Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
14 / 14
Na mayar da ke ga shugabanki." Daga nan ya juya wurin Na'imu, ya ce, "ya saurayi, shin wanene ya sanar da kai inda kuyangarka ta ke? Kuma wa ya shirya maka dabarar da ka shigo nan?" "Ya Shugaban Muminai, " Na'imu ya amsa masa, "saurari labarina, na rantse da darajar kakanninka ba zan gaya maka karya ba." Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ42 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMA Na'imu ya amsa masa, "saurari labarina, na rantse da darajar kakanninka ba zan gaya maka karya ba." Ya gaya masa yadda suka tashi tare da Na'imatu, da yadda aka shirya dabara aka sace ta daga hannunsa, wanda sanadiyyar wannan rabuwa ce ya kwanta rashin lafiya. Ya fadi yadda mai magani Bafarishe ya gano abin da ke damunsa, da yadda ya taho da shi nan Damashka neman Na'imatu. Ya kuma gaya wa Halifa yadda tsohuwa ta zo wurin su nema wa Na'imatu magani, wanda hakan ya sa suka san tana cikin gidan Halifa. Ya fadi yadda tsohuwa ta taimake shi har ya shigo gidan Halifa, da yadda ya rude har ya shiga dakin 'yar uwar Halifa. Na'imu ya kwashe labari kaf, bai rage kome ba, ya gaya wa Halifa. Yayin da Halifa ya ji wannan labari, sai ya cika da mamaki, matukar mamaki. Ya ce a kirawo masa wannan Bafarishen Boka mai tsananin hikima. Da aka kira shi, ya nada shi daya daga cikin 'yan majalisarsa, yana cewa, "wanda duk ya nuna irin wannan basira da fasaha, to, ya kyautu mu rike shi kusa gare mu." Ya yi masa kyauta mai yawa, kuma ya yanka masa albashi. Haka kuma ya ba Na'imu da Na'imatu kyautar dukiya mai yawan gaske, tsohuwa ma ba a manta da ita ba. Suka zauna wurin Halifa cikin farin ciki da jin dadi. Bayan kwana bakwai, suka nemi izinin komawa gida, Kufa, domin hankalin mahaifansu ya kwanta. Halifa ya hada su da 'yan rakiya, suka ka kai su har cikin gida. Na'imu ya sadu da mahaifinsa da mahaifiyarsa. Suka yi zamansu cikin kwanciyar hankali da farin ciki har lokacin da mai katse jin dadi, mai raba tsakani ta riske su. KARSHEN HIKAYAR NA'IMUH DA NA'IMAHTU Yayin da Baharamu ya gama wannan labari nasa, Amjadu da Asadu suka yi mamaki, suka ce, "lalle wannan labari akwai tausayi da ban al'ajabi a cikin sa." Suka raba dare suna hira. Da gari ya waye, Amjadu da Asadu suka hau, suka nufi fada. Da aka yi musu iso, suka shiga suka yi gaisuwa ga Sarki, suka zauna suna zance da shi. Can sai suka ji kururuwa da hargowar mutane, a cikin gari, suna neman gudummawa. Ko kafin a yi haka, sai ga wani dogari ya shigo fadar a guje, rawaninsa ga hannu. Ya fadi gaban Sarki yana haki, ya ce, "Allah ya ba ka nasara, yaki bisa kan mu." Sarki ya dube shi ya ce, "wane irin yaki bayan muna zaune da makwabtanmu cikin aminci?" Dogari ya ce, "Allah ya ba ka nasara, ni ma dai abin ya ba ni mamaki. Ba mu san ko wane Sarki ba ne, yana nan bayan gari ya yi sansani da rundurarsa bila adadin. Babu abin da mutum zai gani sai walkiyar masu da takubba." Sarki ya juya wurin Waziri Amjadu ya ce masa ya je ya samo labarin