Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 14
jirgi da shi, ba tare da ya ce masa uffan ba. Ya tura keyarsa zuwa cikin jirgi. Madugu ya kwance jirgi, ya tuka suka tafi. Mamaki ya ishi Kamaruzzaman har ya kasa hakuri ya tambayi Madugun jirgi dalilin dawowarsa ya dauke shi. Madugu ya harare shi, ya ce, "Ashe kyawun nan naka kyawun banza ne? Sarkin Labunus ya fada mana cewa kai barawo ne, ka taba sace masa wasu kaya lokacin da ka taba kai 'ya'yan zaitun a kasarsa. Shi ne ya ba ni umurnin in komo in tafi da kai wurinsa." Yayin da Kamaruzzaman ya ji wannan jawabi na Madugu sai ya ce, "Na rantse da Allah, ban ko san hanyar birnin Labunus ba, balle har in shiga cikinsa." Madugu dai ya kyale shi bai tanka masa ba, domin yana cike da hushin wannan tafiya. Haka suka ci gaba da keta ruwa, kwana da kwanaki har Allah ya nufe su da shiga birnin Labunus. Da zuwansu sai Madugu ya ja Kamaruzzaman zuwa fada wurin Badura. Ya kuwa sami ana fadanci, Badura na kan karagar mulki, ta sha rawani fuskarta a rufe, kamar yadda takan yi idan za ta fita a cikin mutane. Ta dubi Kamaruzzaman tare da Madugu, nan take ta shaida Kamaruzzaman, kodayake ya rame, kuma ya yi baki. Ta kawo dinari dubu goma ta ba Madugun jirgi ta sallame shi, ya tafi yana godiya. Ta juya ga bayi ta ce su kai Kamaruzzaman gidan wanka, idan ya gama wanka su dawo mata da shi. Daga nan ta tashi ta shiga gida wurin Hayatunnufusi, ta fada mata cewa an dawo da Kamaruzzaman, sa'annan kuma ta ce, "Ina so ki kame bakinki, har sai na aikata wani abin mamaki, wanda za a rubuta shi a takarda ana karanta shi ga Sarakuna da talakawa masu zuwa bayanmu, tsawon zamani." Suna cikin wannan magana sai ga bayi sun zo, suka shaida wa Badura cewa, Kamaruzzaman ya fito daga wanka. Ta umurce su da su tufatar da shi tufafi masu kyau na alfarma, irin tufafin Sarakuna. Bayi suka tafi suka aikata tamkar yadda aka umurce su. Yayin nan Badura ta koma fada, ta tarar da bayi tare da Kamaruzzaman suna jiran zuwanta. Bayan ta zauna kan karagar mulki, ta dubi Kamaruzzaman ta ga ya komo cikin hayyacinsa, yana haske yana kyalli tamkar wata dan daren goma sha hudu. Sha'awarta game da shi ta motsa, amma sai ta danne zuciyarta, ta kudiri aikata abin da ta yi nufi. A wannan rana ta nada shi daya daga cikin manyan 'yan majalisarta, ta ba shi kyuatar bayi da kuyangi da dawaki da rakuma, da alfadarai, da kudi tsaba, masu yawa ta kuma ba shi gida. Sai ya kasance kullum Kamaruzzaman yakan fita fada ya zauna cikin 'yan majalisa ana fadanci, amma bai taba gane cewa Badura mace ce ba, balle har ya shaida ta. Ita kuwa kullum ya zo sai ta yi masa kyauta ta dukiya mai dimbin yawa, kuma tana girmama shi fiye da sauran 'yan majalisarta. Har fadawa dai suka gane cewa Kamaruzzaman dan gaban goshin Sarki ne, sai suka shiga girmama shi. Badura ta ci gaba da yi masa kyauta kullum ya zo fada, har ta kusa ba shi dukkan dukiyar birnin Labunus. Wannan abu sai ya daure wa Kamaruzzaman kai, ya ce a cikin ransa, "Kai! Ruwa fa ba ya tsami banza, wannan kyauta da Sarki ke yi mini kullum akwai alamun lauje