Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 14
mata. Idan kuwa zalunci ne a kaina, to, ka gaggauta yi mini sakayya a kan duk wanda ya zalunce ni. Kai ne mai iko a kan kome da kowa." Yayin da kuyanga ta ji haka, sai ta saukar masa da bugu mai tsanani sai da ya suma. Ta kawo 'yar gurasa da dan tarfen ruwa ta ajiye masa. Ta sa kai ta fita, ta bar shi nan kwance cikin sarka, a some cikin jini. Ya nesanta da masoyansa da dan uwansa.. Bayan ya farka, ya yi kuka, kuka mai tsanani. Ya wake wadannan baitoci:Ya zamani ka saukaka, ka jinkirta. Domin kwa mun tanadi jin dadi a cikina Muna maraita, muna jijjibi da masoya. Tsawonka bai tabbatar mu bisa haka Ka zam azurta mai dufunnan zuciya Domin kewar rabuwa da masoya cikinka Magabta dukansu da ayyukansu bata ne Mai hakuri sannu zuciyarsa za ta samu waraka. Bege da kadaici ne ya wanzar da wani abu Ban samu jin dadi ba ko kadan da waraka Daga bakin cikin rabuwa da abin ganina ba. An jarrabe ni da shiga kurkuku da halaka Bai kasance a gare ni mai debe kewa ba. Face ruhina da idona na korar makiyanka Wanda yake mataimakin al'amarina. Zurfin begena, wuta tasa ba ta bicewa haka. Da bakin ciki da tunani suna hura ta kwarai Tana haskaka da hurawarsu ga cutuka Ni na tabbata cikin bakin ciki na dulmiya Tsawon darena a cikin azaba na habaka. Cewa ni, ana kona ni da wutar bakin ciki Mai huruwa, ga kwarkwata sun samu cimaka Dangin shan giya a hannun mai begenta Ya yiwo jijjibi jiki ya rame a dalilin cutuka. Maraya ba shi da wani mai taimakonsa Ga ni a cikin kurkuku a cikin wuya uku In wayi gari a cikin daurewar hannu da kafa Bakin ciki yana ramar da ni yana son halaka Yayin da ya gama wannan waka, ya ci gaba da kuka yana shekar da hawaye. Ya kasance a cikin wannan gida, kuwwarka banza. Al'amarinsa ke nan. Amma Amjadu kuwa, ya yi jiran Asadu a bayan gari har rana ta take ta sunkuya bai dawo ba. Gabansa ya fadi, idanunsa suka yi kwal kwal suka cika da kwalla. Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ke tare daku32 HIKAYAR SARKI KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN Amjadu kuwa ya yi ta jiran Asadu a bayan gari har rana ta take ta sunkuya bai dawo ba. Gabansa ya fadi, idanunsa suka yi kwal kwal suka cika da kwalla. Ya ce, "kaico dan uwana, kaico abokin tafiyata. Ya bakin cikina, ya bakin cikin rabuwarmu." Daga nan ya gangaro daga kan tsauni, hawaye na zuba daga idanunsa, ya shiga cikin birni ya yi nufin zuwa kasuwa. Ya tambayi mutane sunan wannan birni. Suka gaya masa cewa, sunansa Birnin Matsafa, mafi yawancin jama'arsa suna bautar wuta ne, amma akwai Musulmi 'yan kadan. Ya tambaye su labarin Birnin Labunus. Suka ce masa, Birnin Labunus na Sarki Armanus ko? Ai daga nan zuwa can tafiyar shekara wata uku ce a kasa, ba magama ba cin zango. Ko kuma tafiyar wata a jirgin ruwa. Amma yanzu mun ji an ce wani surukinsa ne, mai suna Kamaruzzaman, wanda yake auren 'yarsa Hayatunnufusi, ke mulkin birnin bisa adalci da tausayin talakawa. Yayin da Amjadu ya ji an ambaci sunan mahaifinsa, sai ya yi ajiyar zuciya, bakin cikinsa ya karu. Ya rasa inda zai nufa, ya sayi abinci ya dauka ya nufi wani sako inda ya lura babu mutane da yawa a wurin. Ya zauna domin ya ci abinci, amma da ya tuna da dan uwansa Asadu sai ya kasa ci. Haka dai ya daure ya yanki loma daya ya ci, ya sha ruwa domin ya