Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
12 / 14
kirar kasar Yaman ta rike a hannunta, a daya hannun kuma ta riki sanda wadda take dogarawa. Ta nufi gidan Na'imu dan Rabi'u, tana tafe tana zikiri tana kaskantar da kanta. Tana cewa, "tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin Sarki. Yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mun shaida babu Sarki sai Allah, mun kuma shaida Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, kuma bawansa ne." Haka dai wannan tsohuwa ta tafi tana ambaton Allah a baki, dukkan mutumin da ya hadu da ita sai ya ce wannan baiwar Allah ce mai yawan ibada. Ita kuwa a cikin zuciyarta babu kome sai kissa da makirci. Ba ta gushe ba tana tafiya har ta iso gidan Na'imu dan Rabi'u daidai lokacin sallar azahar. Tana isa sai ta kwankwasa kofa, wani bawa ya leko ya tambaye ta, "me kike so, ya ke gyatuma?" Ta rauda kai ta amsa masa, "ni tsohuwa ce talaka, mai bautar Ubangiji, na ga lokacin sallar azahar ya yi. Ina so in shiga wannan gida mai albarka domin sauke farali." Bawa ya ce, "ya ke gyatuma, ki sani cewa wannan wuri ba masallaci ba ne face gidan Na'imu dan Rabi'u." Tsohuwa ta ce, "ya dana, ai babu masallacin da ya kai gidan Na'imu dan Rabi'u a wuri na. Ka sani cewa ni ina daga cikin zababbun masu bautar Ubangiji wadanda Sarkin muminai ya ajiye a fadarsa domin yi masa addu'a. Na zo wannan gari ne domin ziyara irin ta addini." Bawa dai ya yi tsaye bisa ra'ayinsa cewa ba za ta shiga ba, sai dai ta nemi masallaci ko wanii gidan na daban. Tsohuwa ta riki hannunsa tana cewa, "yanzu kamar ni da nake shiga gidan Shugaban Muminai da sauran Sarakuna, ba tare da shamaki ba, za a hana ni shiga gidan Na'imu dan Rabi'u?" Suna cikin wannan gardama sai Na'imu ya fito daga cikin gidan domin ganin abin da ke faruwa. Ya nemi bahasin gardamar tsohuwa da bawa, tsohuwa ta gaya masa bukatarta. Na'imu ya yi murmushi ya ce wa bawa ya bar ta ta shigo. Tsohuwa ta bi Na'imu a baya, tana sa masa albarka, suka wuce cikin gida inda suka tarar da Na'imatu tana zaune ta ci kwalliya, tana sheki kamar wata. Na'imatu ta gaida tsohuwa cikin ladabi. Tsohuwa ta dube ta, ta tabbatar wa kan ta cewa lalle Na'imatu yarinya ce kyakkyawa, wadda babu kamar ta a wannan zamani. Sai ta ce mata, "ya shugabata, ina horon ki da ki rika addu'ar neman tsari ga Allah madaukakin Sarki domin ya kare ku daga miyagun idanu, ke da mijinki.37 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN Tsohuwa ta bi Na'imu a baya, tana sa masa albarka, suka wuce cikin gida inda suka tarar da Na'imatu tana zaune ta ci kwalliya, tana sheki kamar wata. Na'imatu ta gaida tsohuwa cikin ladabi. Tsohuwa ta dube ta, ta tabbatar wa kan ta cewa lalle Na'imatu yarinya ce kyakkyawa, wadda babu kamar ta a wannan zamani. Sai ta ce mata, "ya shugabata, ina horon ki da ki rika addu'ar neman tsari ga Allah madaukakin Sarki domin ya kare ku daga miyagun idanu, ke da mijinki, miyagun idanu, ke da mijinki, saboda baiwar da ya yi muku ta kyau." Daga nan