Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 14
babu zanin daurawa. To, ni ba namiji ba balle in kawar da budurcin wannan kyakkyawar yarinya. Kuma idan na bar ta haka har gari ya waye babu shakka Sarki zai sa a kore ni daga kasarsa, ga shi kuma ina ji a cikin raina tabbas a wannan gari zan hadu da mijina Kamaruzzaman. Babu abin da ya fi sai in fada wa wannan yarinya gaskiyar labarina, tun da dai na lura da ita tana da hankali kuma tana da kirki, ba za ta tona mini asiri ba." Badura ta dago kanta, bayan ta gama zancen zuci, ta dubi Hayatunnufusi ta ce, "Ki rantse idan na fada miki labarina, ba za ki tona mini asiri ba." Hayatunnufusi ta kwashi rantsuwa. Daga nan sai Badura ta warware mata kome na game da labarinta da Kamaruzzaman. Sa'annan ta ce, "Na gama ki da Allah ki yi shiru da bakinki, kada kowa ya ji wannan labari, har Allah ya hada ni da mijina, daga nan sai mu jira abin da Allah zai kaddara." Hayatunnufusi ta cika da mamaki da jin wannan labari, matukar mamaki. Ta tausaya wa Badura da Kamaruzzaman bisa wahalhalun da suka sha a kan soyayya har hawayenta suka yi ta zuba kamar ruwa saboda tausayi. Ta yi musu fatar sake saduwa da juna, ta ce, "Kar ki ji tsoron kome, 'yar uwata, ina rokon Allah ya hada ki da mijinki." Sai ta rera wannan waka: "Asiri a gare ni ya tabbata cikin daki, wanda yake kullalle kuma mabudinsa ya bace. Amma daki ko yana kulle, asiri ba ya boyuwa face ga ma'abucin aminci. Asiri abin boyewa ne a wurin zababbun mutane." Bayan ta gama waka, sai ta ce da Badura, "Ki sani, ya 'yar uwata, Allah na rufa asirin wanda ya rufawa dan uwansa asiri. Ni ba zan taba tona miki asiri ba." Daga nan suka rungume juna, kowa na zubar da hawaye. Suka kawanta a shimfida daya, barci ya kwashe su. Can kusan assalatu suka farka, Hayatunnufusi ta kamo wata tattabara, a cikin tattabarunta da take kiwo, ta yanka ta. Ta je bisa shimfidarsu ta diddiga jinin tattabarar, ta kuma cire wandonta ta diga masa jinin, ta sargafe shi wurin da duk wanda ya shigo dakin zai gan shi. Da gari ya iyar da wayewa tangaram, Badura ta shirya ta fita fada kamar kullum. Bayan fitar ta sai ga Sarki da matarsa sun shiga wurin Hayatunnufusi, suna shiga sai mahaifiyarta ta yi tozali da wandon 'yarta da jini a jikinsa, ta duba shimfida, a nan ma ta ga digon jini, ta cika da farin ciki ganin cewa 'yarta ta kai bantenta. Sarki ya tambayi 'yarsa yadda ta kwana da mijinta, ta fada masa cewa a wannan dare dai sun san junansu a matsayin mata da miji. Sarki ya yi matukar farin ciki mara misaltuwa. Tun daga wannan rana Badura ta ci gaba da mulkinta tare da Hayatunnufusi a birnin Labunus, tana sa kuma ana nema mata labarin Kamaruzzaman. Wannan shi ne al'amarinta. Al'amarin Sarki Shahruzzaman kuwa, bayan kwana daya da tafiyar Kamaruzzaman tare da Marzuwan zuwa ga farauta, sai ya yi ta zuba ido yana jiran dawowarsu. Da rana ta farko ta shige ba su dawo ba aka shiga rana ta biyu, sai hankalinsa ya tashi, ya shiga cikin damuwa mara misaltuwa, a wannan rana ya kasa ci ya kasa sha, babu abin da yake yi sai tunanin dansa Kamaruzzaman tare da zubar da hawaye. Ya hakura dai har zuwa kwana na uku, da ya ga ba su dawo ba, nan take ya yi