Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 14
gaya mini wannan, Ta afka kaunar mai son ta. Na bar ta gidansu a kwance, Ta fada cutar mai son ta. Har wasu na cewa ta zautu, An daure ta cikin dakinta. Ni kuwa na san cutar so ce, Ba ta da hauka ko daya gun ta. Sai ga shi na tad da waninta, Kwance cikin jiyya don son ta. Tashi ka saurare ni ka ji ni, Na zo nan domin warakarta. Ni na zo manzonta gare ka, Tashi ka warke wannan cuta." Yayin da Kamaruzzaman ya ji wannan waka, sai zuciyarsa ta yi karfi, kuzarinsa ya dan dawo jikinsa, ya bude baki cikin wata shakakkiyar murya ta marasa lafiya, ya ce, "Ya mahaifina, ku matso da wannan saurayi ya zauna kusa gare ni." Lokacin da Sarki ya ji dansa ya iya bude baki ya yi magana, sai murna ta kama shi. Da farko kuwa har ya harzuka da Marzuwan yana shirin ba da umurni a sare masa kai, amma da ya ji dansa ya yi magana sai fushinsa ya koma farin ciki. Ya riko Marzuwan da hannunsa ya zaunar da shi kusa ga Kamaruzzaman, ya ce, "Maraba da kai bakon farin ciki." Marzuwan ya ce, "Amincin Allah ya tabbata a gare ka ya Sarki tare da danka." Daga nan Sarki ya tambaye shi daga inda ya fito. Marzuwan ya ce, "Na fito ne daga kasar Sin, kasar Sarki Gayur mai fadoji bakwai." Sarki ya ce, "Maraba da kai ya kai wannan bako. Ina fatar zuwanka wannan kasa tamu ya zama sandiyyar warakar dana." Marzuwan ya ce, "Da yardar Allah madaukakin Sarki, zuwana zai zama sanadiyar tashin danka daga cutar da yake fama da ita, shekara da shekaru." Daga nan sai Marzuwan ya dukar da kansa kusa ga kunnen Kamaruzzaman, ya yi kasa-kasa da muryarsa, yadda Sarki da Waziri ba za su ji abin da zai ce ba. Ya ce, "Na zo wannan birni takanas dominka. Na zo maka da albishir daga kasar Sin, na yarinyar da ka gani shekaru uku da suka wuce. Wannan yarinya ba kowa ba ce face gimbiya Badura, 'yar Sarkin Kasar Sin. Kamar yadda ka kamu da ciwon sonta, haka ita ma tana can cikin ciwon sonka, abin nata ma har ya fi naka ban tausayi, domin ita tana can cikin sarka, hannuwa da kafafu da wuya, a zatonsu ta kamu da ciwon hauka. Amma idan Allah ya so, warakarku duka za ta kasance daga sanadiyyata ne." Lokacin da Kamaruzzaman ya ji haka, sai ya ji wani karfi ya shiga jikinsa, ya yi wa mahaifinsa alama da ya tayar da shi zaune. Sarki ya yi kamar ya yi hauka don murna, ya kama Kamaruzzaman ya tashi zaune, ya sa masa matasan kai guda biyu, ya jingina ga bango. Sarki ya sa aka kawo turare kala-kala aka yayyafa ko'ina cikin dakin. Ya dubi Marzuwan ya ce, "Hakika lamarinka mai girma ne, ka yi abin da ya gagari manya-manyan masu magani." Aka kawo abinci kala-kala, Marzuwan ya dauki akushi daya, ya ce wa Kamaruzzaman ya sa hannunsa su ci tare. Kamaruzzaman bai musa ba, ya sa hannunsa cikin akushi, yana cin abinci tare da Marzuwan. Murnar Sarki da farin cikinsa suka karu fiye da na farko, ya yi ta sa wa Marzuwan albarka yana yabonsa. Nan take ya tafi ya shaida wa matarsa, mahaifiyar Kamaruzzaman, halin da dansu yake ciki. Ya kuma fada wa fadawansa