Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
irin siffar jikinsa,ko wanka Darusi zaiyi saiya barsu a cikin kogon dutsen ya nausa can cikin dajin yayi tafiya mai nisa yaje cikin wata korama wacce ko kudi aka baiwa mutum akace ya shigeta ba zai yarda ya shiga ba saboda tana tsakiyar wadansu dogayen tsaunika ne guda bitu kuma wurin akwai duhu sosai.Kai da gani kasan cewa baza a rasa samun mugayen halittun cikin ruwa ba a wajen ko kuma mugayen bakaken aljanu,amma shi gogan naka kai tsaye yake shiga cikin koramar yayi wankansa hankalinsa a kwance dogaronsa kawai shine ALLAH.Kullum Jarumi Darusi ke fita daji ya farauto musu abincin da zasu ci wani lokacin saidai suga ya kaso gada ko barewa,wata rana kuma suga ya harbo katon tsuntus haka zaizo ya fige tsuntsun ya gasa shi sannan ya raba naman kaso hudu daidai ya baiwa kowa rabonsa,sau tari rabon nasa ma ko rabinsa baya cinyewa sai ya kara a kan na Sarila.A ranar kwana na bakwai ne da sassafe lokacin da Jarumi Darusi ya tafi farauta a daji domin ya samo musu abinda zasu ci sai Sarila taji karfin jikinta yazo har ma ta iya mikewa zaune,Yazirina da Mujahid kuwa kowannensu dama tun kwanaki biyu sukaji karayar dake jikinsu ta fara warkewa domin suna iya yin komai da kansu,Yazirina na iya dingisa karyayyar kafar tata shi kuma Mujahid na iya motsa hannunsa.Koda Mujahid Da Yazirina suka ga Sarila ta sami damar iya mikewa zaune da kanta sai suka kamu da tsananin mamaki,cikin murna Mujahid ya dubeta yace,tabbas Darusi dan baiwa ne gashi da karfin damtse na gaban kwantance,kuma gashi da ilmin likitanci,hakika yake Sarila baki da abinda zaki iya saka masa a cikin wannan duniya.Koda jin wannan batu sai Sarila tayi murmushin mugunta tace ai kuwa nice nake da abinda zan saka masa dashi.Ba da komai zan saka masa ba face BUTULCI kuma tukuicin taimakon da yayi mini shine na kashe shi a lokacin daya gama aikinsa ya kaimu Kogon Taskar Ajali.Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Mujahid yace ke Sarila waishin har yanzu kina nan akan wannan batu naki duk da ganin yadda Darusi ya ceci rayukanmu har sau biyu? Sa'adda Sarila taji wannan tambaya sai ta bushe da dariyar mugunta a karo na biyu tace niga ba'a raineni cikin samin menene halacci ba,basan wani abu waishi tausayi ba ko jin kai,abinda na sani kawai shine SARA da SUKAn sassan jikin bil'adama ko Aljan Wannan shine makarantata.Daukan rai kuwa shine babban darasin da nafi kwarewa a kansa.Babu abinda nake so a cikin duniya sama da kudi da mulki,Burina kawai shine na ga ina sarrafa komai da kowa a kan tafin hannuna kamar yadda ake sarrafa waina akan kaskon tukunya.Koda jin wannan batu sai Yazirina ta jinjina kai tace ai kuwa indai haka ne nima cin amanata zakiyi kuma ki yaudareni kaci amanata yayin da muka isa kogon taskar ajali.Sarila tayi dan guntun murmushi tace shin kin manta ne cewa na rantse da darajar iyayena bazan biki a kan wannan dukiya?Yazirina tace hmm ai wanda duk baigwa mutuncin iyayen wani ba to bazai ga nasa ba ma.Ta yaya zakiyi rantsuwa da iyayenki wadanda baki sansu ba,baki ma taba ganinsu ba kiyi zaton cewa zan yarda da rantsuwar taki?Aini kawai yanzu lokaci nake jira domin naga karshen tika tiki.Har Salira ta budi baki zata ce wani abu sai Mujahid ya tari numfashinta ya dubeta cikin alamun karayar zuciya gami da nadama yace ki gafarce ni yake Yazirina kiyi sani cewa nayi miki wani laifi guda daya.Koda jin haka sai Yazirina ta dubeshi cikin alamun matukar mamaki