cikin nadi. Babu makawa akwai wani abu da Sarkin nan yake nufi game da ni. Babu abin da ya fi zama alheri a gare ni face in bar masa kasarsa." Ran nan bayan an tashi daga fada sai Kamaruzzaman ya tari Badura kafin ta shiga gida. Ya durkusa a gabanta ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ni dai har yanzu hankalina bai kwanta ba da irin wadannan kyaututtuka da kake yi mini kullum. Idan ka yarda, Allah ya ba ka nasara, ina so ka karbe dukan abin da ka ba ni, ba na son ko allura, sa'annan ka bar ni in wuce gaba." Badura ta yi murmushi, ta ce, "Don me kake so ka bar mu, ka wuce zuwa wani birni? Bayan a nan kana cikin jin dadi da wadata, da kuma daukakar daraja?" "Ya Sarki, lalle wannan jin dadi da wadata da nake ciki, idan babu wani kwakkwaran dalilin da ya sa ake yi mini su, to, wannan abu shi ne abin mamaki, mafi zama mamaki." In ji Kamaruzzaman, ya ci gaba da cewa, "Ka daukaka darajata fiye da ta sauran 'yan masalisarka wadanda na iske tare da kai, wadanda kuma suke dattijai masu hankali, amma ni ba kowa ba ne face yaro a cikinsu, amma duk da haka, ka daukaka ni fiye da su." Badura ta yi wani boyayyen murmushi, fuskarta na sunke a cikin rawani, sa'annan ta dubi Kamaruzzaman ta ce, "Lalle kana da gaskiya, dan samari. Ba kome ya sa na daukaka darajarka ba, kuma nake ta yi maka kyaututtuka, face saboda kyawunka, da kuma fuskarka mai hasken da ke kunyatar da hasken wata. Tun lokacin da na dora idona a kanka, na ji sha'awarka ta soki zuciyata. Idan za ka yarda in gusar da sha'awata a kanka, to, da kuwa na ba ka dukkan abin da kake so na dukiya, kuma in daukaka darajarka zuwa Wazirina, duk da karancin shekarunka. Kodayake ni ma, ba girme maka na yi a shekaru ba, amma duk da haka jama'a suka amince mini na zama Sarkinsu. Don haka ba abin mamaki ba ne a cikin wannan zamani idan yara sun karbe ragamar mulki daga hannun tsofaffi. Wallahi ya cika mai hikima, wannan mawakin da yake cewa:.. "Kai ka ce zamaninmu muna daga mutanen Ludu, suna da begen juna a cikin kirazansu musamman na kananan yara." Yayin da Kamaruzzaman ya ji zancen Badura, shi yana dauka a cikin ransa Sarki ne namiji mai auren 'yar Sarki Armanus. Sai ya dukar da kansa kasa don kunya da takaici, nan take kuma kumatunsa suka yi ja, kamar wuta mai huruwa, don fushi. Ya dago kansa ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ni kam ba na bukatar duk wani matsayi da za ka nada ni domin dai in yarda da wannan bukata taka ta saba wa Allah. Na fi son in mutu cikin talauci da bautar Ubangiji da in mutu cikin dukiya da sabon Ubangiji." ............ Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan akasuwa 26 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN Da Kamaruzzaman ya ji haka, sai hankalinsa ya tashi, fuskarsa ta yi duhu. Ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ka tuna fa kana da kyakkyawar mata a gida, bayan ita kuma kana da kyawawan kuyangi masu yawa, wadanda babu tamkarsu a fagen kyau. To, don me za ka hadiye mini miyau, ka ce dole sai ni? Ka karkata zuwa gare su mana, ka sami biyan bukatarka." Badura ta ce, "wannan gaskiya ne, amma babu daya daga cikinsu da za ta iya kawar mini da sha'awarka, ni kai nake sha'awa. Ko ba ka ji abin da aka fada ba ne? Abin da zuciya ke so ai shi ake ba ta. Don haka, ka daina wani muku-muku, ka saki jikinka kawai ka biya mini da bukata." Da dai Kamaruzzaman ya ga cewa, idanun Sarkin nan sun rufe bisa aikata abin da ya yi nufi, kuma babu makawa sai ya aikata haka, sai ya ce, "ya Sarki, ina rokonka alfarma daya." "Wace alfarma ce?" Badura ta tambaya. Kamaruzzaman ya amsa mata, "Allah ya ba ka nasara, tun da har idonka ya rufe bisa aikata wannan laifi mai girma tare da ni, to, ka yi mini alkawarin cewa idan ka aikata shi sau daya a gare ni, ba za ka kara nema na da wannan zance ba. Domin ni, ina jin tsoron fushin Ubangiji, wanda yake yi ga duk masu aikata irin wannan aiki." "Af, in don wannan, to, na yi alkawari ba zan kara tonar ka da wannan magana ba idan ka ba ni hadin kai har na biya bukatata yanzu. Daga nan sai mu roki Allah gafara, domin shi, mai yawan gafara ne kuma mai yawan jin kai. Yakan sa bayinsa Aljanna ne ba domin yawan ibadarsu ba, sai don rahamarsa kadai." Bayan ya sa ta rantse da Ubangijin talikai, wanda babu wani ubangiji bayan shi, a kan cewa za ta aikata wannan abu a gare shi sau daya tak, bayan shi ba za ta kara neman sa da maganar ba. Sai ya bi ta zuwa wani daki a cikin gidan. Ita kuma tana cewa, "babu tsimi babu dabara face daga Allah madaukakin Sarki, hakika wannan abu kadararren al'amari ne, daga mai ikon kaddara kome." Bayan sun shiga cikin daki, ta sa Kamaruzzaman ya cire wandonsa, duk kunya ta rufe shi, sai hawaye ke zuba daga idanunsa saboda tsoron irin girman laifin da suke shirin aikatawa. Ita kuwa Badura babu abin da take yi a cikin ranta sai dariya, amma ta kanne ta ki bayyanar da dariyar tata. Ta umurce shi da kwantawa bisa shimfida, tana cewa, "daga wannan dare ba zan kara nemanka da aikata wannan aiki ba sai idan kai ne ka nema. Amma ina tabbatar maka cewa za ka ji dadin wannan abu da za mu yi yanzu, har ba za ka taba mantawa da shi ba, tsawon rayuwarka." Daga nan ta rungume shi ta bayansa, tana shafa kirjinsa da hannayenta. Ta juyo da shi, suka yi gaba da gaba. Ta ce masa, "ka sanya hannunka karkashin cinyoyina ka tashi liman da almajiransa biyu da ke barci, su farka su soma ibada." Kamaruzzaman ya ce, "ya Sarki, ni ban saba da aikata wannan aiki ba." Badura ta ce, "babu makawa ka yi abin da na umurce ka, domin zai amfanar da kai matuka." Kamaruzzaman ya fito da hannunsa ya tura a cikin wandonta, hannun yana rawa kamar wanda zai taba garwashin wuta, ya fara shafa tsakanin cinyoyinta. Ya ji su da sanyi kamar raba, ga kuma taushi da laushi kamar audugar rimi, sai ya ji dadi a cikin ransa. Ya ci gaba da shafawa daga wajen cinyoyinta har ya tura hannunsa kurya. Maimakon ya ji ya taba sandar namiji sai ya ji ya shafi kogon mace. Ya ce a cikin ransa, "A'aha, wannan Sarki ko maza-mata ne?" Sa'annan sai ya ce da Badura, "Allah ya ba ka nasara, ban ji liman da almajiransa biyu ba." A wannan karon sai Badura ta kasa gintse dariyar