Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 14
huta da takaicin wannan bakin ciki da ya kunsa mini." Haka ita ma Hayatunnufusi ta fada masa tamkar yadda Badura ta habarta masa, ita ma tana kuka, ta fada masa har da kuyangarta ya kashe. Ta kara da cewa, muddin ba a hukunta Amjadu ba, to, za ta fada wa mahaifinta Sarki Armanus domin ya nema mata hakkinta a kan Amjadu. Allah ya kiyashe mu da sharrin mata. Haka dai matan nan, Badura da Hayatunnufusi, suka kalallame Kamaruzzaman da karya suka dauki laifin duniyar nan duka suka aza wa 'ya'yan nan nasu, su dai idan asirinsu zai rufu, to, ko da Sarki zai sa a kashe 'ya'yan, ba su damu ba. Suka rika kuka suna marin fuskokinsu. Yayin da Kamaruzzaman ya ji jawabinsu, kuma ya ga suna kuka, har suna marin fuskokinsu sai ya yarda da maganarsu. Nan take ya harzuka, ya cika da fushi har idanunsa suka rika rufewa. Ya zari takobi ya fita waje da nufin kashe 'ya'yansa... Yusuf Æbdullâhi Æ Jibaga ke muku barka da shanruwa'29 HIKAYAN KARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN Yayin da Kamaruzzaman ya ji jawabinsu, kuma ya ga suna kuka, har suna marin fuskokinsu sai ya yarda da maganarsu. Nan take ya harzuka, ya cika da fushi har idanunsa suka rika rufewa. Ya zari takobi ya fita waje da nufin kashe 'ya'yansa. Yana fita sai suka yi kicibis da surukinsa, Sarki Armanus, shi kuma ya zo domin ya yi masa barka da dawowa daga wurin farauta. Sai ya ga Kamaruzzaman rike da takobi tsirara, idanunsa sun juye sun yi jawur kamar gauta, ga kuma jini yana diga daga hancinsa saboda bacin rai. Ya tambaye shi, me yake faruwa. Kamaruzzaman ya fada masa laifin da matansa suka ce Amjadu da Asadu sun aikata gare su. Ya kara da cewa, "na yi niyyar zan kashe su a cikin wannan sa'a, mummunan kisa, domin hakan ya zama misali ga masu aikata mummunan laifi irin nasu." Sarki Armanus, wanda shi ma tuni ya fusata da jin laifin da yaran suka aikata, ya ce "ya dana, hukuncin da ka dauka ya yi daidai, muna rokon Allah ya la'ance su, ya la'anci dukan 'ya'ya masu hali irin nasu." Ya ci gaba da cewa, "amma abin da nake so da kai shi ne, su duka dai 'ya'yanka ne, don haka kada ka kashe su da hannunka, domin idan ka yi haka, abin zai tsaya a cikin ranka har abada, watakila ma sai ka yi da-na- sanin kashe su da hannunka da ka yi wata rana, lokacin da da-na-sanin ba ta da amfani. Domin kuwa masu iya magana sun ce, abin da duk ido ya gani shi zuciya kan rike, amma abin da duk ido bai gani ba, to, zuciya ba ta tunaninsa. Ka tura hauni ya daure su, ya tafi da su daji, cikin rairayin hamada, ya sare kawunansu, ya turbude gawarwakinsu can cikin rairayi." Kamaruzzaman ya ga cewa jawabin surukinsa abin kamawa ne, sai ya mayar da takobinsa kube. Ya nufi fada ya zauna. ya sa aka kira masa hauni. Shi wannan hauni wani tsohon mutum ne mai yawan shekaru, wanda bai taba saba wa umurnin Sarki ba. Da ya zo, sai Kamaruzzaman ya ce masa, "ka tafi wurin 'ya'yana, Amjadu da Asadu, ka daure su da igiya. Ka rufe kowane