tace wane irin laifi kayi mini? Mujahid yace a baya nayi miki karya guda daya nace nine dan baiwar da zai kare ki daga dukkan abin cutarwa.To lallai bani bane wannan dan baiwar Jarumi Darusi ne tunda gashi har sau biyi ko ince sau uku rayuwarki na shiga cikin mugun hali amma na kasa tserar dake sai Darusi ne ya kubutar dake.Dajin haka sai Yazirina tayi murmushi tace aini ma naga Zahiri da idanuna kuma na gamsu cewa Jarumi Darusi ne dan baiwar da zai kubutar da rayuwar gaba dayan jama'ar dake wannan nahiya tamu bawai rayuwata ba ni kadai.Koda jin haka sai Sarila ta dakawa Yazirina tsawa tace kina nufin kenan zaki mika wuya a gareshi ki karbi addininsa?Kafin Yazirina tace wani abu saiga Jarumi Darusi ya shigo cikin kogon dutsen dauke da wata katuwar barewa a kafadarsa.Kawai sai ya dubesu yace ku gafarce ni yau na dan jima a cikin daji ban dawo da wuri ba gashi na barku a cikin yunwa.Caraf sai Mujahid yace haba yakai JARUMIN JARUMAI ai mune ya kamata mu nemi gafararka tunda mun barka da wahalar jinyarmu a cikin kogon dutse har tsawon kwanaki bakwai.Darusi yayi murmushi yace bari nayi sauri na gyara mana naman barewar nan muyi kalaci domin mu tashi mu kimtsa tunda yau ne ranar ci gaba da tafiyarmu kamar yadda muka tsara.Nan take Darusi ya fede barewar nan ya gyara komai a jikinta sannan ya hada wuta ya fara gasawa.Adaidai wannan lokaci ne ya dubi Sarila yayi mata sannu sannan yace ina tayaki murna bisa samun saukin jikin da kikayi a yau,gashi har kin iya tashi zaune.Maimakon Sarila ta dubeshi cikin fara'a tayi masa godiya sai kawai ta murtuke fuska kuma ta daka masa harara ta kau da kai ba tare da tace uffan ba.Al'amarin dayayi matukar bakantawa Mujahid Rai kenan yaji kamar ya tashi yaje ya rufe Sarila da duka domin ji yayi kamar shi ta wulakanta amma saiya basar,shi kuwa Darusi sai yayi murmushi kawai ya kau da kansa ya cigaba da aikin gashon barewar.A cikin abinda baifi sa'a guda ba su Jarumi Darusi sun kammala buda baki nan take suka harhada kayan su suka gama shiri tsaf aka dora Yazirina da Sarila akan dokin Darusi,Mujahid da Darusi kuwa sai suka wuce gaba a kasa.Darusi na ruke da linzamin dokin suka nausa cikin daji.Saida suka shafe kwana tara suna ratsawa ta cikin dazuzzuka su kwana nan su tashi can ba tare da sun hadu da wani mugun abu ba,duk tsawon wannan lokaci kome su Sarila suke bukata sai an tsaya anyi musu kuma duk tsawon tafiyar da za'ayi Darusi bai taba cewa ya gaji ba ko kuma yace a tsaya ayi wata Bukata.Komai wahalar abu kuma koda babu shi a kusa sai Darusi ya bazama yaje ya nemo,duk dawainiyar da Darusi ya saba yiwa Sarila bai fasa ba duk da cewa wani lokacin ma tana kyararsa tana yi masa wulakanci iri iri.A ranar kwana na tara ne suka yada zango a wani dogon daji mai yawan surkuki a wannan lokaci rana ta fadi magriba ta doso,kai kuma a sannan Sarila taji karfin jikinta sosai,da kanta ma ta sauko daga kan dokin kawai sai gani akayi ta zare takobi ta kama tsalle tsalle tana kaiwa iska SARA da SUKA wato ta rinka baiwa kanta horon yaki.Nanfa Mujahid da Yazirina suka kura mata idanu cikin matukar mamaki,shi kuwa Darusi sai ya sauke jakar guzurinsa daga bayansa ya fiddo tanti ya fara aikin kafashi.Cikin sauri Mujahid yazo ya taya Darusi aikin inda ya dubeshi yace yakai Abokina menene dalilin da yasa ka yanke hukuncin mu yada zango anan?Koda jin wannan tambaya sai Darusi yayi ajiyar zuciya kuma ya bude baki cikin karamar murya yadda su Yazirina ba zasuji maganarsu ba