Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
13 / 14
shiga gidan Halifa, sai ta nufi dakin Na'imatu, ta ba ta battar magani ta ce, "ya shugabata, hakika yau Allah ya hada ni da wani bakon mai magani, Bafarishe, wanda ban taba ganin masanin magunguna ba kamarsa. Da na ba shi 'yar battar nan da kika yi fitsari a cikinta, ya dade yana nazarin fitsarin, ya tambaye ni sunanki, da inda aka haife ki, da shekarunki, duka na fada masa. Daga nan sai ya umurci dansa, wani dan saurayi kyakkyawa, kamarku daya da shi, ya hada mini wannan magani da na ba ki. Kuma ya tabbatar mini da cewa wannan magani tamkar yankan wuka yake." Na'imatu ta karbi dan akwati, tana dubawa sai ta ga sunan mijinta rubuce bisa murfinsa. Nan take yanayinta ya canza, ta ce a cikin ranta, "babu shakka mai maganin nan ni ya zo nema, kuma yana tare da shugabana Na'imu." Ta dubi tsohuwa ta tambaye ta, "yaya kamannin dan mai maganin nan yake?" Tsohuwa ta amsa mata, "saurayi ne kyakkyawa, ya sa tufafi na siliki masu kyau. Shekarunsa kusan daya ne da naki, yana da wani dan tabo bisa girar idonsa na dama. Na ji mai maganin na kiransa da suna Na'imu." Ko da Na'imatu ta ji haka, sai karfin jikinta ya dawo, ta dauki maganin ta shanye, jim kadan sai ta yi dariya ta ce, "hakika wannan magani sahihi ne." Ta dauki takardar da ta gani a cikin battar ta warware ta, ta karanta abin da ke ciki. Ta kara tabbatar wa kan ta cewa shakka babu, wannan sakon shugabanta ne kuma mijinta abin begenta, Na'imu dan Rabi'u. Na'imatu ta cika da farin ciki, zuciyarta ta yi fari. Yayin da tsohuwa ta ga Na'imatu ta yi dariya, sai mamaki ya kamata, ta ce, "hakika wannan rana cike take da albarka." Na'imatu, wadda tun da ta kwanta ciwo ba ta ko son jin warin abinci balle ta ci wani abin kirki, sai ta ce da tsohuwa tana so ta ci abinci. Tsohuwa ta umurci kuyangi su kawo mata abinci. Nan da nan kuyangi suka kawo akussan abinci da gorunan abin sha, suka girke a gaban Na'imatu. Ta jawo akushi daya ta fara cin abinci. Tana cikin cin abinci sai ga Halifa ya shigo dakin. Yayin da ya ga Na'imatu na cin abinci da hannunta sai ya yi farin ciki. Tsohuwa ta ce masa, "ya Shugaban Muminai, ina maka bushara da warakar kuyangarka. Ka sani cewa na hadu da wani bakon Bafarishe mai magani, wanda ya san ilimin kowace cuta da maganinta. Shi ne wanda ya hada mini maganin da na kawo mata, tana gama shan wannan magani kuwa, nan take ta sami lafiya." Halifa ya yi murna, ya kawo dinari dubu ya ba tsohuwa, ya ce, "karbi wannan, ki ci gaba da karbo mata maganin har sai ta warke sarai." Daga nan sai ya fita daga dakin. Tsohuwa ta tashi ta koma wurin mai magani, ta ba shi dinarin nan dubu da Halifa ya ba ta, ta kuma kawo wata takarda da Na'imatu ta rubuto ta ba shi. Wannan lokacin sai ta gaya masa cewa, kuyangar Halifa ce take nema wa magani ba 'yarta ba, kamar yadda ta ce farkon zuwanta. Mai magani ya karbi takarda ya ba Na'imu, wanda nan take ya shaida rubutun Na'imatu, hawaye suka zubo masa