dayansu a cikin akwati, ka aza wa alfadara akwatuna. Ka tafi da su tsakiyar rairayin hamada ka sare kawunansu, ka ciko mini goruna biyu da jininsu, ka yi sauri ka kawo mini." Hauni ya dukar da kai cikin ladabi, "na ji, na amsa, Allah ya ba ka nasara." Ya tashi da hanzari ya fita, ya nufi wurin Amjadu da Asadu. Sai ya hadu da su, sun caba ado da kaya masu daraja, za su gun mahaifinsu domin su yi masa barka da dawowa. Yayin da hauni ya gan su, sai ya durkusa a gabansu ya ce, "ya 'ya'yana, ku sani cewa ni, bawa ne umurtacce. Mahaifinku ya ba ni umurni a kan ku, ko za ku bi umurninsa?" Suka amsa, "na'am." Ya tashi ya kama hannuwan kowane daya daga cikinsu ya daure da igiya, ya saka kowa a cikin akwati. Ya aza wa alfadara akwatunan, ya hau dokinsa ya kora, suka fita daga cikin birni, suka nufi cikin daji. Can zuwa rana tsaka, suka isa cikin yashin hamada. Ya sauke akwatuna, ya fitar da Amjadu da Asadu. Bayan ya fito da su daga cikin akwati, ya ga irin kyawun yaran nan, sai tausayinsu ya kama shi, har ya zubar da hawaye. Daga nan ya zare takobinsa, ya ce, "wallahi zuciyata ba ta so abin da zan aikata a gare ku ba. Sai dai ni, bawa ne umurtacce, ku sani cewa, mahaifinku Sarki Kamaruzzaman ya umurce ni da in sare kawunanku, sa'annan in cika masa goruna biyu da jininku, in kai masa. Amjadu da Asadu suka ce, "cika umurnin mahaifinmu, za ka same mu masu tawakkali ga abin da Allah ya kaddara bisa kawunanmu, domin shi ne masani a kan kome." Suka rungume junansu suna hawaye, suka yi wa juna ban kwana. Daga nan sai Asadu ya ce da hauni, "ya kaka, ka yi wa Allah ka fara kashe ni da farko. Kada ka fara kashe dan uwana, Amjadu a gabana, domin wannan zai sa hankalina ya tashi." Amjadu kuwa ya ce da hauni, allambaran shi zai fara kashewa, domin ba zai iya juriyar ganin an kashe Asadu da farko ba. Ya kara da cewa, "ka ga shi kanena ne, don haka zuciyata ba za ta iya jimirin ganin an kashe shi a gabana ba. Suka yi ta jayayya bisa ga haka, suna kuka. Tausayi ya kama hauni, shi ma ya fashe da kuka. Amjadu da Asadu suka ce da junansu, "wannan abu ya faru saboda makircin mahaifanmu, da kuma rashin bayyana wa mahaifinmu gaskiyar al'amari, wannan shi ne sakamakon rufa musu asiri da muka yi. Amma babu tsimi babu dabara face daga Allah madaukakin Sarki, gare shi muka dogara kuma gare shi muke neman taimako." Asadu ya rungume dan uwansa yana kuka, ya wake wadannan baitoci: Ya wanda mafaka da wurin kai kara suke gare shi, Kai ne wanda ya isa ga dukan abin da ya abku. Ba ni da dabara face kwankwankwasa ga kofarka Idan ka juyar da ni wace kofa zan kwankwasa. Ya wanda taskokin kyauta tasa suke cikin fadin Kur'ani Ka amince da mu, cewa alheri dukansa ya taru gare ka. Yayin da Amjadu ya ji wakar dan uwansa, sai ya rungume shi ga jikinsa, shi ma yana kuka, ya wake wadannan baitoci: Ya wanda kyautarsa gare ni ta kasance mai yawa' Ya wanda kyaututtukansa suka suka fi karfin a kidaya. Musiba da dai ba ta same ni ba a cikin zamanina Face na garzayo