yace dajin dake gabanmu kadan mugun daji ne,akwai wata babbar runduna ta yanfashi a cikinsa,kuma sun dana mana mugayen tarkuna na kama mutane yadda komai yawan AYARI basu isa su iya tsallakewa ba.Adadin yan fashin yakai DUBU ARBA'IN kuma zakwakuran mayaka ne na kwatance,idan muka kuskura muka shiga cikin sansaninsu da wannan duhu zasu iya cutar damu. TASKAR AJALI Littafi Na Shida (6) Part B Zasu iya cutar damu.Saukin tama nasan duk irin tarkunan da suke danawa kuma nasan sirrin dajin.Kada ka gayawa su Sarila wannan batu saboda nafi son sai tura takai bango sun gane muhimmancina da amfani na da kuma gaskiyata.Sarila tafi kowa kina a cikinku kuma nasan idan har na kaiku har can kogon Taskar Ajali sai tayi yunkurin kashe ni.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Mujahid yace ya akayi kasan wannan al'amari?Tabbas abinda ka fada shine a cikin zuciyar Sarila har ma furuci tayi akan zata aikata hakan.Darusi yace ubangijina ya kan sanar dani abubuwa da dama a cikin mafarkina walau na tsiya kona arziki,hatta fafatawar da nayi da sarki Damnash a can kofar kogon dutsen nan saida aka nuna mini duk abinda zai faru amma saboda nayi imani da ubangijin nawa dari bisa dari ban fasa yin komai ba kuma hatta mutuwa bana tsoronta akan wannan tafarki da nake kai bare wani bil'adama tunda na san cewa akan gaskiya nake.Ka daina damuwa akan duk irin wulakancin da Sarila zatayi mini gami da wulakanta ni,ina mai tabbatar maka da cewa sai tayi nadamar duk abubuwan da takeyi mini a anan gaba kuma akwai wani babban dalili da yasa kome zatayi mini bazan damu ba.Koda jin haka sai mamaki ya sake turnuke Mujahid yace menene wannan babban dalili kuwa?Darusi yace kayi hakuri zaka ga komai da idanunka,ka sani cewa da zarar mun gama da rundunar yan fashin dake gabanmu tafiyar sa'a kacal zamuyi mu riski wani babban gari waishi Birnin Zamras.Koda jin wannan batu sai Mujahid ya kamu da tsananin mamaki ya ka ya dubi Darusi cikin alamun kaduwa da rashin yarda yace ai kuwa yadda na sami labarin shine daga can birninmu zuwa wannan birni da kake fada tafiya ce ta a kallah kwanaki casa'in,ta yaya zaka ce muna daf da riska alhalin gaba daya yau kwananmu goma sha shida kacal da baro gida?Sa'adda Jarumi Darusi yaji wannan batu sai yayi murmushi yace ai abinda baka sani ba shine ina rokon ubangijina ne yana gajarce mana tafiyar wata uku a cikin sati biyu saboda haka da izinin ubangijin nawa inasa ran cewa zamu isa kogon Taskar Ajali a cikin sati shida maimakon watanni bakwai zuwa tara.Kada ka gayawa su Sarila wannan sirri,wannan amana ce a tsakaninmu.Koda jin wannan batu sai Mujahid ya gyada kai yace lallai kuwa zaka sameni mai ruke amanarka.Bayan su Jarumi Darusi sun gama kafa tantin sai suka yiwa Sarila da Yazirina shimfidarsu a ciki su kuma suka fito wajen tantin suka kunna wuta suka zauna suna jin dumi suna hira amma sai bayan Darusi ya gabatar da sallarsa ta magriba.Yazirina da Sarila kuwa kowaccensu na zaune akan shimfidarta tana cin ragowar gasasshen naman barewar da sukayi guzuri.A wannan lokaci ne Yazirina ta dubi Sarila tace nifa Gaskiya sanyi nakeji sosai saboda haka waje zan fita na zauna tare dasu Mujahid nasha dumin wutar da suka kunna.Koda jin hakan sai Sarila ta murtuke fuskarta tace indai sanyi kikeji ai ba sai kinji dumin wuta ba a waje zaki yi maganinsa,kawai ki kwanta ki lulluba da bargonki mana,kedai kawai kice kina son kije kiyi ta kallon fuskar Mujahid.Yazirina tayi murmushi tace amma dai