Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 14
shi ba, kuma ba zan bar wani mahaluki, mutum ko aljani, ya cutar da shi ba. Ta sunkuya ta sumbaci goshinsa, ta ja mayafi ta rufe masa fuska, gudun [ http://fb.com/ waziriaku ] kada wani aljanin ya zo ya ga fuskarsa, ta fita daga cikin dakin. Ta kada fukafukanta ta tashi sama cikin iska, ta nufi cikin duniya cike da tunanin Kamaruzzaman. Aljana Maimuna na cikin tashi sai ta ji kadawar fukafukai a bayanta, ta waiwaya da sauri sai [ http://fb.com/waziriaku ] ta ga wani Ifiritu ne mai suna Danhash, daya daga cikin bayin mahaifinta Sarkin Aljanu yake biye da ita. Ta juya da sauri ta tasar masa haikan, kamar shaho da kurciya, za ta halaka shi. To, dukkanin aljanu kuwa tsoronta suke ji, hatta mahaifinta Sarkin aljanu yana tsoronta. Domin tana da wasu kalamai da take jifar aljanu da su, wanda duk aljanin da ta [ http://fb.com/waziriaku ] jefa da wadannan kalamai zai kone nan take. Da Ifiritu ya ga Maimuna ta taso masa, sai ya ce, "Don girman Sulaimanu Dan Dawuda ki tsaya ki saurare ni, kada ki halaka ni." Yayin da ta ci ambaton Sulaimanu Dan Dawuda sai jikinta ya yi sanyi, ta ce masa, "Ya kai la'ananne! Hakika ka roke ni da babban suna, ba domin haka ba da na halaka ka. Maza fada mini daga inda ka fito, kuma me ya sa kake bi na a baya? [ http://fb.com/ waziriaku ] Danhash ya ce da Maimuna, "Ya shugabata, ni na fito ne daga kusan karshen duniya a cikin wasu tsibirai na kasar Sin. Na biyo ki ne domin in labarta miki abin da na gani na mamaki wanda ido bai taba gani ba, watakila idan kika ji za ki rubuta [ http:// fb.com/ waziriaku ] mini wata alama ga hannuna wadda za ta kare ni daga cutar dukkan aljanu 'yan uwana." Maimuna ta ce masa, "Fada mini abin da ka gani, makaryaci, la'ananne! Na rantse da hatimin da ke rubuce a jikin zoben Annabi Sulaimanu Dan Dawuda (Amincin Allah Ya tabbata a gare su), idan ka fada mini karya zan fige gashin jikinka da [ http://fb.com/waziriaku ] hannuna, in kware fatar jikinka, sa'annan in kakkarya kasusuwanka in watsar a cikin teku." Muryarsa na rawa, Danhash dan Shamharisha ya amsa, "Na'am, na yarda ya shugabata." [ http:// fb.com/waziriaku ] Aljani Danhash dan Sahamharisha ya ce ya amince da sharadin aljana Maimuna 'yar Sarkin aljanu Addimiryat. Ya ci gaba da cewa, "Ya shugabata, a cikin wannan dare na ziyarci wasu tsibirai na kasar Sin wadanda suke karkashin mulkin babban Sarki Gayur, mai mulkin tsibirai da [ http://fb.com/ waziriaku ] tekuna mai fadoji guda bakwai. A can na gano wata 'yarsa wadda duk fadin duniyar nan, a cikin wannan zamani, babu wani dan Adam da ya kai ta kyau. Ba zan iya kwatanta miki kyawunta ba, ya shugabata, saboda harshena baya da kalmomin da zai iya amfani da su wajen siffanta miki kyawun [ http://fb.com/waziriaku ] wannan 'yar Sarki. Amma dan karamin misalin da zan fada miki shi ne, gashin kanta dogo ne har bisa gadon bayanta, ga shi kuma baki kirin kamar duhun daren bakin cikin rabuwar masoya, fuskarta kuwa fara ce tas cike da annuri kamar safiyar farin cikin haduwar masoya. [ http://fb.com/ waziriaku ] Tana da hanci dogo siriri, karshensa kamar tsinin takobi. Tana da jajayen kumatu masu kama da jan fure ko jar zuma. Lebbanta