Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
11 / 14
allura bisa ga gefen ido, to, da ya zama abin lura ga masu hankali." Daga nan ya tsuguna ya kwance wa Sarki bakin jaka, bai rage masa kome ba. Sarki ya yi mamaki, gayar mamaki, ya ce babu shakka samun adalin mutum mai gaskiya da rikon alkawari kamar Amajadu sai an tona. Ya neme shi da ya zama daya daga cikin waziransa. Amjadu ya amince da bukatar Sarki, aka nada shi Waziri. Sarki ya ba shi gida da bayi da kuyangi da dawaki da tufafi kala-kala, na alfarma. Aka yanka masa albashi. Shi kuwa Bahadaru Sarkin Fada, Sarki ya nemi gafararsa bisa tozarta shi da ya yi, aka yi masa kyauta mai yawa, aka kara masa matsayi. Waziri Amjadu ya kasance yana mulki da adalci a tsakanin talakawa, ya kasance mai yawan kyauta da kyautatawa. Kullum sai ya sa mai shela ya shiga cikin gari yana cigiyar dan uwansa Asadu, amma a banza. Ko wanda ya taba ganin sa ba a samu ba. Amma Asadu kuwa, yana can tsare a dakin karkashin kasa, a hannun matsafa, kullum ana gana masa azaba dare da rana har tsawon shekara guda. Yayin da lokacin zuwa dutsen wuta, wurin ibadar matsafan nan ya zo. Sai tsohon nan da ya kamo Asadu, wanda yake sunansa Baharamu, kuma shi ne shugaban matsafan nan gaba daya, ya sa aka shirya jirgin ruwa da dukan kayan da za su bukata yayin wannan tafiya. Da suka gama shiri tsaf, sai aka fito da Asadu aka saka shi cikin wani katon akwati aka rufe, aka kinkimi akwatin aka nufi bakin teku domin saka shi cikin jirgi. To, ashe lokacin da matsafan nan ke ta kici-kicin sa kayansu cikin jirgin ruwa, Waziri Amjadu na tsaye a bakin tagar dakinsa wanda yake saman bene, yana kallon ruwan teku. Lokacin da ya ga matsafan nan na ta shirin tafiya, sai ya ji gabansa ya fadi, bai san dalili ba. Nan take ya yi umurni a daura masa sirdi. Ya hau tare da wasu askarawa ya nufi bakin teku. Da suka isa inda jirgin matsafan nan yake, ya sa askarawa su binciki jirgin nan. Suka shiga cikinsa suka bincika ko'ina amma ba su ga wani abu da ya dauki hankalinsu ba, suka dawo suka fada wa Amjadu. Waziri Amjadu ya juya da jama'arsa suka koma gida, yana cike da tunanin dan uwansa. Yayin da ya shiga dakinsa sai idonsa ya kai ga wani rubutu da aka yi bisa bangon dakin, ya ga an rubuta: Idan masoyanmu sun yi jijjibi don ganinmu, cewa zukatansu ba su fasa tunaninmu. Sun maishe ni daddauda, sun hane ni jin dadin ci da na barci. Da ya gama karanta rubutun, sai hawaye ya karyo daga idanunsa, ya yi kuka, kuka mai yawa. Su kuwa matsafa da suka gama shiri, sai suka fada cikin jirgi. Baharamu ya yi wa masu tuki tsawa da su yi gaggawa, suka tsunduma cikin teku suka nufi tsibirin Dutsen Wuta. Bayan sun yi nisa cikin teku, Baharamu ya sa aka fitar da Asadu daga cikin akwati, ya kawo 'yar gurasa da ruwa ya ba shi. Suka ci gaba da tafiya kwana da kwanaki har suka fara hangen tsibirin Dutsen Wuta. Yayin nan guguwar teku ta taso, rakuman ruwa suka motsa, teku ya haukace ta rika juya jirginsu yadda yake so, suka debe tsammani daga rayuwa. Iska