gare ka ka riki hannuna. Bayan ya gama waka sai ya juya wurin hauni ya ce, "na gama ka da Allah, wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai shi, ka fara kashe ni kafin ka kashe dan uwana. Domin kuwa ba zan iya jure ganin yadda za ka kashe shi ba." Asadu ya yi kuka, ya ce, "a'a, ni zai fara kashewa, domin ba zan iya ganin an kashe ka a gabana ba." Daga nan sai Amjadu ya ce, "to, mu rungume junanmu, fuskokinmu na kallon juna, sai ya sare kawunanmu a cikin sara guda." Suka rungume junansu, fuskokinsu na kallon juna. Hauni ya daure su da igiya yana kuka. Bayan ya gama daure su sai ya dauki takobinsa, ya ce, "na rantse da Allah, ina matukar takaicin abin da zan aikata muku. Ba ku da wani sako da za a kai wa mahaifinku?" Amjadu ya ce, "babu wani sako a gare mu. Amma ina neman alfarma, ka dawo daga bayana yadda takobinka za ta fara sauka a kan wuyana, ya kasance ni na fara mutuwa. Bayan ka kashe mu, idan ka koma gida mahaifinmu ya tambaye ka, 'me suka ce kafin ka kashe su?' Ka amsa masa, 'ya'yanka sun ce suna gaishe ka, sa'annan sun ce a fada maka, ka yi hukunci ba tare da ka tabbatar da mai laifi ba, tsakaninsu da wadanda suka kawo kararsu gare ka. Sa'annan ka wake masa wadannan baitoci: Ku sani mata shaidanu ne wadanda aka halicce su a gare mu. Muna neman tsarin Allah daga kaidin mata Su ne asalin musiba wadda ta bayyana a tsakanin talikkai, duniya da lahira. Yayin da Amjadu ya gama rera wadannan baitoci, sai ya kara rungume dan uwansa, ya kankame shi ga jikinsa har suka zama kamar mutum daya. Amjadu ya ce da hauni, "ina rokon ka, ka jinkirta mana har in rera wadannan baitoci ga dan uwana. Sai ya rera wannan waka, yana cewa: A cikin matafiya na farko na daga sarakuna mafiya hankali daga gare mu. Da yawa sun wuce cikin wannan tafarki na daga manya da kanana. Yayin da hauni ya ji wannan waka, ya yi kuka, kuka mai yawa har gemunsa ya jike da hawaye. Shi kuma Asadu sai ya wake wadannan baitoci yana cewa: Zamani zai juya daga bayanmu mai bakanta ciki. Bayan mun nesanta, kuka ba ya amfana ga tsoffi da yara kamarmu. Ba darare nake fadi ba su wanzu gare mu na daga daren hira. Dare maciki wanda aka hade abin hadewa a cikin zuciya. Yayin da ya fito zai bata zuciya gida da waje duka. Bayan ya gama wannan waka ya yi kuka har hawayensa suka jika gaban rigarsa, sai ya rungumi dan uwansa, suka manne wuri daya, ka ce su jiki daya ne. Hauni ya zare takobinsa, ya daga shi sama da niyyar zai sare su. Daga takobin nan da ya yi da karfi, sai ya yi wata kara a cikin iska fauu. Wannan kara sai ta razana dokinsa da yake kusa, ya katse igiyar da aka yi masa dabaibayi, ya runtuma da gudu, ya yi cikin daji. Da hauni ya ga yana shirin yin asarar dokinsa mai kimar dinari dubu, da kuma shimfidar dokin, wadda har ma ta fi dokin tsada. Sai ya yarda takobi, ya bi bayan dokinsa da gudu domin ya kamo shi. Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ZANCI GABA INSHA ALLAH30 HIKAYAN KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN da hauni ya ga yana shirin yin asarar dokinsa mai tsada, sai ya yar da takobi, ya bi bayansa da gudu domin ya kamo shi. Ya bar Amjadu da Asadu a daure, suna tsaye cikin zafin rairayin hamada. Doki ya ci gaba da gudu cikin tsoro, yana tayar da kura daga bayansa har ya fita daga cikin rairayi ya shigi cikin wani surkukin daji. Da zuwan hauni bai yi wata-wata ba, sai ya kutsa kai cikin surkukin nan. To, ashe a cikin surkukin itacen nan akwai wani tsohon zaki mafadaci, mai idanu kamar garwashin wuta, fuskarsa abar tsoro ga duk mutumin da ya gan ta. Yayin da zakin nan ya ji motsi, sai ya fito daga inda yake kwance. Yana fitowa sai suka yi arba da hauni. Lokacin da hauni ya ga zaki, ga shi kuma ya jefar da takobinsa, babu wani makami a hannunsa da zai kare kansa da shi, sai ya ce a cikin ransa, "babu tsimi babu dabara, face daga Allah madaukakin Sarki. Hakika wannan bala'i ya auka mini ne sanadiyyar Amjadu da Asadu da na yi niyyar kashewa ba tare da alhakinsu ba." Suka ci gaba da kallon juna, shi da zaki. Zaki na nazarin ta inda zai fada masa, shi kuma yana ta karanta dukan addu'o'in da suka zo a cikin ransa. Amjadu da Asadu kuwa suka yi ta jiran dawowar hauni, zafin rana da kishirwa suka fara koda su, suka yi ta kiran hauni amma ba su ji ya amsa musu ba. Suka ce da junansu, "kai, da wannan azaba da muke ciki ai gwamma a ce ya sare kawunanmu mun huta." Asadu ya ce, "watakila dokinsa tausayinmu ya ji, ba ya so a kashe mu, shi ya sa ya gudu, wannan kuma hukunci ne na Allah madaukakin sarki, mai adalci." Daga nan sai suka yi ta mutsu-mutsu da jikinsu har daurin igiyar ya sassabe, suka kwance junansu. Suka yi shawarar su gudu, sai kuma suka ce, "wallahi ba za mu gudu ba sai mun ga abin da ya faru ga hauni. Suka dauki takobi suka bi sawun hauni da dokinsa. Suka yi ta bin sawu har suka zo hanyar da za ta shiga cikin surkukin itacen nan. Suka ce, lalle hauni da dokinsa na cikin wannan wuri. Asadu da ke rike da takobi, ya ce wa Amjadu, "jira ni nan, bari in shiga in ga abin da ke ciki." Amjadu ya ce, "wallahi ba ni barin ka ka shiga kai kadai, sai dai mu shiga tare, idan mutuwa ce, mu mutu tare kamar yadda muka tashi tare." Suka kutsa kai cikin surkukin nan, suka tarar da zaki ya bangaje hauni, ya aza kafafunsa na gaba bisa kirjin hauni. Shi kuwa hauni yana kwance rigingine, kamar tsuntsun da aka harbe, idanunsa a rufe. Ya daga hannuwansa sama yana ta salati, yana neman taimako daga Allah. Yayin da Amjadu ya ga haka, sai ya fige takobi daga hannun Asadu. Ya nufi zakin nan, ya tsarga kansa gida biyu, ta tsakanin idanunsa. Zaki ya fadi kasa matacce. Yayin da hauni ya ji zaki ya fadi kasa, sai ya bude idonsa ya mike tsaye da sauri yana kaduwa. Yana kokarin cika bujensa da iska sai ya lura da Amjadu da Asadu tsaye a gabansa. Amjadu na rike da takobi, jini na diga daga gare Ta, ga kuma zaki yashe a kasa matacce. Nan take ya fahimci abin da ya faru, ya fadi kasa yana sumbatar kafafun Amjadu, yana cewa, na gode wa Allah da