 'yan unguwa? duk da rashin jin asma'u ai ba zata prtyn dare ba, dn 'yarki ta samu hatsri shi kenan ki bita da mugun zargi, anty tace Allah ya shirya mana, mama ko cewa tayi dama aike tuni baki son laifin asma'u hajiya Aisha momy tace ai ni 'yar gidana ce duk cikin yaranki babu wacce nakeso kamarta. mama ta ce lailla don ba zaune kuke guri guda da ita ba, sun fito mama ta dan tako musu suka tafi gida suna shirin shiga ne anty tace momy ga motar dan gidana yaushe ya shigo kd? mama ta dubeshi yana kokarin parking tace kila ma nan ya kwana ya karaso cike da fara'a yana fdin daga ina ku ke? momy ce ta soma cewa Allah sarki yarinyar nan ce 'yar gidan hajiya saude tsautsayi ya same ta, yace 'yar gidan mama? tace eh yace aina'u ko fatima? anty ta amshe da cewa asma'u din nan, itace wai mota ta kade ta ta suma har ta kwana gidan wata kawar mama din Mamaki ya cik shi yace yaushe? momy tace shekaran jiya da dare, zuwa gidan kawarta gada maman kawar an ce bata ma dade ba a gidan su rahman tsautsayi ya fito da ita tun kilama akan layin ne motar ta kade ta har karfe dayan dare bata farfado ba, ya umar yayi tsaki sannan yace wannan 'yar iskar yarinyar ba wata mota yawonta.... momy ta katse shi to sarkn zargi kai da ba ma anan kake ba na kasan tana yawon taja tsaki ta nufi ckin gida tana fadn ni banason sharri wlh , anty tace momy kenan ta dai tana son yarinyar nan , yace kin sani ne anty? can fa na ganta guraran badarawa tana tafe tana hada hanya kamar me maye, to karewa nine na buge ta kuma bany zaton taji wani ciwon kirki ba, anty tace kai haba? yace Allah kuwa shgarta ma in kin gani rin ta manyn karuwai, Allah dai ya shirya anty tace Amin, yaushe kazo? yace tun shekaran jiya ina nan kd . bani n.d.a bani jaji kin san mun kusan gama course dinnan kuma muna sa ran karin girma ne ,tace Allah yasa yace amin suka shiga ciki WACECE FARIDA JUMARE? Farida jumare 'yar asalin jihar yola ce kyakkyawa tamkar balarabiya , mahaifin ta malam jumare mutum ne shi mai tsananin son abin duniya , haka matarshi maimuna.'ya'yansa sune jarinsa don baya yarda dan talaka ya auri 'yarsa. ya aurar da yara 3 kafin farida daya tana aure a abuja anty sa'adatu, any lami tana kano

Chapter 2 of 16