dan ji nauyi- nauyi ga cikinsa. Ya tashi ya fara zagaya birnin yana neman dan uwansa, har ya iso ga rumfar wani madinki. Da Amjadu ya lura da madinkin nan, kuma ya ga hasken musulci a fuskarsa, sai ya yi masa sallama. Madinki ya mayar masa da sallama. Ya shiga ya zauna a cikin rumfa, ya kwashe labarinsa duka ya fada wa madinki. Madinki ya ce, "ayya dan samari, ai kuwa idan dan uwan nan naka ya fada hannun wani matsafi, to, kai da ka kara ganinsa sai a darussalam. Amma kuma Allah buwayi ne gagara misali, ko da ya fada a hannun matsafi ne, sai ya kubutar da shi ku sake haduwa da juna." Suka yi jim na dan wani lokaci. Madinki ya tambaye shi, "ko za ka yarda ka zauna a wurina?" Amjadu ya amsa, "na'am." Madinki ya yi farin ciki da haka. Amjadu ya zauna a wurin madinki tsawon kwanaki. Madinki ya rika kwantar masa da hankali yana koya masa dinki har ya gwanance. Wata rana Amjadu ya tafi bakin teku ya yi wanka, ya wanke tufafinsa suka yi fes. Da ya gama sai ya shiga cikin birni domin ya bude ido, ya kuma duba ko Allah ya sa ya ga dan uwansa. Ya rika bi kwararo-kwararo, sako-sako yana yawo. Yana cikin zagaya birni, ya karya wata kwana sai ya yi kicibis wata mace kyakkyawar gaske, mai kwarjini da haiba. Yayin da suka hadu kusa da kusa, sai matar nan ta yaye mayafin da ya rufe fuskarta, ta kyabci Amjadu da idanunta ta kwararo masa wani murmushi mai dauke hankali. Sai kuma ta rera wannan waka: Da na gane ka, ka gabato sai ganina ya rufe Ka ce kai ka rufu da idon rana. Cewa kai, kai ne mafi kyawo a cikin kyawawa. Kai ne namiji mafi kyawo daga cikin mazan wannan zamani. Da a ce a wannan zamani namu. An raba kyawo gida biyar ne Da kai ne ka kwashe kashi hudu Sauran halittu kashi daya. Raina fansa ne a gare ka. Yayin da ya ga wannan mata da irin kyawonta, ya kuma ji wakarta, nan take sai ya ji zuciyarsa ta tafi gare ta. Son ta ya damki ruhinsa, bai san lokacin da ya kyabce ta da ido ba, sa'annan ya rera wannan waka: Maganar kundukuki ta baci da kayar tsidau ga wannan abin zantawa. Ransa manesanci ne ga haka, kada ki mika hannuwa zuwa gare shi. Ya tsawaita da aikata wannan al'amari. Gamuwarmu ta tsaya ga idanuwa. Gaya wa wannan da ta zalunce ni Wadda ta kasance fitina a gare ni. Da dai ta yi adalci, ta saukaka ga fusaka wadda ta duhunta. Hakarkarinsa ya konu da wutar bege. Da ta ji wakarsa sai ta yi ajiyar zuciya. Ta kuma rera wadannan baitoci: Kai ne wanda ya shiga tafarki ba ni ce ba. Kai ne ka samar da saduwa, ko da cikawa ta kasance gare ni. Ya wanda asubahinta ke kecewa daga lu'ulu'un kyawonsa Mai saka dare yana kawaita yayin tashinka. Ya kasance babu makawa ga saye na, ka karbi biya. Bayan ta gama waka sai Amjadu ya tambaye ta, "zan bi ki ne na ga gidanki, ko za ki tare da ni kind ga gidana?" Ta langabe kanta gefe guda, ta amsa masa da fadar Ubangiji madaukaki, "maza sune tsaye a kan mata. Allah ya daukaka sashensu fiye da sashe." Da Amjadu ya ji haka, sai ya fahimci jawabinta. ya fahimci tana so ta bi shi ne. Sai ya fara tunanin inda zai kai ta, domin yana jin kunyar mai gidansa, madinki. Ba zai yiwu ba ya dauki mace ya je masa da ita. Don haka sai ya ci gaba da tafiya hanyar da ya dosa, ita kuwa ta bi shi a baya. Suka yi ta ragaita, daga wannan kwararo zuwa wancan, daga wannan lungu zuwa wancan, har dai ta gaji ta tambaye shi, "ya masoyina, shin