kuwa 'yan sirara suna [ http://fb.com/ waziriaku ] walkiya suna sheki kamar narkakkiyar zaiba. Yawun bakinta kuwa ya fi tsohuwar zuma zaki. Tana da zazzakar murya da [ http://fb.com/waziriaku ] tattausan lafazi mai rikitar da mai saurarenta. Kirjinta kuwa abin jan hankali ne ga duk namijin da ya gan shi. Tsarki ya tabbata ga Mahaliccin wannan yarinya da ya tsara mata kome kamar ita ta yi wa kanta. [ http://fb.com/waziriaku ] Ta kasance mai faffadan kirji wanda yake cike da nonuwa biyu mulmulallu kamar kwallon danyen zinariya, suna haske kamar wata daren goma sha hudu. Cikinta shafaffe ne, [ http://fb.com/waziriaku ] kamar ba ta cin kome. Tana da tsukakken kwankwaso da manya-manyan mazaunai kamar tuddan yashi, wadanda lallausan cinyoyin kafarta suke dauke da su. Kafafunta kuwa mike suke santal kamar an kafa mashi ga kasa. Har ina mamakin yadda [ http:// fb.com/ waziriaku ] wadannan madaidaitan kafafun nata suke iya daukar abin da ke samansu. Ya shugabata, wannan dan karamin misali ne kawai na fada miki na daga siffofin wannan 'yar Sarki." [ http://fb.com/waziriaku ] *** Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwa yanzu haka. whtasapp only pls. 08032767547(5) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN Aljani Danhash dan Sahamharisha ya ce ya amince da [ http://fb.com/ waziriaku ]sharadin aljana Maimuna 'yar Sarkin aljanu Addimiryat. Ya ci gaba da cewa, "Ya shugabata, a cikin wannan dare na ziyarci wasu tsibirai na kasar Sin wadanda suke karkashin mulkin babban Sarki Gayur, mai mulkin tsibirai da tekuna mai fadoji guda bakwai. [ http://fb.com/waziriaku ] A can na gano wata 'yarsa wadda duk fadin duniyar nan, a cikin wannan zamani, babu wani dan Adam da ya kai ta kyau. Ba zan iya kwatanta miki kyawunta ba, ya shugabata, saboda harshena baya da kalmomin da zai iya amfani da su wajen siffanta miki kyawun [ http://fb.com/waziriaku ] wannan 'yar Sarki. Amma dan karamin misalin da zan fada miki shi ne, gashin kanta dogo ne har bisa gadon bayanta, ga shi kuma baki kirin kamar duhun daren bakin cikin rabuwar masoya, fuskarta kuwa fara ce tas cike da annuri kamar safiyar farin cikin haduwar masoya. [ http://fb.com/waziriaku ] Tana da hanci dogo siriri, karshensa kamar tsinin takobi. Tana da jajayen kumatu masu kama da jan fure ko jar giya. Lebbanta kuwa 'yan sirara suna walkiya suna sheki kamar narkakkiyar zaiba. Yawun bakinta kuwa ya fi tsohuwar zuma zaki. [ http://fb.com/ waziriaku ] Tana da zazzakar murya da tattausan lafazi mai rikitar da mai saurarenta. Kirjinta kuwa abin jan hankali ne ga duk namijin da ya gan shi. Tsarki ya tabbata ga Mahaliccin wannan yarinya da ya tsara mata kome kamar ita ta yi wa kanta. [ http://fb.com/waziriaku ] Ta kasance mai faffadan kirji wanda yake cike da nonuwa biyu mulmulallu kamar kwallon danyen zinariya, wata yakan aro haskensa daga hasken wadannan nonuwa nata. Cikinta shafaffe ne, kamar ba ta cin kome. Tana da tsukakken kwankwaso da manya-manyan [ http://fb.com/waziriaku ] mazaunai kamar tuddan yashi, wadanda lallausan cinyoyin kafarta suke dauke da su. Kafafunta kuwa mike suke santal kamar an kafa mashi ga kasa. Har ina mamakin yadda wadannan madaidaitan kafafun nata suke iya daukar [ http://fb.com/waziriaku ] abin da ke saman su. Ya shugabata, wannan dan karamin misali ne kawai na fada miki na daga siffofin wannan 'yar Sarki." Maimuna ta yi kasake tana sauraren labarin Danhash [ http://fb.com/waziriaku ]. Shi kuwa ya ci gaba da cewa, "Mahaifin wannan yarinya Sarki ne mai tsananin karfi da jarunta, ba ya tsoron mutuwa ko kadan. Ya tara sadaukai da askarawan yaki, ya ci kasashe da dama a wurin yaki. Ya rusa biranen da ba su bi shi ba, ya mayar da wasu turbaya. Shi ke mulki da dukkan tsibirai [ http://fb.com/waziriaku ] da tekuna da tuddan kasar Sin, shi ne mai fadoji guda bakwai. Sunan wannan Sarki shi ne Gayur, sunan wannan 'ya tasa kuwa Badura. Saboda tsananin son da yake wa 'yar tasa, ya gina mata fadoji guda bakwai. An gina ta farko [ http://fb.com/waziriaku ] da jan karfe, ta biyu an gina ta da farin karfe, ta uku an gina ta da duwatsu masu daraja na kasar Sin. Fada ta hudu kuwa an gina ta ne da karfen Siniyya, ta biyar an gina ta da lu'ulu'u, ta shida da azurfa. Fada ta bakwai kuma ta karshe an gina ta da zinariya. Kowace fada an cika ta da kayan kwalliya masu tsada da daraja, tun daga shimfidu da gadaje abubuwan zama, kayan cin abinci da na shan abin sha, duk masu tsadar gaske ne. Ya kasance 'yar tana zama [ http://fb.com/ waziriaku ] a cikin kowace fada tsawon shekara guda, daga nan sai ta koma wata. Lokacin da wannan 'yar Sarki ta fara girma, labarin kyawunta ya watsu ko'ina. Nan take manya-manyan Sarakuna, ma su ji da kansu, suka fara aiko wa Sarki Gayur da bukatar [ http://fb.com/waziriaku ] neman auren ta. Yayin da uban ya tuntube ta da maganar aure, sai ta mayar masa da jawabi da cewa, "Ya mahaifina, ni 'yar Sarki ce mai jiran sarauta, wacce za ta mulki mazaje nan gaba. Ta yaya zan yadda namiji daya ya mulke ni? Ni ba zan taba yin aure ba har abada." Daga nan mahaifinta ya kyale ta. Da aka [ http://fb.com/waziriaku ] shekara daya sai masu neman aurenta suka karu, suka yi ta turo wa Sarki da dukiya mai yawa a matsayin gaisuwar neman aurenta. Da Sarki ya ga haka sai ya kara tuntubar ta da maganar aure, ita kuwa ta sake fada masa yadda ta fada masa da farko. [ http://fb.com/waziriaku ] A takaice dai, ya shugabata, Sarki Gayur bai daina tuntubar 'yarsa Badura da maganar aure ba har wata rana ta yi tunzura ta ce da shi, "Ya mahaifina, shin sau nawa zan fada maka cewa ba zan yarda namiji ya yi mulki a kai na ba? Don haka babu ni babu auren namiji har duniya ta nade. Kuma na rantse da Allah idan ka kara tuntuba ta da wannan magana, to, zan rufe [ http://fb.com/waziriaku ] kaina a cikin daki tare da takobi mai tsini da kaifi. Zan kafe takobin a kasa, tsininsa yana kallon sama, in kwanta bisa tsinin takobin daidai tsakiyar kirjina har sai tsininsa ya fito ta gadon bayana. Idan na mutu sai ka aura ma duk wanda kake so [ http://fb.com/ waziriaku ] gawata." Da mahaifinta ya ji haka sai ransa ya baci, ya ji tsoron kada 'yarsa ta aikata abin da ta fada, ga shi kuma yana jin kunyar wadansu Sarakuna da suka aiko masa da gaisuwar neman aurenta. Don haka sai ya ce da ita, "To, idan dai wannan ne ra'ayinki, na amince. Amma da sharadin ba za ki kara fita waje ba balle har wani namiji ya [ http://fb.com/waziriaku ] gan ki