da ke tafe da wannan Sarki. Amjadu ya hau doki ya sukwane shi, ya nufi bayan gari. Da ya isa wurin rundunar, sai jama'ar da ke ciki suka gane cewa jakada ne. Amjadu ya ce su kai shi ga Sarkinsu, suka kai shi har gaban Sarki. Ya fadi ya yi gaisuwa, da ya dago kansa sai ya ga ashe Sarkin ma, mace ce, watau Sarauniya ce. Ta dubi Amjadu ta ce, "ba kyawon birninku ne ya kawo ni ba, na zo ne neman wani dan saurayi, bawana. Idan yana wurin ku, ku ba ni shi. Idan kuma kuka ki, zan mayar da wannan gari toka." "Allah ya taimake ki, menene sunan wannan bawa naki? Kuma yaya kamanninsa suke?" Ta ce, sunansa Asadu. Yana da siffa kaza da kaza, ta siffanta yadda Asadu yake. Ta ci gaba da cewa, "sunana Sarauniya Murjanatu, na hadu ne da wannan bawa yayin da wasu matsafa suka je da shi birnina. Na kwace shi daga hannunsu, amma da dare ya yi sai suka lallaba suka sace shi suka gudu." Yayin da Amjadu ya ji zancenta, sai ya gane cewa dan uwansa ne take nema. Sai ya ce, "godiya ta tabbata ga Allah, mai yayewar dukan bakin ciki. Ki sani cewa wanda kike nema dan uwana ne." Ya kwashe labarinsu duka, tun daga fitowar su daga birnin Labunus, da yadda suka rabu, da kuma yadda suka sake haduwa, ya gaya mata. Saruniya ta cika da mamaki, ta kuma yi farin ciki da ta gane Asadu. Ta kawo riguna na musamman ta ba Amjadu, ya karba ya hau dokinsa ya juya zuwa cikin gari domin sanar da Sarki abin da ake ciki. Lokacin da Amjadu ya gaya wa Sarki labarin Sarauniya, sai suka yi farin ciki. Sarki ya hau tare da fadawansa da Waziri Amjadu da Asadu suka nufi bayan gari wurin Sarauniya Murjanatu. Yayin da suka isa wurin ta, suka zauna suna mayar da zance. Can sai suka hangi kura ta tokare sararin samaniya har ta rufe hasken rana, suka rika jiyo karar kofatan dawaki da kururuwar askarawa, kamar kasa za ta tsage. Yayin da kura ta yaye, sai suka hangi rundunar mayaka masu yawan gaske, tamkar kumfar teku, sai takubba da masu ke walkiya cikin hasken rana. Wannan runduna ta taso wa birnin da nufin zagaye shi, tamkar yadda zobe kan zagaye yatsan hannu. Lokacin da Amjadu da Asadu suka ga haka, sai suka buga salati, "daga Allah muka fito, kuma gare shi za mu koma. Wannan wace irin rundunar mayaka ce mai yawan gaske. Babu shakka mu nemi gudummawa daga wannan Sarauniya, idan ba haka ba kuwa za su lakume mu, kamar yadda wuta ke lakume karmami." Sarki ya umurci Waziri Amjadu ya tafi ya jiyo labarin wannan runduna. Amjadu ya zaburi dokinsa, ya nufi wurin wannan runduna. Da zuwan sa aka kai shi wurin Sarki, ya fadi ya yi gaisuwa, ya tambayi Sarki dalilin zuwan sa da rundunar yaki. Sarki ya amsa masa, "ni ne Sarki Gayur, mai fadoji bakwai, Sarkin tekuna da tsibiran kasar Sin. Na fito neman 'yata Badura, wadda kaddara ta raba tsakaninmu, bayan na aurar da ita ga Kamaruzzaman dan Sarki Shaharuzzaman. Tsawon shekaru da yawa, har yanzu ban ji duriyarsu ba. Ko kuna da labarinsu a wannan kasa taku?" Ko da Amjadu ya ji haka sai ya fahimci cewa, wannan tsoho kakansa ne, watau mahaifin uwarsa, Badura. Sai