don farin ciki. Ya warware takarda, ya ga rubutu kamar haka: Daga kuyangar da ta rasa farin cikinta, wadda ta kusa zautuwa domin rabuwa da abin kaunar zuciyarta. Sakonka ya ishe ni, ya kuma faranta mini ciki matuka, kamar yadda aka fada a cikin wannan waka: Wasikarka bushara ce gare ni, ta kawar da dukkan ciwo da damuwa. Kamar yadda damuwar mahaifiyar Annabi Musa ta kau Yayin da aka ba ta shayar da shi. Kamar yadda makantar bakin cikin Annabi Yakubu ta yaye Yayin da aka kawo masa rigar Annabi Yusufa daga Misira. Lokacin da Na'imu ya gama karanta wannan takarda, gaban rigarsa duk ya jike da hawaye. Ashe tsohuwa ta lura da halin da yake ciki, ta tambaye shi, "me ya sa ka kuka, ya dana? Wallahi bai kamaci kyawawan idanun nan naka da zubar da hawaye ba." "Ya shugabata," mai magani ya amsa mata, "me ya fi sauki ga dana ya yi, in ba kuka ba? Me zai hana idanunsa zubar da hawaye? Bayan kuwa yana kusa da kuyangarsa kuma abar begensa, wadda aka sace daga wurinsa. Ki sani wannan shi ne Na'imu dan Rabi'u mijin Na'imatu wadda kika karba wa magani. Babu wani magani da zai warkar da ita daga cutar da take ciki, face ta hadu da mijinta, su ga juna." mai magani ya mayar wa da tsohuwa dinarin dubun da ta ba shi, ya ce, "ya shugabata, ki rike wannan, na ba ki su duka. Amma ina neman alfarma wurin ki, ki yi mini kokarin da wannan saurayi zai sadu da abar begensa. Idan kika yi mini haka zan kara miki wasu kudin fiye da wadannan." Tsohuwa ta dubi Na'imu ta tambaye shi, "da gaske kuwa kai ne mijinta?" Na'imu ya amsa mata, "na'am, ya mahaifiyata." Ta ce, haba, ai biri ya yi kama da mutum. Domin kuwa babu zancen da take yi kullum sai naka. Na'imu ya kwashe labarinsu, yadda suka tashi tare, da yadda wata tsohuwa ta shirya makircin da ta sace Na'imatu, da yadda suka zo Damashka neman ta, duk ya gaya wa tsohuwa. Yayin da tsohuwa ta ji wannan labari nasa, sai tausayinsu ya kamata, ta ce, "ya kai wannan saurayi, na rantse da Allah babu wanda ya kamata ya hada ka da masoyiyarka face ni." Nan take ta hau jakinta ta koma gidan Halifa. Ta iske Na'imatu zaune, ta dube ta, ta yi murmushi ta ce, "Ya 'yata, da ma saboda rabuwa da mijinki Na'imu dan Rabi'u, mutumin Kufa, ya sa kike ta yawan kuka har kika kwanta ciwo?" Yayin da Na'imatu ta ji haka, sai ta ce wa tsohuwa, "hakika yanzu labulen sirrina ya yaye, gaskiyar lamarina ta bayyana gare ki." Tsohuwa ta matsa kusa gare ta, ta dafa ta da hannu ta ce, "ki yi murna, ya 'yata, ki karfafa ranki. Na lashi takobin sai na hada ki da abin kaunarki ko da kuwa zan rasa rayuwata." Daga nan kuma sai tsohuwa ta koma wurin Na'imu ta ce masa, "na iske kuyangarka tana ta begen ganin ka fiye da yadda kake begen ganin ta. Ka sani cewa saboda son ka da take yi ko Halifa ba ta bari ya taba jikinta ba har zuwa wannan lokaci." Tsohuwa ta dubi Na'imu, ta ci gaba da cewa, "ina so in sani idan ba ka da tsoro ko fargabar shiga gidan Halifa. Domin kuwa zan tafi da kai cikin gidan Halifa, in kai ka har dakin