umurni da haduwar askarawan yakinsa. Nan da nan askarawa suka hadu, suka cika kofar fada, Sarki ya hau da kansa suka fita bayan gari, suka bi sawun Kamaruzzaman da Marzuwan. Da suka fita daga cikin birni, sai Sarki ya raba askarawan nan kashi shida ya tura kowane rukuni jiharsa daban, ya ce musu su hadu nan gobe kamar yanzu. Dukkansu suka bazama cikin daji suna neman Kamaruzzaman. Allah da ikonsa sai rukunin da Sarki yake ciki, suka tarar da wurin da Kamaruzzaman da Marzuwan suka yanka rakumi suka yayyaga tufafinsu a cikin jinin rakumin. Nan take Sarki ya shaida rigar Kamaruzzaman, ya sauka daga kan dokinsa, ya ga nama faca-faca ko'ina, wanda ba za iya gane ko na menene ba. Sarki na ganin rigar nan sai ya kwala kara mai tsanani, ya fadi ya suma. Askarawa suka sauka daga kan dawakansu, suka shiga tarairayar Sarki har ya farfado. Da Sarki ya farfado sai ya shiga rusa kuka, yana marin fuskarsa, yana tsige gashin gemunsa. Askarawa ma suka shiga kuka suna marin fuskokinsu, suna zuba kasa bisa kawunansu. Sarki ya hakikance da Kamaruzzaman ya mutu, yadda ya ga rigarsa cikin jini ga kuma namansu, ya tabbata cewa ko dai wata dabbar daji ce ta yi faca-faca da su, ko kuma 'yan fashi ne suka kashe su. Bayan Sarki da askarawansa sun gama alhinin wannan abu da suka gani, sai suka hau dawakansu suka koma da baya, suka hadu da sauran rukunonin askarawa, suka nufi cikin birni. ............ Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin zai fito nan ba da dadewa ba.(22) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN Bayan Sarki Shahruzzaman da askarawansa sun gama alhinin wannan abu http://fb.com/ waziriaku da suka gani, sai suka hau dawakansu suka koma da baya, suka hadu da sauran rukunonin askarawa, suka nufi cikin birni. Yayin da suka isa gida, Sarki ya sa aka yi yekuwa aka ba da sanarwar mutuwar Kamaruzzaman, aka umurci kowa da ke cikin kasar Kalidan da sanya bakaken tufafi na kwana uku domin nuna bakin ciki bisa wannan http://fb.com/waziriaku rashi da Sarki da jama'arsa suka yi. Sarki ya sa aka gina masa kubba a wani gida nasa, aka siffanta wani abu mai kamar kabari a cikinta, ya kira wannan wuri kubbar bakin ciki. Ya kasance kodayaushe Sarki na wurin wannan kabari yana kuka yana bakin ciki tare da rera wakoki, amma yakan fita fada ranar Alhamis da Litinin. Wannan shi ne al'amarinsa. http://fb.com/waziriaku Al'amarin Kamaruzzaman kuwa yana can tare da mai lambu yana taimakonsa ga aikin lambunsa, kullum idan ya tuna da abin da ya faru gare shi sai ya yi ta kuka yana waka. Haka ya kasance a wurin mai lambu har tsawon wata uku. Wata http://fb.com/waziriaku rana yana daga cikin lambu, yana shirin fara ban ruwa, sai ya hangi mutanen birnin nan suna ta taruwa wani wuri, kowane daya daga cikinsu ya ci ado ya kure adaka, kamar dai ana wani gagarumin buki. Daga nan sai ga mai lambu ya zo wurinsa, shi ma ya sa kayansa ma su kyau, ya yi http://fb.com/ waziriaku kwalliya. Ya ce da Kamaruzzaman, "Ya dana, yau ranar hutu ce a wannan birni, domin kuwa yau ne ranar bukin ibadarsu. Rana ce da 'yan uwa da abokan arziki ke kai wa juna ziyara, kuma yau ne ake sa ran jirgi zai zo da kayan masarufi daga kasashen