ina gidan naka yake?" Ya amsa mata, "kara hakuri dai, mun kusa isa." Daga nan sai ya karya kwana ya shiga wani lungu wanda gidajensa duka masu kyau ne, matar nan kuwa ta take masa baya suka ci gaba da tafiya. To, ashe wannan lungu ba shi bullewa ko'ina sai a gaban wani gida. Da suka iso karshen lungun, Amjadu ya gan su a gaban wannan gida, sai ya ce a cikin ransa, "babu tsimi babu dabara, face daga Allah madaukakin Sarki." Ya ga gidan yana da babbar kofa ta karfe, wadda take kulle. Akwai kuma dakali guda biyu na zama, wadanda aka gina da duwatsu, daya a kowane gefe na kofar gidan. Ya zauna bisa dakali daya, ita ma ta zauna bisa daya dakalin suna fuskantar juna. "Ya masoyina, to, me muke jira?" Ta tambaye shi. "Ka bude gidan mu shiga daga ciki mana." Amjadu ya sunkuyar da kansa kasa yana tunanin karyar da zai yi mata. Can sai ya dago kansa ya ce, "ina jiran yarona ne, wanda na ba makullin gidan, domin ya zo ya shirya mini abinci da abin sha, kafin in komo daga bakin teku, wajen shan iska." Sa'annan ya ce a cikin ransa, "idan ta gaji da jira ai dole ta kama gaban ta." Da suka kara jimawa a zaune sai matar ta ce, "ya masoyina, wannan yaro naka ya dade bai zo ba. Bai kamata mu yi ta zama a nan bisa hanya ba." Ta dauki dutse ta nufi wurin kofa. Amjadu ya ce, "ki kara hakuri, yana nan tafe yanzu." Kafin ya rufe bakinsa tuni ta balle makulllin kofar da dutse, ta bude ta shiga. Amjadu ya tsorata ya ce da ita, don me za ki aikata haka? Ta ce masa, ina laifi don mutum ya balle kofar gidansa. Ba ta ko jira ta ji amsarsa ba, sai ta kutsa kai cikin gidan. Amjadu ya tsaya a bakin kofa yana shawarwarin abin da zai yi. Shin ya gudu ne ya bar ta, ko kuwa ya bi ta cikin gidan, kome ta fanjama, fanjam. Bai san lokacin da ta zo ta kama hannunsa ba, ta ja shi suka shiga cikin gidan tana cewa, "haba hasken idona, farin cikin zuciyata, me kake tunani ne ka ki shigowa?" Ya amsa mata, "zan shigo. Ina tunani ne, ko yaron nan ya shirya gidan kamar yadda na umurce shi, ko kuwa yana can wajen shiriritar sa?" Ya bi ta suka shiga ciki, zuciyarsa cike da tsoron abin da zai faru idan mai gidan nan ya iske su. Da suka wuce zaure, suka shiga cikin gidan, sai Amjadu ya ga an shirya shi tsaf, an kawata shi kwarai da kayan alatu iri-iri. Tsakiyar gidan yana da fadi da yalwa. Akwai wani dan tabki da aka gina a tsakiyar gidan cike da ruwa. A tsakiyar tabkin ga wani dan siririn bututu na karfe yana ta feso ruwa daga bakinsa, idan ruwa ya fita ya yi sama, sai ya baje ya dawo cikin dan tabkin kamar ruwan sama. Kewayen dan tabkin kuma duk ciyawa ce tsanwa shar, ta yi furanni masu launi kala-kala, gwanin ban sha'awa. Sauran filin gidan kuma duk an dabe shi da farin dutse. Daga can gefe kuma an yi wata rumfa, an shimfide kasanta da wadansu kilisai na alfarma. A cikin rumfar an jera abubuwan zama da gadaje. Ga kuma wani dan gado na alfarma mai kama da teburi, bisa gare shi an shirya tasoshi na zinariya da azurfa, da kuma akussa, dukkansu rufe da mayani. Ga kuma battoci na giya an jera. A tsakiyar gadon mai kama da teburi an saka wani fure mai daukar hankali a cikin wani dan kasko, an kuma ajiye fitila daga gefe daya. Yayin da Amjadu ya ga wannan irin tsari da aka yi wa cikin gidan nan, sai hankalinsa ya tashi, ya tabbata wannan gida na wani mai sukuni ne, ko kuma mai sarauta. Ya