Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 14
hannunsa daga hannun bawa, ya nufi gidan cikin sauri, ya bar bawa a baya. Bawa ya cika da mamaki yana cewa a cikin ransa, "Ban taba ganin mai gaggawar tura kansa ga halaka ba kamar wannan saurayi, anya kuwa kansa daya?" Ya daga murya ya ce, "Kai wannan mai gaggawar kai kansa ga halaka, dakata tukuna in zo." Kamaruzzaman bai tsaya ya saurare shi ba, ya ci gaba da sauri har ya riga bawa isa kofar gidan. Da suka isa kofar gidan, bawan dake tsaron kofa ya bude musu kofa, ya yi musu rakiya cikin gidan har zuwa bakin kofar dakin gimbiya Badura, wanda kofarsa take a bude sai dai akwai labule wanda ya rufe bakin kofar. Kamruzzaman ya ce da bawa, "Shin in warkar da ita daga nan bakin kofa, ba tare da na shiga wurinta ba? Ko kuwa in shiga inda take?" Bawa ya yi mamaki da jin wannan magana, ya ce, "Idan ka warkar da ita daga nan bakin kofa ba tare da ka gan ta ba, shakka babu, ka cika boka uban bokaye, kamar yadda na ji kana ta kankambar yayatawa." Jin haka sai Kamaruzzaman ya yi murmushi, ya zauna a bakin kofar. Ya saka hannunsa cikin jakar da ya zo da ita, ya dauko takarda da alkalami da tawwada, ya fara rubutu kamar haka: Wannan rubutu ne daga hannun wanda soyayya ta raunata, wanda bege ya haukata, wanda ya gwammace wa mutuwa a kan ya rayu ba tare da abar begensa ba. Shi ne wanda babu mai tausayin halin da zuciyarsa ta shiga, wanda a kodayaushe yake ganin dare kamar yadda ya ga rana, wanda jikinsa ya rame saboda tunani, da dai bai koma jin labarin abar begensa ba tun bayan rabuwarsu. Daga nan sai ya rubuta wadannan baitoci: "Na yi rubutu da zuciyar da ta dabaibaye a cikin sonta. Na yi kukan kadaici har hawayena sun zama jini, jikina ya zama daurarre a cikin sarkar begenta. Tufafi sun zama tsumma a jikina domin rashin wanka da wanki. Ba na zargin kowa a kan halin da na shiga face ke. Hakuri ya wuyata a gare ni face na yi tozali da abar begena." Sai ya ci gaba da rubutun wasikar: Ciwon zuciyata ya kusa warkewa domin tana gab da saduwa da wadda take kauna, wadda in ba ita ba, sai Allah ne kawai zai iya warkar da ita. Tsakanin ni da ke na san babu yaudara a cikin soyayyarmu, idan kuwa akwai Allah ya cire ta daga zukatanmu. Babu amintacce abin amincewa kamar masoyi mai tsare asirin masoyinsa da gaskiya. Sai kuma ya rubuta wadannan layukan a matsayin kammalawa: Daga mutumin da soyayya da kauna suka rikita, daga masoyin da soyayya ta yi wa dabaibayi ta daure shi a cikin kurkuku. Daga Kamaruzzaman dan Sarki Shahruzzaman, zuwa ga shugabar kyawawa ta duniya, daya daga cikin Hurul Aini, gimbiya Badura 'yar Sarki Gayur. Ki sani cewa tun lokacin da na farka da dare na gan ki kwance kusa gare ni, da gari ya waye na neme ki na rasa, tun lokacin na rasa kaina. Na kasance cikin ciwo mai hauhawa, na kasance mai zubar da hawaye babu kakkautawa, na kasance marashin barci dare da rana, na kasance bawan soyayya wanda idonsa ba ya rabo da zubar da hawaye. Na kasance mai kunar zuciya a kodayaushe. Daga kasan takardar ya rubuta wannan baiti: "Amincin Allah