Na'imatu domin ku sadu da juna. Amma ita kam, ba ni da ikon da zan fito da ita daga gidan Halifa." Na'imu ya amsa mata cewa, ai ko da za a bi ta cikin wuta ne, to, zai iya, idan dai har zai sake ganin Na'imatu. Tsohuwa ta ce to, madalla. Ta tashi ta koma wurin Na'imatu. Ta ce mata, "mai gidanki yana matukar son ki, ya damu kwarai a kan sai ya gan ki. Minene naki ra'ayi?" Na'imatu ta yi farat ta ce, "wallahi ina son ganin shi ni ma." Sai tsohuwa ta je ta samo tufafin mata masu kyau, ta kuma samo kayan kwalliya na mata, kamar janbaki da gazar da hoda, ta nade su cikin wani zane. Ta dauka ta nufi rumfarsu Na'imu. Da zuwanta sai ta ce masa zo mu tafi. Ta kai shi gidan wanka, bayan ya fito daga wanka, suka shiga wani daki wanda babu kowa a ciki, suka rufe kofar. Yayin nan ta yi masa kwalliya irin ta mata, ta kitse masa gashin kansa. Ta sa masa awarwaro ga hannuwansa, ta daura masa sarka ga wuyansa. Ta fito da tufafin nan, wadanda suka kasance irin na kuyangi ne, amma masu tsada, ta ce ya sa. Da ta gama shirya shi tsaf, kamar yadda take so. Ta dube shi ta gan shi kamar daya daga cikin 'yan matan Hurul Aini don kyawunsa, babu yadda za a yi a ce namiji ne. Ta ce, "tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Wallahi har ma ka fi Na'imatu kyau a cikin wannan shigar." Sa'annan ta gwada masa yadda zai yi tafiya irin ta mata, ta ce masa ya rika tura kafadarsa ta hagu gaba tare da murguda mazaunansa idan yana tafiya. DAGA Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ40 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN Da ta gama shirya shi tsaf, kamar yadda take so. Ta dube shi ta gan shi kamar daya daga cikin 'yan matan Hurul Aini don kyawunsa, babu yadda za a yi a ce namiji ne. Ta ce, "tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Wallahi har ma ka fi Na'imatu kyau a cikin wannan shigar." Sa'annan ta gwada masa yadda zai yi tafiya irin ta mata, ta ce masa ya rika tura kafadarsa ta hagu gaba tare da murguda mazaunansa idan yana tafiya. Kuma ya rika yin taku daidai, kada ya yi sauri. Na'imu ya yi tafiya kamar yadda ta ce masa. Da ta ga ya yi tafiya daidai, yana rangwada kamar mace, sai ta ce masa, "da yardar Allah gobe da dare zan zo in kai ka wurin masoyiyarka. Idan muka isa gidan Halifa kada ka ji tsoron kowa, ko da mun hadu da dogari ko bawa, ka dan rusunar da kanka kasa kadan, alamun gaisuwa, amma kada ka yi musu magana Ni zan hane su daga yi maka wata magana." Daga nan ta ce masa ya cire tufafin sai zuwa gobe da dare za ta zo ta tafi da shi gidan Halifa. Ta sa kai ta fice daga gidan wankan. Kashe gari da dare sai ga ta ta dawo, ta sake shirya Na'imu da tufafin mata, ta shiga gaba ya bi ta a baya har gidan Halifa. Tun a bakin kofar gidan wani bawa ya so ya hana Na'imu shiga, amma sai tshohuwa ta ce masa, "kaiconka, don me za ka hana kuyangar Na'imatu, babbar masoyiyar Halifa, shiga wannan gida." Yayin da bawa ya ji haka, sai ya yi sauri ya ba su hanya suka wuce. Suka ci gaba da