cewa dansa ya sami sauki, ya yi umurni da a yi shela cikin birni, a fada wa dukkan jama'ar gari wannan labari na farin ciki. Ya kuma ba da umurni da a kawata birni domin yin bukin murnar warkewar Kamaruzzaman. Jama'ar gari suka yi ta farin ciki da wannan labari, aka shiga kawata birni da kayan alatu iri- iri. Waziri kuwa, ko ba a fada ba, kun san ya fi kowa murnar warkewar Kamaruzzama. Marzuwan da Kamaruzzaman da Sarki Shahruzzaman suka kwana daki daya, da gari ya waye Sarki ya fita ya ba su wuri. Daga nan Kamaruzzaman ya kwashe dukkan labarin abin da ya faru ya fada wa Marzuwan. Shi ma ya kwashe labarin abin da ya faru ga Badura ya fada wa Kamaruzzaman, ya kara da cewa, "Na tabbata kai masoyinta ne, ita ma masoyiyarka ce. Ka kwantar da hankalinka, ka karfafa zuciyarka. Da yardar Allah kuma sai na hada ku tare. Kamar yadda aka fada a cikin wannan waka: "Ko an tsare wanda ke so, sai, Ya sadu da wadda ke son sa. Ni zan hada wagga soyayya, Ta masoya biyu su zamto kusa. Ni zan zamto wuya ga jiki, Mai hada kai har da kirjinsa." Marzuwan ya ci gaba da karfafa wa Kamaruzzaman zuciya, ya rika ba shi labaran yadda suka tashi da gimbiya Badura tun suna yara, da wasu labarai, ya rika yi masa wakoki. Hankalin Kamaruzzaman ya kwanta, lafiya ta dawo masa, ya nadi abinci sosai, ya sha abin sha mai yawa. Karfin jikinsa ya dawo, ya mike tsaye, ya ce yana so ya yi wanka ya canja tufafi. Marzuwan ya riki hannunsa, suka shiga wurin wanka, zuka zubar da dattin dake jikinsu, suka yi fes. Lokacin da Sarki Shahruzzaman ya sami labarin cewa Kamaruzzaman ya mike tsaye har ya yi tafiya da kafafunsa, ya shiga wurin wanka, saboda tsananin murna ya sa aka saki duk 'yan sarkar garin. Ya ciyar da musakai da miskinai, ya yi kyauta da tufafi masu yawa ga mabukata, ya sa a ci gaba da kawata birni zuwa kwana bakwai domin yin gagarumin shagali a kan murnar warkewar Kamaruzzaman. Bayan Kamaruzzaman da Marzuwan sun fito daga wurin wanka, suka sanya tufafi masu kyau da daraja. Marzuwan ya dubi Kamaruzzaman ya ce, "Ya shugabana, ka sani cewa na zo wannan birni ne takanas domin labarinka da na ji. Tun lokacin da na sami labarinka, da irin ciwon da ke damun ka, na tabbata cewa kai ne wanda 'yar uwata, gimbiya Badura, ta kamu da ciwon sonka, sandiyyar haka aka jefa ta cikin sarka. Kafin na fito gida na yi mata alkawari ba zan koma ba face na je mata da maganin da zai warkar da ita daga cutar da take fama da ita. Kuma ba kome ba ne maganin wannan cuta face kai. Ban sani ba ko za ka amince ka bi ni, in kai ka wurinta?" Kamaruzzaman ya amsa, "Na'am, na amince ka kai ni wurinta, sai dai na sani cewa mahaifina ba zai taba yarda in yi nisa da shi ba, balle ya amince mini in yi tafiya mai nisa haka." Marzuwan ya ce, "Yadda za a yi shi ne, gobe ka fada wa mahaifinka cewa, ka sami lafiya, amma kana so ka tafi farauta domin ka mike kafafunka daga kwanciyar jiyyar da ka yi. Ka fada masa cewa, kwana daya kawai za ka yi a can. Idan ya amince, sai ka kece sirdin dokinka ka cika shi da dinari ka dinke, ni ma zan yi wa sirdin dokina haka. Mu daura wa dawakai biyu amalanke, sanna kuma mu riki wasu dawai biyu mu shiga cikin daji, amma kada ka bari a hada mu da kowa, mu biyu kawai za mu tafi. Da zarar mun fita bayan gari, sai mu sauka daga kan amalanken mu daura wa dawakan biyu sirdi, mu yi ta yi har Allah ya kai mu birnin Sin." ******. Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan a kasuwa'(15) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN Marzuwan ya ce, "Yadda za a yi shi ne, gobe ka fada wa mahaifinka cewa, ka sami lafiya, amma kana so ka tafi farauta domin ka mike kafafunka daga kwanciyar jiyyar da ka yi. Ka fada masa cewa, kwana daya kawai za ka yi a can. Idan ya amince, sai ka kece sirdin dokinka ka cika shi da dinari ka dinke, ni ma zan yi wa sirdin dokina haka. Mu daura wa dawakai biyu amalanke, sanna kuma mu riki wasu dawai biyu mu shiga cikin daji, amma kada ka bari a hada mu da kowa, mu biyu kawai za mu tafi. Da zarar mun fita bayan gari, sai mu sauka daga kan amalanken mu daura wa dawakan biyu sirdi, mu yi ta yi har Allah ya kai mu birnin Sin." Kamaruzzaman ya yi farin ciki da wannan shawara ta Marzuwan. Ya shiga wurin mahaifinsa, ya nemi yardarsa domin fita zuwa ga farauta, ya fada masa zancen da Marzuwan ya umurce shi da shi. Mahaifinsa ya yardar masa fita zuwa ga farauta, ya ce da shi, "Kada ka wuce dare daya, ka dawo zuwa gare ni gobe. Ka sani cewa ba ni jin dadin abnici face kana kusa gare ni, kuma ni har yanzu ban gasgata ka warke ba gaba daya." Daga nan sai Sarki ya wake wadannan baitoci uku: "Na kasnace wagga rana, A cikin dukkan ni'ima. Duniya duka ta kasnace, A gare ni kamar a ce ma. Fiffiken sauro ya fi ta, Daraja in babu kai ma." Sarki ya yi umurni aka daura wa dawaki biyu amalanke, aka dorawa raguma biyu da wasu dawaki biyu kayan abinci da ruwa. Sarki ya yi ban kwana da shi, ya yi musu addu'ar a dawo lafiya, sannan ya rungume shi ga kirjinsa ya ce, "Na roke ka, kada ka faku daga gare ni face dare daya. Ni ba zan iya yin barci ba face ka dawo." Yayin nan Kamaruzzaman da Marzuwan suka hau amalanke suka kora sauran dabbobin, doki biyu dauke da kayan abinci da na kafa tantuna, da rakuma biyu dauke da ruwan sha suka tafi, ya hana kowa ya bi su har suka fita daga cikin birni. Suka ci gaba da tafiya cikin hanzari, tun daga rana ta farko har zuwa rana ta biyu ba tare da sun tsaya ba. A daren rana ta biyu suka tsaya suka huta, dabbobinsu ma suka huta. Daga nan suka ci gaba da tafiya ba su ja linzami ba sai bayan kwana uku, yayin nan suka iso wani wuri inda hanyar ta rarrabu, a gaba kuma daji ne mai duhun gaske. Da suka iso wannan wuri, sai Marzuwan ya kama rakumi daya da doki daya ya yanka. Ya daddatsa naman dabbobin tare da kashinsu, ta yadda ba za a iya gane ko mene ne aka kashe ba. Ya cire rigarsa da rawaninsa, ya yayyaga su tamkar wanda yayi kurmususu da kura, ya cakuda su da jinin dabbobin nan da yanka, ya jefar da su bisa hanya. Ya umurci Kamaruzzaman ya aikata