Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
3 / 14
juya hagu, amma bai ga yarinyar nan da take kwance kusa gare shi ba. Sai ya ce a cikin ransa, "Wannan wane irin wasa da hankali ne mahaifina ke yi mini? Don me tun kafin na farka daga [ http://fb.com/ waziriaku ] barci za a zo a dauke yarinyar da aka kawo nan domin ta taya ni barci? Ba a ko bari gari ya waye in tambayi sunanta, mu yi zance da juna? Watau so ake yi sai na matsu na furta da bakina cewa ina sonta. To, wallahi ina sonta, bari yanzu in aiki bawan nan ya tafi ya sanar da mahaifina." Kamaruzzaman ya kwalla wa bawan nan kira da karfi, "Ya kai wannan rafkananne!" Bawa ya farka daga barci a firgice yana mutsuttsuke idanunsa da hannuwansa. Ya yi sauri ya debo ruwa ya kawo gaban [ http://fb.com/waziriaku ] Kamaruzzaman, ya durkusa ya mika masa. Kamaruzzaman ya dauki ruwa ya shiga bandakin da ke cikin dakinsa. Ya biya bukatarsa, sa'annan ya yi alwala. Ya fito daga bandaki, ya yi sallar asuba. Bayan ya sallame sallah ya karanta sunayen Allah tsarkaka dari ba daya. Ya yi addu'o'in da zai yi, ya shafa fatiha. Ya dubi inda bawa yake tsaye a bakin kofa yana gadinsa, ya ce masa, "Ya Sawab, shin wace [ http://fb.com/ waziriaku ] yarinya ce Sarki ya sa ta kwana wurina a daren jiya, kuma wa ya zo ya dauke ta da ina barci?" "Wace yarinya kake zance, ya shugabana?" Bawa ya tambaya cikin mamaki. "Yarinyar da ta kwana bisa shifidata mana. Kada ka yi mini wasa." Kamaruzzaman ya daka masa tsawa. [ http://fb.com/waziriaku ] Bawa ya tsorata, ya ce, "Ya shugabana, na rantse da Allah babu yarinyar da ta shigo wannan gida, balle ta shiga nan dakin har ta kwana bisa shimfidarka. Yaya ma za a yi na bari [ http:// fb.com/waziriaku ] wani mahaluki ya shigo inda kake idan ba Sarki ne ya aiko shi ba." + + + Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda yanzu haka na kasuwa... whatsapp only 08032767547(9) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN Bawa ya tsorata, ya ce, "Ya shugabana, na rantse da Allah [ http://fb.com/waziriaku ]babu yarinyar da ta shigo wannan gida, balle ta shiga nan dakin har ta kwana bisa shimfidarka. Yaya ma za a yi na bari wani mahaluki ya shigo inda kake idan ba Sarki ne ya aiko shi ba?" [ http:// fb.com/waziriaku ] "Karya kake yi, munafukin banza. Watau har da kai za a hada baki a yi wasa da hankalina ko?" Kamaruzzaman ya daka masa tsawa. [ http:// fb.com/waziriaku ] "To, ko dai ka fada mini gaskiya, ko kuma ka yaba wa aya zakinta!" Bawa ya rude, ya duka gaban [ http://fb.com/ waziriaku ] Kamaruzzaman yana rantse-rantse, yana cewa shi bai san da maganar wata yarinya ba. Maimakon rantse-rantsen nasa su sa Kamaruzzaman ya sauko, sai suka kara tunzura shi. Ya ce masa, "Ya kai la'annanen bawa, wato kai ma an koyar da kai yadda za a yi wasa da hankalina ko. [ http://fb.com/waziriaku ] Matso kusa gare ni in fada maka wata magana." Bawa ya matsa kusa ga Kamaruzzaman, wai ya ji abin da zai fada masa. To, Allah ya yi Kamaruzzaman kakkarfa ne, kuma ga shi jarumi. Sai ya sungumi bawan nan, ya yi koli-koli da shi [ http://fb.com/waziriaku ] ya kantara da