ya tabbata a gare ta, ita ce wadda ta mallake zuciyata don kyawunta." Da kuma wannan baiti: "Ga zobenta nan da na musaya da nawa, ina fatar haduwarmu za ta maido mini da zobe nawa." Kamaruzzaman ya cire zoben Badura ya nannade shi tare da takarda, ya like bakin takardar. Ya mika wa bawa ya ce ya shiga ya kai mata wannan takarda. Bawa ya riki takarda ya shiga wurin Badura. ****** ****** ****** Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan akasuwa yanzu haka.... whatsapp only pls 08032767547(17) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN Kamaruzzaman ya cire zoben Badura ya nannade shi tare da takarda, ya like bakin takardar. Ya mika wa bawa ya ce ya shiga ya kai mata wannan takarda. Bawa ya riki takarda ya shiga wurin Badura. Lokacin da Badura ta karbi takarda ta bude, sai ta ga zobenta a ciki, nan take ta fara dawowa cikin hayyacinta. Ta karanta takarda gaba daya, ta fahimci sakon da ke cikinta gaba daya. Ta fahimci cewa masoyinta ne, abin begenta, farin cikin rayuwarta, abin tunaninta, shi ne yake waje a kofar dakinta wanda labule ne kawai ya raba su. Sai ta ga abin kamar mafarki ne take yi, ta waka wadannan baitoci biyu: "Hakika na yi nadama na yi takaici, Don rabuwarmu da kai ya masoyi. Hawaye ya yi kwarara babu iyaka, Kullum fatana na gane ka masoyi. Tana gama wannan waka sai ta ji wani irin karfi ya shige ta. Ta riki sarkar da ta yi mata zobe ga wuya, ta takura iyakar karfinta, ta bude zoben, ta cire sarkar daga wuyanta ta watsar. Ta kuma tsinka ta kafafunta, kamar mai tsinka rubabbiyar igiya, ta zubar a kasa. Ta hankade labulen kofar daki, ta yi ido hudu da Kamaruzzaman. Nan take ta fada ga jikinsa, suka rungume juna suna hawayen farin ciki. Bakunansu suka hade suna tsotsar yawun juna, tamkar bakunan uwar tattabar da 'yarta yayin da take ba ta abinci. Bayan sun dade a cikin wannan hali, sai suka saki juna kowa na kallon dan uwansa. Badura ta ce, "Ya masoyina, shin idona biyu ko kuwa mafarki nake yi? Allah mai jin tausayin bayinsa ya kara hada mu bayan rabuwarmu? Tsarki ya tabbata ga Allah da ya sake hada mu tare." Yayin da bawa ya ga wannan abu, sai ya dimauta, ya zura a guje bai garje ko'ina ba sai a gaban Sarki Gayur. Ya fadi ya yi gaisuwa, sa'annan ya ce, "Allah ya taimake ka, Wallah ban taba ganin cikakken mai magani ba kamar wannan saurayi. Wannan ai shi ne shugaban dukkan ma su ba da magani na duniya, domin kuwa ya warkar da 'yarka ba tare da ya shiga inda take ba, daga bakin kofa ya bayar da maganin aka kai mata, nan take ta koma cikin hankalinta." Nan take Sarki ya mike tsaye, kamar wanda aka soka da allura, ya dubi bawa ya ce, "Ka tabbata ba karya kake fada mini ba?" Bawa ya ce, "Wa ni nan in yi maka karya, Allah ya ba ka nasara? Idan ba ta warke ba, ta yaya za ta sami karfin da za ta iya tsinke sarkar da aka daure ta da ita har ta fito da gudu ta rungume saurayin tana sumbatarsa? Allah ya ba ka nasara, kamata ya yi ka tafi da kanka, ka ganar ma idonka, don an ce gani ya kori ji." Sarki ya zabura ya nufi gidan da 'yarsa take, bai ko kula da