Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
4 / 14
ya kwanta, na tabbata cewa babu abin da ya same ka na gushewar hankali. Sai dai wannan al'amari da ya faru gare ka, abu ne da ba a taba gani ba, ko jin labarin irinsa ba." Kamaruzzaman ya rungume mahaifinsa, ya rika magana cikin shagwaba kamar wanda zai yi kuka, yana cewa, "Ya mahaifina, ina rokonka da ka gaggauta nemo wannan yarinya duk inda take, ka nema mini aurenta, na amince zan aure ta. Wallahi ba zan iya rayuwa ba, ba tare da ita ba. Idan kuwa ka ki zancena, ina tabbatar maka cewa, bakin cikin rashinta da tunaninta za su kashe ni." Daga nan sai idanunsa suka fara zubar da hawaye shar shar shar. Sannan ya sake cewa da mahaifinsa, "Na rantse da Allah, ya mahaifina, ba na jin zan iya kara sa'a daya ba tare da na saka wannan yarinya a idona ba." Sarki Shahruzzaman ya rika tafa hannuwansa cikin takaici da mamaki yana cewa, "Babu tsimi babu dabara face daga Allah madaukakin Sarki. Ya Ubangijin talikai, ka gaggauta biya wa wannan yaro bukatarsa." Daga nan ya riki hannunsa, ya ja shi suka koma gida, suka bar wannan gidan gona. Suna isa gida sai Kamaruzzaman ya fadi kwance a kan shimfida. Wasa-wasa abu ya zamar masa ciwo. Sarki kuwa sai ya kasance kullum yana wurinsa, dare da rana, yana zubar da hawaye. Ya daina zuwa fada kwata-kwata. Da Waziri ya ga kwana da kwanaki Sarki bai fita fada ba, sai ya same shi inda yake jiyyar Kamaruzzaman. Ya durkusa ya ce masa, "Allah ya ba ka nasara, har zuwa wane lokaci za ka ci gaba da zama nan tare da danka, ka daina fita zuwa ga askarawa? Ina jiye maka tsoron kada askarawa su yi maka tawaye saboda rashin zamanka kusa gare su, kana lura da abubuwan da ke faruwa a cikinsu. Masu hikima sukan ce idan ka na da raunuka da yawa a jikinka, to ka fara shafa wa rauni mafi tsanani magani kafin ka shafa wa sauran raunukan." Da Waziri ya ji Sarki bai ce masa kome ba, sai ya kara dukar da kansa kasa, ya ci gaba da cewa, "Ya shugabana, shawarar da zan ba ka ita ce, ka dauki danka Kamaruzzaman ka mayar da shi gidanka, wanda yake a bakin teku, a rika jiyyar shi a can. Tunda gidan ba ya da nisa da fada, sai ka rika zuwa fada duk ranar Litinin da Alhamis kana ganawa da Waziranka, da fadawanka, da alkalanka, da hakimai da masu unguwa da dagatai da askarawanka da sauran talakawanka. Ka yi umurni, ka yi hani a cikinsu, ka tube ka kuma nada. Ya kasance dai kana gudanar da lamurran mulki a cikin al'ummarka. Alabashi sauran ranaku sai ka kasance tare da danka, har Allah ya kawo mana hanayar da za a warware wannan matsala tasa. Amma muddin ka ci gaba da hana jama'arka zuwa gare ka, to ina jiye maka tsoro wani abu ya faru ga mulkinka." Wannan shawara ta Waziri ta daki zuciyar Sarki, ta maido da shi cikin hayyacinsa, domin shi har ya manta da wata abu wai ita sarauta. Nan take ya sa aka dauki Kamaruzzaman aka mayar da shi a wancan gidan na bakin teku. Gidan an gina shi ne akan dutse, wani bangare na ruwan teku yana bi ta karkashin dutsen da gidan yake a kai. Tagogin gidan da kofofinsa, wadanda aka yi da zinariya, suna kallon ruwan teku. Rufin gidan kuwa an yi masa fenti da launuka masu ban sha'awa. Daben gidan kuwa an yi shi ne da farin dutse. An shimfide gidan da dukkan shimfidu