bakiyi mini adalci ba idan kika fadi haka tunda nidai banga wani kuskure ba don zuciyar wani ta kamu da AZABAR SOn wani.To waishin ma me yasa kikeyin kishi dani akan Mujahid?Amsar itace kema kin kamu da sonsa kuma hujjata itace kin samu damar kashe shi a baya har sau biyu amma sai kika ki kashe shi a lokacin da kike nemana ruwa a jallo domin ki kashe ni ki rabani da Taswirar dake hannuna.Caraf sai Sarila ta tari numfashin Yazirina tace ke mu ajiye batun soyayya yanzu saboda ita soyayya bata samun kafuwa sosai face ana cikin nishadi da kwanciyar hankali,ki tashi kije kiyi duk abinda kikeson yi daga yau bazan sake sa miki ido ba.Koda gama fadin hakan sai Sarila ta kwanta akan shimfidarta taja bargonta ta lullube jikinta.Koda ganin haka sai jikin Yazirina yayi sanyi ta kasa mikewa ta fita waje don haka itama saita kwanta taja bargo.Kashe gari da sassafe suka tashi duk su hudun sukayi shiri suka nausa cikin daji.Ana fara yin tafiyar ne Mujahid ya tsaya daf da Darusi suka rinka tafiya kafada bai yarda ya gusa daga kusa dashi ba.Koda ganin haka sai Sarila ta dubi Yazirina wacce ke gabanta akan doki guda da suke zaune tare tayi mata rada a kunne tace yake yar uwata ina mai tabbatar miki da cewa lallai akwai wani mugun abu a kan wannan hanya da muka biyo amma Mujahid yasan da hakan bai sanar damu ba.Cikin mamaki Yazirina tace yaya akayi kika san da hakan ko kuwa a cikin madubin tsafinki kika gani?Sarila ta numfasa tace ai tun daga ranar danayi gumurzu da Jarumi Darusi sai komai na tsafina yayi rauni,shin baki lura da yadda Mujahid ya kasance ba ne tunda muka baro kogon duntsen nan ba?Ko yaushe yana daf da Jarumi Darusi yaki yarda ya nisanta dashi,duk yadda akayi ya gaya masa sirrin dajin da muka dosa.Abinda na fuskanta shine zuciyar Mujahid ta fara karkata izuwa yin imani da addinin Darusi shima Darusi ya fahimci haka shi yasa yake kokarin kula dashi gami da bashi kariya,mu kuwa ya barmu da halinmu da dabarmu da kuma abin dogaranmu.Koda jin wannan batu sai hankalin Yazirina ya DUGUNZUMA ainun domin ta fahimci cewa babu wanda yasan irin iyakar wahalar da zasu sha a cikin wannan tafiya,abinda zai hanasu shan wuyar kuwa abu daya ne kuma ba komai bane face karbar addinin Jarumi Darusi.Ita dai Yazirina zuciyarta rawa takeyi kan hakan a duk sa'adda ta tuno da irin wahalar da mahaifinta yasha kafin ya hada wannan sihiri na taskar ajali da yadda ya shafe shekaru masu yawa yana tara dukiyar sai taga cewa lallai ba zata iya hakura ba da mallakarta don cika burin mahaifin nata,a can wani bangaren daban na zuciyarta ta kuwa ta fara gamsuwa da cewar addinin Darusi shine ADDININ GASKIYA tunda gashi yayi abubuwan al'ajabin da babu wani jarumi ko matsafi daya taba yin kamarsu,abu na uku data barshi a can karkashin ranta shine duk yadda zata yi saita tabbatar da cewar ita kadaice zata mori wannan dukiya ta mahaifinta saboda tafi kowa cancanta da hakan.Duk lokacin data kalli fuskar Sarila sai taga kamar bakin kumurcin maciji ta kalla mai shirin kawo karshen rayuwarta.Koda aka kara nutsuwa cikin wannan daji sai Sarila da Yazirina suka dora hannayensu akan kufen takubbansu kuma suka rinka kallon samansu da kasansu da kuma gaba da bayansu.Koda ganin haka sai Darusi ya dubi Mujahid a fusace cikin karamar murya yace shin ka baiyana sirrin wannan daji ne gasu Sarila?Mujahid ya gyada kai da sauri yace na rantse da girman iyayena ban gaya musu komai ba saidai kawai idan jikinsu ne ya basu ko kuma suna