ta nemi ruwa ta yi alwala, aka kawo mata shimfidar salla. Ta tsayu a kan shimfida, ta kabbara salla. Ba ta gushe ba tana salla har sai da rana ta fadi, duhu ya maye gurbin ta. Bayan ta sallame tana shirin mikewa domin kabbara wata sallar, sai Na'imatu ta ce mata, "haba inna, ki tsaya ki huta mana ko kafafunki sa dan sarara." Tshohuwa ta ce, "ya shugabata, ina maganar hutu ga bawa mai neman tsira gobe kiyama. Wanda duk bai nemi lahirarsa ba a lokacin rayuwarsa hakika ya tabe." Na'imatu ta tashi ta kawo mata abinci da abin sha. Tsohuwa ta karba ta yi godiya, ta ce, "madalla da samun abincin bude baki." Na'imatu ta tambaye ta ta yi azumi ne? Tsohuwa ta amsa mata cewa, ai ita kullum azumi take yi. Ta jawo mata aya ta saba'in a cikin Suratul Furkan: "Sai fa wadanda suka tuba suka ba da gaskiya, sa'annan suka aikata aiki na kwarai. Wadannan, Allah zai juyar da miyagun ayyukansu zuwa ayyuka na kwarai. Domin kuwa Allah mai yawan gafara ne, mai yawan jin kai ne." Na'imatu ta zauna suka ci gaba da mayar da zance, ita da tsohuwa, zuwa wani lokaci. Daga nan sai ta ce wa mijinta, Na'imu, "ya shugabana, ka roki wannan tsohuwa ta kwana wurin mu ko ma sami albarkacinta." Na'imu ya lallashi tsohuwa, ta amince da kyar cewa za ta kwana amma da gari ya waye za ta ci gaba. Na'imu ya sa aka shirya mata wani daki wanda za ta kwana a ciki, ya ce kada wanda ya je ya dame ta a yayin da take ibadarta, watakila wannan zuwa nata ya zama alheri a gare su. Tsohuwa ta shige daki. Sai ta kasance wani lokaci ta yi ta salla, wani lokaci kuma ta zauna ta yi ta karatun Alkur'ani. Haka ta kwana har gari ya waye. Yayin nan ta je wurin Na'imu da Na'imatu ta yi musu barka da kwana. Ta ce musu, "ina rokon Allah ya tsare ku da tsarewarsa." Suka tambaye ta ba dai tafiya za ta yi ba tun da sassafe haka? Ta ce musu ita kam ta yi harama. Suka lallashe ta a kan ta kara kwana, amma ta ce a'a, sai dai idan ta kuma dawowa wani lokaci. Haka suka yi sallama, ba tare da sun so rabuwa da ita ba, har Na'imatu na fitar da kwalla. Bayan tsohuwa ta fita daga gidan Na'imu dan Rabi'u sai ta nufi gidan Hajjaj, Sarkin Kufa. Da Sarki ya gan ta sai ya tambaye ta, "ina labari?" Ta amsa masa, "na sadu da kuyangar, hakika babu wata mace da ta kai ta kyau a wannan zamani." "To, za ki iya dabarar da kika sato ta?" Sarki ya tambaya. "Hakika idan kika yi mini wannan kokari zan yi miki kyauta mai tsoka." "Allah ya ba ka nasara." Tsohuwa ta karkace kai. "Ina so ka ba ni akalla wata daya, zan kawo maka ita har gida." Sarki ya ce, "je ki an ba ki." Daga ranar nan sai tsohuwa ta kasance tana ziyartar Na'imu da Na'imatu, wani lokaci ta tafi da safe, wani lokaci kuma ta tafi gidan da yamma.. Suka rika kyautata mata, suna girmama ta matuka saboda yawan ibadarta. Wata rana ta tafi gidan sai ta tarar da Na'imatu kawai a gidan. Suka zauna suka yi ta hira, da za ta tafi sai ta ce wa Na'imatu, "shugabata, ni kam kullum na je dakin ibada nakan rika yi muku addu'a ke da maigidanki, nakan kuma roki manyan waliyyan