kasa. Saboda tsananin zafin kayen nan sai da bawa ya saki tusa. Kamaruzzaman kuwa ya haye ruwan cikinsa ya yi ta bugu, yana cewa, "Fada mini gaskiya ko in kashe ka, ja'irin banza munafuki!" Bai daina bugun shi ba har sai da ya suma. [ http://fb.com/waziriaku ] Yayin da ya ga ya suma, sai ya rika jan shi a kasa har gindin rijiyar da ke tsakiyar gidan. Rijiyar irin mai karfen nan ce, wadda idan aka juya karfen sai gugar sauka kasan rijiyar. [ http://fb.com/waziriaku ] Idan an debo ruwan kuma sai a yi ta juya karfen gugar tana tahowa sama. Da [ http://fb.com/waziriaku ] Kamaruzzaman ya kai bawa bakin rijiya, sai ya kwance gugar, ya daure bawa tamau da igiya maimakon guda. Ya yi ta juya karfe bawa yana yin kasa har sai da ya ji ya shiga cikin ruwa. Daga nan kuma ya yi ta juya karfen, ya fito da shi waje, ya jike sharkaf da ruwa. Lokacin kuwa ana tsakiyar sanyin hunturu. [ http://fb.com/ waziriaku ] Kamaruzzaman ya ci gaba da jefe bawa cikin ruwan rijiya yana fitowa da shi har ya farfado daga sumansa, ya fara kururuwar neman taimako. Da Kamaruzzaman ya ji kururuwarsa, sai ya dago shi sama, ya ce, "Wallahi ba na kyale ka sai ka fada mini wace yarinya ce a ka kawo ta kwana wurina, kuma wanene ya dauke ta ina cikin barci?" [ http://fb.com/waziriaku ] A nan asuba ta riski Shaharuzad, ta katse zancenta mai dadin saurare. WANNAN SHI NE KARSHEN JUZU'I NA FARKO. JUZU'I NA BIYU Mun fara da sunan Allah mai gamammiyar kyauta a duniya, mai kebabben jin kai a lahira. Yabo ya tabbata ga Allah, ubangijin talikkai. Tsira da aminci su tabbata a kan shugabanmu, Annabi Muhammadu, shugaban ma'aika, da alayensa da sahabbansa [ http://fb.com/waziriaku ], da sauran al'ummar da ta amsa kiransa. Bayan haka, wannan shi ne farkon juzu'i na biyu na littafin Dare Dubu Da Daya, wanda aka zanta shi daga zantuttukan masu hankali, masana, mabiya hanyar labarun asali. Kun fara wannan juzu'i daga [ http://fb.com/waziriaku ] dare na dari daya da tamanin da bakwai wanda Shaharuzad take labarta wa Sarki Shaharumana da 'yar uwarta Dunyazad. Ga Allah muke neman tsari, gare shi muke dogaro ga dukkan al'amurranmu. [ http://fb.com/waziriaku ] A dare na dari da tamanin da bakwai, Shaharuzad ta ce, na sami labari ya kai wannan hamshakin Sarki, Kamaruzzaman ya ce da bawa, "Wallahi ba na kyale ka sai ka fada mini wace yarinya ce ta kwana wurina kuma [ http:// fb.com/waziriaku ] wa ya dauke ta lokacin da nake barci." Yayin da bawa ya ga Kamaruzzaman na shirin halaka shi, sai ya ce, "Ya shugana, na san da maganar, kwance ni. Na rantse da Allah zan fada maka kome." [ http://fb.com/waziriaku ] Yayin nan Kamaruzzaman ya fitar da shi daga cikin rijiya, ya kwance masa dauri. Bawa ya zama kamar wanda ya fito daga lahira saboda tsoro da [ http://fb.com/waziriaku ] kuma wahalar da ya sha ta tsunduma shi cikin rijiya da Kamaruzzaman ya yi ta yi. Tufafinsa sun yi sharkaf da ruwa, duk jikinsa sai rawar dari yake yi, kamar tsohon dan taurin da ya jiyo kidan farauta. Hakoransa [ http://fb.com/waziriaku ] na gamuwa, kaf kaf kaf, kamar tsohuwar da aka zaro daga cikin kankara. Kansa duk ya yi