ta dauki jirgin ta jefa shi wani teku na daban, wanda ba su sani ba, tafarki ya saba musu. Bayan teku ya lafa, da suka duba gabansu, sai suka hangi wani birni a gabar teku, wanda yake da wata babbar hasumiya, madaukakiya, a tsakiyarsa. Wannan hasumiya tana da tagogi wadanda suke kallon teku, duk jirgin da zai shigo wannan birni, za a hange shi ta cikin wannan hasumiya tun daga nesa. Ashe wannan birni na wata Saruniya ce, wai ita Murjanatu. Wannan sarauniya kuwa ta kasance musulma, mai tsananin kishin addinin musulunci. Da suka hangi wanna birni, sai madugun jirgi ya ce, "ya shugabana, Baharamu, ka sani cewa mun bace daga tafarkinmu, mun shigo birnin Sarauniya Murjanatu, musulma. Idan kuwa ta gane cewa mu matsafa ne, babu makawa yanka mu za ta yi, babu daya da zai tsira daga hannunta. Ga shi kuma dole mu sauka a birninta mu huta, sa'annan mu sake fita zuwa ga bukatarmu." Baharamu ya ce, "sai mu canza tufafinmu, mu yi shiga irin ta musulmi. Shi kuma wannan (ya nuna Asadu) sai mu sa masa kayan bayi. Idan aka tambaye mu sai mu ce, mu dillalai ne na bayi, bakake da farare Duk mun sayar da na hannunmu, saura wannan farin bawan kawai, amma ba za mu sayar da shi ba, za mu rike shi a hannunmu saboda ya iya karatu da rubutu." Madugun jirgi ya ce, wannan dabara taka ta yi. Suka shirya bisa ga haka, suka canza tufafinsu suka yi shigar musulmi, suka sanya wa Asadu kayan bayi. Da isar su bakin gaba sai suka tarar da Sarauniya Murjanatu da askarawanta suna jiran isowar su, ashe har labarin zuwansu ya isa gare ta. Suka sauka daga cikin jirgi suka fadi suka yi gaisuwa. Ta tambaye su daga ina? Kuma wace haja suka kawo birninta? Madugun jirgi ya duka ya ce, "Allah ya ba ki nasara, mu dillalan bayi ne, muna tafe tare da shugabanmu." Ta tambaya, wane ne shugaban nasu? Baharamu ya matso kusa gare ta, yana rike da Asadu a cikin kayan bayi, ya fadi ya gaishe ta. Ta tambaye shi sana'arsa, ya ce mata shi mai cinikin bayi ne. Ta dubi Asadu, ta gan shi cikin shigar bayi, ta tambaye shi, "menene sunanka?" "Sunana na asali ko kuwa na yanzu?" "Suna biyu gare ka?" Asadu ya amsa mata cikin muryar kuka, "I, sunana na asali Asadu, mai farin ciki. Amma yanzu na koma Mutarrul Maisaramus" Yanayinsa da kalamansa suka sosa mata zuciya, ta kara tambayarsa, "ka iya rubutu?" Ya amsa, "I." Ta kawo tawwada a cikin kaho, da alkalamin gashin tsuntsu da takarda. Ta ce, "rubuta mini wani abu da zan iya karantawa." Ya karba ya rubuta wadannan baitoci: Yaya bawa zai yi da ransa, idan kaddara ta auka masa? Ya Shugaban adilai, ina mafita ga wanda ka daure ka jefa shi cikin kogi. Ka gargade shi da kada ya kuskura ruwa ya jika jikinsa? Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ SHINE MAI KAWO MUKU WANNAN LABARI35 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMA Yayin da Murjanatu ta karanta abin da ya rubuta sai tausayinsa ya kama ta. Ta juya wurin Baharamu ta ce, "ina so in sayi wannan bawa. Nawa ne kudinsa?" Baharamu ya dukar da kai ya ce, "ya Sarauniya, mai karfin mulki, wannan bawa ba na sayarwa ba ne. Na sayar da duka 'yan uwansa, shi kadai ya rage mini. Na yi niyyar in rike shi ga hannuna." Sarauniya Murjanatu ta ce, "ga shi kuwa ya kwanta mini a rai. Lallai ka sayar mini da shi, ko kuma ka ba ni shi kyauta." Ya ce da ita, "Allah ya ba ki nasara ki yi hakuri, ba zan iya rabuwa da shi ba." Sarauniya ta harzuka, ta daka masa tsawa, "to, je ka, an karbe shi da karfi daga hannunka. Kuma ku gaggauta bar mini birni kafin gari ya waye, idan ba haka ba zan sa a washe ku, kuma a kakkarya jirginku." Ta juya ta tafi da Asadu Gidanta. Sarkin tsafi Baharamu ya juya wurin 'yan uwansa yana cewa, babu makawa mu koma gida mu sake shiri. Sa'annan ya umurci mutanensa su cika salkunansu da ruwa, su dan huta zuwa dare su juya da baya zuwa gida. Sarauniya Murjanatu kuwa, da ta iso da Asadu gidanta, sai ta kai shi wani daki wanda tagoginsa suke kallon teku, ta umurci kuyangi su kawo abinci da abin sha. Kuyangi suka shiga girke musu kayan abinci da na sha kala-kala a gabansu. Sarauniya ta umurci Asadu ya ci abinci, suka ci tare har suka koshi. Daga nan sai ta jawo tulun giya har suka yi tatil. Allah da ikonsa sai ya jefa son Asadu a cikin zuciyar Murjanatu, so kuwa mai tsanani. Ba su daina kwankwadar giya ba har sai da suka kusa fita daga hayyacinsu. Daga nan sai Asadu ya mike tsaye ya fita daga dakin da nufin kama ruwa. Da ya fito daga dakin, sai ya ga kofar gidan a bude. Ya yi sha'awar ya dan yi tattaki domin ya mike kafafunsa, sai ya fita daga cikin gidan ya yi ta tafiya har ya iso ga wani lambu wanda yake kewaye da katanga, da ya tura kofar sai ya ji ta a bude. Ya shiga ciki ya mayar da kofa ya rufe, ya ga lambun nan cike da 'ya'yan itace da furanni masu ban sha'awa. Ya tsuguna a gindin wata bishiya ya biya bukatarsa, ya tashi ya nufi wani dan tabki da aka kirkira a cikin lambun domin ya kama ruwa. Bayan ya kama ruwa sai ya yi alwala, ya wanke hannuwansa da fuska. Ya tashi domin ya koma wurin Sarauniya, sai ya ji wata iska mai dadi ta buge shi, ya ji duk kasala ta rufe shi, babu abin da yake so kamar ya zauna wurin nan ya kwashi iskar nan mai ni'ima. Ya tube rigasa, yadda iskar za ta ratsa shi sosai, ya kishingida a gindin tabkin nan, sai barci mai nauyi ya dauke shi. Ya yi ta sharar barci har dare ya yi sosai bai farka ba. Su kuwa matsafan nan da dare ya yi sai Baharamu ya ce musu su yi maza su shirya kayansu domin tafiya. Suka ce, "mun ji mun karba." Suka ce ya ba su lokaci su cika salkunansu da ruwa tukuna. Suka zari salkunan fata suka shiga gari neman ruwa, suka yi ta yawo amma ba su ga rijiya ba wadda za su debi ruwa. Suna cikin yawo sai suka fado inda lambun nan yake, suka gan shi zagaye da katanga. Suka ce a cikin ransu, "babu makawa a sami ruwa cikin wannan wuri." Sai suka tsallaka katanga suka shiga ciki. Suka yi ta zagayawa har suka iso wurin dan tabkin nan da Asadu ke barci a gefensa. Da zuwan su wurin sai suka ga mutum kwance, fuskarsa tana kallon sama, yana ta sharbar barci. Ko da