ya sa ban kashe ku ba, domin na tabbata babu alheri a cikin kashe ku. Kuma ina gode muku a kan kubutar da rayuwata da kuka yi daga halaka. Zan fansar da raina a wurin Sarki domin kubutarku. Daga nan ya mike tsaye ya rungume su. Ya tambaye su yadda aka yi har suka kwance daga daurin da ya yi musu da igiya. Suka fada masa yadda suka yi ta kici-kici har daurin igiyar ya sassabe, daga nan suka kwance kan su, suka dauki takobinsa suka biyo sau. Ya yi ta yi musu godiya har yana hawaye. Suka ce masa, "dauki takobi ka cika umurnin mahaifinmu." Hauni ya ce, "Allah ya tsare ni da in cutar da ku, ai ko wani na ga zai cuce ku, zan kare ku sai inda karfina ya kare. Ku ba ni rigunanku in dulmiya su cikin jinin zakin nan, sa'annan in cika goruna biyu da jininsa in dauka in kai wa mahaifinku, in ce masa na cika aikina. Ku kuma ku nufi naku wuri, domin kasar Allah yawa gare ta. Idan an ki ka da yini wani wuri, wani wurin sai a so ka da kwana." Hauni ya ci gaba da cewa, "wallahi zan yi bakin cikin rabuwa da ku." Suka yi kuka dukansu. Amjadu da Asadu suka tube rigunansu suka ba hauni, shi kuma ya tube wani mayafi nasa babba, ya keta shi biyu, ya ba kowa daya suka rufe jikinsu. Ya tsoma rigunansu cikin jinin zaki, ya kuma cika goruna biyu da jinin. Ya hau dokinsa, ya sukwane shi sai cikin birni. Ya isa wurin Sarki Kamaruzzaman, ya fadi kasa ya yi gaisuwa. Kamaruzzaman ya dube shi, ya ga duk ya fita daga cikin hayyacinsa, sai ya yi zaton hakan na da alaka da kashe 'ya'yansa. Shi kuwa hauni yana tunanin fitar kutsu da yi yi ne daga hannun zaki, yana kuma tausayin Amjadu da Asadu bisa ga halin da za su shiga. Kamaruzzaman ya tambaye shi, "ka aiwatar da umurnina?" Hauni ya sunkuyar da kansa kasa, "na cika umurnin Sarki, kamar yadda ya bukata." Ya jawo riguna duk sun rine da jini, da kuma gorunan da ya ciko da jini, ya ajiye a gaban Kamaruzzaman. "Sun yi maka gardama kafin ka kashe su?" "A'a, Allah ya ba ka nasara. Sun kasance masu hakuri bisa ga abin da Allah ya kaddara musu." "Sun ba ka wani sako zuwa gare ni?" Hauni ya share hawayen da ke kokarin fitowa daga idanunsa, "sun ce a gaya maka, suna gaishe ka. Kuma ba su ga laifinka ba a kan hukuncin da ka yi musu. Sa'annan sun ce in rera maka wannan waka: Ku sani mata shaidanu ne wadanda aka halicce su a gare mu. Muna neman tsarin Allah daga kaidin mata Su ne asalin musiba wadda ta bayyana a tsakanin talikkai, duniya da lahira. Lokacin da Kamaruzzaman ya ji wannan waka, sai ya sadda kai kasa, ya yi jugum yana tunani. Ya tabbatar da cewa babu makawa ya kashe 'ya'yansa cikin kuskure, ba tare da sun aikata wani laifi ba. Ya tuna da irin makirce-makircen mata, sai jikinsa ya yi sanyi. Ya dauko rigunan 'ya'yansa, wadanda hauni ya kawo masa, ya rika jujjuya su ga hannunsa yana hawaye. Sai ya ji takarda a cikin aljihun rigar Asadu, ya sa hannu ya dauko ta, ya gan ta nannade da gashin mace. Da ya warware ta sai ya ga rubutun Badura, ya karanta abin da ke ciki. Daga nan ya gane cewa, Asadu ba shi