ya kara durkusawa a gabansa ya ce, "ai ni ne dan 'yarka, Badura. Ita mahaifiyata ce, Kamaruzzaman kuwa mahaifina ne." Yayin da Sarki Gayur ya ji haka, sai ya sauko daga kan dokinsa, ya rungume Amjadu, hawaye na zuba daga idanunsa. Amjadu ya gaya masa cewa, Badura da Kamaruzzaman suna nan cikin koshin lafiya, suna zaune a wani birni da ake kira Labunus, shi ne ma Sarkin garin. Ya kwashe labarin abin da ya faru tsakaninsa da mahaifinsa da kuma dan uwansa Asadu, da yadda mahaifin nasu ya yi fushi da su har ya umurci hauni ya sare musu kawuna, inda shi kuma haunin ya ji tausayin su, ya kyale su suka gudu, duk ya fada wa Sarki Gayur. Sarki Gayur ya ce, "in Allah ya so, zan koma tare da ku zuwa birnin Labunus, in yi sulhu tsakaninku da mahaifinku." Ya kawo kyautar tufafi na alfarma ya ba Amjadu, wanda shi kuma ya hau dokinsa ya koma wurin Sarkinsa, fuskarsa cike da farin ciki. Ya gaya wa Sarki da Asadu labarin Sarki Gayur. Sarki ya yi farin ciki, ya sa aka aika wa Sarki Gayur da shanu da rakuma da tumaki masu yawa, da kuma buhuhuwan hatsi. Haka kuma ya sa aka ba Sarauniya Murjanatu irin wannan kyauta, ya kuma gaya mata labarin Sarki Gayur da abin da ke tafe da shi. Ita ma ta ce, za ta tafi tare da Amjadu da Asadu zuwa birnin Labunus domin ta lallashi Kamaruzzaman ya yafe wa 'ya'yansa. Ana cikin haka kuma sai aka hangi wata kura daga nesa, ta tokare sararin samaniya, har wuri ya duhunta, ya koma tamkar cikin dare. Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ GOBE ZAMU GAMA DUKA INSHA ALLAH43 HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHARUZZAMAN Ya kawo kyautar tufafi na alfarma ya ba Amjadu, wanda shi kuma ya hau dokinsa ya koma wurin Sarkinsa, fuskarsa cike da farin ciki. Ya gaya wa Sarki da Asadu labarin Sarki Gayur. Sarki ya yi farin ciki, ya sa aka aika wa Sarki Gayur da shanu da rakuma da tumaki masu yawa, da kuma buhuhuwan hatsi. Haka kuma ya sa aka ba Sarauniya Murjanatu irin wannan kyauta, ya kuma gaya mata labarin Sarki Gayur da abin da ke tafe da shi. Ita ma ta ce, za ta tafi tare da Amjadu da Asadu zuwa birnin Labunus domin ta lallashi Kamaruzzaman ya yafe wa 'ya'yansa. Ana cikin haka kuma sai aka hangi wata kura daga nesa, ta tokare sararin samaniya, har wuri ya duhunta, ya koma tamkar cikin dare. Da kurar ta fara yayewa sai suka ga askarawa bisa dawaki dauke da zararrun takubba da masu, suna kururuwa da hargowa. Yayin da wannan runduna ta matso kusa, suka hangi rundunar Sarauniya Murjanatu da rundunar Sarki Gayur a bayan gari, sai suka fara buga ganguna. Sarkin birnin Matsafa ya ce, "hakika, wannan rana tana cike da albarka, mun gode wa Allah da ya hada mu da wadannan rundunoni biyu." Ya juya wurin Amjadu da Asadu ya ce musu, su tafi su samo masa labarin wannan runduna mai yawa kamar farin dango. Amjadu da Asadu suka hau dawaki suka nufi wurin wannan runduna. Ko da da suka isa wurin rundunar nan sai suka ga ashe mayakan birnin Labunus ne, wadda mahaifinsu, Kamaruzzaman, da kansa ya fito tare da su. Yayin