suka dubi fuskarsa da kyau, sai suka shaida shi. Suka cika da farin ciki, suka cika salkunansu da ruwa sa'annan suka ciccibi Asadu suka bude kofar lambu suka fita da shi, suka nufi wurin shugabansu Baharamu. Lokacin da suka zo da Asadu wurin Baharamu, sai suka ce masa, "buga tamburanka, ka kuma busa kakaki don murna. Domin kuwa mun dawo da yaron nan da Sarauniya ta kwace daga hannunmu." Suka ajiye Asadu a gabansa. Yayin da Baharamu ya kyalla ido ya ga Asadu, sai zuciyarsa ta yi fari, ya cika da farin ciki. Ya yi ta yabon abokan tafiyarsa, bisa wannan kokari da suka yi. Ya yi umurni a kwance jirgi da sauri a kama hanya. Suka kwance jirgi, suka saka Asadu cikin akwatin da aka fitar sa shi, suka tsunduma cikin teku, suka tasar wa tsibirin Dutsen Wuta. Wannan shi ne al'amarinsu. Amma Sarauniya Murjanatu da ta ga har dare ya yi Asadu bai dawo ba, sai ta tashi ta shiga ko'ina cikin gidan nan ta duba, amma ba ta gan shi ba. Daga nan ta fita tare da kuyanginta suna rike da shama'a, suka shiga cikin gari suna neman shi. Sai suka iske kofar lambu a bude, nan take Sarauniya ta raya a ranta cewa yana ciki. Suka shiga cikin lambun har suka zo wurin dan tabkin nan, sai suka ga rigar Asadu, yashe a kasa. Suka bincike ko'ina cikin lambun amma ba su ji duriyarsa ba. Haka dai suka yi ta neman Asadu har gari ya waye ba su gan shi ba. Ta tambayi labarin masu jirgi, aka ce mata ai tun cikin dare suka bar garin. Daga nan ta gane babu makawa su ne suka dauke shi. Ranta ya baci, ta yi fushi, fushi mai mai tsanani. Nan da nan ta sa aka shirya mata jirage goma masu sauri, ta kwashi askarawa cikin shirin yaki, ta shiga jirgi daya suka bi bayan jirgin matsafa. Ta yi bushara ga matuka jirage, ta ce musu idan suka tarar da jirgin matsafa da sauri za ta yi musu kyauta mai yawa. Amma idan suka kuskura suka kasa cimma jirgin matsafan har suka kubuta daga hannunta, duk za ta kashe su. Da jin haka sai matuka suka mai da himma ga tuki. Suka yi ta tafiya cikin teku tsawon kwana uku. A kwana na hudu sai suka fara hango jirgin Baharamu da mutanensa. Da ganin haka sai matuka suka kara kaimi, jiragen suka warwatsu da nufin zagaye jirgin Baharamu. A wannan lokaci kuma, Baharamu ya fito da Asadu daga cikin akwati yana gana masa azaba. Ko da ya daga kansa sai ya hango jirage suna keta ruwa daga nesa sun nufo jirginsu. Nan da nan ya gane cewa Sarauniya ce ta biyo su, ya zagi Asadu, ya zungure shi ya ce, "Allah ya wadan ka, ka dai zamar mana kadangaren bakin tulu, kafin Sarauniya ta kashe mu kai za ka fara mutuwa." Sai ya ingiza Asadu cikin teku, tsundum. Suka ci gaba da tafiya suna jiran isowar jiragen Sarauniya. Allah da ikonsa, da yake kuma Asadu na da sauran shan ruwa a gaba, sai ya yi ta ninkaya da hannuwansa da kuma kafafunsa. Iska kuma ta yi ta tura shi har ya yi nisa daga jirgin matsafa. Can zuwa rana faduwa sai iska da rakuman ruwa suka ture shi bakin gaba. Ya tashi ya tube tufafinsa ya matse su ya shanya bisa rairayi yana mai godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya tsirar da shi. Ya zauna tsirara yana jiran tufafinsa su bushe, nan take ya yi waka a kan abin da ya auka masa, ya yi kuka. Da tufafinsa suka bushe, ya dauka ya saka. Ya yi ta tafiya cikin daji, dare da rana, yana ci daga 'ya'yan itatuwa yana sha daga ruwan kogi har wata rana da yamma ya fara hango gari a gabansa. Ya yi farin ciki, ya kuma kara sauri domin ya isa cikin garin. Ko da ya isa bakin garin rana ta fadi an rufe duka kofofin shiga garin. Kwamfa, ashe wannan gari shi ne birnin da dan uwansa Amjadu ke Wazirci, shi ne kuma birnin da aka tsare shi a dakin karkashin kasa aka gana masa azaba, watau Birnin Matsafa. Amma shi bai gane kowane birni ba ne. Da ya ga an rufe kofofin birnin sai ya rika zagaya ganuwar birnin ko zai sami wani wurin da zai kwana kafin gari ya waye. Yana cikin zagayawa sai ya tarar da wani wuri wanda aka zagaye da katanga, ya nufi kofar wurin ya gan ta a bude, sai ya shige ciki. Ashe wurin nan makabarta ce. Ya ga wani kabari a bude, sai ya shige ciki ya kwanta, ya tada kansa da hannuwansa, a haka barci ya dauke shi. Al'amarinsa ke nan. Amma yayin da jiragen Sarauniya Murjanatu suka tarar da jirgin matsafan nan, sai suka yi masa zobe. Baharamu ya ga an zagaye su kamar yadda farin ido ke zagaye da bakin da ke tsakiyarsa. Sarauniya ta tambaye su labarin Asadu. Baharamu ya duka ya yi ta rantse-rantse wai tun da ta kwace shi daga hannunsu, ba su koma ganin shi ba. Ta sa a binciki jirgin. Aka shiga aka yi wa kayansu dai dai, amma ba su ga Asadu ba. Ta sa aka daure su gaba daya, aka koma da su birninta. Da, ta yi nufin kashe su, sai suka ce za su fanshi kan su. Suka bayar da dukan dukiyar da suka zo da ita, ban da jirginsu, ba a bar su da ko allura ba, sai tufafin jikinsu. Suka hau jirgi suka nufi birninsu cike da bakin cikin abin da ya same su. Ko da suka iso bakin gabar tekun birninsu, suka daure jirgi, dare ya riga ya yi har an rufe kofofin birni. Don haka sai suka yanke shawarar su je hurumi su kwana gudun kuraye da kyarkeci. Sai dai abin da ba su sani ba shi ne, daidai lokacin da suke daure jirginsu a bakin teku, a lokacin ne kuma Asadu ya shige cikin daya daga kaburburan wannan makabarta ya yi kwanciyarsa. Suka tasar wa makabarta, suka tarar da kofa a bude. Bayan sun shiga ciki sai Baharamu ya ga wani kabari a bude ya ce a ransa, "babu makawa in ga abin da ya bude wannan kabari." Ya shiga sai ya tarar da mutum kwance yana barci, ya yi matashin kai da hannuwansa. Da ya dube shi da kyau sai ya gane Asadu ne. Nan take ya yi kururuwa, 'yan uwansa suka zo. Ya nuna musu Asadu da ke barci, ya kuma ce musu ai tun da ya yi alkawari sai ya ba Dutsen Wuta jinin Asadu, to, duk inda ya shiga sai ya dawo. Nan take suka daure shi, suka rufe masa fuska. Tun da asuba da aka bude kofofin gari, kafin haske ya bayyana, suka tafi da shi gidan Baharamu, babu wanda ya gan su. Aka daure Asadu cikin sarka aka mayar da shi kurkukun nan na karkashin kasa. Baharamu ya damka shi ga hannun wata 'yarsa, wai ita Bustana, domin ta kula da shi. Ya umurce ta ta rika yi masa azaba dare da rana har zuwa wata shekara da. Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ KE TARE DAKU 35 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN Baharamu ya damka shi ga hannun wata 'yarsa, wai ita Bustana, domin ta kula da shi. Ya umurce ta ta rika yi masa azaba dare da rana har zuwa wata shekara dashekara da za su koma Dutsen Wuta. Ita wannan diya ta Baharamu, budurwa ce kyakkyawar gaske. Farkon zuwan Asadu gidan ba ta nan, shi ya sa aka damka shi ga hannun kuyanga, wadda ta azabtar da shi. Amma Bustana kuwa, tun da ta dora idanunta a kan Asadu, ta gan shi kyakkyawan saurayi, da ido dara-dara farare tas kamar madara, da girar ido kamar ta barewa, sai son sa ya auku a cikin zuciyarta. Wata rana da ta shiga wurinsa sai ta tambaye shi sunan sa. Shi kuwa ya amsa mata da cewa "Sunana Asadu." "Asadu, farin ciki ke nan ko?" Ta tambaye shi, "hakika za ka yi farin ciki. Za ka yi farin ciki a cikin sauran kwanakinka." Ta ci gaba da cewa, "na lura an tsare ka a wannan wuri bisa ga zalunci, bai kamata ka ci gaba da zama wannan wuri ba." Ta yi ta ba shi hakuri bisa ga azabar da aka yi masa a baya, ta kuma kwantar masa da hankali. Ta kwance masa sarkar da aka daure shi da ita. Ta tambaye shi a kan addinin Musulunci. Ya gaya mata cewa, addinin Musulunci shi ne addinin gaskiya wanda Shugabanmu, Annabi Muhammadu (S.A.W.) ya zo da koyarwarsa daga Allah Madaukakin Sarki. Kuma ya tabbatar wa kafirai cewa shi Manzo ne daga Ubangijin talikai, ta hanyar kawo musu ayoyi mabayyana. Ya kuma gaya mata cewa, bautar wuta bata ce mai girma wadda Shaidan jefaffe yake amfani da ita domin karkatar da mutane daga bin tafarkin gaskiya. Ya ci gaba da gaya mata yadda addinin Musulunci yake har zuciyarta ta karkata gare shi. Ta karbi kalmar Shahada daga wurinsa. Ta tashi ta kawo masa abinci mai kyau da nama, da abin sha. Suka ci tare, suka yi salla. Haka ta yi ta ba shi abinci mai kyau, hankalinsa ya kwanta, jikinsa ya murmure. Wata rana Bustana tana tsaye a bakin kofar gida, sai ta ji mai shela yana shela da murya madaukakiya, "wanda duk yake rike da wani saurayi, mai kama kaza da kaza, to, ya fito da shi, za a ba shi kyauta mai tsoka. Duk wanda kuma ya kuskura ya ji wannan sanarwa kuma yana rike da wannan saurayi bai fito da shi ba, idan aka kama shi za a tsire shi a kofar gidansa kuma a washe dukkan dukiyarsa." Yayin da ta ji wannan sanarwa, da ma kuma Asadu ya ba ta dukkan labarinsa, sai ta fahimci cewa shi ake nema. Nan take ta je wurin Asadu ta gaya masa abin da ta ji, ta fito da shi daga cikin dakin da yake kulle, ta riki hannunsa, suka lallaba suka bar gidan, suka nufi fadar Sarki. Da isar su sai Asadu ya ga Amjadu, ya ce, "na rantse da Allah wannan dan uwana ne Amjadu." Lokacin da Amjadu ya gan shi sai ya gane shi shi ma. Suka rungume juna suna zubar da hawaye don farin ciki. Bayan sun dawo daga cikin hayyacinsu, Amjadu ya riki hannun Asadu ya kai shi gaban Sarki, inda