kamar yadda ya aikata, kamaruzzaman bai yi masa musu ba, ya aikata haka ga rigarsa da rawaninsa. Kamaruzzaman ya tambaye shi hikimar yin hakan. Marzuwan ya ce, "Ka sani cewa, yayin da muka wuce ranar farko ba mu koma gida ba, babu shakka mahaifinka ba zai hakura ba, zai biyo sawunmu. Na tabbata kuma ba za mu yi nisa ba zai tarar da mu. Amma yanzu idan ya iso nan ya ga rigunanmu cikin jini a yayyage, zai zaci cewa mun hadu da 'yan fashi ne, suka kashe mu suka kwace mana kaya. Ko kuma ya zaci cewa wata dabbar daji ce ta kashe mu, ta haka sai ya hakura ya koma gida, mu kuwa sai mu ci gaba da tafiyarmu cikin kwanciyar hankali." Kamaruzzaman ya ce, "Babu shakka wannan dabara taka akwai hikima a cikinta." Daga nan suka daura wa dawakai biyu sirdi, suka debi abin da za su iya diba na guzuri, suka yi wa jahar da birnin Sin take tsinke. Suka yi ta tafiya babu dare babu rana har suka fara shiga wani yanki na Kasar Sin. Duk tsawon wannan lokaci babu abin da Kamaruzzaman yake yi sai zubar da hawaye na bakin cikin rabuwa da mahaifinsa, da kuma farin ciki zai sadu da abar begensa. Yayin da Marzuwan ya fada masa cewa sun shiga karkarar kasar Sin, saboda farin ciki sai Kamaruzzaman ya waka wadannan baitoci: "Abar so a guna takan zan gudu, A yayin da ta mallaken zuciya. Ki san babu hanyar gudu a gare ki, Ina nan tafe nan da sa'a daya. Yarda takan kaurace kun jiya, Idan babu kauna cikin zuciya. Na bar mahaifi garan can gida, Yana zub da kwalla kamar maliya. Ni na yi karya da zan je farauta, Ka yafen mahaifi ka zan juriya. Yayin da ya gama wakarsa, sai Marzuwan ya ce masa, "Ya shugabana, duba can gabanmu, mun iso tsibiran kasar Sin na Sarki Gayur mai fadoji bakwai." Da Kamaruzzaman ya ji haka, ya duba gaba gare su, ya hangi gine-ginen birnin Sin. Ya cika da farin ciki marar misaltuwa, ya rungume Marzuwan don murna, ya sumbaci goshinsa. Da suka shiga cikin gari, sai Marzuwan ya nufi da su gidan baki, ya biya musu kudin dakuna, suka huta tsawon kwana uku, gajiyar tafiya ta sake su. Bayan sun huta, sai Marzuwan ya ja hannun Kamaruzzaman zuwa gidan wanka, suka yi wanka suka tsabtace jikinsu. Marzuwan ya tafi kasuwa ya sayo wa Kamaruzzaman tufafi masu tsada irin na bokaye, ya kuma sayo masa kayan aune-aune irin na masu bayar da magani. Ya kawo masa ya ce, "Ya shugabana, ka saka wadannan tufafi a jikinka, ka riki wadannan kayayyaki ga hannunka, ka tafi kusa ga fadar Sarki Gayur. Ka yi kira da murya madaukakiya kana cewa kai boka ne mai bayar da magani, babu cutar da ba ka da maganinta. Idan Sarki ya ji ka, zai turo a tafi da kai wurinsa, zai fada maka labarin ciwon 'yarsa da kuma sharadin da ya gindaya ga dukkan wanda ya warkar da ita ko akasin haka. Ka ce masa ka amince za ka warkar da ita, idan aka kai ka wurinta, ka shiga gare ta. Tana ganin ka za ta warware daga rashin lafiyarta, sai ka ba ta abinci da abin sha har karfin jikinta ya dawo. Wassalam, Allah ya ba ka sa'a." Kamaruzzaman ya riki hannun Marzuwan ya sumbace shi, ya yi ta yi masa