da laifi. Ya lalubi aljihun rigar Amjadu, nan ma ya ga takarda nannade da gashin mace. Ya warware ta ya ga rubutun Hayatunnufusi ne. Ya karanta abin da ta kunsa, ya tabbata shi ma ba shi da laifi. Sai ya fara tafa hannuwa yana sallallami. Kamaruzzaman ya yi kuka, ya yi da-na-sanin daukar maganar mata ba tare da bincike ba, lokacin da da-na-sanin ba ta da wani amfani. Ya tabbata ya auku cikin makircin mata wanda ya dade yana taka-tsantsan domin gudun aukuwa cikinsa. Ya sa aka gina masa wata babbar kubba a cikin gidansa, aka siffanta kaburbura guda biyu a cikin kubbar, kabari daya aka rubuta sunan Amjadu, daya kuma aka rubuta na Asadu. Ya kira wannan kubba da suna 'Kubbar Bakin Ciki'. Ya kasance kullum yana cikin wannan kubba yana kuka. Idan ya rungumi kabarin Amjadu ya yi waka, sai kuma ya rungumi kabarin Asadu ya yi waka. Ya kaurace wa matansa da jama'arsa duka, ya kulle kansa a cikin Kubbar Bakin Ciki' Al'amarinsa ke nan. Amma Amjadu da Asadu kuwa bayan hauni ya tafi ya bar su, sai suka ba jihar da birninsu take baya, suka kutsa kai cikin daji, ba su san inda za su ba. Suka yi ta tafiya tsawon wata guda, suna cin 'ya'yan itatuwa suna kuma shan ruwan tafkuna da koramu har suka fara hango wani tsauni na bakin dutse, gungurum a gabansu. Da suka iso gindin tsaunin sai suka ga hanya ta rabu gida biyu, daya ta zagaya ta gefen tsaunin daya kuma ta hau ta bisansa. Suka tsaya suna shawarwarin wadda za su bi, suka yanke shawarar su bi hanyar da ta bi ta gefen tsaunin, watakila ta fi saurin kai su ga gari, kuma a nan za su rika samun ruwan koramu suna sha. Suka bi wannan hanya tsawon kwana biyar, amma ba su hango ko alamar gari ba. Sai suka juyo da baya, suka dawo mararrarbar hanyoyin nan. Suka dauki hanyar da ta bi ta saman tsauni. Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ke muku barka da shan ruwa 31 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN Amjadu da Asadu suka dauki hanyar da ta bi ta saman tsaunin suka yi ta tafiya tsawon wannan rana har dare ya yi. Suka gaji likis domin ba su saba da tafiyar kasa ba, balle hawan tsauni. Asadu, wanda ya gaji fiye da Amjadu, ya ce, "ya dan uwana, wallahi na gaji sosai." Amjadu ya ce, "yi hakuri dai mu tafi, da sannu Allah zai taimake mu." Suka tsaya suka huta, daga nan suka ci gaba da tafiya, suna jan kafafu saboda gajiya. Da suka kara tafiya, kamar ta kafa hamsin, sai Asadu ya fadi kasa yana kuka, ya ce,"ya dan uwana, ni kam karfina ya kare, ba zan iya kara ko da taku daya ba daga nan." Amjadu ya tsaya suka dan sarara, sa'annan ya saba Asadu bisa kafadarsa. Ya ci gaba da tafiya da shi da kyar, yana nishi. Yana yi yana hutawa. Can zuwa hudowar alfijir suka kai kololuwar tsaunin, suka iske wata korama mai gudana da iccen ruman a gefenta. Suka yi matukar farin ciki, suka sha ruwa daga koramar, suka tsinko 'ya'yan ruman suka ci har suka koshi. Daga nan suka kwanta, barci ya kwashe. Ba su farka ba sai da rana ta take. Suka yi wanka, suka kara ci daga 'ya'yan ruman