zargi.Darusi ya jinjina kai yace tabbas jikinsu ne ya basu cewar munzo waje mai hadari,abinda nakeso dakai shine lallai ka cigaba da nanikata karka bari a sami nazara a tsakaninmu da kai wacce takai taku uku.Koda jin haka sai Mujahid ya gyada kai yace zan lura da hakan.tafiyar rabin sa'a na cika sai gasu Jarumi Darusi sun iso wani katon fili mai tsananin tsawo da fadin gaske wanda za'a iya kiransa da suna 'KARE GUDUNKA.Babu ko bishiya guda daya a wajen kuma babu wani katon dutse ko tsauni sai kananan duwatsun wuta wadanda aka shimfidasu a kas tamkar dama ado akayi dasu a wajen,iya hangen mutum bazai gano karshen wannan daji ba.Kwatsam sai su Jarumi Darusi sukaga wadansu gungun yan fashi suna fitowa ta gabas da yamma,kudu da arewa su da yawa ba adadi tamkar gaba dayan mutanen duniyar ne suka fito.Su dai wadannan yan fashi sun kasance arnan daji,babu komai a jikinsu face walkin fata,kafafuwansu babu takalmi amma kowannensu na dauke da mugayen MAKAMAN YAKI a jikinsa irin wanda idanu basu saba gani ba,sun kasance girda girda wato manya manya,ga tsawo kuma ga kauri kuma duk jikinsu a murde yake cike da kwanji da tarin jijiyoyi,kai da ganinsu kasan cewa lallai sun sami horon yaki.Kafin cikar wadansu dakiku tuni wadannan Arnan Daji sun yiwa su Jarumi Darusi KAWANYA.Koda ganin wadannan yan fashi sai Yazirina da Mujahid suka firgita ainun ita kuwa Sarila ko gezau batayi ba,Jarumi Darusi kuwa sai ya cigaba da tafiya abinsa ya durfafi cikin yanfashin ba tare da shakkar komai ba.Mujahid na biye dashi daf da daf,koda ya iso daf da yanfashin sai suka dare suka basu hanya ba tare da dayansu yayi wani yunkuri ba na kawo musu hari.Koda ganin haka sai Yazirina ta tsikari bayan Sarila tacemaza mana kibi bayansu Darusi domin mu sami albarkacinsa kada su yakemu.Koda jin haka sai Sarila ta waigo ta dakawa Yazirina harara tace da ita ai idan muka bishi a baya da sauri mun muna cewa munyi imani da addininsa kenan kuma mun tsorata.Kada yawan wadannan arnan daji su tsoratar dake shin kin manta ne da irin tsananin jarumtaka ta da kuma karfin sihirin tsafina?Ai wadannan ba komai bane zan iya dasu.Cikin tsananin fishi Yazirina ta daga murya tace ina jarumtakar taki da karfin tsafinki a lokacin da mukayi gumurzu da Aljana Marwisa?Me yasa kika kasa kwatar kanki a hannunta?Inbadon Jarumi Darusi ba da tuni kin dade da shekawa Barzahu,kiyi sani cewa ni nasan Darusi bazai bari a kashe mu ba anan amma abinda banso shine wahala,ki tuna da yarjejeniyar da mukayi a baya ta yan kwanaki mun sha wahala sosai shin yanzu ma so kike musha wata wahalar?Adaidai wannan lokaci ne Darusi da Mujahid suka gama ficewa daga cikin arnan dajin ya zamana cewa banda kallon kallo babu abinda ya wakana tsakaninsu.Koda Mujahid da Darusi suka koma gefe daya sai suka tsaya cak suka zuba idanu suga yadda su Sarila zasu zo su wuce ta tsakiyar yanfashin kamar yadda suma suka wuce.Nanfa Sarila da Yazirina sukaga wani abin mamaki domin shugaban yan fashin ne yazo gaban Jarumi Darusi ya risina ya kwash gaisuwa sannan sukayi maganganu,suna gama tattaunawa sai shugaban yanfashin ya dawo cikin yan uwansa sannan ya fuskanci su Sarila wadanda ke bisa doki a lokacin da sauran yaran nasa suka toshe hanyar dasu Mujahid suka ratsa suka wuce kawai sai Sarila ta dubi Yazirina tace baki da wani zabi wanda yafi ki tayani yakar wadannan yan fashi domin mu kutsa ta cikinsuda karfin tsiya mu isa inda su Darusi ke tsaye,ina mai tabbatar miki da cewa ba zamu iya karar