tafiya cikin gidan har suka yi nisa a cikinsa. Daga nan sai tsohuwa ta ce masa, "kada ka ji tsoron kome, ka shiga waccan kofar," ta nuna masa kofa da hannu, "idan ka shiga za ka ga dakuna da yawa a jere, dama da hagu. To, daga na bangaren hagu, sai ka kidaya kofa biyar ka shiga ta shida, domin nan ne dakin Na'imatu. Duk wanda ya yi maka magana kada ka saurare shi, ka tafi kai tsaye ka shiga wannan daki." Tsohuwa ta ja shi ta kai shi bakin kofa, suka tarar da bawa tsaye yana gadin kofar. Bawa ya tambayi tsohuwa, "wace ce wannan kuyangar da kike tare da ita?" " Tsohuwa ta amsa masa, "shugabarmu ce ta sayo ta." Bawa ya tare kofa ya ce ba za ta shiga ba, domin Halifa ya umurce shi kada ya bar kowa ya shiga ta wannan kofa, sai fa wanda ya sani. Bawa ya kara da cewa, amma idan ita tsohuwar ce za ta shiga, to, ta shiga, amma ita kuyanga bai san ta ba, balle ya bari ta shiga. Tsohuwa ta ce masa, "ka manta ne shugabarmu Na'imatu ba ta dade da samun sauki ba daga ciwon da ya kamata? Ka kuwa san yadda Halifa yake son ta sarai. To, ita ce ta sayi wannan kuyanga domin ta rika yi mata hidima tare da debe mata kewa. Muddin kuwa ka hana kuyangar nan shiga wurin ta, to, ina ji maka tsoron ciwonta ya dawo. Idan kuwa Halifa ya san kai ne sanadiyyar komowar ciwonta, babu shakka zai sa a sare kan ka. Ka yi tunani ka gani." Bawa ya yi tsaye sororo, domin kuwa maganar tsohuwa ta shige shi. Tsohuwa ta juya wurin Na'imu ta ce masa, "ki shiga wurin shugabarki, ina rokon ki kuma kada ki gaya mata cewa wannan bawa ya tsayar da mu a bakin kofa." Na'imu ya dan rusunar da kansa kasa, ya shige ta cikin kofar. To, maimakon ya je ga dakunan da ke bangaren hagu, ya kidaya kofa biyar ya shiga ta shida, kamar yadda tsohuwa ta gaya masa. Sai ya nufi dakunan da ke bangaren dama, ya kidaya kofa shida ya shiga ta bakwai. Da ya shiga dakin sai ya ga an kawata shi da labulayyen bango na siliki, wadanda aka yi wa ado da zinariya da azurfa. An shimfide daben dakin da kilisai masu taushin gaske. Ya ji gaba dayan dakin ya gauraye da kamshin turaren miski. Daga can kuryar dakin ya ga wani gado na alfarma, an shimfida masa shimfidu masu daraja da tsada. Ya tafi ya zauna bisa gadon yana rarraba ido, yana mamakin irin kayan alatun da aka shirya a cikin wannan daki, cewa shi, bai san abin da Allah zai kaddara a kan sa ba. Yana nan zaune yana mamaki, sai ga yarinyar nan, kanwar Halifa, ta shigo tare da kuyanga tana take mata baya. Yayin da kanwar Halifa ta gan shi, sai ta zaci kuyanga ce. Ta ce masa, "wace ce ke, wa ya sayo ki? Kuma wa ya kawo ki dakina?" Na'imu ya yi shiru, ya ki mayar mata da jawabi. Ita kuma sai ta kara cewa, "idan laifi kika yi wa dan uwana, Halifa, har kika boye kanki a cikin dakina, to, ki gaya mini irin laifin da kika yi masa, ni kuwa zan lallashe shi, in ba shi hakuri ya yafe miki." Na'imu dai bai amsa mata ba. Da kanwar Halifa ta ga haka, sai ta umurci kuyangar da suka shigo tare, ta koma waje daga bakin kofa, kada ta bari