da muke ibada tare su yi muku addu'a. Ina ma wata rana za ki tafi tare da ni wannan dakin ibada domin in hada ki da manyan waliyyan Allah ko kya sami tubarrakinsu." Na'imatu ta ce, "ai kuwa ina so wata rana mu tafi tare. Ni dai ba abin da nake so kamar bayin Allah masu yawan ibada." Tsohuwa ta ce, "ki nemi izini wurin mijinki, ko wurin uwar mijinki." Na'imatu ta tashi ta tafi bangaren mahaifiyar Na'imu domin ta nemi izini wai ta bar ta wata rana ta bi wannan tsohuwa. Suna cikin haka sai ga Na'imu ya shigo, tsohuwa ta gai da shi tana sa masa albarka. Daga nan ta fita ta nufi gida. Washe gari tsohuwa ta dawo, ba ta iske Na'imu ba. Ta ce da Na'imatu, "jiya mun kwana muna yi muku addu'a har sai da manyan waliyya suka tambaye ni wai wace ce wannan da kike yawan yi wa addu'a? Na amsa musu cewa yau zan kawo ki wurin su su gan ki." Tsohuwa ta ci gaba da cewa, "tashi maza yanzu ki shirya mu tafi, kafin mai gidan ki ya dawo mu tafi mun dawo, domin ba dadewa za mu yi ba." Na'imatu ta tafi wurin mahaifiyar Na'imu ta durkusa gabanta, ta ce, "ina rokon ki don Allah, ya shugabata, ki yi mini izini in tafi tare da wannan tsohuwa wurin waliyyan Allah. Za mu dawo da sauri kafin mijina ya dawo." Uwar Na'imu ta ce, "ni ina ji miki tsoron mijinki ya dawo bai iske ki ba." Na'imatu ta ce, "na rantse da Allah ba tsayawa za mu yi ba. Za mu dawo tun kafin ya dawo." Tsohuwa ta tsoma bakinta, "ai ko zaunawa ba za mu yi ba. Daga tsaye za su gaisa sa'annan mu juyo da sauri." Mahaifiyar Na'imu ta ce su tafi, amma kada su bari Na'imu ya riga su dawowa. Tsohuwa ta riki Na'imatu ta fita da ita, bayan ta dabaibaye ta da kissa, ta nufi fadar Sarki da ita. Da zuwa ta kai ta wani daki a cikin fadar ta kulle, ta tafi ta fada wa Sarki. Sarki ya ga Na'imatu, ya tabbatar wa kansa lalle ba karya aka yi ba, da aka ce ta fi dukkan matan zamaninta kyau. Yayin da Na'imatu ta ga Sarki ya shiga wurin ta, duk da yake ba ta san ko wane ne shi ba, sai ta rufe fuskarta da mayafi. Bayan Sarki ya kare mata kallo, sai ya kira wani bafadensa ya umurce shi ya hada dawaki hamsin tare da mahayansu zai aike shi zuwa Damashka wurin Halifa Abdulmalik dan Marwan domin ya kai masa kyautar wata kyakkyawar kuyanga. Ya kuma umurci bafaden da cewa ya aza Na'matu bisa rakuma ta musamman da aka kawata da ado. Ya kawo takarda ya ba bafaden, ya ce, "ka ba Sarkin Muminai wannan takarda, sa'annan ka komo mini da jawabinta." Bafade ya tafi ya shirya dukkan abin da Sarki ya umurta. Aka fito da Na'imatu tana kuka, domin rabuwa da Na'imu, aka aza ta bisa rakuma, aka nufi Damashka da ita. Suka yi ta tafiya, dare da rana, har suka isa birnin Damashka. Bafaden Sarkin Kufa ya nemi iso wurin Halifa, aka yi masa. Bayan ya yi gaisuwa, ya kawo sakon Sarkin Kufa da Na'imatu da takarda, ya ba Halifa. Bayan Halifa ya karanta takarda, sai ya umurci bayinsa su shirya wa Na'imatu dakin da za ta zauna a cikin gidansa. Halifa ya shiga wurin uwargidansa ya ce mata, "Sarkin Kufa ya aiko mini da kyautar kyakkyawar