molallai har jini yana fita saboda bugun bangayen rijiya. Da Kamaruzzaman ya gan shi cikin wannan hali sai tausayinsa ya kama shi. [ http://fb.com/ waziriaku ] Bayan bawa ya dan murmure, sai ya ce wa Kamaruzzaman, "Ya shugabana, don Allah ka bari in tube wadannan jikakkin tufafin nawa, in shanya su ga rana. In canja wasu, kada sanyi [ http://fb.com/waziriaku ] ya halaka ni, sa'annan in komo nan in ji dadin fada maka abin da ya faru a cikin daren jiya, domin da ni aka shirya kome." [ http://fb.com/waziriaku ] Kamaruzzaman ya ce da shi, "Tafi ka yi yadda kake so. Ka dai ga 'yar karamar azabar da na yi maka ko? To, idan ka dawo ba ka fada mini gaskiya ba, na rantse da Allah sai na lahira [ http://fb.com/waziriaku ] ya fi ka jin dadi." Bawa ya fita daga wurin Kamaruzzaman, bai gasgata kubutarsa ba. Yana fita waje sai ya dafe keya, ya zura a guje, yana faduwa yana tashi, bai zame ko'ina ba sai gaban karagar [ http:// fb.com/waziriaku ] Sarki Shaharuzzaman. A lokacin kuwa Sarki na cikin magana da Waziri yana ce masa, "Ya Waziri, ka sani cewa tsawon daren jiya ban runtsa ba. Ina cike da tunanin Kamaruzzaman kada wani mugun abu ya same shi a cikin gidan gonar nan. Ka san an [ http:// fb.com/waziriaku ] dade ba a yi amfani da shi. Shin wai ma, menene amfanin tsare shi a can?" Waziri ya ce, "Kada ka damu, Allah ya ba nasara. In Sha Allahu babu abin da zai same shi. Ka bar shi can tsawon wata guda, [ http://fb.com/ waziriaku ] har sai ya bi da kansa, ya koma cikin hankalinsa." Suna cikin wannan zance sai ga bawa, mai gadin Kamaruzzaman, ya fado cikin fadar da gudu, wujiga-wujiga, kamar wanda kura ta biyo. Yana zuwa ya fadi gaban karagar [ http://fb.com/ waziriaku ] Sarki yana cewa, "Kaiconmu ya Sarki mai cikakken iko! Babu makawa danka ba ya da lafiya, ya haukace! Ya buge ni, ya shure ni, ya yi mini kaza da kaza, har na zama kamar yadda kake ganina yanzu." Bawa ya fada wa Sarki dukkan abin da Kamaruzzaman ya yi masa na azaba. [ http://fb.com/waziriaku ] Ya ci gaba da cewa, "Ya matsa mini wai sai na fada masa wace yarinya ce aka tura ta kwana wurinsa, kuma wanene ya dauke ta da yana barci. Na rantse masa, na kuma na rantse masa, babu yarinyar [ http://fb.com/waziriaku ] da ta kwana wurinsa, amma bai yarda ba. Ya shugabana, na rantse da Allah babu wanda ya kwana tare da shi, domin ban daga zuwa ko'ina ba, daga bakin kofar dakinsa ina gadinsa." Yayin da Sarki Shahruzzaman ya ji bayanin bawa, sai ya mike cikin fushi, ya yi tsawa ga Waziri yana cewa, "Ga abin da nake gudu nan! Tashi maza [ http://fb.com/waziriaku ] ka tafi wurin dana, ka samo mini labarin abin da yake ciki." Nan take Waziri ya tashi cikin hanzari, buje yana tade shi, cikin tsoro, ya saka bawa gaba suka nufi gidan gona wurin Kamaruzzaman. [ http:// fb.com/waziriaku ] *** *** *** Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA,.. Whatsapp only pls 08032767547(10) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN Yayin da Sarki Shahruzzaman ya ji bayanin bawa, sai ya mike cikin fushi, ya yi tsawa ga Waziri yana cewa, "Ga abin da nake gudu nan! Tashi maza ka tafi wurin dana, ka