na alfarma masu tamanin gaske. Da aka zo da Kamaruzzaman cikin gidan a ka kwantar da shi bisa shimfida a cikin wani daki da aka kawata da kayan alatu. Sai ya kasance Sarki yana fita fada duk ranar Litinin da Alhamis, ya hadu da jama'arsa, yana hukunci a tsakaninsu. Saura ranaku kuwa sai ya zauna kusa ga dansa yana zubar da hawaye saboda abin da ya same shi na ciwon so. Cikin 'yan kwanaki kadan, Kamaruzzaman ya rame, ya lalace, ya yi baki har ta kai ga ba ya iya cin kome sai abu mai ruwa, shi din ma sai an dura masa. Wannan shi ne abin da ya faru ga Kamaruzzaman dan Sarki Shahruzzaman. Amma abin da ya faru ga Badura 'yar Sarkin kasar Sin kuwa shi ne, bayan aljanu sun ajiye ta bisa shimfidarta, sai ta ci gaba da sharar barci har gari ya waye. Tana farkawa, sai ta duba dama, ta duba hagu, ba ta ga saurayin da yake kwance kusa gare ta ba. Daga nan sai ta yi kara, kara mai tsanani. Nan take kuyanginta, da tsofaffin matan nan masu kula da ita suka shigo wurinta a firgice. Daya daga cikin tsofaffin ta durkusa ta tambaye ta, "Me ya same ki, ya shugabata?" Badura ta harari 'yar tsohuwa ta daka mata tsawa, "Ya ke makirar tsohuwa! Ina kuka kai mini masoyina abin begena, wannan da ya kwana wurina?" *** Waziri Aku *** Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda nan akasuwa yanzu haka'..., Yusuf A jibaga' ke muku barka da dare(12) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN Badura ta harari 'yar tsohuwar dake durkushe a gabanta, ta daka mata tsawa, "Yake makirar tsohuwa! Ina kuka kai mini masoyina, wannan da ya kwana wurina?" http://facebook.com/ waziriaku Tsohuwa ta rude, ta ce, "Ya shugabata, wace irin magana ce wannan kike yi. Wallahi babu wani namiji da ya matso kusa da kofar dakin nan naki balle http://facebook.com/waziriaku har ya kwana cikinsa." "Karya kike yi, makirar tsohuwa!" Badura ta fada cikin tsawa, "Ina kuka kai mini abin begena, mai hasken fuska, mai jajayen kundukuki, mai fararen idanu da kyawawan girar idanu, mai http:// facebook.com/waziriaku matsakaicin jiki, sanyin zuciyata, farin cikin rayuwata, wanda muka kwana ina rungume da shi ga jikina tun da dare har kusan wayewar gari?" 'Yar tsohuwa ta marairaice tana rantse-rantse, tana cewa, "Na rantse da Allah, ya shugabata, mu, ba mu ga wani saurayi ba a cikin http:// facebook.com/waziriaku wannan gida. Kuma muna rokon ki don Allah ki rufa mana asiri, idan har wasa kike yi, kada wannan magana ta kai ga kunnen Sarki. Domin kuwa idan Sarki ya ji labari cewa wai wani namiji ya kwana a cikin http:// facebook.com/waziriaku wannan gida, wa zai kubutar da mu daga azabarsa?" "Ina tabbatar muku cewa wani saurayi ya kwana a cikin wannan dakin tare da ni a http:// facebook.com/waziriaku daren jiya, saurayin da ban taba ganin kyakkyawa kamarsa ba." In ji Badura. Wata kuyanga ta tsoma bakinta, ta ce, "Ya shugabata, watakila dai mafarki ne kika yi, amma babu wani saurayi da ya kwana a http:// facebook.com/waziriaku wannan gida." Badura ta duba yatsun hannunta, sai ta ga babu zobenta, sannan kuma ga zoben Kamaruzzaman da ta cire ta sa a dan yatsanta. Ta dubi kuyanga ta ce, "Allah ya la'ane ki! Don me za ku yi mini karya, ku ce http://facebook.com/waziriaku babu saurayin da ya kwana a dakina. Kina