kuyanga, daya daga cikin zuri'ar Sarakunan Kufa na dauri, wadda ya saya dinari dubu goma." Matar ta ce da shi" "madalla da wannan kokari na Sarkin Kufa. Ya kamata Halifa ya ba shi tukuici mai tsoka." To, ashe wannan magana da Halifa ke yi da uwargidansa duka a cikin kunnen wata kanwarsa take shiga. Nan da nan sai wannan kanwa ta Halifa ta sulale ta nufi dakin da aka shirya wa Na'imatu domin ta gan ta.Yayin da ta ga Na'imatu da irin kyawon da Allah ya hore mata, sai ta ce, "hakika wanda duk ya same ki a gidansa ya yi farin ciki. Kamata ya yi a saye ki dinari dubu dari maimakon dinari dubu goma." Na'imatu ta dube ta ta ce, "ya ke wannan mai annurin fuska, shin fadar wane Sarki ce wannan?" "Nan birnin Damashka ne. Kuma kina cikin fadar dan uwana ne, Halifa Abdulmalik dan Marwan, Shugaban muminai." In ji kanwar Halifa. "Ke duk ba ki san da wannan ba?" "Na rantse da Allah ban san inda nake ba, ya shugabata." "To, amma shi wanda ya saye ki bai fada maki cewa zai turo ki nan ba, wurin Shugaban Muminai ba?" Yayin da Na'imatu ta ji haka, sai hawaye suka zubo daga idanunta, ta ce a cikin ranta, "wallahi an yaudare ni, idan ma na fada musu gaskiya ba yarda za su yi ba. Na damka al'amarina ga Allah Madaukakin Sarki zuwa ranar da gaskiya za ta bayyana." Sai ta dukar da kan ta kasa cikin tunani. Kanwar Halifa ta lura da fuskar Na'imatu ta dan yi duhu saboda tafiya da kuma zafin rana. Saboda haka sai ta tashi ta fita domin ta ba ta wuri ta dan sarara. Washe gari kanwar Halifa ta zo wa Na'imatu da tufafi masu kyau, na alfarma, da sarka ta zinariya. Bayan ta sa Na'imatu ta yi wanka, sai ta ba ta kayan da ta zo mata da su ta sanya. Kayan kuwa suka yi mata kyau kamar an gwada da jikinta, ta kawo wani mayafi ta rufe rabin fuskarta. Yayin nan sai ga Halifa ya shigo wurin su, ya zauna kusa ga Na'imatu. Kanwarsa ta dube shi ta ce, "ya dan uwana, ka yi duba zuwa wannan kuyanga, wadda Allah ya hore wa dukkan nau'i na kyau." Halifa ya umurci Na'imatu ta yaye mayafin da ta rufe fuskarta da shi domin ya ga fuskarta. Na'imatu ta ki yaye mayafin, maimakon haka ma sai ta sa hannunta ta dafe shi, gudun kada Halifa ya ce zai yaye da kansa. A wannan rana dai Halifa bai ga fuskar Na'imatu ba, sai wuyan hannunta kawai ya gani, wanda hakan ya rura wutar begenta a cikin zuciyarsa. Ya ce da 'yar uwarsa, ta yi kokari ta lallasar masa ita kafin kwana uku, lokacin da zai dawo dakinta. Ya tashi ya fita. Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ38 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN Halifa ya umurci Na'imatu ta yaye mayafin da ta rufe fuskarta da shi domin ya ga fuskarta. Na'imatu ta ki yaye mayafin, maimakon haka ma sai ta sa hannunta ta dafe shi, gudun kada Halifa ya ce zai yaye da kansa. A wannan rana dai Halifa bai ga fuskar Na'imatu ba, sai wuyan hannunta kawai ya gani, wanda hakan ya rura wutar begenta a cikin zuciyarsa. Ya ce da 'yar uwarsa, ta yi kokari ta lallasar masa ita kafin kwana uku, lokacin da zai dawo dakinta. Ya tashi ya