ce a cikin ransa, "daga Allah muka fito kuma gare shi za mu koma." Amma ita kuwa matar nan da ta ga yadda aka tsara gidan sai ta cika da farin ciki, ta ce, "wallahi ya kai masoyina, yaronka ya cika umurninka. Dubi yadda ya share gidan tas, ya dafa abinci ya shirya bisa teburi." Ta matsa cikin rumfar nan, ta bude mayanin akushi daya, sai ta ga naman dakwalen kaji soyayye sai wani nash, sh yake yi a cikin mai. Ta jawo abin zama ta zauna tana cewa, wallahi na zo a cikin lokacin da ya dace. Amjadu dai yana tsaye bai kula ta ba, yana ta tunanin abin da zai faru idan mai gidan nan ya same su. Da matar ta ga ya yi tsaye, sai ta taso ta zo wurinsa, ta ce, "m yake damunka, ya masoyina?" Ta yi ajiyar zuciya, ta rungume shi ta sumbace shi. Sa'annan ta ce, "ko dai akwai wata wadda ka shirya wa wannan liyafa, na zo na bata muku shiri? A shirye nake in sha damara, idan ta zo, in yi muku dukan aikace- aikacen da za ku sa ni. " Amjadu ya yi dariya, wadda ba ta kai ciki ba, ya je ya zauna bisa abin zama, gabansa na dar-dar, yana tunani, "ya ya zan kubuta daga mai gidan nan idan ya riske mu?" Ita ma ta zauna tana cike da fara'a da annashuwa, babu abin da yake damunta. Amjadu kuwa ya tsunduma cikin tunani barkatai. Ta jawo akushin nan wanda yake cike da soyayyen naman kaji ta ajiye shi a tsakaninsu, ta bude shi ta fara ci. Ta dubi Amjadu ta ce, "ka ci abinci ya masoyina." Ya sa hannunsa ya yagi naman ya kai bakinsa, maimakon ya ji dadi sai ya ji shi da daci saboda tashin hankali. Ya mayar da hankalinsa ga kofar shigowa gidan, matar kuwa ba ta kula ba. Ta yi ta hadiyar gara sai da ta ji ta kai masabar gatari. Daga nan ta jawo wani akushi cike da 'ya'yan itace, ta ci har ya ishe ta. Ta koma wajen giya, ta balle bakin batta daya, ta bulbula giya har ta cika kasko, ta mika wa Amjadu ita. Ta ce masa, "karbi wannan ka sha, za ta gusar maka da duk wata damuwa da kake ciki." Ya karbi kasko ya kurba, yana cewa a cikin ransa, "ko yaya zan kwashe da maigidan nan, babu makawa zai kashe ni ne." Ya ci gaba da kurbar giya ba tare da ya dauke idanunsa daga kallon kofar gidan ba. Suna cikin haka sai Amjadu ya ji tafiyar mutum, taf, taf, taf, a cikin zaure zai shigo cikin gidan. Nan da nan ya mike da hanzari ya nufi zaure domin ya tari mai shigowa. Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ke muku barka da shan ruwa33 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN Suna cikin haka sai Amjadu ya ji tafiyar mutum, taf, taf, taf, a cikin zaure zai shigo cikin gidan. Nan da nan ya mike da hanzari ya nufi zaure domin ya tari mai shigowa. Matar ta tambaye shi ina za shi? Ya ce mata ya ji ana sallama ne a waje zai je ya dubo. Ya tafi babu ko takalmi a kafarsa. Ashe mai gidan ne tafe, shi ne kuwa Sarkin Fadan garin. Ya gina wannan gida ne domin shan iska a duk lokacin da ya bukata. Yanzu ma ya sa an shirya masa kayan liyafa ne, domin zai zo shan iska da maraice, shi ne ya zo ya duba ya ga ko an shirya kome yadda yake so. Ga mamakinsa sai ya ga kofar gidan a balle. Allah kuwa ya yi Sarkin Fadan nan mutumin kirki ne mai son kyautatawa talakawa, ga shi da saukin kai kamar ruwa. Amjadu ya hadu da Sarkin Fada a cikin zaure, ya yi sauri ya durkusa ya gaishe shi. Sa'annan ya ce, "kafin ka hukunta ni bisa laifin da na aikata maka bari in ba ka labarina tukuna." Ya