Asadu ya kwashe dukkan labarinsa ya gaya wa Sarki. Da Sarki da jama'arsa duk sai da suka zubar da hawaye don tausayi. Sarki ya umurci Waziri Amjadu ya tafi da askarawa a washe gidan Baharamu, a kuma rushe shi. a kuma kawo masa shi a daure. Amjadu ya jagoranci tawagar askarawa, suka rushe gidan Baharamu aka zo da shi gaban Sarki daure cikin igiya. Amjadu ya girmama Bustana bisa ga taimakon Asadu da ta yi. Daga nan suka kara maimaita labarinsu a cikin fada, tun fitowar su daga gida, da kuma rabuwar su har zuwa yanzu kuma da suka sake haduwa. Da suka gama labarinsu, Sarki ya ba da umurni a tafi da Baharamu a tsire shi. Fadawa suka cakume shi za su fita da shi, sai ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ina neman sassauci." Sarki ya ce babu sassauci gare shi sai fa idan zai musulunta. Baharamu ya yarda, ya karbi kalmar Shahada ga Sarki, ya tuba da tsafi. Aka yi murna da musuluntarsa. Baharamu ya dubi Amjadu da Asadu ya ce, "ya shugabannina, hakika dole ku yi murna da wannan haduwa taku bayan rabuwa, domin tamkar yadda Na'imu dan Rabi'u da kuyangarsa Na'imatu suka yi bayan sun rabu ne suka kuma sake haduwa. Aka tambaye shi, su kuma me ya faru gare su? Sai ya kada baki ya ce da su. HIKAYAR NA'IMU DA NA'IMATU. A birnin Kufa, akwai wani attajiri wanda ake kira Rabi'u dan Hatim. Yana daya daga cikin manyan fadawan Sarkin Kufa. Yana da da daya mai suna Na'imu. Wata rana Rabi'u dan Hatim na zaune bisa wundi a cikin kasuwar bayi, sai ya ga an kawo wata kuyanga za a sayar. Wannan kuyanga tana rungume da wata 'yarta karama, kyakkyawa. Sai ya yafuto dillalin da aka damka wa kuyangar, ya tambaye shi, "nawa ne kudin waccan kuyanga?" Dillali ya amsa masa, "dinari hamsin." Rabi'u ya jawo lalitar kudinsa, ya kidaya dinari hamsin ya ba dillali, ya kuma kawo la'adarsa ya ba shi. Ya ja kuyanga tare da 'yarta ya tafi da su gidansa, ya damka su ga hannun matarsa, wadda ta kasance 'yar baffansa ce. Matar ta tambaye shi me zai yi da kuyanga? "Na sayo ta ne domin 'yarta." Rabi'u ya amsa mata, "nan gaba idan 'yar nan ta girma, to, ba za a sami kyakkyawar mace ba kamar ta a duk fadin kasar Larabawa da kewaye." Ta dubi diyar kuyanga da kyau, "ka yi gaskiya, ya kai dan baffana." Ta juya wurin kuyanga ta tambayi sunanta da sunan 'yarta. Kuyanga ta dukar da kai cikin ladabi ta ce, sunanta Taufik, sunan 'yarta kuwa Sa'adatu. "Sa'adatu sa'ar mata." In ji matar Rabi'u, "Lallai wanda ya sayo ki ya yi sa'a, ke ma kin yi sa'ar samun ubangida." Sa'annan ta juya wurin mijinta ta tambaye shi, "Maigida, yanzu wane suna za mu ambaci 'yar kuyangar nan da shi?" Rabi'u ya ce shi ba shi da zabi, duk sunan da ta zaba daidai ne. Ta ce, "to, za mu kira ta da Na'imatu." Maigida ya ce, "Allah ya bar mana Na'imatu." Aka hada Na'imatu da Na'imu wuri guda ana renon su, da ma kuma sa'o'in juna ne. Yara suka tashi tare, kamar 'yan tagwaye. Suna kara girma kyawonsu na kara fitowa har ba za a iya banbance wanda ya fi wani kyau daga cikinsu ba. Har suka kai shekaru goma-goma, Na'imu