iya rantsewa a kan abin da kika fada?" "Na rantse da Allah Madaukakin Sarki, maganar da na fada miki gaskiya ce. Ba zan http:// facebook.com/waziriaku rantse miki a kan karya ba." Wannan rantsuwa ta kuyanga ta dugunzuma ran Gimbiya Badura, ta sake duba yatsun hannunta. Nan take cikin fushi ta zare wata takobi da ke kusa gare ta, ta dauke kan wannan http://facebook.com/waziriaku kuyanga. Sauran kuyangi da tsofaffin nan na ganin haka, sai suka yi waje da gudu, wata na ture wata suna faduwa, suka nufi wurin Sarki. Da Sarki ya ji wannan http://facebook.com/ waziriaku labari, nan take ya tafi gidan da 'yarsa taka tsare, ya ce da ita, "Ya 'yata, me ya same ki?" Ta amsa masa, "Ya mahaifina, ina saurayin da ya kwana wurina a daren jiya?" Daga nan sai shaukin begen Kamaruzzaman ya buge ta, ta juya da idanunta http://facebook.com/waziriaku dama ta juya da su hagu, kamar mai neman wani abu a cikin dakin. Ta dage rigar baccinta har kirjinta ya bayyana, tana tunanin yadda ta rungume Kamaruzzaman, gaba daya ta manta da mahaifinta da sauran kuyangi suna cikin dakin. http://facebook.com/waziriaku Yayin da mahaifinta ya ga haka, sai ransa ya baci, ya daka wa kuyangi tsawa da su kama ta su daure. Cikin kankanin lokaci, kuyangi suka taushe http://facebook.com/waziriaku Badura suka buga mata sarka ga wuya da hannuwa da kafafu, suka daure ta a turken tagar dakinta. Suka rufe dakin suka tafi suka bar ta. Bakin ciki a wurin mahaifinta, ba a ko maganarsa saboda tsananin son da yake yi mata. http:// facebook.com/waziriaku Sarkin Sin ya ba da sanarwa a cikin fadin kasarsa gaba daya, duk wani mai maganin da ya ba 'yarsa magani ta warke, to, zai aura masa ita, kuma zai raba kasarsa biyu ya ba shi rabi. Amma kuma duk mai maganin da ya yi http:// facebook.com/waziriaku ido hudu da 'yarsa, ya kuma kasa ba ta maganin da za ta warke daga cutar da take ciki, to, za a fille masa kai, a sargafe kan a gaban gidanta. Daga nan masu magani suka yi ta barkowa domin jaraba sa'arsu, amma babu daya daga cikinsu wanda ya yi nasara. Duk wanda ya http://facebook.com/waziriaku yi iyakacin kokarinsa ya kasa, sai Sarki ya sa a fille kansa. Haka aka yi ta fille kawunan masu magani har aka kashe mutum arba'in, duka aka sargafe kawunansu a gaban gidan da Badura take tsare. Wannan abu ya ba http://facebook.com/ waziriaku mutane tsoro, domin ba a taba ganin ciwon da ya gagari wadannan bokaye da aka kashe ba, don haka sai kowa ya hadiye kwadayinsa, ya shafa wa kansa ruwa. Ita kuwa Badura kullum begen Kamaruzzaman sai kara mamaye mata zuciya http:// facebook.com/waziriaku yake yi. Duk ta rame ta kare, babu abin da take yi kullum sai kuka, idan ta gaji da kuka kuma sai ta rera wadannan baitoci: "Ni mai bege ce a gare ka, Kai ne wata mai haske idona. Ambaton sunanka karatu, Dadinsa nakan ji dare ko rana. Wutar begenka tana kona ni, Kamar Jahima cikin kirjina. Kullum kwancina ba juyi, Sai hawaye gun sa idona." Sai kuma ta rera wadannan: http:// facebook.com/waziriaku "Na dulmiya kogin kauna, Wa zai cetan ban da masoyi? Miko hannunka na kama, Kar ka bar ni ruwa ya masoyi! Sannu, ba ta warke cuta, Ido na kuka don ka masoyi. Garin masoya ba ya nisa, Ka zo mu gana haba masoyi!" http://facebook.com/waziriaku