kwashe labarinsa, tun daga fitowarsu daga birninsu, shi da dan uwansa Asadu, har zuwa haduwarsa da matar da ke cikin gidan da yadda ta balle kofar suka shiga ciki, duk ya fada wa Sarkin Fada. Yayin da Sarkin Fada ya ji labarinsa, ya ji cewa ashe ma dan Sarki ne, sai tausayinsa ya kama shi. Ya riki hannunsa ya ce, "Ya Amjadu, saurari abin da zan umurce ka da shi. Idan ka aikata shi, ka tsira daga abin da kake tsoro. Idan kuwa ka bijire masa, babu makawa in halaka ka." Amjadu ya ce, "umartan ni, Allah ya ba ka nasara." Sarkin Fada ya ce, "da farko dai sunana Bahadaru. Yanzu ka koma wurin matar nan ku ci gaba da liyafarku, kuma ka kwantar da hankalinka. Zan shigo muku a matsayin yaronka, mai yi maka aikace-aikace. Da zarar na shigo ina so ka rufe ni da fada, kana tambaya ta ina na tafi na bar ku kuna jiran makullin gida. Ka sami bulala ka buge ni da ita, sa'annan ka rika saka ni 'yan aikace-aikace. Idan ba ka aikata haka gare ni ba, babu makawa in kashe ka. Kuma na yi maka wannan kyautatawar ne domin kasancewarka bako, ni kuwa ina matukar karrama baki. Ku yi dukan abin da kuke so a cikin wannan gida har gari ya waye, daga nan kowa ya kama gabansa." Sarkin Fada ya umurci Amjadu ya koma cikin gida. Amjadu ya sumbaci hannunsa, ya yi masa godiya sa'annan ya koma wurin matar nan, fuskarsa tana haske, ya jefe ta da murmushi ya ce, "ya masoyiyita, hakika wannan gida ya haskaka da zuwanki. Madalla da wannan ziyara taki mai albarka." Matar ta cika da mamaki, ta ce, "hakika, yanzu ne ka yi maraba da zuwa na, amma da farko ai kamar ba ka yi farin ciki da zuwana ba, duk ka bi ka bata fuska. Amma menene dalilin canzawarka?" Amjadu ya ce, "na rantse da Allah, na yi zaton yarona Bahadaru ya sace mini wasu sarkoki ne, wadanda kudinsu ya kai dinari dubu goma, ya gudu. Amma da na duba da kyau sai na gan su a wurin da na ajiye su. Ko’ina ya tafi ne, ya dade haka bai dawo ba? Ga shi ya sa mun balle kofar gida. Babu makawa in hukunta shi bisa wannan laifi da ya yi." Ta yarda da uzurinsa. Suka ci gaba da ci da sha, suna annashuwa har rana ta kusa faduwa. Daga nan sai ga Sarkin Fada ya shigo musu, ya canza tufafinsa ya sanyo irin na yaran gida. Ya yi damara da wani kyalle, ya sa wasu tsofaffin takalmi. Da zuwansa sai ya fadi kasa ya yi gaisuwa, sa'annan ya mike tsaye ya harde hannuwansa a bayansa, ya sunkuyar da kansa kasa, alamar ya yi laifi. Amjadu ya dube shi ya watsar. Can ya kara duban sa, fuskarsa a turbune, ya daka masa tsawa, "me ya dakatar da kai zuwa wannan lokaci, sakaran yaro!" Sarkin Fada ya fara yan kame-kame, ya ce, "ya shugabana, wallahi na tafi bakin teku ne domin in wanke tufafina. Ban san da rana za ka zo nan ba, na aza sai cikin dare." "Ka yi karya!" Amjadu ya daka masa tsawa. "babu makawa in hukunta ka bisa wannan laifi da ka yi." Ya dauko bulala, ya umurci Sarkin Fada ya kwanta. Ya yi ta tsala masa bulala. Matar nan ta tashi da fushi ta karbe bulalar daga hannun Amjadu, ta yi ta dukan Sarkin Fada da bulalar nan iyakar karfinta. Sarkin Fada ya yi ta hargowa yana cije hakori don zafin bulala, har sai da ya fitar da hawaye. Da Amjadu ya ga abin nata na nema ya wuce minsharri, sai ya kwace bulalar daga hannunta yana cewa, rabu da shi haka nan. Ita kuma tana cewa, ka bari a kara masa, don kada gobe ya sake aikata kuskure irin wannan. Amjadu