fita. Na'imatu kuwa sai ta kasance cikin damuwa da bakin ciki mai yawa saboda rabuwa da mijinta Na'imu dan Rabi'u. Wannan abu sai ya zamar mata ciwo, ta kasance ba ta ci ba ta sha, sai kuka. Cikin 'yan kwanaki kadan ta rame, fuskarta ta komade. Da Halifa ya ga haka sai hankalinsa ya tashi, ya sa aka nemo masa masu magani da malamai, suka yi ta ba ta sakesaki da sayyu, malamai kuma suka dukufa kan addu'a, amma duk a banza, ciwo sai gaba-gaba yake yi, kamar iska na hura wuta. Wannan shi ne al'amarinta. Al'amarin Na'imu kuwa, lokacin da ya dawo gida sai ya zauna bisa shimfida. Ya yi kira, "ina kike ne Na'imatu." Bai ji an amsa masa ba. Sai ya mike bisa dugadugansa, ya kara kwala kira da karfi, amma babu wanda ya amsa masa, hatta mahaifiyarsa saboda tana jin tsoron abin da zai faru. Na'imu ya nufi dakin mahaifiyarsa, ya iske ta zaune, ta yi tagumi. Ya tambaye ta, "ya mahaifiyata, ina Na'imatu ta shiga ne?" "Ya dana, sun fita tare da tsohuwa mai yawan ibada domin su ziyarci manyan waliyyan Allah masu bauta." "Tsawon wane lokaci suka tafi?" "Tun da sassafe suka tafi, bayan ka fita." Na'imu ya yi jugum yana tunani, "me ya sa kika bar ta ta fita tare da wannan tsohuwa?" Mahaifiyar Na'imu ta amsa masa, "ita ce ta dame ni da in bar ta su tafi, ta ce mini ba dadewa za su yi ba." Na'imu ya ce, "babu tsimi babu dabara face daga Allah Madaukakin Sarki." Daga nan ya fita daga wurin mahaifiyarsa, zuciyarsa cike da damuwa, bai zame ko'ina ba sai gidan Sarkin Dogarai. Na'imu ya ce masa, "kuna aikin me a cikin garin nan har aka sace mini kuyanga? Babu makawa in yi karar ka gun Halifa Shugaban Muminai." Sarkin Dogarai ya ce, "wa ya sace maka kuyanga?" Na'imu ya ce, "wata tsohuwa wadda ta sa tufafin gashi, ta rataya tasbaha mai ‘ya’ya dubu a wuyanta. Tana yawo da sanda da kuma butar karfe a hannunta." Yayin da Sarkin Dogarai ya ji kamannun wannan tsohuwa, sai ya shaida ta a matsayin tsohuwar kuyangar Hajjaj, Sarkin Kufa, domin cikin 'yan kwanakin da suka wuce a cikin wannan shiga yake ganin ta. Don haka sai ya tabbatar a cikin ransa cewa Hajjaj din ne ya sa wannan tsohuwa ta sace kuyangar. Sai ya ce da Na'imu, "ka kawo mini wannan tsohuwa a gabana, ni kuwa zan tursasa ta ta kawo maka kuyangarka." Na'imu ya ce, "to, yaya za a yi na kawo maka ita, tunda ban san ta ba, ban kuma san gidanta ba. Ban da Allah, wa ya san abin da yake boye?" "Wannan haka yake, Allah kadai ya san abin da yake boye," in ji Sarkin Dogarai. "Babu makawa in je wurin Hajjaj in kai kararka saboda sakacinka na rashin duba gari har a sace mutum ba ka kama barawon ba." Sarkin Dogarai, wanda ya fara harzuka, ya ce masa ya tafi duk inda zai kai kararsa ya kai. To, dama mahaifin Na'imu yana daya daga cikin 'yan majalisar Sarkin Kufa, don haka ne Sarki ya san Na'imu sosai. Da Na'imu ya bar gidan Sarkin Dogarai sai ya nufi fada. Aka yi masa iso, Sarki ya tambaye shi abin da ke tafe da shi. Na'imu ya kwashe abin da ke tafe da shi ya gaya wa Hajjaj, nan da nan shi kuma ya ce a kira masa Sarkin