Da zarar ta waka wadannan baitoci kuma, sai ta yi ta kuka, har sai hawayenta sun kafe idanunta sun kumabura. Haka ta kasance a cikin wannan hali tsawon shekara uku. To, gimbiya Badura tana da wani dan uwan shayarwa, watau wanda mai shayarwa daya ta shayar da su lokacin da suna jarirai. Sunan wannan dan uwan shayarwa nata Marzuwan. Wadda ta shayar http://facebook.com/waziriaku da su kuwa ita ce mahaifiyar Marzuwan, domin aikinta ke nan shayarwa. Lokacin da ta haifi Marzuwan a lokacin ne kuma aka haifi Badura, don haka sai Sarki ya damka shayarwar Badura a http://facebook.com/waziriaku hannunta. Ita kuma ta ci gaba da shayar da ita tare da danta Marzuwan. Badura da Marzuwan sun tashi tare tun suna yara kamar 'yan uwa, har suka girma suna tare http://facebook.com/waziriaku kowa yana nuna wa dan uwansa soyayya da kuma kauna irin ta 'yan uwantaka. Tun kafin Badura ta gama girma sosai, har manema aurenta sun fara kutso kai, Marzuwan ya bar garin tare da mahaifinsa zuwa fatauci. Kwatsam, ana cikin wannan hali sai ga shi sun dawo tare da mahaifin nasa. http:// facebook.com/waziriaku Suna sauka, ko hutawa bai yi ba ya tambayi mahaifiyarsa labarin 'yar uwarsa gimbiya Badura. Mahaifiyarsa ta yi jim, sa'annan cikin tausayi ta ce, "Wayyo, ai 'yar uwarka Badura ta http:// facebook.com/waziriaku kamu da ciwon hauka shekara uku da suka wuce. Yanzu haka tana cikin sarka a tsare cikin gidanta. Masu magani, da bokaye da masu bugun taurari, sun yi iyakacin kokarinsu amma sun kasa gano kan ciwonta." http://facebook.com/waziriaku Yayin da Marzuwan ya ji haka, sai fuskarsa ta canja zuwa launin toka, ya ce da mahaifiyarsa, "Ina so in gan ta, na ga halin da take ciki, mu yi zance da juna, watakila ta fada mani ciwon dake damun ta." http://facebook.com/waziriaku Mahaifiyarsa ta ce, "Ai an hana kowa shiga wurinta, amma ka jinkirta mini zuwa gobe, zan san dabarar da na yi na hada ka da ita." Ya ce, "Allah ya kai mu goben." Daga nan sai mahaifiyar Marzuwan ta tashi, ta nufi gidan da ake tsare da gimbiya http:// facebook.com/waziriaku Badura. Tana isa bakin kofar gidan, ta fito da wasu 'yan dirhamai ta mika wa bawan da ke kula da kofar shiga gidan, wanda yake baba ne. Nan take ya sa hannu ya kalmashe kudi yana godiya, yana dukar da kai don http://facebook.com/waziriaku girmamawa ga mahaifiyar Marzuwan bisa wannan kyauta da ta yi masa. Da ta ga bakinsa ya ki rufuwa don murna da wadannan dirhamai da ta ba shi, sai ta ce, "Da ma na zo ne in nemi wata bukata a wurinka." "Fadi bukatarki kowace iri ce, ya http:// facebook.com/waziriaku shugabata." In ji bawa. Mahaifiyar Marzuwan ta ce, "Ina da wata 'ya ce da ta yi aure, ita wannan 'ya tawa babbar aminiyar gimbiya Badura ce. Lokacin da ta ji halin da gimbiya ta shiga, shi ne ta zo wurina ta ce tana so ta zo ta http://facebook.com/ waziriaku duba aminiyar tata domin ta ga halin da take ciki. Ko za ka bar wannan 'ya tawa ta sadu da gimbiya Badura?" Yayin da bawa ya ji bukatarta, sai ya yi shiru zuwa wani lokaci. Can sai ya ce, "Zan yi miki wannan alfarma, ya shugabata. Amma ki bari sai gobe da dare, http://facebook.com/waziriaku bayan Sarki ya fito daga wurinta ya koma gidansa, sai ki zo da wannan 'ya taki, ta shiga ta ga gimbiya." Ta