suka kwanta. Da rana ta yi sanyi suka tashi domin ci gaba da tafiya, amma sai suka ga duk kafafunsu sun kumbura saboda tafiya. Don haka sai suka zauna wannan wuri tsawon kwana uku. Bayan sun huta sosai, karfin jikinsu ya dawo, sai suka ci gaba da tafiya, suna gangarawa kasan tsaunin. Suka yi ta tafiya kwana da kwanaki, har suka kusa su halaka saboda kishirwa. Can sai suka fara hango wani babban birni a gabansu, suka kuwa yi masa tsinke cikin murna da farin ciki. Da suka yi kusa da wannan birni sai suka fara godiya ga Allah madaukakin Sarki. Amjadu ya ce da Asadu ya dakata nan tukuna, ya shiga cikin birnin ya binciki yanayin mutanensa. Ya kara da cewa, "ka san duniya da fadi take, kuma kowane birni da kalar al'adarsa. Bari in shiga in bincika mana wane birni ne wannan, wanda da a ce mun zagayo masa ta hanyar da ta bi kasan tsaunin nan, da mun kwashe shekara cikakkiya ba mu iso gare shi ba. Mun gode wa Allah da ya kubutar da mu." Asadu ya ce, a'a, shi tsoro yake ji Amjadu ya tafi ya bar shi nan shi kadai. Don haka shi zai shiga cikin birnin ya binciko musu yanayin jama'arsa. Amjadu ya ce, "to, tafi. Amma kada ka jima." Ya laluba aljihun wandonsa ya dauko wasu 'yan dirhamai ya ba shi, ya ce ya sayo musu abinci da abin sha idan zai dawo. Asadu ya karbi kudi ya gangara daga kan tsauni, ya shiga cikin birni, ya bar Amjadu nan yana jiran dawowarsa. Da shigarsa cikin birni sai ya hadu da wani tsoho, mai dogon gemu. Gemun nasa ya kawo har ga kirji an kuma raba gashin gida biyu. Yana tafiya yana dogara sanda, ya sa tufafi masu kyau irin na tajirai. Ya nada wani dimemen rawani, mai launin ja, bisa kansa. Yayin da Asadu ya gan shi, sai ya yi mamaki yanayin wannan shiga tasa. Ya matsa kusa gare shi, ya durkusa ya gaishe shi cikin ladabi, sa'annan ya tambaye shi hanyar zuwa kasuwa. Tsoho ya dubi Asadu ya yi murmushi, ya ce, "samari, amma kai bako ne ko?" Asadu ya ce, "I, baffa. Ni bako ne." Tsoho ya dafa kafadar Asadu ya ce, "hakika birninmu ya yi maraba da zuwanka dan samari, birninku kuwa zai yi bakin ciki da tafiyarka." Ya tambayi Asadu, "me za ka yi a kasuwa?" Asadu ya amsa masa, "zan sayo abin da za mu ci ne, ni da dan uwana da na baro a bakin gari. Mun fito ne daga gari mai nisa, watanninmu uku muna tafiya kafin mu iso wannan gari." Tsoho ya ce, "ai kuwa daurinka ya katse a gindin kaba. Yau nake bikin aurar da 'yata, na shirya kasaitacciyar walima ta abinci da abin sha kala- kala masu tsada, domin bakin da za su zo. Mu tafi gidana ka debi dukkan kalar abincin da kake so ka je ku ci, kai da dan uwanka. Hakika Allah ya takaita maka wahala da ka hadu da ni." Asadu ya ce, "to, na gode. Amma mu hanzarta dan uwana na can na jira na a bayan gari." Tsoho ya kama hannun Asadu ya ja shi, suka yi ta tafiya tinkis tinkis har suka shiga wani kwararo matsattse, daga karshen kwararon kuma suka iso ga wani gida mai babbar kofa. Tsoho ya ja Asadu suka kutsa kai ciki, suka wuce zaure suka shiga tsakiyar gidan mai yalwa. Suka tarar da