na kiran Na'imatu da 'yar uwarsa, ita ma tana kiran sa da dan uwanta. Da uban ya lura da sun fara wayo, sai ya kira dansa gefe ya ce masa, "ya dana, Na'imatu ba 'yar uwarka ba ce face kuyangar da na saya maka. Don haka kada ka kara kiranta da 'yar uwarka." Na'imu ya ce, "af, to, idan haka ne sai in rike ta a matsayin matata." Ya je ya gaya wa mahaifiyarsa abin da mahaifinsa ya ce masa. Uwar ta ce, "kuyangarka ce, kana da dama ka sarrafa ta duk yadda kake so." Bayan shekara biyu, kyawon Na'imatu ya fito fili, ya kasance duk fadin garin Kufa babu kyakkyawar yarinya kamar ta. Ta hardace Alkur'ani mai girma, ta karanci wakoki kala-kala, ta gwanance wurin sarrafa kayan kida da busa har babu kamarta a birnin Kufa. Wata rana suna zaune ita da mijinta Na'imu a cikin daki, bayan sun ci sun koshi sun kuma dauraye makogwaronsu da abin sha. Sai ta jawo molo, ta gyara tsarkiyarsa ta wake wadannan baitoci: Yayin da ka kasance shugaba a gare ni, mai tsare dukkan bukatuna. Kai ne takobin da ka kare ni daga makiyana. Me zai sa in nemi kariya daga Amru ko Zaidu? Na'imu ya yi farin ciki da jin wannan waka. Ya ce da ita, "na gama ki da girman rayuwata, ya ke Na'imatu, ki kida mana tambari tare da yin waka." Ta dauki tambari, ta kida shi da hannunta ta wake wadannan baitoci, iska na kwasar zazzagar muryarta: Na rantse da mamallakin rayuwata, mai sarrafa zuciyata. Ba ni saba wa masoyina bisa son zuciya, balle magabta su gani. Ba ni kaurace wa jin dadin barci tare da masoyina Makiyana kuwa na sa tsidau bisa shimfidarsu inda za su aza hakarkarinsu. Na'imu ya yi kyekkewa da jin wannan waka, ya ce da ita, "babu shakka Allah ya yi ma ki baiwa mai yawa wadda ba duka mace take da irin ta ba." Haka dai Na'imu da Na'imatu suka ci gaba da zamansu a cikin farin ciki da kaunar juna har wata rana labarin Na'imatu ya kai ga kunnen Sarkin Kufa mai suna Hajjaj. Sarki ya ji cewa wai duk fadin Kufa babu kyakkyawar mace wadda ta iya kida da waka kamar Na'imatu kuyangar Na'imu dan Rabi'u. Shi kuwa Sarkin nan mutum ne mai son a yabe shi musamman ga manyan Sarakuna. Don haka sai ya ce a cikin ransa, "babu shakka wannan kuyanga ba ta dace da kowa ba face Sarkin Muminai Abdulmalik dan Marwan, domin na tabbata babu kamar ta a cikin fadarsa." Da ma ya san babu abin da Sarkin Muminai ke so kamar kyawawan 'yan mata wadanda suka iya waka da kida. Don haka sai ya kira wata tsohuwar kuyangarsa, gwanar iya makirci, ya umurce ta, ta tafi gidan Rabi'u dan Hatimu ta san dabarar da ta yi ta sace masa kuyangar dansa Na'imatu ba tare da kowa ya san cewa shi ya sa ta ba. Tsohuwa ta ce, wannan abu ai ya fi shan ruwa sauki a wurin ta. Washe gari sai wannan tsohuwa ta saka wasu tsummokaran tufafi na gashi, ta kawo wata tasbaha mai ‘ya’ya dubu ta rataya a wuyanta... Baharamu ya ci gaba da labarinsa, ya ce, Washe gari sai wannan tsohuwa ta saka wasu tsummokaran tufafi na gashi, ta kawo wata tasbaha mai ‘ya’ya dubu ta rataya a wuyanta. Ta sami butar karfe, ta alwala,

Chapter 11 of 14