Dogarai. Yayin da Sarkin Dogarai ya zo, sai ya fadi ya yi gaisuwa, Sarki ya umurce shi ya nemo tsohuwar da ta sace kuyangar Na'imu dan Rabi'u, amma sai ya kyabci Sarkin Dogarai da ido, domin ya san cewa Sarkin Dogarai ya san wannan tsohuwa kuyangarsa ce. Sarkin Dogarai ya dukar da kai ya ce, "Allah ya ba ka nasara, wa ya san abin da ke boye ban da Allah Madaukakin Sarki?" Hajjaj ya ce, "ka tashi dogarai masu dawaki su shiga kowane lungu da sako na wannan birni su duba ta, har bayan gari, da kauyukan da ke kewaye da wannan birni duka su tafi su duba ta." Sarki, Hajjaj Sarkin kufa ya ce da Sarkin Dogarai, "ka tashi dogarai, masu dawaki, su shiga kowane lungu da sako na wannan birni su duba ta, har bayan gari, da kauyukan da ke kewaye da wannan birni duka su tafi su duba ta." Daga nan sai ya juya wurin Na'imu ya ce masa, "idan ba a gane ta ba, zan ba ka kuyangi goma daga gidana, da kuma wasu kuyangi goma daga gidan Sarkin Dogarai, maimakon taka kuyangar da aka sace." Ya yi tsawa ga Sarkin Dogarai, "maza ka nemo masa kuyangarsa." Na'imu ya koma gida cike da bakin cikin rabuwa da Na'imatu. A wannan lokaci kuwa shekarunsa goma sha hudu, amma babu kwarar gashi ko daya a habarsa. Da dare mahaifinsa ya shigo gida, ya ce masa, "babu makawa Hajjaj ne ya shirya kutungwilar da aka sace maka kuyanga, amma ka yi hakuri watakila Allah ya sake hada ka da ita wata rana." Tun daga wannan rana sai Na'imu ya shige dakinsa ya yi ta kuka, ya daina zuwa ko'ina. Idan mahaifiyarsa ta kawo masa abinci sai ya ci kadan ya ture akushin gefe. Nan take ya kwanta rashin lafiya mai tsanani, har ya kasance sai dai a kwantar a tayar. Aka yi magani har aka gaji amma bai warke ba. Ya zauna cikin wannan hali tswon wata uku har iyayensa sun fara debe tsammani. Rannan kwaram, sai ga wani bakon mai magani ya fado garin daga Farisa. Yayin da mahaifin Na'imu ya ji labarin zuwan wannan bakon Boka, kuma ya ji cewa shahararre ne, babu maganin cutar da ba ya da shi, sai fa ta ajali. Nan da nan ya tafi da shi zuwa ga Na'imu. Mai magani ya zauna kusa ga Na'imu, ya riki hannusa, ya yi duba a cikin tafin hannun Na'imu, ya dade yana nazarinsa, sa'annan ya dubi fuskar Na'imu. Daga nan sai ya yi dariya, ya dubi Rabi'u dan Na'imu ya ce, "cutar danka tana tattare a cikin zuciyarsa." Rabi'u ya ce, "Ka yi gaskiya, ya kai wannan mai magani. Ina so ka yi amfani da saninka da kuma fasaharka, ka warware mini dukan cutar da ke damun dana. Kada ka boye mini kome." Boka ya ce, "danka ya kamu da ciwon son wata yarinya wadda a halin yanzu ko dai tana Basara ko kuma tana Damashka. Babu wani magani da zai warkar da shi daga wannan cuta face haduwa da wannan yarinya da yake so." "Idan kuwa ka yi kokarin hada su da juna," in ji Rabi'u, "zan ba ka dukkan abin da ka nema gare ni. Zan yalwata ka da dukiya mai yawa tsawon rayuwarka." Boka ya ce, "wannan abu ne mai sauki gare ni." Ya juya wurin Na'imu da ke kwance kamar ruwa, ya ce masa, "karfafa zuciyarka dan samari, idan Allah ya so bukatarka za ta