kowa ya shigo. Ta je gaban Na'imu ta dubi fuskarsa, ta yi mamaki da irin kyawunsa, ta ce masa, "ya ke kuyanga, wace ce ke? Kuma ya ya aka yi har kika shigo nan? Domin ban taba ganin ki a cikin wannan fada ba." Na'imu dai ya yi kurum, bai ce mata kome ba. Ganin haka sai ta yi fushi, ta riki damutsttsan hannuwansa domin ta finciko shi daga bisa gadonta. Garin ya kubce daga rikon da ta yi masa, sai hannunta daya ya shafi kirjinsa. Sai ta ji kamar ta shafi kirjin namiji, domin ba ta ji alamar nonuwa ba. Nan take ta sake shi, ta ja da baya cikin kaduwa. Yayin da Na'imu ya ga asirinsa zai tonu, sai ya tashi daga kan gado, ya zo gabanta ya durkusa, ya ce, "ya shugabata, ni bawanki ne. Rayuwata yanzu tana hannunki, ina rokonki, ki yi mini rai." "Babu abin da zai same ka. Amma gaya mini wanene kai? Wanene kuma ya kawo ka nan?" "Ya ke Sarauniya, sunana Na'imu dan Rabi'u mutumin Kufa. Na sadaukar da rayuwata ne, na zo wannan wuri domin in sadu da kuyangata, abar begena Na'imatu, wadda Hajjaj, Sarkin Kufa, ya sace daga hannuna ya aiko da ita wurin Halifa." Kanwar Halifa ta ce, "kada ka ji tsoron kome, babu abin da zai same ka na cutarwa." Ta kwala wa kuyangar da ke bakin kofa kira, ta , ta umurce ta da ta je dakin Na'imatu ta kirawo ta. Amma tsohuwa kuwa, bayan sun rabu da Na'imu sai ta nufi nata daki ta zauna, tana ta zullumin kada a sami kuskure. Can zuwa wani lokaci sai ta kasa daurewa, ta tashi ta nufi dakin Na'imatu, ta tambaye ta, "shugabanki ya iso kuwa?" Ta amsa mata, "na rantse da Allah ban gan shi ba." Nan take gaban tsohuwa ya fadi, ta ce, "ai kuwa ina tsammanin ya rude, ya fada wani dakin na daban." Na'imatu ta ce, "babu tsimi babu dabara face daga Allah Madaukakin Sarki. Kaicon halakarmu." Suna cikin wannan hali na fargabar abin da zai faru, sai ga kuyanga ta shigo musu. Ta gai da Na'imatu, ta ce mata shugabarta na neman ta a dakinta. Na'imatu ta ce ta ji, ta karba. Tsohuwa ta dube ta ta ce, "watakila dakinta shugabanki ya shiga, ai kuwa asiri ya tonu." Na'imatu ta bi bayan kuyanga suka tafi, da shigar su cikin dakin sai kanwar Halifa ta ce mata, "ya Na'imatu, ga shugabanki nan zaune kusa gare ni. Ga alama ya bata hanyar zuwa dakinki. Amma daga ke har shi, kada wanda ya ji tsoron kome. Ku kwantar da hankalinku, ni zan taimake ku." Yayin da Na'imatu ta ji haka, sai zuciyarta ta yi karfi, ta matsa kusa ga Na'imu. Shi kuma ya tashi tsaye. suka rungume juna suna zubar da hawaye don farin ciki... DAGA~==>Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ 41 HIKAYAR KAMARUZZAMANA DAN SARKI SHARUZZAMAN Yarinya kanwar Halifa ta ce wa Na'imu da Na'imatu, "ku kwantar da hankalinku, ni zan taimake ku." Yayin da Na'imatu ta ji haka, sai zuciyarta ta yi karfi, ta matsa kusa ga Na'imu. Shi kuma ya tashi tsaye, suka rungume juna suna zubar da hawaye don farin ciki. Suka fadi sumammu Yayin da suka dawo cikin hayyacinsu sai kanwar Halifa ta ce musu su zauna domin su tattauna yadda za su shawo kan Halifa bisa