musulmi. Za su kwana kamar bakwai suna sayar http://fb.com/ waziriaku da hajar da suka zo da ita, daga nan kuma sai su sayi kayan lambu su koma da su. Zan shiga cikin gari in duba in gani ko jirgin ya iso. Ka yi zamanka yau, ka huta, kada ka yi aikin kome, sai dai ka fara shirye-shiryen tafiya." Mai lambu na gama fadin haka sai http://fb.com/ waziriaku ya sa kai ya nufi cikin birni. Bayan mai lambu ya fita, sai Kamaruzzaman ya cika da farin ciki, har hawayen dadi suka rika zuba daga idanunsa. Ya tashi yana murna zai koma cikin dakinsa, sai ya yi tuntube ya fadi, http://fb.com/waziriaku goshinsa ya bugi wani kututturen ice ya fashe, jini ya zuba daga goshinsa har ya garwaya da hawayen idonsa. Ya tashi zaune, ya sami tsumma ya daure goshinsa, sa'annan ya tashi ya ci gaba da tafiya. Yana cikin tafiya, kafin ya kai ga dakinsa, http:// fb.com/waziriaku sai ya ji fakafniyar tsuntsaye a saman wata bishiya. Ya daga kansa sama, sai ya ga tsuntsaye biyu ne suke fada da juna, suna ta cire wa juna gashi. Kamaruzzaman ya yi tsaye yana kallon tsuntsayen nan, can sai ya ga daya ya sa bakinsa ya kame makogwaron abokin http://fb.com/waziriaku fadansa ya matse gam. Wanda aka matse wa makogwaro, ya yi ya yi ya kwace, ya kasa har dai ya gaji ya kai takarda. Da abokin fadansa ya tabbatar da ya mutu, sai ya sako shi ya fado kasa, ya tashi sama ya nufi na sa waje. http://fb.com/waziriaku Mataccen tsuntsun nan ya fado kasa a gaban Kamaruzzaman, har ya daga kafarsa zai ci gaba da tafiya, sai ya ga wasu tsuntsaye biyu sun sauka a kan gawar wannan dan uwan nasu. Kamaruzzaman ya tsaya yana kallon su domin ya ga abin da za su yi. Tsunstu daya http://fb.com/waziriaku ya tsaya daidai kan gawar, dayan kuma ya tsaya daidai bindinsa. Suka daga kawunansu sama, suka kada fuka-fukafukansu suna wani irin kuka mai ban tausayi. Yayin da Kamaruzzaman ya ga haka, sai ya tuna abin da ya same shi na bakin ciki, tausayin tsuntsaye ya hadu da bakin cikinsa, ya yi kuka tare da wadannan tsuntsaye. Daga nan sai ya ga sun tona rami, suka dauki gawar dan uwansu suka binne a cikin ramin nan, http://fb.com/waziriaku suka tashi sama cikin hanzari. Kamaruzzaman na tsaye yana mamakin wannan abu sai ga tsuntsayen nan biyu sun kamo tsuntsun nan da ya kashe dan uwansu. Suka sauka da shi bisa kabarin da suka rufe dan uwansu. Suka yi ta caccakar sa da baki har suka http://fb.com/waziriaku kashe shi. Suka ci gaba da yagarsa, da kafafunsu, suna caccakar sa da bakunansu har sai da suka bude cikinsa, suka yi masa kaca-kaca, sa'annan suka bar shi a nan suka tashi sama. Wannan abu ya dimauta Kamaruzzaman, ya yi tsaye yana http://fb.com/waziriaku kallon gawar wannan tsuntsu wanda tsuntsayen nan biyu suka yi kaca-kaca da namansa. Yana cikin dubansa sai yaga wani abu yana kyalli a cikin bulukotonsa. Ya matsa ya sa hannu ya farke bulokoton, sai ya ga dan dutsen nan na matarsa Badura, http://fb.com/waziriaku wanda shi ne sanadiyyar rabuwarsu, har ya zo wannan birni. Saboda tsananin farin cikin samun wannan dan dutse sai ya fadi kasa sumamme. http://fb.com/ waziriaku Bayan ya farfado, sai ya yi godiya ga Allah madaukakin Sarki, ya ce, "Godiya ta tabbata ga Ubangijin