biya. Zan hada ka da wadda kake so." Ya ce wa Rabi'u ya ba shi dinari dubu hudu domin zai tafi Damashka tare da Na'imu, kuma ba za su dawo ba sai tare da kuyanga Na'imatu. Rabi'u ya kawo kudi ya ba shi. Mai magani ya tambayi Na'imu sunansa, ya gaya masa. Sai ya ce, "ya Na'imu, tashi zaune ka ci abinci ka kuma sha abin sha, ka karfafa zuciyarka, domin yau din nan za mu tashi zuwa Damashka wurin masoyiyarka. Ba za mu dawo ba sai tare da ita." Suka rika shi ya tashi zaune, aka kawo masa abinci da abin sha. Ya ci, ya sha ya koshi, karfin jikinsa ya dan dawo. Rabi'u ya shirya musu dawaki da rakuma domin tafiya, ya kawo dinari dubu goma ya ba mai magani. Na'imu ya yi sallama da mahaifinsa da mahaifiyarsa, Rabi'u ya yi musu addu'ar samun nasara. Boka da Na'imu suka hau dabbobinsu suka mika da tafiya, ba su tsaya ko'ina ba sai garin Aliffo. Suka dan tambayi labarin Na'imatu, da ba su sami wani abin kamawa ba sai suka ci gaba da tafiya har suka isa Damashka. Da suka kwana uku a cikin Damashka, sai mai magani ya kama hayar rumfa a cikin kasuwa. Ya cika ta da kayayyakin magani iri-iri. Ya sayo tasoshi na azurfa da zinariya, a cikin kowace tasa ya zuba nau'in magani daban daban. Ya cika wata tasa da sakesaki, wata kuma saiwowi ne cikin ta, wata kuma ganyaye ne ciki. Ga kuma goruna da battoci, kowace dauke da nau'in magani na shafawa da na turarawa. Ya sa tufafinsa irin na masu magani, ya rike wani abu a hannunsa wanda yake auna marasa lafiya da shi. Ya sayo wa Na'imu tufafi na siliki, irin na bokaye. Bayan ya sa tufafin, Boka ya yi masa damara da wani kyalle wanda a tsakiyarsa aka sa masa wani maballi na zinariya. Ya zaunar da shi kusa gare shi. Mutane suka yi ta mamakin irin kyawun da Allah ya hore wa Na'imu. Mai magani ya ce da Na'imu, "daga yanzu zan rika kiran ka da dana, kai kuma ka rika amsa mini da baba." Na'imu ya ce ya ji, ya aminta. Suka zauna a haka, mai magani yana kiran Na'imu da dansa, shi kuma yana amsa masa da mahaifinsa. Kuma duk lokacin da zai yi masa magana sai ya yi masa da Farisanci, Allah ya sa shi ma Na'imu ya iya Farisancin, sai ya mayar masa da jawabi da Farisanci. Mutane suka rika zuwa suna karbar magani, wasu kuma sukan zo da fitsari ko bayan garin mara lafiya. Shi kuma mai magani zai karba ya auna, ya fadi irin cutar da ke damun mai wannan fitsari ko bayan gari, sa'annan ya kawo magani ya bayar. Cikin ikon Allah kuwa, duk wanda ya karbi maganin sai ya sami sauki. Nan da nan sai labarinsa ya karade ko'ina a cikin birnin Damashka da kewaye. Wata rana suna zaune a cikin rumfarsu sai suka ga wata tsohuwa ta nufo rumfar tana haye bisa jaki. Da ta zo gaban rumfar sai ta ja ta tsaya, ta sa hannun ta yafuto mai magani. Ita wannan tsohuwa da ganin ta za a gane ta fito ne daga babban gida, domin kuwa tana sanye da tufafi na alfarma, wadanda aka saka da lu'ulu'u, aka yi musu kwalliya da zinariya da azurfa. Mai magani ya tashi ya je kusa gare ta, ita kuma tana zaune bisa jaki. Ta mika masa hannu ta ce,"taimaka mini in sauko