wannan al'amari. Suka ce da ita, "wallahi ya shugabarmu, mu kam ba mu da wata dabara ko shawara sai fa abin da kika gani." Ta ce musu, "na rantse da Allah, ba zan bar dan uwana ya cutar da ku ba. Ku zauna mu dan yi nishadi." Ta sa aka kawo musu abinci da nama, da kayan shaye-shaye da tande-tande. Suka ci suka batse, kaskon sha ya zagaya a tsakaninsu, suka sha har ya ishe su. Na'imu da Na'imatu suka yi farin ciki har damuwar su ta soma yayewa. Daga nan sai Na'imu ya kada baki ya ce, "ya shugabata, yaushe ne matsalarmu za ta warware?" Ita kuma sai ta tambaye shi, "ya Na'imu, shin kana son kuyangarka Na'imatu?" Ya amsa mata, "ai saboda son ta da nake yi ya sa na sadaukar da raina na shigo wannan gida." Sa'annan ta juya wurin Na'imatu, ta tambaye ta, "ya Na'imatu, shin kina son shugabanki Na'imu?" Na'imatu ta amsa mata, "ya shugabata, ai son sa ne ya yi sanadiyar rashin lafiya ta wadda ta ramar da jikina. Wallahi ina son shi fiye da yadda kike tunani." "Na rantse da Allah, tunda dai har kuna son juna, duk wanda ya shiga tsakaninku, to, Allah ba zai bar shi haka ba. Kada ku damu, za ku koma yadda kuke rayuwarku a baya." In ji kanwar Halifa. Suka raurawa da farin ciki. Na'imatu ta dauki molo, ta kida shi da yatsunta, kida mai taushi da kwantar da hankali, ta sirara murya tata, ta wake wadannan baitoci: Yayin da makiya suka kitsa rabuwarmu Wani abu bai kasance a gare ni ba wanda za su amfana da shi. Wani abu bai kasance ga masoyina ba, balle su ji dadi. Dukkan munafuki yakan yi mugunta bisa ga bata Kowa ya dogara ga Allah ba ya jin tsoron makiya. Bayan ta gama wannan waka, sai ta mika wa Na'imu molo ta ce, "ya shugabana, nishadantar da mu da wata waka da ke gare ka." Ya karbi molo ya gyara tsarkiyarsa, ya zungure shi da yatsu, ya wake wadannan baitoci: Wata yana koyi da ke, ba domin yana ramewa ba. Rana ita ce tamkarki, ba domin tana faduwa ba. Ni na yi al'ajabi, da yawan al'ajabi a cikin so. Ina ganin tafarki makusanci, yayin da na shige shi zuwa ga masoyi. Yakan yi mini nisa, yayin da na juyo. Yayin da ya gama wannan waka, sai Na'imatu ta cika kasko da abin sha ta mika masa, ya karba ya shanye. Ta cika wani kasko ta ba kanwar Halifa, ita ma ta karba ta kurbe. Daga nan sai kanwar Halifa ta karbi molo daga hannun Na'imu, ta wake wadannan baitoci: Bakin ciki da bacin zuciya, matabbata ne a cikin kirjina. Da yawan tunanin da nake yawan maimaitawa a cikin raina. Su suka rame jikina, da ya zama madaukaki. Jiki ya kasance a gare ni macuci da bege. Bayan ta gama waka sai ta cika kasko da abin sha ta ba Na'imatu, ta karba ta shanye, sa'annan ta karbi molo ta yi waka. Haka suka kasance cikin sha da wake-wake, suna annashuwa. Kirazansu suka yalwata, zukatansu suka yi fari da wakokin da suke yi. Kwamfa, sai ga Halifa ya fado dakin, kamar wanda aka ingizo. Lokacin da suka gan shi sai suka tashi gaba daya, suka fadi suka yi gaisuwa. Yayin da Halifa ya ga Na'imatu rike da molo, sai ya yi murna ya ce, "ya Na'imatu, godiya