talikkai, hakika gane wannan dutse da na yi, http://fb.com/waziriaku bushara ce ta cewa nan ba da jimawa ba zan sadu da abar begena." Daga nan ya sake duban dan dutsen nan da kyau da rubuce-rubucen da ke jikinsa, amma bai fahimci kome ba. Ya sami tsumma masu kyau, ya kulle dutsen a ciki sa'annan ya http://fb.com/waziriaku daura tsumman a damtsen hannunsa. Ya shiga dakinsa ya zauna yana jiran dawowar mai lambu, amma har dare ya tsala bai dawo ba. Kamaruzzaman ya http:// fb.com/waziriaku kwanta a kan shimfidarsa, barci ya kwashe shi, bai farka ba sai da gari ya waye. Yayin da gari ya waye mai lambu bai dawo ba, sai Kamaruzzaman ya dauki kwando da fartanya domin yin aiki kamar yadda ya saba. Ya zo gindin http://fb.com/waziriaku bishiyar dorawa domin ya nome ciyawar da ke wurin. Ya fara noma ke nan sai ya ji fartanyarsa ta karto wani abu a kasa kamar karfe. Ya kara nomawa, ya kara jin wannan abu. Daga nan sai ya ci gaba da nome kasar http://fb.com/waziriaku wurin, sai ya ga wani rufi na karfe ya bayyana, ya share kasar gaba daya sai ya ga ashe kofa ce ta bakin karfe. Ya daga kofar sai ya ga rami ya yi kasa ga kuma tsani ya sauka kasan ramin. http://fb.com/ waziriaku ............ Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwanninku... Yusuf abdullahi A JIBAGA, Ke tare daku(23) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SAHAHRUZZAMAN ( Tare da: Bukar Mada - http://fb.com/ bukarmada ) Kamaruzzaman ya ci gaba da nome kasar wurin, sai ya ga wani rufi na karfe ya bayyana, ya share kasar gaba daya http://fb.com/waziriaku sai ya ga ashe kofa ce ta bakin karfe. Ya daga kofar sai ya ga rami ya yi kasa ga kuma tsani ya sauka kasan ramin. Ya tattaka matakalar tsanin ya sauka cikin ramin, da farko duhu ya hana shi ganin kome a cikin ramin. Bayan dan lokaci sai idanunsa suka waye da duhun rami, sai ya ga ashe wannan rami wata taska ce irin ta dauri wadda http://fb.com/ waziriaku Adawa da Samudawa ke yi domin ajiye dukiya. Ramin dai wani babban dutse ne, mai kamar girman daki, aka rarake cikinsa kamar yadda ake rarake goran duma, aka yi masa kofa a sama. Sai kuma aka gina katon rami aka saka wannan dutse ciki, kofarsa na kallon sama, to, kofar ce aka yi wa kyaure na bakin karfe. Daga nan kuma sai http://fb.com/waziriaku Kamaruzzaman ya ga wasu irin randuna manya- manya, kowace tana iya boye kato kome girmansa. Ya matsa kusa ga tukunya daya ya duba, babu abin da ke ciki sai jan zinari, gangariya, yana daukar ido. Ya duba sauran tukanen ya gan su kowace shakare da zinari. Kamaruzzaman ya ce a cikin ransa, "Ranakun bakin ciki na gab da shudewa a http://fb.com/ waziriaku gare ni, hakika wannan dukiya tsaraba ce Allah ya ba ni, wadda zan tafi da ita wurin mahaifina. Mai lambu ma, daga yau Allah ya hutar da shi daga wahala, sai dai ya rike lambunsa domin sha'awa amma ba domin neman kudi ba." Daga nan ya tattaka tsani ya fito daga cikin ramin, ya mayar da kofa ya rufe, ya mayar da kasar. http://fb.com/waziriaku Ya ci gaba da aikinsa a cikin lambu har rana ta fadi. Zuwa can da dare sai ga mai lambu ya dawo, ya ce da Kamaruzzaman, "Ya dana, ina yi maka albishir da zuwan jirgi tun jiya. Shi ne jirgin da zai dauke