da ke cin ta, ta fashe da dariya har ta fadi bisa keyarta. Bayan ta gama kwasar dariya sai ta ce, "ya masoyina, ba dai har ka manta da abin da ya faru a darenmu na farko ba, daren tarewa?" Daga nan ta kware rawaninta, nan take Kamaruzzaman ya shaida ta a matsayin matarsa, Badura 'yar Sarki Gayur, Sarkin kasar Sin. Suka rungume juna cikin murna da farin ciki marar misaltuwa, suka rika rera wakokin rabuwa da juna. Suka labarta wa juna labarin bayan rabuwa. Kamaruzzaman ya tambaye ta dalilin da ya sa ta tarye shi da wannan irin wasa. Ta ce da shi, "ya masoyina, na yi haka ne domin in yi maka dariya, kuma wannan haduwa ta kasance abar tunawa tsawon rayuwarmu." A wannan dare Kamaruzzaman da Badura suka kwana rungume da juna suka kashe kishirwar begen juna. Da gari ya waye, bayan rana ta fito ta baje haskenta, Badura ta tafi wurin Sarki Armanus, ta fada masa gaskiyar labarinta. Ta ce masa ita matar Kamaruzzaman dan Sarki Shahruzzaman ce. Ta labarta masa yadda suka fara ganin juna, da abin da ya same su bayan rabuwa. Ta kuma fada masa yadda Kamaruzzaman ya bi ta har kasarsu, da yadda ya aure ta. Ta fada masa yadda suka yi niyyar tafiya kasar mahaifin Kamaruzzaman, da yadda shi Kamaruzzaman din ya bace musu, suka ci gaba da tafiya har suka iso wannan birni nasa. Badura ta kwashe kome ta fada wa Sarki Armanus, daga karshe kuma ta ce masa, har yanzu 'yarsa Hayatunnufusi budurwa ce. Sarki Armanus ya mamaki da wannan labari nasu, matukar mamaki. Ya yi umurni da a rubuta wannan labari da ruwan zinariya bisa takard a dakin ajiye kayan tarihi domin 'yan baya su karanta ko za su karu da darussan da ke cikin labarin. Sarki ya sa aka kira masa Kamaruzzaman, ya tambaye shi ko zai amince ya auri 'yarsa, Hayatunnufusi? Kamaruzzaman ya sunkuyar da kansa kasa ya ce, "Allah ya ja zamanin Sarki, a yi mini uzuri har in tamabayi matata Badura, domin kuwa ina da bashinta mai nauyi a kaina." Kamaruzzaman ya tuntubi Badura da maganar. Ta ce masa, "ya masoyina, wannan ai shi ne daidai, domin duk abin da muka yi mata ba mu biya ta ba, bisa ga diyaucin da ta yi mana, hakika ta cika 'yar halas. Ga shi kuma mahaifinta ya wadata mu da alherinsa." Yayin da Kamaruzzaman ya ga cewa Badura ta aminta da zancen auren Hayatunnufusi, kuma ya tabbata ta fadi haka ne da zuciya daya, babu kishi a cikin ranta.sai ya je ya shaida wa Sarki Armanus abin da matarsa ta ce, ya fada masa cewa ya yarda zai auri Hayatunnufusi. Sarki ya yi matukar farin ciki da jin wannan jawabi na Kamaruzzaman. Nan da nan ya sa aka tara masa dukan 'yan majalisarsa, da hakimansa, da alkalai. Ya kwashe labari duka ya fada musu, sa'annan ya ce, "ku sani cewa, ni, na yi niyyar in aurar da 'yata ga Kamaruzzaman, sa'annan in nada shi Sarki a maimakon matarsa Badura. Ko me kuka gani a cikin wannan sha'ani?" Suka amsa gaba daya, "tun da dai shi ne mijin shugabarmu Badura, wadda muka dauka a matsayin Sarkinmu har zuwa wannan lokaci, kuma sirikin mai girma Sarki Armunus, mun amince a nada shi a matsayin Sarkinmu, kai da kaya ai duka mallakar wuya ne. Wallahi mun so, mun