wasu tsofaffi guda arba'in, dukansu sun yi shiga irin ta wannan tsoho da ya shigo tare da Asadu. Asadu ya ga sun kunna wuta a tsakiyarsu, suna yi mata sujuda. Yayin da Asadu ya ga wadannan mutane, da abin da suke yi, sai tsigar jikinsa ta tashi. Ya ji tsohon nan da ya shigo da shi ya kada baki ya ce, "ya ku jama'ar wuta, hakika wannan babbar rana ce a gare mu." Daga nan sai ya daga murya da karfi ya yi kira, "ina kake ne, ya kai Galbanu?" Sai ga wani bakin bawa, dogo kakkarfa, ya fito, hancinsa kamar gajeren wando, ya daure fuska kamar wanda aka ce uwarsa da ubansa sun mutu. Tsoho ya yi masa wata alama da hannu. Nan take ya murkushe Asadu ya daure shi tamau da igiya. Tsoho ya ce, "tafi da shi dakin karkashin kasa, ka damka shi ga hannun kuyangata, gwanar azabtar da mutane. Ta ajiye mini shi kafin lokacin zuwa ibada a cikin teku, wurin dutsen wuta, domin jininsa za mu ba dutse a wannan shekara." Ya ci gaba da cewa, "ka gaya mata cewa, ta rika yi masa azaba dare da rana, ta ba shi abinci sau biyu kullum." Nan take bakin bawa Galbanu ya sungumi Asadu bisa kafadarsa, ya shiga wani daki da shi. Ya daga wata kofa ta karkashin kasa, ya tattaka matakala ashirin ya sauka kasan dakin. Ya ajiye Asadu, ya buga masa sarka hannuwa da kafafu, ya kira kuyanga ya damka mata shi, tare da sakon mai gidansu. Ya juya ya tafi. . Ita kuwa wannan kuyanga ba ta da tausayi ko kadan, ba ta san abin da ake kira da imani ba. Ran mutum da na kiyashi a wurinta duka daya ne. Bayan bakin bawa ya tafi, sai ta dauko bulala ta saukar wa Asadu da bugu ba ji ba gani har ya suma. Ta farfasa masa jiki ko’ina da bulala, sai jini ke zuba daga jikinsa. Ta dauko kosai guda da dan ruwa a cikin kasko ta ajiye kusa ga kansa, ta tafi ta bar shi nan sumamme. Da tsakar dare ya farka, ya ji jikinsa duk ya yi tsami saboda bugu. Ya tuna da dan uwansa, ya kuma tuna irin daular da yake ciki a da. Ya fashe da kuka, ya wake wadannan baitoci: Ku tsaya ga kufan gidaje, ku ba da labari a gare mu. Kada ku zata mu masu zama a gidajen ne. Kamar yadda kuka kasance. Zamani ya raba tarenmu. Hakika ba mu samun waraka daga cutar zuci Face mun sake gamuwa. Azabata ta jibinci jiki da zuciya Hakika yunwa ta kaura, bacin zuciya ya maye wurinta. Ina rokon Allah ya kusata gamuwarmu Ya ije mana sharrin makiya daga gare mu. Bayan ya gama waka sai ya ji kamshin kosai kusa ga hancinsa, ya sa hannu ya laluba kasa, kusa ga kansa, ya dauki dan kosan nan ya lakwame, ya hadiya 'yan ruwan da aka ajiye masa. Ya so ya dan runtsa ya yi barci, amma kwarkwata da kudin cizo suka ce da kai aka hada mu, sun sami sabon jini. Da gari ya waye kuyangar nan ta zo domin ta canza masa tufafi. Yayin da ta fara cire dan mayafin nan da ke jikin Asadu, wanda duk ya rine da jini, sai ya fara tasowa da fatar jikinsa, saboda dukan da ya sha da bulala. Asadu ya yi kara saboda zafin cire wannan mayafi, ya ce, "ya Ubangiji, idan wannan azaba da nake cikinta alheri ce gare ni, to, ka ba ni hakurin jure

Chapter 9 of 14