ka zuwa birnin Labunus, daga can kuma sai ka bi ayarin fatake masu http://fb.com/ waziriaku tafiya birnin Kalidan, inda za ku yi tafiyar wata shida a kasa. Sai ka fara shiri domin nan da kwana shida jirgin zai tashi, bayan 'yan kasuwa sun gama ciniki. Na riga na yi magana da madugunsu cewa idan sun tashi tafiya zan hada ka da su." http://fb.com/waziriaku Da jin haka sai Kamaruzzaman ya cika da farin ciki, ya sumbaci hannun mai lambu don murna, ya ce, "Baba, kamar yadda ka zo mini da wannan albishir mai dadi, ni ma zan yi maka albishir http://fb.com/waziriaku irinsa." "Wane albishir ne wannan?" Mai lambu ya tambaya. Kamaruzzaman ya fada masa taskar da ya gani a cikin rami. Mai lambu ya yi mamaki kwarai, ya yi farin ciki. Ya dubi Kamaruzzaman ya ce, "Ya dana, ka sani cewa http://fb.com/ waziriaku shekarata tamanin ina aiki a cikin wannan lambu, amma Allah bai nufe ni da ganin wannan taska ba, sai kai da ka zo kwana-kwanan nan. Don haka wannan dukiya da ka gani Allah ne ya ba ka ita domin ka rage radadin kuncin da ka shiga, ni kam ba ni da hakkin kome a cikinta. Domin da rabona ce, da Allah ya nuna mini ita tun tuni, http://fb.com/waziriaku kafin zuwanka." Kamaruzzaman ya ce, "Kada ka fadi haka, Baba, tamu ce mu biyu, babu makawa ka dauki rabi daga cikinta." Daga nan ya dauki shama'a, ya ja mai lambu suka nufi wurin ramin nan, suka shiga cikinsa. Ya nuna masa randunan nan wadanda suke makare da zinariya. Suka kidaya tukane, suka ga guda ashirin ne, http://fb.com/waziriaku Kamaruzzaman ya ce, mai lambu ya dauki goma, shi ma ya dauki goma. Mai lambu ya ce masa, "Gobe zan shiga gari in sayo tukwane masu yawa, ka zuba zinariya kasan kowace tukunya, kamar rabin tukunyar, sauran rabin kuma sai ka cika ta da 'ya'yan zaitun na wannan lambu. Ka yi http://fb.com/waziriaku haka ga kowace tukunya, har ka boye zinariyar duka a cikin tukwanen, yadda mutane za su dauka cewa duka 'ya'yan zaitun ne a ciki. Idan ka sauka kuma za ka sayar da zaitun dinka da daraja, domin kalar wannan zaitun ba a samun shi ko'ina sai a wannan kasa tamu, don kyawunsa da dadinsa ake rububinsa a kasuwannin wasu kasashe, ana kiran kalar wannan zaitun Asafiri." Kamaruzzaman ya http://fb.com/waziriaku amince da shawarar mai lambu. Da gari ya waye mai lambu ya shiga cikin gari ya sayo tukwane masu yawa, ya samu masu jakai suka kawo masa a lambunsa. Kamaruzzaman ya rika dibar zinariya yana cika rabin tunya da ita, http://fb.com/waziriaku sauran rabin kuma sai ya tunfaye da 'ya'yan zaitun, ya rufe bakin da ganye, har ya cika tukwane hamsin daga randunansa guda goma, ya bar wa mai lambu sauran goman. Ya cire dan dutsen nan da ya daure a damtsen hannunsa, ya kwance shi daga cikin tsumma, ya saka shi kasan daya daga cikin http://fb.com/waziriaku tukwanen nan, ya yi wa tukunyar 'yar alama yadda zai yi saurin shaida ta. Kamaruzzaman ya zauna tare da mai lambu, suna zance amma zuciyarsa na can na sake- sake, yana cewa a cikin ransa, "Da zarar na isa kasar Labunus, zan bi ayarin fatake zuwa kasarmu, daga can sai in shiga neman http:// fb.com/waziriaku masoyiyata Badura. Ko a wane hali take ciki yanzu? Ko sun ci gaba da tafiya ne zuwa kasar mahaifina, ko