bai saurare ta ba. Shi kuwa Sarkin Fada, Bahadaru, sai ya mike yana matse hawaye daga idanunsa, ya koma gefe guda ya takure yana jiran ya ji umurnin da za a ba shi. Ya tashi ya share dukan gidan, ya kunna shama'u, ya shirya musu shimfidar da za su kwanta. Duk kai-da-kawon da Bahadaru ke yi, babu abin da matar nan ke yi sai faman yi masa tsawa da zagi, ta uwa ta uba. Amjadu ya kufula, ya yi mata tsawa ya ce, "ki rabu da shi haka mana, bai saba da irin wannan fada da kike yi masa ba." Haka dai su Amjadu suka ci gaba da kwasar liyafa har dare ya tsala, Bahadaru kuma ya koma gefe ya makure, nan da nan barci ya kwashe shi saboda dawainiyar da ya sha, ga kuma zafin bulala. Bai jima ba cikin barcin sai ya fara jan rago. Da matar nan ta ji ya fara jan rago, ga shi kuma ta bugu da giya, sai ta ce da Amjadu lalle sai ya dauki takobi ya sare kan Bahadaru, ko kuma ita tashi ta kashe shi da hannunta, domin ita dai ta tsane shi. Amjadu ya tambaye ta don me za ta kashe masa yaro? Ta ce, muddin yana cikin gidan nan ba za ta iya kwana cikinsa ba. Ta tashi ta dauki takobi tana cewa, "idan kai ba za ka iya kashe shi ba, bari ni in kashe shi." Da Amjadu ya ga dai da gaske take yi, ya tuna irin halascin da Bahadaru ya yi masa, sai ya karbe takobin daga hannunta, ya ce, "babu wanda ya kamata ya kashe mini yaro face ni." Da ya amshi takobin daga hannunta, kafin ta farga sai ya dauke kan ta da shi. Kan ya yi tsalle sama ya fada ga jikin Bahadaru da ke barci, gangar jikin kuma ta fadi can gefe guda. Nan take Bahadaru ya farka, ya tashi zaune. Ya ga Amjadu tsaye kusa gare shi, yana rike da takobi, wadda jini ke diga daga jikin sa. Ya duba haka, sai ya ga gawar mace. Ya tambayi Amjadu abin da ya faru. Ya fada masa kome, ya kara da cewa, "babu abin da ta so kamar ta kashe ka, wannan shi ne sakamakonta." Bahadaru ya mike tsaye ya sumbaci hannun Amjadu ya ce, "kash, ai da ka yi mata afuwa. Amma tunda abin ya zamo haka, sai mu yi kokari mu rabu da gawarta kafin gari ya waye." Ya shiga wani daki ya dauko tabarma ya nade gawar, ya samo katon kwando mai murfi ya saka ta ciki, ya mayar da murfin ya rufe. Ya ce da Amjadu, "ka ga kai bako ne, ba ka san ko'ina ba a cikin wannan birni. Ka zauna cikin wannan gida ka jira dawowa ta, zan tafi da wannan gawa in jefa ta cikin teku. Idan na dawo zan kyautata maka matukar kyautatawa, zan taimake ka wajen bidar dan uwanka da ya bace. Idan kuma rana ta yi ban dawo ba, to, watakila ni tawa ta kare. Ka zauni wannan gida da dukan abin da ke cikinsa na dukiya, na mallaka maka su." Yana gama fadin haka sai ya saba kwandon nan bisa kafadarsa ya fita, ya dauki hanyar zuwa bakin teku. Yayin da ya isa bakin teku sai ya gamu da 'yan doka suna sintiri. Da shugabansu ya gan shi sai ya shaida shi, ya yi mamakin abin da ya kawo shi bakin ruwa, cikin wannan tsohon dare, dauke da kaya niki-niki. Shugaban 'yan doka ya bukaci ya ga abin da ya dauko, sai Bahadaru ya fara 'yan noke-noke. Da suka ga dai alamar ba ya da gaskiya sai suka kwace kwando daga hannunsa, suna budewa sai suka ga matacciyar mace nannade a cikin tabarma. Nan take suka buga masa sarka ga hannunuwa suka tafi da shi suka kulle. Da gari ya waye suka yi kwashe shi tare da kwandonsa sai gidan Sarki, suka fada wa Sarki abin da ya faru. Sarki ya husata da jin wannan abu, ya dubi