samo mini labarin abin da yake ciki." Nan [ http://fb.com/ waziriaku ] take Waziri ya tashi cikin hanzari buje yana tade shi, cikin tsoro, ya saka bawa gaba suka nufi gidan gona wurin Kamaruzzaman. Ko da su ka isa gidan hantsi ya yi, suka tarar da Kamaruzzaman zaune bisa shimfidarsa yana karanta Alkur'ani mai tsarki. Bawa ya tsaya daga bakin kofar daki, idan ya ji kyasham sai ya arce. Waziri ya shiga cikin dakin ya zauna [ http:// fb.com/waziriaku ] gefen Kamaruzzaman. Da Kamaruzzaman ya gan shi sai ya dakata da karatu, ya rufe littafin ya ajiye gefe. "Wannan rudadden bawan ne ya je wa Sarki da wani rikitaccen labari wanda ya tayar masa da hankali." In ji Waziri. "Me ya fada wa Sarki wanda ya tayar masa da hankali, fiye da abin da Sarkin ya yi mini, wanda ya [ http://fb.com/waziriaku ] tayar mini da hankali?" Kamaruzzaman ya tambaya. Waziri ya gyara zama ya ce, "Ya je mana afujajan, kamar wanda ya kwaci kansa da kyar daga sabon mahaukaci, ya ba mu labari na karya game da kai, wanda bai kyautu in maimaita wannan karya tasa ba. Domin da ganin halin da kake ciki yanzu, na tabbatar da labarinsa karya ne." "Wai me ya fada muku ne game da ni, ka tsaya kana ta yi mini 'yan zagaye-zagaye?" Kamaruzzaman ya tambaya, ransa ya fara baci, domin ya ga alamar Waziri na [ http://fb.com/ waziriaku ] shirin boye masa maganar yarinyar da ya gani jiya cikin dare. Waziri ya ce, "Ce mana ya yi wai ka tabu! Saboda ka matsa masa sai ya fada maka wace yarinya ce aka kawo ta kwana wurinka, jiya da dare. Kuma wai wanene ya dauke ta da kana barci. Ya ce wai har cikin rijiya ka yi ta tsunduma shi don ya ce maka bai ga kowa ba?" [ http://fb.com/waziriaku ] Yayin da Kamaruzzaman ya ji zancen Waziri, sai ya cika da fushi, fushi mai tsanani. Ya juya ya dubi Waziri ido da ido, ya ce, "Yanzu na tabbatar da cewa ku ne kuka kitsa wa wannan munafukin bawan ya yi abin da kuka shirya masa. Kuka hane shi da ya fada mini kome a kan yarinyar da kuka turo ta kwana tare da ni. Na san ka Waziri da tsananin dabara, wannan ba shawarar kowa ba ce face kai. Kai ne ka sa aka turo ta wajena [ http://fb.com/waziriaku ] domin ta canja mini ra'ayi game da maganar aure. Ta kwana tare da ni, da kuka ga asuba ta kusa sai kuka lallabo kuka dauke ta. To, dabararka ta ci, na yarda zan aure ta, amma tana ina yanzu?" Da Waziri ya ji zancen Kamaruzzaman, sai ya ce, "Na rantse da Allah, ya shugabana Kamaruzzaman, ba mu turo kowa ya kwana wurinka ba a daren jiya. Kai kadai ka kwana a kan shimfidarka, sai bawan da ke gadinka a [ http://fb.com/waziriaku ] bakin kofa. Babu wata yarinya da muka turo wurinka. Yi tunani dai ka gani, ya shugabana." Kamaruzzaman ya ce cikin tausasa murya, "Na kamu da son wannan yarinya da na gani a daren jiya. Ita ce shugabar [ http://fb.com/waziriaku ] kyawawa, mai fararen idanu da jajayen kundukuki. Mun kwana kan shimfida guda tare da ita." "Shin ka ganta ne kuru-kuru da idonka, ko kuwa dai cikin mafarki ka gan ta?" Waziri ya tamabaya, domin lamarin Kamaruzzaman ya fara daure masa kai. Kamaruzzaman ya amsa masa cikin fushi, "Da, da kunnuwana kake sa ran zan gan