kuwa juya suka yi da baya zuwa wurin mahaifinta? Ko kuwa dai wani hatsari ya same su a kan hanya?" Haka dai ya yi ta tunani a cikin ransa. http://fb.com/waziriaku Da mai lambu ya lura da cewa shi kadai ke ta zuba hira kamar aku, hankalin Kamaruzzaman ba ya wurinsa, sai ya kyale shi. Shi ma ya shiga lissafe-lissafen abin da zai yi da tasa dukiyar. Bayan Kamaruzzaman ya dawo daga duniyar tunani, sai ya fada wa mai lambu labarin abin da ya gani na mamaki game da tsuntsaye. Suka yi ta kakabin abin har barci ya kwashe su. http:// fb.com/waziriaku Yayin da gari ya waye, sai mai lambu ya tashi da masassara. Cikin kwana uku sai masassara ta zama zazzabi mai zafi, ya zama daga kwance sai kwnace, wani lokaci kuma sai ya suma, Kamaruzzaman ya rika kuka saboda ganin halin da yake ciki. http://fb.com/waziriaku A kwana na hudu sai ga madugun jirgi ya zo kofar lambun ya kwankwasa kofa, Kamaruzzaman ya tafi wurinsa. Madugu ya tambaya, "Ina mutumin da za mu tafi da shi birnin Labunus?" Kamaruzzaman ya ce, "Ai ni ne." Madugu ya tambaye shi, http://fb.com/waziriaku "Kana da kaya ne?" Kamaruzzaman ya amsa, "Ina da tukwane hamsin na 'ya'yan zaitun." Madugu ya ce, "To, ka shirya zan turo bayi yanzu, su dauki kayan a saka a cikin jirgi. Kai kuma gobe da alfijir ya keto, ka tabbata kana cikin jirgin, domin http://fb.com/waziriaku akwai alamun iska mai kyau wadda za ta dace da yanayin teku." Daga nan Madugun jirgi ya koma, cikin dan lokaci kankani sai ga bayi ya turo. Suka kwashi tukwanen Kamaruzzaman suka tafi da su zuwa ga jirgi, shi kuwa http://fb.com/waziriaku Kamaruzzaman ya koma inda yake jinyar mai lambu. Tun cikin dare rashin lafiyar mai lambu ta yi kamari, gari bai waye ba sai da ya ce ga garinku nan. Kamaruzzaman ya yi kuka mai tsanani a kan mutuwar http://fb.com/waziriaku mai lambu, ya yi bakin ciki, bakin ciki mai yawa. Ya dauki magirbi ya haka rami, ya yi wa mai lambu jana'iza, ya yi masa addu'ar neman gafara ga Allah madaukakin Sarki. Ko da ya gama rufe shi har rana ta take. Ya kulle 'yan kayansa, ya fita daga cikin lambu da hanzari, ya http:// fb.com/waziriaku mayar da kofa ya rufe, ya nufi gabar teku wurin jirgi. Da isarsa wurin sai ya hangi jirgi ya nausa cikin teku. Ya yi kira, ya yi daga hannu, amma duk a banza, jirgi bai tsaya ba balle http://fb.com/waziriaku ya juyo. Ya yi tsaye yana kallon jirgi har ya bace a cikin teku. Kamaruzzaman ya juya ya koma cikin http:// fb.com/waziriaku lambu zuciyarsa cike da bakin ciki. Ya zauna yana kuka yana marin fuskarsa, yana zuba kasa bisa kansa don bakin ciki. ............ Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwa. Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ke tare daku(24) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN ( Bukar Mada - http://fb.com/bukarmada ) Kamaruzzaman ya juya ya koma cikin lambu zuciyarsa cike da bakin ciki. Ya zauna yana kuka yana marin fuskarsa, yana zuba kasa bisa kansa don bakin ciki. Ya tuna cewa yanzu shi kadai zai zauna a cikin lambu, ga shi kuma ya sake rabuwa da dan dutsen nan na Badura. Yanzu shi da fita wannan kasa sai kuma wata shekara idan jirgin ya dawo. Ya ci gaba da kuka, yana rera wakoki. Bayan