yi godiya ga bawa, ta koma gida. Wanshekare da dare ta yi wa danta Marzuwan shigar mata, ta riki hannunsa suka nufi gidan da ake tsare da Badura. Suna zuwa bawan nan ya shaidata, ya bude musu kofa. Ya yi musu jagora har zuwa dakin Badura, http://facebook.com/ waziriaku ya ce musu su wuce kai tsaye, amma kada su dade, ya juya ya koma kofar gida. Da suka shiga cikin dakin, suka ga Badura a daure cikin sarka, tun daga wuya har kafa. Marzuwan ya gaishe ta, bayan ya cire kayan mata da ke jikinsa. Ya fito da shama'a ya kunna, ya dauko wani littafi ya fara karantawa. http:// facebook.com/waziriaku Yana cikin karatun ne, sai hankalin Badura ya koma kansu, domin tun da suka shigo tana cikin tunani ne mai zurfi, don haka ba ta san da http:// facebook.com/waziriaku shigowar su ba. Tana ganin shi ta gane shi. Ta kada baki ta ce, "Ya dan uwana, ina ka shiga cikin duniyar nan har labarinka ya yanke daga gare ni?" Marzuwan ya ce, "Ya 'yar uwata, na tafi fatauci ne, ni da mahaifina, muka dade a can tsawon zamani. Ina dawowa na sami labarin http:// facebook.com/waziriaku halin da kike ciki na cuta, na ce ba zan koma ba face na zo na gan ki, na jarraba irin nawa maganin da na samo daga yawon fatauci, ko Allah ya sa warakar cutarki ta kasance ga hannuna." Da ta ji jawabinsa, sai ta dan yi murmushin karfin hali, ta ce, "Ya dan uwana, kai ma ka yarda da zancensu na cewa ciwon hauka ne ya kama ni?" http://facebook.com/waziriaku Marzuwan ya ce, "Na'am." Ta ce, "To, ba haka ba ne. Ni, ina da hankalina ras! Sai dai kamar yadda mai waka ke cewa: "Sun kira ni da hauka don so, To ina laifin hauka ga masoyi? Ku kira shi ya zo zan warke, Silar hauka a gare ni masoyi." http://facebook.com/waziriaku Ta ci gaba da cewa, "Idan har akwai cutar dake damu na, to ciwon so ne." Marzuwan ya ce, "Ki fada mini http:// facebook.com/waziriaku labarin abin da ya faru gare ki, watakila zan iya taimaka miki, in fitar da ke daga cikin wannan hali." *** Waziri Aku *** Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin zai fito nan ba da dadewa ba . Za mu ci gaba ranar Assabar gobe kenan insha Allah.(13) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHARUZZAMAN Marzuwan ya ce da Badura, "Ki fada mini labarin abin da ya faru gare ki, watakila http://fb.com/ waziriaku zan iya taimaka miki, in fitar da ke daga cikin wannan hali." Badura ta ce, "Ka sani, ya dan uwana, wata rana ina cikin barci da dare a cikin dakina, sai na farka na ga wani kyakkyawan saurayi kwance yana barci kusa gare ni. Ka ce shi tsumagiyar turare ne, ko kuma tsumagiyar Hindu, harshe ba zai iya kwatanta kyawunsa ba. Yayin da http:// fb.com/waziriaku na gan shi sai na zaci ko mahaifina ne ya turo shi domin ya jaraba ni a kan maganar da yake ta yi mini ta aure. Saboda wannan zaton, sai na ki tayar da shi daga barci, na kuma ki taba shi, don kada gari ya waye ya fada wa mahaifina abin da ya faru tsakaninmu. Na kwanta abina, na juya masa baya har http:// fb.com/waziriaku barci ya dauke ni. Yayin da na farka da safe sai na ga zobensa a dan yatsana, shi kuma ya cire nawa. Ya dan uwana, tun lokacin da na ga wannan saurayi zuciyata ta so shi, ban kara jin dadin barci ko abinci ba. Kullum son shi da begen shi sai karuwa suke yi