godiya. Daga nan ya saka tufafi, ya riki kayan magani ga hannunsa, ya zama kamar wani bakon boka, ya nufi fadar Sarki Gayur. Da ya isa kofar fada, sai ya daga muryarsa ya ce, "Ni ne boka uban bokaye, ni ne lamiri mai gani har hanji, na auri doguwa ta aure ni. Ina mai neman sa'a, a ba shi? Ina wanda ya yi mafarki, a fassara masa? Ina wanda aljani ya kama, a fitar masa? Wa yake fama da wata cuta da ta gagari masu magani? Ga boka uban bokaye." Yayin da mutanen gari suka ji shi, sai suka kewaye shi, rabon da su ji tallar maganin wani boka a wannan kasa har sun manta. Suka ga Kamaruzzaman saurayi ne kyakkyawa, kamar dan saurayin aljani, wanda babu kamarsa. Wani dan tsoho tukuf, dan gajere kamar a kife da kwando, ya dogaro sandarsa ya kutso mutane ya tsaya a gaban Kamaruzzaman, ya daga kai ya dube shi, ya ce masa, "Dan samari, kada ka jefa kanka cikin halaka don kawai kwadayin auren gimbiya Badura, bokaye da yawa, wadanda suka fi ka ilimin sanin magunguna da taurari, duk sun hallaka sanadiyyar wannan yarinya. Kawunansu na nan makale a gaban gidanta, idan ka gan su, sun ishe ka ishara. Amma na hore ka, ka kubutar da wannan kyakkyawar sura taka daga halaka." Kamaruzzaman bai ko kula wannan dan tsoho ba, ya kara daga murya, ya yi kira da karfi, "Ni ne boka uban bokaye, ni ne lamiri mai gani har hanji, na auri doguwa ta aure ni. Ina mai neman sa'a, a ba shi? Ina wanda ya yi mafarki, a fassara masa? Ina wanda aljani ya kama, a fitar masa? Wa yake fama da wata cuta da ta gagari masu magani? Ga boka uban bokaye." Mutanen gari suka tausaya masa saboda kyawunsa, suka hane shi kada ya jefa kansa cikin halaka, amma ya ki. Suka ce masa je ka, ai mai rabon shan duka ba ya jin kwaba sai ya sha. Shi kuwa yana cewa a cikin ransa, "Babu tsimi babu dabara, face daga Allah madaukakin Sarki." Ya ci gaba da tallar magani da murya madaukakiya a gaban fadar Sarki Gayur. **** **** **** Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin (15) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN Marzuwan ya ce, "Yadda za a yi shi ne, gobe ka fada wa mahaifinka cewa, ka sami lafiya, amma kana so ka tafi farauta domin ka mike kafafunka daga kwanciyar jiyyar da ka yi. Ka fada masa cewa, kwana daya kawai za ka yi a can. Idan ya amince, sai ka kece sirdin dokinka ka cika shi da dinari ka dinke, ni ma zan yi wa sirdin dokina haka. Mu daura wa dawakai biyu amalanke, sanna kuma mu riki wasu dawai biyu mu shiga cikin daji, amma kada ka bari a hada mu da kowa, mu biyu kawai za mu tafi. Da zarar mun fita bayan gari, sai mu sauka daga kan amalanken mu daura wa dawakan biyu sirdi, mu yi ta yi har Allah ya kai mu birnin Sin." Kamaruzzaman ya yi farin ciki da wannan shawara ta Marzuwan. Ya shiga wurin mahaifinsa, ya nemi yardarsa domin fita zuwa ga farauta, ya fada masa zancen da Marzuwan ya umurce shi da shi. Mahaifinsa ya yardar masa fita zuwa ga farauta, ya ce da shi, "Kada ka wuce dare daya, ka dawo zuwa gare ni gobe. Ka sani cewa ba ni jin dadin abnici face kana