ta, yau ga dattijon wofi. Da idona na gan ta, kuma na dade ina kallon kyakkyawar fuskarta. Har girgiza ta na yi ta yi da hannuwana domin ta farka mu yi zance, amma da yake kun umurce ta da [ http:// fb.com/waziriaku ] cewa kome na yi mata kada ta kula, sai ta yi kamar barci ta ke yi, ta kyale ni. Da na gaji da tayar da ita, na ga ta ki tashi, sai na kwanta kusa gare ta har barci ya dauke ni. Ko da na farka da safe sai na ga har kun sa an dauke ta.""Babu shakka wannan mafarki ne, ya shugabana Kamaruzzaman. Ko kuma watakila ka yi wasu ciye-ciye ko shaye-shaye da suka kawar maka da hankali kafin ka kwanta. Ko kuma mai yiwuwa siddabaru ne na miyagun [ http://fb.com/ waziriaku ] aljanu." In ji Waziri. "Kai tsohon banza! Ni za ka yi wa wasa da hankali, bayan wannan munafukin bawan ya ce zai fada mini gaskiya. Ya fada mani da shi kuka shirya kome. Ni za ka fada wa cewa wai mafarki ne nake yi, bayan na ga abu kuru-kuru da idona ina farke?" Kamaruzzaman na fadin haka, sai ya tasowa Waziri ya kama gemunsa ya ja shi [ http://fb.com/waziriaku ] da karfi. Waziri ya ji kamar ransa zai fita. Kamaruzzaman ya dunkule hannu ya yi ta dimar Waziri, hannunsa daya yana rike da gemunsa. Waziri ya yi ta ihu yana hargowa, da dai ya ga babu ko shakka Kamaruzzaman zai halaka shi, sai ya ce a cikin ransa, "Bari in yi dabarar da bawan nan ya yi, tabbas wannan yaro ya haukace." "Dakata, dakata, na san da zancen, ya [ http:// fb.com/waziriaku ] shugabana." Waziri ya fada cikin karaji da zafin duka. Daga nan sai Kamaruzzaman ya daina bugun shi. Waziri ya ci gaba da cewa, "Ka gafarce ni ya shugabana, Sarki ne ya ce in boye wannan magana, kada in sanar da kai. Hakika mu ne muka shirya wannan dabarar, muka turo wannan yarinya ta kwana wurinka domin mu gani ko za ka amince da [ http://fb.com/waziriaku ] maganar aure. Amma yanzu ka ga na wahala ga hannunka, na sha bugu kamar jaki. Ka sake ni in dan sarara in huta, na yi alkawari zan fada maka kome game da wannan kyakkyawar yarinya da ka gani." Da jin haka sai Kamaruzzaman ya sakar masa gemu, ya ce, "Ka dai ji kunya, tsohon banza! Don me ka tsaya yi mini karairayi, bayan ka san da zancen? Ba ka tashi fada [ http://fb.com/ waziriaku ] mini gaskiya ba sai da ka sha wuya. Maza ka fada mini labarinta." "Kana nufin kyakkyawar yarinyar da ta kwana wurinka jiya da dare?" Waziri ya tambaya yana daddafa gemunsa. "I, ita nake nufi. Ka fada mini, ya kai Waziri, wacece wannan yarinya, wa ya kawo ta wurina lokacin da nake barci, wanene kuma ya dauke ta kafin gari ya waye? Ka fada mini tana ina a halin yanzu, [ http://fb.com/waziriaku ] domin ina so in kara ganinta. Idan dai har an jarraba ni ne da kyawunta a kan bukatar mahaifina ta in yi aure, to, na yarda zan aure ta in huta da wannan matsi da tsangwama da kuke nuna mani don na ki yin aure. Yanzu na amince, bari na kara fada, na amince zan yi aure. Ka tafi ka fada wa mahaifina, ya kai Waziri, a aura mani wannan yarinya domin zuciyata [ http://fb.com/ waziriaku ] ta riga ta mace cikin sonta. Babu wata mace da nake so yanzu idan ba ita ba. Ka tashi yanzu da hanzari ka tafi wurin