da wadannan mutane ba don haka kawai mu tsayar da hankalinmu wajen kutsawa ta tsakiyar su da karfin tsiya har mu wuce.Koda gama fadin hakan sai Sarila ta zare takobinta ta kwarara uban ihu,hatta shugaban yanfashin wanda babu kamarsa a girma,kwarjini da kirar sadauki saida hantar cikinsa ta kada sakamakon jin wannan mugun ihu na Sarila.Itama Yazirina saita zare tata takobin a lokacin da Sarila ta sakarwa dokin linzami ta nufi tsakiyar yan fashin.Ai kuwa sai shugaban yanfashin da dukanin yaran nasa suka rugo da gudu izuwa kansu kai kace beraye ne guda biyu aka ajiye a gaban miliyoyin maguna.Bama Sarila da Yazirina ba hatta dokin nasu idan wadannan yanfashi suka dasa masa wawa fiye da kaso tara cikin gomansu ba zasu sami koda tsoka guda ba.Koda ya rage saura baifi taku biyar ba ayi mugun gamo tsakanin yanfashin dasu Sarila sai shugaban yan fashin ya dako tsalle sama yana ruke da wano dogon mashi ya kawowa Sarila suka a kirji.Cikin bakin zafin nama Sarila ta kade mashin da takobin hannunta ita ma ta daka tsalle sama daga kan dokin ta doki kirjin shugaban yanfashin da kafarta gudaDa kafarta guda yayi baya taga taga har taku uku ya tsaya kyam!A lokacin da Sarila tayi wata irin fanka a sama tamkar an murza katantanwa ta tare hare haren da dakarunsa suke kawo mata na sara da suka kuma ta maida martani.Ita ma Yazirina dake zaune a bayan dokin haka ta shiga kare hare haren yanfashin tana maida martani.Nanfa wuri ya yamutse aka ruguntsume da masifaffen yaki,hatta jarumi Darusi sunyi matukar burge su bisa jarumtakar da suka nuna yanzu domin basu taba zaton cewa zasu iyayin hakan ba amma inda tambayar take shine zasu jure wannan bakin artabun har zuwa wani dogon lokaci kuwa?Abin fatan shine Allah yasa kada suy karkon kifi.Ana fara wannan gumurzu sai Sarila ta rinka kutsawa ta cikin Arnan dajin da dokin nasu da karfin tsiya ta banke su suna karawa gaba saidai kaga maza na zubewa kasa tamkar ana sassabe a gona,amma abin haushin kuma abin tashin hankali shine sara da sukan da Sarila da Yazirina ke yiwa arnan dajin baya tasiri a jikinsu.Duk sa'adda takubbansu ya hadu da jikin arnan dajin saidai kaji kara na tashi tamkar haduwar karfe da karfe fa zarar sun banke yanfashin da doki koda karfin naushi sun zube kasa sai su ga sun mike tsaye zumbur sun cigaba da artabun ba tare da alamar sun jigata ba.Da zarar dokinsu Sarila yakai tsakiyar yanfashin sai kuma akaga an dawo dashi baya can farko da karfin tsiya,saida akayi haka har sau uku ba tare da sun sami nasarar koda kashe mutum daya ba jal daga cikin yanfashin kuma suma yanfashin ko lakutar jikinsu dayansu basu samu ba.Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalin Sarila da Yazirina kenan saboda sun san cewa jiki da jini sai a hankali.Dole ne su gaji idan aka cigaba da wannan gumurzu ahaka izuwa tsawon lokaci,shi kuwa shugaban yanfashin koda ya cewa wankin hula zai kaisu dare sai ya fusata ainun ya shammaci Sarila ya soke dokin nasu da mashin hannunsa a ciki take dokin yayi tutsu dasu yana haniniya suka rikito kasa daga kansa a lokacin da dokin ya baje kasa matacce.Maimako n Sarila da Yazirina su karaya sai suka kara kaimi suka cigaba da yaki maimakon su cigaba dakai Sara da Suka sai suka fara kai NAUSHI da BUGU.Gashi dai yanfashin suna jin naushin suna faduwa kasa amma sai kaga suna mikewa tsaye zumbur suna cigaba da gumurzun.Koda aka shafe rabin sa'a ana wannan artabun sai labari yasha bamban domin a sannan ne Sarila da Yazirina