kusa gare ni, kuma ni har yanzu ban gasgata ka warke ba gaba daya." Daga nan sai Sarki ya wake wadannan baitoci uku: "Na kasnace wagga rana, A cikin dukkan ni'ima. Duniya duka ta kasnace, A gare ni kamar a ce ma. Fiffiken sauro ya fi ta, Daraja in babu kai ma." Sarki ya yi umurni aka daura wa dawaki biyu amalanke, aka dorawa raguma biyu da wasu dawaki biyu kayan abinci da ruwa. Sarki ya yi ban kwana da shi, ya yi musu addu'ar a dawo lafiya, sannan ya rungume shi ga kirjinsa ya ce, "Na roke ka, kada ka faku daga gare ni face dare daya. Ni ba zan iya yin barci ba face ka dawo." Yayin nan Kamaruzzaman da Marzuwan suka hau amalanke suka kora sauran dabbobin, doki biyu dauke da kayan abinci da na kafa tantuna, da rakuma biyu dauke da ruwan sha suka tafi, ya hana kowa ya bi su har suka fita daga cikin birni. Suka ci gaba da tafiya cikin hanzari, tun daga rana ta farko har zuwa rana ta biyu ba tare da sun tsaya ba. A daren rana ta biyu suka tsaya suka huta, dabbobinsu ma suka huta. Daga nan suka ci gaba da tafiya ba su ja linzami ba sai bayan kwana uku, yayin nan suka iso wani wuri inda hanyar ta rarrabu, a gaba kuma daji ne mai duhun gaske. Da suka iso wannan wuri, sai Marzuwan ya kama rakumi daya da doki daya ya yanka. Ya daddatsa naman dabbobin tare da kashinsu, ta yadda ba za a iya gane ko mene ne aka kashe ba. Ya cire rigarsa da rawaninsa, ya yayyaga su tamkar wanda yayi kurmususu da kura, ya cakuda su da jinin dabbobin nan da yanka, ya jefar da su bisa hanya. Ya umurci Kamaruzzaman ya aikata kamar yadda ya aikata, kamaruzzaman bai yi masa musu ba, ya aikata haka ga rigarsa da rawaninsa. Kamaruzzaman ya tambaye shi hikimar yin hakan. Marzuwan ya ce, "Ka sani cewa, yayin da muka wuce ranar farko ba mu koma gida ba, babu shakka mahaifinka ba zai hakura ba, zai biyo sawunmu. Na tabbata kuma ba za mu yi nisa ba zai tarar da mu. Amma yanzu idan ya iso nan ya ga rigunanmu cikin jini a yayyage, zai zaci cewa mun hadu da 'yan fashi ne, suka kashe mu suka kwace mana kaya. Ko kuma ya zaci cewa wata dabbar daji ce ta kashe mu, ta haka sai ya hakura ya koma gida, mu kuwa sai mu ci gaba da tafiyarmu cikin kwanciyar hankali." Kamaruzzaman ya ce, "Babu shakka wannan dabara taka akwai hikima a cikinta." Daga nan suka daura wa dawakai biyu sirdi, suka debi abin da za su iya diba na guzuri, suka yi wa jahar da birnin Sin take tsinke. Suka yi ta tafiya babu dare babu rana har suka fara shiga wani yanki na Kasar Sin. Duk tsawon wannan lokaci babu abin da Kamaruzzaman yake yi sai zubar da hawaye na bakin cikin rabuwa da mahaifinsa, da kuma farin ciki zai sadu da abar begensa. Yayin da Marzuwan ya fada masa cewa sun shiga karkarar kasar Sin, saboda farin ciki sai Kamaruzzaman ya waka wadannan baitoci: "Abar so a guna takan zan gudu, A yayin da ta mallaken zuciya. Ki san babu hanyar gudu a gare ki, Ina nan tafe nan da sa'a daya. Yarda takan kaurace kun jiya, Idan babu kauna cikin zuciya. Na bar mahaifi garan can gida, Yana zub da kwalla kamar