so." Sarki ya kume don farin ciki, ya umurci alkalai su rubuta takardar auren Kamaruzzaman da 'yarsa Badura, daga nan kuma aka shiga shirye-shiryen bikin aure da nadin sarauta gaba daya. Kafin ranar biki aka kawata birnin Labunus, kwararo-kwararoda lungu-lungu, da kayan kwalliya iri daban-daban. Da ranar biki ta zo aka goce da shagali, aka yi kamar wata guda ana shagali, sa'annan kowa ya kama gabansa yana addu'a ga sabon Sarki. Shi kuwa tsohon Sarki ya ba da kyaututtukan tufafi ga hakimansa da kuma fadawa, ya rarraba sadaka ga mabukata, ya sa aka sallami dukan 'yan sarkan garin.....27 HIKAYAR SARKI KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN Kafin ranar biki aka kawata birnin Labunus, kwararo-kwararoda lungu-lungu, da kayan kwalliya iri daban-daban. Da ranar biki ta zo aka goce da shagali, aka yi kamar wata guda ana shagali, sa'annan kowa ya kama gabansa yana addu'a ga sabon Sarki. Shi kuwa tsohon Sarki ya ba da kyaututtukan tufafi ga hakimansa da kuma fadawa, ya rarraba sadaka ga mabukata, ya sa aka sallami dukan 'yan sarkan garin. Kamaruzzaman kuwa ya shimfida mulkinsa cikin adalci da tausayin talakawa, ya sa aka rage kudin haraji da na jangali, ya zama mai yawan kyauta ga talakawansa. Ya zauna tare da matansa biyu, idan yau ya kwana dakin wannan, gobe sai ya kwana dakin waccan. Dukan bakin cikinsa ya yaye, zuciyarsa ta koma fari fat, kamar takarda. Ya manta da kasarsu, ya manta da mahaifinsa Shahruzzaman. A kwana a tashi, Allah ya arzuta shi da 'ya'ya biyu daga matansa, dukansu maza, kyawawa, suna haske kamar watanni. Babban sunansa Amjadu, wanda Badura ta haifa masa, sai kuma Asadu, wanda Hayatunnufusi ta haifa masa. Suka tashi kamar 'yan tagwaye, sai dai Asadu ya dan fi Amjadu kyau kadan. Suka tashi cikin kulawa ta musamman, suka nakalci ilimin addini da na mulki, suka san dukan ilimi na taurari da na yanayin kasa, har suka fi dukan mutanen zamaninsu. A fagen yaki kuwa, an horar da su hawan doki, sun iya sara da takobi, sun gwanance wajen iya suka da mashi da kuma jefa shi, sun san dukan dabaru na harba kibiya. Sun iya kokawa da zamiya. Amjadu da Asadu suka zama tamkar Antaru a fagen jarunta. Suna ci gaba da girma kyawunsu da kwarjininsu na kara fitowa. Mutane duka, maza da mata, suna kaunarsu, har suka cika shekaru goma sha bakwai. Yaran nan fa suka tashi cikin kaunar juna, tare suke wasa, tare suke cin abinci, a wurin barci ma bisa shimfida daya suke kwana. Mutane suka rika mamakin hadin kai na wadannan yara, sai ka ce ba 'yan uba ba. Yayin da Amjadu da Asadu suka kai munzalin mutane, sai mahaifinsu Kamaruzzaman ya fara koya musu sha'anin mulki. Duk lokacin da zai tafi farauta ko rangadi, ya kan bar su a gida ne, su yi mulki har zuwa lokacin da zai dawo. Su kuwa sukan rika raba mulkin a tsakaninsu, idan wannan ya hau karaga yau, gobe sai wannan ya hau, har zuwa lokacin da mahaifin nasu zai dawo. Ba a kuwa taba kawo wa Kamaruzzaman koken 'ya'yan nan nasa, a kan yadda suke gudanar da mulkinsu ba. Bisa ga kaddara da kuma rudin shaidan jefaffe, da kuma raunin tunani irin na mata, sai