Bahadaru ya daka masa tsawa, "Allah wadaranka, ashe dai kai barawo ne, mai kashe mutane yana kwashe musu dukiya. Mutum nawa ka kashe a cikin wannan birni?" Bahadaru ya dukar da kansa kasa bai ce kome ba. Sarki ya kara daka masa tsawa, "wa ya kashe wannan mace?" Ya amsa, "ni na kashe ta, Allah ya ba ka nasara. Babu tsimi babu dabara face daga Allah madaukakin Sarki." Sarki ya kara husata don jin wannan amsa tasa, nan take ya ba da umurni a tsire shi. Dogarawa suka cafe shi, suka yi waje da shi domin zagayawa da shi a cikin gari kafin a kai shi wurin da za a tsire shi kamar yadda Sarki ya yi umurni. Mai shela ya tafi tare da su cikin birni, kwararo-kwararo, lungu-lungu, yana sanar da jama'a cewa duk mai son ganin yadda za a tsire Bahadaru Sarkin Fada, to, ya hallara kofar fada. Amjadu kuwa ya zauna a cikin gida yana jiran dawowar Bahadaru, har gari ya waye rana ta fito, bai dawo ba. Ganin haka sai Amjadu ya ce, "babu tsimi babu dabara face daga Allah mai girma da daukaka. Yalla ko wani abu ya faru gare shi." Yana nan yana jimamin abin a cikin ransa, sai ya ji mai shela yana shelar za a tsire shi a kofar gidan Sarki da tsakiyar wannan rana. Yana jin wannan shela sai hankalinsa ya tashi tausayin sa ya kama shi har ya zubar da hawaye. Ya ce a cikin ransa, "wannan mutum da tawakkali yake, shi ya yarda ya amsa laifin da ba shi ne ya aikata ba domin kawai ya kubutar da ni daga halaka. Na rantse da Allah ba zan bari a kashe shi ba bisa laifin da ba shi ne ya aikata ba." Nan take ya zabura ya rufe gida, ya bi bayan mai shela har ya cim masu. Yayin da ya same su sai ya ce da Sarkin Dogarai, "ranka ya dade kada ku kashe wannan mutum, domin ba shi ne ya kashe matar ba. Ni ya kamata ku kashe'. Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ ke tare daku a awannan lokaci34 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN Amjadu kuwa ya zauna a cikin gida yana jiran dawowar Bahadaru, har gari ya waye rana ta fito, bai dawo ba. Ganin haka sai Amjadu ya ce, "babu tsimi babu dabara face daga Allah mai girma da daukaka. Yalla ko wani abu ya faru gare shi." Yana nan yana jimamin abin a cikin ransa, sai ya ji mai shela yana shelar za a tsire shi a kofar gidan Sarki da tsakiyar wannan rana. Yana jin wannan shela sai hankalinsa ya tashi tausayin sa ya kama shi har ya zubar da hawaye. Ya ce a cikin ransa, "wannan mutum da tawakkali yake, shi ya yarda ya amsa laifin da ba shi ne ya aikata ba domin kawai ya kubutar da ni daga halaka. Na rantse da Allah ba zan bari a kashe shi ba bisa laifin da ba shi ne ya aikata ba." Nan take ya zabura ya rufe gida, ya bi bayan mai shela har ya cim masu. Yayin da ya same su sai ya ce da Sarkin Dogarai, "ranka ya dade kada ku kashe wannan mutum, domin ba shi ne ya kashe matar ba. Ni ya kamata ku kashe, domin kuwa na rantse da Allah ni ne wanda ya kashe ta." Da Sarkin Dogarai ya ji haka sai mamaki ya kama shi, ya kwashe su gaba daya suka koma wurin Sarki. Ya fada wa Sarki abin da Amjadu ya ce. Sarki ya juya wurin Amjadu ya tambaye shi, "kai ne ka kashe yarinya?" Amjadu ya amsa, "na'am, ya Sarki." Sarki ya kuma tambayarsa, "me ya sa ka kashe ta? Maza gaya mini, kuma kada ka zanta mini face gaskiya." Amjadu ya ce, "Allah ya ba ka nasara, hakika labarina abin mamaki ne, wanda da za a rubuta shi da tsinin

Chapter 10 of 14