ta tabbata ga Allah wanda ya warkar da ke daga ciwo." Daga nan sai ya dubi Na'imu, wanda yake cikin shigar mata, ya ce wa kanwarsa, "ya 'yar uwata, wace ce wannan kuyanga?" Ta amsa masa, "ya Shugaban Muminai, kuyangarka ce. Ita tana daga cikin kawayen Na'imatu wadda ko abinci ba ta iya ci sai tare da ita, kamar yadda aka fada a cikin wannan waka." Abokai biyu sun taru, ya za a yi su rabu? Sai fa cikin rashin sani. Aboki yakan debe wa aboki kewa. Halifa ya cika da mamaki, ya ce, "wallahi ita ma kyakkyawa ce kamar Na'imatu. Gobe kuwa zan sa a shirya mata nata daki kusa ga na Na'imatu, saboda wannan shakuwa tasu. Zan sa a kawata mata dakin tamkar yadda aka kawata dakin Na'imatu." Daga nan kanwar Halifa ta gyara masa shimfida ya zauna. Ta sa aka kara kawo kayan abinci. Aka kuma kawo na kwalama da makulashe, tare da abin sha iri-iri. Suka ci abinci tare da Halifa. Bayan sun gama cin abinci sai ya cika kasko da abin sha, ya yi wa Na'imatu alama da ta dauki molo ta yi waka. Ta dauki molo, bayan ta sha kasko biyu, ta wake wadannan baitoci: Ya mafi daukakar mutane a cikin wannan zamani. Wanda babu tamka a gare shi, mai alfarma cikin al'amari. Ya makadaici a cikin daukaka da kyauta cikakkiya. Ya shugaban Sarakuna ga kowace jiha. Ya mamallaki ga sarakunan kasa. Mai ba da mai yawa ba tare da gori ba. Allah ya wanzar da kai bisa turmuza hancin makiyanka. Shi adanta kushewarka fiye da daukakarka. Yayin da Halifa ya ji wannan waka sai ya cika da farin ciki. Ya kara cika kasko da abin sha ya ba Na'imatu, ya umurce ta da kara yin wata waka. Ta karbi kasko ta shanye, ta tsuke zaren molo, ta wake wadansu baitocin. Lokacin da Halifa ya ji wakarta, sai ya dimauta da fasaharta da kuma zakin muryarata. Ya ce, "na rantse da Allah wannan waka ta yi dadi. Na rantse da Allah har ta fi zuma zaki. Wallahi Allah ya yi miki baiwa, ya Na'imatu. Ga ki da fasahar waka, ga kuma murya mai dadi da kwantar da hankali." Haka dai suka ci gaba da nishadi tsawon wani lokaci, har dare ya raba ba su sani ba. Daga nan sai kanwar Halifa ta ce masa, "ya Shugaban Muminai, ni kuwa na karanta wani labari mai dadi, na wani babban Sarki, a cikin littafi, da kana da sha'awa da na gaya maka shi." "Wane labari ne wannan mai dadi? Gaya mana shi mu ji." In ji Halifa. Ta ce da shi "ka sani cewa, ya Shugaban Muminai, a birnin Kufa, an yi wani saurayi wanda ake kira Na'imu dan Rabi'u. Yana da wata kuyanga wadda aka rene su tare tun suna yara har suka girma tare. Bayan sun isa mutane sai soyayya mai tsanani ta ratsa zukatansu, suka so junansu matuka. Daga karshe dai har Na'imu ya riki wannan kuyanga a matsayin matarsa. Suna nan kan haka, cikin jin dadi da farin ciki, sai rannan wata kaddara ta raba tsakanin su. Aka sace wannan kuyanga bisa ga yaudara, aka sayar da ita ga wani babban Sarki na wata kasa daban. To, saboda tsananin son da Na'imu ke yi wa kuyangarsa, sai ya sadaukar da ransa, ya shiga duniya wajen neman ta. A kwana a tashi har Allah ya hada