maliya. Ni na yi karya da zan je farauta, Ka yafen mahaifi ka zan juriya. Yayin da ya gama wakarsa, sai Marzuwan ya ce masa, "Ya shugabana, duba can gabanmu, mun iso tsibiran kasar Sin na Sarki Gayur mai fadoji bakwai." Da Kamaruzzaman ya ji haka, ya duba gaba gare su, ya hangi gine-ginen birnin Sin. Ya cika da farin ciki marar misaltuwa, ya rungume Marzuwan don murna, ya sumbaci goshinsa. Da suka shiga cikin gari, sai Marzuwan ya nufi da su gidan baki, ya biya musu kudin dakuna, suka huta tsawon kwana uku, gajiyar tafiya ta sake su. Bayan sun huta, sai Marzuwan ya ja hannun Kamaruzzaman zuwa gidan wanka, suka yi wanka suka tsabtace jikinsu. Marzuwan ya tafi kasuwa ya sayo wa Kamaruzzaman tufafi masu tsada irin na bokaye, ya kuma sayo masa kayan aune-aune irin na masu bayar da magani. Ya kawo masa ya ce, "Ya shugabana, ka saka wadannan tufafi a jikinka, ka riki wadannan kayayyaki ga hannunka, ka tafi kusa ga fadar Sarki Gayur. Ka yi kira da murya madaukakiya kana cewa kai boka ne mai bayar da magani, babu cutar da ba ka da maganinta. Idan Sarki ya ji ka, zai turo a tafi da kai wurinsa, zai fada maka labarin ciwon 'yarsa da kuma sharadin da ya gindaya ga dukkan wanda ya warkar da ita ko akasin haka. Ka ce masa ka amince za ka warkar da ita, idan aka kai ka wurinta, ka shiga gare ta. Tana ganin ka za ta warware daga rashin lafiyarta, sai ka ba ta abinci da abin sha har karfin jikinta ya dawo. Wassalam, Allah ya ba ka sa'a." Kamaruzzaman ya riki hannun Marzuwan ya sumbace shi, ya yi ta yi masa godiya. Daga nan ya saka tufafi, ya riki kayan magani ga hannunsa, ya zama kamar wani bakon boka, ya nufi fadar Sarki Gayur. Da ya isa kofar fada, sai ya daga muryarsa ya ce, "Ni ne boka uban bokaye, ni ne lamiri mai gani har hanji, na auri doguwa ta aure ni. Ina mai neman sa'a, a ba shi? Ina wanda ya yi mafarki, a fassara masa? Ina wanda aljani ya kama, a fitar masa? Wa yake fama da wata cuta da ta gagari masu magani? Ga boka uban bokaye." Yayin da mutanen gari suka ji shi, sai suka kewaye shi, rabon da su ji tallar maganin wani boka a wannan kasa har sun manta. Suka ga Kamaruzzaman saurayi ne kyakkyawa, kamar dan saurayin aljani, wanda babu kamarsa. Wani dan tsoho tukuf, dan gajere kamar a kife da kwando, ya dogaro sandarsa ya kutso mutane ya tsaya a gaban Kamaruzzaman, ya daga kai ya dube shi, ya ce masa, "Dan samari, kada ka jefa kanka cikin halaka don kawai kwadayin auren gimbiya Badura, bokaye da yawa, wadanda suka fi ka ilimin sanin magunguna da taurari, duk sun hallaka sanadiyyar wannan yarinya. Kawunansu na nan makale a gaban gidanta, idan ka gan su, sun ishe ka ishara. Amma na hore ka, ka kubutar da wannan kyakkyawar sura taka daga halaka." Kamaruzzaman bai ko kula wannan dan tsoho ba, ya kara daga murya, ya yi kira da karfi, "Ni ne boka uban bokaye, ni ne lamiri mai gani har hanji, na auri doguwa ta aure ni. Ina mai neman sa'a, a ba shi? Ina wanda ya yi mafarki, a fassara masa? Ina wanda aljani ya kama, a fitar masa? Wa yake fama