ya hau doki ba. Yayin da ya isa gidan, gimbiya Badura ta gan shi, sai ta rufe fuskarta don kunya, ta waka wadannan baitoci: "Banin son waninsa idan ba shi ba, Don me zan ambaci waninsa bayan ga shi? Kada a aurar da ni ga waninsa face shi, Ni tasa ce shi kuma nawa ne babu kyashi." Yayin da Sarki ya ji wakarta, ya tabbatar da ta sami lafiya, sai ya ji kamar ya tashi sama don murna, ya sumbaci goshinta saboda tsananin son da yake yi mata. Ya juya wurin Kamaruzzaman ya tambaye shi labarinsa, da kuma inda ya fito. Kamaruzzaman ya fada masa sunansa da sunan mahaifinsa da kuma kasar da ya fito. Ya kwashe labarin abin da ya faru tsakaninsa da gimbiya Badura a daren da suka ga juna, da yadda ya cire zobenta, duka ya fada wa Sarki Gayur. Sarki ya yi mamaki, matukar mamaki. Ya ce, "Babu shakka wannan labari naku bako ne, akwai abubuwan mamaki a cikinsa. Ya kamata a rubuta shi cikin littafi a ajiye domin 'yan baya su karanta sa'annan su karu da darussan dake ciki." Bayan sun koma fada, Sarki ya kira alkalai ya sa suka rubuta takardar shaidar auren Badura da Kamaruzzaman, aka saka ranar daurin aure. Sarki ya yi umurni da a kawata birni kafin zuwan ranar daurin aure. Aka kawata birni da kayayyaki na kawa, masu kyau da daraja. Da ranar daurin aure ta zo, mutane suka taru daga kowane yanki na kasar Sin, suka shaidi auren gimbiya Badura da Kamaruzzaman. Aka yi shagalin da ba a taba yi ba a duk tsawon tarihin kasar Sin. Kamaruzzaman ya tare da amaryarsa a daren farko, suka debe kishirwar begen juna. Kashe gari Sarki ya shirya kasaitacciyar walima, ya gayyaci jama'ar jazirorin Jawariyya, da na jazirorin Basaraniyya. Aka gabatar da abin nishadi na daga kade-kade da bushe-bushe. Aka jera kabukkan abin ci, da kasaken abin sha. Aka tabbata kan haka tsawon wata guda, sa'annan kowa ya kama gabansa. Kamaruzzaman na zaune da matarsa cikin farin ciki da kwanciyar hankali, sai rannan da dare ya yi mafarki da mahaifinsa, Sarki Shahruzzaman. A cikin mafarkin ya ji mahaifinsa na cewa, "Don me za ka guje mini, ya dana? Wane laifi na yi maka wanda na cancanci irin wannan hukunci daga gare ka?" Sai ya ji yana waka wadannan baitoci: "Hakika watan duhu ya gan ni abin tsoro, Na bude kuben idona ga duban taurarinsa. Ya zuciya jinkirta mini ko zai juyo gare ni, Ku ji kaina ga abin da aka jarrabe ni a kansa." Daga karshen wakar sai ya ji mahaifin nasa ya ce, "Ya dana, haka da ka yi mini ka kyauta ke nan?" Nan take Kamaruzzaman ya farka daga barci, zuciyarsa ta koma gida wurin mahaifinsa. Da gari ya waye, sai Badura ta lura da cewa yanayin mijinta ya canja ba kamar yadda ta saba ganinsa ba. Ta tambaye shi dalili, ya fada mata mafarkin da ya yi. ............ Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwa' kuna iya saye don morewa karanta DADa dan labarai irin wannan... YUSUF A JIBAGA' KETARE DAKU(19) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN Bayan Kamaruzzaman ya huta sosai sai ya tashi ya nufi kofar shiga wannan birni, wanda bai san kowane birni ne ba. Ya shiga cikin birni yana tunanin inda zai nufa. Amma ga mamakinsa, sai bai ga mutum ko daya ba a cikin wannan birni, ya ci gaba da tafiya har ya kusa isa daya kofar birni wadda ake shigowa daga bangaren teku. Birnin ya kasance yana kan gabar teku ne, don haka yana da kofofi guda biyu, daya wadda ake shigowa daga bangaren da babu teku, ita ce wadda Kamaruzzaman ya shigo ta cikinta, daya kofar kuma ana shigarta ne daga bangaren teku. Yayin da Kamaruzzaman ya nufo wajen bangaren teku na birnin, sai ya iso wani makeken fili inda mutanen birnin suke yin lambuna. Ya zo ga kofar wani lambu da aka zagaye da katanga, mai lambun na ganinsa sai ya yi sauri ya fito, ya yi wa Kamaruzzaman sallama, ya amsa masa sallamarsa. Da mai lambu ya ji Kamaruzzaman ya amsa masa sallama, sai ya ce, "Tsarki ya tabbata ga Allah madaukakin Sarki. Yi sauri ka shigo daga ciki kafin wani mutumin wannan birni ya gan ka." Ya riki hannun Kamaruzzaman ya ja shi zuwa cikin lambu. Kamaruzzaman bai yi gardama ba, ya bi mai lambu suka shiga daga ciki yana mamaki. Da suka shiga cikin lambu sai Kamaruzzaman ya tambayi wannan mai lambu, wanda ya kasance tsoho ne, shekaru sun yawaita a kansa, ya ce da shi, "Baba, wane birni ne wannan? Kuma don me kake tsoron wani daga cikin mutanen wannan birni ya gan ni?" Mai lambu ya ce, "Ka sani ya kai dana, mutanen wannan birni matsafa ne. Yaya aka yi ma har ka zo wannan birni?" Kamaruzzaman ya kwashe dukkan labarinsa ya fada wa tsoho mai lambu. Mai lambu ya cika da mamaki, matukar mamaki, ya dubi Kamaruzzaman ya ce, "Ikon Allah! Lalle wannan al'amari naka abin mamaki ne. Ka sani cewa daga wannan birni zuwa birnin musulmin dake kusa gare mu, tafiyar wata hudu ce a cikin teku, idan kuma ta kasa ne, to, tafiyar shekara daya ce cur. Duk shekara akwai jirgin ruwa da yake kawo kayan masarufi daga tsibiran birnin Labunus, wanda yake shi ne birnin musulmi mafi kusa da wannan birni. Idan ya kawo kayan masarufin yakan debi kayan lambu ya koma da su, ya ajiye wasu a birnin Labunus ya wuce da wasu a birni Kalidan, birnin mahaifinka. Daga nan kuma wannan jirgi ba zai sake dawowa ba sai wata shekara. Ka kuwa yi sa'a, yau saura wata uku wannan jirgi ya zo." Kamaruzzaman ya yi shiru yana jujjuya maganar mai lambu a cikin ransa, ya ga dai babu abin da ya fi face ya jira zuwan wannan jirgi nan da watanni uku. Ya juya wurin mai lambu ya ce masa, "Ko za ka yarda na zauna nan wurinka, in rika taimakonka ga aikace-aikacen lambunka?" "Me zai hana?" In ji mai lambu, "Ko banza na tsufa ga shi ba ni da wani mai taimako." Mai lambu ya kawo wata 'yar guntuwar riga, iya gwiwa mai launin shudi, ya ba Kamaruzzaman ya saka, ya cire tufafinsa masu kyau ya ajiye. Ya koya masa yadda ake ban ruwa, da yadda ake budi, da kuma noma. Kamaruzzaman ya ci gaba da taimakon mai lambu kullum. Idan yana cikin aiki ya tuna da mahaifinsa ko Badura, sai ya yi ta zubar da hawaye yana wake-wake. Al'amarinsa ke nan. Amma Badura kuwa, yayin da ta farka daga barci, ta duba kusa gare ta, ba ta ga Kamaruzzaman ba, sai kuma ta lura da an warware mata kubakar wando, ta nemi dan dutsen da