suka dan fara gajiya har yanfashin suka fara samun damar gabzar musu naushi a fuskokinsu da sassan jikinsu.Nan da nan kuwa aka fara hada musu JINI da MAJINA amma saboda bakin naci gami da tsananin juriya irin ta JARUMAN KWARAI sai kuma suka cigaba da maida martani.Babu yadda Sarila da Yazirina basuyi akan su kutsa ta cikin yanfashin da karfin tsiya su fice amma sai suka kasa,abin ma daya daure musu kai shine lokaci guda yanfashin suka daina kai musu hari da makamansu sai naushi da bugu da hannu da kafa,aikuwa koda aka sake shafe wata rabin sa'ar sai Sarila da Yazirina suka jigata ainun saboda sarkin yawa yafi sarkin karfi ya zamana cewa basa iya kai hari sai kare kai.Sannau a hankalo kare kan ma ya gagaresu,a sannan ne fa akayi musu laga laga da tsabar naushi da bugu suka zube kasa wanwar jini na yoyo ta cikin hancinsu da bakinsu kuma suna numfashi sama sama kamar ransu zai fita.Bisa mamaki sai sukaga yanfashin sunki kashe su sun ja da baya cikin yi musu KAWANYA kuma sun bude hanya saiga Jarumi Darusi da Mujahid tare da shugaban yanfashin kafada da kafada sun taho gare su,wasu yaran yaran yanfashin na janye da dawakai guda hudu.Koda suka zo daf dasu sai Darusi ya dubi Sarila cikin murmushi yace ga dawakai nan ku tashi ku hau mu cigaba da tafiya domin isa birnin Zamras.Koda jin wannan batu sai Sarila ta yunkura cikin matukar karfin hali ta mike tsaye sannan ta baiwa Yazirina hannunta ta kama ta tashi tsayen.Sarila da dubi Darusi cikin alamun tsananin fishi da kiyayya tace ya zaka raina mana hankalinmu,zuwa birnin Zamras tafiya ce ta kwana casa'in daidai?Kuma me yasa ka barmu muka sha wannan bakar wahala haka alhalin kana da ikon wucewa damu lafiya.Koda jin tambaya sai jarumi Darusi yayi murmushi yace dama so nake kiyi mini wannan tambaya da bakinki saboda komai da lokacinsa.Tabba s daga birnin Zamras tafiyar sa'a daya ce kacal abinda yasa na barku kuka sha wannan wahala a hannun wadannan yanfashi shine har yanzu bakuyi imani da ubangijina ba amma ko yanzu kuka karbi addinina ba zaku kara fuskantar wata matsala ba da izininsa.Idan kuwa kuka karbi addinin nawa har sai mun isa kogon taskar ajali kamar yadda kukayi alkawari to duk masifar da muka hadu da ita zan barku da ita ne in yaso karfinku da tsafinku ya ceceku,bazan taba taimakonku ba face naga zaku hallaka muraran kamar yadda nayi alkawari da farko.Koda gama fadin hakan sai Jarumi Darusi ya juya ya karbi doki guda daga dawakan hudu ya haye shima Mujahid sai yayi sauri ya karbi guda ba tare da yin wata gardama ba sai Sarila da Yazirina ma suka karbi dawakan suka hau,faruwar hakan keda wuya sai shugaban yanfashin yazo gaban jarumi Darusi ya sake risina a karo na biyu cikin girmamawa yace ya batun alkawarin da kayi mana cewa zaka koyar damu yadda ake bautar Allah a cikin wannan addini naka mai daraja.Ka sani cewa tuni a halin yanzu mun daina fashi kuma duk abubuwan da kuka umarcemu munayi bamu ajiye daya ba.Koda jin haka sai farin ciki ya lullube jarumi Darusi yace da zarar na dawo daga kogon Taskar Ajali zanzo na cika wannan alkawari a gareku,yanzu abokan tafiyata da suka jarraba jarumtakarsu a akan taku sun jigata ainun kuma kun san irin- bala'in dake cikin birnin Zamras don haka ba zamu iya shiga dasu a haka ba,saboda haka ina neman alfarma na shiga dasu cikin birninku domin a sami likitan da zai duba lafiyarsu kuma ya basu maganin da zasuji karfin jikinsu.Koda jin haka sai farin ciki ya turnuke shugaban yanfashin tare da