zuciyarsa ta so ki." Tun daga wannan rana Sarki Gayur ya sa aka kulle gimbiya Badura a cikin daya daga fadojin nan nata guda bakwai, ya ajiye wasu mata goma masu yi mata hidima a cikin fadar. Ya rubuta takardu ga Sarakunan da ke neman aurenta. A cikin takardun ya shaida musu cewa ta sami tabin hankali, tana nan ana nema mata [ http:// fb.com/waziriaku ] magani, su saurara tukuna har a ga abin da Allah zai yi. Yanzu shekara guda ke nan ana tsare da ita, ba ta fita ko'ina. Ni kuwa tun daga ranar da aka tsare ta, kullum sai na je inda take yayin da take barci, in kashe kwarkwatar idanuna a kan kyakkyawar fuskarta. [ http://fb.com/ waziriaku ] Idan na ga gari ya kusa wayewa, sai in sumbace ta a kan goshinta, in fito in koma fadar Sarkin aljanu. Ba ni da niyyar cutar da ita, kuma ba zan bar kowane aljani ya cuce ta ba, muddin na fi karfinsa, shi ya sa ban taba fada wa wani wannan [ http:// fb.com/waziriaku ] labari ba sai ke, ya shugabata. Yanzu ma da na hadu da ke can wajenta zan tafi, ko za ki tafi tare da ni domin ki gasgata abin da na fada miki. Idan kuma ki ka tabbata zancena gaskiya ne, to ki rubuta mini wani abu a hannuna wanda zai kare ni daga sauran aljanun da suka fi ni karfi [ http://fb.com/waziriaku ]." Yayin da Danhash ya gama labarinsa sai ya sunkuyar da kansa a kasa, yana mai matukar ladabi ga Maimuna. Ita kuwa da ta ji ya kai karshe da labarinsa, sai ta fashe da dariya, ta tofa masa [ http://fb.com/waziriaku ] yawu a fuska ta ce, "Allah waddanka ya kai la'ananne! Ni na zata za ka fada mani wani labari mai ban mamaki fiye da wannan. To, idan maganar kyau kake yi, saurayin da na fito daga wurinsa yanzu, duk duniyar nan babu wanda ya kama ko da dan yatsan kafarsa ne, a fagen kyau [ http://fb.com/ waziriaku ]. Watakila ma waccan 'yar Sarkin da kake ta rurutawa idan ta gan shi sai ta rude, ta durkusa a gabansa tana sumbatar yatsun kafarsa. Kai kuma idan ka gan shi, ban san irin kidimewar da za ka yi ba, domin wannan saurayi shi ne sarkin sarakunan kyau na wannan lokaci." Cikin kaduwa da mamaki [ http://fb.com/ waziriaku ] Danhasha ya tambaya, "Wane ne wannan saurayi? Ina yake?" Maimuna ta ce, "Kamar yadda na sami labari, bayan na fito daga dakinsa. Kaddararsu iri daya ce da ta 'yar Sarkin da ka ba ni labari yanzu. Shi ma wannan saurayi dan Sarki ne, ubansa ya yi, ya yi da shi a kan ya yarda a yi masa aure amma ya ki. Uban ya yi fushi da shi ya sa aka rufe shi cikin gidan [ http://fb.com/ waziriaku ] da nake zaune. Yau na fito zan tafi yawon shan iska sai na ga hasken fitila yana fitowa daga dakin da yake tsare, na shiga na gan shi. Da fari ban yi zaton mutum ne ba, na aza wani mala'ika ne saboda tsananin kyawunsa. Hakika wannan saurayi babu tamkarsa ga kyau a cikin wannan zamani. Mu sauka nan kasa in nuna maka saurayin da na gani, tunda ba mu yi nisa da [ http://fb.com/waziriaku ] gidan ba, ya kai la'ananne, domin ka tabbatar da cewa ka yi kuskuren saurin yanke hukunci a kan waccan 'yar Sarkin. Daga nan kuma mu tafi birnin Sin in ga 'yar Sarkin da kake ta kururutawa." Danhash ya rauda kansa cikin ladabi ya ce, "Na ji, na amince." [ http://fb.com/ waziri. Za mu ci gaba (6) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN Yayin da Danhash ya gama labarinsa sai ya sunkuyar da kansa a kasa, yana mai matukar ladabi [ http://fb.com/waziriaku ]ga Maimuna. Ita kuwa da ta ji ya kai karshe da labarinsa, sai ta fashe da dariya, ta tofa masa yawu a fuska ta ce, "Allah waddanka ya kai la'ananne! Ni na zata za ka fada mani wani labari mai ban mamaki fiye da wannan. To, idan maganar kyau kake yi, saurayin da na fito daga wurinsa yanzu, duk duniyar nan babu wanda ya kama ko da dan [ http://fb.com/waziriaku ] yatsan kafarsa ne, a fagen kyau. Watakila ma waccan 'yar Sarkin da kake ta rurutawa idan ta gan shi sai ta rude, ta durkusa a gabansa tana sumbatar yatsun kafarsa. Kai kuma idan ka gan shi, ban san irin kidimewar da za ka yi ba, domin wannan saurayi shi ne sarkin sarakunan kyau na wannan lokaci." Cikin kaduwa da mamaki Danhasha ya tambaya, "Wane ne wannan saurayi? Ina yake?" Maimuna ta ce, "Kamar yadda na sami labari, bayan na fito daga dakinsa. Kaddararsu [ http://fb.com/ waziriaku ] iri daya ce da ta 'yar Sarkin da ka ba ni labari yanzu. Shi ma wannan saurayi dan Sarki ne, ubansa ya yi, ya yi da shi a kan ya yarda a yi masa aure amma ya ki. Uban ya yi fushi da shi ya sa aka rufe shi cikin gidan da nake zaune. Yau na fito zan tafi yawon shan iska sai na ga hasken fitila [ http://fb.com/waziriaku ] yana fitowa daga dakin da yake tsare, na shiga na gan shi. Da fari ban yi zaton mutum ne ba, na aza wani mala'ika ne saboda tsananin kyawunsa. Hakika wannan saurayi babu tamkarsa ga kyau a cikin wannan zamani. Mu sauka nan kasa in nuna maka saurayin da na gani, tunda ba mu yi nisa da gidan ba, ya kai la'ananne, domin ka tabbatar da cewa ka yi kuskuren saurin yanke hukunci a kan waccan 'yar Sarkin. Daga nan kuma mu tafi birnin Sin in ga 'yar [ http:// fb.com/waziriaku ] Sarkin da kake ta kururutawa." Danhash ya rauda kansa cikin ladabi ya ce, "Na ji, na amince." Suka sauka cikin gidan gona, Maimuna ta ja Danhash zuwa dakin da Kamaruzzaman yake kwance. Ta yaye mayafin da ya rufe masa fuska. Fuskarsa na bayyana [ http://fb.com/waziriaku ] sai Danhash ya ga kamar rana ce ta fito don haske. Maimuna ta kura wa fuskar Kamaruzzaman ido na wani dan lokaci, sa'annan ta dubi Danhash ta ce, "Duba nan ya kai la'ananne!" Ta nuna masa fuskar [ http://fb.com/ waziriaku ] Kamaruzzaman da hannunta. "Waccan 'yar Sarkin da kake kodawa ta kai kyawun wannan?" Danhash ya kafa wa Kamaruzzaman idanu, ya girgiza kansa ya ce, "Ya shugabata, hakika kina da gaskiya, amma na rantse da Allah 'yar Sarkin da na gani ta shafe wannan fat, da kyau. Watakila don ke mace ce, shi ya sa kike ganin kyawunsa da yawa haka, amma ki gafarce ni. [ http://fb.com/waziriaku ]" Yayin da Maimuna ta ji kalamansa, sai fuskarta ta yi duhu don fushi, ta dangware shi da fiffikenta bisa ga kansa. Ta ce masa, "Yi gaggawa ka dako waccan yarinyar ka kawo ta nan. Mu kwantar da [ http://fb.com/waziriaku ] ita kusa da wannan saurayi, mu dube su da kyau mu ga wanda ya fi wani kyau daga cikinsu. Mu tafi in raka ka don kada wani aljani ya tsayar da kai bisa hanya." Suka fita daga [ http://fb.com/ waziriaku ] cikin dakin, suka kada fukafukansu suka tashi sama da hanzari kamar iska. Jim kadan sai ga su sun dawo, Danhash yana dauke da