ta nannade a kubakar wandon ta rasa. Ta ce a cikin ranta, "Babu Sarki sai Allah." Ta tabbatar da cewa hakika wani bakon al'amari ya faru gare shi na daga asirin dake jikin wannan dan dutse. Domin kuwa Kamaruzzaman ba zai bar ta ba, tsawon wannan lokaci, ba tare da ya dawo ba. Ta so ta fada wa bayi da kuyangi batan Kamaruzzaman sai ta ji tsoron kada su ji tsoro su ce za su koma da baya, ko kuma su yi mata tawaye. Saboda haka sai ta bude kyankyandin da Kamaruzzaman yake ajiye tufafinsa, ta dauko babbar riga da wando da rawani. Ta saka kayan, ta nada rawani, ta yi amawali, kamar dai yadda Kamaruzzaman yake yi. Ta fita daga cikin tanti, ta kirawo wata amintacciyar kuyanga tata, ta fada mata kome, da kuma nufinta na son su isa birnin Kalidan, Kasar mahaifin Kamaruzzaman, ba tare da sauran bayi da kuyangi sun gane Kamaruzzaman ba ya tare da su ba. Ta yi wa kuyanga shiri da tufafinta, kamar ita ce gimbiya Badura. Ta fito cikin bayi, babu wanda ya gane ta, da ma kamarsu daya da Kamaruzzaman, a fuska da kuma jiki. Ta bayar da umurni a aza wa dabbobi kaya a ci gaba da tafiya. Nan take bayi suka cire tantina, aka dora wa dabbobi kaya, aka kawo mata dokin Kamaruzzaman ta taka ta hau, aka jawo wa kuyangarta dokin Badura, ita ma ta hau, ayari ya motsa, suka ci gaba da tafiya. Suka ya ta tafiya kwana da kwanaki ba tare da sun tsaya ba har suka fara hango gine-ginen wani birni can nesa da su. Da suka zo gab da birnin, sai Badura ta ba da umurni a sauka a huta a bakin kofar wannan birni, ta tura wani bawa da ya shiga cikin birni ya samo musu labarin sarkin birnin da yanayin jama'arsa. Aka sauke wa dabbobi kaya, aka kafa tantina, kafin dan aike ya dawo. Bayan wani dan lokaci sai ga bawan nan ya dawo, ya ce wa Badura, "Allah ya ba ka nasara, sunan wannan birni Labunus, jama'arsa kuwa duka musulmi ne. Sunan Sarkinsu Armanus, yana da wata kyakkyawar 'yarsa da yake tsananin kauna, sunanta Hayatunnufusi." ............ Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwa' kuna iya sayen sabon fassaran dare dubu da daya'.... Whatsapp only pls 08032767547(20) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN Dan aike ya dawo ya ce wa Badura, "Sunan wannan birni Labunus, jama'arsa kuwa duka musulmi ne. Sunan Sarkinsu Armanus, yana da wata kyakkyawar 'yarsa da yake tsananin kauna, sunanta Hayatunnufusi." Badura ta sallami bawa, ta fada wa sauran bayi da kuyangi cewa, za su huta a wannan wuri na kwana biyu kafin su shiga cikin birni su ga Sarki. To, ashe kuma lokacin da tawagar Badura suka sauke kayansu labari ya kai ga kunnen Sarki, sai shi kuma nan da nan ya tashi dan rahoto domin ya samo masa labarin mutanen da suka sauka a bayan garinsa. Dan rahoto ya koma ya shaida wa Sarki cewa, tawagar wani dan Sarki ce wai shi Kamaruzzaman dan Sarki Shaharuzzaman na birnin Kalidan, hanya ta biyo da su ta nan suka ya da zango. Da jin haka, sai Sarki Armanus ya hawo tare da wasu fadawansa ya nufi bayan gari domin ganin wannan bakon dan Sarki. Yayin da Sarki da fadawansa suka iso wurin da tantinan nan suke, sai