mahaifina ka shaida masa wannan magana, kuma ina so ka maido mani da jawabi yanzu-yanzun nan." Waziri ya ce, "Na ji na dauka." Ya tashi da sauri ya fice daga cikin dakin Kamaruzzaman yana godiya ga Allah da ya kubutar da shi daga hannun wannan yaro da bai halaka shi ba. Ya fita daga gidan gona yana sauri, buje yana tade masa kafafu, ya fadi ya tashi, har ya isa wurin [ http:// fb.com/waziriaku ] Sarki Shahruzzaman. . Yayin da Sarki ya gan shi cikin wannan hali sai ya tambaye shi, "Ya Waziri, wane mutum ne ya aikata maka wannan abu haka? Yaya nake ganin fuskarka duk ta kumbura haka kamar wanda ya fito daga filin daga?" Waziri ya ce, "Ya shugabana, na zo maka da albishir." [ http://fb.com/waziriaku ] "Wane irin albishir ne ka kawo mani?" Sarki Shahruzzaman ya tambaya. Waziri ya ce, "Babu shakka danka Kamaruzzaman ya haukace, mummunan hauka." Yayin da Sarki ya ji haka sai ransa ya baci, hasken da ke fuskarsa ya koma duhu. [ http:// fb.com/waziriaku ] Ya dubi Waziri ya ce, "Ya kai Waziri, wane irin hauka ne ya samu dana?" Waziri ya kwashe labarin dukkan abin da ya faru tsakaninsa da Kamaruzzaman ya fada wa Sarki." Da Sarki ya ji haka sai ya ce cikin fushi, "Ka sani cewa, ya kai Waziri, zan ba ka goron wannan albishir da ka kawo mani na haukacewar dana. Goron [ http://fb.com/waziriaku ] da zan ba ka kuwa shi ne datse kanka da takobi, ya kai karen wazirai. Domin kuwa kai ne wanda ka ba ni shawarar in tsare shi cikin wannan gidan gona. Na rantse da Allah idan dai har dana ya haukace da gaske, babu makawa sai na tsire ka a gaban fada kowa na kallo, ka yi mutuwar wulakanci." [ http://fb.com/waziriaku ] Daga nan Sarki ya mike tsaye cikin hanzari ya nufi gidan gonar da aka tsare Kamaruzzaman, Waziri ya bi shi a baya jikinsa na rawa don tsoro. Suna isa, Sarki ya wuce cikin gidan kai tsaye tare da Waziri. Kamaruzzaman na ganin mahaifinsa, sai ya tashi tsaye daga kan abin zama. Ya zo gaban mahaifin nasa ya durkusa ya gaishe shi cikin ladabi sa'annan ya mike tsaye ya mayar da hannuwansa [ http://fb.com/waziriaku ] ga bayansa ya harde su, ya sunkuyar da kansa kasa. Sarki da Waziri da Kamaruzzaman suka yi tsaye cirko-cirko, tsawon sa'a guda babu wanda ya ce uffan. Daga nan sai Kamaruzzaman ya dago kansa, ya dubi mahaifinsa, idanunsa cike da hawaye har yana gudana kan kundukukinsa. Ya waka wadannan baitoci: "Yafe mani laifukana, kafafuna na kakkarwa domin laifukan da na yi. Bawa na neman afuwar ubangijinsa. Na aikata laifi, ina neman yafuwarka da gaggawa. Shin har zuwa yaushe ne wannan yafuwar za ta kasance?" Yayin da [ http://fb.com/waziriaku ] Sarki ya ji wannan waka daga bakin dansa, sai ya cika da farin ciki. Ya rungume shi, ya sumbaci goshinsa. Suka zauna kan shimfida, Sarki ya zaunar da Kamaruzzaman kusa gare shi, ya harari Waziri ya ce, "Ya karen wazirai! Me ya sa ka fada mini karya game da dana? Ka ce ya aikata kaza da kaza, har ma ka ce ya haukace. Ka jefa raina cikin damuwa." [ http://fb.com/waziriaku ] *** Waziri Aku *** Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, Wanda yanzu haka na kasuwa (11) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN Yayin da Sarki Shaharuzzaman ya ji wannan waka daga bakin dansa, sai ya cika da farin ciki. Ya rungume shi, ya sumbaci goshinsa. Suka zauna kan shimfida, Sarki ya zaunar da Kamaruzzaman kusa gare shi, ya harari Waziri ya ce, "Ya karen wazirai! Me ya sa ka fada mini karya game da dana? Ka ce ya aikata kaza da kaza, har ma ka ce ya haukace. Ka jefa raina cikin damuwa." Sarki bai ko jira jin ta bakin Waziri ba, sai ya juya wurin Kamaruzzaman ya ce, "Dana, wace rana muke ciki yau?" "Yau Assabar, karshen mako. Gobe Lahadi, sai Litinin, Talata, Laraba, Alhamis sai Juma'a." Kamaruzzaman ya amsa wa Sarki. Sarki ya ce cikin murna, "Ya dana, Kamaruzzaman, farin cikin raina, Wallahi zancenka haka yake, ban ga alamun tunaninka ya jirkita ba. To, amma wannan wane wata ne?" Kamaruzzaman ya ce, "Yanzu muna cikin watan Zulkida ne, yau kwanansa goma sha shida. Daga shi sai Zulhijja, sai Muharram, sai Safar, sai Rabiu Awwal da Rabiu Sani, sai Jimada Ula da Jimada Ahir, sai Rajab, sai Sha'aban, sai Ramadan, sai Shawwal." Sarki Shaharuzzaman ya raurawa da farin ciki, ya dubi Waziri ya tofa masa yawu a fuska ya ce, "Tsohon banza, makaryaci! Don me kake ce wa dana mahaukaci? Lalle ba kowa ne mahaukaci ba face kai, ya kamata a daure ka a turu." Waziri ya goge fuskarsa da hannun rigarsa, ya so ya yi magana sai wata zuciyar ta ce masa, "Kara jira dai ka ga abin da zai faru." Sai ya yi shiru bai ce kome ba. Sarki ya juya wurin Kamaruzzaman, ya dafa kafadarsa ya ce, "Ya dana, shin mecece gaskiyar maganar da bawan nan mai gadinka da Waziri suka je mini da ita? Sun ce, wai ka matsa musu sai sun fada maka labarin wata yarinya da ta kwana wurinka. Wace yarinya ce wannan kake magana a kanta?" Yayin da Kamaruzzaman ya ji wannan tambaya daga mahaifinsa sai ya yi dariya, ya dubi mahaifin nasa ya ce, "Ya mahaifina, Wallahi na gaji da irin wannan wasan da kuke yi mini haka nan. Na riga na fada wa Waziri, ya shaida maka cewa na amince zan yi aure, kamar yadda ka bukata. Amma fa ba zan auri kowa ba face yarinyar da kuka turo ta kwana wurina jiya. Saboda na tabbata kai ne ka turo ta wurina domin ta canja mini ra'ayi. Ka sani ya kai mahaifina, wannan tarko naka ya kama ni. Ka gaggauta aura mini ita ko na sami nutsuwa." Nan take fuskar Sarki ta canja da jin wannan jawabi na dansa, ya ce, "Don girman Allah wanda ya halicce ka, ka bar kokarin saka kanka cikin zancen shirme. Wace irin yarinya ce wannan wadda kake ta zancen wai na turo ta, ta kwana wurinka, kuma na sa an dauke ta kafin safiya? Na rantse da Allah, ya dana, ban san kome ba game da wannan zance naka, babu shakka ba kome ba ne wannan face mafarki. Domin lokacin da ka bar wurina jiya, ka yi ta tsine wa mata, kuma kana cewa, 'Allah ya tsine wa duk wanda ya ba da shawarar a yi mani aure.' Ka sani cewa duk abin da mutum ya kwanta da shi a cikin ransa, to, babu makawa mafarkin wannan abu zai yi. Ka kwanta ne da maganar aure a cikin ranka, shi ya sa ka yi mafarki da wannan yarinya da ka ce ta kwana kusa gare ka. Amma in bayan kai da bawa mai gadin ka, babu wanda ya kwana a cikin wannan