gimbiya Badura ta auku a cikin son Asadu. Ta kasance idan ya zo wurinta, takan ja shi da wasanni da hira, wani lokaci har takan rungume shi ta sumbace shi. Shi kuwa Asadu bai dauki wannan abu a matsayin wani abu ba, a tunaninsa duk tana yin haka ne kamar yadda mahaifiya kan yi wa danta. Amma ita abin ba haka yake ba a cikin zuciyarta, shaidan ya rigaya ya yi mata huduba, babu abin da take so irin ta kwanta shimfida daya ita da Asadu, su ji dadin juna Abin kamar hadin baki, ashe ita kuma gimbiya Hayatunnufusi shaidan ya rigaya ya gama kawata mata Amjadu, babban burinta kullum shi ne ta kwana tare da shi. Kullum sai alamomi take nuna masa na soyayya, amma shi ko a mafarki tunaninsa bai yi daidai da abin da take nufi ba. Ya dauka tana nuna masa soyayya ne a matsayinta na mahaifiyarsa. Soyayyar 'ya'yan nan nasu fa ta tsananta a cikin zukatansu matuka, har barci ya fara kauracewa daga idanunsu, suka daina jin dadin abinci da abin sha. Ana nan wata rana sai Kamaruzzaman ya shirya ya fita zuwa ga farauta, ya bar ragamar mulki ga 'ya'yan bisa ga al'ada. A ranar farko sai Amjadu ya hau karagar mulki, yana umurni yana hani, yana hukunci a tsakanin talakawa da adalci. Da Hayatunnufusi ta ga Amjadu ya kasa gane manufarta, duk da irin alamomin da take nuna masa, sai ta yanke shawarar ta fito fili ta amaye masa abin da ke cikin zuciyarta. Ta dauko takarda da alkalami ta fara rubuta wasika kamar haka: Daga wadda soyayya ta tarwatsa birnin zuciyarta, wadda ta zama abin tausayi a cikin son wanda bai san ana son shi ba, ita ce wadda take azabtuwa a kodayaushe domin begenka. Ya zama wajibi a gare ni, a cikin wannan sa'a, in bayyana maka irin sarkakiyar soyayyarka da ta dabaibaye mini zuciya wadda har ta kai ga ba na iya cin abinci balle barci, idanuna kullum ba su rabo da zubar da hawaye domin begenka. Raina yakan yi zafi, kirjina yakan kuntata domin rashinka. Na kasance mai bakin ciki da kuncin rayuwa domin begenka. A takaice dai, wannan takarda ba za ta isa in bayyana maka irin soyayyar da nake yi maka ba, da kuma irin bakin cikin da nake ciki domin rashin fahimtata da ba ka yi ba. Burina mu kwana shimfida daya, mu wadatu da ni'imar juna. Wassalam, daga Hayatunnufusi... Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ke muku barka da shan'ruwa28 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN Ta rubuta wasu baitocin waka na soyayya daga kasan takardar, ta yanki wani sashi na gashin kanta mai santsin gaske, kamar siliki, wanda da za a sayar da shi a kasuwa, da kudinsa ya lashe baitulmalin wata kasa, saboda kyawunsa. Ta shafa masa turaren miski, ta nannde takardar da shi. Ta kira wani bakin bawanta, ta aike shi da takardar zuwa ga Amjadu. Bawa ya riki takarda ya tafi yana gaggawa, ba tare da ya san kaddarar da ke jiransa ba tattare da wannan takarda, domin kuwa mai kaddarawa - Allah - yakan kaddara kome kamar yadda ya so. Da zuwan bawa, sai ya fadi ya yi gaisuwa a gaban Amjadu, ya fito da takarda ya mika masa. Ya karba ya bude, ya karanta sakon da ke ciki, nan take ya fahimci abin da Hayatunnufusi ke