Badura 'yar Sarkin Sin. Tana sanye da wata rigar barci wadda aka yi kawa da [ http://fb.com/ waziriaku ] zinariya da azurfa, daga kowane gefe na rigar an rubuta wadannan baitoci: [ http:// fb.com/waziriaku ] "Abubuwa uku ne suka tsoratar da ita daga barin ziyartar mu. Tsoron mahassada wadanda suke raunana ba ya isowa gare mu. Hasken goshi na daga adon tufafi ba mu tara shi ba. Hasken goshin baiwa ce ta daga alherinsa." Suka shiga cikin dakin suka kwantar da ita kusa ga Kamaruzzaman. Suka matsa kusa suka dubi fuskokinsu [ http://fb.com/waziriaku ]. Kai! Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin Sarki, mai yin halitta yadda ya so. [ http://fb.com/waziriaku ] Domin kuwa wadannan yara sai suka kasance kamarsu daya, sai ka ce an tsaga kara. Babu wanda za ka ce ga wanda ya fi dan uwansa kyau daga cikinsu. Sun kasance kamar yadda El Mubin ya waka a cikin wadannan baitoci: "Ya ke zuciya ban dawwamar da ke ba a cikin son daya! Don me kike tsalle-tsalle tsakanin son wancan da wancan. Ki zabi daya wanda ya fi kyau." [ http://fb.com/waziriaku ] Kamar kuma yadda wani mawakin ke cewa: "Na ga biyu kwance a kasa. Zuciyata ta kasa zabar daya daga cikinsu." Danhash da Maimuna suka ci gaba da kallonsu, suna nazarin su [ http://fb.com/waziriaku ]. Daga nan sai Danhash ya ce, "Na rantse da Allah, ya shugabata, wannan saurayi kyakkyawa ne, amma yarinyar ta fi shi kyau." Maimuna ta fusata, ta daka masa tsawa ta ce, "Karya kake yi, ya la'annane, makahon banza wanda bai san kyau ba. Kara [ http://fb.com/waziriaku ] dubansa da kyau, da idanunka guda biyu ka gani." Ta sunkuya ta sumbaci Kamaruzzaman a kan goshinsa har sau uku, ta waka wadannan baitoci: "Yaya haka? Wa ya isa ya kushe ka a gabana. Babu wani abu da na fi ganin kyawunsa a cikin raina, bayan kai. Dare da rana idanuna sun kasance marasa barci. Ina tozalta kwayar idanuna ne da sonka kowace rana. Ni mai bege ce, bege ya buge ni har na zama zabiya domin kai." [ http://fb.com/waziriaku ] Yayin da Danhash ya ji wannan waka ta Maimuna sai ya yi murmushi, ya yi mamaki gayar mamaki. Ya ce, "Wallahi kin shagala da begen wannan saurayi har babu mai iya kushe maki shi [ http:// fb.com/waziriaku ]. Amma ki sa idon nutsuwa ki dubi wannan yarinya ki ga irin kyawun da Allah ya yi ma ta, wane wannan saurayi." Ya sunkuya ya sumbaci goshin Badura [ http:// fb.com/waziriaku ] sa'annan ya waka wadannan baitoci, duk da ba ya da fasahar tsara waka: "Idan na nuna kauna ga abar begena, sai su tunzura da fushi. Yana yanke hukunci idanunsu rufe. Ku hakura da hukuncin Allah domin tawa ta zarce taku. Saboda bege idona ke zubar da hawaye. Zan iya daukar dukkan hukunci a kan wadda nake bege." Da Maimuna ta ji wakarsa, sai ta yi dariya, ta dube shi ta ce, "Hakika [ http://fb.com/ waziriaku ] wannan 'yar Sarki tana shere ka. To, amma yanzu a yi maganar gaskiya, tsakanin ita da saurayin wa ya fi dan uwansa kyau. Ban da son rai fa!" Danhash ya ce, "Ya shugabata, ai babu mai raina zakin madi, amma idan aka lasa zuma dole a raina shi. [ http://fb.com/waziriaku ] Ko shakka ba na yi, 'yar Sarkin ita ce ta fi shi kyau." "Makaryacin banza! La'ananne! Dan Sarkin shi ne ya fi ta kyau!" Maimuna ta daka masa tsawa. Suka ci gaba da