sauran gaba dayan jama'arsa,ya dubi Jarumi Darusi yace munfi kowa murna da karbarka a matsayin bakonmu idan da hali ma muna neman alfarmar kuyi kwana uku a cikin birninmu kafin ku wuce izuwa birnin Zamras.Darusi yayi murmushi tace zan duba na gani idan da halin yiyuwar hakan sai ayi.Nan take shugaban yanfashin tare da sauran jama'arsa suka yiwa su jarumi Darusi jagora suka nufi birnin nasu yar guntuwar tafiya sukayi ta cikin wata duhuwa suka hango bukkokin birnin na arnan daji masu tsananin yawan da mutum zai iya shafe kwana biyu yana kirga su ba tare da ya gama ba.Tun daga nesa su Sarila suka jiyo bugun tambura na tashi anayi musu lale marhaban,ashe tuni labari ya riske mutanen garin cewa ga jarumi Darusi can ya dawo.Kafin su isa kofar garin kuwa gaba dayan mutanen birnin mazansu da matansu,yara da manya sun fito sun jeru a kofar birnin sunyi sahu sahu suna ta shewa da farin ciki dauke da kyaututtuka iri iri,al'amarin da yayi matukar daurewa Mujahid,Sarila da Yazirina kai kenan suka cika da tsananin mamakin dalilin da yasa gaba dayan mutanen wannan birni suke matukar kaunar jarumi Darusi haka kuma suke girmamashi gami da murnar ganinsa.Nanfa maza da matan suka tashi rike da kyaututtukan saboda yawansu.Gaba daya matan wannan gari suna sanye ne a cikin suturar data rufe jikinsu tsaf kuma da yawansu sun kasance KYAWAWAn gaske ababan kwatance.Duk da irin tsananin kyau irin na Sarila da Yazirina saida kyawun matan arnan dajin ya burge su saboda yanayin kalar jikinsu wankan tarwada ne kuma fatarsu tana sheki sosai kuma ga laushi,sun kasance dogaye masu madaidaicin kaurin jiki,suna da kira mai kyau irin wacce kowane 'da namiji ke dimaucewa idan ya gani,sannan gashin kansu dogo ne ya zuba har kasan mazaunansu ga tsananin baki da kyalli tamkar madubi.Kai tsaye Sarkin Arnan dajin ya wuce dasu jarumi Darusi izuwa gidansa.A gaba dayan birnin babu wani gida da aka kera shi yayi kyau kamar na sarkin domin shi da tubali akayi shi kuma yana da girma sosai,a tsakiyar birnin yake kusa da tsohon dakin bautarsu amma a halin yanzu ma an rushe dakin bautar tun a ranar da jarumi Darusi yazo birnin.Cikin wani katon daki aka shigo da Jarumi Darusi tare da Miujahid,Sarila da Yazirina kuwa sai aka shigar dasu can cikin gidan wajen matan sarki aka kaisu wata babbar turaka wacce ta kawatu ainun aka kwantar dasu aka shimfide,saida wata likita tazo ta duba su ta basu wani magani suka sha sannan suka ji jikinsu ya daina tsami tamkar basu sha lugudan duka ba.Take sukaji kwarin jikinsu.Nan take aka kawo musu abinci da abin sha suka ci sukayi hani'an sannan aka nuna musu kewaye sukaje sukayi wanka suna fitowa daga wanka sai kuyangi suka shafe musu jikinsu da wani irin mai mai kamshi da taushi sannan aka kawo suturu irin na mutanen garin aka basu suka sanya.Acan turakar da aka sauke jarumi Darusi da Mujahid kuwa ana kaisu sai aka barsu su biyu jal!A cikin dakin har izuwa tsawon dan lokaci tamkar an manta dasu daba daya.Kwatsam!Sa i ga wata santalelitar kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance wacce a gaba daya matan dake garin babu mai kyanta ta shigo cikin dakin dauke da farantin abinci.Fuskarta cike take da annuri tanayin murmushin farin ciki tamkar wacce aka yiwa bushara an bata duniyar gaba daya.Koda Mujahid yayi arba da wannan kyakkyawar budurwa saiya dimauce ya fita daga haiyacinsa ya aiyana a ransa yace ina ma ace Yazirina ce wannan kyakyawar budurwa da nafi kowa dacewa

Chapter 9 of 14