shi da ita a cikin gidan Sarkin da ya saye ta. Sun hadu da juna ke nan ko mayar da zance ba su gama yi ba, sai ga Sarkin nan ya fado wurin da suke. Yayin da Sarkin nan ya gan su tare, sai ya sa aka sare kawunansu, ba tare da ya yi wani bincike ba." Kanwar Halifa ta dubi dan uwanta ta ce, "ya Shugaban Muminai, shin hukuncin da wannan Sarki ya yanke ya yi daidai kuwa?" Halifa ya girgiza kansa ya ce, "wallahi wannan Sarki bai yi aiki da hankali ba. Ya kamata ya yi la'akari da abubuwa guda uku, kafin ya bi wani mataki a kan su. Na farko, ya tambaye su, shin suna son juna? Na biyu, tunda suna cikin gidansa ne, sai ya rike su a matsayin baki, ya kyautata musu kamar yadda aka umurce mu da kyautata wa bako, daga bisani sai ya yanke hukuncin da ya ga ya kamata gare su. Abu na uku kuwa, ya kamata ya kwatanta kansa a matsayin mutumin da zai yanke wa hukuncin, ya gani idan shi ne aka yanke wa hukuncin an yi masa adalci." Yayin da kanwar Halifa ta ji haka sai ta ce, "ya Shugaban Muminai, ka umurci Na'imatu ta rera mana waka, kuma ka saurari abin da za ta fada a cikin wakarta." Halifa ya umurci Na'imatu da yin waka. Ta dauki molo, bayan ta kada shi sai ta wake wadannan baitoci: Ha'incin zamani bai gushe ba yana zambatar mutane. Yana wautar zukata, yana gadar da tunani Yana raba masoya bayan haduwa. Sai ka ga hawaye na zuba bisa kundukuki Kwatankwacin bakin cikin kashe rai, mani'imci. Zamani ya hada tsakaninsu bayan rabuwa Don me za ka shiga tsakanin wadannan masoya? Yayin da Halifa ya ji wannan waka sai ya cika da tsananin farin ciki. Kanwarsa ta ce masa, "ya dan uwana, yana daga cikar kamalar mutum ya tsaya bisa ga magana guda, ba a san dattijo da magana biyu ba. Ka riga ka yanke wa kan ka hukunci bisa ga abin da zan bayyana maka yanzu." Ta dubi Na'imatu ta ce ta mike tsaye, haka kuma ta ce da Na'imu shi ma ya tashi tsaye, suka mike tsaye. Ta dubi Halifa ta ci gaba da cewa, "ya Shugaban Muminai, wannan da ta mike tsaye ita ce Na'imatu, kuyangar Na'imu dan Rabi'u, wadda Hajjaj dan Yusufa, Sarkin Kufa, ya sace daga gare shi, ya aiko maka da ita, ya yi maka karyar cewa ya saye ta dinari dubu goma." Ta nuna Na'imu, ta ce, "wannan kuma ba mace ce ba. Shi ne Na'imu dan Rabi'u shugaban Na'imatu." Ta tashi ta zo gaban Halifa ta durkusa kasa, ta ce, "ina rokon ka, don alfarmar kakaninmu masu albarka, don Hamza da Akilu da Abbas, ka yafe wa wadannan masoya biyu. Ka mayar musu da matsayinsu da suke ciki, domin neman tsira gobe kiyama. A halin yanzu, rayuwarsu tana hannunka. Ni dai na shiga tsakani, ina neman alfarmar ka yafe musu, kuma ka mayar masa da kuyangarsa." Halifa ya yi murmushi, ya dubi 'yar uwarsa ya ce, "wallahi kin fadi gaskiya, dattijo ba ya magana biyu. Ni ba zan saba abin da na fada ba daga farko." Ya juya wurin Na'imatu, ya tambaye ta, "ya Na'imatu, wannan shi ne shugabanki?" Na'imatu ta amsa masa, "i, Allah ya ba ka nasara." Halifa ya ce, "babu abin da zai same ku na cutuwa daga gare ni.

Chapter 13 of 14