da suka yi arba da mahaifinsu, sai suka fadi suka yi gaisuwa. Lokacin da Kamaruzzaman ya ga 'ya'yansa, sai ya yi kamar ya some don farin ciki, ya rungume su cikin kirjinsa, dukkansu suna kuka. Ya ba su labarin yadda ya gane gaskiyar lamari, tsakaninsu da iyayensu mata, da kuma yadda hauni ya fada masa cewa bai kashe su ba har ya fito neman su. Ya nemi gafarar su, suka gafarta masa. Sa'annan suka fada masa labarin zuwan Sarki Gayur, suka nuna masa inda rundunarsa take. Kamaruzzaman ya hau tare da 'ya'yansa, da wasu mukarrabansa, suka nufi wurin surukinsa, Sarki Gayur. Da suka kusa isa wurin, sai Amjadu ya zaburi dokinsa ya yi gaba, ya riga su isa wurin sansanin Sarki Gayur. Ya gaya masa labarin zuwan Kamaruzzaman. Nan da nan Sarki Gayur da wasu na kusa gare shi suka hau dawaki suka tari Kamaruzzaman. Bayan sun gamu, suka ba juna labarin bayan rabuwa. Suka yi mamakin wannan haduwa tasu, matukar mamaki. Mutanen cikin birni kuwa da suka ji labarin abin da ake ciki sai suka fara tunanin me ake ciki, kowa ciki ya duri ruwa, suna zaton yaki ne. Suka yi ta fitowa da kabukkan abinci da nama, da tulunan ruwa da abin sha, suna kawo wa baki. Wasu kuma suka rika debo harawa da ciyawa suna kai wa dawakin askarawa. Wasu kuma suka fito da kayan kida da na busa aka fara kade-kade da raye-raye ana shewa. Mutane na cikin wannan bidiri, sai kuma aka hango wata kurar ta rufe ko'ina na sararin samaniya. Aka rika jin kasa na girgiza kamar za ta tsage. Gunjin dawaki da bugun ganguna suka hadu tamkar aradu na sauka. Mutane duk aka tsaya cik ana sauraren isowar wannan runduna. Da kura ta yaye sai aka ga dukkan askarawan wannan runduna suna sanye da bakaken tufafi, don yawansu sai suka zama kamar tururuwa daga nesa. Sarkin birnin Matsafa ya ce, "babu tsimi babu dabara face daga Allah Madaukakin Sarki. Wannan kuma rundunar wane sarki ce?" Sauran Sarakunan nan suka ce masa, kada ya ji tsoro, idan ma har makiyi ne, to, za su taimake shi wurin yakarsa. Suna cikin wannan zance sai ga 'yan sako sun zo daga cikin rundunar. Suka fadi gaban Sarakunan nan hudu suka yi gaisuwa. Daga nan sai suka ce, "Sarkinmu ya ce a sanar da ku, ya fito daga kasarsa da ke yankin Farisa domin neman dansa da ya fito daga gida, shekara da shekaru. Idan yana wurin ku ku fito da shi, idan kuwa kuka ki, to, zai darkake wannan gari naku, ya mayar da shi turbaya, kamar yadda ya yi wa biranen da biyo ta cikin su." "Haka ba zai faru ba," in ji Kamaruzzaman, "mene sunan wannan Sarki naku?" "Sunansa Shaharuzzaman, mai mulkin tsibirai da tekunan Kalidan." Lokacin da Kamaruzzaman ya ji an ambaci sunan mahaifinsa, sai ya yi wata kara mai tsanani, ya fadi kasa somamme. Aka shafa masa ruwa ya farfado. Da hankalinsa ya dawo, sai ya dubi 'ya'yansa Amjadu da Asadu, idanunsa cike da hawaye, ya ce musu, "ku tafi tare da wadannan manzanni wurin kakanku, Sarki Shaharuzzaman. Ku yi masa bushara da kasancewa ta a wannan wuri." Sai kuma ya ce a cikin ransa, "Allah Sarki, har yanzu mahaifina yana sanye da bakaken