gardama, har Maimuna ta [ http://fb.com/waziriaku ] kai matuka ga fushi ta taso masa haikan za ta halaka. Ya fadi gabanta yana ahi, yana ba ta hakuri. *** Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda yanzu haka na kasuwa... ZANCI GABA INSHA ALLAH(8) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN . Aljana Maimuna ta rikida kudin cizo, ta shiga [ http://fb.com/waziriaku ] karkashin rigar Badura, ta dubi daidai saman cibiyarta ta zabga mata cizo. Nan take ta yi firgigi ta farka, ta tura hannunta cikin rigarta tana susar wurin da kwaron ya cije ta tana fadin, "Wash! Wannan wane irin kwaro ne mai zafin cizo?" Tana cikin soshe-soshe sai ta ji wani [ http://fb.com/ waziriaku ] nannauyan numfashin mutum kusa gare ta. Ta yi zumbur ta tashi zaune, ta dubi wanda ke kusa gare ta cike da mamakin yadda aka yi har wani ya kwanta kusa gare ta. Ta dubi fuskar Kamaruzzaman ta cikin hasken fitilar da ya haske dakin. Ta ja gwaron numfashi, tsarki ya tabbata ga Allah [ http://fb.com/ waziriaku ] madaukakin Sarki wanda ya halicci wannan kyakkyawan saurayi. Ta kura masa ido tana kallon girar saman idonsa mai kunyatar da ta barewa don kyau. Ta ga wani dan madaidaicin baki sai kace zoben annabi Sulaimanu. Da wasu lebba suna sheki [ http://fb.com/waziriaku ] kamar madubi. Ta ga kumatunsa jajaye masu kalar furen wardi. [ http://fb.com/waziriaku ] Yayin da Badura ta ga Kamaruzzaman sai yawun bakinta suka kafe, nan take wutar begensa ta ruru cikin zuciyarta. Ta ce, "A'aha! Yaya aka yi wannan bakon saurayi yake kwance kusa gare ni bisa gado daya? Kai, amma na rantse da Allah ban taba ganin saurayi mai kyau kamar wannan ba. Da na san cewa yana cikin wadanda suka nemi aurena da tuni na amince [ http://fb.com/waziriaku ] da shi a matsayin mijina. Daga nan sai ta fara girgiza shi da hannuwanta tana cewa, "Ya masoyina, abin begena, tashi in shayar da kai madarar soyayya." Maimuna ta danne kansa da fiffikenta daya, ta sakar masa barci mai [ http://fb.com/waziriaku ] nauyi. Saboda haka duk da girgizar da Badura take yi masa bai ko motsa ba balle har ya farka daga barci. [ http://fb.com/waziriaku ] Da Badura ta ga bai da alamar tashi, sai ta kara girgiza shi da karfi tana cewa, "Ya masoyina, na damka ragamar rayuwata a gare ka, tashi in gwada maka kakkyawan kirjina da maza da yawa suke mutuwar son gani. Tashi in nuna maka [ http://fb.com/waziriaku ] cibiyata mai tsadar gani ga kowane mahaluki. Ka tashi ka sarrafa dukkan gabobin da kake so ga jikina, na mallaka maka kaina gaba daya." Amma ina, Kamaruzzaman bai san wainar da take toya ba, ya dulmiya cikin barci. [ http://fb.com/ waziriaku ] Badura ta ci gaba da cewa, "Haba masoyina, don me za ka kyale ni ina ta magana ni kadai? Idan kana takama da kyau ne, to, ai ni ma an ce kyakkyawa ce, watakila ma na [ http://fb.com/ waziriaku ] fi ka kyau. Ko kuwa dai mahaifina ne ya hana ka yi mini magana ko ka taba ni?" Kamaruzzaman dai bai ko motsa ba balle ya kalle ta, sai barci kawai yake yi. [ http://fb.com/ waziriaku ] Tsananin so da begen Kamaruzzaman suka karu a cikin zuciyar Badura. Ta dimauce, hankalinta ya gushe, ta ci gaba da cewa, "Yi mani magana, ya shugabana. Yi mani magana, ya abokina. Ka amsa mani ya