Badura ta fito daga cikin tantinta, tana cikin shigar Kamaruzzaman, ta zo gaban Sarki ta fadi ta yi gaisuwa, Sarki ya amsa mata, sa'annan ya ce bai kamata su zauna a wannan wuri ba, su kwashe kayansu su shiga cikin gari. Suka bi umurnin Sarki, suka cire tantina, suka labta wa dabbobi kaya, suka rankaya cikin birni. Aka saukar da bayi da kuyangi a gidan baki, ita kuwa Badura Sarki ya saukar da ita a wani bangare na gidansa. Bayan kwana uku sai rannan Sarki Armanus ya shiga bangaren da aka saukar da Badura, ya kuwa same ta ba ta dade da fitowa daga wanka ba, fuskar nan tata tana sheki kamar farin wata, amma tana cikin tufafi na maza ne, wadanda aka yi wa kwalliya da zinariya da lu'ulu'u. Bayan Sarki ya zauna sai ya ce, "Ya dana, na zo neman wata alfarma ne a gare ka." Badura ta ce, "Wace alfarma kake nema a gare ni, Allah ya ba ka nasara?" Sarki ya ce, "Ka sani cewa shekaru sun yawaita a kaina, na fara tsufa har sha'anin mulki na neman ya gagare ni, ga shi ba ni da magaji namiji. Amma ina da 'ya daya, wacce kusan kamarku daya a wajen kyau. Idan ka yarda, ina so in aura maka ita, ni kuma in yi murabus in nada ka a matsayina." Yayin da Badura ta ji zancen Sarki Armanus, sai ta sunkuyar da kanta kasa, nan take zufa ta tsattsafo daga goshinta, kunya kuma ta rufe ta. Ta ce a cikin zuciyarta, "Kaka-tsara-kaka, yau fa ana dara ga dare ya yi. Yanzu idan na fada masa gaskiya cewa ni mace ce ya ya zai ji? Kuma a wane matsayi zai dauke ni? Kuma ni ba abin na gudu ba cikin dare, na san zai sa a kamo ni, watakila idan ya yi fushi da ni ya sa a kashe ni. Babu abin da ya fi face in amince da bukatarsa, daga baya na san dabarar da zan yi." Sai ta daga kanta, ta ce da Sarki, "Allah ya ba ka nasara, na ji, na amince." Sarki ya cika da farin ciki, ya tashi ya fita wurin jama'arsa ya fada musu abin da ake ciki, ya kuma ce musu a je a fara kawata birnin Labunus da kewayensa, a shiga shirye-shiryen kasaitaccen bukin auren 'yarsa da bakon dan Sarki. Washe gari Sarki ya kira dukkanin hakimansa, da Waziransa, da alkalai da limamai da fadawansa da jama'ar gari. Ya sauka daga karagar mulkinsa ya dora Badura a matsayin sabon Sarkin Labunus, ya umurci dukkanin mahalarta da su yi mata mubayi'a. Daga nan dukkanin jama'a suka rika zuwa daya bayan daya suna yi wa Badura Mubayi'a, babu daya daga cikinsu da ya gane cewa mace ce, dukkansu sun dauka cewa dan Sarki ne, suna masu tsananin mamakin baiwar da Allah ya yi masa ta kyau da kwarjini da farin jini. Bayan jama'a sun gama yi wa Badura mubayi'a, bisa al'adar kasar Labunus, aka buga ganguna domin tabbatar da nadin sabon Sarki. Daga nan kuma sai tsohon Sarki Armanus ya shiga shirye- shiryen auren 'yarsa Hayatunnufusi da sabon Sarki. Da ranar daurin aure ta zo, mutane suka hadu daga kowane bangare na tsibiran kasar Labunus. Ango da amarya suka zauna wuri guda, fuskokinsu na haske, kai ka ce watanni biyu ne suka jera. Aka yi dukkan abubuwan da za a yi na al'ada, aka rubuta takardar auren Kamaruzzaman da Hayatunnufusi, daga nan kuma sai aka goce da shagali. Aka yi kwana