tufafi domin nuna bakin cikin rabuwa da ni." Da ya tuna irin tsananin son da mahaifinsa ke yi masa, sai ya sake fashewa da kuka. Kamaruzzaman ya fada wa sauran Sarakunan labarin kuruciyarsa, da yadda mahaifinsa ke son sa, da yadda aka yi ta fama da shi a kan ya yi aure, da kuma abin da ya raba shi da gida, da wahalhalun da ya sha duka, ya fada musu. Suka yi al'ajabi matukar al'ajabi. Suka tashi gaba daya suka nufi sansanin Sarki Shaharuzzaman. Yayin da Kamaruzzaman da mahaifinsa suka ga juna, sai suka sauka daga kan dawakansu, suka rungume juna, don tsananin farin ciki sai da suka suma. Bayan sun farfado, hankalinsu ya kwanta, sai Kamaruzzaman ya kwashe labarinsa kaf ya fada wa mahaifinsa. Ya nemi gafararsa a kan rashin komawar sa gida. Haka dai kowa ya bayar da labarinsa, da irin wahalar da ya sha. Sarkin birnin Matsafa ya sa aka shirya gagarumin biki domin murnar haduwar wadannan Sarakuna. Aka kwana bakwai ana shagali, babu dare babu rana, daga nan kowane Sarki ya yi haramar komawa kasarsa. Aka daura auren Asadu da Sarauniya Murjanatu. Amjadu kuwa ya auri Bustana, diyar Baharamu, sarkin tsafi na da. Daga nan Sarki Gayur da Sarki Sharuzzaman da Sarki Kamaruzzaman da 'ya'yansa, da Sarauniya Murjanatu, suka yi sallama da Sarkin birnin Matsafa, tare da alkawarin za su rika ziyartarsa a kai a kai, suka dunguma suka nufi birnin Labunus. Yayin da suka isa, Kamaruzzaman ya tafi wurin surukinsa, Sarki Armanus, ya kwashe labarin tafiyarsa ya gaya masa. Ya kuma gaya masa yadda ya sadu da 'ya'yansa da mahaifinsa da kuma surukinsa, uban Badura. Sarki Armanus ya yi mamaki. Badura ta ga mahaifinta, suka rungume juna suna kuka don farin ciki. A nan ma aka shirya wani kasaitaccen buki. Bayan wata guda, sai Sarki Gayur ya dauki 'yarsa Badura tare da jikansa Amjadu zuwa birnin Sin. Yayin nan ya yi murabus ya nada Amjadu a matsayinsa. Shi kuwa Kamaruzzaman sai ya nada Asadu, wanda yake jika ne ga Sarki Armanus, a matsayin Sarkin Labunus, ya bi mahaifinsa, Shaharuzzaman, zuwa kasarsu ta Kalidan. . Lokacin da suka kusa isa, sai suka dakata a bayan gari suka tayar da 'yan bushara su kai labari. Ba a dade ba kuwa, sai ga 'yan tariya sun zo da kade-kade da bushe-bushe. Aka dunguma aka shiga cikin birni. Aka kawata birnin Kalidan da kayan kwalliya, tamkar yadda aka yi a ranar bikin haihuwar Kamaruzzaman. Aka share wata guda ana biki. Daga nan sai Shaharuzzaman ya yi murabus, ya nada Kamaruzzaman a matsayinsa. Sai ya kasance daga lokaci zuwa lokaci, wani daga cikin Sarakunan nan zai kai wa wani Sarkin ziyara har kasarsa. Suka zauna cikin jin dadi da kwanciyar hankali, har mai katse jin dadi, mai raba da da mahaifi, mai raba masoya ta zo musu. Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ KARSHE KENAM INSHA ALLAH' SAIKUMA INMUN HADU AWATA HIKAYAN, WhatsApp 08032767547 This Document is compiled by Shuraihu Usman - 08140419490 YEAR of compilation - 2023; Published to Taskarnovels.com.ng An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 14 of 14