gida." Idanun Kamaruzzaman suka yi ja, suka cika da hawaye, ya ce wa mahaifinsa, "Ya mahaifina, ina so ka rantse mini da Allah, wanda ya halicce ka, ya sanya maka rayuwa, wanda kuma zai shake rayuwarka, idan kwananka ya kare, cewa ba kai ne ka turo wannan yarinyar wurina ba, ba ka san daga inda ta fito ba, kuma ba ka san wanda ya turo ta ba." Sarki ya ce, "Na rantse da Allah madaukakin Sarki, Ubangijin Musa da Ibrahim, ban san kome ba game da wannan yarinya da kake zance. Ni ina ganin ba kome ba ne wannan, face yaye- yayen mafarki." Kamaruzzaman ya ce, "Yanzu kuwa zan nuna maka shaidar cewa, wannan yarinya da na gani, ba yaye-yayen mafarki ba ne. Na gan ta da idona kuru-kuru, yayin da nake farke cikin hankalina. Amma bari in tambaye ka wani abu." Sarki ya ce, "Menene wannan abu?" Kamaruzzaman ya ce, "Shin ka taba ganin wanda ya kwanta barci, ya yi mafarki yana yaki, yaki mai tsanani. Da ya farka sai ya gan shi da zararren takobi rike ga hannunsa har takobin na digar da jini?" Sarki ya ce, "Ban taba gani ba, ban kuma taba jin haka ba. Ai wannan ba abu ne mai yiwuwa ba" Fuskar Kamaruzzaman ta washe da wannan amsa da Sarki ya ba shi, har ya yi murmushi hakoransa suka bayyana. Sannan ya gyara zama, ya nutsu, ya dubi mahaifinsa ya ce, "Ya mahaifina, Wallahi kwatankwacin wannan abu ne ya faru gare ni. Ka sani cewa, ina cikin barci jiya da dare, sai wani kwaro ya cije ni na farka. Ko da na farka sai na ga wata kyakkyawar yarinya, wadda ban taba ganin mace mai kyau kamarta ba, tana kwance kusa gare ni tana barci. Na girgiza ta domin ta tashi in ji ko wace ce ita, amma ba ta farka ba. Na yi niyyar in sumbace ta, sai na ji kunya watakila kana nan labe kana kallonmu, domin a zatona tarko ne ka dana mini da ita, ka ga me zan aikata gare ta, tun da na bijirewa bukatarka ta yin aure. Da na tuna da wannan a cikin raina, sai na sa hannu na cire zobenta, na saka shi a dan yatsana na kwanta, barci kuwa ya dauke ni. Yayin da na farka da asuba, na duba ko'ina babu yarinya babu dalilinta, na dubi hannuna domin na ga ko mafarki ne na yi, amma sai na ga zobenta a hannuna, kuma sai na lura da ta cire nawa zoben ta tafi da shi." Kamaruzzaman ya ci gaba da cewa, "Ya mahaifina, Wallahi ba domin wannan zobe nata ba, da ban tayar da maganar ba, sai in dauka mafarki ne kawai na yi. To, amma ga zobenta nan a hannuna." Ya cire zobe ya mika wa Sarki. Sarki ya karbi zobe ya jujjuya shi ga hannunsa, ya gan shi zobe ne mai tsada, mai daraja, ya girgiza kansa cikin mamaki, ya ce, "Hakika wannan abu da ya faru gare ka, ya dana, rikitaccen al'amari ne mai wuyar kan gado. Amma ba laifin kowa ba ne wannan face Waziri, wanda shi ne sanadin tsare ka a cikin wannan gida." Sarki ya shafa kan Kamaruzzaman ya ce, "Ya dana, ka kwantar da hankalinka, da yardar Allah madaukakin Sarki, za mu sami hanyar warware wannan rikitaccen al'amari cikin sauki ya zuwa ga cikar burinka. Kamar yadda wani mawaki yake cewa: "Da sannu al'amari kan juye, Farin ciki ya kan komawa. Sa'ar zamani takan lauye, Mai kuka ya zan darawa." Sarki ya ci gaba da cewa, "Ya dana, yanzu hankalina

Chapter 3 of 14