nufin aikatawa tare da shi na zina da cin amanar mahaifinsa. Nan take annurin fuskarsa ya gushe, idanunsa suka hau suka yi ja don fushi. Ya shiga la'antar mata da ayyukansu na cin amana. Ya ce, "Allah ya wadan mata bisa ga ayyukansu na cin amana. Marasa tunani, marasa imani!" Ya dubi bawan nan, sai kuma duk fushin takarda ya koma kansa, dama an ce zomo ba ya fushi da makashinsa sai maratayinsa, ya zare takobi, ya daka masa tsawa, "Allah ya wadaran ka, bakin bawa, mai baki kamar gawayi. Don me za ka dauko sakon zina da cin amanar shugabanka ka kawo mini?" Bawan nan bai sami ta cewa ba, sai Amjadu ya dauke kansa da takobi. Ya nade takarda, tare da gashin nan ya tura a cikin aljihun rigarsa. Ya shiga gida wurin mahaifiyarsa, ya fada mata abin da ya faru, ya kara da cewa, "wallahi ba don gudun bacin ran mahaifina da dan uwana Asadu ba, da na tafi yanzu na sare kan ta, kamar yadda na sare kan bakin bawanta." Ya shura takalminsa ya fita yana la'antar halayen mata. A wannan dare ya kasa cin wani abin kirki, ya kuma kasa barci saboda takaici. Ita kuwa Hayatunnufusi da ta ji labarin abin da Amjadu ya aikata ga bawanta, sai ta yi fushi da shi, ta zazzage shi, ta kuduri aniyar hada masa wani tarko na sharri idan mahaifinsa Kamaruzzaman ya dawo. Washe gari kuma sai Asadu ya hau karagar mulki, ya yi umurni ya yi hani, ya tube ya nada, ya yi hukunci bisa adalci ga talakawa. Can bayan rana ta yi zawwali, lokacin sallar azahar ya yi. Sai ga wata tsohuwar kuyanga ta kawo masa sakon takarda daga gimbiya Badura. Ashe ita kuma soyayyar Asadu ta ci ta, har ta kasa hakuri ta rubuto masa takarda, ta yanki gashin kanta mai santsin gaske, wanda da za a saye shi da kudi, da ya yi barazana ga tattalin arzikin wata kasa, saboda darajarsa. Bayan ta shafe gashin da turaren miski, sai ta nannade takardar da shi. Asadu ya karbi takarda ya bude, sai ya ga an rubuta: Daga wadda ta dulmiye a cikin kogin soyayya, zuwa ga shugaban kyawawa na zamaninsa. Shi ne wanda yake kunyatar da farin wata don haskensa, yake dusashe zinariya don kyawunsa. Shi ne wanda ya juya baya ga masoyiya mai tsananin begensa, ya rufe idanunsa kamar da dai bai san da zamanta ba. Wannan sako ne daga zuciyar mai bege, wadda son ka ya raunana jikinta, begenka ya kakkarya kasusuwanta, tunaninka ya zama abincinta, zuwa ga Yarima Asadu, farin cikin zuciyata. Ka sani hakurina ya kare, babu sauran zagaye-zagaye, sonka ya riga ya mamaye dukan jijiyoyin jikina, ba kuwa zan samu nutsuwa ba sai ranar da na gan mu kwance bisa shimfida daya, muna shayar da junanmu ruwan soyayya. Na sadaukar maka da dukan kaina, sai abin da ka ga dama da ni. Daga zuciyar mai bege. Badura. Daga kasan takardar kuma ya ga ta rubuta wasu baitoci na wakar soyayya. Yayin da ya karanta takarda ya fahimci sakon da ke ciki, sai ya nade ta kamar yadda aka kawo masa ita, ya saka a cikin aljihun rigarsa. Zuciyarsa ta cika fal da fushi. Ya la'anci mata, ya la'anci halayensu na cin amana da yawan sha'awa. Saboda tsananin fushi sai ya rika ganin tsohuwar kuyangar nan da ta kawo masa takarda kamar ita