bakwai ana buki sa'annan kowa ya kama gabansa. A daren da amarya za ta tare, mata suka je suka gyara mata dakinta, aka shimfida shimfidu masu daraja, aka saka labulayye a kowane bango na dakin. Ango ya fara shiga ya zauna yana jiran isowar amarya, zuwa wani dan lokaci, sai ga tsofaffi sun rako amarya zuwa dakinta. Da suka iso da ita a bakin kofar dakin, sai suka tura ta ciki, su kuma suka koma abinsu. Yayin da Badura ta ga tsofaffi masu kawo amarya sun tafi, an bar su su biyu kadai a cikin daki, sai ta tuna da mijinta Kamaruzzaman, hawaye suka zubo daga idanunta. Ta yi tagumi tana tunani. Yayin da ta gama tunaninta sai ta riki hannun Hayatunnufusi, ta zaunar da ita bisa shimfida, ta sumbaci goshinta. Ta tashi ta dauki buta, ta shiga bandakin da ke cikin dakin, ta yi alwala. Ta dawo cikin dakin ta kabbarta salla. Duk lokacin da ta yi raka'a biyu sai ta sallame, ta tashi ta kabbarta wata. Ba ta daina salla ba, sai da ta lura cewa barci ya dauke Hayatunnufusi, sa'annan ta sallame, ta yi addu'o'in da za ta yi, ta je ta kwanta kusa ga Hayatunnufusi. Da gari ya waye Badura ta riga Hayatunnufusi tashi daga barci, ta shirya ta nufi fada. Tsohon Sarki da matarsa, mahaifiyar Hayatunnufusi, kuwa suka shiga wurin 'yarsu. Bayan sun shiga cikin dakin, sai mahaifiyar Hayatunnufusi ta dubi shimfidar da 'yarta ta kwana tare da angonta, amma ba ta ga abin da take son gani ba. Sarki ya tambayi 'yarsa yadda suka kwana. Hayatunnufusi ta kwashe labari ta fada musu har da wakar da ta ji angon nata ya rera. Mahaifanta suka fahimci dai babu wani abu da ya shiga tsakaninsu a wannan dare na sha'anin miji da mata. A fada kuwa Bdura ta harde bisa karagar mulki, fadawa sai faduwa suke yi a gabanta suna kwasar gaisuwa. Ta nada ta tube, ta yi hukunci, ta sallami 'yan jarun da suka cancanci sallama, ta daure masu laifi da suka cancanci daurewa. Ta ba askarawa umurni, ta rarraba taimakon kudi ga mabukata, ta yi kyautar tufafi ga hakimai da fadawanta. Jama'a suka yi san barka ga wannan sabon Sarki nasu mai adalci da yawan alheri, suka rika yi wa sabon Sarki addu'ar dorewa a kan karagar mulki, babu daya daga cikinsu da ya gane mace ce. Haka Badura ta ci gaba da jan ragamar mulki har dare ya yi, aka tashi daga zaman fada. Ta shiga gida wurin Hayatunnufusi. Ta same ta zaune a kan shimfida ta shirya mata abinci kala-kala. Ta zauna suka ci abinci tare, suka sha abin sha, da lokacin barci ya yi, Hayatunnufusi ta saka tufafinta na barci ta zauna bisa shimfida tana jiran angonta. Badura ta je ta zauna kusa gare ta, ta sumbaci goshinta, ta tashi ta shiga bandaki ta yi alwala, ta fito ta fara salla. Ba ta daina yin salla ba sai da ta ga barci ya yi awon gaba da Hayatunnufusi, sa'annan ta sallame salla, ta yi addu'o'in da za ta yi, ta je ta kwanta kusa gare ta. Da gari ya waye, ta tashi ta yi salla ta kimtsa ta nufi fada, ta bar Hayatunnufusi tana barci. Ta je ta kame bisa karagar mulki, ta yi umurni ta yi hani, tsawon wannan rana. Bayan Badura ta fita zuwa fada sai Sarki Armanus da matarsa suka shiga wurin 'yarsu domin