kwana biyu, ya ci gaba da aikin lambu kamar yadda ya saba, ya shiga tasakar nan ya kwashe sauran zinaren nan, rabon mai lambu, ya zuba shi a cikin wasu tukwane hamsin, ya zuba 'ya'yan zaitun a sama, ya sa ganye ya rufe. Ya zauna jiran dawowar jirgi wata shekara. Wannan shi ne al'amarinsa. Amma jirgi kuwa ya ci gaba da tafiya cikin teku dauke da tukwanen Kamaruzzaman, iska kuwa ta yi masa kyau har ya isa birnin Labanus. Bisa kaddara, lokacin da jirgi zai tsaya a bakin gaba, a lokacin kuma gimbiya Badura tana zaune a bakin taga, bisa benen gidanta, tagar kuma tana kallon teku. Sai ta ga wannan jirgi na 'yan kasuwa dauke da kaya niki-niki. Tana ganin wannan jirgi sai ta ji gabanta ya fadi, amma ba ta san dalili ba. Nan take ta sauko daga kan bene, ta debi wasu askarawa suka nufi wurin jirgi. Yayin da ta isa wurin jirgi har dillalai da 'yan kasuwa masu sari sun kewaye jirgi suna jira a fara fitowa da kayan cikinsa. Yayin da jama'a suka ga sabon Sarki da askarawansa, sai suka ja da baya, suka fadi suka yi gaisuwa. Badura ta matsa kusa ga madugun jirgi ta tambaye shi, "Wace haja kuka zo da ita?" Madugun jirgi ya amsa da cewa, "Allah ya ba ka nasara, mun zo da yadiddika, da zannuwa, da kwayoyin magani, da kayan kwalliya na mata, irinsu; katambiri, hoda, jagira, janbaki, kwalli, turare na ruwa da na hayaki. Akwai kuma kayan lambu irinsu, karas, albasa, tafarnuwa, citta, gauta, yalo. Da kuma 'ya'yan itatuwa kamarsu, lemu, mangwaro, gwaba, tuffa, inabi, tsada, da kuma 'ya'yan zaitun na Asafiri wanda babu irinsa a wannan kasa. Kadan ke nan daga cikin dimbin kayayyakin da muka zo da su, Allah ya taimakeka." Lokacin da Badura ta ji ya ambaci 'ya'yan zaitun sai yawunta suka tsinke, domin kuwa babu abinda ta fi sha'awar ci kamar zaitun. Ta kuma tambayarsa, "Wane adadi kuka zo da shi na 'ya'yan zaitun?" Madugu ya dukar da kansa kasa ya ce, "Allah ya ba ka nasara, tukwane hamsin ne kawai muka zo da su, ko su ma na wani mai lambu ne, saurayi, wanda ya yi jinkiri bai zo ba har jirgi ya baro shi a can." Badura ta ce, "Babu makawa ku sayar mini da dukkanin tukanen nan guda hamsin, da akwai wasu ma, da na saye su duka. Zan biya ku kudin, duka lokacin da kuka koma sai ku ba shi kudinsa." Madugu ya ba da umurni aka sauke tukwanen Kamaruzzaman. Badura ta matsa kusa ga tukunya daya ta yaye ganyen da yake samanta. Ta ga 'ya'yan zaitun masu kyau, ta mayar da ganyen. Ta juya wurin Madugun jirgi ta ce masa, "Nawa ne kudin wannan zaitun?" Madugu ya ce, "A kasar da muka fito ba shi da wani daraja sosai, dududu kudinsa ba zai wuce 'yan daruruwan dirhamai ba." Badura ta ce, "To, a nan fa, kudinsa zai kai nawa?" Madugu ya ce, "A nan kasar kuma kudinsa zai kai dirhami dubu, Allah ya ba ka nasara." Nan take Badura ta jawo lalitarta ta kirga dirhami dubu ta ba Madugun jirgi, ta umurci askarawa suka dauki tukwanen 'ya'yan zaitun, suka juya zuwa gida. Da dare ya yi, bayan Badura da Hayatunnufusi sun gama cin abinci, sai Badura ta dauko tukunyar zaitun daya ta zazzage a cikin akushi domin su ci, sai suka ga jan zinare na zubowa tare da 'ya'yan zaitun daga cikin tukanyar. Ta dubi Hayatunnufusi cikin mamaki ta ce, "Wannan ai zinariya