a cikin raina, babu abin da nake yi face tunaninsa da kuma wakokin begensa, wannan shi ne sanadiyyar halin da nake ciki har mahaifina yake ganin kamar na http://fb.com/waziriaku haukace." Tana gama wannan magana tata, sai idanunta suka cika da hawaye, ta yi kuka, ta waka wadannan baitoci: "Zuciya takan narke don shi ya, Yaya zan yi in ji dadi ni babu shi? Begensa ya cikan dukkan zuciya, Dole idanuwa su zan ba sa barci. Shi ne jinin jiki wannan mai gudu, Yaya rayuwa takan zama in babu shi? Karfi ya tafi, haka kyawo ya gushe, A gare ni don yawan tunaninsa a zuci." Da ta gama wannan waka, sai ta ce, "Wannan shi ne abin da ya faru gare ni, ya http://fb.com/ waziriaku kai dan uwana." Da Marzuwan ya ji wannan labari nata, ya sunkuyar da kansa kasa na wani lokaci yana tunani. Zuwa wani lokaci ya dago da kansa ya ce, "Ni, na gasgata dukkan abin da kika fada mini. Hakika wannan al'amari naki abin al'ajabi ne, ya 'yar uwata. Da yardar http://fb.com/waziriaku Allah kuma na yi miki alkawari, idan na sake fita zuwa fatauci, zan yi iyakar kokarina na ga na samo miki wani abu wanda zai zama tamkar maganin da zai yi sanadiyyar warakarki daga wannan cuta ta bege. Amma yanzu ina horon ki da ki zama mai http:// fb.com/waziriaku hakuri ga wannan yanayi da kika tsinci kanki a ciki." Suka yi sallama da juna, ya tashi tare da mahaifiyarsa suka koma gida. http://fb.com/ waziriaku Bayan 'yan kwanaki kadan, Marzuwan ya yi shirin fita zuwa fatauci, a wannan karon shi kadai zai tafi ba tare da mahaifinsa ba. Bayan ya yi sallama da mahaifansa sai ya kama hanya ya tafi. Yana ta tafiya, ya shiga wannan birni ya fita, ya fada wancan tsibir, ya tsallaka wancan, yana saye yana sayarwa. Duk http://fb.com/waziriaku birnin da ya shiga kuwa, sai ya tsinci ana labarin haukan gimbiya Badura. Ya ci gaba da tafiya, ya yi nisa da kasar Sin da biranenta, har Allah ya kai shi wani birni mai suna Tayrab. http:// fb.com/waziriaku Ya yada zango a cikin wannan birni, ya taba ciniki. Yana cikin kasuwanci a wannan birni wata rana sai ya ji ana labarin wani dan Sarki da ya kamu da ciwon hauka. Da ya matsa kusa wurin masu zancen sai ya ji wai sunan dan Sarkin Kamaruzzaman dan Sarki Shahruzzaman. Ya tambayi birnin da wannan dan Sarki yake, aka shaida masa cewa birnin yana tsakiyar tsibiran http://fb.com/waziriaku Kalidan ne, kuma daga nan tafiyar wata daya ce a cikin jirgin ruwa, ko kuma wata shida a kasa. Da ya kara kwana biyu a wannan birni, sai ya shirya hajarsa, ya biya kudin jirgin ruwa wanda zai nufi tsibiran Kalidan. Da aka gama yi wa jirgi lodi, ya nausa da su cikin teku, iska ta yi http:// fb.com/waziriaku masa kyau. Bayan tafiyar wata daya, suka fara hango gine-ginen birnin Sarki Shahruzzaman. Suna gab da shiga kofar birnin sai wata mahaukaciyar iska ta taso tare da rakuman ruwa, suka kifar da jirgin, mutanen da ke ciki kowa ya yi ta kansa, babu wanda ya san halin da dan uwansa yake ciki. Shi kuwa Marzuwan da ya yi ninkaya ya gaji, sai ya yi sallama da rayuwa. Ya sha ruwa http://fb.com/ waziriaku cikinsa ya cika, idanunsa suka jujjuye, igiyar ruwa ta ja shi ta nufi karkashin gidan nan na kan dutse da shi, inda ake jiyyar Kamaruzzaman. Allah da ikonsa, wannan rana ta kasance http:// fb.com/waziriaku