da wata cuta da ta gagari masu magani? Ga boka uban bokaye." Mutanen gari suka tausaya masa saboda kyawunsa, suka hane shi kada ya jefa kansa cikin halaka, amma ya ki. Suka ce masa je ka, ai mai rabon shan duka ba ya jin kwaba sai ya sha. Shi kuwa yana cewa a cikin ransa, "Babu tsimi babu dabara, face daga Allah madaukakin Sarki." Ya ci gaba da tallar magani da murya madaukakiya a gaban fadar Sarki Gayur. **** **** **** Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin(16) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN Kamaruzzaman bai kula da gargadin dan tsoho da sauran jama'ar gari ba, ya ci gaba da tallar magani, a kofar fadar Sarki Gayur, cikin murya madaukakiya, "Ni ne boka uban bokaye, ni ne lamiri mai gani har hanji, na auri doguwa ta aure ni. Ina mai neman sa'a, a ba shi? Ina wanda ya yi mafarki, a fassara masa? Ina wanda aljani ya kama, a fitar masa? Wa yake fama da wata cuta da ta gagari masu magani? Ga boka uban bokaye." Allah da ikonsa sai Sarki Gayur ya jiyo muryarsa, ya juya ga Wazirinsa ya ce, "Tafi da sauri ka zo mini da mai tallar maganin can." Waziri ya tashi da hanzari ya fito waje, ya tarar da jama'a sun zagaye Kamaruzzaman suna kallonsa. Ya kutsa ya jawo hannunsa suka nufi wurin Sarki. Da zuwansu gaban Sarki, sai Kamaruzzaman ya fadi kasa, ya gayar da Sarki cikin ladabi da girmamawa, sa'annan ya waka wadannan baitoci: "Takwas na cikin girma, na tara dukkansu. Daya bai gushe ba a cikinsu daga gare ka, tsawon zamani, domin sakankancewarka da tsoron Allah, da girmanka, da baiwarka, da lafazinka, da harshenka, da iliminka, da daukakarka, da nasara a kan makiyanka. Allah ya dawwamar da mulkinka tsawon zamani, ya Sarki mai adalci." Sarki ya yi murna da jin wannan waka, ya yi mamakin fasahar Kamaruzzaman da kuma ladabinsa, ya riki hannunsa ya zaunar da shi kusa gare shi. Ya dube shi da kyau ya ce, "Na rantse da Allah, ba ka yi kama da bokaye ba. Ina ba ka shawara da ka tsirar da rayuwarka da kuma kyawunka daga takobin hauni. Ka sani cewa na riga na yi alkawari duk wanda ya yi ido hudu da 'yata kuma ya kasa warkar da ita daga cutar da take ciki, zan sa a sare kansa a sargafe shi a gaban gidanta. Amma kuma duk wanda ya yi nasarar warkar da ita, zan aura masa ita, zan kuma raba kasata biyu in ba shi rabi." Sarki ya dafa hannun Kamaruzzaman ya ci gaba da cewa, "Wallahi, na rantse da Allah, idan ka shiga wurin 'yata, kuma ka kasa warkar da ita, babu makawa zan sa a sare kanka, kyawunka ba zai amfana maka kome ba." Kamaruzzaman ya dan yi murmushi ya ce, "Na amince da wannan sharadi naka, Allah ya ba ka nasara. Ai tun kafin na zo nan, na san da wannan alkawari da ka yi." Sarki ya sa aka kira alkalai, suka shaida abin da Kamaruzzaman ya fada. Daga nan Sarki ya hada shi da wani bawa ya ce, "Tafi da wannan saurayi wurin gimbiya Badura." Bawa ya riki hannun Kamaruzzaman suka nufi gidan da Badura take tsare. Da suka kusa isa gidan, saboda dokin ganin abar begensa, sai Kamaruzzaman ya kwace

Chapter 5 of 14