masoyina. Ka fada [ http:// fb.com/waziriaku ] mani sunanka abin begena. Don me kake da girman kai haka?" Kamaruzzaman dai bai motsa ba, domin kuwa aljana ta danne masa kai da fiffikenta. [ http:// fb.com/waziriaku ] Badura ta kamo hannun Kamaruzzaman sai ta ga zobenta a dan yatsansa. Ta yi kara, kara mai tsanani cike da farin ciki. Ta ce, "Oho, na rantse [ http://fb.com/waziriaku ] da Allah kai ma kana sona, kamar yadda nake sonka, to, don me za ka juya mini baya, ka ki yi mini magana? Watau ka aikata abin da ranka yake so gare ni lokacin da nake barci, daga nan kuma ka cire zobena ka sa a dan yatsanka ko? To, na bar [ http://fb.com/ waziriaku ] maka zoben, amma zan cire naka maimakon nawa, kuma sai na rama abin da ka yi mani." Ta sa hannu ta cire wani zobensa daga yatsun hannunsa, ta saka shi ga dan yatsan hannunta. Daga nan sai ta daga 'yar rigarsa [ http:// fb.com/waziriaku ] ta barci, kirjinsa da cikinsa suka bayyana. Ta sunkuya ta sumbace shi ga fuska, ta tsotsi bakinsa, ta sa hannunta tana shafa kirjinsa da cikinsa. Fatar jikin Kamaruzzaman mai santsi ce kamar jikin kifi, sai ta hadu da tattausan hannun Badura a lokacin da take shafa masa kirji. Ba ta ankara ba sai ta ji santsin fatar jikinsa ya kwashi hannunta zuwa ga kasan cibiyarsa, har ya shiga cikin wandonsa, ta taba masa mazakuta. [ http://fb.com/waziriaku ] Ta yi sauri ta janye hannunta cikin tsananin jin kunya. Amma wanna abu sai ya tsokano mata da sha'awa mai karfi, kamar yadda aka fada, sha'awar mata ita ce ma fi karfi daga sha'awar maza [ http://fb.com/waziriaku ]. Ta kware rigarta, nonuwanta suka fito fili, ta kwanta kusa ga Kamaruzzaman ta jawo kansa ta aza bisa kirjinta, ta sa hannuwanta biyu ta rungume shi. A haka barci ya kwashe ta, tana rungume da Kamaruzzaman. [ http://fb.com/waziriaku ] Aljana Maimuna ta dubi Danhash, wanda ya sunkuyar da kansa kasa cikin jin kunyar ganin yadda Badura ta mika kanta gaba daya ga Kamaruzzaman, ta ce masa cikin fara'a, "Ka gani, [ http://fb.com/waziriaku ] ya kai la'ananne! Dubi yadda abin begena ya kawar da kansa daga abar begenka, bai ko taba jikinta ba. Amma dubi yadda abar begen taka ta rude, ta rikice, ta sadaukar da kanta gaba daya ga abin begena. Wannan shi ya tabbatar mana da cewa abin begena ya shafe abar begenka fat da kyau. Amma babu kome, na yafe maka a kan jayayya da ka yi da ni." [ http://fb.com/waziriaku ] Daga nan ta kama hannunsa ta rubuta masa abin da ya bukata daga gare ta. Ta juya wurin [ http://fb.com/waziriaku ] Kashkash ta ce da shi ya taimaka wa Danhash su dauki Badura su mayar da ita dakinta kafin gari ya karasa wayewa. "Na ji, na yarda." Kashkash ya ce cikin girmamawa. Suka tafi shi da Danhash suka warware hannuwanta daga jikin Kamaruzzaman, suka dauke ta suka tashi sama da ita. Cikin kyibtawar ido suka ajiye ta bisa shimfidarta a cikin dakinta da ke kasar Sin. [ http://fb.com/ waziriaku ] Maimuna kuwa ta ci gaba da tsayuwa a gaban Kamaruzzaman tana kallon kyakkyawar fuskarsa. Da ta ga gari ya kusa wayewa sai ta sunkuya ta sumbaci goshinsa, ta fita ta koma cikin rijiyar da take zama. [ http://fb.com/ waziriaku ] Yayin da gari ya waye, Kamaruzzaman ya farka daga barci. Ya juya dama, ya

Chapter 2 of 14