daya daga cikin ranakun da Sarki ba ya fita fada, yana nan tare da dansa, da kuma Wazirinsa a cikin dakin da Kamaruzzaman yake kwance. A daidai lokacin Kamaruzzaman na kwance, kansa na bisa cinyar Sarki, kwana biyu ke nan bai ci kome ba, ko ruwa ya kasa sha. Wani bawa yana tsaye da mahuci a bayansu yana yi musu fita, Waziri kuwa http://fb.com/waziriaku yana tsaye a bakin taga yana kallon ruwan teku, ya dunkule hannuwansa a baya. Can sai Waziri ya hango Marzuwan ruwa ya jawo shi ya nufo karkashin wannan gida da shi. Nan take tausayinsa ya kama Waziri, sai ya matsa kusa ga Sarki ya ce masa, "Ya http://fb.com/ waziriaku shugabana, ga wani bawan Allah can ruwa ya ciwo, ka yi mini izini in tafi in ceto shi idan yana da rai, watakila sanadiyyar ceton wannan mutum, Allah ya tausaya mana ya ba danka lafiya." http://fb.com/waziriaku Sarki ya ce da Waziri cikin fushi, "Kar ka cika ni da surutu ya kai karen Wazirai, ka sani duk wannan rashin lafiyar da dana yake ciki, kai ne sanadinta. Ka tafi ka ceci wannan mutum, amma ina shaida maka cewa, idan wannan mutum ya zo nan ya ga halin da dana yake ciki, kuma http://fb.com/waziriaku ya fita waje ya tsegunta wa waninsa, na rantse da Allah sai na sare kansa tare da kai." Waziri ya yi sauri ya fita waje, ya nufi inda ya hangi ruwa na tafiya da Marzuwan. Da ruwa suka zo da Marzuwan daidai wurin da Waziri ya tsaya, http://fb.com/waziriaku sai Waziri ya sa hannunsa ya kamo gashin kan Marzuwan ya fito da shi waje, ya kwantar da shi bisa yashi. Waziri ya dube shi da kyau ya ga yana numfashi sama- sama, ya durkusa a gabansa ya sa hannuwansa ya http://fb.com/waziriaku rika dannan cikin Marzuwan ruwa na fita ta bakinsa. Ba a dade ba, sai Marzuwan ya farfado, ya tashi zaune. Waziri ya sa ya cire kayansa da suka jike da ruwa, ya ba shi wata riga ya sanya, ya bashi wani rawani irin na fadawa ya nada a kansa. http://fb.com/ waziriaku Da Waziri ya ga hankalin Marzuwan ya dawo ga jikinsa, sai ya ce masa, "Tashi mu shiga cikin gida, amma fa ka sani cewa, Allah ya kubutar da kai daga halaka ta sanadiyyata, don haka ina rokonka kada ka zama sanadiyyar halakata." http://fb.com/waziriaku Marzuwan ya cika da mamaki, ya tambayi Waziri, "Ta yaya zan zama sanadiyyar halakarka?" http:// fb.com/waziriaku "Saboda yanzu za mu shiga cikin gida inda Sarki ke jiyyar dansa Kamaruzzaman." http://fb.com/ waziriaku Yayin da Marzuwan ya ji an ambaci Kamaruzzaman sai murna ta kashe shi, domin da ma shi ne wanda ya zo nema a wannan gari, amma bai bayyana farin cikinsa a fuska ba. "Wane ne kuma Kamaruzzaman?" Marzuwan ya tambayi Waziri. http://fb.com/waziriaku Waziri ya amsa masa, "Shi ne dan Sarki Shahruzzaman, yana nan kwance ba shi da lafiya, rai-kwakwai-mutu-kwakwai, an yi magani har an gaji amma kullum ciwonsa sai ci gaba yake yi har http://fb.com/waziriaku an hakura an zuba wa sarautar Allah ido. Na hore ka, idan muka shiga wurinsu kada ka yarda ka daga kanka, balle har ka kalli wannan dan Sarki. Idan kuwa ka kuskura ka kalle shi, to, Sarki zai sa a kashe ka, a kuma kashe ni." Marzuwan http://fb.com/waziriaku ya ce da Waziri, "Na gama ka da Allah ka fada mini ciwon da ke damun wannan dan Sarki." Waziri ya ce,"Mu ma ba mu san ciwon da ke