ce!" Cikin gaggawa suka tashi suka dauko sauran tukwanen, suka zazzage su a cikin dakin, a cikin kowace tukunya suka ga tamkar yadda suka gani ga ta farko. Wannan abu ya yi matukar ba su mamaki da kuma daure musu kai. Garin tone- tonensu sai Badura ta tono dan dutsen nan nata a cikin zinarin, ta dauke shi ta duba sosai, ta gane dan dutsenta ne wanda Kamaruzzaman ya kwance a kubakar wandonta, ranar da ta tashi ba ta gan shi ba. Nan take ta yi wata irin kara don farin ciki, ta fadi kasa sumammiya. Bayan ta farfado, ta nuna wa Hayatunnufusi dan dutse, ta ce, "Wannan dan dutse da kika gani shi ne sanadin rabuwata da abin begena, babu shakka kuma yanzu shi zai yi sandin sake haduwarmu." A cikin wannan dare dai, babu wadda ta runtsa tsakanin Badura da Hayatunnufusi don farin ciki. Gari na wayewa, Badura ta kintsa ta fita fada ta kame bisa karagar mulki. Ta aika maza-maza a zo mata da Madugun jirgi. Yayin da Madugun jirgi ya zo sai ya fadi a gabanta ya yi gaisuwa, fadawa suka ce, "An gaisheka!" Badura ta dubi Madugun jirgi ta murtuke fuska, ta yi masa magana cikin tsawa, "Ina kuka baro mai zaitun din nan?" Madugu ya sunkuyar da kansa kasa ya amsa, "Allah ya taimake ka, mun baro shi ne a garin Matsafa, bayan ya sa kayansa a cikin jirgi sai ya yi jinkiri bai zo ba har jirgi ya tashi." "Babu makawa ku koma ku dawo mini da shi." In ji Badura. Ta ci gaba da cewa, "Domin kuwa ya aikata mana laifi mai girma wata shekara da ya kawo mana 'ya'yan zaitun, ya yi mana sata ya gudu. Zan sa a tsare dukkan kayan da kuka zo da su, idan ba ku kawo mana shi ba kuwa, to, zan sa a nemo ku duk kasar da kuka shiga a yanka ku daya bayan daya." ............ Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwa'.. DAGA ==>Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ(25) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN ( Bukar Mada - http://fb.com/bukarmada ) "Babu makawa ku koma ku dawo mini da mai kayan nan." In ji Badura. Ta ci gaba da cewa, "Domin kuwa ya aikata mana laifi mai girma wata shekara da ya kawo mana 'ya'yan zaitun, ya yi mana sata ya gudu. Zan sa a tsare dukkan kayan da kuka zo da su, idan ba ku kawo mana shi ba kuwa, to, zan sa a nemo ku duk kasar da kuka shiga a yanka ku daya bayan daya." Madugu ya koma wurin 'yan uwansa ya kwashe abin da ya faru tsakaninsa da Sarki ya fada musu. Ya ce da su, "Babu makawa yanzu in koma garin matsafa domin dauko yaron mai lambun nan da muka baro." Aka sauke wa jirgi kaya, Madugu ya shiga ya tuka shi, ya karkata fuskarsa ga jihar da suka bar Kamaruzzaman. Ya yi ta keta ruwa dare da rana, babu tsayawa. Allah mai iko ya nufe shi da isa birnin matsafa a cikin dare. Ya daure jirginsa bakin gabar teku, ya nufi lambun da Kamaruzzaman yake. A cikin wannan dare kuwa, Kamaruzzaman na zaune yana tunanin abar begensa, har yana rera wadannan baitoci: "Wannan dare ya yi tsawo, har taurari sun ki gushewa. Daren da saboda tsawo nake ganinsa tamkar yinin tsayuwar Alkiyama." Yana cikin rera wannan waka sai ya ji ana kwankwasa kofar lambu. Ya tashi domin ya ga mai kwankwasa masa kofa. Yayin da ya bude kofa Madugun jirgi ya gan shi, sai ya cafki hannunsa ya nufi wurin

Chapter 7 of 14