daga kan jakin nan." Mai magani ya rike hannunta, ta sauko daga bisa jaki. Tsohuwa ta tambaye shi, "kai ne Bafarishen mai maganin nan da ya zo daga Kufa?" Ya amsa mata, "na'am." Daga nan ta zaro wata 'yar batta karama, cike da fitsari, ta mika masa, "ina da wata 'ya tawa da take kwance babu lafiya." Mai magani ya karbi batta, ya yi nazarinta cikin dan kankanin lokaci. Ya dubi tsohuwa, "gaya mini sunan wannan diya taki, domin in buga taurari da sunan nata in ga lokacin da ya fi dacewa gare ta, ta sha magani."39 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN mai magani ya karbi batta daga hannun tsohuwa, ya yi nazarinta cikin dan kankanin lokaci. Ya dube ta, "gaya mini sunan wannan diya taki, domin in buga taurari da sunan nata in ga lokacin da ya fi dacewa gare ta, ta sha magani." "Ya kai wannan Mai magani, sunanta Na'imatu." Tsohuwa ta amsa masa. Mai magani ya tsuguna, ya share kasa. Ya shiga yin wadansu zane-zane, idan ya yi sai ya share ya kara zana wasu. Can sai ya dago kansa ya ce, "sunanta kadai ba zai wadatar ba, sai kin gaya mini sunan garinta na ainahi, domin na ga kamar ba a wannan gari aka haife ta ba. Sa'annan kuma ki gaya mini yawan shekarunta a duniya." Tsohuwa ta ce, "shekarunta goma sha hudu, kuma an haife ta a garin Kufa." Mai magani ya kara dukawa ga zane-zanensa, can kuma sai ya tambayi Tsohuwa, "kin ce a Kufa aka haife ta, to, yaushe ta zo wannan birni?" Tsohuwa ta amsa masa, " 'yan watanni kadan da suka wuce." Duk zancen nan da Mai magani ke yi da tsohuwa Na'imu na sauraren su. Yayin da ya ji an ambaci sunan kuyangarsa Na'imatu, sai ya yi kamar ya some don murna. Daga nan mai magani ya kara dukawa ga zane- zane bisa kasa yana sharewa. Zuwa wani dan lokaci ya dago kansa, ya ce wa tsohuwa, abu kaza da abu kaza shi ne maganin da za a hada mata, ta ba 'yarta. Tsohuwa ta yi farin ciki, ta mika masa dinari goma ta ce, "Allah ya yi maka albarka, ya kai mai magani. Yi sauri ka hada mini, ko na koma gida da wuri, in kai mata." Mai magani ya juya wurin Na'imu ya fada masa kalar maganin da zai hada wa tsohuwa. Tsohuwa ta dubi Na'imu, wanda tun lokacin da ta shigo rumfar ba ta lura da yana wurin ba, fuskarta ta juye zuwa tsananin mamaki. Ta ce, "Wallahi wannan saurayi ya yi kama da ita, kamar an tsaga kara." Ta tambayi mai magani, Na'imu dansa ne ko kuwa bawansa ne? Ya amsa mata da cewa dansa ne. Na'imu ya shirya wa tsohuwa magani, ya saka shi a cikin wani dan karamar batta, girman tafin hannu. Ya dauko takarda da alkalami ya rubuta wannan sako: "Idan Na'imatu ta ni'imta ni daga gani na idonta, babu mai arzurta misalin arzikina. Ba kwa kamanta kyawonta da kyawona ba, domin sun ce an bayar a gare ta kyawo ashirin tamkar nata." Ya nade takarda ya sa ta cikin batta tare da maganin, ya rufe bakin battar. Bisa murfin batta kuma ya rubuta sunansa da haruffan Kufa, ni ne Na'imu dan Rabi'u mutumin Kufa. Ya mika wa tsohuwa batta, ta karba ta yi sallama da su. Ta hau jakinta ta koma fadar Halifa. Da ta

Chapter 12 of 14