damunsa ba. Iyakar abin da kowa ya sani shi ne, shekaru uku da suka wuce, mahaifinsa, Sarki Shahruzzaman ya yi, ya yi da shi a kan ya yi aure, amma ya http://fb.com/waziriaku buga kansa ga kasa, ya ki. Wannan ya fusata Sarki matuka ya nemi shawarata, na ce da shi a tsare shi a wani gidan gona, watakila bayan kwana biyu ya ji tsoro ya amince da bukatar Sarki. To, tun ranar farko da http://fb.com/waziriaku ya kwana a cikin wannan gidan gona, sai ya tashi da safe da maganar wata yarinya wadda ya ce wai ta kwana tare da shi a kan shimfida daya, har suka yi musayar zobe da ita. Muka ce masa mu, ba mu san da zancen ba, wasa-wasa sai abu ya zamar masa ciwo, Sarki kuwa ya dauki laifin duniyar nan na sanadiyyar http://fb.com/waziriaku rashin lafiyar dansa ya dora a kaina. Yanzu shekara uku ke nan, duk lokacin da yaron nan ya bude baki ba ya maganar kome sai ta wannan yarinya." http://fb.com/waziriaku Yayin da Marzuwan ya ji zancen Waziri, sai ya ce a cikin ransa, "Shakka babu, wannan dan Sarki shi ne wanda na zo nema, kuma shi ne wanda zai zama sanadiyyar warakar 'yar uwata gimbiya Badura." Ya tashi ya bi Waziri suka shiga cikin gida. Da suka isa cikin dakin sai Waziri ya sami wuri ya zauna, amma http://fb.com/waziriaku Marzuwan sai ya tafi kusa ga Kamaruzzaman ya kura masa ido. Yayin da Waziri ya ga haka sai ya kusa ya suma don tsoro, ya tabbata halakarsu ta zo. Ya harari Marzuwan, ya yi masa ishara da ido, wai don dai ya daina kallon Kamaruzzaman, amma a banza. Marzuwan ya ci gaba da kallon Kamaruzzaman, ya http://fb.com/waziriaku tabbatar a cikin ransa tabbas wannan shi ne wanda 'yar uwarsa take tsanin bege. * * * Waziri Aku * * * Wannan tsakure ne daga sabuwar fassarar labarun DARE DUBU DA DAYA, wanda littafin nanan akasuwa.(14) HIKAYAR KAMARUZZAMAN DAN SARKI SHAHRUZZAMAN Marzuwan ya ci gaba da kallon Kamaruzzaman, kamar bokan da ke nazarin wata sabuwar cuta a jikin mara lafiya, ya tabbatar a cikin ransa tabbas wannan shi ne wanda 'yar uwarsa take tsanin bege, wanda sanadiyyar begensa har ake tsammani ta zautu. Bayan wani dogon lokaci Marzuwan yana kallon Kamaruzzaman, sai ya daga murya ya ce, "Tsarki ya tabbata ga Allah wanda ya halicce shi kyakkyawar sura kamar yadda ya halicce ta kyakkyawar sura, fuskarsa kamar fuskarta, kundukukinsa tamkar kundukukinta." Ko da Kamaruzzaman ya ji wannan magana, sai ya bude idanunsa, ya karkata da kansa inda wannan magana ke fitowa. Yayin da Marzuwana ya ga haka sai ya waka wadannan baitoci: "Ga ka kana murna da fadata, Bayan da ka zan mai cuta. Kai ka karkata gun zancena, Wanda nake yi don kyawunta. Kai mai bege ne na gan ka, Ta jefe ka da kyan tsarinta. Kowa ya gane ka yakan ce, Wannan ta jefe shi da sonta. Don haka tashi ka ban gorona, Ga ni na zo maka labarinta. Gorona na zuma zan karba, Don jin dadin labarinta. Ita ce wannan kyakkyawa, Mai haske a saman fuskarta. Ga ta da haiba ga ta da zati, Kowa na begen muryarta. Ta fi dukan mata a wurina, Balle kai mai son tsarinta. Kasko na madaci ya kan zan, Zazzakar zumuwa don shan ta. Ku bar zunden sa da wauta, Ya fada tarko don son ta. Yatsun hannunsa na duba, Sai na ga yatsun tamkar nata. Idan har ta shafa musu lalle, Waye zai ce bai sha'awar ta. Ita ce ta

Chapter 4 of 14