ce Badura, nan take ya sa takobi ya cire kan ta. Ya zauna yana ciccika shi kadai kamar kwado. Ya tashi ya shiga gida wurin mahaifiyarsa Hayatunnufusi. Ya same ta kwance kamar wadda babu laka a jikinta, saboda zulumin abin da ya faru tsakaninta da Amjadu. Ya kwashe abin da ya faru ya fada mata, daga nan ya yi tir da halin mata, ya fita ya nufi wurin dan uwansa Amjadu. Ya fada masa abin da ya faru tsakaninsa da mahaifiyarsa Badura, ya kara da cewa, "Wallahi ba don gudun bacin ranka ba, da na je na sare kanta bisa wannan laifi da ta aikata." Amjadu ya amsa masa, "ya dan uwana, na rantse da Allah abin da ya faru gare ka, shi ne ya faru gare ni tare da mahaifiyarka Hayatunnufusi. Wallahi ba don kai ba, da tun jiya na sare kan ta." Ya kwashe labarin abin da ta rubuta masa duka, ya fada wa Asadu. Suka kwana a cikin wannan dare cikin damuwa da bakin cikin abin da iyayensu suka aikata, suka kasance suna Allah wadai da halin mata. Suka yanke shawarar su bar maganar a tsakanin su, su rufa wa matan nan asiri. Domin idan mahaifinsu ya dawo ya sami labarin abin da suka aikata zai iya kashe su don fushi. Washe gari Sarki ya dawo daga farauta, bayan ya zauna fada na dan wani lokaci, ya sallami askarawa da suka tafi farauta tare. Ya tashi ya shiga cikin gida wurin matansa. Ya tarar da su a kwance, kowace kamar kazar da kwai ya mace wa a ciki. Sun riga sun kiste makircin da za su yi wa yaran nan gun Sarki, domin suna jin tsoron kada yaran su riga su ga Sarki, asirinsu ya tonu. Yayin da Kamaruzzaman ya gan su haka sakaka, sai ya tambaye su abin da ke damun su. Suka tashi da hanzari suka riki hannunsa suna sumbata, suka ce, "ya Sarki, ka sani cewa albasa ba ta yi halin ruwa ba. Domin kuwa 'ya'yan da ka rena da hannunka, suka kuma tashi a cikin arzikinka, su ne suka karya wa matanka irli." Da Kamaruzzaman ya ji haka sai annurin fuskarsa ya gushe, nan take ya cika da fushi ba tare da ya tsaya yin tunani ba. Ya dubi matansa ya ce, "ku fada mini dukan abin da ya faru bayan tafiya ta." Badura ta tausasa murya, ta langabe kai ta ce, "ya Sarki mai adalci, ka sani cewa danka Asadu ya ci zarafina fiye da kima, ya keta mini mutunci. Tun kwanakin baya yake ta aiko mini da wasiku da kuma sakonni wai yana so na. Wai shi duk duniya babu macen da yake so ya kwana tare da ita sai ni. Ni kuwa na hane shi da haka, na yi masa fada, amma bai bari ba. Rannan da ya ga ka fita farauta, sai ya je ya sha giya ya yi tatil, ya dauko takobi ya zo wurina. Ya ce lalle yau sai ya biya bukatarsa gare ni, ko dai in yarda da lalama ko kuma ya yi mini da karfi. Da bawana ya ji haka sai ya taso domin ya kare ni daga gare shi, amma sai ya sa takobin nan ya dauke kansa. Ni kuwa da na ga babu dama, tilas na yarda ya aikata dukan abin da yake so gare ni." Tana gama fadin haka sai ta fashe da kuka, ta ci gaba da cewa, "ya zama wajibi a gare ka, ya Sarki mai adalci, ka kwato mini hakkina a kansa, a yi masa hukunci mai tsanani bisa wannan mummunan laifi da ya aikata gare ni. Kuma Wallahi idan ba a hukunta shi ba, to, ni zan kashe kaina in

Chapter 8 of 14