su ji yadda ta kwana da angonta. Hayatunnufusi ta kwashe labari ta fada musu tare da wakar da ta ji Badura ta rera, ta kara da cewa, "Ya mahaifina, wallahi ni dai ban taba gani miji mai ibada kamar wannan miji nawa ba, babu abin da yake yi tsawon dare daga kuka da waka sai salla." Sarki ya ce, "Zancen banza! An fada masa cewa an kawo masa ke ne domin ya koya miki kuka da waka? Ko kuwa salla ce ba ki iya ba da zai koya miki? Ga shi tsufa ya zo mana muna so mu ga jikokinmu kafin mu mutu amma ya tsaya shiririta. To, ki fada masa aure kika zo yi ba koyon kuka da waka ba. Idan muka dawo gobe, rana ta uku ke nan, ba tare da wani abu na tsakanin mata da miji ya wakana a tsakaninku ba, babu makawa zan tube shi daga matsayin da na dora shi a kai, in kuma sa a yi masa korar kare daga wannan birni namu." Sarki da matarsa suka fita fuu, cikin fushi. ............ . GOBE ZANCI GABA' INSHA ALLAH (21) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN Sarki Armunus da matarsa, mahaifiyar Hayatunnufusi, suka fita daga wurin gimbiya Hayatunnufusi cikin fushi. Bayan dare ya yi, an tashi daga fada, sai Badura ta shiga gida, ta tarar da Hayatunnufusi ta shirya mata abinci da abin sha, tana jiran dawowarta. Bayan ta zauna sun ci sun sha sun koshi, sai ta tuna da mijinta Kamaruzzaman, ta tuna daren amarcinta da shi, ta yi ajiyar azuciya, hawaye suka zubo daga idonta, ta rera wadannan baitocin waka: "Rabuwarmu ta kasance hukunci ne na Allah, tamkar rana mai rabuwa da haskenta zuwa ga kowace jigawa, tana furata ishara tata, ina fahimtar rubutunta. A kullum begena ya kan zama mai daduwa, ba shi karewa. Ni na ki hakuri, domin kuwa hakuri abin ki ne yayin bege. Zuciya ta kuntata, ta raunana. Amma an ce duhu yakan yaye idan asuba ta zo." Tana gama waka sai ta sumbaci Hayatunnufusi a kan goshinta, ta mike za ta shiga bandaki domin ta yi alwala sai Hayatunnufusi ta rike mata riga, ta ce, "Haba angona, shin kai ba ka jin kunyar zalunta ta, bayan dimbin alherin da mahaifina ya yi maka?" Yayin da Badura ta ji haka, sai ta koma ta zauna, ta ce, "Ya amaryata, me ya yi zafi kike fadin wannan magana?" Hayatunnufusi ta ce, "Ni ban taba ganin mutum mai son kai kamarka ba. Ta yaya za a kawo ni gare ka a matsayin amarya, amma tsawon kwana biyu ba ka kusance ni ba? Ko sona ne ba ka yi? To, ni dai ina yi maka hannunka-mai-sanda, domin kuwa kullum sai mahaifina tare da mahaifiyata sun tambaye ni yadda muka kwana, ni kuwa ina fada musu gaskiya. Mahaifina ya yi matukar fushi da kai da ya ji cewa ba ka kusance ni ba tsawon kwana biyu, ya kuma yi alkawri idan ya dawo gobe ya ji cewa ba ka kusance ni ba, to, zai tube ka daga sarauta, ya sa a kore ka daga kasarsa. Amma ni na san mahaifina a kan zafin zuciya, watakila ma ya sa a kashe ka. Ka ji abin da ake ciki, ya masoyina, yanzu dabara ta rage ga mai shiga rijiya." Yayin da Badura ta ji zancen Hayatunnufusi sai ta sunkuyar da kanta kasa, kunya ta kamata. Ta ce a cikin ranta, "Ta faru ta kare, an yi wa mai dami daya sata. Yau fa ake yin ta, ga bukin zuwa amma

Chapter 6 of 14